Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi dariya tace" kila rowa Dan zasu mana"

Mummy kam kala batace ba tayi gaba abinta.

Hajiya tace" kuzo munshiga ciki, matar Yayaki na na zuwa su gaida ki"

"Allah sarki hajiya da so kuwa nagasu kisan ayi biki ba na Nan" cewar Essha

Aina'u tace" Kar kidamu Zaki gansu har ki gaji"

Suka shiga ciki sashe Daddy, Hajiya sai matsifa take" Sadik yazo bai huta ba shaidanu yara harsu shiga dashi gari"

Essha tayi kewa sosai yau ganta ciki family ana hira sai taji sanyi a ranta, Delicious food kala kala aka tanadar mata kowa a guri nasan ta ci nashi tazama Yar lele, Big mum ta Kira sukasha hira sosai, suna Gama waya da big mum ta Kira Pooja, abun tausayi Arundh haryanzu kuka take, karshe ma Pooja kashe waya tayi hira da ba'ayi kenan ba.

Wurare la'asar duk kowa ya watse, masu aure kowa yayi hanya gida mijishi, aka barta dasu mummy dasu amir, sai a lokaci ma ta lura da canzawa mummy, gashi ta damu na Rashi dawowarsu khairat, tunda suka fita Basu dawo ba har ana neman magrib, hajiya dakata ta kirasu su dawo, sai da Isha suka shigo, su Sha fada sosai kuwa aguri Hajiya.

Amir dakashi ya bashi abinci, yamishi wanka ya shiryashi suka wuce masalaci. Har lokaci mummy Bata saki fuskar ba.

Essha na idar da sallah Isha ta shigo daki mummy da sallamata, ta samaita a daddurma tana ja carbi mummy ta amsa sallama, Essha ta karaso shigowar ta zauna a gefe mummy, mummy ta shafa Addu'a ta kalli Essha fuska, Essha ta gaida ta, ta amsa ba yadda ta saba amsa gaisuwarta ba, Essha Bata ji dadi haka ba murya a hankali tace" mummy ko dai laifi na Miki ne Naga tunda munka shigo ki ka canza?

Mummy ta kalleta shiru Bata Bata amsa tambaya ta ba can Tace" ina da magana dake ama ba yau ba sai gobe inda ki ka huta"

Essha taji gabanta ya fadi tace" mummy dafata dai lafiya ko?

Mummy zatai magana, sukaji an bude kofa an shigo da sallama duk suka amsa, Sadik ne Yana sanye da jalabiya fari fat, yamishi kyau, ya shigo da murmushi shi as usual hannu shi rike da iPad da packet din Laddu( alewa ne na kasa India)

ya nufi mummy yace" Granny I bought this for you, open your mouth, it's sweet it won't hurt your tooth"

Mummy batayi niyya murmushi ba sanda tayi taji tana matsifa son yaro.

Sadik ya bude baki yace" Granny Haaa?

Ya dauki laddu daya yakai saiti bakita, Mummy ta bude baki a hankali yasa mata, tana taunawa Tace

" Wai waga abun zaki shi yayi yawa ama akwai dadi" tanayi ta na lumshe Ido..

Sadik bai daiji abunda ta fada ba gani yadda takeyi da fuskar ne yabashi dariya.. Essha ta Mike jiki a sanyaye zata fita mummy ta dakatar da'ita

"Ki kaishi guri Daddy ku karami tun safe yake yake tambaya shi, yanaso ganishi"

Murya a sanyaye tace" toh mummy, Sadik let's go"

Sadik ya make kafada wai shi da mummy zai kwana, sanda tayi dagaske sanan ya binta, ya na daga ma mummy hannu, suna fita Mummy ta zuba tagumi ta rasa gane kan almari..

Essha na fita sukaci karo dasu Amir, Sadik ya musu murmushi ya Mika musu packet din Laddu sanan yace" good night uncle Amir, good night uncle Walid"

Duk suka shafai Mai kai, Amir yace" sis tare fa zamu kwanta ina Kuma za ki kaishi?

Tace" Mummy ne tace na kaishi guri Daddy k yanason ganishi"

Walid dayacika baki da laddu yace" sis yanaga yanayi ki yan canza lafiya daiko?

