Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

leda fari baiya gani abunda keci.

Big mom ta a aje kulla a gaban hunaisat, ta amshi roba da ke hannu anty zainab shima ta aje a gabanta , har da Kaya hannu Aina'u duk ta hada ta aje.

Big mom tace" hunaisat? Ta amsa da na'am momy"

Big mom tace" kiga Wana kula ta bude kaza amare ne ya shs Hadi sai kamshi kawai ke tashi, tace" toh inason ki cinye kiban kula , zan aiko a daukamin, da wanan ma ta nuna gora tace " tsumi ne duk ki shanye su, kinaji na ko, na roba na Kuma ta nuna na lalle Hadi tace" yanzu nakeso kishiga ki watsa a jiki kizo anty ki zata turareki"

Hunaisat tace" toh momy" ta fada Tana tura baki, ta dauka ta wuce ciki toilet dashi.

Big mom tace" Essha ki tabatar da ta shanye komai kinjiko, intaki kizo kigayamin, kijiko daughter?

Essha tace" toh mum zan yi yada kikace"

Big mom ta fice daga daki taja Aina'u saboda zata tayata hada kayayaki, Aina'u ba haka taso ba, taso ayi agabatane😆.

Essha sai a sanane taga anty zainab tace" la aunty zainab tundama kene a tsaye"

Anty zainab tace" eh Essha nine , Ina waya zai barki ki gani"

Tace" la aunty yihakuri, Ina wuni?

Lafiya klau ta amsa"

Tace" mummy na Wai na gaisheki"

Anty zainab tace" Allah sarki Ina amsawa, gobe zamu wuce zamu bi tagari naku ai "

Essha tace" eya anty zaku wuce gobe?

Anty zainab tace" inshallah"

Hunaisat ta fito daga toilet rike da robar , sai tura baki kawai takeyi, anty zainab ta ja ta tace" zona yata yihakuri ke fa amaryace, zo na turareki , kawuki na jirana"

Essha tace" anty Nima nazo?

Ta amsa da toh Essha zo ba matsala"

Duka ta hadasu ta turaresu ciki da bai, agama sai tashi kamshi kawai suke Mai dauka hankaki .

Anty zainab tace" ni na wuce saura Kar kici, Essha ki kula da itafa?

Tace" zanyi anty"

Anty zainab na fita hunaisat ta Soma guna guni tace" ni wlh na gaji da ci abubuwa na, waensu fa kamar zanyi amai"

Essha tayi dariya tace" yariya gwamnati ki a ke taimaka "

Hunaisat tace" ni banso"

Essha tace" wlh Allah inbaki ciba zana je nagayama big mom cewa kice baza kici ba" ta Mike tsaye.

Hunaisat ta tare ta tace " haba mana lovely sis zauna Allah zan ci ama zakitayani ko?

Essha tace" ayah? Na amare ne fa?

Hunaisat tace" Allah sis bazai Miki komai ba"

Tace" dagaske kikeyi?

Hunaisat tace" Allah sis believe me"


Tace" tom nayarda" su biyu suka cinye kaza , Essha ma tafi ta ci har da tsumi suka Sha tare, ballema hunaisat batasha sosai ba, Wai zai sata amai, Essha baki. Kwadayi duka ta shanye harda na leda duka suka hada suka cinye.

Suna Gama ci Aina'u ta shigo taga duk su cinye sai kashi🦴 ya rage.

Tace" wlh yanmata na baku kyauta min ba, Ina ta sauri nazo ashema ku cinye"

Essha tace" yi hakuri sis da Allah Kar ki fada ma mom tare mukaci "
Bata amsaba ta sharesu ta haye gado ta kwanta , Essha ta matso kusa da ita ta yaye bargo tana mata cakulkuli ,

Aina'u tace" ya'isa ya'isa tafada Tana dariya, ya wuce bazan fada ba, wlh ke Kuma Allah yasoki "ta nuna hunaisat.

Eh din" hunaisat ta fada Tana mata gwalo.

Aina'u tace" habawa ai Allah yakaimu gobe muga baki Rashi kunya yanda zaiyi"

Hunaisat ta amsa da ameen" ta murguda mata baki.

Essha ta Mike ta tatara kuloli takaima big mom, ta wuce guri hajiya ta mata sai da safe.

