Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi rai sosai .. Yana kallo mutani yadda duk inda suka wuce sai a kalleta waensu ma har day yi Mata magana.. Aliyu sai huce yake shi, dun Essha batasan ma Yana bayataba..

"Wai Maiyasa Dad baza su daura Mana aureba? This rubbish, maza su rika gani min ita ohh no, nasan waena masu gaisuwa ma bana Allah da Annabi bane I will do something"...

Baigama zance zuci sa ba yaji wani daga nisa na Kira Suna ta

"Hey Doctor Essha"

Yana kallo ta Jan ta tsaya, mutumi Kuma ya karaso da saurishi yace"Barka da zuwa Doctor, Suna na Doctor Jawal mustapha Jawal, am your colleague, night duty nakeyi shiyasa bamu hadu da Safe ba.. ki zo lafiya?

Essha zata bashi amsa taji a dagata gabadaya ta..Mutumi ya bin su da kallo suna hada Ido da Aliyu ya sukunyar da Kai ciki sauri Yana cewa"aa yallabai kenan barka dai?

Aliyu bai amsaba ila wani mugun harara da ya binshi dashi, nandana jikishi ya duri ruwa ya wucesu jeje..


Essha sai wurga kafa takeyi zata sauko duk kunya ya gama kamata, ds haraba asibiti gabadaya kallo ya koma kansu ne.waesu harda daukasu hoto.

Aliyu baidamuba. daga ita har Sadik ya Kara gyara musu riko daya musu.

Doctor Kamila Ganisu haka sanda ta dara ita ta ciro nata waya ta kashe musu hotuna tace" Honey Dina zai ga Wana su Buddy shi a fada tarko so" tayi dariya tay guri nata motar.


Sai tafiya yakeyi bai tsaya ba sanda ya iso guri motoci su, Security da suke tare yay sauri ya karbi Sadik daga hannu shi yasa shimfida shi ciki motar..


"Bring me down" Essha ta fada cike da matsifa

Bai sauketaba ya Kara matse ta dam a jikishi..

"Nace ka saukeni wicked guy, duk inda naje sai ka bani kunya Allah ya isana bazan yafe b...

Bata karasaba ta dago suka hado Ido ...

"Why did you stop,karasa man, ko zagi na zakiyi I like so baby please continue I want to be hearing your voice" ya fada ciki murya shagwababu yara..

Essha ta kufala sai kokari sauka take ta kasa, karshe da takasa sai ta koma dukan kirjisa.

Sai "ashhh wassssshhh" yakecewa Yana dariya can yace" zan so iriki goma su cigaba da dukana cus it doesn't hurt sai dai Kara sanyaya min zuciya da yakeyi please Baby continue"

Essha ta fashe da kuka ta kife Kai a kirjishi..

"Ohh Know Subhanallahi nasa Baby na kuka please forgive meee bazan Kara ba please kibar kukana it hurt me"

"Toh please ka saukeni kaga mutani sai kallo mu sukeyi da Girma Allah na rokeka ka saukeni please" Essha ta fada a hankali..

Aliyu ya dago fuskar ta sai Kai Mata kiss tayi sauri ta tareshi da taffu hannuta" please don't kiss me, wlh babu kyau ni fa ba muharama ka bace am not ur wife babu aure a tsakanimu, banason banason if u keep doing that I will dislike you" ta fada a tsawace.. ita kanta batasan ta fadaba

Aliyu ya sauke ta da sauri a hankali Yana mamaki abunda ta fada deep down Yana cike da murna" dama she likes me.. pretending kawai takeyi wow Alhamdullilah!!

Zai tabata ta buge Mai hannu Tace" please nace Kar ka Kara tabani" in Yana tabata ita kadai tasan yanda takeji..

Aliyu ya zame hannu shi da sauri"Baby I promise myself bazan Kara tabaki ma har sai ki zama malakina... But please repeat what you just said?

Ta tura baki tace"bansaniba"

Yayi murmushi Yana shafa Kai yace" okay okay nagane...

Ta dago tace" Mai ka gane?

