Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bridge Mashallah abun Sai son barka, Ruwa ya cika Babbar kogi dam gwani sha'awa har ta tuna lokaci suke zuwa da Essha wanka a Rafi lokaci ana kwailaye.. gaskiya tsari garin ya canza sosai kowa nata harkokikisa gwani burgewa

Haka har Motoci yay karaso zuwa Babbar Fada na Mai Girma Yakanaje, tun daga kofar gidan kana hangowa zakasa na sarauta ne, tsari gida yasha design irin na Manya manya sarakai, Kace gida sarki Kano ne, abunda ya bambata kawai Sama tambari saurantane a Zane watoh takobi su crossing juna(βš”οΈ) Sana akasa *YAKANAJE* Sai tutar Nigeria da Kuma tutar sarauta, gaskiya masaurata Yakanaje yagaji da haduwa..

Suna dosa Babbar gate Nan Babu abunda zaka iya juyowa Sai busa irin ta sarauta, dama an San da zuwasu, Baya an bude musu second gate Nan Dogorai Suka yo kan Mototoci da kirari da busabusai har suka Parker a parking lot..Nan Suka soma fitowa daga Motoci su

Duk Kara na Bai sa Essha ta farka ba, Bacci ta take hankali kwance..Besty zata tashe ta kenan Nan Taji ansoma musu knocking a window ..sauke glass din tayi taga ko wanane Aliyu tagani magiya yariga ma ta, ta bude mishi kofa tabasu minti Daya zaiyi Magana da Essha

Besty Kai kawai ta girgiza Tana Murmushi ta bude kofar ta fito, Aliyu cikin sauri ya shiga, ya gayama driver ya basu wajen.. aikuwa Kamar jira yake Nan Dan yasauka Yarage daga Aliyu sai Essha a motar

Bayan ya natsu ya juya Yana kallonta, Bacci ta take sosai hankali kwance kana iya juyo sautin saukan Numfashi ta a hankali.. ji yayi so da kaunarta na Kara shigashi a hankali.. Yana Kara gode ma Allah Babyshi ne ta haifaaa masa Cute boy, akasan zuciyarsa ya na rokon Allah yasa su sake haifa Yara Goma Sha (πŸ˜…) shinkashi tsanda ya Dara ..

Can yajin tayi motsi a birkice ya dago yaga dai haryazu bacci take, Yatsa sa yasa a baki Yana tunani yada zai ta da ta batare da ya tabata Kar tayi fushi, Nan hankali shi ya shagalta da kallon Cute face din ta da Dan bakinta da take turowa a hankali duk ciki bacci..

Bai Ankara ba yajin Essha ta sulale ta kwanta kan ciyarshi cikin bacci Tace" Besty I'm so tired"
Aliyu Suma zaune yayi ya rasa abunyi, Nan ta Kara juyi gyale da ta yafa ya sauko zuwa kafadan ta, laullausa Gashi kanta suka baje ma ta a fuska..

Aliyu Murmushi yayi yace"Tsarki ya tabbata ga Wanda ya kagi wanan halita ya Subhanallah" Bai Gama rufe baki ya ji ta Kara mirginawa, Aliyu Ido ya zaro Yana tuna ni inyabar ta zata ta damishi danya Aiki..

Gashi kanta ya soma yayayewa daga Fuskar ta, a hankali ya soma Kiran suna ta... Essha Ciki bacci Taji ana Kira suna ta a hankali duk zaton ta Besty ne, batasaniba gogane, turo Baki tayi idon bacci Tace" Besty uhmm uhmm da Allah kibar nayi bacci"
Aliyu yayi Murmushi cikin ranshi yace" Lallai za'a yi dramer queen ana"

"Essha Essha Essha wake up mun iso fa" ya Fada a hankali

Essha Jin murya da na Besty ba yasa cikin dauriya ta bude ido,Nan ta farga dacewa ai jikin wani ta kwanta bana Besty ta ba, a zabure ta mike tasa Kara ta Makele can kuriya kofa tana haki..

