Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta da ya gaji da hargitsewa.

"Mummy tsoro nakeji inaji fargaba mummy, su aurar da ni, they have ruined my life" ta Kara sauti kukata, daddy ya matso kusa da su ya shafa kanta, a firgice ta juya tana gani shine ta rugumeshi " Daddy zuciya, daddy kasana, zan mutu daddy, ka raba aura na wlh banso, shikena an aura dani daddy na bazai kaini makarataba balle na cika burina har yakai ga kirana DOCTOR ESSHA, nasan daga Rana ita yau zan daina sa .... Ta dakata, jiki ta har rawa yake saboda tsumayi kuka" daddy why me? Why? Why?

Daddy haweye fuskata yashiga gogewa shima dauriya kawai yayi, Yana rike haweye bai barsu su sauka ba ya daure yayi murmushi Yana girgiza Kai yace" ya'isa haka Essha daddy, ki daina ai'bata aureki Kar ki mantafa aure sunnah ne na Ma'aiki (S.A.W), aure rahma ne Kuma alkharine, magana karatu inshallah ba abun da zai hanaki bearing suna DOCTOR ESSHA" yaja mata kumatu yayi murmushi " ba abunda zai saimeki inshallah, ni da mummy ki dasu hajiya muna tare da ke"
Daki ya dauki shiru, bakaji komai sai shesheka kuka Essha da hajiya, Essha na kuka zafi da ke damunta, hajiya Kuma tausayi hali da Essha ke ciki shiyasa ta kuka, Essha sai zabura take ita daya, haryanzu da alama tsoro a atare da ita, daddy nata aiki lallashi, can ya Mike yace" Essha zanje sallah ankira zuhur"

" Ni ma zanyi sallah daddy" ta fada Tana share hawaye , tun jiya banyi sallah ba"

" Toh mummy ki da antyki zasu tamaika miki" ya fice da sauri baison ya rasa jam'i.
Nurse din ta kalli mummy tace" hajiya bara na taimaka mata dun ba'ason tayi kwakara motsi saboda dinki dake jikita"

Essha ta makale kafada ta tura baki tace" uhm uhm mummy nane zata taimakamin"

Nurse tayi murmushi ta shafa kanta tace" okay beauty badamuwa Bari na baku waje" ta fice..

Mummy ta Mike ta dauki flask din da hajiya suka kawo da safe, tafasheshe ruwa ne dam , tashiga toilet ta juye a baho wanka, da taimako anty zainab ta kaita toilet, ta zuba gishiri kadan ta Kara surka ruwa, sanda suka Kai ruwa Rana Essha ta Amince ta shiga ruwa zafi, ihuta yagama cika asibiti, kuka tasaki da Karfi tana Kira hajiya da daddy ta su zo su taimaketa, Wai balle Essha iyaye raki.. sanda mummy ta tabbatar ta gasu sosai sanan ta cire ta tasata tayi wanka janaba ta Dora alwala tafito, tan Dan ji dama dama, Dakar take takawa mummy na rike da ita, har su ka Kai baki gado, haweye kawai take sharewa ta hura baki, ita kadai tasan yanda takeji a zuciya ta, sai tsine Aliyu takeyi, yasha Allah yaisa ba adadi.

Mummy ta shimfidar mata daddurma tabata riga da skirt na atamfa tasa da hijab , a zaune duk ta Rama sallolita tana hawaye..

ABUJA
************************
Gari na wayewa ummi tasa su a gaba sai fada take musu" tun jiya nagaya muku cewa su shafi Aliyu ama kuka ki yarda da batuna, gashi har su na nema sumishi illa, Allah sarki bawa , Yana ban tausayi , ke Kuma aljana Essha, Allah yama jikana kataga karfe dake" Mami ta amsa da ameen sanan tace" ummi maiye mafita?