Shima ya tura baki ya yi iri murya ta yace" basaniba"

Haka dayayi yabata dariya ama sai ta dake taja tsaki ta Kama zata wuce.. har zai riko ta sai yatuna alkawari da yayi. Ciki sauri ya shawo gabanta..

Murya rarashi yace"Please Baby.. bai karasaba ya tsaya ya na kallota yanason ne ta daga ido ta kalleshi ai kuwa ta daga. Ya zuba Mata lumsasu sexy eyes Dina Nan ta saukar da nata da sauri..

Tace" gida fa zan wuce ka tsare min hanya imba zakayi magana ba ni kaba hanya na wuce" ta fada kamar raha ita a nata matsifa takeyi..

"Uhm shine nakeso muje tare" ya fada

" No kowa yayi hanya shi ai ba tare muka zo ba, Ni fa kaban hanya na wuce 6:20 ya kunsa" ta fada kamar zatayi kuka..

Ya tareta"please Baby Kar kiyi kuka, bai kamata kibin hanya ke kadai ba.. kiga ke mace ne. So kike Yan kungiya su sake tareki su daura Miki aure da wani ba ba huh?

Essha ta dago ta baka Mai harara ta bin gefeshi ta wuce..

Ya tsaya Yana kallo ta na tafiya ya Kira sunata"Esshhhhhhhaa"

ta ja ta tsaya cak..ji tayi duk duniya nan babu Wanda yakaishi iya Kiran suna ta.

Aliyu ya tako a hankali ya karaso inda take ya hada hannuwashi alama roko"please, not for my Sake.. Da Allah ki zo muje please da Allah ne na hadaki kinji?

Essha ta juyo a hankali ta kalleshi duk yayi zubin tausayi ta sauke ajiya zuciya tace"Ok naji but my car"


"Bring the car key Moses zai biyomu dashi"

Essha jiki a sanyaye tasa hannu ta ciro car key din ta Mika Mai tanu na mishi motar,ya Mika ma Moses din..

Dakashi ya bude Mata kofar ta shiga Suka sa Sadik a tsakiya. Driver ya tada motar..

Shiru kakeji a motar, dun Essha titi ta koma bin da kallo tana tunani yadda zatayi ta karbi wayashi ta Kira Pooja.. tasan Pooja da tauri kai"Wai ma ya akayi ya samu number ta har suka Saba? Ta tambayi kanta

"Sadik man" taba ma kanta amsa.. ohh nooo. Nasan yanzu na koma na kirata da wani layi ba daukawa zatayi ba na shiga uku"

Aliyu kam hankali shi kwance he's so happy.. Yana addu'a Allah yabarsu tare haka.. sai shafa kan Sadik yake Yana zuba murmushi..

Can yaji Kara message ya shigo wayarshi ya bude yaga message din Pooja ne tasa"Hey Lover Boy, nasani Sarai zakaiya cewa zaka bata wayarka, toh please Kar ka Bata in Kuma ka Bata ni baruwana daku .. kabarta mu gasata kadan nasan halita Sarai Bye"

Aliyu yayi murmushi kamar ta San abunda yakeshiri yi kenan gashi Aunt Pooja ta dakartashi. Ya kalli gefeta yaga haryazu titi take bin da kallo yay murmushi kawai ya kauda Kai..


Baya wasu awani su iso gida..lokaci har anfara kiraye kiraye sallah magarib.

Essha gani ba kowa yasata ta bude kofa ta sauko da sauri dun Kar kowa yaganta.. batasaniba Daddy ta na kallosu daga window dakishi... Dun ya kureta yasa ya fito da niyya zan shi masalaci. Yana fitowa Aliyu da shumaci ya fito ya gaida Daddy har kasa.. Daddy ya amsa ciki sakewa fuska.

Essha ta gaisheshi bai amsaba karashe kada Kai yayi ya ficewarshi zuwa masalaci..

Ta Mike ta baka ma Aliyu harara ta dauki handbag dinta ta wuce ciki.

Su Mummy suka Mata Sannu da zuwa.. ta amsa .