Aliyu dariya tabashi yanda yaga duk ta rude gyale ma ta Kara jefardashi Sai ta koma kamar Barbie saboda kanta a bude itama batasaniba..

Daukan gyale yayi ya rike a Hannu Yana Dariya yace" Gashi ki yafa kanki a bude "

Cikin sauri ta fizge kayata tana harara shi..

Murya na rawa Tace" me...me yakawo Kanan Ina Besty na?"

Bai amsaba ta Murmushi kawai yadinga zubawa Yana Jin Dadi moments Dina kamar su dawoma a haka..
Essha Jin Bai amsaba yasa ta sukunyar da kanta kasa tana Wasa da gyaleta so take ta fita ba halin ya Dana lock Kuma batason ta rokeshi...

Shikam kallon ya dingayi kamar zai cinyeta harda lagwabar da Kai da gyara zama.. Essha Jin kallon yayi yawa ne yasa ta dago Kai Nan idonsu ya tsarke Dana juna.....










Please vote like Comment and share πŸ™πŸ™



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ


*WRITING BY*
*J Hajara*


🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“š πŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

7️⃣5️⃣&7️⃣6️⃣
Kallo juna suke ido ciki ido ba kyafatawa, Essha sai taji kwaya idon na driving nata crazy nasa ta cigaba dun kallo cus he got such a beautiful nd sexy eyes da duk mace da ya kalleta da shi , bazata so ya daukesu ba.
Abubuwa take gani ciki masu wuya fasara Nan take taji jikita ya mutu. da farko da ta farka daganishi taso ta mishi Rashi mutuci ne gani kwaya idoshi yasa jikita ya mutu takasa ko motsi ne. Cike da kunya ta saukar da na ta Ido tana tambaya kanta" tayaya yashigo baya tare da besty nake?ko dai mafarki na keyi ne kuwa? But besti...

Bata karasaba taji saukar soft hand nashi a gefe fuskar ta Yana shafawa Yana cewa" Baby am Soo happy today words can't express how happy I am today huh"

Essha ta runtse ido da Karfi duk a takure take tana zaune ne ama tanaji sauti bugawa zuciya ta.. ta rasa dalili.. tanaji yada sauti murya shi ke fita zuwa kunnuwan ta zuwa ga gagan jikita suna isa suka Kara kashe Mata jiki, she wants to cry ama kuka yaki zuwa.

Aliyu yadago fuskata yace" look at me mana baby, bakya murna da gani nane?

Essha daji haka kamar an zugata ta hada fuska .

Yace" Eyya Baby wato fushi kike dani? Toh ayafemin mana please Baby keman fa kisan ba laifina bane, ki yafemin da Allah kinji" ya fadi haka Yana kaimata light kiss a both soft kumatu ta.. sai da taji yarrrr a jikita. Tayi sauri kauda fuskar ta a saitishi

A hankali yace" Baby please forgive me plzzzzzzzz"

Ta sukunyar da Kai dun mamaki kanta takeji mutumi da takeji haushi shi ne yau ta kasa aiwatar da komai biyemishi ma takeyi tayi ajiya numfashi deep down tace ma kanta" focus focus Essha Focus"

Ciki murya shagwababu yara yace" Please Talk I want to hear ur voice,. please talk kince ki yafemin please kinji, in baki fada ba zan Miki kuka please say it naji sanyi a Raina, please forgive meee nasa ba laifina bane ama please forgive me na karbi laifi kince wani Abu plzzzzzzzz Baby zanyi kuka fa"

Essha ta dago ta kalleshi da mamaki yanda yake behaving kamar Sadik so ajebotically(πŸ˜…)

A hankali kamar murya rada tace" Na yafema "

Ta juya ciki sauri zata bude motar ta fita taji motar a kulle. Ta juya ta kalleshi fuskar tuhuma, bai damuba, ido daya ya kashe Mata ya ciro keys a aljihu Yana nunamata, ta Kai Hannu zata kwace ya jawota jikishi ya rugume Yana murmushi saiti kunneta ya rada mata" I love uuuuu Baby and I really miss uu"

Ta ja karamin tsaki ta fizge jikita, ta masa Jan karshe door ta takure a wajan tana hararashi. Nan suka Soma ji ana knocking. Essha ciki sauri ta gyara gyaleta tanaji haushi kanta. Nan kuwa knocking aka cigaba dayi da Karfi gaske Dan ko mutum na barcci ne in yaji Wana knocking din zai farka.