Ta gyada Kai ta Kama hannu Sadik sukayi sashe Daddy k, suna zuwa da Sallama suka shiga, Daddy k baiyi bacci ba idoshi biyu ya Kuna NTA news @10 Sadik da gudu yaje ya haye cinyarshi, Daddy k yayi murmushi yace" wash aboki zaka karyani, sai yanzu iyaye naka suka dama mun gaisa ko?

Essha tayi murmushi tace" ai daddy aguri ka ma zai kwana, ni na wuce sai da safeku"

"Toh Likita Allah yatashemu yamiki Albarka"

Ta amsa"Amin daddy"

ta wuce side nasu ta Tara dasu Amir zaune su Kuna Tasha sport suna kallo tace" bros sai da safe ku"

Walid yace" sis wait da Allah?

Ta tsaya tace"yadai ?

Yace" Gobe in Allah yakaimu zamu fita da boy"

Amir ya Mike yace" yes sis mantawa nayi, bagayamiki ba, gobe zamu fita yawo dashi kinsa Sunday free time ne Monday zamu koma school, please grant us that permission mufita da boy kinji?

Tayi dariya tace"Amir Sadik fa Dankune, ai basai ku tambayi izini naba, Allah yakaimu gobe, ina da ina zakuje?

Walid yace" thanks sis, ShopRite kawai zamuje, movie munkeso kallo a cinema din guri da za'a fara 2pm, toh zamuje 9am Boy yasamu fun kafi time din yacika"

Yana Kira ShopRite Essha taji gabanta ya fadi, sai taji batason tafiya, bayanda taiya tace" okay Allah yakaimu sai da safe ku"

Suka amsa da bye sis mungode..

Walid yayi ihu murna yace" ye bro we will rock with your new car"

Amir yayi murmushi yace" bakada matsala yaro in aka wanane"


Essha na koma daki ta kwanta Sam Bata iya runtswa ba sai juye juye kawai take, Bata ki ace gari ya waye ba taji mak mummy zata gayamata, magana aiki da zata fara zuwa gobe ma bai damaita ba cus she knows her work tafi damuwa taji abunda Mummy zata fada mata.

Karshe toilet ta fada ta Dora alwala ta fito ta Soma nafila tana roko Allah ubangiji ta ya kawo mata sauki a alamurata, har Asuba tana idar da sallah subhi ta Kara gyara kwanciya bacci barawo ya saceta.

Tana ciki bacci ne taji ana tashita"mum wake up its nine"

Ta bude Ido a hankali, Sadik tagani a gefeta ya Sha wanka ya hade, jikishi sanye yake da white t-shirt da red jeans trouser,kana yasha gyara, kafarshi sanye yake da wata hadadiyar sneakers red mai, gefe takalmi a zangaya shi da white line, hannushi rike da p-cap red, gaba aljihu rigashi kuwa puzzle game ne.

Essha tayi murmushi tace" you guys are ready ko?

Ya daga mata Kai, ta Mike ta jawoshi gefeta tace" now say Mum's rules let me hear"

Yayi murmushi yace" rule number 1: Start everything with Bismillah, rule number 2, Don't talk to strangers, rule number 3, always be obedient, don't be sturborn"

Tayi murmushi tace"excellent my boy , hi five? Ya Mika mata hannu suka tafa..

Amir yashigo shima ya hade a ciki manya kanya yayi kyau yace" good morning sis?

Ta amsa da kai, yace" mu zamuwuce sai mun dawo, boy common let's go, sis mummy na kiraki"

Sadik ya sauko ya rike Mai hannu, Essha na kallosu gabanata tsanata faduwa yakeyi tace" Amir da Allah kuladashi kansa Sadik da kirniya"

Yace" sis Kar kidamu he's safe inshallah"

Itama ta sauko tasa teddy slippers nata ta biyosu, ta cima su khairat na hada table na breakfast, suka gaisheta ta amsa, ta gaida mummy har kasa ta zauna a gefeta, Sadik zasu fita ya dawo da gudu ya Bata peck a goshi yace" bye Granny, bye mum"

Ta daga Mai hannu tana murmushi..


