Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

scientist su gunadar mishi da Test Dina, Nan suka shiga Aikisu ba Kama kafa yaro.. Baya AWA Daya results ya fito. Ba na kan Aliyu yake ba Dake duk suna san condition dinshi akan Baya Haihuwa.. ya duba nasa Isa da na Idress duk Basu Matching ba, cikin ranshi yace" kodai kamani ne kawai da gaske?" Wani Zuciya yace ya duba results din Aliyu Yana dubawa sanda yayi Suma tsaye yayi gani abunda idonshi ya gani.. kasa gasgata wa yayi sanda yasake wani test din har Sau uku duk abun Daya ya ke nuna Mai.. cike da rudewa da Mamaki ya shirya duka results cikin Jakarshi ya fito cikin saurin ya tada Motar shi Sai gida Tycoon..

Yana shigowa duk aka mimike..

Kankare murya yayi yayi Jim kadan dun Bai ma San ta Ina zai fara ba.. can dai ya Mika ma Tycoon file din dake dauke da results yace" Idress da Isa ...."

Isa da Idress zuru zuru sukayi hankali su a tashe suna jira suji Mai zai ce

"Ba Dansu bane..."

Wani naunaya ajiya Zuciya duk Suka sauke

"Ama Aliyu.." ya daga Kai yana kallon Tycoon

" I'm so sorry Yallabai 99.9 percentage na gwajin da muka duba Wana yaro na Aliyu ne"

Nan kaji wancan ya yayi tsit, shiru kakeji ba sauti dada kakeji Sai bugun Zuciyoyisu...


Tycoon yay ta maza ya bude results Yana kallon yaga tabbas haka ne zubewa yayi kan kujera..

Mami Kuka tasa Tace Sam bazai yuba Sai da asake gwadawa....

"Hajiya har Sau uku Ina duba Abu daya yake nunawa, ama dai zaku iya tura zuwa wani Asibiti a Kara dubawa.."

Tycoon idonshi ya kada ya daga musu Muryashi na Rawa yace" Doctor Aminu na tare da mu tun ba yau na tabata bazai Mana karya ba, Ama taya ya haka ya faru, With his condition" zubur ya mike ya dauko waya...





🤸🤸🤸🤸🤸🤸🤸🤸


👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
*DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️



*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️


*M.W.A*


_Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
____________________________




6️⃣8️⃣


Tycoon jiki na Bari cike da tashi hankali ya ciro wayarshi a aljihu shi ya bude ya dialing number Aliyu, buga daya Aliyu yayi picking, ya Soma gaidashi cike da girmamawa.

Tycoon bai amsa ciki baci rai yace" Aliyu kana ina ne?

Aliyu yaji tambaya a bazata yace" Daddy ina India mana na fadama ko ka Manta ne? Lafiya dai ko naji murya ka haka?


Tycoon tambaya ba murya na rawa yace" inasa gani ka, na baka na da three hours Aliyu ka dawo gida"

Aliyu ciki rudewa yanayi da daddy nashi yake sounding yace" Daddy laf......

Tycoon ya katse shi a tsawace yace" bana san ji wani tambaya daga baki ka I said just come back home"

Ya kashe waya kit, jikishi na karkawa yayi Kama zai fadi da sauri Ammi dake gefeshi ta tareshi ya zauna Yana kada Kai cike da damuwa....


Duk parlour akarasa Mai baki magana Dan duk a razane suke Aliyu ne da Dan Kai abun da mamaki yake..


Tycoon ya daga Kai ya kalli Sadik da duk ya tsorata da gani canzawa shi lokaci daya ya ka kula murmushi yace" come"

Yaki zuwa ya makale ma Isa a jiki Nan ya Soma kuka Wai zai su koma dashi guri mummyshi, lalashi duniya ama Sadik yakiyi shiru, da suka tambayi a ina mummy nashi take, ko amsa su baiyi ba ya cigaba da kukashi...