Tana dawowa ta cire hijab din da tasa, tayi shiri kwanciya , zata kwanta hunaisat tace" sis zokiga anko ki, kigashi ta daga atamfa da lace duka dogaye rigunane diki"

Tace" sis wlh nagaji da safe na gani , ta koma tayi addu'a bacci, tace " sis ainan , amarya sai da safeku , suka amsa da Allah ya tashemu"

Hunaisat ma tabar chatting da take yi da Anas ta mishi good night , ta kashe wutar daki ta kwanta.









Comment & share 🥰😘🙏🙏



Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by-j-hajara



1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣




Washe gari

Da misali karfe goma ne za'a daura aure, su Essha tunda suka farka da asuba Basu samu su koma ba, gida cike tam da baki nisa Dana kusa, sai shirye shirye daura aure kawai sukeyi.

Amarya hunaisat a shiryata ba karami kyau tayi ba, Mai makeup Anas ya turata ta tsantsara ma amaryashi makeup da yanmata amare, har su maryam suzo, su ma susha ankosu ba karami kyau sukayi ba.

Can na hango Essha da Aina'u wow yanmata sufita, inbaka kalli Essha sosai bane baza ka gane taba, ta hadu karshe haduwa, duk inda suka wuce sai a kallesu akara.

Suna kan tafiya suka hannu dasu Yaya Usman, a hanya sufito daga part nasu dukasu Sha shadda farare kal kal Suma su fito.

Salis ne yace" wow sis kifito daker na ganeki, na zanta kowata bakuwa ne mukayi daga Makkah"

Tace" Kai Yaya salis Banda shairri fa"

Allah sis ya fada"

Usman yace" ko kyau, Bata ma iya kwaliya ba, Aina'u ne kawai tayi kyau"

Tace" oho dai jealousy, don nafi budurwa ka kyau"

Yaja mata hanci yace" Allah yakiyaye kifi budurwa na kyau, gata a kusa dake "yanuna Aina'u , Aina'u ba karami kunya taji ba, ai da gudu tabar wajan.

Abba yace" Yaya gashi kasa inlaw na ta gudu Wai ita kunya" ai duka suka fashe da dariya

Suka sata a tsakiya Wai adole sai suyi hoto, ai kuwa dole ta tsaya, suka kashe hotuna kalakala, salis ya aiki Sameer yace ma Aina'u ta fito da hunaisat za suyi hoto, aikuwa nandana yaje, ya dawo yace" gasu zuwa Yaya"

Suna zuwa aka sake Dora selfie kalakala ba adadi.

Salis yace" dole na tura ma Yaya Abdul Wana yayi missing (Abdulhamid Yana service a imo shiyasa bai zoba).

Khasim yazo yakira Essha yace mata ga daddy ta a guest room Yana neimata, ai da sauri ta je ta samaishi, tare dasu hajiya yake, ta gaishesu.

Tace" lah daddy yaushe kazo?

Yace" tun 7:00am Ina garina"

Ta shagwabe fuska tace" dad jiya fa munyi waya baka cemin zakazo ba"

Yace" yi hakuri Essha mantawa nayi"

Tace" ya mum da su autar mum?

Kowa lfy su ce na gaisheki, ama fa mufeedat batasan nazo ba"

Tace" eya daddy daka kawo ta"

Yace" no guri da nisa, Bata Saba ba"

Tace" toh dad bara na wuce"

Yace" okay inza wuce zankiraki"


Karfe goma dai dai aka daura aure hunaisat da Anas.

Aciki gida Kuma hunaisat ne zaune sai kuka😆, da ace amarya amarya, zata fara kuka, su aina'u kam su samu nayi, sai tsokanar ta sukeyi, Essha na gefe ta tana lallashita, Anas ma yakira Taki daga waya, Essha nata mata dariya a boye.

11:00am akafara walima, wata babba malama ne aka gayato, Kai gsky taiya wa'azi da nasiha Mai ratsa jiki Mai sauraro, sai guri 4:00pm akatashi a walima, 6:00pm nayi akafara shirya amare da karfe bakwai,angoye za su da motar akwashesu, amare suka sake sabon waka su hadu👌.

Daddy Essha tun two na Rana suka wuce dasu anty zainab har da Aina'u Wai zasu biya ta lafia.

