Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hussh Ya saki ajiya zuciya yace" inner peace"

Aliyu yay murmushi yace" oya zo ka kwanta gobe akwai school Kar makara"

Sadik ya cire iPod din ya aje yay karatu bacci ya kwanta.. Aliyu shima addua yay ya tofa Mai yaja Mai bargo yamishi peck a cheeks both side yace" sleep well Boy"

Sadik ya lumshe ido yace" you too Dad"

Aliyu ya Mike Yana sallati ya zubo wayoyishi a side drawer ya nufi toilet yasake daura alwala yafito ya sa jallabiya fara fat.. ya daura hula tana kaji hadisi ya shimfida daddurma sanan ya fara Sallah ciki natsuwa.. Sallah yake through out har asuba ya ratsa....

*Morning 6:45Am*

πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
Β  Β  Β  Β  *DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

*Written by J Hajara*

🌍 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈβœοΈ

Β  Β  Β  Β  Β  *M. W. A*

Β Β  '''Kungiyar d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www. Facebook. Com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________

*Bismillahi Rahman* *Rahim πŸ™*

πŸ™πŸ₯ΊπŸ™πŸ₯ΊπŸ™πŸ₯ΊπŸ™πŸ₯Ί
Dedicated this page to all Doctor Essha's fans domin kun cacanta.

9⃣4⃣&9️⃣5️⃣
Morning 6:45Am

Aliyu sanye suke da Eye mask(πŸ₯½ na bacci) Aliyu na sanye da Mai Zane Cat eyes,Sadik Kuma na sanye da na Spiderman.

Ammi ce, ta shigo da sallamarta tana binsu da kallo Cike da so da annashuwa ganisu, ta taho a hankali tagefe Sadik ta shafa lallausa gashi kansa tana murmushi, na wani Siraru kwalla suka soma siyaya ciki sauri tashare ciki ranta Tace
" Allah sarki Allah Mai iko ba yadda ba ya ikonsa, har na cire Rai gani Kwai Aliyu Sai gashiiii........"
Tik tik tik tirrrrrrrrrrrrrtsk, makake agogo dake mane a bango daki Mai kyalin da kyawu ne yasa Kara, haka ya katse ma ta zance zuci da ta ke, nan ta juya taga har 7:06Am Sam ta ma manta abu da ya kawo ta daki. Shagalta tayi da kallo kyakyawa jika nata, zuwa tayi dama ta tashishi yayi shiri Makarata, da Alama dai yau zai makara.
A hankali tasoma Mai cakulkuli. Sadik na ciki bacci yasomaji anamai cakulkuli, dariya yasoma yana" Daddy Daddy" Yana dariya harda mirginawa duk zatonshi Daddyshi ne.

Ammi tace" maza tashi ba Daddyka bane, kasan karfe nawa kuwa? Daddy ka ya biyema kuna ta shara bacci oya oya wakeup wakeup" ta fada tana jamishi yatsu kafa.

Addu'a tashi a bacci ya karanto sanan ya Mike Yana dariya ya zare Eyes Mask Yana kallonta" Goood morning Granny.."

Ammi ta kauda fuskata gefe Bata amsaba. Yagane Mai take nufi, nan yarike kunne yace" oh Sorry Grandma, Ina kwana? .."

Ta rike kunnuwashi" Inkasakemin wani turanci Sai na balla waena kunnuwa marasa jin magana. Maza tashi muje ka shirya Kar ka makara."

Sadik ya shafa kunnuwashi da ta murza Yana dariya yace" Grandma baza Kara ba, ai I'm still learning Sai nazo nafiki iyawa," yaturabaki ciki harshe turaci yacigaba

" Kuma ni yau Daddyna ne zai shiryani yakai ni school ba Nanny da Driver ba."

"Bazaiyuba, you are already late, yaushe Daddy ka yatashi,yashirya kanshi bale yace zai shiryaka har yakaika zuwa school? Common tashi muje kafi Raina ya baci."Ammi ta fada tana hararashi ciki wasa.

