Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakaimu, Zaki hadu da Daddy, ni baruwana, Allah yasoki ma zaiyi tafiya yau, sai Sunday zai dawo. kila ma boy ko gaisuwa baiya da hausa ba"

Ya dubi Sadik yace" hey greet me with Your mum's language"

Sadik sai Ina Ina yake yanason ya tuna gaisuwa da mummyshi ta koyamai da hausa ama yakasa sai "En... En " yake tacewa har ya ba Amir dariya..

Amir ya rugumeshi Yana dariya yace" Don't worry boy, nasan ba laifika bane, is ur mum's fault, da Bata koya maba, Kar kadamu Autar mummy da grandpa zasu koyama, Dani zankoma school, mummy ka Kuma. Tasan ma ranta fada sai Tasha shi guri daddy , dun wanan rubutace"

Essha ta baka Mai harara ta nemi guri ta zauna..

Yayi murmushi yace" oho dai ni dai bazan dukuba"

Essha tayi dariya tace" Allah Amir ka rainani"

Yace" Allah sis acire maganar wasa fada zakishs aguri Daddy, balle yanzu da muka koma uke gabadaya ba kamar lafia bane, zai Dan Sha wuya kafi yasamu friends dun kisa baya ji yaresu Suma basa ji nashi, kiga ko shine da Sha wuya, Anya ma yasa wasu abubuwa aka kasashi kuwa?

Tace" gashi gaban ka tambeyeshi"

Yace" okay tom, boy bara nafara ma Dana India, what is the name of your prime minister ? Nasan Wana zaka sani"

Sadik yayi murmushi yace" *NARENDRA MODI*"

"Toh Who is the current president of Nigeria? Amir ya sake jefo Mai wani tambayar

Sadik ya sake saki wani murmushi Yana su sa Kai can yace" *President *MOhammadou Bu'aali* "


Daga Essha har Amir duk suka fashe Mai da dariya, sadik ya Tsaya shiru Yana ya tabe fuskar Kamar zaiyi kuka, gani haka Amir ya dakata ya rugumeshi yace" No boy don't cry, u tried, that's the correct answer"

Sadik yadago yace" really?

Amir yabashi amsa da "yes boy"


Sadik yace" then why are you laughing? Ya fada kamar zaiyi kuka. ....


Amir yace" am laughing at your pronouciation, it's Muhammadu Buhari, not Mohammadou Bu'aali, give me five "

Yayi murmushi ya Mika mishi hannu suka tafa...

Amir yasa hannu a dimple na Sadik yace" sis Allah boy Kama yake min da wani, kamarsu ma har ta baci "

Essha daji haka ta Mike da sauri a tsorace murya na rawa tace" Amir jiramu ake, abun na hada ma sadik baso yasani, tashi muje sauri nake" tayi haka ne da ta kawar da zance, kafi su Mike ma hartayi waje, jikita har Yana Bari, Amir zaiya tsareta da tamboyoyi tasashi Sarai.

Tanaji murya sadik na sallama nannyshi, Yana mata godiya Khirr da ta hadamai, tana kallosu suka fito Amir rike da hannushi, daya hannu kuwa food flask ne ya rike na Khirr da nannyshi ta zuba Mai.

Suna shiga ta tada motar sai gida, Tana Gama parking sadik ya bude ya sauka da saurishi Yana kwala ma Arudhati Kira tazo taga uncle Amir.

Essha da sauri itama ta sauka tabin bayashi tace" wait Kar kashiga Ina zuwa"

Taja Amir suka shiga ciki tabarshi a tsaye, suna shiga suka tarar da yara da manya acika sosai harda colleague nata naguri aiki, yara dukasu sanye suke da birthday cap na pj masks, Pooja ta karaso tace" Ina sadik Dr?

Essha tace" surprise party ne basan yasani"

Pooja tayi murmushi tasa aka kashe wuta guri gabadaya, guri sai yayi dulum Kamar bakowa, sai Kara Ac kawai kakeji.