Sai baya Isha tuku motar angowaye suka zo,amare suriga su Shirya dama.

Hunaisat ba baki sai kuka, ankaita guri big mom tayi mata nasiha Mai ratsa jiki tasa mata albarka, daddy ta ma haka, hajiya kuma sai kuka itama😅( kunsa hjy da sauri kuka). Su maryam har idansu ya fara kwalla, Essha kam ta jima da kuka, big ne keta aiki lallashi.

Suka fito,aka kwashe su a motar direct guri reception aka nufa, Kai guri ya hadu, an Soma biki aci asha, an rabar gargaje.

Antashi a taro lafiya, amarya aka wuce da ita gida angota dake rigasa, Essha suna ciki Yan rakiya, da za su wuce ta rike gam Tana kuka Wai Essha Kar ta tafi(Allah sarki kamar ba hunaisat ne Mai surutu na). Sai taba Essha tausayi.

Yaya usman nata kira Essha tayi sauri tazo su wuce, Wai duk yanmata su wuce Mai take jira aciki,be San dare ya musu gashi 12:00am yayi, Kuma akwai Dan tazara kadan tsakani rigasa da anguwa dosa, Essha Bata kulashi ba, takira Anas yata lallashita tukun ta saki Essha,

Tace " sis ciki murya kuka da Allah kizo da safe kijiko?

Essha tace" karkidamu Zaki gani inshallah" Essha tasan fada kawai take bazata samu zuwa ba,sbd tafiya safe zasuyi, ta fada ne kawai don taji sanyi, ta musu saida safe, Anas ya dauki hunaisat suka wuce ciki, har da manewa a kafada shi, Essha tayi dariya a ciki tace tundama gulma ma ne Aina'u sai taji wanan" ta fita(amarya asuba ta gari)

Essha na Isa baki motar Yaya Usman sai fada yake Tamata aka tsanyawa da tayi.

Tace" Allah yaya usman baza ka gane bane"

Yace" min shiru" yaja motar suka bar anguwa, suna karasawa gida, Yana parking ta fice daga motar don batasan matsifa gashi ta gaji,

Yaya Usman yace" Allah Ina kamaki baza kiji da dadi ba" ko kullashi batayiba ta wuce ciki, direct daki ta wuce ta watsa ruwa ta kwanta da kewa amarya da Aina'u.

*************************
Abuja

Aliyu tun da yayi Sallah asuba, ya koma bacci bai farka ba, sai wurare 12:00am, shima Mami ne dakata tazo ta tasheshi, aka yazo yayi breakfast , don ta lura jiya bai ci abinci kirkiba.

Tana tashi ya wuce toilet, yayi wanka,brush, ya fito daure da towel a kugunshi, Mami na guri wardrobe tana duba minshi Kaya da zai sa.

Tace" iyye son, baka da kunya ko? Turawa na su Bata min kai, shine zaka fito a haka ko?

Yace" Kai Mami"

Tace" ga Kaya ka Nan , kayi maza maza ka shirya, kazo kayi breakfast"

Yace" tom Mami bani two minutes" ta fice, jeans trouser ne navy blue da sai singlet da top shima navy blue ama yana da layi layi fari aciki, ya shirya tsab dashi , gashi na yasha gyara, sai walkiya yake, ya fito sai kamshi ke tashi.

Ya nufi part din Mami ya tar da ita zaune Tana kallo news a AIT, ya tsuguna har kasa ya gaisheta, ta amsa.

Tace" ga breakfast a kan dinning maza ciye komai dake guri"

Yace" Mami sumin yawa fa"

Tace" ni fa banason ji complain, nace ka cinye komai kaba empty plates and you should be fast"

Yace" toh Mami"

Soyaye arish ne da kwai,sai coffee☕da farfesu Kaya ciki, yanaci abinci Yana Dana waya.

Mami ta kalleshi ta jijiga Kai tace" boy better keep that phone and concentrate on your food"

Yace" okay maaaa da Karfi" Yana dariya.

Tace" ka girma ama haryanzu baka sani ba, waensu kamar ka su ajiye yara uku ko hudu ama u haryanzu muna rainoka"

Ya yamutsa fuska yace" haba Mami kibar zance na, next year inshallah ,kina rike da jikaki"

Tace" Allah ya nunamana "
Ya amsa da ameen mamina"

Yana Gama ci abinci, ya Mike ya kwanta a cinyata yace" Mami inason muyi magana ne"

Tace" ohk boy inajika" ta rage volume din tv.