Aliyu yasa key ciki sauri ya murza ya bude motar, Yana budewa sukayi Ido hudu da Ammi ta harareshi tace" toh sannu shugaban marasa kunya sauko kazo kasa min yariya agaba Mai zata maka eyee, baka ji nane nace ka sauko"
Essha Gani Ammi yasa duk kunya ya kamata ta Kara takurewa a gefe guda ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsuta duk ta rasa sukuni kanta.

Aliyu ya Soma susa sushe Rashi gaskiya Yana murmushi ya sauko ya tare kofa Yana dariya.

Ammi ta Kara wurga Mai wani harara tace" sannu ubana, toh ma sa daga na bakai nazo daukoba, kazo ka tsare min yariya a ciki motar ga zufa, na rasa uba da kake bata oya common wuce ka bani waje"

Aliyu ya ki motsawa Yana Mata dariya, Ammi tasa hannu ta ja shi gefe tana binshi da harara. Ta leka ciki motar taga Essha sukunyar da Kai duk ta takure wajen daya.

Ammi tayi murmushi taji yariya takara birgeta tace" Allah sarki yariya kirki fito kinjiko Kar ki Kara biyemishi, Aliyu da ana Banda awards a bagare rashi kunya toh na tabata Miki shine zai zo na Daya"

Aliyu ya na dariya yace"Kai Ammi nifa bahaka nake ba, itace she always make me go gaga"

Ammi ta dukula hannu ta wa sa Mai Tace"na baka Nan kaji min Mara kunya toh ni ba Mami ka bane bale na biyema" ta kalli Essha tace" Yanta shareshi fito kinjiko ku a ke jira"

Essha tasa kafa ta fito a hankali kanta a kasa, Ammi ta riketa nan Essha ta Soma kame kame kunya takeji zata kunce hannuta. Ammi ta ganota tayi murmushi tace" kajinta kunya na kikeji, toh kisaki jiki ki Nima Mummy ki ne kinjiko"

Essha ta dago Kai a hankali ta kalleta Ammi ta lumshe Mata Idon tana murmushi tace" feel free with me you are the precious gift da muke ta jira yau gashi Allah yakawoki, Essha you so much love you"

Essha ta sukunyar da Kai tarasa Mai zatace. She feel guilty ita batason dansu gashi suna nuna Mata so" wayyo Allah na na yanzanyi" ta furta a hankali.

Ammi ta rike hannu ta suka Soma tafiya zuwa ciki palace din, kafi sukai Ammi taja ta tsaya taji Kamar ana biyedasu tana waigawa taga Aliyu ne taja tsaki tace" Wai Mai kake jira baka wuceba?

Aliyu ya susa Kai yace" uhum uhm Ammi ni tare zamu shiga"

Ammi ta rike kai tasaki takai mishi duka wasa ya goce Yana dariya, itama tayi murmushi taja hannu Essha zuwa ciki.

Kana shiga palace din kamshi turare ne Kota ina, Girma palace din na da girma sosai, Royal couch furnitures ne aka tsagaya parlor dashi gwani kyau, sai kujera da Marmataba yake zaune shima kanshi abun kallone, yanda aka tsara Fada ikai bako ne sai ma kamata da abunda ya kawo ka ka shagala da kallo. A decorating palace din in a royal way.Marmataba dake zaune yasha rawani ga fadawa da dogarai gefe da gefeshi fuskarsu daya da Tycoon sai dai shi yafi Tycoon kwari jiki. Gabadaya family a hade a palace din ana jira isowarsu Aliyu