Essha ta fito ta samaishi a zaune Khirr dishi yake ci hankali kwance Yana ganita yamike yace" mum Kai huwa?

Bata bashi amsaba tayi murmushi tace" shigo" ta koma ciki da sauri...

Sadik ya shigo a hankali gani yadda guri yayi duhu bagani komai yasoma Kira suna mummyshi bai ji ta amsaba ya Soma tafiya Yana Kai tsakiyar parlor aka Kuna haske, ballon dake tsakiyar parlor yabada Kara shining glittersβœ¨βœ¨πŸŽ‰πŸŽ‰suka fara Mai poping a jiki, Nan aka fara singing mishi happy birthday , Sadik yakasa motsi ya bude baki cike da mamaki da annushuwa, he was surprised, ya bin parlor da kallo Yana murmushi idoshi ya sauka aka cake, ihu murna yasa, ya daka tsale ganishi kawai nayi a gaba cake din, camares sai daukoshi hoto ake, saban mamaki ma kasa magana yayi, da gudu ya rugume Essha ya rakwafar da ita yabata peck a goshi Yana hawaye yace" *mujhe **tumse Pyaar hai mum* "(I love you mum) thanks mum, thank you thank you, Pj masks are my favorite" ya Kara rugemeta.

Yan guri video suke musu sbd subasu sha'awa, Pooja ta janyeshi tace" common boy come and cut your cake" ta dagashi ya rike hannu Essha Dana Amir suka karasa gaban cake din, sadik yakasa rufe baki saban murna.
Pooja ta dauki lighter ta kunna wuta candle na guri yasake canzawa sai glowing yake, kowa na murna yanayi guri, waensu na tafi wasu Kuma na hotuna, birthday boy nananda ya murtuke fuskar, Idona yayi rau rau kamar zaiyi kuka, narasa dalili canzawarshi, guri kuwa bawanda ya lura dashi.

Murya Pooja naji tanacewa" Boy say ur wish and blow your candle"

Kowa aka natsu kallo yakoma kan sadik daya shiru duk yanayishi ya canza.

Pooja ta matso gefe Essha tace" Dr maiyasameshi?

Essha ta kalleshi shiru duk jikita yayi sanyi tace" Nima bansaniba"

Amir yace" sis ko ki mishi wani abune kafi kunshigo?

"Aa amir kana kallo fa ya shigo na da fara'a shi farat daya kawai yacanza ni ba'a abunda namai"

Amir yaiso gaba Sadik ya tsuguna yarike Mai kumatu yasoma Mai magana da turanci yace" common boy, yaufa Ranar ka ne , Yar Ranar murna ne a gareka , duk na a taru ne saboda Kai, Kar ka canza mana maza, ga mummy ma gan anty Pooja ga Arundh"ya pointing Arudhati dake rike da water gun...

"Kaji boy give me that ur smile"

Sadik ya da saki fuska kadan ama kwaya idonshi kwalla ne cike dam kiris suke jira su zuba..


Amir yamike ya kaishi gaban cake din yace" common boy say ur wish and blow ur candles"

Sadik yadaga Kai yakalli mummy shi Nan take hawaye suka zubo, da sauri ya share karta gani, idonshi a kanta yakai baki zai hura.


Arudhati takaraso ta tareshi tace"wait sadik, u didn't say ur wish, say it before blowing the candle"

Sadik yayi shiru na waesu minti na, ya sauke wani nanauya ajiya zuciya yasoma furta wish nashi, a hankali yake furtawa yace" *I wish to see my Dad*" Anashi zato a ranshi yake fada, baisan ya fito fili ba. Haryana sauke ajiya zuciya.......






.



Da Allah ku manage ba time muna busy shiyasa πŸ™‡πŸ™‡πŸ™‡




More comment more typing ❀️❀️


β™₯️Love you guys β™₯️



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara


🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ

M.W.A


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer= whatsa
_________________________


5️⃣8️⃣&5️⃣9️⃣



Sadik nagama fada haka Yan guri sai duk jikisu yayi sanyi, su tausaya Mai, anasu tunani mahaifi shi mutuwa yayi, Essha binshi kawai take da kallo har idonta ya Tara kwala tarasa baki magana.