Yace" maiya sa bakiso yariya da idriss keso"

Ta kalleshi tace" wato ma karana yakai maka Koh?

Yace" no Mami bahakabane, Mami just tell me the reason, Allah inbata Miki ba muma hk"

Ta nufasa tace" hmmm, boy yariya kwata kwata Bata da tarbiya ko kadan"

Yace" Mami fadamiki akayi ko da idonki ki ka gani?

Tace" wato ma Kare danuwanka kakeyi Koh, to tashi kabani wajen, shikuma zai dawo ya sameni"

Mami kiyi hakuri please " ya fada Yana ficewa daga parlor, direct sashi Ammi ya nufa, su Rahman ya Tara dasu Salma da siyama suna kallo , ama ita Salma hankalita ma baya gun, duk suka gaisheshi, ya amsa yace" kuban waje zanyi magana da Salma, duk suka fice, yara ge dagashi sai ita, Bata ma sa yashigo ba, sanda taji kamshi turareshi ne ta yi sauri juyawa suka hada Ido tayi sauri sukunyar da Kai.

Tace" good morning Yaya ? Murya a sanyaye, ya amsa ba yabo ba fallasa.

Yace" zonan magana nakeso muyi dake"

Ta tashi daga inda take ta koma gefenshi ta rakube.

Yace " Salma Ina son nabaki hakuri akan abunda yafaru jiya, I realized my mistake,duk abunda Ammi ta fada mishi duk yagayamata"

Tace" badamuwa Yaya nagode, hk Allah yaso"

Ya mata magana aka haydar , tace" Yaya duk zanbi dakamin zan karbeshi hannu bibibbiyu"

Yace" yawa little sis nagode"

Yakira haydar yafada mishi, haydar bakarami murna yayi ba,

Yace" Kai buddy yau kabani joy Sosai sosai"

Aliyu yace" naji ka kula min da kanwa sosai"

Haydar yace" Kar kadamu ai yanzu tazama nawa"

Yakashe waya, ya turaminshi number ta, yatambeyata Ina ammi?
Ta amsa da tana side din daddy"

Yace" ok baza dubasu"

Yana shiga side din, ya Tara da Ammi tana shafa ma tycoon Robb a kafa, da sauri yakarasa ya karbeta yace" Ina kwana Ammi, dad? Suka amsa.

Ammi tace" sister ka ta kira Wai na gaisheka, tayi nauyi baza ta iya zuwaba"

Yace" Allah sarki fauziyya Allah ya sauke ta lafiya , zakirata anjima"

Tycoon yace" yaushe zakaje gidasu suhaima?

Aliyu ya su sa Kai, ya ce im im dad anjima zanje"

Tycoon yace" promise me zakaje?

Ya daga Kai ya kalli daddy yace promise Kuma ?

Tycoon yace" of course nasa ka, zaka iya cewa ka manta"

Yace" dad bazan mantaba"

Tycoon ya Mike yace " toh uwargida , sarauta mata nizan wuce" Ammi ta Mike Tana gyara mishi tie dake wuyashi tace" Allah ya tsare, ya dawo mana dakai lafiya"

Aliyu yace" dad Ina zakaje kuma?

Tycoon ya kalleshi yayi murmushi ya shafa mishi Kai yace" son bazama, meeting zani a South African🇿🇦, sai gobe ko Monday na dawo"

Yace" toh dad Allah baku sa'a?

Yace" ameen" yakira Mami tazo tamishi sallama suka rakashi har baki motar, ga escorts a gefe sukai 15 suna jira karasowashi, dukasu majiya karfi, susha baki eyeglass.

Tycoon na karasowa daya daga ciki ya sauri bude mashi kofa, har yashiga , yasake fitowa, yarike kunne Aliyu da na Isa har sanda suka sa Kara.

Yace" nasan kune bakoji magana, toh Ina Kara shaida muku inza kufita , kufita da bodyguards naku, Nigeria is not lk other countries is not save, Kuna jina ko tun tun Kai Aliyu" yakara murda kunne Aliyu.