*************************

Aliyu naji Daddyshi ya kashe kira ya Soma bin waya da kallo, ya soma tambaya kanshi" mai yasamin Daddy? Ko dai workers nasu ne suke rikici basuyi aiki da ya kamata ba?
Ya ma kanshi tambaya da babu amsa, ya tabe baki ya Mike ya tada suhaima dake ta shara bacci a gefeshi, ya sanar Mata zan su koma Nigeria yanzu na. Suhaima ta Mike tana Bata fuska Tace" haba darling shekaran jiya fa mukanzo kace zamun koma da gagawa haka, ka Manta ne haryanzu fa baka Gama amsa medication naka ba"

Yace" Daddy ne yace mundawo Kuma yaban na da three hours yanason gani na"


Suhaima ta Kara Bata fuska tace" shin Daddy baisan baka da lafiya ba ne da zai ce ya baka na Dan three hours ka dawo, muna India ne fa ba gida nijeria ba"


Aliyu bai amsaba ya fara hada kayashi, ya fada toilet sauri yayi wanka ya fito, Yana fitowa Kira Daddy na sake shigowa, Suhaima ta amsa, Tycoon naji muryata ya katse Kira Yana ja tsaki..

Suhaima ta daga Kai ta kalli Aliyu tace" Wai Mai ke faruwa ne?

Aliyu yace" Nima bansani ba, ta shi kawai ki shirya muje Kar yayi fushi"

Suhaima ta Mike tana ja tsaki ko wanka batayi ba ta bude jaka da Aliyu ya shirya musu Kaya ta fito da gown yellow ta shirya tsaf, ta tsaya kallo Aliyu da ke daura igiya sneakers nashi fari, yayi kyau sanye yake da hoodie blue, ya hada da white jeans trouser. sai binshi kawai take da kallo tana murna a zuciya ta Aliyu ya zama nata har abada..

Yana Gama Shiri ya Mike ya kwashi wayoyisa yace" let's go"

Tayi gaba Yana binye da ita janye da trolley nasu har suka isa reception ya ma Yar ma ma'aikata hotel din keys ya fito, securities sukayi kanshi sa sauri suka karbi trolley da ke hannu shi...

Ya shiga motar suhaima ta zauna a gefeshi tana kumbere kumbere bai kulata ya kalli driver yace" Airports za muje gida zamukoma"

Driver din dayake Dan India ne harda kukashi yace" yallabai zanyi kewarka naji dadi aiki da kai"

Aliyu Yana murmushi ya tabbing shoulder nashi yace" Kar ka damu we will meet next time, let's go and drive fast"

Duk aka tada motoci ciki minti kalila suka isa Airports, Aliyu dakashi yaje ya yanka musu tickets din flight zuwa Nigeria, suyi Sa'a kuwa akwai Mai tafiya, ciki one minute suka Gama shirya komai, suna shiga jirgi ya daga ya Lula zuwa Nigeria. .. ..




*************************

Walid nagama sanya coins ya sauko ya nufi table da suka zauna yaga wayam ba Sadik ba Amir, yayi murmushi yace" bro Amir da San yawo ina suka je Kuma?

Bai Gama rufe baki ba sai ga Amir shima ya sauko yace" Bro harka ka dawo, ina boy yake" ya fada Yana waige waige ko zai ga Sadik..

Walid yace" a'a bro tare fa na barku na Kai zan tambaya ai"

Amir ya hada fuska yace" tell me you are joking, nabar boy a zaune Yana game, I went to use the toilet, wait wai tun yaushe ka dawo ne?


Walid yace" yanzu na na dawo"

Amir ya ware Ido yace" wat!!! Yanzu fa, wayyo Allah, Walid, Boy ya jira bai ga min dawo bane shiyasa ya Mike, Kai tsayuwa bai gamu ba, let's find him"


Walid ya zubar da tickets yayi hanya dama, Amir yayi hanya hagu suka fara nema Sadik suna kwala Mai kira shiru kakeji ba Sadik, lungu da sako na storey building din ShopRite ba inda Basu duba ba ba shi. ...

