Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kamar ya rugume ta ya ta shaka Kamshi ...

"10...9...8..7.." Mc take kirgawa cikin Babba Murya..

Essha daga ido tayi tana kallonshi taga duk ya rude, tasan ba'abunda yake dubawa, dun da Yana dubawa da yagani, sunashi na nane baro baro kwance tsakiya tafi Hannu ta an zanashi Mai style, bazata iya barishi ya ta ba ta ba, har ya wanke ma ta kafa dun tana tsoro fushi Daddy, haka yasa ta gyara murya yadago Yana kallon ta.Subhanallah is eyes are something they are melting her down, gira ta daga mishi shima yada ga mata, hakan dayayi ba karami dariya yaso ya Bata ba, idonta ta sauke kan sunashi dake kwance a zannashi ya zaunu kan tafi hannuta, yanabi kuwa idonshi karaf idonshi yasauke kan sunashi, ya Kai Hannu zai taba ta, tayi sauri jan Hannu baya, Aliyu nai nai yayi da ido kamar zai Mata kuka.. a zuciyata tace" like father like son ba inda Sadik ya baroshi a hali, duk komai nasu daya"
Juyo wa yayi ya shaida ma Mc ya gani, nan aka soma tafa mishi..

Sumy Sai murna take taxi betting, Fawaz kuwa Bata Mita wayo ta mishi..

Ancigaba da taro aka ci aka Sha. Su Sofia wakar Palak Mucchal suka sa aka playing na *Prem ratan dhan payoo* " sanda suka daga maza da Mata dun su shiga rawar Ango da Abokaina sa guduwa sukayi, duk kowa yasha rawar Prem ratan har su fi Essha Khan ma iya rawar.
Bayan antashi taro Ammi da kanta ta tasa keyar Aliyu da Sadik, dun tasa damu Essha zasuyi, tana kallon yadda Aliyu ke kallon Essha Kamar zai cinyeta har tausayi Essha takeji.

Angama taro kowa ya watse. Dayake a Uke za'a daura Aure, shi yasa su Ammi suka zo, duk suka tare a family house dinsu na Mai Yakanaje.

Washegari dauriAuren Young Tycoon Aliyu Umar da Amaryasa Dr. Essha Ahmad. Dauri Auren da yasamu wakilta Manya mutani na kasa dana waje..An daura kan Sadaki dubu Hamsin. Mallam Dagana da iyalasa duk su samu halarta daurin Auren, Harda kuka shi, dun ya tuna Dauri Auresu na farko an Hannu Yan Ta'adana kowa rike da bindiga hankali kowa a tashe.

Bayan daurin Aure,
Essha a cikin Gida ba'a take Sai kuka tun su Mummy na ma ta Fada har tasoma Basu tausayi nan Suma suka shiga tayata, dakyar dai Daddy ya lallashesu sukayi shiru.

Karfe biyu ranar aka shirya gagarumin Walima, wata Babbar Mallam suka gayato, anci ansha an watse Walima lafiya.

Misali karfe 4:00 akazo dauka Amarya nan Essha ido ya raina fata, akaita guri su Daddy duk su ma ta huduba zama Aure Mai ratsa jiki Essha ba abunda take Sai kuka, Hajiya tayi lallashi tagaji har ta koma Matsifa" Haba Aishatu Sai kace wata karama Yariya tun da safe kika ishe mutani da kuka ko ancemiki Aure mutuwa ne, ke ma a haka wai kisan Mijin kenan a Zamanimu ko kana kasuwane ko dadali haka za'a zo a dauke ace a daura ma Aure kiga kenan ku amuku Babba gata"

Su Besty ba dun son ransu ba su ka soma Dariya.. Essha kam kanta na kife a sama cinya Daddy Sai shesheka kuka take Su Mummy na gefesu.can ta dago ta kalli Daddy Murya kuka Tace" Dad.. Daddy Maganar zuwa Aiki na?"

"Essha Wana Kuma na Mijiki Zaki tambaya, yanzu yafimu iko da ke. rokona gareki shine ki kasance Mai biyaya agareshi da girmamashi.kisani Aljanarki na can karkarshi kafasa.Addua na shine Allah yabaku zama lafiya" Daddy yafada Yana share kwala.