Su Amir suna tada motar suka dauki hanya Abj, Sadik na gefe window sai bin kasamu namu yake da kallo, suyi tafiya awa daya suka isa ShopRite
Suna shiga ciki, Walid ya gyara ma Sadik zama p cap nashi, suka samu table suka zauna, Amir ya musu order su ice creams, drinks da su snacks, suna Sha suna hira hankali kwance..


Gidan Tycoon
*************************
Ammi ne zaune, cinyar ta Sofia ne kwance wow su Sofia angirma, sai zuba ma Ammi shagwabe take son ranta, Isa na zaune a kan carpet, Mami na kan dinning ita da Idrees da Rahma suna having breakfast, gefe Rahma Kato teddy ne dayayita hudu Mai kyau.

Ammi sai hararata take cike da matsifa tace" wlh Isa bakaisa ba, Kuma baka kyauta ba, Rahma ne zaka kawo mata tsaraba Teddy, Sofia Kuma hannu rabbana, toh bazai sabu ba, duk yanda zakayi dai ka kakawo mata nata, asamu zama lafiya"

Isa yace"Ammi kiyi hakuri, Sofia fa ta girma, Kuma ta girme ma Rahma kiga kenan dole a nunamata ta girma"

Sofia ta fashe da kuka tace" kiji fa Ammi, Yaya Aliyu tare yake tsaya mana abun, shine zakacemu na girma, kaje har Dubai kazo ma Rahma da Teddy nikuma Empty wlh Ammi da sake"

Mami tace" common shut that ur stupid mouth, ki girma bakisan ki girma ba"

Rahma tasa dariya tana ma Sofia gwalo..

"Ammi ki ganta ta na min gwalo ko?

Ammi ta Mike a fusace taje dinning ta dauko Teddy tace" tunda haka ne kema ki rasashi kenan har ki iya mata gwalo"

Idrees yace" yihakuri Ammi ki bar mata, itanefa autar, Sofia Kar ki damu za'a siyo mata nata"

Ta baka Mai harara tace" when?

Isa yace"Ammi duk ranar Dana koma"

"Baku isaba, yau Dina nakeson kasiya mata nata inhar Kuna neman zaman lafiya, toh yau nakeson Naga autar na da Teddy"

Mami tayi dariya taji tanakara son Ammi, har taiya fifita Yar kishiya akan nata, Allah sarki Ammi Mami ta fadi haka a zuciya ta, tace" Ammi ki shagwaba ta dayawa, Teddy na fa tana dasu bawai ta rasa bane, toh ima irishi takeson , ai'na za'a samu kalla Teddy Mai girma haka?

Sofia ta shagwabe fuska tace" Ammi akwai a ShopRite Wanda ma yafi wanan girma"

"Yawwa tashi kuje ya sanya Miki"

Jin Ammi ta fadi haka ta Mike da murnata ta dauko gyale ta yafa ta kalli Rahma ta mata gwalo tace"Kuma zanyi waya da Yaya Aliyu yazomin da Sari, zance Kar ya kawomiki"

Mami tace"oho dai"

Isa ya Mika ya na hararata Yana kwafa, Ammi tagani tace" lah Sofia maza dauko min mayafi na rakaku danaga Alama zai ita karya Mike a hanya"

Ya marairace fuska yace" haba Ammi ba abunda zan matafa"

Tace" yi min shiru nasan halika Sarai tashi muje"

Sofia ta Mika mata mayafi ta yafa, zasu fita Mami ta Mike Tace" da Allah kuda jirani na dauko handbag Dina, akwai small Shipp danakeso yi"

Sofia tana tafiya tace" Mami Meet us in the car, mun muyi gaba"

Bada jimawa ba, Mami ta fito suka shiga motar, motoci uku na guards na baya dasu masu rakiya, duk aka tada motoci zuwa ShopRite, suna isa , aka bude musu,Sofia tayi sauri ta shiga tayi hanya guri Saida Teddies da aka kilace su a glass manya manya dasu, Su Ammi na biye da ita, Mami kam guri shopping ta nufa, guri Saida Teddies badai nisa daga guri zamasa Sadik, Mami hartagama shopping, Sofia na na guri zaba teddy ruwa ido yahanata zaba da wuri, Isa na gefe yanaji kamar ya bugeta ba hali ga Ammi ta kasa ta sare tana kareta...