Walid ya karaso ya karbi Handbag dinta ciki tsokana yace" barka da dawuwa Matar a gida Young Tycoon"

Essha rakwashi ta zuba Mai tundama tana ji da haushi ta amshi jakata ta wuce ciki. ..

Su khairat sai Dariya suke mai da Allah ya Kara ...


Essha tana shiga toilet ta fada ta watsa ruwa ta Dora alwala ta fito ta shirya ciki simple gown tayi Sallah magrib, ta jira Isha'i ta bin ta na idarwa ta tada ... Shafa'i da wutr ta idarwa tayi Azkar ta shafa.

Ta Mike ta dau wayata ta dialing number Pooja Yana ta ringing Taki dagawa, ta Kira yafi a kirga still ba a daukaba.. ta damu sosai Bata taba tunani Pooja will be serious hakaba..

Ta dialing number Bestie Tana daga. Ba sallama ba gaisuwa taji Sumy ta fashe Mata da dariya..

Essha tace" ke Wai lafiya ki? Daga nakira mu gaisa shine kike min dariya ki kyauta Bye nagode"

Bestie ta rike dariya tace"Haba dai naisa iminki dariya bude WhatsApp dinki yanzu Zaki ga message na tura Miki zakiga abunda nake ma dariya"

Essha ta katse Kira ta kunna Data messages suka fara shigowa ta bude na Bestie taga pic ne man ta tura Mata. Ta bude pic din. Tana Sallati dun Hotosu ne lokaci da Aliyu ya dauke da Sadik. ..

Essha tasa Hannu akai tace"wayyyooo Allah nashiga uku, Allah kadai yasan inda hoton na zai tsaya yanzu"

Ta Mike ta fara zarya a daki Nan taji Kara message ya shigo da sauri ta duba taga Pooja ne ta turo Mata da message. Ciki sauri ta bude taji Kamar ta fasa kuka still hoto ne harda Kari A&A FAMILY........




Ariga min afuwa da uzuri masoya πŸ₯Ί πŸ₯ΊπŸ™πŸ™πŸ™


Baby Salmah wish you quick shifa 😘😘 😘


#Comment#πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°
#Share#πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ


*WRITING BY*
*J Hajara*


🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“š πŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________


8️⃣3️⃣&8️⃣4️⃣


"Wayyo Allah na... Yanzu in Daddy yagan hoto na Mai zan ce mishi.. ni dai kam na banu gaskiya am not happy with the person da ya dau hoto na" cewa Essha da keta fama Safa da marwa a daki..

Ta nemi guri ta zauna a bedside tana tuna incident din.. abun ma dariya ya bata can karshe makwashita ta furta"Mad guy" tana dariya..

Taji budewa kofa an shigo da sallama.. ta dago ta amsa ... Mufeedat ce ta shigo.. ta karasa gefe ta, ta zauna tace"Sis Essha Mummy na kiraki..that you should go and have your dinner"

Essha ta Bata fuska tace" No ni na koshi"

Mufeedat ta Mike tace" zanje nagayama Mummy cewa kice baza ki ci girki taba" ta fada Tana tafiya..

Essha ta Mike da sauri ta kamata tana dariya tace" Autar Mummy dun kawai nace na koshi shi ne harda shairri"

"Eh mana.. Mummy tace tasaki.. tun abinci safe baki ci komai ba..so ki zo muje ki ci abinci ko naje na fada Mata kince baza kici ba"

Essha ta ja Mata kumatu tana dariya tace" yanda kike zakewa na..nasan ba Mummy ce tayi girgiki ba..ke ce ko.adai dai kenan toh bazaci jagwal ba ehen" cewa Essha.. ta koma gado ta kwanta..

Mufeedat tayi rau rau da ido zatayi kuka tace"Sis saboda ke fa.. yau nayi kirki shine kince baza ki ci ba toh zanje na hadaki da Daddy" ta fashe da kuka ta bude kofa ta fita..

Essha ta sauko da gudu ta bi bayata tana"am sorry little sis yihakuri, kawai na loosing appetite ne shiyasa but zanji kiyi hakuri"

Mufeedat ta ja ta tsaya.. har Essha ta karaso wurinta. Ta Bata hannu su ka karasa wurin Dinning..