Aliyu yace" assh daddy inshallah ama kunne na zafi"

Isa yace" dad walahi zan fita dasu"

Tycoon yasaki musu kunne ya shafa musu Kai yace" yawwa good children ku kula da kanku"

Suka amsa da " thanks dad , Allah yatsare" yashiga ,aka tada motoci sai airport.

Mami ta juyo garesu tace ku dai ji abinda daddyku ya fada Koh"

Siyama tace" kyalesu kawai Mami, su ma su San hali daddy ai"

Isa yace" toh malama muji"

Siyama tace" Mami kina ganishi Koh"

Mami tace" yi hakuri daughter muje ciki"

Aliyu ya nufi side nashi kenan Ammi ta kirashi, ya bi bayata,

Tace" ummi fa tace lallai kaje ka gaisheta, almost six years kenan Bata saka a idon taba, tace so kake ta mutu sana kaje gani gawata, so abunda nakeso dakai, yau ko gobe kaje kadubata"

Yace" Ammi sai dai gobe, tsohuwa na tajika fitina da takura"

Ammi tace" wato ummi nane Mai takura ko?

Yace" uhm uhm Ammi yhkr, kiga basai naje ba, kawai zakirata na gaisheta"

Ammi tace" toh baka Isa ba, umarni nake baka, ba shawara ba, gobe Sunday kashirya kaje kaduna find"

Yace" toh rankishidade naji" yashafa mata kumatu Yana dariya"

Ammi tace" iyye Aliyu ka Raina ni fa kamaryar Dani kaka ka a gida na"

Yayi dariya yace" Ammi afuwa, ni zan fita"

Ina zakaje? ta tambaya

Yace" gidasu suhaima"

Tace " uhmm Aliyu tunda yanzu karfe daya ne kabari sai kayi sallah sai kaje Koh"

Yace " haka ma yayi"


Two nayi, yakira suhaima yace mata gashina zuwa, ya kashe Kira baiko jira yaji amsataba, yakira Hafiz ,

Yace" buddy muhadu mana ka rakani gidasu suhaima"

Hafiz yace" shifa ba inda zai je, amarya kana Bata da mutunci ko kadan , ka Kira haydar ko fawaz kila suje, ama kasa Suleiman ko kallo ka ba zaiyi ba"

Aliyu yace" banso rakiya ko dayaku, kuyi zamaku" ya katse kira.

Ya wuce dakisu su rahma yasamesu su idar da sallah ,

Yace" yanmata Ammi kushirya kurakani "

Sofia tace" Yaya Ina zamuje?

Yace" gidasu anty ku"

Ai da sauri suka shirya sharp sharp, suka fito suka sallami Ammi da Mami,. Zasu fita a motar daya , chief security ya taresu yace" yallabai kayi hakuri , oga yace Kar nabarka kafita batare da yara na ba"

Ya numfasa yace musu toh muje"

Aka karo motaci,aka tada motar suka fice daga compound din, har ga Allah Aliyu ba haka yaso fita da waena mutani, mtchewew yaja tsaki.

Su iso gidasu su suhaima , suna shiga suka wuce parking lot, daya daga ciki bodyguards yaje ya musu iso ciki gida.

Ciki babba parlor gida aka musu iso, Aliyu yasaki fuska ba yabo ba fallasa, rahma da Sofia na gefe suyi tsit kamar ruwa yacisu, da su San hali yayasu Sarai .

Kaya cinye cinye kalla masu aiki suka jera musu a gaba, haka ma nasha, bawanda ya kalli abubuwa da aka jera, tunda ka Aliyu harsu Sofia, hankali su na wayoyisu.

Ana Gama dire abubuwa cinye cinye hajiya binta ta sauko Tasha lace Mai tsada tayi kyau tace" sannu da zuwa Aliyu " har kasa ya durkusa ya gaisheta, ta amsa da fara'a , su rahma ma suka gaida ta,

Tace" lafiya klau yanmata zaiya sani sunaku ?

Sofia ne ta amsa ni suna Sofia ita Kuma rahma"

Hajiya binta na murmushi tace" wow nice name kuyi kyau fa"

Rahma Mai baki tambaya tace" Ina antymu?