Sadik ya sauka daga kan gado Yana kumbure kumbure Yana mita cewa "Shi dai Daddyshi ne zaikaishi School"
Ammi itama tamike ta dafashi ta tasashi hanya fita ciki mita tace "Aiko bakaisaba ga ka kai Mai Daddy ko, wuce mu tafi nima Ina da Daddy na fa.."

Dariya yayi yace" Daddy na yafi naki kyauuuuu" yaja kyauuuuu da karfi haryana kyakyatawa.

Aliyu tashi yayi zaune Yana kallonsu Yana murmusawa.

"Oho dai naji, kadai taya ni mishi Addua Allah yajikashi da rahma" Ammi ta fada tana shafa kanshi

Sadik a sanyayaye yadago Yana kallanta "Sorry Ammii inshallah bazanmata ba zanriga mishi Addua da dukan musulmai dasuka rigamu gidan gaskiya"

Ammi ta Kara shafon gashi kansa tace" Yauwa Yaron Daddyshi ka kyauta, muje anshirya ka, kar ka makara. "

Suna isa Baki kofa ta juyo kallonta ga Aliyu tace" kasamaini kafi kafita Office, akwai maganar da zamuyi."

Ya soma su sa keya Yana bit bit da ido kamar Mara gaskiya yace" Okay Ammi Sai na fito."

Sadik ya waving mishi Hannu Alama Bye bye Yana murmushi,shima Murmusawa yayi ya Mayar masa da "Take Good care of yourself Boy"

"Inshallah I will Papa"

Suna fita, Ya fada kan gadonshi Yana ajiye zuciya, shafar gemu yakeyi Yana zuba lalausar Murmushi. Shi kadai yasan Farinciki dayake ciki, jiyake kamar ya jawo Asabar Dina tazama Gobe,Ya ga Essha Shi agefeshi ko zai Kara samu kwanciya Hankali.

Zama yayi yasoma lalubar wayarsa daga side drawer ya kunnota, Number Essha ya Danna, Number ya tsura ma ido yanaji Kamar yakira ama Yana tsoro, can ya yake maybe ma tana Bacci bazai barta ta huta kar ya tadata. " Mai Ammi zatagayami?.. Oho." Yatambaya kanshi sanan yakara bama kansa Amsa.

8:00am
Dai dai yagama shiryawa, ya fice zuwa side din Mami. Sai washa hakora kawai yake Kamar Wanda aka mishi Kyauta Aljanah(☺️) su Siyama nata tsokanarshi bai damu ba, Sai ma biyemusu da yarigayi( Unsual).

Mami kam Sai bishi take da kallo Mamaki a zuciya tace" yo ko dai an fada ma Aliyu maganar Aure nan ne? Kai da wallaki(Wai goro a Miya), in ko hakane lallai su kyauta, dun ban kaunar naga Son Dina ciki damuwa." Duk zace zuci da take hankalinta na kanshi taga har ya zage yaci Breakfast sosai, Gashi yasake da kanenshi sosai yaushe rabo?

Ya dago kai" Umm Mami Wana kallo fa?

"Ah ah bakomai, naga Boy din na ne yakara min kyau da Safe nan Kamar wani sabon Ango."

Aliyu ya waro idanuwa nan nasa Cike da zolaya yace "Mami Nagode, ama sabo Ango Kuma? Ya fada Yana rike dariya da ya kumtsa kar Mami taganonshi Asirisu ya tonu, ya tabbata Sai Su Suleiman su yankashi. "Mami Wai Sabon Ango nii?" Ya fada Yana susa gaba goshi da Dan karami yatsa
Buga cikita yake dun yaji Mai zatace, Zata fadamishi ne ko itama boyemishi zatayi?

Mami taganoshi tayi Murmushi irin tasu ta Manya a zuciya tace" Two can also play the game"
Ta kalleshi tana Kara fadada Murmushi ta tace" nasani ko Boy Dina yakusa Angocewa?."

Aliyu kai kawai ya girgiza yasan halin Mami tsarai she can play Along. Mikewa yayi yace" Mamina Allah yasa haka, bara na shiga gun Ammi tana jiran, Mamina daganan zan wuce office kimin Addua"

"Allah yataimaka ya kareminkai, A dawo lafiya"

"Ameennn Mamina" Yana Amasawa ya fice ya nufi side din Ammi.

