Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Isha a mosque dake kusa da hospital din.

Tana Parker motar a compound dinsu taga neighbors nasu suna fitowa daya baya babba da yaro, suka rugume ta suna kuka su matukar Saba wa dasu. Most especially ma mata tana yawa taimakosu da Basu kulawa aka lafiyarsu Dakar ta lalashesu suka rabu tashige gida da sauri don itama dauriya kawai takeyi, tana shiga ta tarar har Amir yagama hada musu Kaya, da gobe da wuri zasu wuce flight din safe ne 6:00am cib na safe zasu tashi, Sadik ma yayi bacci, ajiki Amir..

Essha takasa kunne da kyau don tunda tashigo shesheka kuka takeji, da sauri ta leka room nata taga Pooja ne keta aiki lallashi Arundh, daketa fama zaga kuka itama kanta Pooja kuka takeyi.

Pooja haushi ya dauke ta ta tura Arudh dake jikita tagaji da lallashi, Essha da gudu ta karaso ta tare Arudhati ta fado a hannuta ta kalli Pooja Rai bace ciki harshe Hindi tace" maita miki? Arundh wats wrong with you?

Arundh ta Mike Tana share hawaye tace" You and Sadik are leaving me, ba Wanda zan Kara wasa dashi " ta fada tana shesheka kuka.

Essha naji hk taji wani kuka yazo mata ta daga Kai ta kalli Pooja da itama kuka takeyi, tarasa Mai zatace kawai itama sai ta fashe, duk guri akarasa Mai lalashi wani daga Pooja har Essha, Dakar dai Essha ta daure ta Saida nata kuka ta lalashi Arundh ta Manta Alkawari baya tayi hutu ita dakanta zatasa uncle Saif ya kawota, Arundh tasoma murna daga haka har bacci ya dauketa a cinya Essha. Essha ta kalleta ta share hawaye ta kalli Pooja tana hawaye, Pooja ta playing many roles a rayuwata , baza ta taba manta wa da ita ba, ba abunda zata iya cewa da Pooja sai godiya da fata Allah yasaka mata da Alkhari"

Ta Mike ta Kai Arundh ta kwantar da ita ta dawo ta zauna a gefe Pooja da haryanzu kuka takeyi, Essha ta kirkiro murmushi ciki harshe Hindi tace" haba Aunty Sadik, kuka fa kamar na mutu" ta rugume tace" haba Baby Saif yihakuri kibar kukana, ai zakiriga visiting muma Muna zuwa ko? Kiga kenan zakisan Nigeria da kiketason kisani ko? Ta fada Tana share mata hawaye..

Pooja ta Mike ta juya mata baya tana share hawaye, Essha ita ma ta Mike tazo ta dafata ta juya da ita suna fuskata juna Essha tayi murmushi tace" na Miki Alkawari zan riga zuwa"ta fada Tana ja mata kumatu.

Pooja ta sauke hannu Essha murya kuka tace" waye mahaifi Sadik?

Essha ta bude baki dun mamaki tambaya ya Bata dun tunda suke da Pooja Bata taba tambayata ba, Pooja ta katse mata tunani" Dr tell me waiye mahaifi Sadik? Doctor Kar kimin karya kigayamin gaskiya"

Essha ta kada Kai, kwalla yacika mata idon ta rufe baki tana tace" bansashiba, Pooja bansashiba"

Pooja cike da mamaki amsa da Essha ta Bata, ta karaso gaba Essha tasa hannu tana jijigata ciki da tsawa tace" tayaya zakice min bakusan mahaifi dankiba, tunda nake dake na taba tambayi ki?

Essha ta girgiza Kai fuskana ya Gama baci da haweye gabadaya..

"Toh kigayamin gaskiya please nd please Doctor, Sadik he's in pain, daurawa kawai yakeyi saboda baison gani bacinraki, kullum baida wani buri daya wucd yaga mahaifishi, yaro ki tun Yana karami kinason kisamishi bakiciki rufewa yakeyi baison kigane, why because he's a strong boy.

