Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can't wait any longer please ki tausayi min"

Tausayi da wani sabo Sonshi ne ya shigeta, Su zama Daya Mai ya rage Kuma.. Kallon kwaya idonshi take taga har su canza launi, Bata gani komai a ciki Sai wutar Sonta ne yake ta ruruwa a ciki..

Lips dinshi ta sumbata a hankali "Yes Handsome" ta fa da a hankali

Murmushi yayi" Then I will take good care of you all night my lady."

Essha kumatu ta Kamar zasu fashe tsaban blushing, dauka ta yayi cak irin Bridal style , Bakin gado ya zaunar da ita a hankali, kasa kusa da ita ya zauna, kallon juna suke cike da so da kauna.

A hankali ya daga kafarta na dama zuwa kan kafashi da ya kalmasa, Soft kiss ya Mana ma karami yatsarta

" sumbata karami yatsa kafa na Alama ce na Biyaya da Kuma sadaukarwa, na sadaukar da Zuciyata da Soyayata Agareki Gimbiyata"

Kalmomishi,Yanda yake Kallon ta, bayanan da soyayarshi agareta yasa cikin wani yanayi tana ji a ranta zata iya sadakar da komai dominsa.

✨✨✨✨✨✨✨✨
Ba karami soyaya bane Masoya na suke nuna ma junasu, kwana 7 sukayi a paris sanan suka wuce gaida Essha Khan a India, Essha Khan da Imran suyi murna ganisu sosai, Essha kuwa Tasha shairri gun Essha Khan ba ta da tacewa Aliyu ne ke ra kare ta,kwanakisu hudu a India shima dakar Aliyu ya Amince, Daga India Kasa Mai tsarki Suka nufa domin yin Umra( Allah ya nufe mu da Zuwa mu ma🙇🙏) da ma acan zasu hadu da Family members Suma daga Maldives Umrah suka nufo.dama suna waya dasu Time to Time..

Bayan su sauka a Riyadh Essha na ganisu Ammi wani kunya ne yakamata, Kai ta sukunyar tama kasa hada ido dasu, kanta a kasa tasoma tafiya domin tarba su ji tayi a jayonta a rugume" kaji min Ja'ira Yariya Ammi naki ne Zaki Jin kunyata? Wanan Munafuki Mai katon Kai Bai ji kunya na ba Sai ke?" Ammi ta Fada cike da zolaya tana dariya

Essha ji take kamar kasa ya bude tashiga saban kunya, Aliyu kam ba ruwanshi Sai ma Wasa da dariya da suka cigaba da Ammi kamar ba Dan da Uwa..

"Ammi Wai ina saura ne naga ke kadai ce?"

"Aliyu kasan halin Daddy ku, da Son Securities up and down, Private jet dinshi Yasa a dauko zasu zo a ciki, naga bazan iya jiransuba da hayaniyasu na yasa na taho abina a commercial, su ma kusa isowa dun jirgi tare Suka taso"

" Kai Ammi wlh Duk Ummi ta Bata Mana ke da halinta"

" Dakatan kaji Dan na Kar ka ba zagar min Uwa, Wlh Naji Dadi ganiku, Sadik ya hanamu sakat kulum Sai kuka Mummy kamar wani Mai Sha Nono, Kai ma Rashi ganishi da bakayi ba ne harda tambaya"

"Kai Ammi ba da shairri fa, Allah kawo su dai lafiya"

"Ameen"

"Yawwa Essha Duk abunda ya miki, kizo ki fadamin nasan Mai Zan masa"

Kanta a kasa tanq Murmushi ta na Dan satar kallon Aliyu taga yacika fam, Nan tasoma dariya a hankali" Okay Ammi ba Damuwa.."

"Mummy Mummyyyyyyyy Papppa" murya Sadik suka jiyo , juyowa sukayi ci kin sauri, Da saukowarsu kenan, Tycoon ke rike dashi Yana gani su Ya katsa natsuwa, Sanye yake da Gray Jalabiya da hula taba kaji hadisi, Kaya su mishi kyau sosai kamar Yaro balarabe..

Aliyu ya bude mishi Hannu Alama zai mishi Oyoyo, Yana zuwa share Aliyu yayi yaje ya rugume Mummy shi...Aliyu kasa magana yayi

"Mummy I missed you"

"I missed my Boy too. Sadik Wai baka ga Papa bane?"

