Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hutawane a part nashi"

Ummi tace" kasaraku gabadaya ku, karya zan muku, duka ma'aikata na tambeyesu, su ce min baizo ba , kareshi kawai kukeso yi " ta katse Kira

Parlor ya dauki shiru duk suyi jugum ba walwala , tun tun Mami tafi daga hankali ta..

Saiga rahma ta shigo rike da waya a hannu ta tace" Ammi ga waya yaya, daga sashe nake , Yana ringing ya Manta da ita bai tafi da itaba"

Da sauri Mami ta karbi waya Tana taba ya unlocked da kanshi Alama baisan a security ba, ta duba missed call Kira Ammi ne harda na suhaima tace " Ammi kiga ni Ashe waya na gida da daya ya tafi Kuma gashi layi can switched off"

Isa dake zaune tuntuni baiyi magana ba dun yasa Yana magana Mami zata huce haushi akanshi yace" toh Mami ki Kira su bro fawaz ko suna tare "

Tace" good idea barana Kira" tana neman number kenan Kira na shigowa waya , taga ma fawaz dine , ta dauka tasa a loudspeaker... Fawaz yace " buddy ka kyauta , toh gamuna zuwa muna baki gate"

Mami tace" inalilahi fawaz takira sunashi

Yace" ah a Mami ne , Ina kwana ? Bata amsaba ta jefa mishi tambaya da cewa " tundama ba tare kuke ba ?

Yace" a'a Mami ya fitane , mugamu a guri parking lot '"

" Maza ku karaso ta kashe waya

Isa yace " inalilahi ba lafiya"

Ammi ta daka mishi tsawa tace" min shiru duk ba iriku kenan ba marasa ji magana '"

Tana rufe baki su haydar suka shigo dukasu hudu , da sallamarsu , suka amsa a hankali kowane nasu a matukar tsorace
suke , don in magana yaje kunne daddyshi ba Karami tashi hankali zasu shigaba.

Suleiman yakalli siyama yace" little sis maikefaruwane nagaku haka?

Kamar zatayi kuka tace" yayane yace zaije kaduna , tun 8:00am Kuma bai fita da guard's ba, an Kira ummi tace baizoba , mu zatama Kuna tare gashi yanzu har 1:05pm Kuma ga wanan waya ya mata da ita , daya layi daya tafi da ita Kuma a kashe".

Haydar yace " inalilahi 😟 ama buddy bai gayama na zanshi kaduna ba , ama ba komai everything will be fine"

Ammi tace" Allah yasa , ama da Allah Kar wani ya gayama daddyshi har Allah yasa agashi, tun tun ku...ta nuna Sofia da rahma da har idonsu ya fara Tara kwalla