Ummi ta rike haiba tace" mafita kenan ana sallamorshi atara malamai Yan ruqiya kawai suriga mishi tofi har tasakeshi"

Tycoon ya Mike yace" ummi ni zan wuce asibiti"

Tace" bamugama magana ba"

Yace" duk abunda kika ga yadace shi za a yi, sai na dawo"

Mami ta Mike tace" jirani na dauko mayafi na muje"

Yace" sai ki fitoh"

Suna isa asibiti Tycoon ko yaji ra a bude minshi kofa ya bude kofar da kanshi, guards na gani hk da sauri suka bi bayashi ya dakatar dasu.. I C U ya wuce Mami na biye dashi, suka Tara a canza ma Aliyu room an cireshi a I C U. Mami tayi ajiya zuciya tace" Alhamdullila son yasamu sauki tunda acireshi a ICU" tana magana saiga haydar yamusu iso zuwa harzuwa daki da Aliyu yake , Allah sarki, Hafiz suna na a zaune su zuba uba tagumi harsu dan fada kamar a jikisu ciwo yake, Tycoon ya binsu daya baya suka yi musabaha cike da girmamawa suka gaida mummy ta amsa .

Tace" Allah ya muku albarka" suka amsa da ameen Mami

Tycoon ya nufi gado Aliyu ya ke kwance kamar gawa, baya ko motsi, fuska na tayi fayau, lips nashi duk su bushe, ya shafa ganshi kan Aliyu yayi ajiya zuciya sanan yace" boy Allah yabaka lafiya suka amsa da ameen, ya nemi guri ya zauna a gefeshi ya kalli fawaz yace" Doctor yajiki nashi?

Fawaz ya su sa Kai yace" da sauki dad.gani sauki ne shiyasa aka canza mishi room.

" Ya farka dai ko ? Mami ta tambaya

Yace" eh mami ya farka around two na dare, sai sambatu yakeyi Yana Kira suna dai Essha, shine kawai mikamishi allura bacci, inshallah na bada jimawa ba zai farka"

" Inalilahi waina ilaihi raju'un, Essha Essha haba haba, wanan Essha mutum ce ko aljan da zata adabi rayuwa dana" Mami ta fada ta rike Kai ta fashe da kuka..

Suleiman dake gefe ta ya Mike ya dafata yace" Mami ba kuka zakiyiba, addu'a zakimishi, Allah yabashi lafiya, yanzu Yana farkawa yaji kina Kira suna Essha Dina Kara rikecewa zaiyi"

Mami ta hada hannu ta na addu'a Tana haweye tace" Allah ga Dana na, ka. Fitar da shi daga ciki wanan hali dayake ciki, Allah na rokeka" suka amsa da ameen, suna amasawa sukaji an bake kofa anshigo bako sallama, suna daga Kai sukaga suhaima ne, dogo riga ne a jikita na atamfa ta cugale dauri dankwali bako mayafi s jikita, car key ne da waya a hannu ta kirar iPhone 11 pro max, Suleiman na gani itace ya baka mata harara, ya Mike ya fice, saura ma suka bi bayashi, don bakarami haushi ta sukeji ba, toh su San hali, ita kam ko ajikita kallo sama da kasa ta binsu dashi taja tsaki.

Suleiman suna yaja tsaki yanemi guri ya zauna yace" wlh I hate this girl, gsky an cuce Buddy, yariya batasan daraja mutani ba, Mai karanci addini" ya Kara ja wani dogo tsaki..

Hafiz yace" Nima ko kallo ta basanyi Mai Kama da sisiya, wlh ko a office ko kallo Bata isheniba, Allah ancuceshi , dubeta ma Kama kara, Allah yasa ma aljanana Essha Dina , aljana ce dagaske, Allah zan iya biyata tayimin maganita yariya ba tarbiya kawai (lolz kuji Hafiz fa).

Haydar yace" Kuna ma da lokaci ta kenan bara kuga hoto da ta daura a page nata na Instagram guri misali karfe 3 na dare fa" ya ciro wayar shi daga aljihu Yana nunamusu hoto suhaima, suhaima ne zaune a club, su hudu itace kawai mace a ciki su, tasa dogo riga ne a cikita ya matse ta sosai ko rabi cinyar ta baiyi ba, fixing da tayi na attach duk ya barbaje tukunyar shisha ne a gabansu, tana tsakiyar maza, hayaki take fesowa cike da korewa a fuska yan samarin.