Mummy zuwa tayi ta dagata" Essha bar kuka na, ya isa haka Kar kisa ma kanki ciwo kai, Masu dauka Amarya ke suke jira, Kar mu Bata musu lokaci.Stop crying okay ? I don't want to see my baby crying share haweye ki kinji Likitana"

Essha Kai kawai ta gyada tasake rugeme Mummy, Mummy Sai lallashi ta take, karshe kasa jurewa tayi itama tasoma kuka. Daddy dakar dai ya rabasu yakama Hannu Essha suka fito waje zuwa wajen Motar daukan Amarya, dama duk motoci ashirya suke ita kawai ake jira, Essha Kam turjewa tayi taki shiga Wai Sai Lallai tare da Daddy zata je, Duk ta birkice kamar Ba Dr.Essha nan na mu ba. Juyi duniya Essha taki shiga Motar ta rike Daddy Kam kamar zata cinyeshi tana zuba uba shesheka, Allah yasa ma ba make-up a fuskarta dun tsab da ya dagule dun kuka. Haka Daddy ba yadda yaiya yasa a dauko mishi car key dinshi Yasa ta ciki Motar shi shima yashiga Nan aka tada Motoci Daddy na biye dasu Sai Abuja, Bayan awa daya su isa, ba tsaya wani biye biye ba Direct katafaren Gida ta aka wuce da ita, dake gidama ba nisa Dana Tycoon duk an Tara dasu Ammi acan za'a yi buda Kai, Mamaki karara a fuskokisu gani Daddy Essha ne dakashi ya kawota Dakita. Tana fitowa wasu jere Mata sukazo da kayayaki a Hannu Nan aka daura ma ta Alkyaba Mai balain kyau, Ummi(Kakar Aliyu) handbangles(warwaro) na gold Mai kyau da sheki tasa Mata a Hannu na aka soma bita da Turare wuta ana guda, masu Algaita kuwa ana ta busawa kirari kuwa ba'a magana, duk da abubuwana tana na rike da Daddy ta Kam taki sakinshi. Yan guri abun har Dariya yasoma basu.

"Essha da kafa dama Zaki shiga Sana kiyi addua" Daddy yafada Yana rike da ita. Kai kawai ta iya dagamai dun muryata ya dishashe dun kuka, sanan tayi abunda yace. Suna Shiga bayan angama gai gaisawa Daddy sallamarsu ya fice da wayo Essha batasaniba dun tashiga Toilet fitowar tayi kawai bataga Daddy ta ba.. bayada taiya haka ta hakura, Su Besty Sai zolayarta suke ko Amsa musu ma batayi dun gabadaya jikinta a macce yake. Haka har aka Gama buda Kai su Ammi Sai ririta ta suke kamar Yar jikisu. Baya wasu Awani kowa ya watse, dun har Essha Khan, Arundh da Imran ma su koma, Essha Khan dazata koma su sha kuka kamar baza su Kara gani junan ba, dole Besty ta Kira Aliyu yazo ya lallashi Baby shi dun tazama cry cry. Aliyu da Fawaz suka kaisu Airport aka barta daga ita Sai Besty hata Sadik ma Mami ta wuce dashi..

Besty zaune sama dressing mirror daki Amarya Essha, Itakam Amarya Kwance take luff a tsakiyar makake gadonta da ya gaji da tsaruwa,Gado na kewaye da Net purple irin na zamani Mai shege kyau, gaskiya daki ya tsaru, uwa uba gida Fada tsari gida wani Bata lokaci ne dun yagama tsaruwa daga sama har kasa, ko a kasa wajenema Albarka.

"Uhmm Besty?" Sumaiya tafada tana kallon Essha

Essha dagowa tayi da zauna murya a hankali Tace" Yadai Besty?"

"Dama dama magana nakeso muyi all this while ba samu dama ba."

