Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH๐Ÿ’”


_by NoorEemaan_๐Ÿ“šโœ๏ธ


Banyarda a juyamin labarin nan ta wacce hanya ba. Nawane mallakinane saboda haka akiyaye!
Wanna littafin kyauta ne (free novel)



Any resemblance of story or life style should be considered as a coincidence!


I dedicated this whole book to my lovely mom. Allahu yakara miki tsawon rai uwa ta gari๐Ÿ’



In the name of Allah, most gracious, most merciful.


My first novel(littafina na farko).

*Assalamu alaikum jama'a, wannan novel din ba sabo bane, zan sake reposting din shi saboda sababbin fans dina da basu karanta ba, idan ina ganin comments zan ringa baku two updates kullum*

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



1-2

(Not edited)


*Hassan ladan street zoo road kano*


Maidaidaicin gidane mai dauke da dakuna 4 falle~falle, sai kitchen hadi da toilet. Tsakar gidan babba ne babu laifi, kasan amalale yake da tiles.

Wata yarinya da'a shekaru bazata wuce 17/18yrs ba, zaune akasan tiles duk da uban sauro dake cizonta hakan bai dameta saboda halin maraici, kewa, kunci, da damuwar da take ciki.




Saukar abu taji ajikinta wanda hakan yasa ta dagowa. "gashi ki wanki min su, su zansa gobe" cewar wata budurwa da'a shekaru zata kai 21yrs.

Mikewa ta yi zaune cikin sanyinta domin cika umarnin da aka bata

"Ke FAHEEMAH ki tabatar baki yi bacci ba idan ankawo wuta ki gogemin su" wannan budurwar ta fadi cikin izzah da wulakanci.

"Toh aunty jameela" cewar faheemah cikin cool voice dinta.

bayan ta gama wankin ta kakkabe kayan da kyau domin suyi saurin bushewa saboda 12:00am suke dawo da wutan nepa.
Zama ta cigaba dayi awajen har abbuh'nta ya shigo ya rufe gidan kallo daya ya mata ya dauke kai, hawayene suka zuba mata kana ta dafa kanta dake sarawa sosai yau kusan kwana uku, amma ba wanda ta isa ta fadawa domin ya siya mata magani, Toh waya damu da Ita balle ya damu da damuwarta? tuno hakan yasa wasu hawaye masu zafi zubo mata....

A bangaren abbuh kuwa, idan ya ganta sai ya dinga tunanin itadin wacece agareshi? Tunani yakeso yayi ko zai tuno wani abu a'kanta, amma yakasa da wanna tunanin ya shiga dakinsa inda ya tarar da mami tana jiransa...




*FAHEEMAH*
Bayan nepa sun kawo wuta ta kwashe kayan duk da basu bushe yanda akeso ba, amma tana sa iron zai ida bushewa domin nepa ba tabbas, bama wanna ba matukar bata goge kayan nan ba ta shiga uku a hannun aunty jameela, domin tasan cewa tana da kaya da yawa da sai wanda takeso zata sa, amma saboda kawai ta sata aiki shiyasa ta ce ta wanke mata su, lokuta da dama sai ta dinga tunanin wani laifi ta aikatawa anty jameela ta tsaneta har haka.




Bayan ta gama ta dauro alwala kamar yanda mahaifiyarta ta sabar mata, tuno da umminta data yine yasa kwalla sake ciko idonta kasancewarta mai saurin kuka, shimfuda tayi a kasan mai uban sanyi, duk da cewar katifarsu babbace amma bata kwanciya saboda a cewar jameela gadon yayi musu kadan su biyu su kwanta.

Addu'an bacci tayi duk da cewar idanunta a soye suke ba alamun bacci, dakin ya dau shiru sai dariyar jameela dake tashi a dakin tana chatting a wayarta kirar infinix hot8. Lumshe idanu Faheemah tayi hadi da tuno rayuwarta ta baya.....



_mu cigaba ko ya?_๐Ÿ˜š


๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH ๐Ÿ’”


_by NoorEemaan_๐Ÿ“šโœ๏ธ


ELEGANT ONLINE WRITER'S ๐Ÿ“šโœ๏ธ



free novel

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



"Don't disobey Allah for the sake of someone you love.๐Ÿ’—
Because the heart of one you love is in the control of Allah. "


(Not edited)


3-4

Abubakar idris sunan abbuh, dan Asalin jahar katsina ne a unguwar charanji yan albasa, Iyayensa sun rasu tun yana da shekara sha bakwai, kawunsa mai suna anas ne ya cigaba da rikonsa tare da matarsa mai suna bintu.