Cike da tashi hankali suka sauko, Amir ya sanar ma ma'aikata guri batawa yaro su. Suma sun shiga tashi hankali ba kada ba, su ka sa aka kulle kofofi ShopRite gabadaya ba shiga ba fita, duk activities da akeyi aka tsayar dashi cib, baka ji komai sai hayaniya mutani, aka sake sabo searching, securities suka Kara searching lungu da sako, har elevators na guri su duba gabadaya ko ya makale a ciki, ba shi... Ayi searching sosai har baki gate ba yaro ....



Amir da Walid jikisu ya mutu ba Karami tashi hankali suke ciki ba, Amir ya zube a kasa Yana kuka.... Manager din guri yazo ya dafashi yace" are you really sure kuzo na da karamin yaro?


Amir ya amsa da Kai..

Walid ya ware Ido ya Mike ya dafa manager yace" Sir ur cameras, ku du ba ko za'ayi dace"

Manager yace" good idea"

Amir Walid da Manager sukayi hanya office da ake viewing din CCTV cameras, suna zuwa, security da Aiki a office din ya Soma tambaya su da wani lokaci suka shigo"

Walid ne yayi iya amsawa yace" around 10pm"

Security ya fara searching mutani da suka shigo around 10pm, Yana kaiwa kuwa camera ya hasko fuskokisu Amir lokaci da suka shigo, har inda Walid yake gyara ma Sadik p cap har zamasu a table, manager yasa security yakara zooming fuskar Sadik da kyau, yayi haka suka cigaba da kallo har Walid ya Mike,ana kaiwa guri da Amir ya Mike computer na ta dauke kit, kamar a kasheta ayi ayi ta bada light ko motsi karshe ma spark computer yayi komai ya disconnect...

Amir yasa hannu akai Yana" inalilahi waina ilaihi raju'un inalilahi waina ilaihi raju'un, wayyo Allah Mai zamugaya ma Sis"

Manager ya rikeshi shima duk a rikece yake yana"calm down we will know what to do, please calm down"


Amir yaja hannu Walid suka fito daga camera room, Walid jikishi har Bari yake, murya na rawa yace" bro....... Yayi Shiru ya sharce haweye zanyi magana kenan yaji waya dake Baya aljihu ya Soma ruri gabashi yayi mummuna faduwa ya sa hannu ya ciro waya a hankali, Sis khairat ne ke ta yawo har Yana vibrating sosai a hannushi, ya daga ya nuna ma Amir...

Amir yace" inalilahi Mai zamuce"

Walid bai taka Mai ba Yana rike da waya har kira ya tsinke wani Kira yasake shigowa bai dauka ba.. duk suka zuba ma waya Ido har Kira ya sanke tsinkewa.... Jikisu har Yana kadawa..

Can waya Amir ya Soma ringing da sauri ya ciro waya daga aljihu ya duba yaga mummy ne....
Ya daga ya nuna ma Amir number dake kirashi
Walid yace" bro kawai mun amsa mungaya musu hali da ake ciki"

Amir ya girgiza Kai yace" no bro I can't ina tsoro"

Walid ya dauki waya ya accept Kira jikishi na rawa yasa a loudspeaker, maimako yaji murya mummy sai yaji murya khairat ne

Tace" oho ni ne baza ku amsa Kira na ba sai na mummy ko, toh zan Rama Kar kuji komai, dama ba wani Abu bane, Na Kira ne na gayamuku Daddy ya dawo, hajiya tabani sako na gayamuku kun dawo gida Daddy yagan jikashi dats all"


Walid murya na rawa yace" yau ... yaushe daddy ya dawo?

Ta amsa da" misali 12 ya shigo ama yanzu yaje masalaci Sallah"

"Oh gashi ma ya shigo, Daddy ga Yaya Amir zai baka ku gaisa da Sadik kafi su iso"

Bangare Daddy yayi murmushi ya karbi waya yasa a kunne yayi sallama.

Murya Walid na rawa ya amsa Sallama

Daddy yace" are you okay yanaji murya ka na rawa..

Walid yasoma inda inda ya kalli Amir, Amir ya sukunyar da Kai..