Sadik ya make kafada" Nayi fushi dashi"

Aliyu zugunawa yayi ya rike shi yace" Khalifa I bought some many things for you, Gayamin maiyasa kake fushi da Daddy"

Sadik ya tura Baki yace"Daddy ba Kai bane ku katafi ku ka barni, Kuma yanzu Kai kadai Mummy ke so, ta daina Sona"

Aliyu yayi Murmushi ya rugameshi yace" Aa Mummy ba ta daina sonka ba, Mummy tafi kowa sonka a duk duniya na, Kuma kasa babu kyau fushi ko?"

Sadik ya kada Kai,a hankali yace"Daddy kamin Alkawari baza ka sake bari na ba"

" nayi Alkawari"

"Pinky promise Daddy?"

Aliyu ya bashi karami yatsa shi Suka hada yace"Pinky promise, oya give Daddy a big Hug"

Sadik da murnashi ya rugameshi duk ana kallo su gwani sha'awa.. Essha ta gaisa da su Mami da Tycoon, Albarka yake ta zuba Mata suna Addu'a.

Su Rahma gani Essha ba karami murna sukayi ba, Sai laile suke da ita ..

Babba Bus yazo ya kwashesu zuwa garin Medina, dama Su Tycooon ake jira, Satin su Daya cib saying Umrah duk Suka dawo gida Nigeria..
Nan gida Nigeria, suna dawo tare da Aliyu Suka Kai ziyara Uke.
Essha zasu koma Taki binshi haka da magiya da roko tasamu ya barta, Tayi kewa su Mummy sosai yadda take shagwabe ma su Mummy ko Autar Mummy Mufeeda batayi haka ba, Kullum Sai suyi Riga Riga gun kwanciya a cinya Mummy, Khairat dai ta hakura ita ne ta karbi girma ma gabakidaya.. Ameer da Walid Kam ba'a magana su duk sufita ma Girma da tsayi.. kwanata shida Daddy yasa Ameer ya komar da ita gida Mijinta..


✨✨✨✨✨✨✨
Bayan Wata Biyu

Essha ta koma aikinta suna zamasu cikin koshin lafiya..

Fitowa tayi daga wanka taji wayanta yayi Kara Message,dubawa tayi taga Hubby Aliyu ne ya tura, " Jaaan I have a surprise for you, shirya kizo ki sa maini a Airport. Zan jiraki love you 😘"

Essha ta Kada ido"Abban Sadik and surprise"

Shirya wa tayi, ta fito Ma'aikatan gidan Nan ta kausan gaisawa . Ba'a fi mintina 40 ba ta Kai, tana zuwa ta kirashi ya fito..

"Monday fa za'a fara zuwa Aiki Ina zamuje Kuma?"

"Jaan Kaduna ne na fa Kuma gobe gobe Nan Inshallah Zan mu dawo abun Zan nunamiki,Sadik Kuma daga school na wuce dashi gida can "

Kai kawai ta kada mishi Alama ta amince

Ba'a fi two minutes ba aka fara Kira Matafiya, Bodyguards dinsu na biye dasu da kayasu, VIP suka wuce, Gefen jirgi ba kowa Sai su, Sai Bodyguards Biyu dake bakin kofa.. suna Gama gyara sitbelt dinsu jirgi ya Lula sarari samaniya.

Essha Sit belts dinta ta cire, ta gyara zama suna fuskarta juna.. zobe hannuta ta soma Wasa dashi

" I...wa...nt to te...ll you something" Ta Fada batare da ta kalleshiba

Aliyu ya murmusa rugume ta yayi ta gefeshi kanta na kan kirjisa"Jaan imbakeso tafiya nane ki Fada min, Zan sa su koma right now"

Essha Kara lagwabewa tayi a jikishi" Uhm uhm ba hakane dama Abu nakeso na Fada ma"

Mikewa yayi yana shafo fuskarta a hankali Yana zuwa kan sirri dogo Hanci nata yaja shi a hankali "Auchhh" ta Furta

Dariya yasoma yi ya sumbaci sama Hanci yace" Toh fadamin Mai ke damu Baby na???