*Bayan shekara bakwai*


Zuwa wanna lokacin zaman abbuh yafi yawa a kano inda yake sana'ar siyarda kayan kitchen a kasuwar kwari, inda abokin kawunsa ne ya masa hanya ta dalilin wani abokin dake kano, bayan wasu watannin Kawu anas ya bijiro masa maganar aure inda abbuh ya barwa kawun zabi ya zabar masa.



*Hajara*
kawu ya zaba masa saboda lura da yayi cewar tana sonsa saboda tana yawan zuwa gaishe da su kawu musamman idan abbuh ya zo katsina.


Su kawu sun nema masa auren hajara inda nan take aka basu saboda akwai tsananya mai kyau atsakaninsu.


Bayan daurin aure aka kawo amarya unguwar dandishe dake kano inda nan abbuh ya kama musu haya.


Bayan 2yrs hajara ta haifi ya mace ranar suna yarinya taci suna jameela. Jameela nada shekara daya abbuh ya hadu da haleema kyakyawar bafulatanan adamawa yar gaba da layinsu ce tana sana'ar siyarda awara a kofar gidansu.



Mahaifiyarta ta rasu inda ahannu kishiyar mama'nta ta taso, wanda ba laifi tana kulawa da ita, haleema na da kanwa guda daya mai suna zainab inda kishiyar mamanta ne ta haife ta, akwai shakuwa atsakaninsu da zainab ษ—in.



A hankali soyaaya ya fara shiga tsakaninsu inda abbuh ya sanar mata da yana da mata da y'a daya ta kuma amince tana son kayanta a haka.


Abbuh yaje katsina yasanar da kawu bello domin suzo nema masa auren haleema, aka sanya lokacin aure wata hudu.

Ranar da abbuh ya sanar da hajara maganar auren nasa yaga tashin hankali, xage~zage ta kama yi hadi da alwashi Kala Kala abbuh yayi ta rarrashinta da kalamai masu kwantar da hankali amma kamar kara tunzurata yake sake yi , da safe tayi ficewarta batare data nemi izinin abbuh ba.


โ˜…โ˜…โ˜…

*Katsina*

"Hajara ki tattara ki koma inda kika fito, banda bakin halin irin naki ba'a kishiya ubanki yamin? yaro dan albarka da baya gajiya da mana hidima" cewar mahaifiyar hajara.

"Kai! kai!! a hayaniyar me nake ji?" Cewar mahaifin hajara dake shigowa gidan, labarta masa komai maman hajaran tayi, shima fada ya shiga mata daga baya ya dora da nasiha inda yace ta kwana da safe ta tafi saboda yamma tayi, jinsu kawai hajara keyi amma ita tasan meta kudurta aranta.



Bayan biki haleema ta tare a gidanta dake kofar ruwa B, inda suke zamansu da abbuh lafiya, tsakanin abbuh da hajara ma kadaran kadahan ne.


Bayan 3yrs haleema ta haifi kyakyawar yarta, ranar suna yarinya taci suna *FAHEEMAH* bayan suna da wata uku abbuh ke sanar da haleema ya gama ginin gidansa dake zoo road, kansancewar yanzu babu laifi kusuwancinsa na tafiya cikin rufin asirin domin Yanzu shagonsa ya zama uku.


zaman haleema da hajara babu laifi domin duk neman fadan da hajara zata yi, haleeman bata kula ta, hakan ke sake tuzurata, sai idan abbuh na gida haleeman ke samun sauki, kullum tana daki matukar ya fita sai dai idan alwala zata yi ko girki take fitowa.


Shima da hajara ta ganta zata fara zaginta ta kuma rakata da harara, Hakan na matukar bawa haleema tsoro hadi da sata fargaba domin bata saba da tashin hankali, kuma koda wasa bata fadawa abbuh ba (wanda matansa ke kiransa da alhaji) domin bata so a dalilinta su samu matsala a zamansu.