Wata arniya daga ciki colleague na Essha ta karaso gefe Sadik ta dafashi fuskar tausayi tace" Don't worry son, you will meet your Dad in heaven, am very sure he is here with you, Jesus Christ has bring him down to celebrate your birthday with you, now blow ur candle"

Sadik bai tanka mata ba yajaye hannu ta yakarasa gaba Essha da harta fara hawaye, ya rike hannuta yace" mummy stop crying, let's go and blow the candle together"

Essha ta kalli Pooja , Ta kada Kai ta mata thumps up tace" You deserve it Doctor, Do it"

Essha ta murmusa a hankali ta sukunyar da kai, suka hura atare one blow ya mutu, Nan aka sa tafi. Sadik ya yaka cake yayi kamar zai sama ma Essha a baki har ta bude baki kawai gani nayi ya dangwala mata a goshi da kumatu ta, duk aka sa dariya, yakara yaka yasa ma Essha, Amir da pooja.

Essha takai hannu kamar zata yanka cake din, Bata yanka ba, tasa yatsa ta lakuta cream din cake din ta shafa Mai a fuska, duk suka fashe da dariya, Essha ta kada Mai hannu a fuskar tana murmushi Alama ta Rama, sai daukasu akeyi domin su burge. Amir har Kira su mummy yayi Video call Bata kusa khairat da mufeedat ne suka dauka,wow su zama yanmata, Suma suka wishing Sadik happy birthday, mufeedat harda guntu kukata na Rashi zuwa da Amir bai je daitaba, su jima sosai kamar karsu rabu, sanda Amir ya shaida musu cewa gobe zasu dawo sanan sukaji sanyi suka kashe.

Aci asha a watse a taro birthday lafiya, Gifts kala kala Sadik yashasu, gifts boxes su cika room nashi dam(hhhh yaro dun ba daddy ka kenanπŸ˜‰)




*************************

Aliyu tunda suka koma lodge nasu yakasa sukuni, yarasa Mai ke Mai dadi, yasan ba results din daakace gobe sun dawo bane, dun yariga yasani abun daya yake nunanawa, so bazai damu kanshi ba.

Ya kwanta rigine ba riga dagashi sai wando suit daya cire, ya lumshe idon sai tsaki yaketa ja.

Suhaima ma yau taga bambaci,yau ko kallon dun da suka dawo daga hospital Bata ishe Shiba, Abun ya taru ya mata yawa, tanason ta koma Asibiti na gashi Aliyu ya canza mata lokaci daya, abun mamaki yake bata, Aliyu ne zasuyi tafiya ba shawara kawai yace su zo asibiti, kodai maganine ya karye?

"A'a wlh yanzu sai na Kira mummy, Dan wlh bazaiyu ba" ita kadai a toilet tana ta sambatu ta.

Ta fito daga toilet ta samaishi a kwance, Aliyu naji fitowarta ya bude idon, idon su kada suyi jawur kamar ja gauta, suhaima ta tsorata dagani kwarya idon, kawai sai ta daburce abun da Mara gaskiya, dun kallon da Aliyu ke binta dashi ita kanta ta kasa fasara iri kallo.

Aranta tace"anya likita nan bai tura mishi results bako? Wayyo !! Ta ciji yatsa can tacigaba" Kai no, kafi suyi haka sai na sa yanda zanyi na koma asibiti na, let me just pretend for now"

Takara Dora zama towel, tabin jikita da kallo, dun Aliyu tun dazun data fito shima yake binta da kallo .

Tasaki murmushi tace" nasan shape da skin Dina yake kallo". Takara bin jikita da kallon tana saki wani miskili murmushi.


Suhaima ta tafi single ba Oyoyo ba bye byeπŸ˜†πŸ˜‰, ko hips dima babu a haka har slimming tea tanasha, nonuwa misili kamar na wata kwaila, ita a dole model Bata San ta tsufa ko jikita ya lalace.

