Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakewa fadima tana sane? Lallai ya dade yana zaluntar wannan baiwar Allah da yayanta, yau ta fada masa abunda bai taba tunani ba kuma shi kansa baisan hujjarsa ta nuna banbanci tsakanin yayansa da yayan dan uwansa Al amin ba. Lallai mai haquri bai iya fushi ba yau fadima ta zame musu horo, yasan tabbas abunda ta fada gaskiyace tsantsan duk yayansa babu mai masa biyayyar da Mimi keyi masa kuma babu wacce yayiwa auren wulaqanci irinta. Kuma wlh baisan abunda yasa yakewa Mimi haka ba, kuma yasan da Anty ko Umma yakewa yayansu abunda yakewa Mimi wlh da sai anyi yaqin duniya na uku. Muryarsa a tausashe yace da mama dake shirin fita daga parlourn "ban baki izinin fita daga gidannan ba daga ke har maryam" Umma da Anty suka kalleshi jin abunda yace suka jinjina kai. Domin sun dauka zai saki fadima ne nan take, da daya daga cikinsu ce da tuni ya sender ta gida.



Mama na fitowa daga dakin Baffa ta tsugunar da Mimi a bakin fanfo da nufin wanke mata jinin daya bata jikinta. Jafar da ya gamajin abunda ke wakana yayi saurin xuwa kitchen ya dakko mata ruwa a freezer ya miqa mata, ta karba ta wankewa Mimi fuska dashi. Nan take habon ya tsaya, taja hannun Mimi suka shige dakinta.


Jafar ya furta "jarumar uwa" ta jure abubuwa da yawa akan yayanta sannan lokaci daya ta kwatarwa Mimi yancinta. Ya dunga farin cikin jin Mimi ta gama iddah yace "in shaa Allah maryam matata ce"



Har magruba tayi mama bata fito ta dora girkin dare ba duk kuwa da cewa ita ke da girkin. Anty ta samu Baffa har daki yayi tagumi tanayi masa mitar cewa, mama bata dora girki ba mai zasu bawa yara suci? Ya dago ya kalleta yace "ku masu yaya bakuje kun girka kun basu ba sai ita me ya guda daya? Saboda haka karku dameni" Anty ta ruqe haba cikin ranta na jinjina soyayyar fadima a gurin Baffa, wato duk abunda tayi batai laifi ba kenan? Har marin da tayi mata 🀣. Ala tilas taje ta dora jellof din taliya dan lokaci ya qure kuma itace me qananan yaya.


Bayan ta gama ta hana kowa sai Baffa kawai ta xubawa ta kaima masa daki, shi kuma ya tambayeta da cewa kin kaiwa fadima? Ta harzuqa tace "aini bata shanye ni ba kamar yadda ta shanyeka ba, saboda haka ban kai mata ba dan ba xamanta nake ba. Ana cikin hakan Umma ta shigo tana tambayar Anty ina nata abincin? Tace nima dafawa nayi ni da yayana kema kije ki dafa dan ba baiwarku bace ni. Umma tace dakata karkiyimun fitsara inba haka ba yanxu in wanka miki mari dan naga sai anmareki kike samun nutsuwa πŸ˜‚. Anty da jin haka ta harzuqo suka fara cacar baki ita da Umma. Baffa ya katsesu da cewa ko suyi shiru su bashi guri ko kuma kowacce ta tafi gidansu. Anty ta cije lebe da cewa ai dole kace mu tafi gida, ita wacce ta qare maka zagi daxu ai ta kwana lfy saboda ta iya bun malamai.


Daya fita sallar isha ya biya ya siyowa mama da Mimi qatuwar kaza da fura roba biyu, jin cewa ba a basu abinci ba. (lallai mama ta motsa kwanji πŸ˜„) ya shigo Anty na alwala a tsakar gida kuma taga ledar daya shiga da ita dakin mama. Har ta miqe xata bishi sai ta tuna marin da tasha daxu dan haka ta koma ta xauna.


Yasameta xauna akan kujera ita da Dady suna kallon mbc 3 Mimi kuma tana kujera zaman mutum daya da digital casbaha a hannunta tana dannawa. Baice musu komaiba sai ajiye ledar da yayi kan qafar mama ya fita.