Essha ta girgiza Kai tana Murmushi tace" Haba Besty ya kike haka, kamar wata stranger, ni ne fa Besty ki "

"I'm sorry nakasan tsaya Miki a lokaci da kike bukatana most, ni har kunyaki nakeji, da Allah ki yafe min ba laifi na bane and I don't know what..." Bata karasaba ta sukuyar da kai kasa tana Wasa da hannuwata tana haweye.. Essha ta sauko a hankali tazo ta dafata, ta na share ma ta haweye Dake zuba tace" Haba Besty Maiye na Damuwa komai ya wuce, ki daina takura ma kanki..ni ba abunda kika min Umarni Daddy ki kikabi kiga ko ni ne ma baranaso abunda zai Bata ma Daddy na Rai ba kinjiko ki daina kuka nan"

Besty ta gyada Kai tana share kwala Tace" Da Allah Ina nema wata Alfarma, da Allah ki yafe ma Daddy na nasan ya Miki laifi, please ki yafe mishi, Gashi duk takura mana da yake yi bai tsira ba, dun Yaya Nazeer ashe kwaya suke Sha Kuma suna saidawa harda ma Yara fyade babu Wanda yasani a gida Sai ranar SSS sukazo nemanshi dun Akama Abokaina sa a Airport zasu fitar da Cocaine hardashi shine ya gudu, har yau ba'a San inda yake ba..." Ta dakata tana shesheka kuka.." Sanadiyar haka ya hadasa ma Daddy Ciwo zuciya, Wanda haka shine yazama ajalinsa" takarashe ta fashe da sabon kuka, Essha sume tsaye tayi ta kasa gasgata ma kunnuwata abunda taji Besty tazama Mairainiya "Inalilahi waina ilahi rajiun " ta maimaitashi ba adadi a hankali ta rugume Besty tasoma lallashita tarasa Baki magana haweye kawai taji suna zuba mata
"Da Allah Essha ki yafe ma Daddy please na rokeki" ta Fada tana hade hannuwa ta alama roko

" Inalilahi Ya Nazeer wani kala rayuwa ne ya jefa kasa Mai ya rasa oh Allah ka shirya Mana zuria ka Kuma jikan Daddy da Rahama, Wlh Besty ni Daddy bai min komai ba in ma yamin toh na Dade da yafe masa Allah yajikashi yasadashi da rahmarsa.."

"Ameen πŸ™‡ Thank you so much basan da Wani Baki zan gode Miki ba, Sai dai nace Allah yabarki tare da Aliyu" ta Kara goge haweye ta jinyo tana Murmushi"Allah dana sa Abba Amira(Fawaz) ke suke nema Dana Dade da taimaka musu, yanda yake bani labari Aliyu yasha wahala naimaki Da Allah Besty ki rikeshi da Amana"

Essha ta rolling ido tana Murmushi tace"whatever naji, hold on ya'akayi ki ka hadu da Fawaz bayan da Bashir na barki"

Besty ta ja dogo Numfashi " Hmmmm long story, Fawaz Ina IT ne nazo wuce wa Accident yafarun a hanya dama ance mukawo report everything that is happening haka dai na dinga bin labari hatsari har zuwa asibiti da aka Kai victims din, shikuma Shine Likita da zai dubasu kiga Dalili haduwa mu kenan" ta Fada tana rufe fuska Essha tace" Awwwn My Baby is in love. what about Bashir ?

labari abunda yafaru a Bliss park kaf ta zayyana mata, Essha, Khalid da Besty ta su suka Bata Tausayi, daji labari har ta bude wani sabo babi kuka.. murya kuka ta kalli Besty Tace "I'm sorry Besty nice sila rabu...."

"A a a yishiru nasan Mai Zaki Fada " Besty ta kasaita cikin sauri "dama can he's not my true love, Fawaz yanzu shine Malaki zuciyana, guess what Khalid ma yayi Aure yarashi ma Biyu yanzu kuma fa First born dinshi sunaki yasamata, Bai da wani a yanzu face yagaki, kullum Sai ya tambayeni ke..naki gayamasa ne dun nasan halishi yanzu zai tada wani karami rikici kuma Aliyu barai so haka ba, kiga da Aure ki yanzu zaku iya haduwa"

Allah Sarki Khalid Yan Ta'adana dai Basu masa Adalci ba

PleaseπŸ™πŸ™πŸ™πŸ€— Comment and share Thank you πŸ€—πŸ₯°


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
Β  Β  Β  Β  *DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

*Written by J Hajara*

🌍 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈβœοΈ

Β  Β  Β  Β  Β  *M. W. A*

Β Β  '''Kungiyar d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www. Facebook. Com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________

*Bismillahi Rahman* *Rahim πŸ™*

*ALHAMDULLILAH*
😌😌😌😌😌😌😌😌

9⃣8️⃣&9️⃣9️⃣

"Ga Amarya Ga Ango" Fawaz yaketa rerewa Aliyu na biye dashi Yana jijiga Kai har suka karasa ciki..