Fawaz ya ja tsaki yace" tir da hali iri nata, ni narasa dalili da yasa for the first place daddy ya Amince da aure na, wlh da abani irita guda goma goda aban Yar karkara wancan batasa komai ba" duk suka fashe mishi da dariya..

Hafiz yace" ahaf Kar kudamu nasan buddy zaiyi maganita, zanta gane kureta, Allah sarki buddy yaro kirki Allah yabaka lafiya" suka amsa da ameen..

Ciki daki kuwa, suhaima Chewgum take fasawa fas fas kas kas batama San da su Tycoon a daki ba, hankali ta na waya tana chatting, yantsu zaro zaro yasha pink artificial nails, Mami sai binta take da kallo mamaki, Bata cemata uffan ba, ita akullum tir takeyi da Wana Hadi aure batasan maiyasha kan maigida nata ba da ya nace sai ya aura ma Aliyu Wana gataleliyar, kwanaki baya har batawa sukayi akan magana aura Ammi ne tabata hakuri tace su zubamishi idon Allah yasa haka shine mafi alkhari..

Mami ta tabe baki ta bita da kallo.. Tycoon yace" a'a daughter welcome ga guri ki zauna"

Suhaima har ta Dan firgita da taji magana ta daga Kai suka hada Ido da tycoon ta saki murmushi tace" good morning Dad " a tsaye ko ta Dan ragwafa.

Yace" morning daughter ga Mami ki " ta juya ga kallota ga inda yanuna mata, Mami sai binta take da harara kamar idon zai fadi.. na take taji shakku Mami ta sukunyar da Kai tace" good morning ma"

Mami ta amsa fuska a hade ta kauda Kai..

Suhaima Sumi Sumi taja jiki zuwa gefe Aliyu tace" dad ya Mai jiki?

Ya amsa da sauki Yana shafa kafa Aliyu, yana shafa kafa kuwa, kamar ace ma Aliyu ya farka, ai da sauri Mami da Tycoon suka Mike , Tycoon ya rike hannu shi Yana murzawa yace" Aliyu bude Idonka kaji "

Aliyu dayayi kamar zai bude sai yakara lumshe dasu, har yazo yabudesu gabadaya..

"Aliyu, Aliyu " yaji daddy shi na Kira, bai iya amsawa ba, ya yinqura zai tashi Tycoon yayi sauri taimaka mishi ya zauna yace" son sannu yajiki? Bai amsaba ya binshi da kallo yasoma motsa baki yanasa yayi magana ama yakasa. Mami ta rike mishi hannu tace" boy badai jiki bane ko?

Kamar ansashi magana dole yasoma magana a rarabe yace" da...ddy m..ami, kun..gan..ta, kug...amin Essha na"

Tycoon yace" subhanallahi, Aliyu ba kabar magana Essha Dina ba?

Ya dafa saiti zuciya shi yana cewa" daddy zuciya na zata buga da Allah ka taimakeni kanemo mi Essha, daddy imbahakaba wlh zaku iya rasani" da sauri Mami ta rugumeshi tana shafa bayashi Alama rarashi tace" boy kadaina fada haka, kaji ko, take it easy, ba abunda zai saimeka, this Essha you are talking about , we don't even know whether ita mutum ce ko aljan, I probably guess ita jinnu ce, don inba jinnu ba, babu mahaluki da zai'iya rayuwa a ciki wanan daji, ka Manta da ita kaji ko"

Ya girgiza Kai yana haweye yace" no Mami bazaniya mantawa da itaba, she's my wife, my happiness" Mami kalloshi ta tsaya Yi ta mamaki dan nata, daga jiya zuwa yau duk ya canza ya birkece aka mace, har da kirata matashi, Kai gaskiya na yarda Wana aiki jinnu ne...