Ta zauna mufeedat ta serving nata Tuwon shinkafa miyan taushe. Kadan ta ci ta mike..

Mufeedat dake tsaye gefeta tace" Sis badai ki koshi ba?

Tace" Eh autar Mummy na koshi, let's go"

Ta ja hannuta zuka fito zuwa main parlour inda suka tarda Family zaune suna kallo .. Essha ta nemi guri ta zauna gefe Mummy ..

"Kinci abinci kuwa? Mummy ta tambayeta..

Tace"Eh Mummy naci"

Mufeedat tace" Mummy kadan ta zakula ta tashi"

Mummy ta kalleta, ciki sauri tace" Allah Mummy na koshi , around 5 fa naci Snacks da Malt am full Allah Mummy na koshi"

Mummy tace" toh naji Essha, ya Office din?

Ta amsa da"Alhamdullilah mum"

Mummy tace" badai matsala bako?

Tace"Komai normal mum, naji dadi aiki a wurin"

Mummy tace" toh MashaAllah, Allah ya taimaka"

Ta amsa da ameen..

Nan suka cigaba da kallo film din ama badan Essha da ta fada duniya tunani..

Amir dake kwance sama Sofa sai chatting yakeyi, Naga ya Mike zumbur ya nufo Essha yace" Sis Zokigan, yaushe kuka dau hoto na? Wow wlh kuyi kyau"

Mufeedat tace" Yaya mungan"

Essha ciki ranta tace"Allah yasa ba hoto na bane"

Amir yace" Sis kamar fa dukaku bacci kuke a kafa...

Essha ta taso ta rufe Mai baki ta kwace waya a hannushi tana kallo hoto.. posting akayi asa Young Tycoon and family Essha tace"Inalilahi waina ilaihi raju'un a Instagram fa wayyyooo ni Aisha na shiga uku"

Khairat da Walid har suna hada Baki guricewa"Sis lets See, hoto Mai akayi posting"

Essha tace" bazan nuna ba parrots kawai"

Walid ya Kama baki yace" uhmm inji Mai ciwo hakori, nayi shiru"

Mummy tace" Essha wani hoto ne muga?

Essha ta Soma bara bare baki tana wuki wuki da Ido kamar Mara gaskiya ta bude baki zatai magana sukaji shigowa Daddy da Sallama shi ya shigo rike da carbi.. duk suka amsa. Essha duk ta tsorata a zuciya ta tace" shikena asirina zai tonu"

Daddy ya binsu da kallo daya baya daya yace" lafiya nagaku a haka? kuyi wani zuru zuru daku, Kamar marasa gaskiya"

Ciki sauri Amir ya bashi amsa yace" Daddy ba komai everything is ok" ya fada Yana kallo Essha..

Daddy ya kalli Essha yace"zonan"

Nan take taji cikita ya duri ruwa, ta tako a hankali ta karasa gabashi ta zuguna tasoma inda inda tace" Walahi Daddy shine ya nace zai dawo dani,nima banso ba, walahi talahi Daddy ba laifina bane.. Shine ya nace sai n...

" Common Shut up, did I ask you? Daddy ya katseta..

Ta girgiza Kai, har idota ya Soma Tara kwala..

Daddy yace" toh rantse rantse na maiye? Ki tsargu kenan?

Tayi shiru ta kasa bashi amsa kanta a sukunye tana hawaye..

Daddy yace" Essha kar kiga kamar na sake Miki da yawa kinema ki ja min magana, toh Ina Miki gargadi da kima mutuci kanki, Know what to do at the right time kinajina?

Tace"Ehhh Daddy .. da Allah kayi hakuri "

Daddy yayi murmushi yace" bakomai am just warning you ne kiriga kiyeyewa..tashi" ya Mike ya kalli su Amir yace"Good night guys zanje na kwanta"

Khairat tace"Daddy da wuri haka?

Daddy yayi Mika yace" Eh Khairat na gaji shiyasa sai da safeku" ya wuce dakishi..