Suna Shiga Essha ta daga Kai a hankali tana bin Yan fada da kallo . Ba cika sosai ba, su daddy ne dan Yan fada sai su bestie dasu Haydar da kanne Aliyu
Essha ta Soma ji kirari na tashi a gefeta ta kalli guri taga Aliyu ne ke kwasa gaisuwa a gaba Mai martaba dogarai ke masa kirari" **Takawa ka* *lafiya Yarima,* *Makiyaka fadawaka** *Sarki ya amsa gaisuwarka* *rankashidade* "

Taga ya Mike ya koma gefe ya zauna yana kallota sun hada Ido sai kunya ya kamata, Taji Ammi ta rike Mata hannu takai ta har gaba Mai martaba suka Gaisa a kunyace. Itama Tasha nata kirari. Ammi ta mikar da ita tanemi guri gefe Bestie ta rakube.

Mai martaba yayi gyara murya nan Fada kaji tsit. Yace ma liman dake gefeshi ya bude musu taro da addu'a. Nan kuwa liman yashiga sharoro addu'a Yana Kai karshe aka shafa.
Baya nan
Tycoon ne yasoma magana yabada labari haduwar Aliyu da Essha Nan Yan fada suka Shiga mamaki waensu harda guntu kwallasu yabasu labari tass.

Kowa yan fada ayi tsit ana saurarashi yakai Aya labari cike da murna yace" am so happy, Allah na yayi ikoshi a inda bamu taba zato ba, Yan kungiyar na Allah yamusu albarka, da ace zangasu yanzu zamu su Kyauta da bazu taba mancewa dashi ba" duk suka fashe da dariya.

Duk ya fada suka jijina ma Daddy Essha iri kokari da yayi. Daddy har Yana kuka. Gaskiya yayi namiji kokari he's a strong Dad.

Baya a natsu duka agama sani juna Mai martaba ya kalli liman yace" Mall liman haryanzu da aure tsakanisu ko babu?

Daddy yace" Nima abunda nakeso nasani kenan dun Kar mushiga hakki"

Liman yace" da Hadi auresu zuwa yanzu shekara nawa kenan?

Idrees ya amsa da" shekara bakwai kenan mallam"

Liman yace"toh madala, a addinace dai idai mace tayi Wana shekaru batare da mijitaba toh babu aure ko da kuwa a gida daya suke zaune in wani suna kwana a gado daya, na aurataya baishiga tsakanisu ba har zuwa kawo Wana lokaci hakika babu aure ko da kuwa bai furta Mata saki ba, ama in miji na da bukatar matarsa sai an sake daura aure( πŸ™ Sisters inda gyara somebody should help outπŸ™‡)


Liman na fadi haka Aliyu Nan take gabashi ya Soma faduwa liman zaiyi magana Aliyu ya katseshi" walahi inason matarta na Amince ku daura mana aure please liman ka taimaka an daura" ya ciki murya tausayi.

Essha daji haka ta Soma kuka Mara sauti ta kwanta a cinye Siyama,



Duk akayi tsit ana jira anji Mai Daddy ko Tycoon za su ce, duk cikisu Babu Wanda ya bude baki dun yayi magana sai kallo juna sukeyi, shi Tycoon kam ya kasa maganane saboda Yana shakkar Daddy daji nauyi. Daddy kam shi bai da dalili dun yamafi son a daura dun yasomaji tausayi Aliyu.

Can duk anyi shiru Daddy yaga shiru yayi yawa ya kalli Liman yace" Mallam ba damuwa an daura Allah yasa haka yazama mafi alkhari"


Duk suka kalleshi cike da mamaki iri kyau hali iri na bawa Allah na da wuya ansamu kamarshi..

Ammi ta kalli Essha taga yanda take kuka sai bataji Dadi ba ta kallesu tace" gaskiya haka baizuyu ba, Essha dai ba yariya bace, ku fara tambaya ta ita Amince toh, ama andaura.aure batare da yarda ta ba, toh Wana ba adalci bane" ta juya ga Daddy ta hada hannuwata Alama roko tace" da Allah Alhaji Kar kace zakasa ta ta Amince na Dole ku bar ta , ta Amince da kanta, Aliyu Dana ne nasa Yana sonta, tun haduwarsu na fari, so baza Amince amanta na Dole kamar yanda Yan kungiya suka Mata ba saboda mu ba jahilai bane"

Ta juya ga Aliyu da fuskar yagama yi ja saboda tashi hankali tace" Aliyu...