"Basan ya akayi kazama likitaba a yadda kake ahaka" Aliyu yafada Yana dariya.

"Ohoooo dai, kasan dai you have to respect me cus you are married to one of us now" Dariya Mugunta yafashe dashi sanan yacigaba" Ba ta ba sani Dr. Essha cry cry baby bane Sai yau, kana da Babba Aiki a gabaka" Fawaz yafada still Yana Dariya..

"And that's why she's my Baby"Aliyu yafada Yana Murmushi

"Ahh Allah gabadaya a gajiye nake " yafada Yana Stretching hanneyasa

"da Allah ka haura ka kiramin tawa Baby kafi kowa sani yadda nayi kewata" Fawaz yafada Yana bita mishi ido harda daga gira daya sama..

Aliyu Murmushi kawai yayi Yana jijiga Kai yace

" Allah ka Kirata kawai su sauko" Yarage Murya sosai

" kafi kowa sani inta fito a dakinan Essha Kuka zatayi nagaji dagani Kukata Allah.Please ka Kira Sumy Sai su sauko tare please "

"Okay nagane Zan kiranta, ama fa da sharadi?" Fawaz yafada Yana kutsa Dariya

"Ohhsjj Harda Kira a waya ma Sai anyi cin Hanci?"

"Ai ba cin Hanci bane, ka manta Shugaban kasarku ya hana aiki banza, inko ba kashiryabs.."

kallon wristwatch dinshi yayi ya nemi guri ya zauna

" Yanzu Karfe 9:45 kaga kenan Goma ta kusa haka zamu tazama har safe mu barsu su ta hirarsu duk muyi zero_zero kenan wazai fi cutuwa sabo Ango Kai kenan"

"Toh toh Naji Buddy kafada ko Mai Zanyi at this very moment, ama fa Kasani zakama kane"

Fawaz yayi dariya

"Eh Naji ai duk laifika ne, kai kajawo so you have to face the consequences"

"Banganeba Mai Hadi sharadi da ni kuma.?"

"Ba ka tsaya kallon love ba har aka rude dakai ka ka sa nuna sunaka" labari betting dinsu da Sumaiya ya bashi Yana mita..

Aliyu Abu ma Dariya yabashi yace" So yanzu Mai kakeso nayi? Kawai Mummy zaka ajewa little ones kuyi wucewarku" yafada Yana Dariya

Fawaz harara shi yayi yace" Tare da ku zamuje Kuma duka komai Kai zaka biya ehen I don't want to go broke dun kawai zanje kallon kwalo" yafada Yana Mikewa daga zama dayake..

"Naji in wanane Matsala ka angama, ka sanar ma su Haidar su shirya Next week muna Qata__ar In Sha Allah"

"Haba Buddy dagaske kake? "

Aliyu yayi Murmushi yace" Yes that's in har kakira Madam din ka kenan"

Dariya Fawaz yayi yace"Angama Rankashidade Ango Dr. Essha " ciro Wayarshi yayi ya dialling Number Besty..

πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

"Besty Kamar fa wayanki ne ke vibrating ana Kira a silent ki ka sane?"

Besty Dake gaba Mirror tana gyara dauri ta juya Tace" Please ki Amsa Abban Junior ne, May be su dawo ne"

Essha jikin a Sanyaye ta picking tasa a Handsfree Fawaz sallama yayi Essha ta Amsa, dayaji Murya Esshe ne Gaisawa sukayi Sanan yacigaba da zolaryata. Essha Kam Murmushi tarigayi Kamar Yana gabata ta Mike ta Mana ma Besty Wayata a kunne, tana kallonsu sanda suka Gama zuba soyayarsu tsab a waya sanan ta kashe ta juyo ta kalleta.