Da sallamarshi ya shigo ya tarar da Ammi a makeke Parlour ta da yagaji da haduwa, idona Da Medicated Eyeglass hankali ta gabadaya na kan makaken Plasma Tv da ya kusa cinye Rabin Bango,Aljazeera News take kallon, tana sipping Lipton. Amsa sallama Tayi,nan ta ije (β˜•) Cup din sama table dake gefenta a hankali,ta dauki remote ta rage Kara Tv, sanan ta Mayar da hankalinta kanshi.

"Ammi Good morning?.."

"Naji Dan Turawa Ina kwana" nan ciki mita tacigaba "yoh ka tsaye min akai Wai kai kana gaisuwa, gaskiya turawana suna Bata muna yara" Ammi ta fada tana Jan karami tsaki.

Aliyu yay girgiza kai Yana Dariya"kaiii Ammi gaisuwa ne fa, Banda Sadik Ashe harda mu ma gyara yashafa"
Yafada Yana kallon Agogo Rolex da ke daure gwani sha'awa a sisiyar hannushi..

"Ammi I'm getting late 8:50, ko dai na tafi ne in nadawo Sai muyyii......."

Bai karasaba Ammi ta katseshi" Sai dai kuwa office din ya jira badai niba, ko karfe biyu zamu kai kuwa."
Ya soma whinning Kamar yaro Yana" Kai Ammi zan fa....."

"Assalamualaikum"
Mami tashigo da sallamarta dayasa Aliyu dakantar da zance da yake
Ammi ce kadai ta iya Amsawa

Aliyu kam Yana tsaye duk ya rude Sai binsu yake da kallon tuhuma nan ya Kara gyara tsayuwa yana sauke naunauye ajiya zuciya
"Ammi,Mami Mai nayi ne naga Alamu Kamar so ake a hada Meeting akaina" ya fada Yana Kara bisu da kallo ba lau ba.
Nan yasoma Murmushi dole

" Okay okay Na fahimta maganar Aure tunda ku ki gayamun, Allah yasa Ina da masu so na da suka fadamun"

"Whatt!!!" Ammi da Mami suka furta harsuna Hada baki(Lokaci guda).

Aliyu bai ma San yafada ba rudewa gani su sanshi a tsakiya ne yasashi sukubarta Baki.

"Ah lallai, tou kasanar da masu sonka din kar su yarda muyi ido hudu dasu, da ko zasu sha mamaki abunda zan musu." Ammi ta fada tana hararashi sama da kasa tana Kara kunsa dariya gani yada duk ya rude.

"Ammi, Mami wlh ba laifi su bane.."Ya fada a shagwabe

"Kwantar da hankali ka Boy, ko su basu fada ba, nima Ina da niyya gayyama, dun banason gani Boy Dina aciki damuwa ko kunci bana ji dadi" Mami ta fada tana tapping nashi a hankali a baya..

Aliyu naunauye ajiya zuciya ya sauke ya rugume Mami Side hug yace

" Shiyasa na ke Kara sonki Mamina"

Ammii ta jefesu da harara wasa Tace" Abeg abeg muji, duk da haka ba abunda zai hanani punishing din su Haydar da kafarsu za suzo krrr"

"Mami da Allah ki rokemin Ammi ta yafemusu It's not their faults" ya fada a shagwabe.

"kar kadamu Boy, nasan Ammi baza tamusu komai ba" Mami ta fada, nan ta gyara zamata a gefe Ammi, suka sa Aliyu a tsakiya,dake tsaye Yana ta bisu da kallon.

"Wai baza ka nemi guri ka zauna bane? Kanata wani bimu da kallo Kamar mu maka sata" Ammi ta fada.

Yada Ammi Tayi serious haka yasa yacire takalmasa ciki sauri ya haye lallausa carpet din ya zauna Yana kallonsu. Hankalisa a tashe har yasoma Tara zufa duk da sanyi Ac da ya cika Parlour.