Suhaima dake tsaye taji duk kalamai Aliyu kefada ai sai ta tsandare a guri, zuciya ta yayi baki,tasoma fitar dawani haweye Mai zafi , ranta yakai kololuwar baci, tanuna kanta" wato ma Aliyu wata yakeso baniba , dun su Raina min hankali shine sukece aljana ce,har dawani kirata my wife my happiness,kan burar ubancan, wlh ko waye ita saita gane kurata" ta fice a daki a fusace..
Su Tycoon ma hankali su baya kata, basumasan ta fice ba,

Aliyu ya rike hannu daddy shi yace" please dad ka taimakeni"

Yawun Mai daci Tycoon y hadiye ya dora hannushi a sama gashi kan Aliyu yana shafawa har sanda ya daina kuka sanan yace" Aliyu kayi hakuri, dakai fa mukaje nemamta bamuganta,mu nemata murasa, Kai bana tunani ma akwai wani dan Adam dake zama aguri, inason ka dauka cewa faruwa haka daga Allah ne, yayi hakne don ya jarraba Imani ka, na tabbatar idan kayi hakuri wata Rana zai zama labari"

Yajijiga Kai yace" no no daddy bazai iya jurewa ba, daddy she's hurt, tana bukatar taimokona, nasan duk inda take hankalita yafi nawa tashi, daddy help me please "

Tycoon yaja numfashi yace" kayi hakuri mana Aliyu be strong"

" a'a daddy bazaiyab, Ina ratsa ta, na ratsa fariciki na, she's my first love, daddy bazakara samu wani fariciki ba, inhar Essha Bata tare dani"

Tycoon yace" haba son , zaka samu fariciki inshallah fiye da kake zato, nasani wanan duk abunda kake na dan lokaci ne da an daura aureka da suhaima shikena zata mantar da Kai so called Essha"

" a'a daddy I can stop loving Essha, sonta a jinina take, Kuma bazata ba so wata baya ta ba, zan auri suhaima ne kawai saboda ........

Mami ta katseshi tace" ya'isa boy don't talk again, bakada isheshe lafiya "

Yace" daddy promise me Ina warke zaka barni naje nemanta, da Allah daddy promise me that, daddy dun girma Allah kada kace aa "

Tycoon ya sauke nannauyar ajiya zuciya yace" na Amince maka, ama da sharadin...

Ya zabura yace" daddy shara din daka gindayamin zanbi "

Tycoon yace" akodayaushe in zaka fita, zaka Riga fita da masu tsaro lafiya, sama da ashiri, ka Amince?

Ya sukunyar da Kai kasa gsky baiji dadi wanan sharadin ba, ama ya zainyi, dole zai Amince sbd ya nemi sanyi idanuwanshi, yadaga Kai yace" na Amince dad"

Tycoon yasake cewa" kuma duk abunda ummi zata daura ka akai, Kar kamata musu" Aliyu ya kalli mami yasake kallo daddy shi, fuska shi da alamu tambaya ama sai Bazar dun haushi ummi yake ji, ita tafara Kira Essha da aljana..

Murya ciki sanyi yace" na Amince"

Tycoon yace" yawwa good boy, yanzu Bara na Kira Hafiz su zo su taimaka ma , kayi wanka ka Rama salloli dake kanka "

Yace" zaniya daddy"

Mami tace" a'a boy Karka yi musu, jiki ja ba karfi..

Baya Akira Hafiz, ya taimaka mishi yashiga dashi toilet din ya fito yaja mishi kofa, Baya Hafiz ya fita, ta Dade a tsaye, Essha yake tunawa da iri hali daya barta a ciki, waensu zirori haweye masu zafi suka zubo mishi , ya sa hannu a gashi kanshi ya cakudasu, ji yake kamar yasa ihu ko zaiji sauki yanda zuciyashi ke mishi, ya kunna shower ya Soma wanka, yana gama yayi na tsarki ya dora alwala yafito , Yana dafa bango da sauri ya taimakamishi , yasa jalabiya, Mami ta shimfidar mishi daddurma, ya hau ya tada sallah, duka ya Rama salloli daake binshi, bayan ya idar yadade a zaune ya na roko Allah ya bayyana mishi matarshi, Yana haweye...

Mami ta dagashi tace" boy ya'isa hka, hakuri zakayi, tashi kasa wani abun a cikika, kasha magani, kaji?