" Am ..Daddy Sadik ne muke nema ba'a gashi ba"

Daddy yace" what!! Mai kakecewa?wani Sadik ?

Essha da ke zauna tana yanka kumba jin Daddy ta ya Kira Suna Sadik yasa ta Mike zumbur ta karaso gaba Daddy.. tana sauraro taji Mai zaice...

Ciki tsawa Daddy yace" Walid answer me ina yake?

Walid Ya na haweye yace" Daddy Sadik ya bata, ba mungashiba"
Daddy ya tsaya shiru ya kasa motsi sai bin waya yake da kallo
Essha ta fizge waya da sauri a hannu Daddy jikita na Bari tace" Walid.. maiyefaru ne? ka gayamin"

Amir ya amsa yace" sis da Allah kiyi hakuri munkasa cika alkawari da muka dauka zamun kula da Sadik ki yafe mana"

Jiki ta ya Soma bari tace" Amir tell me what happened ina Sadik?

Amir Yana kuka ya fara Bata labari yada akayi..

Essha nagama ji ta saki waya ya fadi ta ji wani jiri na neman daukata, Mummy dake bayata da fitowata kenan na gani Essha za ta fadi ta karasa da sauri ta tareta ta fadi a hannu ta a take a guri Essha ta sume, Mummy tasa Kara tana jijigata, da sauri su Daddy sukayi kansu, Daddy k Anty zainab da hajiya ji Kara da Mummy tasa yasa suka fito da sauri zuwa sashe Daddy,

Kafi su iso har Essha ta farfado..

Mummy ta dagata tace"maiyasa maiki Essha ina kkemin ciwo tell me"

Essha Bata amsa tamike ta tana kuka kalli Daddy Tace" Daddy give me ur car key?

Mummy ta riketa tace" ina zakije?

"Mummy Sadik ya Bata ba agashiba Mummy am trouble"

Daddy k yace"wani Sadik din?

Sadik din Sis Essha" khairat ta bashi amsa..

Hajiya ta fashe da kuka Tana wayyo Allah munshiga uku..

Daddy yace" hajiya ba abunda yakamata kice ba kenan sallati zanki ringayi"

"Kuzo muje zama bai gamu ba"

Daddy da daddy k zasu fita Essha ta Mike Tace Daddy zanbiku"


Ya amsa da let's go..

Suna fita Baya su tada motar Daddy da kanshi yake tuki sai sharara gudu kawai yake a titi Kamar zasu tashi, kafi su isa ya sanya a police station ya kaimisu report da police dasu Daddy aka duguma sai ciki ShopRite, suna zuwa suka samu a kulle koina, Daddy ya Kira Amir ya sanar musu gasu a baki kofar gate, Amir ya sanar ma manager aka bude musu suka shiga...

Daddy ko saurara manager guri baiyi ba yasa polisawa sun fara aikisu Suma sunyi nasu kokari, ba abunda Esshakeyi a guri sai kuka,Karshe dai daya daga cikisu yabasu Daddy shawara akai hoto Sadik gida Tv ko Allah zai saa a dace ..

Duk sukayi na'am da zanceshi, Essha ta bude waya ta tura ma Dan Sanda hoto Sadik ta gayamai details akanshi harda Kaya da yasa yau...harda number ta bayar..

Ba bata lokaci sukai Hoto Sadik gidajeje Tv... Abun na kudi ba'afi mintina kowani channel hoto Sadik ne ana cigiyashi....


************************

Aliyu suna Sauka ya kira drivershi yazo da saura securities, suna zuwa ba bata lokaci ya sanar dasu gida Daddyshi zansuje, Ana tada motoci sai gida Tycoon, Suna Gama parking aka budemusu kofa suka fito, Aliyu bai jira suhaima ba yayi hanya Sashe Daddyshi, yashiga da sallama abun mamaki ya bashi dun ya Tara da family gabadaya hardah
Ummi kaduna....


Su Idrees kadai suka amsa Sallama mashi, Suhaima ko sallama haka tashigo...