"Uh...mm Uhmmm in...Ina da ju..na Biyu" tafada a hankali, A tsorace take batasan yazai reacting ba, Sumewa zaune yayi bakishi a bude, Essha kada Kai tayi tana Murmushi tasaba gani, cikin pulse nata ta bude ta Ciro chocolate ta bare ta tusa Mai abaki, sanan ya farfardo daga Suma Zauna dayake.. Hannu ta ya riko Idonshi ya Tara haweye, Essha ta Kara tsorata ta rasa yazatayi, haweye ne fal ke zuba a idonshi can Kuma taga yasoma Murmushi

" Jaan tabani Naji, na tabbatar ba mafarki nake ba, Ni Aliyu Zan kuma zama Uba"

Essha Daji yafadi haka ta sauke naunaya ajiya zuciya tana dariya, Hannushi ta citza tana dariya" Aliyu you are not dreaming, I'm really pregnant" tafada cike da murna

Aliyu mikewa yayi yasa kanshi a cikita" Alhamdullilah Alhamdullilah Essha I'm going to be a Father again, Sadik zai samu kanwa ko kani Alhamdullilah Essha Thank you Thank you"
Riko hannuwata yayi ya Kai kan lips dinshi Yana haweye Yana Murmushi yace" Thank you Jaan Thank you for loving me basan da Mai Zan saka Miki ba I love you Jaann I love you I love you"

Essha rugume shi tayi"I love you Too Hubbina"

"Bani lokaci da kika Reno cikin Sadik Essha I'm so sorry about that, Essha Allah Wana tare zamu Essha word's can't express how I'm feeling right now. Mai yasa Baki Gayamin da wuri ba Jaan?" Yafada ya na pecking kumatuta

"Nima bansaniba jiya ne, nace bara na duba cause inaji signs din, Dana duba Kuma na kiraka Zan Fada ma kace Kuna meeting "

"Subhanallah I'm so sorry Jaaan, can't wait na Fada ma Sadik zai zama Babba Yaya, how old is the pregnancy?"

"Dana Duba it's shows one month, wata Daya harda kwanaki" ta Fada a hankali

Ya Shafa shafefe Ciki yasa saitin kunne sa yace" Aslm Baby Papa ne,listen to me da Allah Ina roko ki ko ka Kar ka wahala min Da Jaan din ta, please Baby Papa" ya Fada a hankali

Essha ture kansa tayi " kana magana da Cikin da ko Rai ba a hura masa ba You are not serious Allah harda warning" ta Fada tana dariya.

Aliyu shagwabe fuska yayi yace"Yes n Banason Baby ta wahala min da ke ne. Jaan Fada min duk abunda kikeso Zan mikishi.."

Essha ta riko haibarsa Tace" ko Mai nakeso zaka min Kuma za ka bani? "

" komai namiki Alkawari inhar Bai fi Karfina Inshallah Zan miki shi kuma Zan Baki "

Essha Murmushi tayi Tace" Aliyu Kai nakeso, I want to spend the rest of my life with you, ba abunda nakeso a duk fadin duniya na Sai soyayarka, shi kadai ta isheni..."

Aliyu Murmushi yayi ya hade bakisu, Wani passionate kiss suke ma junasu Mai cike da so da kauna,

Hade Hanci su yayi duk suna sauke Numfashi yace" Essha inhar wanane ki Gama samushi da dadewa kullum sonki karuwa yake a cikin Raina, Jaaan ba na iya Jin Zan iya rayuwa babuke.. Jaan ki Riga da ki zama ciko Numfashi na imbabuke toh Nima tawa rayuwa yazo karshe, Jaan ke ta dabance a jikin Mata Allah ya Miki Albarka Ya sauke ki lafiya ya bar mu tare cikin So da kauna"

"Ameen Hubby na" ta Fada tana share minshi haweye dake zubowa..