Ta karasa gaban Aliyu ta ta kife kanta a ruwa cikishi, baice mata uffan ba, kauda Kashi gefe daya yayi yaja karami tsaki, deep down yanaji kamar yarasa wani abun Mai mahimaci ne a rayuwashi, yanaji suhaima kuwa kamar asa mishi dolene, yanason yafadi abunda ke zuciya shi ama Yana kasawa ji yake kamar anrike mishi baki..

Suhaima ta Mike ta zauna agefeshi tana shafa mishi Kai tace" Darling maike damunka ?

Aliyu ya runtsa idon, shin kanshi ko bindiga za'a azamishi a Kai yafadi maike damushi baisaniba, sai dai akasheshi, shi dai kawai yanaji zuciya ba dadi Kuma Yana mishi zugi sosai.

Suhaima ta Mike ta cire towel ta tsaya tsirara a gabashi, ta shafo fuskarshi Tana wani kada jiki, dun taja ra'ayishi , batasaniba Aliyu ko sau daya bai taba sha'awa jikitaba, Yana dai biye mata ne dun biyar bukatar ta, Yana son mace Mai full chest da back, ba iri nata ba, yanaji a jikishi kamar yata ba samu haka when? where? Yakasa tunawa.

Ya shareta ya kauda Kai ya lumshe, dun jiyake kanshi na Sara Mai kamar zai fadi, ya rike Kai da sauri, zuciya shi namishi zafi , ya rike matashi dayayi karfi kamar dutse, na jikishi yadau rawa wani azababe Kara yasaki nan take ya sume.

Suhaima ta tsorata towel taja da sauri ta isa reception ta Kira securities, da sauri aka Kira ambulance, suna zuwa aka daukeshi sai asibiti ciki gagawa suka isa, suhaima ta aza Wanda sukaje da farko ne za'a kaishi mamakita taga wani dabane, ba haka taso ba, tasa hannu akai , kamar tayi ihu ita kam zuwa ta India bai mata dadi ba, harta fara tsorata Kar asiri ta ya tonu.. Tana kallo doctors suka wuce dashi
Emergency room ..

Suhaima saboda Rashi yarda tafara zargi sa hannu mummy ta, dun kwanaki Hajiya binta ta mata magana cewar akawar dashi kawai su samu dukiya, suhaima Taki amincewa, tunda suke baitaba yi iri na yau ba...

Cike daburce tafara "wlh mummy ne, mummy in kikashe min Aliyu wlh sai na kashe ki" ta fara sambatu ita kadai..

Ciki sauri ta isa motar ta ciro wayata, mutani sai binta suke da kallo, saboda towel ne kadai ta Dora a jiki, gashi doki na kuwa har baya.


Jiki na rawa ta dialing number Hajiya binta, tana dagawa cike da matsifa tace" wlh mummy in Aliyu ya mutu sai na kasheki, Better go and meet that your stupid so called mallam ki gargadeshi, Aliyu nawa ne, banakuba, kudi ko nawa kikseso inkia tambaya ina baki, maikikarasa ? maikikarasa? Shine kikasa ya kwanta ciwo ya anka ya mutu ko?

Hajiya binta ta sausauta murya tace" Baby maikike fada wai ? Nifa tunda kikace Kar a kasheshi na bar zance, ki yarda dani, Baby kisa inaji magananarki ai, yanzu ina Aliyu yake?

Suhaima tace" mummy tunda munkazo bagane kan Aliyu ba, Yana nema ya canza, Aliyu shi da konayi abun koyanaso ko baiso tsorana nasa dole ya Amince da abun dole, ama mum ya canza da Allah ki Kira malamin na muji maike tafiya"

Hajiya binta tace" toh Baby na kashe inazuwa"

Tana kashewa ba'a fi minti na ba hajiya binta ta Kira, da sauri ta daga , tana dagawa ihu hajiya binta kawai ya cika mata kunne..

Suhaima ta rikece tace" Wai lafiya kike ihu haka?