Comment &$hareπŸ₯°πŸ˜˜πŸ˜




πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

_WRITING BY_
_H Hajara_

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________________



```Fans kuyi hakuri kuji ni shiru Kwana biyu sakamako rashi lafiya da nayi..Ina matukar godiya ,da iri nuna kulawaku agareni nagode sosai ...```


*especially doctor Essha fans group inayi ku sosai naji dadi addu'a o inku.. this page naku ne inayiku iri trillion Dinaβ€οΈπŸ’™πŸ’›..iya wuya anatare πŸ₯° love u guys😘😘.*



2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣


Mami tace" Isa kiramin Joseph "

Isa yadana wani Abu kamar waya..

A jiki an rubuta security alert, ko minti daya baiyi da danawa ba sai ga chief security ya shigo da sauri shi..

Mami ta kalleshi tace" Kai da yaraka kuje kune nemi yarona, imbahakaba.....bata karasa ta kada yatsa sanan tace" and you guys should be fast"..

Jiki ladabi chief security yace" okay ma"..

Haydar ya Mike yace" Ammi zanbinsu ?"..

Tace" toh Haydar sai kun dawo , Allah ya bayanashi" suka amsa da ameen" ..

saura ma suka Mike suka ce zasuje..

Ammi ta kada Kai tace" Hafiz da Allah Kar ku Bari maihafishi ya yaji Wana magana ku jiko? "..

Yace" inshallah Ammi Kar kidamu"..

Suka bi baya chief security..


Suna fita chief security na fita ya shaida ma yaranshi su shirya zasu fita, Suma duk jikisu yayi sanyi su San suna ciki tashi in har tycoon yaji labari na .

Wani Babba gate dake gefe haraba mansion din chief security ya nufa, security gate ne , sanda ya Dana wasu lambobi kafi gate din ya wangale kanshi..

ciki babba fili da aka gyarashi sumul sumul , helicopter ne masu ji da kansu dal har uku , ruwa navy blue , jiki helicopter suna TYCOON ne baro baro aciki..


Chief security da wani daga ciki matuki helicopter din Mai suna mike.. chief security ya karbo keys din helicopter din daga guri Mai kula da guri .. ya Mika ma Mike daya , suna shiga ya daga masu Suleiman hannu da saura yarashi , su Suleiman na shiga suka gyara zama sit belts , helicopter biyu su ka dauka, Suleiman da haydar na tare da Mike, Hafiz da fawaz suna ciki na chief security .. motoci ana waje ana jira sutashi.. suna dagawa zuwa sarari samaniya suka dauki hanya kaduna, tafiya suke kasa kasa kamar za su sauka ma mutum akai, ba'a abunda kakeji sai Kara helicopter a hanya kaduna, ba inda Basu duba ba, lungu da sako ,ama ba Aliyu ba labarishi jiki a mance sukasake juyawa, su fawaz su matukar shiga tashi hankali aranshi gani aboki nasu, har su fi security dima .. su Ammi naji dawuwarsu suka fito da sauri da zima ko angashi ..

Mami ta nufi haydar da kanshi a kasa ta tasa hannu ta daga shi Yana kallota murya kuka tace" haydar ina yake ? Ina boy Dina ? Tana magana tana jijigashi

Yace" Mami hakuri zakiyi inshallah za'agashi ya fada murya na rawa"

" Haydar boy ya fita gidana tun 8:00am gashi ganshi uku tayi har da minti na,ba'asan inda yashigaba iyye Wai Wana wani iri duniya ne muke ciki"ta durkusa a kasa tana kuka...

Ammi ta dagata da sauri tace" ki daina kuka za'a ganshi inshallah, kuzo mu shiga ciki"

Mami ta juya ga chief security tace" ku bance min dagani baga amfani ku ba" ...

Da sauri suka bar gun don Suma sunfisu ciga tashi hankali

*******************
Suhaima ne zaune da hajiya binta, sanye take da wani half gown a jiki, wata maid nata na kasa tana gyara mata kumba kafa, a hankali ta dubi hajiya binta ta shagwabe fuska... Hajiya binta tace" yadai Baby na?