Essha please nd please kigayamin inda papi Sadik yake ni zan kaishi"








Manage please 🙏


Comment and share 🌺♥️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️




Love you guys ❤️❤️


👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️


*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer= whatsa
___________________________




6️⃣2️⃣&6️⃣3️⃣



"kishi sa ne yasa bakison ku hadu" cewar Pooja

Essha naji haka ta daga Kai Rai a bace tana kuka tace" keep shut pooja, na tsaneshi" ta juya zata fice a daki.

Pooja tayi sauri ta rikota tace" daga tambaya shine zakiyi fushi, juyo please magana zamuyi"

Essha taki juyowa zuciya ta zafi yakemata.
Pooja tace" toh inhar papi Sadik da bakison naganine toh yau nagashi, nagashi da wata alamu sununa matarshi ce, nasan ki ci amanaki yayi shiyasa kika kujeshi, bakiso sa"

Essha daji haka da sauri ta juya tana ware idanunu gabata na tsanata faduwa, ta rike hannu Pooja takasa magana duk t rikece.

"Yadai daga magana duk kibi ki rikece, tabbas Naga Mai Kama da Sadik , over Kama ma Abu daya kawai zai nuna ma Sadik shi babbane, Kuma Ina ganishi na tabatar mahaifi Sadik ne jikina ya bani haka"

Essha ciki rudewa ciki Ina Ina tace" a..a.a in..aa ki...ka.gan....shi, tell me you are joking"

Pooja taja tsaki tace" Doctor ki kalli idanona kiga Alama wasa ana, tabbas na ga Mai Kama da Sadik, a office nagashi yafito daga office din Dr. Agart Kumar, Essha mamaki ganisa ne ya hanani magana har suka bace min dagani, na bin bayasu ba gasu ba, Kuma na tabatar Miki Yana Delhi, Da Allah Essha kiyi magana kiga gobe Zaki wuce ko sau daya ki hada Sadik da papishi, please nasan kisan inda yake, please"

Essha ta jijiga Kai Tana kuka jikita sosai yake rawa ta sulale a kasa a hankali ta hada Kai da gwiwa kuka take sosai Mai cin Rai tausayi kanta takeji, Pooja kenan ta Soma tuhumata ina ga Takoma gida, Allah kadai yasa abunda zai faru, abubuwa da suka faru shekara bakwai da suka wuce tafara taryosu akanta, Tace" toh maiyazoyi office din Dr agart? Ta mikar da Kai tasa hannu ta cakuda gashi kanta tana kuka ita kadai tasan yada takeji a ranta, fuskana har ya canza kala zuwa ja Saba kuka da takeyi.

Pooja ta matso ta zauna a gefeta ta dafata tace" Dr kiyi hakuri inhar haka danayi yabata Miki Rai yasaki kuka, da yarda Allah bazan Kara tambeyaki ba, you a strong woman gashi yau nasaka ki ki zubar da haweye, kiyi hakuri nasan Sadik inyaji haka he will not be happy with me, saboda nasan mahaifiyar shi kuja, Wanda nagani yau a hospital, I will pretend kamar baga Bata ba ganishi ba, nasan kamace kawai, I know kishi ne yanzu haka yasaki kuka na, it's not easy, ga soyaya da kishi shi zalla a kwarya idoki"

Essha ta daka mata wani tsawa sanda pooja ta tsorata, Essha ta nuna saiti zuciya ta tace"stop it Pooja I hate him, I hate him" ta Mike ta kifa Kai da bango ta fashe da sabo kuka...


Pooja ta taso a hankali ta dafata tana dan bubbga mata kafada tana calming nata,sai guri yayi tsit shesheka kuka Essha ne kawai ke tashi, can Pooja ta katse shiru da cewa" you hate him and then y do you married him?

Ciki Hindi tacigaba" ko dai iyeyeki ne suka tilasta Miki dole sai ki aureshi?

Essha girgiza Kai Alama a'a

" Then why did you hate him?

Essha Bata amsa ba ta jiki a hankali ta zauna a baki gado tana share hawaye, Pooja ta biyota ta zauna a gefeta tana jira amsa da zata Bata. Essha murya kuka tace" Pooja tunda muke dake Bata taba baki labarina bako, toh yau zanbaki"

Ta dakata na waesu mintina can ta fara Bata labari tun tasowarta da family nata, friendship nasu da Bestie, soyayarta da Khalid Bata dire ba sanda ta Bata labari haduwarsu da aura mata Aliyu da sukayi komai sanda ta koshe ta fadamata , takai karshe labari tayi shiru ta zuba ma Pooja idon dake ta dirsa kuka Kamar yanzu abun yafaru, tasan Pooja da tausayi ga ta da sauri kuka, Pooja kukata tikiri take rusa tsakanita da Allah, dan gaskiya labari Essha ya jijigata yabata tausayi da mamaki.

Essha taga kuka Pooja bamai karewa bane ta mikar da ita ta kaita toilet ta wake Ido, tabata towel ta goge fuskar suka fito, duk suka zauna.

Essha ta kalleta tace" ki dai ji labarina"

Pooja ta gyda Kai Tana hawaye tace" kina nufi tundaga Ranar baki Kara haduwa da Aliyu ba?

"Eh" Essha ta amsa.

"Ama ko sau daya baki taba bincekawa ki nemoshi ba Koda a internet ne?

Essha Bata amsaba ta Mike tana tura baki tace" bansaniba, baki tambayi besty na ko Khalid ba, so called Aliyu kawai kike tambaya toh bansaniba, ke jeki internet din ki nemoshi, rubbish"

Ta Mike zata fita Pooja tasake rikota tana murmushi tace" yi hakuri, Aliyu ne yaban tausayi daji yanayi kalamashi na fahimce he fall for you, ai baga laifishi a Nan ba da zakice ki tsaneshi, Essha think, think, you love this guy, stop deceiving yourself"

Essha ta share hawaye ta baka mata harara tace" sai kiyi tayi "

"Ohh sorry ya magana bestie itama baku kara haduwa ko waya bako?


Essha ta gyada Kai Tace" tun daga Ranar ko na kirata Bata daga waya, ta ma yi aure, Amir yagayemin tun 6years back, harta ma haihu, nasan Walid ya samamu sabo numberta, kullum ina Kira Yana ringing Bata dagawa, nasan haryanzu umarni Daddy ta takebin dun tana tsorashi sosai" ta fada Tana share hawaye..

Pooja ta rugume ta Tace" lallai Doctor ke jarumace, kiga rayuwa ama haka kika jure kika bar ma Allah komai, Bestie ki nasan inhar Daddy ta yasan gaskiya zai barta ku cigaba da kawaceku by God grace,. But for now you are my bestie" ta saketa ta ja mata kumatu ta juya baya tana tura baki tace" ina kishi saboda anfison wancan bestie akaina"

Essha tayi dariya ta rugume ta Tace" haba dai Yar lukuta na you are so special ai kinji ko? Ita ma ta ja mata kumatu tace" duk ki bi ki Bata mana Arundh da rigima" duk suka sa dariya ..

Pooja tayi gyara murya da gani tsokana zata nema tace" uhm Mrs Aliyu, dagaske wancan Dana gani taredashi matarce?

Essha Bata amsaba ta ja dogo tsaki, taja pillow tana kumbere kumbere ta fita daga daki zuwa daki Pooja, tana shiga ta aje pillow ta fada toilet ta watsa ruwa, tafito tasa riga da wando na bacci ta zauna tayi addu'a baci ta gyra kwanciya a gefe Arundh, ta ja bargo ta rufe musu jiki Tana sauke ajiya zuciya, tana son tayi bacci ta kasa, data rufe Ido fuska Aliyu take gani, haka kuwa baka ta mata Rai yakeyi ta ja dogo tsaki ta dauki abun rufe idon na bacci tasa duk da haka bai hanata sake gani shi ba, sai tsaki take ta ja a haka bacci barawo ya saceta..

Kiraye kiraye sallah assalatu ne ya ta data, ta Mike da addu'a tashi a bacci dauke a bakita, ta bude kwaya idonta data rufe da rufe da mask na Ido ta ta sauko a hankali ta fice ta tada Amir da Sadik ta koma daki tashiga toilet tayo alwala ta fito ta shimfidar daddumar , tana shimfida wa aka fara sallah, tasa hijab har kasa tayi sallah ta a sukuni, baya ta idar ta zauna tayi ta Azkar sai kusan 5:45 ta Mike da sauri ta Manta ma flight din safe zasu bin, da saurita ta Kara hada kayayaki su day Amir baigama hadawa ba, tana kan hadawa Amir da Sadik suka shigo, Pooja na biye rike da tray ta shako kayan breakfast a ciki , Essha ta karba Tamata godiya ta Mika su Amir, Sadik yasa hannu zai tashi Arudh, Essha ta hanashi tace" barta tayi bacci ta"

5:53 harsugama shiryawa tsaf,Pooja ji take kamar tayi kuka, tasan ma nata kadane dun bataga su ba karamin lalashi zatayi ba.

Ta kwashesu a motar zuwa Airports suna isa 6:00am na cika, da zuwa su ba'afi mintina b aka fara Kira jirgi zai daga, Pooja ta rugume Essha dukasu kuka suke na rabuwa da juna, Sadik ma kuka yake zai bar Aunt Pooja, Amir ya dagashi ya rugume suka shiga jirgi, Essha na biye dasu tana daga ma pooja hannu tana hawaye, Allah sarki ayi sabo azo a rabu ba dadi.

Essha na shiga ta duba seat number ta, ta zauna su Sadik na gabata ta Mike ta shafa Mai Kai , gyagadi yakeyi dun Sadik baida wuya bacci, Amir yagyara Mai kwanciya ya Dora Mai sit belts, video game karamin dake hannushi, ya karba ya ije Mai a gefeshi, Essha ta zauna itama Tana gyara belt nata, gabata faduwa yakeyi, ta lumshe Ido kamar Mai bacci tana ji jirgi ya daga ta saki ajiya zuciya tana roko Allah ya saukesu lafiya.

*Few hours later*

Nigeria gida, da komai lalacewarta Muna Alfahari da ita.

Nnamdi Azikwe international Airport Abuja.

Ciki ikon Allah jirgi su Essha ya landing lafiya, Essha naji su land ta sauke ajiya zuciya tace" Alhamdullila" ta kalli su Amir da bacci suke Hankali kwance ta Mike ta tada Amir, sanna ta samo tapping Sadik a hankali tace" Sadik wake up , open ur eyes, you in Nigeria welcome home" ta fada Tana murmushi

Sadik daji haka da sauri ya bude ido ya juya ya kalli kofa yaga har anfara sauka ya mike, sit belt ya dawodashi, yasa hannu ya cire belts din ya Mike zai yi hanya fita, Amir ya rikoshi Yana dariya da turanci yace" easy boy, Allah Allah kake kaga kasarna ko? To gode ma Allah first"

Sadik yayi murmushi yace" Alhamdullila"

Essha gani kallo da waensu daga ciki passengers din ke bin Sadik dashi ne yasa ta tsargu da sauri ta dauki hanbag nata ta ciro face masks baki tasa ma Sadik Wanda kwaya idoshi da tunda hanci kawai ake iya gani

Amir yabata fuska yace" sis yaza ki rufe Mai fuska Kuma?

Tace" Amir sauko kawai muje nasan su mummy nanan suna jiramu Kar mu Bata musu lokaci"

Amir bai tanka ba ya rike hannu Sadik sukayi gaba, tana biye dasu, suna sauka, Essha tayi hanya guri kwashe musu Kaya da har ta hangi su mummyko, Sadik ya saki Hannu Amir, yana ihu murna Yana zangeya Airports din Yana" ye am in Nigeria, am so happy" Yana kan ihu da tsale ne yaji ya buge mutum, video game dake hannushi ya fadi, yadaga Kai yaga waya ya buge, yaga mutumi har ya tsuguna ya dauki video game din ya rike a hannu yadaga Kai Yana ma Sadik murmushi, La Isa ne kanni Aliyu ga uban escort Dina na fama a bayashi..

Sadik ya tsaya kalloshi shiru ..

Isa yayi murmushi yace" little boy ka buge ni ka kasa bani hakuri ko? To banza baka video game naka ba har sai ka ce min sorry"

Sadik baigane maiyake nufi ba shi fuskarshi ma kawai yake kallo Yana shafa nashi fuskar, abun mamaki yake bashi yaga Mai kama dashi(lol yaro dama baka ga Daddy ka ba kenan)

Isa yakara maimatawa yace" tell me sorry"

Sadik naji haka yayi murmushi yace" sorry uncle"

Isa yayi murmushi yace" boy gayamin sunaka, maiyasa ka rufe fuska bakaji zufa ne?

Sadik da bagane hausa yakeyi ba sai bin bakishi kawai yake da kallo, can yaji Uncle Amir na kwala Mai Kira ya juya da gudu tabar guri"

Isa Yana" tsaya ka karbi game na ka"

Sadik bai tsayaba bai ma fahimce abunda yake fada ba,juyawa kawai yayi yadaga Mai hannu..

Isa yayi murmushi Yana kallo video game din, ya Mika ma daya daga ciki security dake bayashi yace" bin bayashi Kai kaimishi"

Ya amsa da "okay sir"


Sadik kafi yaisa guri dasu mummyshi sukai sukayi kicibus da uncle Amir,

Amir yace" Boy bakaji ko?zaka daga ma mummy ka hankali Ina ka shigane?

Sadik yarike hannushi yace" let's go uncle" kamar bashi Amir ke ma fada ba.

Amir ya dafa goshi yace" ohhh gosh sai shirmana nake bai ma ji abunda na fada ba, ke kam Sis Zaki banu da Daddy, Boy ko zo na kashe ka da hausa baisaniba"

Sadik yajijiga mishi hannu yace" uncle what are you saying?

"Ohhni Amir, I said let's go" ya rike hannu suka Kama hanya, tunkafi su isa Amir ya hango su khairat Walid harsu hunaisat da Aina'u, motar biyu suka zo dashi.


Walid da mufeedat dagudu suka zo suka daga Sadik, Essha na tsaya a gefesu tana murmushi tace" what!! Tuntuni Ina tsaye babu Wanda yamin Oyoyo, wato boy naku kadai kuka gani ko"

Walid dake rugume da Sadik yayi murmushi yace" Eh ni shi nazo tarba my one and only son"

Essha tace" oho dai Nima ganawa mummy zanje na rugumeta" ta fada tanufi guri mummydake tsaye sai fama zuba murmushi take da gudu ta rugumeta tace" Oyoyo mummy na I really miss you"

Ta kalli gefeta tagasu hunaisat tace" lah Sis hardaku, a lallai kuyi kokari" ta zunguri Aina'u tace" Mrs Usman mijiki Mai ra'ayi tsiya na haryabaki kika fito da wanan tsoho ciki Kai lallai ni Yar gatace"

Aina'u tayi dariya tace" ai Yana ciki Yana ji ki" ta fada Tana nunanu ciki motar..

"Ohh ni Yaya Usman bai canza ba shine ko ya fito"

Hunaisat tace" kaima ai ba canzawa kikayi ba surutu da shagwaba nanan"


Essha tayi dariya ta Kama baki tace"nayi shiru, ina tsohuwa Mai ran karfe?

Usman yafito daga ciki motar Yana murmushi yace" tana na ta shirya Miki liyafa sai Wanda ki ka zaba , ni fa Boy Dina nazo tarba bake ba, ina yake?


Essha ta tura baki a shagwabe tace" kowa boy boy yanzu shikena a cikiku ba Wanda yazo tarba na guri boy naku ku ka zo, ni Ina Daddy na? Nasan shi zai kulani ai"

Duk suka sa dariya, mufeedat tace" Daddy yayi tafiya sai gobe zai dawo yace mubaki hakuri, Daddy karami kuwa baiji dadi jikisane shiyasa bai zo ba"

"Allah sarki" Essha ta fada zatayi sake magana mummy ta dakatar da ita " yarana hiraku ba Mai karewa bane, ku zo mukarasa gida ko cigaba, ina shi Wana raino jajaye kunnuwan yazo mutafi"

Khairat tace" Kai mummy miji naki ne raino jajaye kunnuwan toh anfasa aure da ke da anty zainab ko big mum za'ayi"

"Oho dai Nima bance inaso ba" mummy ta fada cike da barkwaci duk suka fashhe da dariya...

Duk suka shiga motar, ciki motar su mummy kowa na zumidi taba Sadik, kowa naso shine ace ya zauna kusa dashi, Amir ya raba fada ya Dora Sadik a cinyar shi, zasu tada motar kenan aka fara musu knocking, mummy ta zuge glass din kasa taga baki mutum maiji da Karfi yasha black coat da eyeglass baki mummy tace" yadai lafiya dai ko?

Yace" yihakuri Ma, yallabai ne yaban wanan naba wani yaro danaga yashiga motar na, nashi ne" ya Mika mata video game din, mummy ta amsa Tana juya a hannuta tace" Aya nane ba Bata hanya kayi ba?

"Yes nane, yaro na sanye da facemask baki Dana bi bayashi motar na yashiga"

Tace" oho " ta juya ga Sadik dake back sit tace" kai renon masu jajaye kunnuwan nakane, ka wani sa facemask na rigima da basan dalili sawaba"


Sadik da baji yaren ta yakeyi bA hannu kawai yasa ya karba, tace" iyye ina ma magana baka ba amsaba shine kawai zakasa hannu ka karba, kaji min yaro"

Sadik kanshi na kasa Yana kokari kunna video game din baimasan tanayi ba"

Ta juya ga security tace" mungode a ma wani yallabai kenan?





Happy Juma'at Kareem 💓 💓💓💓 💓💓💓



Comment and Share 🥰

Love you guys 😘😘



👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️



*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️



*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
_________________________



6️⃣4️⃣&6️⃣5️⃣

Security yace" oga nane" ya Bata amsa ya juya yayi wucerwasa..

"Oga nane? Mummy ta maimatar amsa da yabata..

"Shi oga nashi baida suna ne, a'ina Sadik yasashi daga zuwa shi" ta juya ga Sadik" Kai Raino jajaye kunnuwan ai'na kasashi daya baka wanan?

Sadik hankali kwance game nashi kawai yake bugawa, Amir najita yayi tsit, dayasa inyagayamata Sadik wani dramer za a kwashe, gwara yayi shiru insu je gida tasani..

Walid dake gefesu yace" Boy, Granny na magana dakai ka mata shiru" ya fada Yana shafa Mai Kai.

Sadik ji ankira Boy, granny yasa yadago Kai ya kalli mummy.

Mummy tace" ugo na nabaka, ko uwarka ina magana Bata share ni balle Kai tasisi dakai"

Sadik yanayi yanda take Magana ne yabashi dariya harda kyakatawa shi, duk suka zuba mishi Ido.
Khairat tace" Walid cire Mai abun fuskar na yasha iska"

Walid kamar jira yake yasa hannu ya cire Mai face mask din, daga mummy harsu duk suka bude baki suna kalloshi, yanda yake dariya gwani sha'awa..

Mufeedat ta Kai Hannu daidai dimple nashi tana murmushi tace" wow I have a cute boy, Kai wlh saina kaishi school dimu, na nunama Yan ajimu, yaro sister na Mai kyau ne"

Khairat ta harareta tace" pheeeww, go away, ni ne zan riga fita dashi bakai ba"

Walid ya dagashi daga cinyar Amir ya dawo cinyarshi yace" duk ku Gama ci musu ku bai inda Zaku je dashi, Kuna Mata ina zai biku, toh tare zamuriga fita yawo, ba Wanda zai bi a acikiku, nagaya muku kenan"

Amir gani kallo da mummy ke bin Sadik dashi ne yabashi dariya yayi dariya yace" yadai mummy,karfa gari kallo miji wuyaki yayi ciwo" ya fada cike da barkwaci duk suka fashe da dariya..

Mufeedat tace" mummy ta ga miji cute boy ta rude, ta kasan daina kalloshi, please mummy ki juya Kai ki kalli gaba Kar wuya ya Miki tsami" duk suka sa dariya harda kyakatawa..

Mummy batace uffan ba, ama yanayi fuskar ta ya canza alamu ba lafiya, ta juya ga driver Tace" muje Driver Kar mubata masu Usman lokaci"

Driver kamar jira yake ambashi umarni ya tada motar, Usman ma ya tada nashi tundama su yake jira, suka dauki hanya uke.

Suna tafiya ciki kowane motar hirar kawai ke tashi, Essha duk ta ishe su hunaisat da surutu suna biye mata, ciki motar su Mummy kuwa hira sosai ke tashi, su khairat sai selfie kawai suke ta kashewa, har Sadik ya Saba dasu.

Ita kam mummy duk jikita yayi sanyi dagani fuskar Sadik, sai zance zuci kawai take ita daya tana tambaya kanta" Aya Essha ba canza mata yaro akayi ba ko, dun wanna tabbas ko makaho ya shafa sai yaji kamani yaro tycoon Dina a tare dashi, toh Wai mashi ina Yan kungiya da tare Dan Tycoon da kullum da masu tsarosu? Aya Essha ba yaro su ta dauka ba ko? Eya yallabai dayasa a kawo Video game dina eya bashi bane mahaifi Wana yaro? Da ga alama nagani Wanda ya kawo daya daga ciki securities su ne, wanan yaro baza dai ace kamanine ba, jinine ke aiki cus Blood is thicker than water, wayyo Essha yaushe kika canza ne? Maiye abun naki Dan daki ka canza ki ka dauko Wanda su ka fi karfi mu? Maiye daliliki nayi haka? Toh shi asali Danaki ina kika kaishi? Ko dai mutuwa yayi ne?ki ka dauko musu reino Dan ? Ta rike haiba " No wonder biri yayi Kama da mutum shiyasa tun baya arbain ko sau daya ba ta taba bashi muji muryasa ba, ohh Essha why why, maiyasa kika yi haka, in daddy ki yasani munshiga uku, Essha na Allah yasa dai baki canzaba" Nan taji hawaye Mai dumi su sauko mata tayi sauri ta goge..

Taji driver na horn ya katse mata tunani data ke ciki, taga har su karaso gida, tayi sauri Kara gyara fuskar ta, maigadi ya bude musu , suka kusa ciki.

Manya manya flat ne guda biyu a jere, tsari gini yayi, daya bagare Daddy Karami, na gefe haggu Kuma na Daddy, gida Babba gida ne ya tsaru sosai ba amagana.

Sugama parking duk suka fito, Walid da Amir suka kwashe Kaya zuwa ciki, Daddy karami, Anty zainab da hajiya duk suka fito tarbasu da fara'a a fuskokisu. Essha na gani hajiya da gudu ta je ta rugumeta harda guntu hawaye ta.

Hajiya tace" toh likita karasa ni kikeso kiyi Wana Shaka haka"

Essha tayi dariya ta sake ta rugume Anty zainab, ta tsuguna har kasa ta gaida Daddy karami, ya amsa sai samata albarka yake tayi yace" ina aboki nawane Yana ina?

Ta juya ta duba dube" Sadik, Sadik"

Usman yace" su khairat ana sauka suka fita dashi, Nima ko ganishi banyiba"

Anty zainab

Please Login or Register in order to submit comment