" Mami bazaniya ba " ya girgiza Kai

" A'a boy zaka'iya, daddy shi kasa baki mana"

Tycoon yayi ajiya zuciya yazo ya dafashi yace" haba gadagaa na, nasaka fa da jarumta da juriya, maiyasa bazakayi hakuriba, uhm aliyu, yihakuri please ko kadan ne kaci kaji boy, sai kasha magani... ya dauki fruit salad dake hannu Mami ya deba ya kaimishi baki .. Aliyu ya girgiza Kai Yana yamutsa fuska yasa hannu ya janye spoon din fruit suka zuba yace" daddy kayi hakuri bazaiya ci komai ba, daddy zuciya na zugi takemin.. ya rike saitin zuciyarshi yacigaba"daddy inhar basa Essha idona ba, tona tabbatar muku bazantaba rayuwa ciki walwala ba, daddy rashita zai sa nasha wuya, nazama kullum aciki kunci"

Haydar ya tareshi yace" haba buddy yakake magana iri wana, so kake ka jefa su daddy da ka ka ciki tashi hankali, Essha Essha Essha bamusantaba, wani halaka bai taba hadaka da maisuna ba, tabbas sai yanzu na gasgata magana ummi, Essha Dina aljana ce ta aureka, ta shanye ma zuciya... Ya dafashi yace" look at me, Aliyu yakamata ka farka, mu yaketa, da adduo'i, addu'a makami mummini, kaga mata kala kala ma su kyau, aji dukiya , su so ka ka kisu, shine daga jiya zuwa yau zaka fada so haba buddy impossible..........








Comment &shareβ€οΈβ€οΈπŸ™πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
______________________

3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣

Aliyu ya sauke hannu haydar daga dafashi da yayi yace" haydar, Essha ba aljana bace mutum ce kamar kowa. Tabbas da basan so ba, na kasa yarda da wata kalama Wai ita so tsakani ya mace da namiji, in aka cire na iyaye, duk Mai soyaya Ina daukar shine kamar Mara aiki yi, gashi yanzu na fada tarko so. Wlh aka Essha zan iya sadaukar da komai nawa inhar zan ganta" ya rufe fuskashi da taffuka hannuwashi Yana kuka yace" basan a wani hali take ciki ba, tana matukar bukatar a tare da ita, Wai Maiyasa ma ku dauko ni ba tare da ita ba why? Yadaka tsawa ya Mike ya na buga kanshi a bango, da sauri haydar da Suleiman suka rikeshi duk yabasu tausayi. Ya kwace kanshi daga rukosu ya zo gaban tycoon Yana tangadi, tycoon da saurishi ya tallafoshi ya rugumeshi Yana rarrashi shi. Ya kalli mami da duk fuskata ya baci da hawaye, Abu mamaki ya ke Bata, Wai yau Aliyu ne ke kuka, kuka ma aka mace. Taji murya Aliyu nacewa" Daddy maiyasa kuka barta acan, why why ?

" Aliyu kuka ya'isa haka, tun jiya da safe ake ta nemanka lungu da sako ama ba inda bamu duba ba, karshe a gefe gate din gidasu ummi muga, bamusan waye ya ajekaba" Tycoon ya fada Yana share mishi hawaye.

Mami ta share hawaye tace" sai yanzu na Kara yarda da maganar ummi gaskiya ne, aljannace ta shafi boy"

Aliyu ya rike Kai da Karfi kamar zai cire Yana girgizawa yace" no Mami Essha mutum ce, ba aljana bace, Mami kubar kirata da aljana.. ya rike hannu daddyshi yace" daddy Kar yardadani, da Allah ka taimakeni wlh zuciya ta zata iya feshewa"

Tycoon yace" Aliyu take it easy mana, be strong, in har kanaci abinci, kana Sha maguguna ka, har ka warke toh zamu nementa Kar kadamu"

"No daddy baza taba warkewa daga ciwo danakeji a zuciya ta ba inhar bagantaba" Aliyu ya fada kamar zai zauce.