" Mummy tun jiya nake trying number Hubby yana shiga ama bai dauka, yau Kuma switch off ne gabadaya, kila ma da gangan ya kashe waya "ta fada murya a shagwabe

Hajiya binta tace" yo Baby na Mai kike ci na baka na zuba, nasha fada Miki cewa Kar kisami damuwa, shi Aliyu guda nawa yake, kawai ki Kira Daddyshi ki gaya Mai"

"A'a Mummy wallahi tsoro Daddy shi nakeyi, Allah Mummy shakkashi nakeji bazan iya ba" ta girgiza Kai

Hajiya binta ta tafa hannu tace" iyye baby duk fadi duniya na Ashe akawai Wanda kike shakka da tsoro , haba dai*2 Kar ki badani mana , kamar ba baki Kisha ba , ta nuna kirjita.. kwantar da hankali ki ai na Gama da uba , yaro muke jira yanzo hannu,kisan nawa na kashe da wuya danasha kafi tycoon ya Amince da aure, Dan kutumar burar uba danya Kai ne dasu, sai ayi dagaske, kawai ki kirashi ki gayamai"

Suhaima ta daka tsale tace" hoho sai mummy na" ta tura Mai gyaramata kumba tace" ke banza tashi ki bar na, kice ma lami akwai pant da brazier na Dana cire tasa yanda zatayi dasu Kuma ta gyarami daki"...

Da sauri jiki na Bari Yar
aiki ta Mike tace" toh hajiya " ta fice. Suhaima ta binta da kallo tana yamutsa fuska..

Tace"Mmmy nakirashi yanzu ba matsala?"
.

" Ai baby na ki kwatar da hankali ki kamar kiyi filo da gawa, kirashi kawai ai mugama dashi"

Suhaima har da gyara murya za'ayi waya da siriki, ta dauki wayata ta dialing hot line din Tycoon da bakowa ke dashi ba sai family nashi..


CAPETOWN, SOUTH AFRICA..

Tycoon ne zaune a baki beach na babba birni Capetown na kasa south Africa, gaba da bayashi duk bodyguards ne, zaune yake aka kujera beach , da Dan karami table agabashi, samashi kuwa umbrella ne babba Mai fadi Yana Kare minshi rana, sai danne danne kawai yakeyi a laptop dake gabanshi Yana sipping Liptop...

Bodyguards dake rike da wayoyyisa ya karaso da sauri yace" Sir ur phone is ringing Kuma hot line ne" ya fada cike da girmamawa..

Fuskashi na kan laptop din yace" okay answer it, kila Aliyu be, basa matsala shi ba tun jiya bai kiraniba "

" A'a Sir bashi bane " bodyguard din ya fada Yana Mika mishi waya..

Ya karba yasa a kunne, suhaima ko sallama tace" hi Dad"

Tycoon yayi murmushi yace" ohh siyama Daddy yakike?

Suhaima ta Bata fuska tace" Suhaima ne sir"

Yace" ohh Suhaima yakike?


Ko amsawa batayiba murya tsoro tace" uhm uhm da..da ma..dama ....

Yayi murmushi yace" saki jiki kiyi magana kinji suhaima am ur dad"

" Uhm Aliyu ne, tun jiya Ina Kira shi bai daukaba, yau Kuma a kashe, shine na Kira naji ko lafiya " ta fada murya a shagwabe....

Dam yaji gabashi ta fadi yace" shi Aliyu ne number shi a kashe?

Ta amsa da eh Daddy"

Yace" hold on, kashe bara nakirashi"







Comment & shareπŸ˜˜πŸ˜˜β€οΈπŸ™




πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

_WRITING BY_
_J Hajara_

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________________

2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣


Nan take ya dialing number Aliyu, number akashe, yanaa trying ba adadi, yace bara na mishi video call" ..ya jayo laptop nashi, daya Dana number Aliyu ko ringing baiyi sai yanuna disconnect, inyakara trying abun daya yake nunanawa.. .. " bara nakira ammishi dai naji ko lafiya" yakirasu duka bawanda ya dauki waya..lokaci kam su Ammi sufita dukasu suduba ko aganshi ,Basu fita da wayaba... Ranshi ya Soma baci kawai yace bara yamusu video call direct da number gida yaga ko lafiya...layi ya Soma ringing ba'a dauka har Kira ya dauke, yasake dialing ...