"Aliyu inason kabude kunnuwa ka da kyau kajini, inason kamin abun guda banason ka takura ma Essha, banason kaje wajenta ko ka kirata har Sai tazama malakika, kuma ba Shawara nake baka ba Umarni ne. Kar ka ce zaka takura ta, yariya na ta sadaukar da komai nata, ta raini Danka ga maganar mutani Sam ba Bata da wani lokacin kanta, shiyasa nakeson wanan week din kafi An daura Aure na I want her to enjoy a single life for once, kar kowa ya damaita daga Kai har Sadik din." Ammi ta fada

Aliyu jiyake kamar an fansa Mai Kai da guduma.

" tayaya zai iya jurewa dai dai da ranar daya bai ga Essha ko jin muryataba, Kuma duk Daliloli da ta kawo Sam ba daliline Mai karfi dazai hanashi ganitaba" ya raya ma kanshi.
Ammi batasan kamar dutse Mai karfi ta dora Mai ba. Ya bude Baki zaiyi magana Mami ta dakatar dashi tace" Dakata Aliyu, Ammi Tayi gaskiya Ana, it's just for four days ai, Saturday tazama naka, yariya tana bukata time din kanta, Aure dai wanan ba fashi, Nasan jin haka dai baimaka dadi ba ama ka daure, inshallah Doctor Essha dai matarkace har Abada"

Tunda yaji Mami ta kirashi da Asali sunasa yasan cewa dagaske suke, Sai dai yaji dadi Mgnr Mami ta karshe" Wayyo Allahna tayaya zan iya ?.." ya furta a hankali
Ya gyada kai a hankali murya a sanyayaye yace" Inshallah haka zaayi ba Matsala"

Yana fada haka ya Mike yasa takalmasa ya fice. Mami ta kalli Ammi tace" Ayya mu kyautamishi kuwa..?"

" Kyalleshi yanatasamu yariya mutani a bagas shima yaji." Ammi ta fada

" Muna rokon Allah dai yanuna Muna ranar biki na Rai da lafiya"

Da Ameen Ammi ta Amsa.

πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

Essha jirgi su bai dire a koina ba Sai kasar India, Delhi. Nan suka booking jirgi zuwa Lucknow, suna sauka Sanyi gari ya fara tarbasu.

Essha Sai Mita take ma Essha Khan (Pooja) har akazo daukasu zuwa masaukisu.

Washegari sukafito zuwa *Faulrahman Spa beauty and Saloon* Mrs Abdulrahman nada kirki sosai tamusu tarba Iri na Alfarma, nan Aka soma Aiki ba Kama kafa yaro Essha tun daga Gashi Kai har izuwa gagan jiki From top to bottom duk aka soma wankeshi, (πŸ˜…Amare e no easy) skin dinta Sai wani sheki yake ko ita da ta kalli kanta a mirror sanda ta razana dun ta wanku ta gogu, Kamshi kuwa ba'a magana, Essha Khan itama ba'a barta a baya kawa Amarya duk su sha gyara.
Aiki da za'ayi musu na wata Uku cikin kwanaki uku aka gamashi, gaskiya su iya aiki, Essha inta kyalli kanta a mirror ji take kamar ba itaba. Hata Ruwa wankata ma na musaman ne, a hada Wana a murza wancan Flowers masu shegen Kamshi kuwa a ciki ba'a magana, hata kalar Ruwa ma Kamar Madara yake. Kai mutan India na da abu Mamaki.

Ranar ta uku, Essha zaune take gaba dressing mirror daure da towel, Sai wani karami towel Kuma ta daure kanta dashi, fitowar ta daga wanka kenan harma ta Saba da gurje ta dasukeyi, a ranta Tace" finally yau karshe zata huta" ama zata missing ma'aikata sosai, ciki kwanaki nan duk su Saba.
Body lotion take shafawa , tana bin jikita da kallo tana Kara gode ma Allah, fata nan Sai sheki, Shi ake Kira skin like Milk. A hankali take shafa lotion kamar tana shafa ma jikin baby,baya yagama ta warware towel da ta yane kanta Tayi, ta kunna hand dryer tasoma busar da laulausan Gashi nan, hankalinta na kan wayanta, blowing gashita take ama hankalinta ya karkata zuwa tunani Aliyu, nan tasoma rayya ma kanta ko dai ya daina Sonta ne? Kusan satin daya kenan bai kirataba, Sadik ma dan Wayan dasukeyi shima yadaina Kira. Ta missing text messages dinsa masu sanyaya mata Rai, his handsome face, his lips nan tariga blushing kumatu nan yay jawur Kamar tomatoes" Essha don't be a perv, kinsan bakisonshi ko?.." ta scolding kanta tana gyada Kai, Murmushi ta sake tasan cewa "she's just deceiving herself ne, dun ta Dade da fadawa cikin kogi son Aliyu subul"