Sadik vannila ice cream ne a gabashi baiwani Sha sosai ba puzzle game na Mickey mouse yake ta hadawa...

Walid dake zaune ya Mike yace" bros zanje na sanyo tickets na movie di na kafi ya kare, zanbiya Kuma. Na sanya coins dun zamuyi game da boy"

Amir yayi murmushi yace"yawwa Walid Kama kana Raina, abunda nakeson fada kenan, sai ka dawo"

Walid ya wuce.

Amir ya Mike ya kalli Sadik yace"Boy let me use the toilet, don't go anywhere" ya kada Mai hannu

Sadik ya kada Kai Yana murmushi, Amir yasha fa Mai Mai yace" sai na dawo, good boy"

Amir ya wuce suka barshi shi kadai zaune, afi mintina acikisu babu Wanda ya dawo, Walid ya sanyo tickets, gurin Sanya coins ne a cika shiyasa baidawo da wuri ba, Amir Kuma Yana fita daga toilet ya hadu da wani course mate nashi sunata zuba hira, a tunanishi Walid ya riga yadawo shiyasa ya kwantar da hankali shi suka cigaba da hira..

Sadik yahada puzzle har yagaji, shiru shiru aciki su babu Wanda ya dawo, har ya fara gyagadi, yajigana da chair dayake, har yayi bacci..



***********************

"Wai haryanzu bakusamu teddy da ya muku bane? Ammi ke Kuma ki tsaya biye ma shirmata" cewar Mami..

Isa ya harari Sofia yace" wlh kuwa Mami, ni da friends Dina zamu fita fa, ama Wana stupid girl din tana Bata min lokaci"

Sofia ta tura baki zatayi magana, Ammi ta tareta tace" yi shiru kallesu, natsu ki zabin Wanda ya ranki keso"

Sofia tayi murmushi tace"yawwa Ammi na"

Mami tace" uhmm kafi kugama dai bara na nemin guri na huta kafi ku Gama shirmeku"

Ammi tayi dariya tace"dayafi Miki"

Mami ta juya tabin gurin da kallo, bawasu mutani sosai a downstairs din anfi yawa a sama, tables da suka jera, two table's ne daya ma an cikashi, ta kalli damata guri table dinsu Sadik, daka chair din Sadik ya Bata baya, Bata ga fuska yaro dake zaune a Kai ba tace" yawa nasamu guri zama, bazaiya juri tsayuwa ma shirmena na"

Ta karasa table din hankali ta na kansu Ammi, Mami tana murmushi, tana Alfahari da ita, a matsayi Yar uwa ta dauke ta ba kishiya ba,ta ja chair ta zauna tana kallo Sofia nata zuba shirme Ammi na biye mata, Nan taji Kara faduwa Abu kusa da'ita, ta Kai duba ta kasa taga Mai yafadi taga p-cap ne da puzzle game na robar , su fado lokaci daya ta tsuguna ta kwaso tace" Allah sarki Dan samari ba........magana makale mata yayi , gabata yayi muguwar faduwa sakamako tozali datayi da fuskar Sadik daketa shara baccisa Hankali kwance, Ido Mami ta ware sosai Dan ta tabbatawa kanta abinda ta gani, da sauri cike da razana ta goge idota" Wai son ne kemin gizo Yana karami ko dai maikamadashi ne?

Jiki Mami na rawa ta Mike taje kusa da Sadik ta shafi fuskarshi abun mamaki ma Dan digo baki karami dake fuskar son nata duk yanadashi, abun da yakara razana ta Yana bacci murmushi dimples nashi suka Kara lotsewa gabadaya, jiki ta na rawa takai hannu ta tabo dimples din murya kuka tace" inalilahi waina ilaihi raju'un, hasbiyalahuu waniimal wakil, walahi son ne, Wana sonane, ko dai gizo yakemin ne Yana karamin?

Takara murza Ido da kyau ta bude taga tabbas ba gizo idonta kemanta ta fashe da kuka......