Cike da tashi hankali hajiya binta Tace" ba lafiya Baby, mallamin na ya mutu, Dana kira layi ne yaro aikishi ke shaida min cewa ya mutu"

Suhaima taji zufa na keto mata ta koina cike da tashi hankali murya na rawa tace" munshiga uku mummy asirimu yakusa tonuwa, shikenan mummy wayyo yazanyi da Raina, tun ba'ayi nisa ba Aliyu ya fara chanzamin" ta fashe da kuka...

Bagare Hajiya Binta kuwa sai tsale da rusa ihu takeyi kamar wani natane ya mutu, can tayi shiru ta daga waya Tace" Baby ki na kusa na tuna walahi na tuna"

Ciki kuka suhaima tace" Mai kika tuna mummy rayuwana yazo karshe"

Hajiya Binta tace" No baby ki kwantar da hankali ki, asiri dake jiki Aliyu bazai taba karyewa ba na tuna na har abada haka mallamin ya fada , yace na har abada ne, so babu abunda ya damemu da nutsuwarshi, Baby acigaba da gashi kawai "

Suhaima tasaki wani wahalale ajiya zuciya tace" harnaji sanyi mummy, ni zan koma asibiti da aka duba mu dazu kafi Aliyu ya farka karsu zo su tona muna asiri"


Hajiya binta Tace" Baby Kar ki koma ki manta dasu kawai, Yana farfadowa kawai ku dawo, inyatambeyeki kice ki barshi a hospital din kawai"

"Mummy na kena kaki na ja" suka sa dariya...

Doctor yafito yace" tasameshi a office "

Suhaima ko kunya Kaya dake jikita tabin bayashi cike da yanga , suna Isa ta zauna tukan yace ta zauna.likita sai bin jiki ta yake da kallo, itakam ko ajikita .

ciki harshe turanci tace" Doctor what's wrong with my husband?

Yayi gyara murya yasoma Mata bayani shima ciki harshe turanci yace" sperm pains ke damushi, sbd sperms ya mishi yawa a Mara, Kuma binceke mu yanuna Yana cike da damuwa sanadiyar haka ya affecting zuciya shi kadan, ama ba wani matsala babba bane, zamu bashi medication da yarda Allah zai warke, sai kuriga Kara bashi kulawa"

Suhaima ta jijiga Kai Alama ta gamsu da bayanishi.

Doctor yace" But Wait are you guys not sexual active?

Suhaima ta kada ido aranta tace" ni ne zan sake ma mishi jikina wanan Mai jaraba tsiya ya jagwalgwalani karshe ya barni da tsufa jiki chab"

Doctor ya kada mata hannu yace" madam am talking to you"

Ta jijiga Kai tace" ohh sorry"

Yasake maimata tambaya " are you guys not sexual active? Yanada mata ama yabar sperm ya mishi yawa maiyasa?

Suhaima ta Mike cike da matsifa tace" it's none of ur business, just focus on your work, ka bashi duk wani magani da zai taimekeshi ba ka tsaya kana min banza tambaya ba"

Ya Mike shima yace" yahakuri madam, duka wana a ciki aikimu, muriga da mubashi injection dazai flushing ama inyakara Bari hatsarine ga lafiya .........

Suhaima Bata Bari ya karasa ba tayi ficewata tana bambami"






















Comment &shareβ™₯️β™₯️


Love you guys ❀️❀️❣️


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara


🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“š πŸ–ŠοΈ

M.W.A


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
__________________________




6️⃣0️⃣&6️⃣1️⃣


Suhaima na Tana bambamita ta wuce daki da aka kwantar da shi, tana shiga ta Tara da ya farka, a zaune ma yake, daya daga ciki bodyguards na mishi tausa a fafade bayashi.

Suhaima da sauri ta karasa gefeshi tana bin bodyguards din da harara Yana gani haka yajeye ya koma gefe.

Ta dafashi ta rage murya tace" honey ka tashi? sannu ya jiki?