"lafiya bai kirani ba? Ko dai yadaina So na ne?.." ta fada tana tura Baki " Lalala " tabawa kanta Amsa " ko dai nakirashi ne uhmm?" Ta sake tambaya kanta tana citza yatsa " I will call him, dun kawai naji muryashi, sanan sanace Sadik na ke nema, yawa that's what I you'll do" ta fada ta kada yatsu.
Ta dauki wayata kenan, Esssha Khan tashigo Baki ta bude "Wow!!! This is what we called skin like Milk.." nan ta juyo cikin harshe Indiyanci" Essha kigaki kuwa, So mashallah Wana in Aliyu yaganki a haka Sumewa zaiyi. Kisamai? Nasan abunda zamuyi" Essha Khan yafada tana rike da haiba , Murmushi mugunta take sakewa..

Essha ta jefa mata harara tace" What? .."

"Kaya zakisa shopping zamuje" Essha Khan tafada cikin yaren Hindi

Essha ta rolling idanuwa ta nan Tace" oh hoo Which shopping again, ko ki manta na tuna Miki flight din mu fa by 4pm zai tashi"
Essha Khan Tace" Dalla sauran awa biyar fa, we can Meet up. Oho bakison ki rasa flight ance an fasa dauri Auren jibi ko?

Essha ta Kara rolling idanuwa ta ja tsaki tace" Banda Lokaci ki.."

"My Doctor please save that rolling of Eyes of your's for him, I'm very it gonna drive him crazyyyyyy." Essha Khan ta fada tana mata gwalo.
Essha jefata Tayi da pillow, Essha Khan cikin saurin ta cabke Ta fashe da dariya mugunta, ta rugume pillow, ta kalli Essha with seriousness..

Essha ta kada Kai Tace" What again?

Essha Khan (Pooja) cikin hidunstan Tace"Essha a duk lokacin da zuciya ta kamu da Son abun da take muradi, bayanashi ake ba boyeshi ba, dun boyeshi ba karami cutar da mutum yake yiba, Essha ki fi kowa sani illar haka. Deep down nasan kinason Aliyu ko ba ki fada a Baki, fuskarki ta zayyanamu haka, stop hiding your feelings for Godsake" ta hada hanayata alamar roko" Please Dr. Ina rokoki, da Allah badan komai ba ki sanki ranki da Aliyu, ki kaunaceshi, Aswear to God Aliyu na mutuwa sonki, he can do anything for you, you are just there forming hard to get. Kisamu ba'a ma Mazan yanzu haka fa, Pls pls pleaseeeeee and please ki son Aliyu Kamar yadda yake sonki Inshallah you'll never be disappointed please."

Essha kanta a sukuye tana Wasa da yantsu hannuta, ta ma rasa Mai zatace, can dai ta numfasa ta dago ta murde Baki a hankali ta kada ta rakwasa hannuwata, tasoma susa susa Kai kamar karama Yariya tace" Thank you Poo.. sorry Namecy I will think about it"

Essha Khan ta Mike tazo kusa da ta soma mata cakulkuli" Essha basan daga wane Planet aka jefokiba, I don't want you to think about it, I want you to act, act right now, nasan kinason Shi, imbakifadamin kina sonshi ba, baza taba kyallekiba har Sai ki fada" ta cigaba da cakulkuli. Essha Kam Sai dariya take, taki ta fada nan Essha Khan ta sanata da cakulkul "I love you him, wlh inasonshi is okay" batasan ma tafada ba,

Essha Khan Tace" louder banji ba"

"I said I love him"

"Louder banji ba"

Cikin Kara Essha Tace"I love himmmm Namecy is okay naa.." ta fada tana dariya tana sauke ajiya zuciya. Essha Khan itama dariya take Tace" Munafuka, see how you're blushing."
Essha ta kalli mirror taga yada kumatu ta su sukayi ja jawur, na tarufe fuska tana dariya.