Bayan wasu mintina jirgisu ya sauka a Kaduna garin Mallam

Bayan su sauka motoci Kusan Shida su zo tarbasu, duka Motoci na da Plate Number din *Young Tycoon* ...
Aliyu na Allah su shiga ciki Motar Sai Mita yakeyi tasa gown da gelle kawai Bata sa hijab ba, Essha uffan batace mishi ba tasan halin shi dakishi.
Har su karaso Baki motoci a bude musu kofa za su shiga kenan Essha tasoma ji ana kwala ma ta Kira, Essha ko a bacci aka tasheta tasa Mai wanan Murya, jikinta gabadaya yayi sanyi juyowa tayi Bata amsaba tana kallon kokari yake ya kusa ciki jama'a a haka kuwa Bai daina Kiran suna ta ba
"Esshaa Essha Esshaa" idonta akanshi..

Aliyu ya juyo Yana kallon ta yaga yanayi ya ya canza yace" Jaan wa ke ta kwalla Miki Kira haka? "

Essha ta daga Kai tana kallonshi a hankali"Kha..Khalid ne" ta Furta a hankali..
Aliyu nandana ido ya kada, Ya hade Rai tam kamar Bai taba dariya na Gadaga ya motsa..har Yana wani citza lebe, Ko ba ta Fada ba tasan Khalid tsoho saurayita, Sumy tabashi labari shi,

Suna kallonshi har ya karaso kusa dasu, Bodyguards su so su gamashi Aliyu ya musu Hannu su kyalleshi ya karaso..

Sam Khalid Bai canza ba Sai dai Kara kyau ma da yayi, da Murmushi a fuskarshi kamar kullum dun Khalid dama akwai fara'a ya karaso gabasu, Essha ya daga ma Hannu Yana Murmushi, Essha itama ta daga mishi Hannu tana Murmushi duka su sukasa cewa komai, Khalid Murmushi yadingayi Yana kallon gefen, Essha Kam sukuyar da Kai kasa tayi itama tarasa tacewa, Aliyu kallonsu yake ya cika Fam kamar zai fashe shi kadai yasan yada yakeji..
Essha taga shiru bana karewa bane ta kakare murya yadda taga Aliyu na kallon Khalid Kamar zai yanyakashi ne ya Bata dariya kuntsa dariya tayi Tace

"Khalid Yakake kwana da yawa?"

Khalid Sai a sanan ya kalleta Kai yajijiga a hankali ya Amsa da Alhamdullilah, Nan suka sakeyi shiru

Essha rike Hannu Aliyu tayi dun yaji sanyi dun yakunsa fashewa"Khalid meet Aliyu My Husband"

Aliyu Jin ta kirashi da My Husband ne yasa yadan ji sanyi a ranshi.

Khalid ya Mika mishi Hannu suyi musabaha Aliyu kallonshi kawai ya tsaya yanayi, Sanda Essha ta Dan tabashi Sana ya miko Hannushi sukayo musabaha Aliyu zai zare Hannushi Khalid ya riko Hannu yace" dakata, Ina son ka rike ta da kyau da Amana duk ranar da kaci Amana ta Sai kayi nadama zuwaka duniya" kamar radar haka ya gayama sa cikin kunne

Aliyu dariya kawai yayi ya Susa Kai, Guy ya burgeshi Bai ma San Mai zai ce Mai ba.. Hannu shi ya saka a hankali Nan suka jiyo murya Yariya karama na cewa" Daddy Daddy Muna ta jira ka, Ashe na kazo"

Duk suka mayar da hankali kan Yariya bazata wuce shekara 7bakwai ba Dake rike da Karami Teddy, Kyakyawa da ita.. Khalid Murmushi ya Mata yace" Sorry Babyna, Bazan Kara ba" ya Fada Yana rike kunnuwa alama tamishi afuwa

Essha na gani Yariya tasa cewa itace Yariya Khalid da ya Mata takwara a hankali ta taso zuwa gefen Yariya Tace" Essha"

Essha karama ta juyo hankali ta kan Essha, ihu murna tasa ta rugume Essha, Da Mamaki Essha tasoma binta da kallo

"Aunty kina da kyau sosai, kullum Sai Daddy na ya ban labari ki, Ina da hotuna ki Dayawa inason in na girma naza ma likata irinki, A Riga kirana Doctor Eessha Daddy" ta Fada cike da fara'a

"Kisamai Mummy na batason hotoki kullum Sai ta yaga tana tsoro da kishi takwara na tafita kyau, I love you Namecy"

"Kiyi hakuri Esshaa na da surutu sosai Kar ki biye ma ta " Khalid ya Fada jikinsa a Sanyaye
Essha Bata kulashiba ta rugume Essha Karama tana kuka Tana dariya Tace" I love you too Little Doctor Essha, in Sha Allah ma Sai ki fini.."ta Fada tana kuka sosai jini Khalid take rugume da ita Kuma takwara ta Allah sarki rayuwa kenan..