Wai hajiya maikike shiri yi ne" Daddy ya katseta.

Ammi ta juyo tace" inaso Kare ma Essha hakkita ne da kuke neman danemata shi "

Liman yace" eh Hajiya tayi gaskiya bara munji daga yariya ta Amince ko Bata Amince ba"

"Aishatu ki Amince a sake daura Aure ki da Aliyu eh ko aa?


Essha duk jikita ya hau Bari gashi duk ido akanta harwani zufa take hadawa. Aliyu idoshi na kanta so yake su hada ido ama Taki dagowa wani hawaye tashi hankali ne ke siyaya a idonshi . Bakita har wani rawa yakeyi ta bada amsa takasa. Bataya tsaya wani tunani ba ta bude baki a hankali zatace aa Bata Amince ba Sadik ya shigo shi dasu Sofia ya fada akan cinyar ta Yana" Mummy na koshi na koshi sosai"

Essha ta rugumeshi ta fashe da kuka, duka guri an tausaya musu daga ita har Aliyu ba Wanda zaka kalleni idoshi ka ga ba kwalla aciki saboda tausayi.

Essha ta gyada Kai kawai ta Mike ta fice a palace din rike da Sadik tana kuka.....



WassssshhhπŸ₯΅πŸ₯΅πŸ₯΅Nima nayi nawa😭😭
Kai DOCTOR ESSHA fans group Kuna da Amana nagode sosai Allah yabar zumunci daga yanzu zaku riga samu update kullum 😁πŸ₯° nagode da kulawarku Wana page naku ne kuyi yanda kukeso dashi πŸ₯°πŸ₯°

Ya Allah sisters daughters frieds namu Wanda suke zana WAEC ubangiji Allah yabasu sa'a yasa sufito da 9credit Ameen ya Allah πŸ™β˜ΊοΈπŸ™πŸ™πŸ™β€οΈ



More comment πŸ™β€οΈmore typing β€οΈπŸ™β€οΈ
Love you guys πŸ₯°




πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ


*WRITING BY*
*J Hajara*


🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“š πŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

7️⃣7️⃣&7️⃣8️⃣

Tana ficewa Aliyu ya Mike da himma zai bin bayata, Mami ta dakatar dashi. Ammi ta kallesu tace" da Allah kuyi hakuri abata Nan da sati kafi anji na bakita"

Ta juya ga Daddy tace" da Allah Kar ka takura Mata kan Aliyu. Yanzu addu'a mu suke bukata, Allah ya zabe mafi alkhari"

Duk suka amsa da ameen sukayi na'am da zance Ammi. Tycoon yasa Siyama ta dubata. Mami da Siyama suka fice wuri dubota. Suna fita koina su duduba har ciki gida su duba Bata. Suka fito compound suna tambaya dogarai. Dogarai suka Basu amsa da yanzu yanzu ta fice Tana kuka.

Mami ciki tsawa tacemusu"maza maza ku bi bayata"

Dogarai ciki sauri suka bi bayata. Suna kaiwa baki hanya su duba koina Bata ba alamata ciki sauri suka koma suka sanar ma Mami. Mami ta juyo ciki palace din ciki tashi hankali ta sanar masu Tycoon.

Aliyu ya Mike a razane har jikishi na rawa yace"Ma..mi i...na tabi? Ya fada a rarabe.

Mami tace"Boy ina za sani, Allah yas...

Daddy yayi murmushi ya katseta yace" ku kwantar da hankali ku, Essha daga na baida zataje sai gida. Ina da tabbaci tana gida"

Aliyu daji haka ya ajiya numfashi Mai karfi Yana lumshe ido, shi kadai yasa maiyakeji. Fatashi daya Allah yasa Essha ta Amince da maganar Mai da auresu. Cus he can't bear losing her for the second time.