" Hmmmmm" Mami ta ja dogo numfashi... Tace" Hafiz, haydar ku tatara mubar asibiti na mukoma gida Naga kamar Kara rudewa yakeyi"

"Toh mami" suka amsa..

Fawaz ya ya Hado mishi maguguna aka Kira babba likita suka bashi sallama, Aciki motar ya ki kulla kowa titi kawai yakebin da kallo, harsuka isa gida, suna isa parking lot , kafi angama parking yasa hannu ya bude motar ya fito, ya wuce side nashi Yana tangadi, fawaz da Suleiman da gudu suka bi bayashi, suka taimaka mishi ya karasa ciki.

Suna bude kofar parlour sukaci karo da manya manya malamai su takwas ga Al'qurani a gebasu, su zagaye parlour suna karatu, ummi da Ammi suna zaune akan couch gabasu kasko ne ga Kaya hayaki lodi Lodi a gabasu, Aliyu ya binsu da kallo al'ajabi, sukayi sallama, suka amsa.

Ummi tace" yawwa malamai ku dagata gashi ma ya dawo, Suleiman ku kawoshi tana ya zauna a tsakiyar su"

Aliyu ya Bata fuska Yana hararata yace" Ammi ki gayamata ba'abunda zanyi"

Tycoon da Mami da shigowar su kenan yace" kamata sharadin da mukayi da Kai a asibiti ko?

Yace" Daddy wlh mutum ce, ku fahimce ni"

" Ssshh bansaji komai kayi yadan tace, je ka zauna"

Ya nufosu jiki a sanyaye ya zauna a tsakiyar malamai.

Fawaz ya kalli Ammi yace" Ammi abanshi wani, Abu yasa acikishi yasha magani Naga kamar za'a jima"

Ummi tace" eh ku kawomishi abinci yaci yasha magani kafi a fara"

Ya Galla mata harara yace" ni na koshi banzaiya ci komai ba"

Ammi tace" baka isa ba, Hafiz jeka kawo magani, ni baza naje na hadomai wani abun da zai ci"

Yace" Ammi ni na koshi banzaiya ci komai ba"

Ta harareshi tace" mun shiru, banasan nakara ji murya ka ana, abinci sai ka ci shi, sana afara" tayi hanya kitchen dake side din, sharp sharp ta hada mishi pototo with kidney sauce, da coffee, tasa mutumishi ne. Ta fito ta jera a dinning table, takira su fawaz, zu zo suyi breakfast tasan tun jiya rabuwasu da abinci ga idanusu yanuna, baya su zauna tayi serving nasu, ta debo na Aliyu ta dire mishi agabashi ya kauda fuska, ta tsuguna agabashi tace" Aliyu Allah ka ci abinci na, ko na sabba ma"

Ya marairace murya yace" Allah Ammi bazan iya ci komai ba"

Ummi tace" iyye ku shagwaba Wana Kato da yawa, kamar shi haka ace ana wani lalashi shi, irishi a kauye su aje hudu biyar, ku gashi ku sagarta dashi, sai abunda yafada, irishi tsumagiya (bulala πŸ˜† )za ku neman ku chala mishi, ama ku........

Mami ta katse ta Tace" yihakuri ummi, yaro ne, Yana bukata lalashi"

Ummi tace" iyye Wana kato ne, yaro, Mai aure wata gobe"

Aliyu ya hada fuska tam jiyake kamar ya wulata a waje.

Ammi ta zauna daf dashi ta rike mishi haiba tayi maganar kasa kasa Wanda daga ita sai shi sukeji tace" haba mana dan lalle Mami da daddyshi, yihakuri kaci wani abun ko, ummi kishi take shiyasa, inshallah zakaga ta, ama fa sai kaci abinci" yayi murmushi Wanda har dimples nashi suka lotse gabadaya.. Tycoon ya zuba musu Ido Yana kallo su gwani sha'awa uwa da Dan kenan, rabuwashi dagani murmushi Aliyu tun shekara jiya ama gashi Ammishi, ko minti bai bugaba, tasashi murmushi..