"Toh Amarya, zamu wuje Yana jirana a kasa, Aci Amarci lafiya" tafada tana bitaa Mata ido..

Essha rau rau tayi da ido kamar zatayi kuka

" Ni wlh Essha Daddy da Mummy sugama shagwaba Mana ke, Mutum ya girma bai San ya girma ba .Allah inkika min Kuka baza Kara zuwa gidanki ba"

Essha tayi sauri ta goge haweye ta dasuka soma zubowa ta sauka daga Gado cikin Sauri dun har Besty ta fice ,tana rike da Hijabin ta da tayi sallah dashi cike sauri ta bita. Nan ta hadu da ita a Baki kofa, Besty zugureta tayi a goshi sanan ta rugumeta..

"Kisan ai baza wuce ba tare da na sallamaikiba,Take care of yourself kinji? Allah yabaku zama lafiya ya kawo kazanta daki"

A hankali Essha ta Amsa da "Ameen"

Nan Waya Besty yashiga ruri, da sauri ta dago Tace" Zo muje suna jiramu"

Saukowa sukayi Fawaz Sai Safa da Marwa yake a Makeke parlor Yana kallon hanya stairs yaga ta sauko ko Sai ya haura dagashi..

"Matana ko yau,gobe jibi za'a Basu Hira na bazai taba isansu ba haba karfe Goma fa hardawasu mintina" Fawaz ya Fada Yana sake dialing Number ..

"Haba Abban Junior Wana Mita haka?"

Ajiya zuciya ya sauke yace" Toh Alhamdullilah ki sauko, zo mu tafi kafi Buddy ya kora mu dagashi"

"Ni naisa??"

Dariya duk sukayi

Fawaz ya juya kallashi ga Essha "Toh Amarya mu zamutafi Sai kwana biyu,Aliyu nasanshi shi dai bashi da Matsala in Sha Allah zaiyaaa....."
Besty ta katse shi da cewa
"Ohh Essha kenan Mai Matsala ko??"

"A a' a 'a ba fadaba Kar ki hadani da wanan Cry cry Baby ta hanamu fita"

Essha shagwabe fuska tayi ta matso kusa da Aliyu ta soma duka kirjisa a hankali Kamar zatayi kuka, haka datayi ya ba ma kowa Mamaki Aliyu kam Suma tsaye yayi ya kasa ko da motsi Sai binta kawai yake da ido dun ta Gama narka dashi.. Muryata tarage ta Kara shagwabe fuskarta tayi ta turo lallausa pink lips dinta Kamar karama Yariya tace

"Kanaji Dr na Kira na Cry cry Baby ko?"

Fawaz da Besty Fashewa sukayi da Dariya.

Kanta ta kifa a kirjishi tana share haweye karya

"kana gani ko harda Dariya"

Aliyu nan Nan yagama shiga Shock ya dawo, Jiyake kamar mafarki yake, Gashi kansa ya sosa a hankali Yana Murmushi ya tallafo ta gabadaya ciki jikinsa ciki zuciyarshi yace

" Wlh Essha zata zautar dani"

"Kana gani fa Basu daina ba" tafada a hankali Kamar Mai Jin bacci

Aliyu ya hade Rai tam ciki sigar Wasa yace" Besty ke da mijinki ku zo ku bar min gida, tun da Babyna zakusa a gaba Kuna Mata dariya..oya oya kuzo ku fice"

Besty sallati tasoma tace" daga taimako shine harda sharri, Addua fa za'a muku "

Fawaz ya Dora Hannu a kugu yace" Yau naga ikon Allah kuce ko ra da hali zaku Mana, Dan Albarka da Addu'ar tamu iri na Manya shine bakuso Shine harda sharri"

"Habibti kyallesu Zo muje dakansu za su nemai mu" Besty ta Fada tana rike da Hannu Mijinta

"Eh muji Addu'ar mugode bama so Zo ku fice" Aliyu yafada Yana Dariya ..