Khalid kasa daurewa yayi sanda yasoma haweye.. Aliyu nagani haka cikisa yayi sanyi sosai, Yaji tausayi shi ya kamashi, in shine aka rabashi da Essha ai basan ta inda ma zai fara ba.. Nan hankali shi ya koma kan Essha yaga tana Tama takwara ta Wasa suna ta kyakkyatawa waya ya Ciro ya daukesu..

Kar Essha taga Daddy ta na kuka yasa yazo ya dauketa dama Aliyu akwai Son Yara cikin wani super market Dake Airport din Suka shiga, toys Teddy wasu tsiyakatu duk ya kwaso manta, Yariya nada sauri sabo duk tasaba Da Su cikin kan kani lokaci, Su fito daga Super market, Essha da Takwara suna rike da Hannu juna, wani Rafakacece Teddy ne a Hannu Essha karama Dakar ta iya daukashi ta ba Essha ta tayata rikewa ma ki tayi, Aliyu Kam a barshi da Kaya Niki suna zuwa ya Mika ma Khalid, Khalid yaso yaki karba sanda Essha tasa Baki sanan ya karba Yana Godiya..

"Mummy Mummyyyyyyyy kiga abunda Namecy na da Uncle Suka tsayo min"

Wance aka Kira da Mummy ta dago Kai Suka hada ido da Essha, Essha ta ganeta Faiza ce cousin sister dinshi Ashe ya Aura, dama ta Dade tana sonshi Gashi Allah ya cika Mata burinta , Auren zumunci aka hadusu..

Suna hada ido Faiza Murmushi yake Tama Essha, Essha Kai ta girgiza kawai Tana Murmushi haka dai Suka gaisa, Faiza nata cin Rai, Essha Kam ko a jikinta Hannu ta ma a sakele jikin Aliyu har suka Gama gaisawa, Da za su wuce.. Essha karama Dakar ta rabu da Essha tana ta kuka, sanda Essha ta ma ta Alkawari zata Riga zuwa dubata sanan ta amince Suka wuce...

Da za su wuce Aliyu ya dafa Kafada Khalid yace" Mallam Khalid ka kula min da Essha she's a good girl may be ma tazama sirika ta in the future"

Khalid Murmushi kawai yayi suka wuce.

Suna wucewa, Aliyu ya juyo ya rugume ta yace" Jaan Allah I'm jealous"

Essha Murmushi tayi ta na shafa Gashi kanshi Tace" I know ama Essha taka ce kadai Kar kasamu Damuwa"

✨✨✨✨✨✨✨✨
Suna ciki motor Essha rufe Mata ido yayi, Gashi duk ta gaji.

" haryazu ba mu Kai ba? gidan Ummi ne yau da nisa haka"

"Jaan Kar kidamu mu kusa insowa, bafa gida Ummi bane gidamu zamuje"

Essha tayi shiru ba ta Kara cewa komai ba har bacci ya dauke ta, can taji ana tashi ta ta bude ido,zata bude ido, Aliyu ya tare ta da sauri

"Babe ba Ni mintina kafi ki bude"

" Nifa na gaji I want to sleep"

"Okay Zaki iya budewa yanzu "

Essha ta sauke kyalle, guri tasoma bin da kallon a rayuwa ta baza ta taba mantawa da na wanjanba, sabani taga Daji, gani guri tayi ya canza a mishi bukkoki irin na tura wa na, gurin ko'ina Sai kyalli ya ke,
Hankali ta ya tafi gabadaya kan wani Bukka a cikin jerin bukkoki ma duk yafinsu girma..
Ta tuna shekara 8 dasuka wuce, Ko da kudin aka ce tazo baza ta Zo ba Gashi yanzu an gyara koina kamar a turai..