.. More comment more typing ❤️❤️❤️❤️❤️




Love you guys 💛💛💛




👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
*DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️



*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️


*M.W.A*


_Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
____________________________

6️⃣6️⃣&6️⃣7️⃣


Mami Kuka ta fashe da shi tana Sallati "Wanan tabbas Boy din nane Yana Karami" Kara matsowa tayi daf dashi ta tabashi dun ta tabatar ba gizo yake Mata tana tabashi har wani motsin yayi sanan ya koma Bacci.. Mami jikin na barin ta Kira Su Ammi su zo su ga abun Mamaki.. har da Kukata.. Tana zuwa gabasu Ammi kasa magana tayi Sai nuna musu in da Sadik yake kawai da Hannu ta na haki..

"Mami lafiya Me yafaru? Me yasa me meki?" Duk suka tambaya cikin rudewa suna bin wajen da kallon

Mami kasa Magana tayi tasoma Jan Hannu Ammi zuwa teburi da Sadik ke Baccishi hankalishi a kwance, duk Isa Suka biyo bayasu. Suna zuwa P_Cap din Sadik ya rufe mishi fuska yasa Basu ga fuskarshi sosai ba,Ammi Sai waige waige take taka abunda ya tsoronta Mami haka ama Sam ita Bata ga komai ba..

"Wai Mami Me yafaru ne? Da Allah kiyi magana" Ammi ta Fada duk tagama rudewa gani halin da Yar uwata keciki

Mami tasoma Nuna Sadik da Yatsa" Boy Dina wlh Boy Dina ne, bawanda zai fadamin nayarda cewa Wana ba jini mu bane"

Ammi tace" Wai Mami me kike nufi ne fahimtar da Mu kibar mu cikin Duhu"

Mami kwalla ta Share taje kusa da Sadik ta tallofoshi ta sauke mishi P_Cap Daya rufe mishi ta juyo dashi gabansu tana kuka Tana haweye, Gani Fuskar Yaro da Wanda yake Kama dashi duk ya firgitasu...Mami tayi Murmushi Tace" Kuma ku gani ko? Da wa yake Kama"

Isa da Sofia har suna hada Baki guri cewa "Yaya Aliyu"

Ammi Kam suma tsaye tayi, can a hankali tasoma takawa taje gaban Mami Fuskar Sadik ta soma shafo fuskarshi duk ta rude" tabbas ba bambaci wanga Yaro da Aliyu lokaci Yana karami" ta Fada tana Kara binshi da kallo, Sadik Bai ma San sunayi ba Sai Bacci shi yake kwasa dake ya kwaso gajiya Hanya..

" Tabbas da Aliyu na Haihuwa Sai nace wanan jinishi ne"Mami ta Fada

Ammi idon ta har ya kada Tace" Mami ba Wai ba Ina ji a jikina wanan Yaro jini na ne, Mami Wlh naji haka a jikina"

Isa yace" Mami, Ammi Kamani ne fa kawai kufi kowa sani condition da Yaya ke ciki, Kuzo muje kafi iyayensa su dawo su dauka ko cutar da Dansu zamuyi"

Nan Mami da Ammi Suka yanke hukunci zasu jira na AWA Daya inhar Iyayensa Basu dawo ba zasu wuce dashi Sai dai ko duk abun zai faru ya faru.. Isa ya cika kamar zai fanshe yanada wanje zuwa Gashi Sai bata minshi lokaci kawai ake bayada ya iya haka sukayi zama jira suna Gadi Sadik, suna jira suga zuwa iyayen Yaro har AWA Daya da mintina su wuce shiru Basu ga kowa ba.. Ammi ta Mike Tace" Ina Sai dai fa iyayen Wana yaro su zo nemenshi a gida dun daukanshi zamuyi" ta rike kumatu ta na nazari sanan ta cigaba "Ayya ba ije munashi sukayi dun su San jinimu ne, suga shigamu gaskiya wanan yafi karfi Kamani akwai Abu a kasa"

Mami ta Amsa" tabbas kuwa toh inmba Dan Aliyu bane wait Isa ko Idress" ta juya kallonta ga Isa razana yayi har Yana zaro ido yace"Allah Mami Wlh ba Dan na bane zaku iya tashi shi ku tambeyeshi wallahi Mami bana aikata abunda kuke Tunani" ya Fada Kamar zaiyi Kuka

Ammi Kai ta kada cike da gamsuwa tasan halin Isa Sai dai Yaran Zamani ne ba'a yabansu..