Aliyu bai amsaba yadaga Kai ya kalleta da mamaki karara a fuskarshi aranshi yace"subhanallahi dah towel Dina ta fito kenan"

Suhaima ta katseshi tace" honey yadai Ina magana kayi shiru kodai jikine?

Aliyu bai tanka ba ya Mike ya dauki rigarsa yasa, ya Kama hanya zai fita, suhaima jiki na Bari tayi sauri Tasha gabashi duk a tsorance take, hankali ta a Tashe yake, tunda suke tare bai taba shareta ba komai girma laifita kuwa Nan take gabata yasoma faduwa ta ayana ma ma ka ta kila asiri dake kanshi ne ya karye, ta rike kirji Tana" wayyo Allah na"

Aliyu yakalleta yace" lafiya? Uhm let's go back, ni na warke , bara zauna a hospital ba, Kuma kiga iri Kaya dake jiki bai kamata ba" ya juya ya wurga ma securities wani kallo nanada suka fice suka Basu guru..

Suhaima na gani haka tasaki wani ajiya zuciya harta ji sanyi a ranta ta saki murmushi ta samo zance zuci" Ashe dai haryanzu magani naci, mulki ne kawai ya matsa" ta dafashi Tana kada Ido ta Kai Hannu ta shafa fuskarshi tayi kasa da murya tace" Honey baka warke ba fa, kakeso Bari hospital, kajira ko jibi haka kagama warkewa sai mun koma gida ko? Towel Kuma Dana daura na fito ai duk saboda Kai ne,Honey na ba lafiya shiyasa duk na rude, ba fito da Kaya ba"

Yace" okay naji, kisan gobe zanmuje muduba results ko.........

bai karasaba ta katseshi Tace" Honey ina ne ba mujeba, Wanda ma girma su da aikisu duk Sufi hospital da mukaje, honey duk results daya fa yake nunawa, in mu koma gobe su kace zasu bamu wani medication kasan yi haka babu kyau kamar muna ma Allah shishigine. Zan iya zama dakai a duk hali da kake ciki ko baka haihuwa Wana ba damuwa bane ama tunda kace bahakaba................ta sukunyar da Kai ta fashe da kuka munafurci..

Aliyu duk jikishi yayi sanyi da kalamata, da sauri ya dagota ya rugume ta a kirji shi cike da tausayi kanshi yace" wife yi hakuri, shikena bara mukoma ba, nagode da kika tuna min da haka"

suhaima harda shesheka karya tana mishi gwalo baisaniba, shikam sai lalashita yakeyi harta Saida kuka munafurci tace" yanzu honey ya jiki?

Ya amsa da sauki yace" wife ni bansa zama asibiti na zan koma Lodge namu, sai doctor yariga zuwa dubani har kwanki su cika haka yamiki ko?

Ta gyada Kai, aranta kuwa shewa take da murna tace" hohoho sai ni shegiya, Aliyu Kai da yara Kuma ai sai dai na dangi ko na makwabta, na Gama da zuciya ja da gaga jikaka ba yanda za'ayi Dani"

Aliyu ya tabata yace" wife ina ta magana kiyi shiru"

Tayi firirit da ido tace" sorry honey maikake cewa ne?

Yace" nace kije motar ki jirani zanje nasami Doctor naminshi bayani yada muka Sara ko?

Tace" okay honey ba matsala sai ka fito"

Tayi hanya waje, Tana fita Aliyu ya koma gado ya zauna shiru, yanasa ya nemo ma kanshi mafita ama yakasa Sam, tunani imba na aiki bane, indai wani ne daban daya rufe ido suhaima ce kawai yake gani. Ya Mike gabadaya jikishi a mance yake, zuciya shi yamishi nauyi kamar dutse ne aka aza mishi akai, Dakar yake takawa yafita zuwa office din doctor Yana bude kofar, Doctor naganishi ya Mike ya taro shi da sauri ya bashi kujera ya zauna, ba Bata lokaci ya Soma Doctor bayani abunda yakawoshi.