Hajiya binta tace" tana zuwa, yanzu zaku ganta" Bata gama rufe baki ba sukaji Kara takalmi kwas kwas ,

Hajiya binta tace" gata ma ta karaso bara nabaku guri"

Suhaima ita da feenat susha gayu suyi kyau , ko sallama basuyi ba, dukasu susha fitted English gown da high heels, kana ba ko daukali, kitso attachment ne har gado baya sai sheki, suyi kyau a fuska , ama aciki su suke kamar pencil 😄.
Dagudu suhaima ta nufi Aliyu Wai zata rugumeshi tana karasa ya goce ta fadi a cushion dayake zama, Abu ya matukar Bata mata Rai ya disgata agaba friend nata, ama ta daure ta fuske kamar ba'ayiba.

Feenat tabude baki kawai tana kallo aliyu, gaskiya guy Dina ya hadu wow suhaima tayi sa'a miji Wana giant and handsome guy haka, tace Ashe dole ta nacemishi ta fada azuciya"

Suhaima tace"welcome back darling, ya hanya ?

Lfy ya amsa ba yabo ba fallasa"

Tace" feenat ga aliyu, nasan baki taba ganishi ba"

Feenat ta washe baki kamar gona auduga tace" sannu da zuwa " ya amsa .

Sofia da rahma na gefe suna kallo ikon Allah.

Rahma ta rage murya tace" Sofia mun gaishesu "
Sofia tace" ai Yaya bai ce nayi gaisuwa ba, bazan yiba, dubesu fa ko kyau Basu dashi, suyi kwaliya kamar zombie🧟(😆) "

Rahma tace" nidai baruwana zan gaishesu"

Sofia tace" then go ahead, who stop you" ta juya Kai ta cigaba da buga game,

Duk abuna suhaima da feenat basusan su Sofia na parlor ba, sanda suka tsinci murya rahma na gaisuwa, suhaima ne ta amsa da wow preeties yakuke?

Rahma ta amsa Tana ta minsila Sofia aka ta daga kai"

Sofia tace" ohh assh"

Suhaima tace " oh sorry ya sunaku ? Suka fada mata.

Tare da darling kuke ta sake tambaya

Eh suka amsa

Sofia tace" kece auntymu ? Eh tadaga mata Kai

Sofia tace" toh Mai yasa Yaya daya gaki ya hada fuska?
Nantake suhaima taji wani dum , tambaya yazo mata a bazata, tarasa wani amsa zatabata, Aliyu ne ya amsa dun yasa Sofia da iya zare zance, har Mami zata iya gayamasu.

Yace" ohh little sis , fushi nake da aunty naku"

Rahman tace" why yaya?


Aliyu yayi murmushi aka zuciya shi Kuma yace another one 😅, yace" tun jiya nake Kira number ta Yana ringing Bata daukaba, ya juya ga suhaima yace hakane ko dear " ya kashe mata ido daya

Tace " eh hakane " har murya ta na rawa, am busy ne shiyasa, a zuciya ta tace ni suhaima nashiga uku Ashe haka take"

Rahma tace" toh Yaya kayafemata please?

Yace" nayafemata"

Rahma tace" anty yaya, ya yafemiki kinjiko"

Suhaima tace" oh thanks little angels nagode sosai, Mai zakuci ?

Sofia ta yamutsa fuska Wai tana kyakyamin su tace" mun koshi"

Suhaima tace" ga cookies baza kuci ba?

Rahma ta amsa da a'a mun gode anty"

Su dan taba hira ba yabo ba fallasa, sai da sukayi sallah la'asar sanan suka bar gida.

Suna dawowa daga rakiyasu ,

Feenat tace" shegiya nawa kiyi sa'a husby fa, ya hadu ama fa kamar magani Nan bai aiki fa"

Suhaima tace" ke share mom tace Kar indamu Wai tunda za'ayi aure ita zata handle komai" hhhh sukayi shewa har da tafa hannu .


Aliyu a hanya su na dawowa, rahma da Sofia suka duga ma Yaya Aliyu dariya, Wai amaryashi na Kama da zombie, kamar mujuya, sai su fashe da dariya, Sofia har kokoyo yanda suhaima ke magana, Aliyu abun ya dameshi ya daka musu tsawa, sukayi shiru kamar basuba.

Suna isa gida ko gama parking ba'ayiba ya sauka ya wuce part nashi , Yana shiga toilet ya watsa ruwa, ya fito , triquater kawai yasa fari, baisa riga ba, ya nufi guri motsa jiki, ya Kira Dan liti yazo mishi da ruwa.