Dimin da taji shiya tabbatar mata abinci ya kawo musu, kuma dama shiri take ta tashi ta samar musu abunda xasuci. Dan yau jin ranta take sawai, abunda yake ranta shekara da shekaru yau ta amayar dashi. Dan haka ta dakko musu faranti da cups sukaci kazar suka sha fura suka qulle dakinsu suka kwanta, daga ita har Mimi basu garka ba sai asuba sun sami bacci me nauyi. (dole tunda anraba xuciya da damuwa)


Mrs
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 3⃣3⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Baffa kwana yayi yana tunani, haqiqa yayi kuskure yayiwa fadima abubuwa da yawa kuma babu wanda ya taba fada masa yayi ba daidaiba. Tabbas yaci amanar Al amin, yayansa kwaya biyu yakasa hadawa cikin nasa yayan ya rike. Kuma dole su Faty sunada gado a dukiyarsa domin tunda Al amin ya mutu ya tattara abunda yabari ya riqe, ko mama bai sallama ya bata tumunin takaba. Su bai basu dukiyarsu sun mora ba su baiyi masa da tasa ba. Dole zaisan abunyi akan dukiyarsu, ko bebawa su Faty tasu ba dole zai sallami mama da tumuninta.



Ta bangaren Mimi kuwa, baisan dalilin tsanar da yayi mata ba. Amma yasan akwai tagomashin matansa wadanda Kullum cikin kawo masa sukar Mimi suke. In yayi kallo xuwa hallayyar yarinya sai yaga yarinyace sassanya wacce ko acikin gida ake hira da wahala kaji harshenta, sai dai in anyi abun dariya tayi. Gata da kirki da qarfin xuciya, duk da bata cika lfy ba Kullum xaka sameta cikin aiki ko a tsakar gida ko a dakin uwarta. Bata da qashin cewar bazatai aiki ba saboda akwai yan aiki a gidan kamar yacce yayansa keyi. In kuma yanason ai masa abu misalin gyaran daki ko wani aiki to Mimi yake sakawa domin tana tsayawa ta yishi babu hainci wanda ko matansa basu iya yimasa shi tsaf kamar nata.


Dan haka ya fuskanci xuga ce jigon tsanar da yakewa Mimi, sai kuma issue din rashin aurenta da wuri wanda ya dauki hakan iya shege. Dole ya kawo canji domin yanason fadima kuma bazai iya rabuwa da itaba, yanxu gashi tana shirin rabuwa dashi saboda Mimi. Nan take yaji rabin tsanar da yakewa Mimi ta tafi. Afili ya furta Fadima nagode da kika karantar dani kuskurena da wuri tunkan in mutu Allah ya kamani da haqqin xumunta dana marayu. Kuma daga yau xan sakarwa yarki mara tayi irin rayuwar da take so.


Lokacin da yafito domin tafiya masallacin asuba ya kirawo masu aikin gidan yace su karbi aikinsu yau sannan ya fita.


Mimi kuwa bayan ta iddar da sallar asuba ta gaida mama, mama tace mata kije kiyi registration din tafiya service din yau. Mimi tayi rau rau tace " mama ai anrufe sun kusama tafiya camp domin har call up dinsu ta fito" mama tace to kiyi haquri haka Allah ya shirya kaje wata shekarar"
Anan kitchen din cikin parlour suka hada break fast sukaci, domin mama ta quduri aniyar kwatar yanci. Tunda ya hanata tafiya ai sai tayi yajin a dakinta.


Badaru yadda suka kwana da Nafee jiya yauma haka suka kwana, domin shima ya bar mata abunta yace ta jiqa tasha. Aransa kuwa cewa yake ni da xan kwana da maryam yau dan anhanani wannan ruwan daurayar ai ba wani abu bane.



Wajen qarfe goman safe yaje gidansu, dake asabar ce kuma basa fita kasuwa weekend da wuri duk ya samesu a parlour. Har Badamasi da yazo weekend.


Ya zauna ya kwashi gaisuwa gurin iyayensa, ya juya suka gaisa da Badamasi sama sama domin Badamasin yanxu yake samun lbrin saki da kuma maida maryam da Badaru yayi sannan da zancen auran da yayi. Dan haka yaji yayi mugun tsanar Badaru sabida maryam.