Mummy ta Mike Tace" Nima na wuce sai da safeku"

Amir yace" Kai Mummy Yanzu fa Nine ne, Daddy ya wuce keman yanzu Zaki binshi"

Mummy tace" Eh.man Mai zan zauna na muku ku ga tafiyana, ku tabbatar kuyi addu'a kafi ku kwanta"

Suka amsa da"zamuyi inshallah mum good night"

Tana wucewa Amir ya juya kan Essha yace" Sis bani wayana Nima daki zan wuce"

Essha da duk jikita a mance yake ta Mika Mai waya a hankali tace" please bro Kar ka nuna ma kowa please na rokeka"

Yayi murmushi yace" Sis trust me bawanda zanunama wa I promise you"

Tace" yawwa thanks bro sai da safeku"

Walid yace" ana kus kus intai tsamin maji, uhm bara naje nayi Video call da Boy Dina(Sadik) sai da safeku"

Essha tayi dariya ta kalleshi ta girgiza Kai batace komai ba ta wuce zuwa dakita..

Amir ya jawo Walid yace"mlm baka'isaba tare zamuyi"

Khairat da mufeedat suka jashi suka zaunar dashi khairat tace"ai ba boy din ka bane Kai kadai hardamu oya call him damu za'a yi"

Yayi dariya ya dialing number Sadik .. duk suka zauna agefeshi suna jira Sadik ya dauka.. ba'afi second ba Sadik ya amsa cike da murna ganisu..

Essha nashiga daki ta fada gado ta kududune da bargo ta ja waya ta dake gefen gado.. ta bude taga ankirata har five missed calls gani number yasa taja karami tsaki ta sake gyara kwanciya ta, ta tashi ta kashe wuta daki ta zauna baki gado tayi addu'a ta gyara kwanciya.. sai juye juye take takasa bacci.. can taji Kara message yashigo wayata ta lalubo waya daga gefeta ta kunna ta bude message din taga Number Aliyu ne ta saki wani naunaya ajiya zuciya ta bude message din dun ta karata" Hi Sweet in the middle" ya jero emoji aciki Mai kanen idon πŸ˜‰ sanan ya daura da" just wanna say Goodnight dream about me"

Essha ta dafa Kai Tana dariya tace" Wana Sam baida kunya ni ne ma Sweet in the middle din hmmm"

Ta aje waya ta lumshe ido Nan kuwa bacci ya dauketa ciki kwanciya Hankali..



After one week
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

Essha a kullum tana zuwa office.. tayi matukar sabawa da su.. matsala ta daya yanzu. Na Rashi daga Mata Kira da Pooja batayi, Har Bestie ma yanzu itama tashiga layi a kullum sai ta kirasu har Kira ya tsinke baza a daukaba. Yana matukar damuta. and again Aliyu tun Ranar da ya sauke ta a gida Bata sake sashi a idota ba.. kullum sai Mata text message.. ta rasa dalili dayasa tay kewashi haka she really miss his beautiful and kind face. Tanason ganishi ko zataji sanyi yanzu ta daina yaudara kanta ta Amince ma zuciya ta da ganga jikita tanason Aliyu.. ta rasa maiyasa yaki zuwa wajenta ..

Wana bakomai bane illa shawara Pooja itace ta zu zuga Aliyu aka yashare Essha na kwana biyu suga iya gudu ruwata, Aliyu daurewa kawai yakeyi shikanshi yanason ganita he really Miss her.. Su Haydar ne ke ta kwanta Mai da hankali aka ya jure ya dage da addu'a ya riga hadata da Allah inshallah zata sonshi (kunji πŸ˜‚ abokaina arziki) Aliyu tsoroshi daya Kar Monday ya zagayo a sake tambaya ta Tace bazata koma ba.. sai addu'a yake ba dare ba Rana Allah yasa ta Amince asake daura musu aure, duk ya ra rame ya Hana kanshi sukuni, Aliyu baisan addu'a shi ya Dade da karbuwa ba dun Dr Essha ta Dade da fada sonshi.

Sadik Yana samu kulawa sosai guri family gabadaya gata sosai suke nuna Mai da So da kauna.. Ammi da Mami ne suke koya Mai Hausa dun har ya somaji..