"Dauke shi muje kasashi a Motar lokaci na kurewa dun ba Bari Dan na Zanyi ana ba dun Bazaiyi Kafara shi din Jininane" ta Fada tana share haweye tana tsoro abunda zai biyo baya..

"Ammi Kamar fa Satashi kenan zamuyi, Allah Ku canza shawara Babu komai fa Kamani ne nasan Daga Yaya Aliyu har Ya Idress Babu Wanda zai aikata haka" Isa yafada yana pleading dasu

Mami ta daka mishi Tsawa" Common daukeshi muje imbaza ka dauka ba na Kira Bodyguards a waje dun nasa su sa Aikisu"

Isa gani Kar ya Bata ma Su Ammi Rai ne yasa ya sukuci Sadik a hankali Sai cikin Motar Dake kamar Hadi Baki cikin gurin kowa na sha'anisu ba'a ma lura da cewa su dauki Yaro ba, Tsayaya da ba'a yi ba kenan Suka ja Motar su, suka nufo gida suna zuwa Bayan angama parking Su Ammi parlour Tycooon Suka wuce Sadik na jikin Mami da kanta ta daukoshi Sai Bacci sa yake.

Tycoon zaune a makake Parlour shi Yana karanta jarida gani su Ammi ne su Fado ciki parlour cirko cirko da Yaro a Hannu yasa ya mike ciki sauri ba jira..

"Lafiya naganku a haka? Yaro wa ku ka kabe badai ku kashe shi ba who's the Driver in charge Driving you guys na hanasu tafiya ranshi han....."

"Daddy, ba'a abunda kake tunani bane " Isa ya Fada Yana Susa kunne, su Ammi Kam su sanshi a uku...

"Toh Alhamdullilah yanada Rai so what's happening?" Tycoon ya tambaya Yana cire Medicated Eyeglass dinsa..

Sofia caraf ta Amsa" Daddy su Ammi ne Suka dauko wanan Fine Sleeping prince Wai dun Yana Kama da Yaya, Kuma fa Daddy dagaske Kamar tsak Daya da Yaya lokaci Yana karami"

"Wani Yayan?" Tycoon ya tambaya

"Yaya Aliyu" duk suka Amsa

Mami ta Mika Ma Tycoon Sadik , Baki Bude yake cike da Mamaki irin wanna Kamani Nan yasoma kallonshi tun daga sama har kasa aikuwa tsak Aliyu..

Na Sadik ya soma motsin Yana murza Ido duk su ka zuba mishi na mujiya..

A hankali yasoma Bude idanushi kafi suka Bude fal.. a tsorace yasama bin Yan parlour da kallo, dun lokaci har su Ummi Idress Yan family Members an halaro Dun gani Mai Kama da Aliyu..

Sadik gani bako fuskoki yasa ya tsorata Yana ta nema Uncle's dinshi da ido Bai gansu ba yasa yasoma kuka.. Tycoon Sai tambeyeshi yake da Hausa sunashi..Sadik shiru yaki amsawa.
Dun Bai San su ba Baya son ya karya ma Mummy sa rule da Tace " don't talk to strangers"

"Akawo ma Abinci? Me zakaci?"

Sadik Bai Amsa ba kanshi na kasa Sai kuka yake yi, worst part din ma Baya ma ko Jin Hausa ko sannu bayaji..

Rahama tace" Ko dai kurma ne?"

Sadik Bai da Jin abunda ta Fada kallonta kawai yakeyi Yana kuka, Nan Isa ya shigo, rike Da bottle duk su Ammi su sansu a tension. Sadik na ganishi ya ganeshi Su hadu jiya a Airport ai kuwa da gudunshi ya sauka yaje ya rugume Isa yana kuka yana cewa" Take me to My Mum"

Da Mamaki kowa ke binsu da kallo Isa Kam rikicewa yayi.. ya bude Baki zaiyi Magana yajin saukan Mari..