Akwai ranar da faheemah ta juye wa hajara klin mai yawa a ruwa abunka da yarinya, ai hajara na fitowa ta wanke mata Mari hadi da cillata kofar dakinsu kanta ya bugu da bango, hakan yayi daidai da shigowar abbuh da fitowar haleema da ta ji ihun faheemah, abbuh kan hajara yayo ganin hakan yasa hajara ta ruga daki hadi da danna sakata, duk yanda yayi ta bude ta taki , akan ya sak'e bata ransa.


"Wallahi bazan bude ba, yarinya ta Mun asara kiln har 2kg ace bazan magana ba"


"ke kike siyowa? ke baki san yarinya ba ce? Meta sani? Ki bude dakin nan kafin in bata miki rai" cewar abbuh.

"Wallahi bazan bude ba Alhaji" ta fada cikin daga murya.

Cikin bacin rai abbuh yace "Toh kifito ki tafi gidanku"

"ba inda zani babu shaida"cewar hajara.

"Hakane? Nace haka kika ce? Toh na sak...."


Haleema take zaune tallafe da yarta da bata motsi cikin tashin hankali tayi saurin cewa "Alhaji faheemah bata motsi fa"


Domin bata so adalilin yarta asoma kashe auren da'aka Gina bisa tubalin gaskiya shiyasa tayi saurin katseshi.

Jin haka yasa abbuh kasa karasawa maganar sakin, ruwa ya debo ya yayyafa mata amma bata motsa ba, "Dauko hijab dinki mutafi asibiti" inji abbuh.

mikewa haleema tayi cikin sauri tana sharar kwalla suka fice daga gidan...


Abangaren hajara kuwa tayi matukar tsorata jin abinda abbuh ke kokarin yi, domin duk abinda take masa bai taba yin fushi haka ba ballantana ma aje ga maganar kokarin yin saki, jitayi ta kara tsanar Faheemah fiyeda na baya.




Kwanansu Faheemah bakwai a asibiti aka sallamesu, wanda hajara bata zo ba hakan ya kara bata ran abbuh, haleema dai lallashin ta shiga yi domin bata son adalilin hakan su samu matsala da hajaran...


๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH ๐Ÿ’”


_by Noor Eemaan_๐Ÿ“šโœ๏ธ






free novel



Life is so confusing,what we want we don't get, what we get we are not satisfied with, what we expect never happens &what we hate generally repeats.....


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



(not edited)



5-6

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Faheemah nada shekara Tara Jameela nada shekaru sha daya inda babu shakuwa atsakaninsu domin mami(hajara) bata Barin suyi wasa tare idan ma faheemah taje dakinsu da kuka take dawowa domin mami taki jinin ganin Faheemah, hakan yasa ummie(haleema) hana ta zuwa kullum suna dakinsu saboda kaucewa fitinar mami.



โ˜…โ˜…โ˜… Mami ce zaune da kawarta hajja hindu wacce suka hadu akasuwar sabon Gari suka kulla kawance kasancewar halinsu yazo daya.

"Wallahi kitashi tsaye akan wanna kod'add'iyar kishiyar taki da yarta, amma da anyi magana sai kice bakya son shige-shige bin yan tsubbu"


" hmmm kedai bari hajja hindu babu abinda yafi damuna kamar cikin jikinta"cewar mami.

" ai bama wanna ba kina ganin idan wanna yartata mai suffan aljanu ta Kara girma suka kai munzanin aure aka ajiye faheemah da jameela kina ganin za'a dau yarki ne?"

Bata rai mami tayi jin abinda hajja hindu tace.

" kiyi hakuri fa kawata kinsan gaskiya ce saina fada..."


Suna a haka saiga jameela ta shigo ta dawo school ta fada jikin mamin, "ke baki ga uwar taki ba?' Sai data turo baki kana ta juyo tace "Ina wuni" amsawa hajja Hindu tayi, hadi da mikewa sanna ta Kara jadaddawa mami tayi tunanin akan maganarsu kana ta fice


"Mami meyasa faheemah ta fini fari da gashi da kyau? kowa a makarantan mun sonta yake har malamai sonta suke saboda ita ce take zuwa na daya ajinsu" cewar jameela cikin jin haushin Faheemah saboda mami tariga ta datsa mata kiyayyar faheemah a azuciyarta tun basu girma haka ba, kara turo baki tayi kana tace "kuma wallahi dan dai abbuh yace mu dinga tafiya tare school da na daina saboda na tsani hada komai da ita" jameela ta kara faษ—a cikin jin haushin faheemah.