Monday, 2:56am

Essha zaune take a office nata, ta kifa Kai a table ta rasa Mai ke Mata dadi, wata nurse ta shigo rike da files, Essha naji shigowar ama ba Mike ba.. Nurse din ta fara buga table din a hankali. Essha ta Mike. Nurse din ta gaidata.. ta amsa..

Nurse din ta aje files din kan table din tace" Doc files din new patients ne aturosu nane ganiki, ran Friday zu zo Basu samaiki ba shiyasa suka sake dawuwa yau he's the files ma"

Essha ta gaida Kai kawai batace komai ba.. ta dauki Shade(πŸ‘“) ta manna a Ido ta Soma duba files din, sanda tagama dubawa ta dago tace" kince musu su shigo"

Nurse din ta gaida Kai tace" okay Ma" ta fita can sai gata ta dawo da tace" Doctor gasuna su iso"

Essha tace" let them in"

Nurse din ta Basu hanya suka shigo, Mata biyu ne sai namiji daya shima yadan manyata dun fur furane gabadaya kanshi.. da Sallama suka shigo Essha ta amsa ta nuna musu kujera su zauna.

Tunda suka shigo tsoho na kebin Essha da kallo ita kam ma batasan yanayi ba dun laptop nata ta jawo ta Soma rubuce rubuce sanan ta dago Kai ta kallesu tace" wacece Hasiya Saeed aciki ku biyu?

Yar dattijuwa tana nuna yariya dake gefeta tace" gata, itace ba lafiya, wlh likatan Sam Bata iya bacci Mara ke Mata ciwo, yau ma Dakar taiya mikewa"

Essha ta Mike rike da Stethoscope ta rataya a wuya tace" Allah sarki let me check her, tana da aure ne?

Matar ta amsa da" a'a likitan Bata da aure"

"Shekaru ta nawa? Essha ta sake tambaya


Matar tace"Sha bakwai"

Essha ta gyada Kai, ta umarci yariya ta tashi ta kwanta a gado duba marasa lafiya..

Matar ta taimaka Mata ta kwantar da ita.. Essha tasa handglove ta dago ta kalli tsoho ta tsorata Dan iri kallo da yake binta dashi ta daure tace"Baba ka Dan bamu wajen zan dubata"

Matar da suke tare ta dafashi tace" haba mallam dakai fa take Magana"

Tsoho yayi sauri ya gyara zama babba rigashi yace"toh toh naji bazan fita" har zai fita yasake dawuwa da fara'a a fuskashi ya kalli Essha yace" yariya inku gama inada magana dake"

Essha ta dago Kai ta kalleshi tace" ni Kuma?

Yace" eh kefa nasan baki ganeni ba ama dai ku gama tukun" Yana fada haka ya sa Kai ya fice..

Matar tace" yihkr likita tsufa ne duk kesashi haka da Allah kiyi hakuri"

Essha girgiza Kai Tana murmushi tace" aa badamuwa"

Nan tasoma duba Mara lafiya Tana Mata tamboyoyi, yariya na Bata amsa.. Essha ta mikar da ita tasoma rubuce rubuce Tana gamawa ta Danna wani kararawa sai ga wata nurse ta shigo , Essha ta mika ma Nurse din paper dake hannuta tace" ki kaita amata Tests dake ciki guri, inku gama ga Wana paper scanning ne zasu Kai ta su kawo min results din ina jirasu"

Ta juya gun Matar dattijuwa tace" Mama tare zakuje zaa Mata tests da scanning, Nurse dinna zata kaiku in agama sai ku kawomin results din ki fahimta?