Doctor yace" badamuwa"

Zai Mike doctor yatareshi yanason magana dashi ya Kara gyara zama yace" inajika"

Doctor yace" yallabai kadaina Bari sperm na taruwa har yakai da yasa ma pains, maguguna da allurai dakakesha ba mafita bane, kana da matar ko Killa may be bakasamu time ne, please ka rage aiyuka ka ba ma jikika hakkishi"

Aliyu najishi ya lumshe ido yarasa inda zai sa kanshi yaji sanyi, Wai Yana da matar, shiyanaji son suhaima ne kawai ama wani Abu nata bai taba burgeshi ba, sha'awa ma dayakeji inta taso masa ne kamar yadda kowane Dan Adam lafiyeye keji" bai tanka ma likita ba ya Mike ciki harashe turanci yace" bye zai kazo " ya fada Yana ajiye mishi address na hotel da suke, bai jira amsa likata ba ya fice.

Yana isa haraba asibiti gefe da aka Parker motoci, bodyguards na gani yafito da sauri suka Mara mishi baya aka bude Mai motar yashiga, Yana shiga ya tarda suhaima chatting ma take hankali ta a kwance, Aliyu ya kada Kai ya kishigede, ya lumshe idon yanaji aka tada motoci bada jimawa ba suka isa haraba hotel din, baijira suhaima ya bude ya fito yayi gaba,Yana shiga daki toilet ya fada ya watsa ruwa, ya daura alwala yafito ya zira jalabiya ya shimfida dadurma ya Rama sallolisa.

Yana idarwa suhaima na shigo ta fada kan gado" wash honey na gaji yunwa nakeji"

Bai amsaba ya cigaba da ja carbishi, gani haka yasa tamike inda sabo tasa ba da halin Aliyu na kyaluwa, ta Kira reception ta musu order abinci. Tana ajiya Kira bada jimawa ba aka fara Danna door bell ta Mike ta bude waitressce ta shigo dauke da tray, pizza ne da roasted chicken akai sai kwalba wine, da hot Lipton dake turiri duka akai, ta karba ta sallami ta.ta nemi guri ta zauna ta narki abincita so ranta, baya ta gama ta daga Kai ta kalli Aliyu da haryanzu carbi shi yakeja tace" honey tashi kaci abinci"

Ya kada mata Kai alamu bazai ciba, ya Mike ya cire jalabiya yarage dagashi sai boxer, gani yanda marasa ke murada masa ne yasa ya dauki Lipton yasha, shima basha dayawa ba ya ajiye, ya kalli suhaima da harta gyara kwanciya ba wanka ba sallah, ya Soma buga mata kafa a hankali yace" wife bakiyi sallah bafa kina nufi a haka Zaki kwanta?

Ciki magagi barcci tace" Bari kawai honey da safe zanyi, towel ai ba matsala bane"

Aliyu yaki Amince wa da haka yasata a gaba dole ta Mike taje tayi wanka, alwala ma Rabin da Rabin tayi ta fito, tasa night gown da yakaimata har kasa ta zari gyale ta yafa tafara dogara sallah, tanayi tana binshi da harara, Aliyu na kallota ya gyaramata sallah kuwa kamar anrike mishi baki, two minutes kawai Wai ta idar da sallah mahgrib da Isha, ta fada gado ko ko mayafi ma Bata cire ba harda guntu munshari ta, Aliyu kam kasa magana yayi, ya gyara mata kwanciya yaja musu bargo. Asuba ta gari


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ


Essha tun 6 baya angama birthday Bata zauna ba, hospital nasu ta wuce ta musu sallama aka gobe zata wuce, Doctors,nurses harda patients da suka Saba harda kukasu, Dr. Essha zata barsu itama sanda tayi nata hawaye, tashiga office nata ta tatara document nata masu mahimaci tabar office din ta wuce office din babba Doctor, tana zuwa tacima office din a rufe ta bada letter a bashi, sai misali 9pm ta dawo gida duk a gajiye, ta godema tayi sallah magarib

Please Login or Register in order to submit comment