Tycoon cike da baci Rai ya Mike ya zabga ma Aliyu Mari, a razane kowa ya juya Yana kallosu cike da mamaki dun Aliyu Dan lele Tycoon ne.....


Aliyu ya rike kunci ya daga Kai Yana kallo Tycoon da mamaki karara a idonshi.... Suhaima kam she was shock taji gabanta yati wani mummuna faduwA...

Mami ta Mike tana kuka sosai ta rike Aliyu shima ita yake kallo murya na rawa tace" Duk girma Allah son ka gayamin gaskiya Kar ka kunyatar da ni"

Aliyu sai kallota yakeyi bai fahimceta ba, ta gano haka yasa taja hannushi zuwa gaba Isa, Sadik na kwance a cinyarshi yasha kuka har yayi bacci... Ta daga Sadik daga cinya Isa ta rugumeshi tana kuka, can ta dagoshi ta Mika ma Aliyu, Aliyu kasa motsi yayi Yana bin Sadik da kallo yaji faduwa gabashina tsanata, ya kura ma Sadik Ido sai yaji yanaji sanyi a ranshi da son yaro da ynazu yanzu ya game minshi jiki gabaya..

Ammi ta kakare murya da tasa Aliyu ya dago Kai Tace" ur Son ko, nasa kaji haka a jikika so tell us yaushe haka ta faru bamu saniba"

Suhaima na kallosu tana ji wani bacin Rai na taso mata, a ranta tace" lallai in Aliyu ya amsa danshine akwai karami yaki a gidana.. mutani na Basu sani bane" ta kada Kai...

Aliyu yabin Yan parlour da kallo Kamar dolo yanasan yayi magana ama yanaji kamar arike Mai baki...

Tycoon ya isa gaba Aliyu Yana kuka yasake Kai minshi Mari na biyu ciki tsawa yace" answer Before I get mad at uuu"

Zai Kai Mai wani Mari Ummi ta taso dakyar ta kareshi ciki kuka ta Soma" kashe min shi zakayi,ku sashi a gaba Wana na jefa nashi tambaya Wana nayi, waye bai kuskure a rayuwa, in ya amsa Dan na nashi ne yazakuyi dashi, kasheshi zakuyi eyeyyy nace kashe shi zakuyi"

Tana rufe baki waya dake hannu Ammi yasoma ruri tayi Kamar bazata daukaba can da ya damesu da Kara ta bude cover din fuskar waya taga Ashe ma fauziyya ne..

Ta na dagawa tace" Ammi ki bude Channels News yanzu na zakiga suna cigiya yaro wlh Ammi Kamar Yaya sak, bude ki ganni sauri surname nashi ma suna Yaya ne...

Ammi turn on your TV kiga ikon Allah."

Dayake waya a loudspeaker yake, Siyama ta Mike da sauri ta dauki remote ta kunna Kato plasma Tv daya kusan cinye Rabin bango parlor, tana kunna kuwa kafi tanema Tasha Channels news, Hoto Sadik da details nashi suka bayana a AIT news...

Hankali kowa yakoma kan Tv, reporter ya soma Kira numbobi waya ga duk Wanda yaga yaro zai Kira... Tycoon ciki azama ya dauki wayashi ya Soma kwashe number Yana Gama kwashewa ya dialing number..........







Lovely Fans comments and share 💙💙💙💙

Any mistake da ku kani typing errors ne and remember nobody is ferfect😁😁😁😁😁


Love you guys 🥰🥰🥰t



👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
*DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️



*WRITING BY*
*J Hajara*



🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️



*M.W.A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
____________________________


*Dedicate this page to my lovely daughter AISHA 🥰she's priceless to me❣️❣️💃💃 dear kiyi yanda kikeso da page din naki ne🥰😘😘😘*


6️⃣9️⃣&7️⃣0️⃣


Tycoon ya dialing number, ya Soma ringing ba a daukaba, karshe Anty Mai yake zumunci 😄 ne ta amsa" The number you are trying to call is not answering please try again later thank you" Kira ya tsinke.. ya sake trying Wana karo sai yasa Kira a loudspeaker, Kira sai tir tir yakeyi Yana ringing ba'a dauka ba, hankali kowa ya dawo kanshi, har Kira ya tsinke still ba a daukaba, bai hakura ba ya sake dialing number..