Dan liti yazo da ruwa ya samaishi Yana kan push up yayi ba adadi , ya Mike , Dan liti ya Mika mishi ruwa da karami towel, ya share zufa, ya rataya towel din a wuya, ya kafa baki tas ya shaye ruwa yayi wurgi da gora a dustbin.

Dan liti yace" sannu yallabai" ya amsa da hannu, zai sake magana yace" please Dan liti yaisa banaso ji hayaniya"

Dan liti yace" afuwa rakashidade Allah ya huci zuciya ka, ya kwashe mishi wayoyyisa,

Aliyu ya wuce toilet , Yana kan shower yaji ana Kira sallah mahgrib , Yana gama ya dora alwala, ya fito yasa jallabiya Mai ruwa chocolate , ya wuce masalaci , Yana zuwa ana tada sallah , baya su idar ya tsaya ya karatu alqur'ani har akayi Isha, ana idarwa yayi Azkar , ya wuce ciki gida , yayi sallama , ma'aikata ne keta zirya hada table , dukasu suka gaisheshi ya amsa, ya tambeyesu Ammi , suka amsa da tashiga sallah.

Ya kwanta aka dogo hadade cushion dake parlor, ya kwanta shiru, ya lumshe idon kamar Mai bacci, Kuma ba bacci yakeyi ba , yarasa maike mishi dadi, jiya da yau haka kawai sai yaji gabashi na faduwa, ya rasa dalili.
Mami ta shigo tace" son lafiya dai ko " ta taba goshi taji ba zafi.

Yace" lafiya mami, na gaji ne "

Tace" eya sorry boy, taso kaci abinci sai kaje kasha magani" ya Mike yaje ya zauna a dining room table , Mami tayi serving nashi.
Ammi fa yatambaya

Mami tace" tayi baki , oya boy ci abinci cika"

Yaci abinci sosai yabin da ginger juice.

Yace" mamina sai da safe"

Tace" boy baza ka tsaya munyi hira ba"

Yace" Mami inaso na Kwanta da wuri saboda gobe zanje kaduna da safe"

Tace" guri ummi Koh?

Yace" eh Mami good night"

Tace" sleep well my boy"

Yace " thanks Mami "

Yana zuwa daki yarage Kaya jikishi, ya rage dagashi sai boxer ,ya Kara kure A.C daki, abun mamaki naga ya dauki wani karami remote yadana, sai ga wuta daki ya canza color daga fari zuwa dim light, ya dauki wayashi yaga missed calls dinsu fawaz , sai na suhaima Dana wani friend nashi dake Russian, ba Wanda yakira acikisu , Airports direct yakira Yana tambayesu ko akwai flight din zuwa kaduna na safe"

Agent din ya amsa da no sir , babu na safe, saina karfe hudu, yace okay thanks , agent din yace u r welcome sir thanks for calling , ya kashe waya yayi addu'a bacci ya gyara kwanciya.

Washe gari, Yana idar da sallah asuba yafara hada Kaya,yace two days kawai zanyi na dawo gsky, Yana Gama hada Kaya ya wuce ya gaida Ammi da Mami ya sanar musu 8:00am zai wuce kaduna.

Mami tace" flight din karfe nawane ?

Yace" no Mami ni bazan iya jira jirgi ba, har 4 ba "

Ammi tace " na shirya su rahma su rakaka?

Yace" Ammi kibarsu zasu sami ciwo Kai"

Ammi tace" uhmm ama dai ka sanar ma driver ka ko?

Yace" a'a Ammi ama zangayamusu, Ammi Mami Ina Gama shiri Zaku gani"

Mami tace" ka tababatar kayi breakfast fa "

Toh Mami".

Yakira Dan liti yazo ya hada mishi breakfast, ya sanar mishi zaiyi tafiya , zai je kaduna"

Dan liti yace" yallabai jirgi zaka bi?

Yace" a'a Dan liti"

Dan liti yace" toh yallabai naji cewa hanya Abuja zuwa kaduna ana gyara , ba hanya"

Aliyu ya tsaya shiru , yasa dan liti da sauraro news Kuma bai karya, ko nafasa

Please Login or Register in order to submit comment