"Ehen saura Abu daya" Essha Khan ta fada ta kane mata ido daya.

"Ohwooo what is it again?" Essha tafada tana yarfa Hannu

"Yawwa tunda ki admitting kinasonshi, I want you to call him right now"
Essha ciki ware ido Tace" Whattt? Hell Nooo" tafada tana mikewa tana gyara daura zama towel dake jikinta.

Essha Khan ta tafa Hannu Tace"What? Water, yes ohhh na ma manta Ashe daga Nigeria kike, dama na sha ji da gani cewa Nigeria girls basu iya soyaya ko nuna soyaya ba most especially aka ce Yan North. I'm not surprise thoooo" gyara zama tayi ta cigaba da latsa wayata can Tace" uhm let me call my Habibi nasan Yana can Yana kewana Kamar yanda nake kewashi" ta fada tana ma Essha gwalo. ta Fadi hakane dun ta pissing dinta, tasan halin Essha tsarai, batason abun zai taba mata kasarta.

Ai kuwa nan Essha ta fusata Tace"Zan nunamiki kuwa Naija girls no dey carry last"

"Zamu gani ai" Essha Khan ta fada, Murmushi kasakasa tarigayi taji dadi gani yadda ta fusata ko ba komai she will do the needful.

Essha wayata ta zaro daga charging ta bude ta soma dialing Number Aliyu, Bata ma tsaya searching number ba,Essha Khan da Mamaki take bin ta da kallo, wato har ma hadace number shi Tayi. Ta Kara gyara zamata sosai tana kallo Essha taga Mai zata iya. Essha Sai Safa da Marwa take a daki, Number Aliyu na ringing ba'a daukaba, nan tasoma citzo yatsa tana jefa Essha Khan da harara, layin dai nata ringing har Sau uku ba'a picking ba, har zata give up ta daure ta sake dialing...

ABUJA, NIGERIA.

Aliyu kwance yake akan Makeke gadonshi, dayagaji da haduwa, ya dawo office agajiye likis ko suit din ma bai cireba. Haushi kowa yake ji a gida, saboda an hanashi magana da Babyshi, bai ma San hali da take cikiba, duk ya damu, Four days kenan ama yanaji Kamar shekaru ya dauka bai gantaba har tsoro yakeji, yayi mamaki yadda Sadik baya ko tambaya Mummysa, yasa duk zugi Ammi ne, Yana kwance Sai kwafa yaketa yi akai akai, ga hayaniya yan taro biki da suka soma zuwa duk su soma cika mishi kunne, A Cike yake fam Kamar ance Tak ya fashe. Nan ya juyo Kara wayasa na ringing, tsaki ya ja yada na ma waya mute bai ko duba maikiraba, dunshi a zatonshi Suleiman ne ko Haydar, Ana ta Kira Yana muting din Kira, Kira na hudu na shigo wa, Amsa Kira yayi zai soma Matsifa kenan, nan yaji Murya da baitaba zatonba tana mishi Sallama. Firgit yatashi zaune yasoma adjusting Tie dake wuyashi dun Kara ma kanshi iska, Murya ta kawai na neman dauke mishi Numfashi saboda zakisa(🌚) a rarabe ya Amsa sallama dun kasa gasgatawa yayi. Ya sauke waya a kunne yakara kallon Number dun ya tabbatar itace, Foreign Number yagani, nan zufa yafara keto mishi takoina, buga zuciya sa ya tsanata ciki ranshi yace" Badai Essha guduwa tayi anka batason Aure? Ta Kira dun tabani hakuri inalilahi"

"Yakake?" Ya jiyo muryata, numfasawa yayi bai amsaba..