"Wai tsaya Abban Sadik baka ma bada kudi buda Kai ba fa??" Besty ta Fada

Fawaz ya dafa goshi yace

"Fisabililah ku tausaya ma Ango na Mana, Ina wani Buda Kai Kuma baya ga Amarya a like da jikin mijata"

Aliyu fuskar Essha ya shafo dun idanuwa ta a lumshe suke, gajiya ne rubuce karara a fuskarta, Murmushi yayi yasa Hannu a Aljihu ya Ciro bandir din kudi ya daka ma Besty a Hannu

"Lalala na fahimci Nan guri ba'a sona Halin Yan uba ake nuna min,duk shawara Dana kawo Sai an gwasilaini ba Damuwa" Fawaz yafada Yana gyara zama hula shi..

Aliyu yace "Ai gaskiya ta Fada ko?"

Besty ta jefa kudinta a jaka Tace" Kalleshi dai, Muna Godiya Allah ya Kara danko kauna"

Sanda suka Gama zolayar juna su, sanan Fawaz ya shararo Addu'oi da musu fatan Alkhari, sanan suka rakasu har bakin Motarsu . Essha wucewarsu taso tayi kuka, haka dai ta daurai dun Besty ta Mata Alkawari baya sari daya kullum zata Riga ganita..

Aliyu rike hannuta yayi suka koma ciki dun duk yaga jikinta yagama mutuwa, suna komawa ciki ya zaunar da ita a hankali Sai kallon juna suke ido ciki ido, sufi minti na a haka Essha ta daurai ta sauke idonta a hankali kasa tasoma Wasa da zobe dake yantsa hannuta..

"Ki gaji ko??"

Essha da Kai ta Amsa mishi Alamar "eh"
Saukowa yayi ahankali ya durkusa gefenta Kafata ya rike Wanda yasa Essha ta dago Kai a zabure dun ta tsoro ta..

Karami dariya yayi yace" Bafa cinyeki Zanyi ba, in kina ma tunani wani Abu ne Kar kidamu I will wait any time you are ready" ya Fada yana kashe Mata ido daya..

Essha Murmushi tayi ta sukunyar da kanta dun maganar shi ba karami kunya ya ba ta ba. Tana kallonshi yasa Hannu ya cire ma ta takalmi Dake kafarta yasoma ma ta tausa a hankali . Taji Dadi tausanan sosai dun jitake Kamar zatayi bacci

" Su gajiyar min da Babyna" ya Fada a shagwabe Yana kallonta

Essha Murmushi kawai tayi tana kallonshi, Nan yaciga da ma ta tausa Yana sumbarta kafar a hankali Essha har tasoma lumshe ido taji ya Kira sunata

"Eeessha"

"Uhm" ta Amsa tana bude ido, Kiran suna ta dayi kawai yasa tasake Jin wani harbi kifiyar sonshi ta cake ta, The name was so perfect daga bakinshi..

"I want to show you something ama in ki gaji sosai ne, zaiya bari zuwa gobe" ya Fada Yana Susa Gashi kansa..

Murmushi tasake mishi Tace" Wane kakeso nayi? Na kwanta nayi bacci ko Kuma na biyo ka ka nuna min ?"

"Nafiso ki Gashi cikin dare Nan but I don't want to be selfish muje kawai kiyi wanka Sai ki kwanta"

Essha make kafada tayi Ta turo Baki tace" ni na fasa bacci muje ka nuna min"

Aliyu yanda ta tura Mai Baki haka a cloud 9 ta kusa jefashi,Jiyake Kamar ya rarumo lips dinta yata tsosa, a ranshi yace" inta sake haka ya tabbata zai karya Alkawari dun he can't wait any longer" haka dai ya share tunani ya jijiga Kai Yana Murmushi yace" ki tabata?"

Kai tasake daga mishi Alamar "eh"

"Badun Essha bane wa ya isa ya amsa min magana da Kai " ya Fada haka a ranshi..

"Okay let's go" tana mikewa ya dauke cak irin riko bridal style yamata, Hijabi kanta a hankali ya ya cire Mata ya aje, Essha ba ta da tacewa shigidewa tayi a kirjishi ta lumshe ido,tana shekar dadanan turareshi ..wani side na gida ya nufa daba, dayafi wancan girma, da kafa ya turo kofar a hankali ya bude, kallonta yayi na Dan lokaci yaga Dan tafiya na har tasoma bacci, hura Mata isaka yasoma yi a hankali..