*************************
Bangare Essha dukasu zaune suke a ciki police station na Apo dake na gari Abuja, ba abunda takeyi sai kuka, Su Daddy duk jikisu yay sanyi, a lokaci ne Essha ta Soma ji wayata na ruri ta Share hawaye ta juyo da waya taga special number ne Mai 0800000000(😁😁Kar wata fa ta Kira number Tycoon ni dai ba ruwana 😁)

Number yabata tsoro taji gabanta ya fadi ta kalli Daddy Tace" Daddy my phone is ringing na amsa kaga new number ne"

Daddy k ya karbi waya daga hannuta Yana kallo number nata rawa a screen, har Kira ya tsinke Daddy bai accept ba..

"Layi naki new sim ne? Daddy ya tambaya

"Eh Daddy, jiya nasa, Kuma number ne nabada aka duk Wanda yaga Sadik ya sanar damu ta layi" ciki sanyi murya ta fada..

Walid yace" Daddy ku amsa kira insu sake Kira, kila ayi sa'a Mai number Wanda ya gashine please Daddy don't ignore the call"

Inspector naji haka ya karaso ya karbi waya daga hannu Daddy k yace" No amsa Kira is very risky, wanan number bai zai wuci number kidnapper's din bane, so baza mu amsa ba har sai muhada da nau'ra da zai tracing number"

Daddy k yace" inspector kayi gaskiya ana"
Bai gama rufe baki ba wani Kira nasake shigowa, inspector yaki dagawa har ya tsinke ya ciro waya shi zai kwashe number wani Kira ya sake shigowa, Essha ciki zafi nama ta Mike ta warce waya daga hannu inspector , yazo da niyya zai karba tayi sauri ja da baya, ta Danna receive tasa a kunne Tana kuka..

Tycoon naji a amsa Kira yayi ajiya zuciya...

Essha tana kuka tace" please ku ganshi ne, Yana hannuku, da Allah ku taimaka don't harm him, duk abunda kukeso zanbaku da Allah Kar ku cutar dashi"

Tycoon bai amsaba, Aliyu naji sauti murya dake fita a ciki waya yaji zuciya shi na bugawa fat fat da sauri ya rike saitin guri, yanaji kamar yataba sani Mai murya,Yana rike da saiti zuciyarshi yanemi guri ya zauna a kasa carpet dabas, duk ana kalloshi, shikanshi ya rasa maike damushi, tunani ya Soma a'ina yasa Mai murya, where? When?

Yana kan haka yasakeji sauti murya ciki waya Daddy shi na" please please kuyi magana da Allah" ciki murya kuka Essha ke magana..

Haka kuwa yakara rikitar da Aliyu, ya rike Kai dayaji Kamar Yana juya minshi, murya na mishi amo a kunnuwan" please please"

Tycoon ya gyara murya yace" wace ce ke?

Essha ciki sauri ta amsa" ni mahaifiyar sa ce, please Kar ku cutar dashi da girma Allah, nasa Sadik na tare da ku, ina ji a jikina"

Tycoon yayi murmushi iri tasu na manya yaji yariya ta burgeshi yace" tabas Danki na guri na, Ina nace kizo ki dauki Danki Zaki iya?

Yayi magana Yana kallo Aliyu dake rike da kanshi..

Essha na kuka tace" zan iya, Da Allah Kar ku tabashi, ko nawa kukeso zanbaku"

Daddy yayi murmushi yace" ba musan ko sisi ki, kawai kizo ki dauki Danki, na gaba sai ki kiyaye"

Essha ta girgiza Kai Kama Yana ganita tace" inshallah, toh kafadamin address Dinka?