Rahma da shigowanta falon kenan taga Kira Daddysu, wana abun dai kamar tv ya bayana sai surutu yake Yana cewa" alert alert Daddy is calling" da gudu tafita sukaci karo dasu Ammi a hanya..

Jiki a sanyaye tace" Ammi daddy ne ke Kira Kuma video call ne"

" Inalilahi waina ilaihi raju'un" shine abunda Ammi ke ta nanatawa. ..

"Ammi kawai muje mu amsa Kar anunamishi komai nafaruwa" Suleiman ya fada...

Siyama tace" eh haka za'ayi Ammi "

Suna shiga wani Kira nasake shigowa, duk suka zauna suka natsu kamar ba komai..Haydar ya picking kira... Tycoon ne ya bayana a screen, dun dole duka suka sa murmushi dole,ya bin ya parlor da kallon daya baya daya, suka gaisheshi ciki girmamawa, ya amsa..

Ya Kai dubanshi ga Haydar ya jefa minshi tambaya" Haydar ina takwaraka?"..

Haydar yaji tambaya a bazata ya kasa motsi in ya kalli Ammi sai ya kalli mami... Ammi ta mishi Alama yayi shiru...

" Haydar nace Ina abokika? Yasake tambaya

Haydar ya tsure ya rasa wani amsa zai bashi ...

Sofia ta amsa charaf idota da haweye ta Soma magana tace" Mami , Ammi kuyi hakuri, ta juya ta kalli tycoon tace" Daddy Yaya tun safe yatafi kaduna, kuma Ummi ta Kira tace baizoba, ba Ina ba'a duba ba'a ganshi ba" ta fashe da kuka ...

Isa yasa hannu akai yace " shikena yau munshiga uku"

A fusace Tycoon ya Mike cike da kidima da razana har jikishi na Bari yace" Aliyu nawa ne ba'agani ba tun safe" kit ya kashe Kira....

Mami da Siyama suka fashe da sabon kuka... Ammi tayi lalashi har ta gaji ita kanta daurewa takeyi.. su Fawaz ba motsi sanda aka Kira sallah la'asar tukun suka Mike zuwa masalaci ...


Tycoon na katse Kira jikishi sai rawa yakeyi, yakasa natsuwa ... Yace" ismail maza maza kiramin pilot " ba da jimawa sai ga pilot ya karaso...

Yace" muje ku Nigeria zamu koma yanzu na" Yana jikishi na bari...

Ko yajira a bude minshi motar dankashi ya bude yashiga, aka tada motoci sai airport, private jet dayazo dashi ya wuce direct ya shiga , da sauri guards suka bi bayashi suna shiga jirgi na tashi.. bada jimawa su ka sauka Nigeria, kaduna airport , da sauri guards suka sauke motoci dake ciki jirgi.. saboda emergency iri haka suke ajewa..

A ciki motar kuwa sai ma driver matsifa yake Wai bai sauri, gudu kawai suke akan hanya kamar zasu tashi a sama , har suka karaso anguwar su Ummi , sai horn kawai suke zubawa , da sauri gate man ya bude gate din suka shigo...

Ummi dake sama balcony tana sauraro redio taga shigowar motoci tace" wato shakiyi yarona sai yanzu ya karaso, zanyi maganika ka ai" ta dauki walking stick nata ta fara saukowa tana zuba matsifa... Tana sauka taga Tycoon ne.

" Wato ma Kai ka rakoshi kenan ? Ummi ta fada cike da matsifa tana ta leleka ko zantaganshi..

Tycoon ya nufo Ummi yace" Ummi ba'aganshi ba, Wai yazo na kaduna " ya fada jikishi na Bari"...

Ciki tashi hankali da razana tasake tace" Aliyu din, inalilahi wayyyooo nashi ga uku na Ina gada gana yashiga " ta fashe da kuka ta sake walking stick din Kamar zata fadi, Tycoon da sauri shi ya rike ta..

Yace" Ummi Kar ki tada hankali ki za'agashi insha Allah nayi waya da commissioner yansanda, ya tura yarashi a bazama nemeshi, Kar kidamu Ummi" Yana magana muryashi na rawa"..

Ummi ta share hawaye tace" toh naji, Umaru nasa kawai dauriya kake yi , wuce ciki kasamu ka huta".