Ran mamine ya kara baci hassada na cinta ta ko ina haleema da yarta su musu nisa dole ta tashi tsaye akansu domin bata so ace RAYUWAR take hangowa yarta yazama Faheemah ce zata samu...




*FAHEEMAH*
"Ummie dan Allah idan kin haifa min baby zaki saka masa suna FU'AD"
tafada cikin shagwaba da yarinta.

murmushi ummi tayi kana tace "Faheemah a Ina kika ji sunan nan?"

Murmushi daya bayyana milk color hakoran ta tayi kana tace "Da muka taho yanzu daga makaranta, Ina tsayen jikin wata mota ina jiran aunty jameela tazo mutafi shine naji murya wata yarinya tana cewa "please ya Fu'ad kaga mai agwaluma can ka siyamin" Faheemah'n ta fada tana kwaikwayon yanda yarinyan tayi, dariya ummie tayi kana tace "ke yanzu banda shirmenki daga jin suna shikenan kice asawa baby?"

"Allah ummie yana da kyau, kuma yana kirki, ya siyawa kanwarsa agwaluma kinga sai suyi kama da baby mun a halayya"

" kinga ni tashi kiyi shirin islamiyya" cewar ummi

"dan Allah ummi kinji" tafada tana bubbuga kafa irin na shagwaba, tasan faheemah bazata barta ta huta idan ba wayo ta mata ba, "shikenan na yarda zan fadawa abbuhnki ya duba ma'anar sunan" murna faheemah ta kama yi , Murmushi ummie tana jin kaunar yartata...



*Bayan wata biyar*

ummie ce zaune da katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe, faheemah na mata tausa saboda kafafunta dasuka kumbura.

"Faheeta!"



"na'am ummiena"


"inaso kiyi hakuri da duk yanda rayuwa zata zo miki, kada kiyi wasa da sallah, duk sanda kika kai ga shiga damuwa kiyi karatun alkur'ani. Sannan kibi umarnin duk abinda maminku zata ce miki matukar bai tsaba addininki ba, kada ki raina jameela ita din gaba take dake, kinji ko?"


"Toh ummie" ta amsa a hankali.


Amma haka nan gabanta ke faduwa yau kwana uku kenan kullum sai mami ta mata nasiha, duk da karancin shekaratunta ta fahimci abinda ummienta kecewa saboda yarinya ce mai nutsuwa.


"ummie toh ba kina nan kullum ba, sai ki dinga fadamin abinda zan dinga yi kullum kinji" cewar faheemah murya asanyaye.

Murmushi ummie tayi kana tace "zanso kasancewa tare dake y'ata, amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi...


โ˜…โ˜…โ˜…

da safe ummie ta fara nakuda inda faheemah tasa kuka sai antafi da ita asibitin.


Bayan 3hrs ummie ta haifi da namiji murna sosai abbuh yayi haka ma faheemah an mata karin jini saboda ta zubar da jini da yawa.
"Dan Allah ki Kiran min yata da mijina" cewar ummie cikin sanyin murya


"ok" nurse ta ce kana ta kirasu tana fadin

"banda hayaniya please".

Bayan sun shigo, ummie tace "Faheeta baki zo kinga FU'AD din naki ba"

Abbuh ne ya musu kallon karin bayani, Murmushi ummie tayi kana tace "dan Allah kacikawa faheemah burinta tana matukar son sunan"

abbuh murmushi yayi yana mamakin wayon faheemah wai har tasan ta zabawa kaninta suna, daukan jaririn yayi hadi da rada masa sunan domin ya San sunan yana da ma'ana mai kyau.

kallon faheemah yayi hadi da cewa "Allah ya raya mana FU'AD"



Murna sosai faheemah tayi, babu jimawa ummi ta fara tari sosai,Bayan wasu minutes tarin ya lafa, cikin galabaita tace "Faheeta ki kula da kaninki sosai kinji, sanna kiyiwa maminku biyayya ki kula da addininki, banda wasa da Sallah, ki kula da mutuncinki , naso kwarai naga mijin faheeta... sai tayi murmushi kana ta cigaba , na so na bashi amanarki da hannuna sai ,dai bana jin zanga wanna lokaci" ta karasa hawaye masu dumi na gangaromata,

"haleema me kike cewa haka ne? ba abinda zai same ki, har fu'ad sai kin aurar kinjiko? kin ga faheemah na kuka" cewar abbuh a rikice domin maganarta ta matukar taba shi.