Nan aka fara Kira Sallah Asr. Duk suka mike. Su Ammi zasu shiga ciki suyi sallah Tycoon ya dakatar dasu da cewa in su idar da sallah su fito zasuje gidasu Essha ba Bata lokaci.

Mami ta amsa" da toh shikena sai mu fito"

Duk maza suka wuce zuwa masjid.


Essha lokaci da ta fita napep ta tare kamar Daddy ta yasani gida tasa Mai napep ya kaita. Suna zuwa baki gate nasu ta ciro kudi da ita kanta batasan nawa bane ta biya Mai napep ta ja hannu Sadik, haweye ke sauka a fuskata shabe shabe Kamar a bale famfo. Sadik sai tambaya yakeyi"Mummy what's wrong with you? Why are you crying?

Takasa bashi amsa taja hannushi kawai suka Shiga ciki. Ta tarda su Mummy dukasu hardasu Amir, Walid, Daddy karami da hajiya a baki kofa sunyi zugum Kamar a musu mutuwa. Duka fuskakokisu yanuna tsatsa tashi hankali da suke ciki.

Essha ta karaso gabasu takara tsanata kuka ta. A rikece duka suka nufo ta.

Hajiya ta dafata tace" Essha aina ku ka ganshi? Inashi Abbanaki?

Essha Bata amsa ba takara karfi kuka nata Kai wanan karon na shagwaba ne.

Mummy ta juyar da inta suna kallo juna tace"bakijine ba tambaya ki akeyi ba? Ina Daddy ki?

Essha Bata amsaba tasaki hannu Sadik tayi ciki direct dakita ta wuce ta fada gado tana Tana Kara tsanata kukata.

Mummy cike da mamaki suke bin bayata dukasu.

Daddy karami ya kalli Hajiya yace" hajiya Wana kuka da takeyi ya nuna alamu ba lafiya"

Hajiya ta zuba tagumi. Mummy ta nemi guri ta zauna gefe gadon ta daura kan Essha a cinyarta ta Soma share Mata haweye ciki murya lalashi tace" Essha gayamin maiye sameki? Ina kika baro Daddy ki? Ko dai wani Abu yasamaikune?

Essha still Bata amsa ba, kuka ta tsaida ta riga sauke numfashi tana shesheka.

Mummy tace" Essha kince wani Abu Mana ko hankali mu ya kwanta musan mataki da zamu dauko. Rashi maganakifa bashi ne mafita ba you have to talk kinji"

Essha ta Saida shesheka tana kallo Sadik.

Amir ya ja hannu Sadik ya daurashi a cinyarshi yace" Boy where is your grandpa?

Sadik ya amsa da" he is with my Dad"

Dukasu suka dago suna kallo Sadik da mamaki a fuskokisu. Daddy karami ya nantata" Daddy shi fa toh ai'na suka hadu!

Bai gama rufe baki ba suka Soma ji horn da jiniyar mototoci natashi a kofar gida.

Basu tsaya wani tunani ba duk suka mike suka fito. Essha ko motsawa batayiba Dan tasa su Daddy tane. Kara makewa tayi karshe gado ta na zance zuci.

Walid ya bude gate din, motoci suka sa Kai ciki gidan.

Su Daddy karami Mamaki ma ya hanasu magana sai bi motoci suke da ido har motoci suka gama parking.

Securities nandai suka sake fitowa suka bude motoci. Daddy da Tycoon suka fito lokaci guda. Saura ma duk suka firfito.

Aliyu ne karshe fitowa Hajiya ciki firgici ta matso gabashi ta Soma ta tabashi Nanda idonta ya cika da kwalla bakita na rawa ta kalli Daddy Tace"Ahmadu wa nake gani gabana, Kamar dai Aliyu nake gani Miji Essha da Yan kungiya su ka aura mata ko dai idona gizo yake min kuwa?

Hajiya takai hannu Tana shafa fuskarshi kwalla na zuba. Aliyu ya riko hannu ta Yana murmushi yace" kaka idonki ba gizo yake minki ba ni ne"


Hajiya ta fashe da kuka tace"dama kana raye?