Ya girgiza Kai yace" Ummi bazataba samu wani kwanciya hankali ba har sai Naga Aliyu, kiyi hakuri Ummi"..

Ummi tace" Aya Umaru Kar kadaga hankali da yawa fa, Ina zuwa"... Sai gata ta fito,Yan aiki maza ne biyeda ita suna rike da babba daddurma da plastic chair, Uncle Bello nabinsu a baya hannushi rike da bottle water...

Ummi tace" Kai ku shimfida a gabanshi"... Suka shimfida, taje kusa da je kusa da Tycoon da sai safa da marwa yake, wayoyyishi sai Kira akeyi yahanasu amsawa.. jikishi sai Bari yake...

Ummi tace" Umaru zauna ka huta "..

Yace" Ummi kiyi hakuri, baza iya zama ko samu sukuni ba har sai Naga Aliyu "..

Ta kada Kai Tana hawaye tace" haba Umaru da wane zamuji , dubi fa Bari kakeyi a tsaye, Dana shiga ciki maihaifiyarshi ta Kiran, tana kuka Wai kaki daga wayoyisu, Alama dai kenan kana fushi dasu, haba dawane zamuji" ta fada Tana share hawaye...

Yace" ya'isa Ummi daina kuka, bayi fushi dasuba, gashi zan zauna... Ya zauna.. " Abba Salma mu zauna"..

Ummi ta gyara zama tace" inba fushi kakeyi dasu ba, gayamun Maiye dalilika na ki daga musu waya, Aliyu ko da masu Kama da gunki na(guards πŸ˜„) ya fita in Allah ya rubuta wani abun zai samaishi toh fa bazai tsalake ba saiya faru, saboda haka ka kwantar da hankali ka insha Allah za'agashi ciki koshi lafiya kuwa, ba abunda zai samaishi, Kuma ai Aliyu ba yaro bane"..

Uncle Bello yace" gaskiya ne Ummi, insha Allah za'agashi".

Yace" Allah yasa" ya Mike tsaye

" Ina zakaje? Ummi ta tambayeshi

Yace" masalaci zanje Ummi, ankira sallah la'asar"..

Baigama rufe baki ba bodyguards Mai rike da wayoyyisa yazo da sauri yace"Sir, commissioner ne ke kira"..

Ya amsa da sauri yasa a kunne yace" hello kungashi?"..

Daya bangare commissioner yace" Sir lungu da sako, ciki gari da baya ta, hanyoyi titituna ba inda bamu duba ba, yallabai ka Kara hakuri, dakaina nayi jagora , ama Kar kadamu yallabai zamu Kara himma, sai aganshi yau Dina ba gobe ba"..

Tycoon duk ya firgita baiya magana sai bin waya yake da kallo... Karshe ma katse Kira yayi ...Ummi sai kuka..

Yasa hannu a baya yaje ya dawo*2 iyayi sai furza da iska..

Can yace" Abban Salma kashiga da Ummi ciki ni zanje sallah "..

Ummi tace" Umaru zaka iya fita jiki ja fa yannuna bakada lafiya ?"..

Yace" Kar kidamu Ummi sallah zanyi"..

Ya wuce bodyguards na binshi a baya hagu da dama, fuskar na ya hadashi tam kamar baitaba dariya ba, har yakarasa baki masalaci, dakanshi ya dura ruwa a tap yayi zauna yayi alwala hannushi na rawa saboda baci rai, mutani masalaci kam sai mamaki sukeyi yau tycoon ne a gabasu, mutumi da suke gani a tv yau ganshi su ganshi a zahiri.... Yana idar da alwala ya wuce zuwa ciki masalaci guards zasu bimshi ya dakatar dasu da hannu, baya an tada jam'i suyi sallah su idar, ya zauna yadade a zauna Yana roko Allah yabayana mishi Aliyu shi ...sai misali karfe biyar ya fiti, jiki shi duk yayi lagwas, guards ne a baki kofa masalaci suna jira fitowa shi, da Uncle Bello hardasu commissioner, hannu kawai ya daga musu bai yi maganaba, ya tsaya shiru sai bi anguwa kawai yake da kallo....


Shiru shiru bakaji motsi, yakai dubanshi ga gate dinsu Ummi.. kawai idonshi ya sauka a wata motar kirar range Rover, can Parker nisa da gate din, ya tsaya shiru Yana kallon motar.

sai ga commissioner ya karaso gefe shi" Sir munkarasa ciki ko, yamma nayi Sir,Naga alamu sunu na kamar bakaji dadi"..