Tycoon ya fadamata address da number gida Yana gama gayamata ya kashe waya baijira Mai zatace ba, Tycoon ya nemi guri ya zauna, ya zuba uba tagumi, ya tsura ma Aliyu idon, can ya numfasa yataso yazo gefe Sofa daaka shimfida Sadik dake baccisa, Tycoon ya shafo fuskarshi Yana hawaye, yaji Yana bala'in son yaro, ya dago ya kalli Dan lele nashi da haryanzu kanshi a sukunye yake, Tycoon yakira sunashi a hankali" Aliyu?

Aliyu bai amsaba yadago, kwaya idonshi su canza kala zuwa ja jawur, Tycoon yakai duba gefe fuskar shi yaga shati Mari da yamishi ne gashi baro baro har wuri yay ja abinkada fari mutu, sai yaji ya tausaya Mai yataso yazo gabashi ciki sanyi murya yace" Aliyu ka gayamin Dan Kane?

Aliyu bai amsaba karshe ma hannu kawai ya daga Alama baisaniba..

Ammi ta dafa Kai cike da takaici.

Sadik ya farka ya Mike zaune Yana susa idon, can yasoma kuka..

Suhaima na daura Ido akanshi taji ta tsaneshi sai Harara kawai take binshi dashi tana ja karami tsaki..

Sadik ya bude ido a hankali Yana kuka, idoshi ya sauka aka Aliyu dake zaune tsakiyar carpet, Aliyu shima shi yake kallo sake bake baki yayi Yana kalloshi take gabashi ya Soma duka uku uku, fuskar shi sak yagani a fuskar yaro, yaji abun ya tsargashi mishi tun daga tafi kafarshi har zuwa tsakiyar kanshi, tunda ya Dora idonshi akan yaro yaji abun na mishi yawo akanshi zuwa jikishi..

Sadik ya Mike da saurishi ya Fada jiki Aliyu Yana kuka, Aliyu jin sauti kuka yayi har tsakiyar kanshi, kirjishi ya Soma zafi yasa hannu ya rugumeshi, jikisu na haduwa yaji wani mugu sanyi Mai dadi na ratsashi Ido ya lumshe ya kwantar da kan Sadik akan kirjishi..

Duk abunda yakeyi akan idosu Tycoon.Sadik duk zatoshi Isa ya rugume baisa asali uba gayya bane..

Sadik na kwace kan kirji Daddy shi yace" please uncle take me to my mum, please uncle am scared"

Aliyu bai tanka Mai ba, binshi kawai yake da Ido.
Sadik ji shiru ba amsa mass ba yasa ya dago da Kai ya kalli fuskar Aliyu, ya Saida kukashi, ya bude baki cike da mamaki Yana kallo fuskar Aliyu da shima ya tsura mishi nashi Ido..

Sadik ya sa hannu ya shafa fuskar Aliyu ya juya da sauri Yana neman Isa, yagashi zaune a gefesu.. Isa yayi murmushi ya kada Mai hannu, Sadik ya juyo ya sake shafo fuskar Aliyu, sai yayi murmushi..

Gabadaya Hankali kowa na kansu..

Sadik yasa yatsa a kumatu Aliyu yaga ko zai lotse, Yana sa kuwa Aliyu yay motsi da baki, guri suka lo lotse.. Sadik na gani haka ya fashe da dariya harda kyakatawa shi yanayi Yana wasa da fuskar Aliyu, kowa ya ratsa dalili dariya shi..


Ammi ta share hawaye aranta tace" jini kenan uhmm"

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
Essha ta Sha dramer sosai da yansanda aka baza su barta taje ba, su anasu tunani kidnapper's ne suka daukeshi, Kar ta je su kasheta.. Essha taki amincewa da haka ta nace ita Sam sai ta tafi..

Inspector ya Mike a fusace yace" kina tafiya muncire hannumu daga case dinki, duk abunda ya samaiki kiyi kuka da kanki ke ki ka ja, kidnapper's basa Kira ayi sauri tafiya ko Zaki kowamin aiki ne? Tafiya wurisu yatzu ba a shirya ba hatsari ne babba"

Daddy k ya rike inspector Yana bashi hakuri yace" yallabai kayi hakuri baza mun ta

Please Login or Register in order to submit comment