Tycoon Jikinshi har rawa yake saban bacin rai ya nuna Isa da ke dafa da kumatushi idonshi har ya Tara kwalla..

" Isa ni zaka tozarta , duk tarbiya da na baku abunda zaka saka min kenan" ya Fada Yana dafa kirjisa yay kasa kamar zai Fadi Idress dasu Ammi su ka yo kansa cikin saurin..

Sadik Kam Kara tsorata yayi ya Kara ruguman Isa da kyau Yana kuka..

"Daddy Na rantse ma Da Allah ba Dan na ba ne ba hasalima yau nasoma ganishi " ya dago Fuskar Sadik yace" Da Allah ka gayamusu iyayen ka da Allah ka ce wani abun"

Sadik da bajin yare yakeyi ba, Yanda yaga Babba Mutum a gabbashi Yana kuka Sai yabashi tausayi haweye da ke Fuskar Isa ya share ya Kara shigewa jikinsa ya boye fuska " Don't Cry please just take me to my Mum" ya Fada a hankali .. Wayyo Isa jiya ke kamar yasa Hannu ya akai ya fasa ihu yanzu shikena Babu Wanda zai ceceshi Sai Sarki Allah..
Ammi Kam Basu da tacewa Sai kuka yau suna cikin tashi hankali..

Tycoon wayar ya dauko ya Kira family Doctor dinsu yazo cikin saurin Yana son ganishi.. Isa har Hamdala yayi

za'a yi DNA test zaagano gaskiya.. duk Suka zauna kowa Jikinshi a mace.. ana jiran karasowa Likita

Tycoon kasa zama yayi Sai Safa da Marwa kawai yake a parlour.. juyi duniya yayi da Sadik yazo kusa dashi yaki zuwa.. tura Hannu Tycoon yake ya Kara makalewa jikin Isa.. (Yau Isa yaga ta kanshi) Abinci kala kala an kawo mishi ya ki ci..Ruwa ma yaki Sha in Suka sanshi a gaba da tambaya Sai dai ma ya fashe da kuka dun ba Yaresu yake ji ba..

Bayan mintina 30 Dan Dattijo Likita ya shigo da Jakan aikishi, Sosai Su trusting Doctor Aminu yafi shekara Ashiri Yana musu Aiki..

Tycoon Mika mishi Hannu yayi sukayi musabaha sanan ya nuna mishi Sadik, shima kanshi Likita Mamaki ne ya cikashi gani wanan irin Kamani haka..

"Doctor inaji a jikina wanan Yaro ba Kamani ne bane kadai jini na ne DNA test kawai za'ayi mu tabatar kafi mu soma nema mahaifiyarshi"Tycoon ya Fada still be zauna ba

Likita ya kada Kai yace" Kar kadamu Yallabai, yanzu za'a yi abun da kace ama zan koma da abun gwanji Can Asibiti mu domin gunadar da test din"

"Koma Ina za'a je aje munasan mu San gaskiya" Ammi ta Fada

"Okay toh dawa dawa za'a muje?" Likita ya tambaya

"Dukasu daga Isa har Idress Kai harda Aliyu" Tycoon ya Fada Rai a bace..

Idress dim yajin kirjishi ya buga shi da yake da Matar Wayyo yau su shiga uku..

Likita ya deba jinisu, Aliyu da ba shi kusa, Likita yace asamo mishi Gashi kan Aliyu, tun da bayanan..Ammi da kanta ta Mike zuwa side shi tana Addu'a Allah yasa Dan liti Bai wanke su Combs ko dustbin dinshi ba.. tana zuwa kuwa tasomu Brush din da ya tacce kanshi last akan dressing mirror kafi wucewarsu.. da sauri ta dauka tazo dashi ta ba ma likita.sili Biyu na Gashi Aliyu Likita ya cire cikin Brush ya tambayi Ammi ta tatabata na Aliyu ne Kai da kada alama she's very sure..

Da Wayyo da Dabara yasa Isa ya plucking Gashi Sadik haka kuwa akayi.. sallamarsu yayi ya fice.

Doctor Aminu direct Asibiti su ya nufa, Lab ya wuce ciki sauri ya Kira lab

Please Login or Register in order to submit comment