Tun kafi ta Kai kusa da Bukka tanaji sauti Favorite Music na tashi"🎶🎶Angel Angel You are my My Angel Angel Angel You are my My Angel🎶🎶

Da Sauri ta Ta shiga Mashallah ya gaji da haduwa ko a turai, Balloons ne da Red roses flowers Suka cika daki, Sama hadade Gado ma, roses aka decorating dashi..

Aliyu fitowa yayi daga wani gefen na Cikin Bukka rike da Guitar Yana rere wakar Yana zangaya ta Yana zuba ma ta roses ajiki,har yagama reream wakar.. Farinciki dake fuskar Esshaa baya misaltuwa..

Zatayi magana ya Dora Mata yatsa akan lips" ko wani ki ancesa zuwa anjima, muje kici Abinci nasa kina ji yunwa kar na bar Baby na da yunwa"

Essha ta rolling ido "ahaf kace min ta Babyka kake ba Ni ba"

"A'a aa ni ban Fada ba" ya Fada Yana rike da Hannu ta, kan wani Circle table an decorating dinshi da Abinci kala kala ... Drinks kuwa Cocktails ne, yogurt, milkshake Soda gansuna har wani Candles masu Kamshi aka jera a tsakiyar taburi, Wana ko a turai Albarka..

"Abinci na fa suyi yawa ?"

"Don't worry Jaan, The guard's are here we will dive in together but firstly let's enjoy our date" ya Fada Yana Jan ma ta kujera ta zauna. Da kanshi ya serving, favorite dinta ya serving wato Spaghetti and Meatballs ..

Essha Murmushi tayi Tace" duk kasan abubuwa da nakeso, I know it's Sadik that told you"

" Nasan abunda Zaki Fada kenan, da Allah in akwai wani favorite din kifada min yashiga list dina nema"

Murya kasa kasa tana kallonshi Tace" Ai kane boyeye Favorite din, shiyasa I want to be having you everyday just like this Spag" ta Fada tana saka Loma Spag dinta harda lumshe ido tana biye dariya...
Aliyu dayaji ta Fadi haka har kusan shekewa yayi da Ruwa dayake Sha.

"Bad child" ya fada Yana Dariya

"I'm only Bad for you" ta Fada tana tsuke taliyarta a hankali harda kashe minshi ..

Tuntsewa yayi da dariya sosai yace" okay be a bad girl "

Essha Murmushi tayi Tace"angama Rankishidade"

Baya sugama cin Abincisu, su watsa Ruwa, Su Rama duka sallolisu..har suyi shiri kwanciya Tycoon ya kirashi Vd call meeting zasuyi da wasu company.. pecking dinta yayi a sama kai, kumatu da lips sanan ya fice zuwa Amsa Kiran..

✨✨✨✨✨✨✨✨

Bayan wasu mintina, Aliyu ya shigo..

Rugumeta yayi ta baya Yana Murmushi yace"
"Did you miss me Baby?" Ya Fada Yana Dan Wasa da kalaba kitson kanta...

" I missed you so much Hubbina" ta Fada tana Kara shigewa jikishi tana bin gurin da Kallo

Lasar kunne ta yayi yace"Mai ki ka tuna ?"

"Abubuwa da dama" ta bashi amsa tana Murmushi

Kunne ta ya Dan citza hade da hura Mata iska yace" Kamar me?"

Yadda ya Mata magana ne yasa ta kasa magana.. Ya zura Hannu ta kasan Rigar Yana shafa cikinta hade da Wasa da cibiyarta while Yana tsotsar wuyanta ..a hankali ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya gani sakonshi na Isa Inda ya dace, Zip din rigar ta ya zuge a hankali hade da ma ta tafiya tsusa a baya.. Juyota yayi ya hade bakinsu, Hot hot romance yake zu ba Mata Wanda ya gigita tafita ma a hayaci ta, Karshe zubewa sukayi kan gado, Baki Aliyu dauke da Addu'ar saduwa da iyali suka rayya suna ma'aki (S.A.W)...

Kwana Biyu sukayi gun Daji Nan, sun shirya ko wani karshe shekara zasu Riga zuwa...

Essha ta soma zuwa Aiki ta, Ma'aikatan ta suyi murna daganita sosai, Tana Aiki ta da kula da Family dinta yada yakamata...