Daddy yazo yaja ta yace"hajiya zo mushiga ciki magana bana nabane"


Suna Shiga su Mummy suka musu tarba na mutuci . Aliyu yasoma baza Ido Yana neman Essha, baiga gatanba sai wansu yanmata biyu yagani masu Kama da ita . Wato khairat da Mufeedat kenan. Sai yaji jikishi yayi sanyi yakasan dago Kai. Yanaji Daddy na basu Mummy labari haduwar su har shirya magana auresu da dagawa ana jira Essha, ya kwashe Tass yanda akayi ya shaida musu.


Daddy karami yace"kaji wani ikon Allah ko. Kai gaskiya Nima naji dadi haka. Ke mufeedat je ki kirawota"

Ammi tace" aa ku barta ta huta. Kar ku sake daga Mata hankali"

Hajiya tace" aa kunji wani daura ma karya gindi, tundama Saboda Wana magana ne yasa ta shigo gida da kuka kamar ace Mata na mutu"

Ji magana hajiya yasa duk suka fashe da dariya.

Hajiya Tasha mur ta kalli Aliyu tace" yaro Sha kurumika Kamar ka mayar da mataka ka gama bi'izinilahi"

Aliyu haryashi sanyi a ranshi ciki sansayar murya yace" nagode hajiya Allah ya Kara girma"

Tace" Bari godemin Dana ni kadai nasan wahala da Yan kungiya suka baka ga jinya so ai Dole ta koma gidaka"

Tycoon yaji Dadi haka nan aka Shiga hira kamar a Saba da juna.

Ciki daki Essha kuwa. Ita dasu Bestie ne da su Siyama su Santa a gaba tun Bata magana hartazo ta sake dasu. Yanmata su shiga ranta. Bestie kam sai kallota takeyi tanason tamata magana akan Aliyu ama tana tsora kartasake tsokolo wani tsuliya dodo taja bakita tayi shiru tana ta Mata dariya kasa kasa.

Essha ta kalleta ta tura baki tace" munafuka shine harda min dariya ko? Ta halbeta da pillow.

Bestie ta cabke ta fashe da dariya tace" da Allah siyama kunji nace wani abun? Kawai dai kice min ki tsargu ne"

Siyama tayi dariya tace" karfa ki Bata Mata Rai dun zaiya Kai karaki guri Ya Aliyu" ta fada ciki wasa.

Bestie ta rike kirji tace" ni wa da Allah ku rufa min asiri maza su binne ni ba mataba"

Duk suka fashe da dariya ama Banda Essha. Tayi shiru tana kallo gefe daya. Rahma ta tapping nata a hankali tace" Anty yadai ana hira ke kiyi shiru?

Essha tayi murmushi kawai tace" bakomai dr"


Sukacigaba da hira sai wurare 6 na yamma family din Tycoon suka shirya zasu koma. Tycoon Yama Daddy sha Tara na arziki da farko Daddy ki karba yayi sanda Tycoon yariga hadashi Allah da Annabi Sana ya karba Yana godiya.

Suka rakasu har baki motar, Aliyu ba haka yasoba shi da za a barshi ma kwana zaiyi. Sai kumbere kumbere fuska yake tayi su Haydar na mishi. Yana kallo su Rahma sun fito suna rike da hannu Sadik tare zasu wuce, Still ba Essha cikisu ya ja karami tsaki yaji sanyi kadan yau zai kwana da danshi na cikishi. Sai binshi kawai yake da idon, suzo za sushiga motar ya saki Hannu Rahma zai koma ciki tace" hey boy where are you going?

Sadik Yana tafiya ya na" sorry aunt, one minute, i want to say goodbye to my mum"

Siyama tayi murmushi tace" yawa Dan albarka toh sai ka dawo munjiraka"

Aliyu ya zagaya ciki sauri ya bi baya Sadik bawanda ya lura dashi. Yaga Sadik

Please Login or Register in order to submit comment