bai amsaba,shidai hankalishi kawai na kan motar na.. " Abba Salmah waye da motar na a anguwar na daya Parker shi a gefe gidaka? Ya jefa ma uncle bello tambaya..

Uncle bello yace" yallabai wata motar kenan ni bagantaba?"..

Yayi nuni da motar dake can a Parker a gefe gate... Inbaka lura ba bara kasan da wani motar aguriba..

Uncle Bello yace" Kai gaskiya babu, ama basan dai ko wani bako bane mukayi.."


Dai dai lokaci da suke magana aka motar, iska ya kada, kofa ya bude dayake ba rufewa akayiba, an jigina ne, Tycoon yaji gabanshi ya fadi, dun kamar ya hangi mutum a ciki, ama baigani sosai saboda akwai Dan tazara a tsakani su...

Ya Soma tafiya yanu fi guri motar....

Commissioner yace" sir Ina zakaje kuma?"..

Hannu kawai yadaga minshi(Ashe Aliyu yayi gadone).... Yayi Tata ki har guri motar ama baikaba yaga ko waye ba..





Comment &shareπŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ™


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

Writing by J Hajara

🌍MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ


Kungiya d'aya tamkar da dubu.masu Nazari da Aiki da ilmi, burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________



2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣


Har zai juya kawai ya hangi hannu mutum ya fito, da sauri yakarasa guri motar, gabanshi na faduwa , Yana karasawa wa zai gani Aliyu ne, kwance shabe*2 kamar baya numfashi, ya yake salati da Karfi sanda su commissioner suka firgita, da sauri su su ka karasa wajan, Tycoon yakara bude kofar backsit din yashiga ya talafoshi, abunda yakara razana shi gani jini da ke jikishi yasa yakara rikecewa, ya talafo fuska Aliyu yace" Aliyu bude idoka nine Aliyu, nace ka bude idonka daddy ne"

Su commissioner da karaswasu kenan suka taimaka mishi aka fitar da Aliyu daka ciki motar,, Tycoon duk ya rikece dagani hali da Aliyu keciki..

Commissioner yace" yallabai ka kwantar da hankali ka tun da aganshi....

Tycoon ya katse shi da cewa" maza ku Kira min ambulance "...... Ciki hanzari uncle bello ya Dana kira number ambulance din hospital dayake zuwa, bada jimawa ba suka karaso..... tycoon dakashi ya sukuce Aliyu yasashi a motar ambulance.

Dai dai Ammi na Kira waya uncle bello, ya amsa, yaji duk murya yaji duk murya a shake Alama Tasha kuka tace" Yaya haryanzu fa bw Aliyu ba labarishi gashi har magriba ta gabatoh"

Uncle Bello yace" Hajara, alhamdullila Zaki ce don aganshi, yanzu haka asibiti za'ayi dashi, ki kwantar da hankali ki"

Ammi ta rude da taji cewa" za'akaishi asibiti tace" subhanallahi, maiyesameshi? Aina aka gashi? Aciki wani hali? Ta jero tamboyoyi duk lokaci daya....

Uncle Bello yace" hajara wa na tamboyoyi haka nace ki kwantar da hankali ki"

Ciki tashi hankali tace" a'a Yaya gamuna zuwa" ta kashe..

Aliyu kam tuni aka wuce dashi wani babba private hospital dake ciki gari kaduna, likitoci ciki gagawa suka karbeshi, ana bashi taimako gagawa .. .

Tycoon ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai ziriya kawai yake a baki daki, addu'a kawai Allah yasa Aliyu ya farka, ya fi hour daya, haka ma guards duk inda yabi sai su binshi da sorry sir".. commissioner da uncle Bello su na ta rokeshi ya zauna ya huta, ko kulasu baiyiba, harsu Ammi suka karaso, duka family din, hardasu Suleiman..

Likitan ya fito daga daki, da sauri Tycoon ya nufeshi, Ammi da Mami ma haka, don dagani alamu shine likitan