Aliyu yace"Allah Ammi" ta gyada mishi Kai... Ai da sauri ya dauki coffee, ya shanye tas ya aje cup, tayi dashi yaci abinci, yakici ta hakura ta bashi magani, sanan aka fara ruqiya, bin malamai yake da kallo, suna qira'a ya na ratsashi, yanaji wani sanyi aranshi,( Aya Allah rahma), tun Yana bin har bacci ya bige dashi agun.

Ummi tasa kabara tace" ai sutafi shikena sauki yazo.. Tycoon dakashi ya daukeshi ya haura dashi dakishi har ka gado, ya gyara Mai kwanciya, Yana fata Allah yasa komai yazo karshe.


*************************

Suhaima tuki take Rai a bace, speed tasa ma motar tana gudu Kamar zata tashi a sama, sai dai a kauce mata a hanya badai ita ta masa ba, har ta karasa gida, wani mahaukaci horn take dannawa kamar zata ballashi, Kara ya cika ko'ina . Baba maigadi har yafara bacci, Yana ji Kara horn a firgice ya farka, ya fara Bari dun yasa Mai horn din dako Alhaji ma baya haka, da sauri ya Mike don yaje ya bude mata gate, suka ci karo a hanya har ta shigo, tabar motar a waje, suhaima ta dauki hannu ta zuba ma tsoho na lafiyayu Marika har biyu, ta hankadashi da kafa, Allah sarki tsoho na zaiyi jika da ita.tana ya mutsa fuska tace" Kai tsoho na koreka a aiki"

Ya durkusa Yana kuka yace" da Allah hajiya ki tausayamin, wanane kadai hanya samu ci na da iyalaina, ki taimakeni" Yan aiki gida duk suka zuba musu idon tsoho yabasu tausayi, suhaima takama hanya. Baba maigadi yabin ta Yana kuka yace" hajiya inshallah bara na Kara kuskureba, ki ceci rayuwa na" ya tsuguna a kasa Yana rokota.

Ta juya ta dakamishi tsawa Rai a bace tace" Kai talaka banza, talaka wofi, bakasan aiki ka ba, sbd haka ka bacemin dagani , Kar na huce fushi na akanka, na koreka na koreka" ta Kara hankadashi da kafa, ta wurga ma wani Ma'akaci car key nata da sauri ya cafke ta wuce ciki. Baba maigadi durkushe yake Yana ta rusa kuka, ya Mike yashiga daki tatara kayashi yabar gida ya na kuka.

Suhaima na shiga ciki Rai a bace, feenat zaune Tana latsa waya, taji shigowarta ta Mike da fara'a tace" ke Wai Ina kika shigane, ki dawo Rai a bace, to nvm, tun dama accessories Dana muna order ne a Jumia nazo na nunamiki , koyayi" ta Mika mata waya , suhaima na amsa ta buga waya a bango, ya bada Kara Tass, ta daka tsawa dayasa feenat ta firgita tace" banza inanana Ina fama da zuciya ta, Ina fama da Aliyu ya Soni, ama ke ta accessories kike, Yana na can wata yake Kira bani ba, wata yakeson daban, baimasan Dani a lissafishi ba" ta dauki glass cup dake gaban feenat ta hadashi da center table dake tsakiyar parlour, ta fisge dogo home theater, takama duka babba plasma da aka kawatar da parlour dashi. Feenat zata riketa ta daga mata hannu tace" hey u stupid don't touch me, soyayar Aliyu zai kasheni" ta cigaba da rutsa Kaya Mai amfani dake parlour, yan aiki da feenat Dan suyi yukiri riketa sai tamusu rauni, duk taji musu Rauni a jiki, Bata sadudaba sanda ta ta tabbatar ta runguza komai Mai amfani dake parlour, ta durkusa a kasa ta fashe da kuka , duk ta hargizai, ta dago Kai ta nuna kata tace" ni Aliyu zai cimi mutuci yace bai sona wata yakeson, ni " ta Kara fashe da kuka,

Feenat a tsorace tazo gefeta, tana dar dar, tana tsoro Kar tasake hi mata wani Rauni ta

Please Login or Register in order to submit comment