"saura kwana biyu bikimu ko?" Ya tambaya a sanyayaye
Da "Uhmm" ta Amsa
Wani yawu Mai daci ya hade ya runtse ido sanan yace" nasan Dalili ki na kirana......" Nan yayi shiru itama uffan ba ta ceba, Aliyu Sai ga Hawaye Shar Shar ke zuba yacigaba" ki..ki...ki Kirane domin kiban hakuri baza ki Aure ni ba, haka yasa ki ka gudu...... please kar Kima iyayeki haka kidawo, Zan fahimtar dasu, Sai a fasa Aure, Essha wlh baranaso abunda zai sa ki ciki tashi hankali ko yatakuranki, ko abunda zai hadaki dasu Mummy please come back..." Ya fada ciki shesheka kuka, harda rike saitin zuciyashi, radadi take mishi dun zafi.

Essha yanda taji duk ya rikice ne yasa tasoma dariya, Tana Mamaki Aliyu ne ke kuka akanta haka, Sai taji takara sonshi wato ana shi tunani guduwa tayi. Ta Kara fashewa da dariya hartana shekewa, Aliyu kam jin dariya ta na ba karami rudashi ta Kara yiba.. yarasa tacewa shikenan zai sake rasa Essha a karo na biyu..

Essha ciki serious tune ta Kira cikake sunashi"Aliyu Umar" bai amsaba dun yasa yau tashi ta kare Mai tunda har ta iya Kiran sunashi haka.. can dai ya daure ya Amsa dun yasa imbai Amsa ba bazatayi maganaba

Essha yanda ya amsa ya so yabata dariya ta cije ciki laulausar muryata Tace" Inason ka kwantar da hankali ka, Essha na kane kadai, ko da Wasa Bata kawo ma zuciya ta zance guduwa Aureka ba, bayi a baya ba balle yanzu, all I'm thinking right now is how to spend the rest of my life with you, a kullum bada wani buri ila nakasancewa a karkashi inuwarka,da kulawarka da Kuma Amsa suna **Doctor Essha Matar Aliyu Kuma uwar yayyan* *Aliyu** ..."
```
Aliyu suma zaune yayi, Wayyo Allah Dadi, Ina zai saka kanshi, Alhamdullilah Allah yakarbi Addua shi, Babyshi tasoma Sonshi,dama ance Addua Makami mummini. Wani haweye Farinciki yaji ke zubamai, runtse idanuwa sa yayi yace" Ima Mafarkine nata bacci har abadan" duk zatonshi a zuci yayi maganar baisancewa ta fito filin ba.
Essha karami dariya tayi tace
"lalala ba mafarki ka keba, Kar kasamu Damuwa nama Alkawari I will always be by your side from now till infinity"
Kara runtse idanuwa sa yayi Yana sauraro zazakar muryata dake rasa koina na jikisa.. Jiyake Kamar yayi fifike yaje yasamaita Murmushi Mai da Kara yayi yace" Jaan(Sweetheart dayaren Hindu) ya subhanallah I can't wait to make you mine, a kullum Sai nayi mafarki Wana ranar.."

Essha ta kada ido kamar Yana gabata tace" Dalili dayasa zaka sake Aurena kenan? Just to be yours after that you will get bored of me......Sai Kuma kaje ka nemi wata....."

"Shhhhsssssshhh" ya katseta sanan ya Mike ya shigide da jiki kan gado Yana shafa Gashi Kai Yana Murmushi, Essha shine ke Hira dashi haka, dagaji murya ta yasan tayi fushi, ko shima abunda ta fada ya tsoratashi, inhar zata bashi Umarni ma ya daina kallon Mata tsab zai daina (πŸ˜…) inya rabu da ita Ina zai saka kanshi.

Ya sake wani Murmushi Mai Dan Kara yace" is that what you are afraid of? "
Shiru Bata amsaba. Yacigaba da shafa gashi kanshi Yana fadada Murmushi yace" My silly doll. Don't you know what you mean to me? Just close your eyes and walk into my imagination with me hmm?"

A hankali Essha ta lumshe idanuwa, tana sauraro muryashi.
"baya shekara mu Goma da Aure,Sadik na da Kari kanne Uku a'a Hudu kyakyawa, maza biyu, Baby girls dake suke kama ama su biyo halina, My boys looks like me but boths has your Eyes da halin ki," yayi karami dariya sanan yacigaba"Sadik ya girma yana can University, kanneshi a shirya suke zasu

Please Login or Register in order to submit comment