"zo nan faheeta"

da gudu ta fada jikin ummie tana kankameta hadi da fashewa da kuka duk da karancin shekaratun, amma tana jin kamar ummie tafiya zatayi ta barta, tafiyar da ba'a dawowa. "Inasonki ummiena dan Allah karki barni kinji?"

"nima inasonki yar albarka, kimin alkawarin zakiyi dukkanin abinda nace kiyi"

" zanyi ummiena namiki alkawari"

" Shukran ,ya binti (nagode diyata)"

cewar ummie saboda tasan faheemah na matukar so tayi mata magana ta labarci a wasu lokutan, ta kuwa yi dariya tana runguman ummie.

"Alhaji maminsu bata zo ba?"

Kai kawai ya gyada mata, saboda duk maganganun ta ya Sanyaya masa jiki.

Murmushi ummie tayi cikin karfin hali ta ce "kace Ina gaisheta, sanna ga amanar su faheemah ta kulamin dasu".



Shak'uwa mai karfi hadi da salati ummie tafara wanda ya daga hankalinsu, da gudu ya fice domin kiran doctor...


Cikin kwarewa doctor ya shiga duba ummie har ma da baby ya tabbatar wa abbuh da cewar rai yayi halinsa.
( kullun nafseen za'ikatul maut. Allah ya jikan wandanda suka riga mu gidan gaskiya, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kalmar shahada) suman tsaye abbuh yayi, domin cikin mintuna kalilan ace sun mutu? jiyayi maganar kamar saukar aradu , jiyayi kamar karya doctor ki yi, rufesu doctor yayi hadi da yiwa abbuh kalamai masu kwantar da hankali, ganin doctor ya rufe ummie da baby ne yasa faheemah fuskantar abinda yafaru domin tana gani a TV , sai idan ya mutu ne ake rufesa, ihu ta saki hadi da yaye rufin da aka masu tana jijjiga su tana kuka kamar zata shide, janye ta abbuh yayi cikin karfin hali, kana ya daga waya da kyar yafara sanarwa yan'uwa da abokanan arxiki.

Bayan sun koma gida abbuh da kansa yayi mata wanki ita da baby aka sallacesu kana aka tafi kaisu gidan su na gaskiya, ganin haka Faheemah ta fasa kara kana ta suma.


Mummyn zaynab ( kamar yadda faheemah ke kiranta) data kasance kanwar ummie ita tayi karfin halin yayyafa mata ruwa.... hakika mutuwan ummie ta daki mutane dayawa kasancewarta mutuniyar kirki, mami ma ba laifi taji mutuwar za'ace.



Daga wanda ranar Faheemah ta dawo shiru shiru, wanda hakan ya kara taba zuciyar mutane musamman abbuhnta,wani soyaaya mai matukar zafi yake mata.


*Bayan kwana arba'in*


yan'uwan ummie suka ce zasu tafi da faheemah, abbuh yaki, saboda yace itace zata dinga debe masa kewar haleema saboda suna matukar kama, basu ja dashi ba saboda abbuh'n ya matukar basu tausayi.....


๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH ๐Ÿ’”



_by NoorEemaan_ ๐Ÿ“šโœ๏ธ



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



My dear sisters, think well before you start dating him. Going to the date is okay, but before marriage never go to bed. Don't allow love to make u blind &end up staying in ur father's house with on unnecessary pregnancy.


7-8

(Not edited)



Haka RAYUWAR FAHEEMAH ya kasance cikin kaidaici magana inba dole ba batayi hakan yasa abbuh Kara jin tausayinta hadi da kaunarta.


โ˜…โ˜…โ˜…

*Bayan shekara daya*


hajja Hindu ce zaune tare da mami suna hira, "kawata daga wanna lokacin ban kuma jinki ba, gashi wayarki bata shiga cewar mami"

Hmmm! Kedai bari wallahi bama kasar munje Cairo, yata ce ba lafiya tana eye problem amma alhamdulillah tasamu sauki sosai."

" Allah sarki... cewar mami kana tace kawata Ina cikin damuwa"

"damuwar

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment