Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar ta buge Mai hannu dun haushi takeji ama ina duk ta tsorata gashi kunya ya guri take.

Aliyu yatsa middle finger shi yana share mata duk wani digo hawaye dake zuba murya kasa kasa yace" Baby please open your eyes ninefa, Aliyu your husband ko ki manta ni ne?

Ya Kara matsowa daf da ita harsuna ji numfashi juna..

Ammi da Mami a sanyaye suka kalli juna ko bai fadamusu ba su gane wanane Essha..

Aliyu ya shafo fuskarta murya kasa kasa kamar zai Mata kuka yace" please Baby open your eyes, I really miss them kisan hali da nashi ga kuwa na Rashi ganiki, please love"

Siyama, Sofia da Rahma gani fuskar Essha ne yasa su bude baki harsu na hada baki guri cewa"wow Yaya yasamu Mai kyau"

Aliyu zai Dora hannushi akan waist nata, Fawaz ya katseshi da sauri Yana murmushi da ko ba'a fadamai ba yagane, cus no girl can make his buddy go Gaga like this sai Wana Mai zubi huru'in din, Suhaima kam dama bana Allah bane toh gashi gaskiya tayi hallisa" ya kalli gefeta yaga sai zare Ido take cike da tashi hankali, duk tagama jikewa da zufa duk Ac parlor , Fawaz yaja karami tsaki yace" baki ga komai koba yanzu aka fara yau sai kiyi nadama zuwaki duniya"

Ya mayar da hankali shi kan Aliyu yayi murmushi Sana yayi gyara murya daya ya farfado da Aliyu lovers mood dayaso fadawa dun ya ma manta akwai mutani a parlour..

Fawaz yace" Buddy kabar su Daddy fa a duhu ka fahimce musu komai"

Aliyu ya shafa Kai cike da kunya yayi murmushi yace" oops sorry " yaje gaba Ummi ya riko hannuta ya jawota har gaba Essha yace" Ummi ga Mata na Essha Wanda ki ke Kira da Aljana toh gata yau a gabaki"

Ummi da bude baki tana bin Essha da kallo mamaki..

Tycoon yace" Matar ka? Where? When did you meet her?

" Eh Daddy matace itace Wanda Yan kungiya na suka daura min aure da ita 7years back, guess what dad? She's the love of my life Ammi Mami meet Essha"

Ammi ciki Rashi fahimta tace" Wanda Yan kungiya suka aura ma how?

Suhaima ta Mike a fusace jikita na kalli Aliyu tace" What Aliyu? Calling this.....

Aliyu ya katse da sauri yace" hey hey don't you spoil my mood keep that ur stupid mouth shut"

Suhaima ji haka tsoro da fargaba da take ciki ne ya tsanata kamar tasa hannu akai ta zabga ihu takeji, a ranta tace" Wana Mai kama da Aljana kenan true love nashi, wayyo Allah na shikena Aliyu ya kubce min, wlh bazai yuba"

Su Ammi mamaki ya cikasu yau Aliyu ne ke ma Suhaima tsawa harda kirata Stupid, Ammi ta rugume hannu ta tabe baki..


Daddy ya Mike ya nuna Aliyu yace" Dama Kaine suka aura matar?

Aliyu ya sukunyar da Kai yace" eh nine"

Daddy zaiyi magana Essha ta juyo da sauri tasoma ja hannu Daddy Wai yazo su fita.. ciki kuka take rokon Daddy ta yazo su barna ita baza ta zauna ba.. a lokaci ne Sumy taga fuskarta ..

Ta bude baki cike da mamaki ta Kira sunata"Bestie"

Fawaz ya kalleta yace" dear ki santa ne?

Sumy ta kada Kai Tana hawaye..

Essha ji murya da tasani ne Kuma baza ta taba manta da Mai murya ba yasa ta juyo a hankali, Bestie ta tagani, Sumy na kuka tazo da gudu ta rugumeta dukasu suka fashe da kuka..

Sumy tace" Kiyemin Bestie please forgive me nasan ba kyauta ba na barki a lokaci da kike tsanani bukatana, please forgive me"

Essha ta tapping baya ta a hankali tace" bakomai ni bakimin komai nasa bayi ki bane"

Ta juya ta kalli Daddy tana share hawaye tace" Daddy please kazo mu bar na ba wuri zama na bane"

Aliyu ya karaso da sauri Kamar zaiyi kuka yace" No Baby da Allah karkitafi, I have suffered a lot, please stay, Ammi da Mami na za suyi murna da zamaki please don't go"

Ya zuguna kasa gaba Daddy yace" please kuyafeni, an daura min yarka bada izinikaba, bayi kaina bane, please forgive me da Allah Kar kutafi, wlh ina sonta please"

Tycoon ya nufesu ciki Rashi fahimta yace" Wai maikefaruwa ne? Aliyu kasa su ne?

Aliyu ya Mike da sauri ya rike hannu Tycoon muryashi na rawa yace" Daddy , Essha ne da Daddy ta da Allah kace musu Kar sutafi"

Tycoon ya kalli Daddy yace" Da Allah ka ganar da mu, nakasa fahimta inda Aliyu ya dosa"

Daddy ya ajiye numfashi takaici Aliyu yakeji wato ma iyeyeshi basusan da maganar aure ba, ya numfasa ya kalli Aliyu da duk a rikece yake yasake maimatar Mai tambaya da Kaine mijita?

Aliyu ya amsa da sauri, Daddy ya kalli Essha dake kuka a gefeshi yace" wanane mijinaki?

Ta amsa da Kai..

Yace" shine mahaifi Sadik ko?

Tasake gyada Kai Tana rike da hannu Daddy ta duk a tsorance take"

Tycoon ya kalli Daddy yace" Duk girma Allah na rokeka ka fahimta damu"

Daddy ya kalli Aliyu yace" Bani aguri akayi Aliyu Basu labari abunda ya faru"

Aliyu ya sukunyar da Kai kasa can ya dago Yana kallo Essha da haryanzu Bata bar kukaba ya yamutsa fuska her cries hurt him sosai ciki sanyi murya,kwala nabin gefe fuskar shi yace" Daddy kayi hakuri basanardaku ba, kune a lokaci ku kasa fahimta na, nobody believe wat am saying, Ummi ta Kara rikitar da zance da cewa Wai da aljana nayi gamo"

Ya rike hannu Daddy yace" please ka fahimce ni, nasa bakaji Dadi cewa iyeyena Basu da da maganar aure na da Essha ba, please ka....

Daddy ya katseshi" Aliyu baka da wani baki da za ka Kare kanka, ga Dankana mu bar maka, Essha zo muje"

Daddy Ya ja hannuta zasu fita ta juya tana kallo Sadik, ya biyosu da sauri ya rike Hannu Mummy shi ciki yare da yasaba magana yace" Mummy ina zakije, maiyasa Mai ki kike kuka?

Daddy ya juyo ya rikeshi yace" Sadik kana so sani waye Daddy ka ko?

Sadik ya kada Kai.

" Toh ga Daddy ka go and meet him"
Daddy ya nuna Aliyu.

Sadik ya juya cike da murna ya rugume Aliyu ya kalli fuskar shi Yana haweye yace" papa are you my papa?

Aliyu kuka yaci karfishi ya gyada Mai Kai, Sadik Yasa hannu ya share Mai haweye yace" papa why did you leave me? Did you miss me?

Aliyu kasa amsawa yayi ya rugumeshi kawai Yana kuka, Sadik ya kwanta a jikishi lamo he's so happy yau gashi ga Daddy shi..

Sofia tazo ta karbeshi a hannu Aliyu Tana nunamishi family..

Daddy ya kada Kai yace" Essha zo mu wuce"

Zasu fitar Aliyu ya dakatar dasu Yace" please Karka min Haka ka tausaya min"

Ya juya gun Tycoon yace" please Daddy ka gayamishi ba laifi na bane, Da Allah Mami Ammi ku ce wani Abu"

Ammi taji tausayi Dan nata ya kamata ta matso gefe Daddy ta gayamai gaskiya, tun lokaci da Aka hanashi Kar ya fita sai da securities yaki yayi tauri kai, Tass ta bashi labari harda batashi da ganishi da hali da ya tsince kanshi duka Ammi ta sanar ma Daddy..

Daddy yayi ajiye zuciya shima ya tausaya mai..

Ammi tace" da Allah kayi hakuri munsa laifi mune" ama sa muso muji yadda akayi aure, ni tundama tun lokaci da na daura Ido aka Sadik nasa jininane, da Allah ku zauna please"

Daddy ya kada Kai ya zauna..

Tycoon ya kalli Aliyu yace" toh Muna sauraronka"

Haweye da suka zubo masa ne ya share ya kalli Essha na waesu mintina Sana ya fara basu labari haduwarsu, haryakai karshe labari ciki kuka.

Kowa na parlour kuka yakeyi Dan tsanani tausayisu, kowa yayi shock daji labari..

Ammi ta taso ta rugume Essha tana kuka ta kwantar da ita aka cinye ta..tana lallashi ta..

Mami Tace" Allah sarki Essha ke nafi tausaya ma, baya rabuwaku wani hali kika tsince kaki?

Essha na cinya Ammi ta kada Kai ta Soma Basu labari har zuwata karatun a India har dawuwata kasa shekaran jiya..
Su Ammi su matukar tausaya mata
Fawaz da mamaki ya kalleta yace"dama kece Dr Aisha Ahmad?

Ta gyada Kai..

Tycoon yace"Allah Mai ikon"
Ya kalli Daddy yace" lallai kacika uba nagari, kayi abunda mutani dayawa zasuyi koyi dakai, gaskiya naji dadi haka"

Ammi ta share hawaye ta kalli Aliyu tace" ya'akyi ka Manta baya bikika ka Manta da ita, ba ka nemanta ba"

Ya daga hannu yace" ni kaina basaniba, I don't know why"

Parlour gabadaya yay tsit.

Suhaima zuciya ta na tafarfasa da za'a barta wuka saf zantaiya kashesu bin kowa take da harara..

Idrees ya katse shiru da cewa" Bro magana infertile naka dat means kwa daya kake dashi kenan a duniya, kenan daga Sadik baza ka sake haihuwa ba?

Fawaz ya amsa Rai a bace" wanan karyane" ya nuna suhaima yace" yau dubuki ya cika"

Suhaima ta mike a razane tace" Mai nayi dazakace min dubuna ya cika"

Fawaz yay dariya yace" agayamiki duk abunda kikeyi bamusanibane"

Ya ciro wayarshi ya daga musu yace" Ammi Mami duk hali da Aliyu yashiga...



Manage please πŸ™πŸ™πŸ™






Have a lovely dayπŸ₯°πŸ₯°

Inayi ku iri trillions DinaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ


*WRITING BY*
*J Hajara*



🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“š πŸ–ŠοΈ

*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
______________________________


7️⃣3️⃣&7️⃣4️⃣


Fawaz yace" Ammi Mami duk hali da Aliyu ya shiga Suhaima ce sila, Kar guga laifishi, Aliyu laifiyashi kalau he's normal, Suhaima gata itace Mara lafiya dun adade da cire Mata mahaifa sakamako abortion da ta rigayi haka yajawo lalacewa maihafarta shiyasa akacire dun ta cutar da Aliyu shine ta Dora mishi cewa Wai baya haihuwa toh karyane baki take hadawa da likitoci tana bribing nasu suke canja ma Aliyu results"

Dukasu suyi shock daji Wana labari..

Ummi ta tafa hannu tana sallati tace" Ashe ke tatiriya yariya ne aka aura ma gadangana Yaro kirki wlh nikam ki cuci rayuwarshi Allah ya isa bazamu taba yafewa ba"

Fawaz yace"Ummi Wana Suhaima dakike gani toh tafi Haka dun har asiri tamishi d......

A fusace Suhaima ta katseshi tana Bari tace" wlh karya yake duk abubuwa dayake fada muku karya ni lafiya na kalau Bata yi abortion ba bawani namiji danataba sani imba Aliyu ba, ba wani shaida da zai nuna cewa asiri nama Aliyu yanasona inasonshi tundama baki ciki kuke gani na da Aliyu toh ta Allah bataku"

Fawaz yayi murmushi yace" kigama cika baki ki yau sai na tona asiri ki, yau dubuki ya cika"

Ya bude wayashi ya daga masu Tycoon yace" Daddy Wana document dakake gani results din Aliyu ne da Suhaima na last da suka je duba a babba asibiti dake Delhi, l
Rashi gani dawuwarsu ne yasa Doctor da ya dubasu ya tura min da results din ask you can see komai ya nuna Aliyu lafiya shi kalau, Suhaima ne bama ma mahaifa a jiki ta"

Su Ammi duk su rude daji Wana batun mamaki ma yahanasu cewa kala.

Uban gaya zuciya shi sai tafarfasa takeyi Kama anasaminshi fetir yaji duk duniya ba Wanda ya tsana kamar Suhaima fuska na ya hadashi tam.

Suhaima ta karaso gabashi tana" Darling wlh karya yake baki suka hada da likitan da Sumi shairin wlh karyane"

Aliyu ya tugudeta ta fadi..

Fawaz yace" in karya nake akawai shaida da zai prooven dina gaskiya ina zuwa"
Yafice a parlor can saigashi ya dawo da feenat kawar suhaima binyedashi sai wani matashi sanye yake da suit da labcoat Alamu dai sununa likitane.

Suna shigowa Suhaima nagani Feenat gabata ya tsanata faduwa sai zufa takeyi ba kokwartawa, ta bude wayata da sauri ta ma Feenat Text da cewa"
Da Allah Feenat Kar kitona min Asiri kimin Rai, today is a bad day to me da Asiri dake ke Kai Aliyu yariga da ya warware please ki rufan min Asiri" ta tura mata..

Feenat ta bude text message din taja tsaki, ta kalleta ta baka Mata uban harara Sana tace" ke walahi kiganina bana tsoro a mutu tunda har asirina ya tuno toh nakowama sai ya fito, wata ke Suhaima na Miki Ranar shine kika sakamin da tsiya harkiiya samu mijina kigayamishi Dan Dana haifar ba nashi bane ki Kuma kwana da nawa miji kiban kunya.toh walahi talahi yau ba'abunda zai hanani na fasa Miki kwai da kika Dade kina tarairayashi, jama'a ku ganta Nan ita da uwarta suka asirice muku Dan har ya manta da masoyiyarshi Soyaya duniya ya Dora Mata.. nasan halita Sarai zata iya min butulci ko wataran ta wasan min kasa a idon shiyasa Ranar da aka kawo magani duk abunda suke fada nayi recording gashi"

Ta bude wayata ta play musu record duk abunda ya wakana tsakani Hajiya Binta da su.. sanda sukaji gabadaya sanan tasa stop,

Aliyu naji Hadi dayasha yaji wani Amai na tasomai watama ma madara akabashi Wanda aka tatse da pant, pant dima na waina kazamiya ya rike kirjishi yana" wayyo Allah na Suhaima ki cuceni ki gamadani"
Suhaima ta rike mai Kafa tana kuka tace" Da Allah kayafemin walahi Sonka ne yaja"

Feenat taja dogo tsaki tace" walahi karkayarda munafukace, maihafa data ke karyatawa toh gaskiya tun kafi kuyi aure ta zubar da ciki da yakai Hudu karshe mahaifata ya lalace Wana likita ya cire gashi agabaku ku tambeyeshi bazanyi karyaba, toh intankaitama inbaka a gari toh tana hotel da sugar daddies, kai mutuwar mahaifitama bana Allah da Annabi bane uwarta ta kashe dun suci dukiya kaima su so su kaika Allah nasoka shiyasa haryanzu kana numfashi"

Aliyu yarike Kai Yana sallati, su Ammi duk su girgiza daji labari, Tycoon ya nemi guri ya zauna a hankali Yana haweye yayi nadama sosai, dun shine sila..


Feenat ta girgiza ma Suhaima takada dake hannu ta Tace" ki gawana takkada saki ne datzu mijina ya yakamin saboda ke, haka ya tunzurani yasa Nima na rama kiji ko da dadi, Ur own case is different kiga tafiyana Kuma wlh daga yau ni dake muraba jaha, zan koma gida iyeyena na tuba na koma ga Allah Allah yasa dai haryanzu ubana da Rai" ta karkada gyalete ta fice..

Suhaima ta kifa Kai a kasa ta wani fashe da kuka Mai uban kara tana fizge fizge..

Aliyu Rai a bace yace" Suhaima na sakeki na sakeki na sakeki, I curse d day I met you in my life, ki cuceni ki rabani da masoyita kisa Dana yatashi aciki marairaci alhali ubashi na raye, ki tashi ki ficemin daga gida kafi na halakaki bazata ba yafemikiba" ya daka Mata tsawa da r
Tsanda mutani dake ciki parlour suka tsorata.

Suhaima ta Mike tana dariya tana kuka tana fizge gashi attached dake kanta sai ta koma Kamar mahaukaciya tace" Aliyu ka sakeni wlh nikam inasonka duk Wanda ya yunkuri rabamu sai na kasheshi aure mu na na daram dam bainda zaje.. ke Essha ko wakike da Suna"

Ta nufi Essha ta zata kaimata Mari Siyama ta rike Mata hannu ta zuba Mata lafiyayu maruka guda biyu tace" kul banza Yar matsiyata ko da Gigi wasa Kar ki kuskura kice Zaki daura hannuki akanta, dun ta fi karfi ki, saboda Haka ki Kama hanya ki ficemuna a gida Wanda akasashi dole ya auroki toh ya koreki sai ki bacemuna dagani Banda kadarama ba Mai Yaya zaiyi dake dubekifa Kamar Soyeye gadagare, ai Yaya sai ita saboda Haka fita, wlh ko kallota Kika sake yi sai na kwakulo Miki Ido waje kisani Sarai oya pak and go"


Zata fita Ammi ta tare ta rike Aliyu tace" gadangana yhkr ka yafemata taje can taji da hali ta kaji please forgive her"

Ya girgiza Kai Yana haweye yace" No Ammi bazataba yafemataba she's a witch a bitch I will not forgive her, let her go ko fuska ta ma banason gani na tsaneta I hate her I hate her"

Mami tafara tapping bayashi tana bashi hakuri ya yafe mata yaki Sam cewa shi bazataba yafe Mata ba.. Tycoon kuwa uffan baice ba dun yasa Aliyu da kafiya yasa suna Bata lokaci su ne kawai.

Siyama ta rike hannu Essha tace" Sis beauty kiyi hakuri please da Allah ki bashi hakuri ya yafemata she need his forgiveness ko zata samu rahma Allah. Kiji Sis please kije"

Essha ta kalleta shiru ta share hawaye can ta girgiza Kai Alama zataje..

Siyama tayi murmushi tace" thanks my beautiful inlaw"

Isa ya zungure ta a goshi Yana dariya.

Essha ta tako a hankali ta isa gaba Suhaima ta rike Mata hannu, kowa yayi mamaki da haka..
Suhaima tana kallota tana huci jitake Kamar a Bata wuka ta bulla Mata ciki..

Essha na kallo iri kallo date ke binta dashi sai Bata damu ba tayi kakulo murmushi ta Soma magana ciki sanyi murya tace" I don't know your name, but abunda zafadamiki shine a rayuwa baki kyauta ma kaki ba, ki aikata abubuwa da yawa ama haka basa kiyi nadama ba why saboda kina biyewa son zuciyarki, I know it's not easy to love da bai San kinayi ba, when you love maimako ki tuna da Allah sai dat moment ki ka Manta dashi Kika biyewa son zuciyarki,toh yanzu wa gari ya waya... Ur friend naki daki ka trust ga abinda tasaka Mikidashi.mijimiji ki dakikeso,har Saba Allah kikayi dun ki samu sonshi gashi yau ya sakeki tundahaka ba alamu nadama a idoki yanzu ma nasan a can kasar zuciya ki jikike kamar ki kasheni,u have kill urself silently u have ruined ur life"

Suhaima kuka take sosai Mai kashe jiki..

Essha ta cigaba da Mata nasiha Wanda ya kashe jiki Yan parlour gabadaya ba Suhaima kadai ba.. kowa ka kalla da haweye a idonshi...
Tycoon dasu Ammi suka Kara ji son Essha sosai.. dukasu murna suke su Sami surika nagari..(😯hmm ni banzace komai ba πŸ˜†)

Suhaima kalamai Essha su kashe Mata jiki na take taji wani nadama da tsoro Allah yashigeta kuka take sosai tana tsine ma Mummy ta itace sila dun ko sau daya Bata taba santa a hanya tanuna Mata cewa what she was doing was wrong Bata Mata fada.. yau stranger ne wace ta tsana take gayamata gaskiya.. " mum I hate youu I hate youuu"

Ta rarufo tazo gabasu Ammi Tana rokosu gafara su yafemata abunda tamusu... Su tausaya Mata sosai sukace su yafe... Tazo gaba Aliyu da sauri ya kauda fuskar shi baima son gani ta.. .. ta Soma rokoshi ama ko kallo banza bai Mata ba.. sanda Essha ta sa baki sana yace ya yafemata.

Aliyu na cewa ya yafemata ta rugume Essha tana Mata godiya sanan ta fice a guje Tana kuka Mai cin Rai.. ko motar Bata hawa ba ta fice a guje batama San inda kanta yake ba.. harta zo baki titi tasa hannu a Kai tana regretting zuwata duniya.. harta shiga titi batasaniba motar dake baya ta sai horn yake Mata ta kauce a hanya dun ta kasa dun Bata ma jishi ga motar burki shi ya kunce haka motar na yayi sama da ita datsake dawuwa ta fado jiki motar jikake kakaskas ta gama karyewa motar Taki tsayawa haka yasake hayeta Mai motar dagani haka bai tsaya ba ya Kara motarshi wuta ya gudu. Mutum a cika akanta dun Suhaima Rai yayi hali sa. Gashi guri babu Wanda ya sata.. Allah yasa ta fito da waya, da motar ya daga ta waya ya fadi a gefe titi wani ya dauko yaga fuskarta ne a jiki waya, abun takaici waya na security, Yana da Ilmi aka waya nadana yashiga Emergency yaga numbobi uku tasa tanada My darling my mum saina my Best friend.. ciki sauri ya dialing number Aliyu yanata ringing ba'a dauka ba, Aliyu nagani kirata yayi banza da Kira yazata. Intace ta kira.

Kira na tsinkewa gani bai Daukaba yasa ya dialing number my mum ... Buga daya Hajiya Binta ta dauka cike fara'a tace" My love yau she Kika dawo kasane?

Mai Kira yace" hajiya baitabace kizo da gagawa ba lafiya"

Hajiya Binta a rikece ta Mike Tace" maiyefaru maiyasamin Baby na?inashi Aliyu yake?

"Hajiya ni basaniba kawai kizo da gagawa" ya gayamata Address din wuri..

Bata kashe waya ba ciki tashi hankali ta dauki car key ta shiga motar ta fice a guje ba'a jima ba ta karaso wuri gani mutani su taru yasa ta fito da sauri ta nufesu gabata na faduwa.. tana zuwa Mai zata gani Suhaima tagani motar ya tataka ta Dakar zakaiya ganeta tasa wani mahaukaci ihu ta yi wurgi da wayata ta fado jiki Suhaima tana kuka kamar zarariya tana" Baby na baki mutuba u can do this to me nooooo never wake up" ta riga jijigata tana kuka can kaji shiru.. mutani da. Ke kasu suka daga Mata hannu sukaji Alama itama ba rai. Ashe hadiye zuciya tayi ta mutu..

Mutani susha mamaki haka masu Imani da tausayi suka kwashesu akaisu masalaci aka wanka sutura aka musu Sallah akai kaisu makwaicisu.. har a jarida sanda aka buga har gida television duka..





😁😁😁😁😁😁😁


Juma'at Kareem πŸ₯° πŸ₯° lovely Readers na gode da kulawarku.. kuyi manage please haryanzu da mutani Muna busy Sosai

Nasan Nama Sallah nan na ba kareba πŸ˜πŸ˜πŸ˜‹πŸ˜‹ toh in aci dai ariga surka da lomotil da tauna dabino da tsaro badai tsoroba Kar ciki yaje operation da toilet nidai baruwana πŸ˜†πŸ˜†
πŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸ€ΈπŸ€Έ
Have a great day ❀️❀️
Love you guys πŸ₯°πŸ₯°




πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
Β  Β  Β  Β  *DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

*Written by J Hajara*

🌍 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈβœοΈ

Β  Β  Β  Β  Β  *M. W. A*

Β Β  '''Kungiyar d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www. Facebook. Com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________

*Bismillahi Rahman* *Rahim πŸ™*

*ALHAMDULLILAH*
πŸ˜ŒπŸ˜πŸ˜ŒπŸ€—πŸ˜€πŸ˜ŒπŸ˜πŸ˜Œ
7️⃣5️⃣


Mutuwar Suhaima ya kidimasu sosai, Tun tun ma Aliyu sai jikisa yay sanyi ko ba komai Matar ce then, Essha Kam har kuka sanda tayi.. Nan Parlour tsit kakaji saboda mutuwa ba abun Wasa bane( Allah yasa muyi kyakkyawa karshe)

Bayan wasu mintina, Tycoon ya Kira kanishi Mai Yakanaje Sarki Uke yafadama mishi suna zuwa.. Dakar Daddy ya yarda ya Amince zai bisu, yaso shi da Essha su wuce, su Zo su samaishi a garin, Bayan da ya iya haka ya hakura ya Kira Daddy k ya sanar musu a gansa su fara yi gaba zasu Zo su saimaisu a gida.. Daddy k na ta Murna ya sanar ma Inspector, inspector Wani iri yaji ya ba Daddy k hakuri, Daddy k yayi Murmushi yace" Kar kadamu na fahimta ai aikika kakeyi" Nan su dasu Walid suka Kama hanya.


Tycoon yasa aka shirya Motoci, Yan gida gabadaya Suka shirya zasuje dama suyi kwana Biyu da Zuwa..
Aliyu yaso yashiga Motar da Essha take ama Ammi ta kasa ta tsare sanda taga yashiga wani daban tukun hankalinta ya kwanta.

Motocinan sun jero Hanya Sai gudu kawai suke, Essha da Besty Motor guda suke, su na ta Sha hirarsu har Pooja ta Kira suka gaisa.yanda Essha ta riga Hira da Pooja ne ya kashe ma Besty jiki, Taji aranta shikenan ta rasa Bestfriend dinta Nan Haweye ya soma taruwa ma ta Essha na waya hankali ta ya dawo kan Sumy gani yanayita ya canza, ta sallami Pooja ta dafa Besty murya a hankali Tace" Besty.." Sumy ta daugo a hankali Tana kallonta, Essha Kai ta girgiza a hankali ta na Murmushi tasan halin Besty ta da kishi Ashe haryazu Bata canza ba..
"Besty Ke kadai ce Besty na after you na you saboda haka Kar kidamu kanki inaji dakai sosai a
Har ciki Raina Ba'abunda ya canza Kuma Pooja Bata da Matsala Ina son kema tazama friend dinki.." Essha ta Fada tana ma ta cakulkuli. Besty tasoma dariya tana share haweye ..

Essha Tace" Kar dai Pooja ta kwace mike nasan halinta "...

Dariya Suka fashe dashi..
Ba'a fi mintina ba Essha tasoma Bacci dama da gajiya Hanya a tare da ita..Bacci ta take hankali a kwance
Besty hankali ta ya koma kallo titi.. ba'a fi 40 minutes ba Suka karaso ciki garin Uke garin Gada.
Besty Kara zama Tayi tana bin gari da kallon rabon da Uke kusan shekara Tara kenan .. Babba Gadarsu(BridgeπŸŒ‰) take bin da Kallo taga yadda aka Canza salon tsari zuwa na kallan London

Please Login or Register in order to submit comment