Tycoon yace" Doctor how is my son doing ?... Kowa ya tsaya cirko cirko Ana jira amsa likita..

Likitan yayi ajiya zuciya yace" sir ka kwantar da hankali ka, ba wani Abu bane Mai tsanani dogo Suma ne yayi sakamako kwaya dayasha, bincike mu ya nuna, kwayoyine suka so suyi mishi illa har yakaishi da Suma"

Kwaya?!!! Harsu na hada baki guri Kira....

Mami ta rude ta cakumo likita a gaba riga tace" what the you by that, Dana baya shaye shaye"... Likita duk ya tsorata sai zaro idon kawai yake,..

Suleiman ya zo ya janyeta yace" Mami kiyi hakuri munji bayani likita, Nima nan zan shaidin Aliyu akan baya shaya shaya " yakali doctor yace" doctor yajikishi yazun?

Doctor kam ya gama tsorata balle yaga family din tycoon dashi tycoon baison yayi kuskure da saurishi ya amsa yace" yes jikishi da sauki inshallah Nanda few minutes ma zai iya farfadowa inshallah"

Tycoon yace" doctor jini dake kayashi fa?!

" Sir muyi iya bincikemu, ba wani ciwo da yaji kila shafaminshi akayi bamudai sani ba" doctor ya fada...

Ammi tace" zamu 'iya ganishi?

"Eh hajiya zaku'iya shiga".. doctor bai Gama rufe baki ba Tycoon ya shiga, saura suka bin bayashi ciki hanzari...kwance yake, hannushi da Kari drip, idonshi a lumshe haryanzu bai farka ba, bawanda bai tausaya mishi dagani hali da Aliyu ke ciki. Tycoon ya zauna a gefeshi yarike hannushi, daki ayi shiru kamar ba mutani aciki , har aka Kira sallah magariba, Aliyu bai farka ba, jikisu a mace suka je sallah, har akayi isha'i , suna idarwa suka sake komawa daki. Daki dal yake da wutar lantarki koina kamar Rana, Ammi,Mami da su rahma suna zaune ne akan katuwar daddumar da akan shimfida a daki, kowa da carbi a hannusu suna casbaha,duk suyi shiru kamar a musu mutuwa, rabonsu da abinci tun breakfast na safe, ba karami tashi hankali suka shigaba, da sallama suka shiga, suka amsa.. Tycoon ya nemi guri a daya Dana ciki kujera dake kusa da gado Aliyu , ya zauna shiru, ya kalli gefeshi yaga su fawaz ne duk su zuba tagumi Suma idonsu na kan Aliyu harsu bashi tausayi, uwa uba Idrees da tun zuwashi yakasa sukuni..

Tycoon ya girgiza Kai yace" haydar kuje gida ku huta, inshallah abokiku zai farka, ai abun yazo da sauki tunda aganshi ko?Isa ka dauki ummi dakai"

"a'a daddy kayi hakuri mu zamu zauna, Kai kaje gida ka huta, dasu Ammi , Kuma ma am a doctor zan iya kuladashi" fawaz ya fada..

Idrees yace" gaskiya ne daddy, yakamta kaje ka huta , kusa wani abun a ciki ko, kaga su rahma yarane Kar yamusu illa"

Tycoon yayi ajiya zuciya yarike hannu Aliyu tam kamar za'akauce mishi, baice uffan ba,can yaji kamar Alama hannu na motsi, kafi yayi wani abun ya sake hi Aliyu ya Kara rike hannu shi gam, da sauri ya daga Kai ya kalli fuska yaga kamar ya farka,bakishi na motsi kamar abun yakeso furtawa, same time idonshi a rufe. Tycoon ya Mike da murna yace" Alhamdullila, Aliyu bude Idonka daddy ne" ai su Mami daji haka duk suka yo kansu..

Aliyu kam ya farka ama dishi dishi yakai gani mutani da ke kanshi, kafi ya bude idon gabadaya a hankali, Yan bi Yan daki da kallo daya baya daya, yayi mamaki ganishi ana,jikishi gabadaya ya mance, ya sake binsu da kallo har Yana Kara Ware Ido.. Essha yake so gani ama batanan, a razana ne ya Mike yana dube dube..

Tycoon ya rikeshi yace" Aliyu Alhamdullila ka farfado"

Yakalli daddyshi , bakishi na rawa

Please Login or Register in order to submit comment