Mama ta Mike Tace" nagane likita sai mun dawo"

Su ka fice tare da nurse din.. suna fita Essha ta jigina da chair ta lumshe ido tana tuna magana tsoho na sai tambaya kanta take"when did we meet? At where? Kai bansashiba Killa Mai Kama Dani ne ama ni bantaba ganishi ba" Sai taryo fuskarshi take ko zata tuna inda tasashi ama takasa..

can taji anturo kofa anshigo da sallama ta amsa tasa Mai murya Haka yasa ta saki murmushi ta dago Kai ta bude baki da hanji tana kalloshi.. Sadik ne sanye da School uniform Navy blue and white kana yasha gyara sai walkiya yake, kafashi yasha sneakers baki na school, bayashi rataya yake da school bag shima baki Yana murmushi ya karaso gabata yasa hannu ya rufe Mata baki yace" Mummy kure baki" yanayi yanda yayi hausa sai yabata dariya tasoma kyakatawa da turanci yace" Mummy ai nayi kokari ko"

Essha na dariya ta gayda Mai Kai ta rugumeshi tace" tun yaushe ka Soma zuwa makarata?

Yace" last week mum, Mummy ki daina min English granny ta Hana am learning my language"

Essha ta ware Ido she was surprised Sadik ne yay hausa Haka ta furta"Wow boy shake me, kayi kokari wa ke koyama?

Yace" granny ne"

Tace" ama granny tayi kokari"

Tayi shiru tana kalloshi yayi murmushi ya ja Mata hanci yace" mum baki tambayi Dad ba"

Tace"Sadik zo zauna tukun yanzu dai waye kawo ka Nan"

Ya kada kafada Yana murmushi Yace" I will Never tell, you should guess"

Tayi murmushi tace" nasani ai Daddy Kane"

Yayi dariya yace" yes, you guess it right"

Tace" maiyasa bai shigo ba?

Sadik yace" Masalaci yaje, inya idar da Sallah zai shigo"

Ta hada fuska ta kalleshi tace" maiyasa baka binshi zuwa masalaci ba?

Yayi dariya yace" Mummy calm down, ai muyi Sallah a School"

Ya sauke school bag nashi yafito da leda restaurant ya bude ciki yafito da chocolate da hamburger, da soyamilk. Yace" mum Bismillah"

Ta shafa Mai Kai tace" ci lafiya"

Ya Bata fuska ya bude hamburger yakai mata baki yace" Mum eat, if not Nima banza ci ba"

Essha tayi murmushi tayi gasa daya ta soma feeding nashi har ya cinye ta bude fridge ta mikamishi bottle water Nan sukaji sallamar..

Suka amsa.. dattijuwa nane suka sake dawuwa ta kalli Sadik tace" yi gaisuwa"

Sadik ya sauka ya tsuguna har kasa shi a Dole zaiyi gaisuwa da hausa yace"Inna anniku"

Gaisuwar Sadik duk yabasu dariya, Nurse ta dagashi tace" Fine Boy ina Iniku ake cewa ba Inna anniku ba ka gane"

Sadik ya boye fuska Yana murmushi shima yace" aunt thanks for correcting me"

Nurse tace" you are welcome fine boy"

Nurse din ta Mika ma Essha results din ta fice Tana daga ma Sadik Hannu..

Essha ta bude results din tasoma dubawa ta dago dun tayi magana charaf Idon ta ya sauka kan tsoho Nan sai bin Sadik yake da kallo Yana murmushi, Essha tayi shiru dai batace uffan ba, ta kalli Mama tace" Mama results Yana nuna cewa yarki PID ke damuta"

Charaf Sadik yace" Mum what's The meaning of PID?

Essha ta harareshi tace" banason na karaji muryaka ana am I cleared?

Ya gyada Kai yaciga da cin Chocolate nashi..

Ta kalli patients nata tacigaba tace" Mama PID Yana nufi Toilet infection shine yamata kamun har yake sosai har yake rike Mata Mara, zan Bata maguguna Tasha nan nada sati biyu tasake dawuwa mu dubata.. inshallah ma zata warke sai dai Kuma ku riga kiyayewa dun..

"Assalamualaikum? Sallama daya katse Essha harta kasa cigaba da bayanita dun ji Mai murya ba karami Kwantar Mata da hankali yayi ba har tana sauke wani naunaya ajiya zuciya ta bin kofa da kallo.. takasa amsa Sallama ma.. Su Sadik ne suka amsa..

Aliyu ya shigo da Murmushi a fuskarshi as usual ya turo kofar ya jigina akai Yana kallota he feel happy daya ganta har Yana wani lumshe Ido..

Please Login or Register in order to submit comment