Foundation ta bude na taimakon Mata da Marayu, tana Kuma women empowerment .. Ta samu promotion da Awards kala kala.. ranar da Association of Gynaecologist na Africa Suka Bata Best Gynaecologist of the Year Daddy har kuka sanda yayi he's very proud of her..
Cikin ta yasoma girma ta dauki Maternity leave..

✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan Wata Tara da kwanaki, Essha Ciki ya girma Haihuwa yau ko Gobe.. Rahma, Sofia Sadik da Essha takwara ta tazoma ta visiting dun yanzu su Saba Sosai da Faiza har kawace Suka kula. Essha karama a Family din ba Wanda Bai Santana dun Yariya akwai sauri sabo..

Dukasu Agwalima Suka zuba a Tray suna ta aiki sha.

Ammi ta shigo" Duk fa Yan gidana yanzu Agwalima Suka koma Sha, daga Manya har Yara"

"Ammi ba ki sani Ba,Minal Budurwa Ya Isa Muna waya da ita jiya take ban labari Wai tana zaune Sai ga Yaya ya Kira ta Wai ta fito tana fitowa taga Shi ya sauke Mata Rabin Buhu Agwalima Wai Birthday gift dinta" Rahma ta Fada ai duk su kwashe da Dariya

"Toh ai Agwalima abun sone, Allah ya ma Mummy Sadik Albarka da ta hadani da Agwalima" Isa dake shigowa ya Fada Yana Murmushi

Aliyu ne ke biye dashi, Gefen Essha ya nufa har tausayi take bashi cikin ta yayi girma sosai Dakar ma take takawa, Gefen kafarta ya zauna ya soma massaging kafa a hankali, tajin Dadi tausa ama Sai ta sukunyar da kanta kasa dun haryazu kunya su Ammi take Aliyu kam ba ruwanshi...su Ammi ma ba ruwasu sabgar gabasu suke..

Kallanta yayi cike da so da kauna Yace" I have a surprise for you tashi muje na nuna miki"
Ya Fada Yana Mikewa.. taimaka ma ta yayi ta Mike yasa Sofia ta dauko Mata hijab...

Abun Mamaki taga hardasu Ammi su shirya zasu binsu, Kallon tuhuma take ta binsu dashi su Kuma Sai Murmushi su ke zu ba Mata...

Duk aka shirya, cikin Motar tace" Da Allah ka Gaya min Mai zaka nuna min I'm scared"

Aliyu ya Yi Murmushi yace" Jaan Baki yarda da ni bane is just a surprise zaki gani, yanzu zamu i'sa in Sha Allah" ya Fada Yana shafa kanta...
Kasa magana tayi ta na ta Kallon hanya ..

Aliyu gani sukusa isa yasa Ciro Handky zuwa fuskarta Essha rolling idonta tayi tana dariya Tace" Again..."

"Yes again" ya Fada Yana
kwaikwaya muryata, kyalle yasa ya rufe idonta dashi yace" Sorry Jaann it's a surprise"

Murmushi tayi idonta rufe da kyalle Tace" Kar kadamu"

Ji tayi Motar ta tsaya, Tana Jin motsi shi ya fita yazo gefenta ya bude Mata kofar rike hannuta yayi a hankali ya taimaka Mata ta fito.. tana ji hayaniya harda murya su Ammi,Besty ta ma da su Fawaz, Allah Allah take Aliyu ya bude ma ta ido taga Wana kala surprise da ya sa Dangi da Abokaina Arziki Suka halaro..
rugume ta taji anyi batasan ma ko waye ba, Murya Mummyta "Mufeeda Wana rugume haka Bake gani halin da ta ke ciki ne?"
Cike da fara'a da murna tace
"Mummy yaushe kukazo Mai ke faruwa ne?" Mummy Bata amsata ba ta cigaba da gaisawa da mutani wajan.. tana harara Mufeeda
"Mummy nayi kewata ne fa ? Sis Essha nasa kema ki yi missing na ko?" Ta tambaya a shagwabe

Essha cike da murna" la Autar Mummy na nima nayi missing din ki sosai"

Murya Daddy ta dasu Amir da Walid da Daddy karami suna gaisawa da su Tycoon ne yakara Razanata.

Please Login or Register in order to submit comment