"Wakeup Jaaan,bude idanuwaki"

Essha a hankali tasoma bude su, gurin dilim dim da duhu cikin saurin takara maidasu ta rufe takara rikeshi gam..

"Da Duhu banso Duhu please ka Kuna haske" tafada murya ta tana rawa.

Abu ya Danna Sai ga haske kota Ina kamar ranar

"Sorry Jaan bude toh yanzu"

Daya tasoma budewa sanda taga haske Sana ta bude duka. Guri tasoma bi da kallo bakita a bude Wow guri ya mata kyau, a hankali ya sauke ta, daf da kunneta ya whispering Mata "thank you for giving me another chance again"

Essha Murmushi kawai tayi tana bin wanja da kallo tana zuwa dai dai zakiyar parlour taji zubar flowers a jikita, zabura tayi tana dariya..Taji bacci dake idonta duk ya washe, Suma tayi a tsaye da taga Parrots biyu rike da Zane hotota su nufo ta Sai rerewa sukeyi su na cewa

" Barka da Zuwa Dr.Essha, Barka da Zuwa Dr .Essha"

A Hannu ta suka aje, juya wa tayi tana kallon Aliyu Hannu yasa a Aljihu Yana Mata Murmushi Yana furta "I love youuu"

Haweye ta share tana kallon katon frame din fuskar ta dake hannuta, Zane ya zannu dun a ciki drawing din ma haweye takeyi, da Hannu ta nuna Zane Tace" Wana fa?" Matsowa yayi daf da ita yasa Hannu Yana tracing zane, ya dago Kai Yana kallonta ita ma shi take kallo Murmushi yayi ya sosa kai(Yadai zama alada Aliyu sosa Gashi ba)

"Baya rabuwa mune a Wana daji, nayi nema nayi cigiya har nagaji, babu Wanda ma ya yarda dacewa You are existing, Ummi cewa ma tayi da Aljana nayi gamo, har rukiya sanda akami, nakasa bacci na kasa cin Abinci, Saboda ni ka dai nasan halin da na barki,mukoma na dasu Daddy ama wayam muka gani kamar ba abunda yafata faruwa a wajan haka ya Kara tabbatar masu Daddy da Aljanar nayi gamo a hanya.. daji na shi yazama gurin wuni na, dun kullum naje na duba Ina addua Allah yasa nagaki ko Zan samu sukuni, Da Daddy yagane cewa wurin nakeso zuwa Daji gabadaya aka cire Babba titi aka mayar da wanjan, narasa inda za sa Kai na ji tsayi Shiyasa nakira Mai Zane na mishi Description dinki kiga Zane kenan, Wana haweye Kuma kisan tun lokaci da na fara ganiki kuka kike nace yasa harda haweye dun na dau Alkawari in Sha Allah Zan zama Mai share shi, toh da hotona nake samu sauki, Baya Aure na da Suhaima kuma bansa Abun da yafaru Kuma ba but deep down dai nasan something is missing inside me" nannauya ajiya ya sauke Yana kallo Zane" nasan a lokaci ki tsane ni, bakison gani na, Kuma na tabata kisan koni waye ne, Mai yasa bakizo gareni ba Jaaaan? Kifi kowa sani I'm one of your patient you are the only Doctor in this world that can save me.." Hada goshisu yayi Yana haweye sanan yacigaba" ako dayaushe bani da wata burin face na bude ido na ganki, jinake a yanzu Ina rasa ki, kamar an datse min Numfashi na ne, Essha kece Farinciki na, you are weakness, kece muradin raina, Essha Dariya ki Dariya na, kuka ki kuwa shine kunci na, a duk lokaci da na ganki kina zubda da haweye jinake Kamar ana soya min wadi soka daga gaggan jikina, this is a dream come true Alhamdullilah, kullum Sai na yi mafarki wanan ranar Gashi ta tabata, Jaaan

Please Login or Register in order to submit comment