Badaru ya kalli Abbansu yace "Abba inaga da yamma xanje in dauko maryam din, saboda inason inkaita store tayi shoping din kayan abincinta da kanta inyaso sai mu wuce gida daga can"


Abban yace to babu laifi, bari na fadawa Alh Buharin saboda karkaje bata kimtsa ba" Umma dake gefe tana murmushi aranta taji dadi ga dukkan alamu Badaru ya gane mahimmancin maryam, dan haka tace "Alh ai da ya kira maryam din da kansa yace ta shirya da wuri zaizo da yamma"


Badaru ya sunkuyar da kai cikin kunyar abunda xai fada yace "ai bani da lambarta" babu wanda yace masa komai sai Badamasi dake watsa masa harara kamar ya tashi ya dakeshi.


Abba ya ciro wayarsa yace bari na fada masa da kaina. Lokacin da kiran Abba ya shigo Baffa na xaune yana karyawa Umma na gefensa ga dukkan alamu itace tayi girkin tunda mama tayi bore.


Ya daga suka gaisa, har yanxu jikin Baffa a sanyaye yake. Abba ya fada masa buqatar Badaru. Baffa yace "ai Alh inaga sai dai mu haqura domin yarinyar har ta gama iddah, kaga babu maganar kome kenan?"


Abba dajin abunda Baffa ke fada yasa wayar a hands free domin Badaru yaji abunda Baffa yace. Abba ya maimaita abunda Baffa yace "ta gama idda?" Baffa yace "eh"


Badaru ya dafe qirji yace "to cikin jikinta fa? Xubarwa tai?" Baffa da yaji abunda Badaru yace saboda hands free din da aka saka yace "ita dai tace babu ciki kuma iddarta ta cuka tun kwana 6 baya"


Abba yayi saurin cewa "to ai abun bai baci ba har yanxu, tunda yayi nufin maidata sai mu kawo sadaki in anjima a maida auren" Badaru yayi saurin gyada kai cikin gamsuwa da abunda Abba yace"


Sai dai muryar Baffa ta katse masa hanxari inda yake cewa "Alh sai dai muyi haquri inaga iyakacin xaman da Allah ya rubuta musu kenan, domin nima na kawo batun maida auren maryam ta nuna bata da raayin kuma xama dashi dana takura sai anmaida auren adalilin hakan nima xaman lfyar gidana ya tabu, domin uwarta tace baza a kuma yiwa yarta auren dole ba har tana barazanar dauke yarta su barmun gidana. Ni kuma inason matata kaga garin gyara kuskuren Badaru aurena zai mutu, gara kawai a haqura."



Abba ya kashe wayar cike da jin haushin Baffa, yana mitar kamar Buhari ya zauna mace na juya shi? To kada Allah ya sa maryam din ta dawo, metafi Badarun ai Badaru ba illah ce dashi ba babu inda xaije neman aure ba a bashi ba (kuji san kai?)


Badaru tunda ya gama jin abunda Baffa ya fada gabansa ya yake ya fadi, qirjinsa ya dunga bugawa sai yanxu ya tabbatar ya tafka kuskure. Tabbas yasan maryam bata sansa, wlh da yasan haka xata kasance da bai saketa ba. Ta xubar masa da cikin da yake ganin shine tsanin da xai dunga hadasu. Umma kuwa hawaye takeyi jin maryam ta bar xuriar ta, tasan Badaru yayi rashi.


Badamasi kuwa dake gefe fuskarsa a washe sai murmushi yake. Ya dunga godewa Allah a xuciyarsa, yace lokacin aurena yayi, maryam ta dawo. Jin fadan abba yaqi qarewa kuma Abban baya blaming kowa sai Mimi, shiyasa ya matsa gaban Abban, baice komai ba sai wayarsa da ya ciro ya kunna recording din da ya tabayi wanda Badaru ke tsagin Mimi da korarta daga gidansa. Yace Abba ku saurari wannan"



Sukayi tsit har Badaru suna sauraran recording din harya qare sannan Badamasi ya dora musu da sauran abunda yagani na zamantakewar auren da kai Mimi asibiti da yayi da kuma abunda yakeji lbr gurin abokan Badaru.



Jikinsu yayi mugun sanyi, Umma kuwa kuka take tana kallon Badaru a razane. Ta kalli Abba cikin kuka tace "Alh kaji abunda nake fada maka ko? Kake goyon bayansa, wlh nasan sharri yayiwa yarinyar nan, ai dole tace baxata xauna dashi ba saboda ya azabtar da ita, inma cikin ne ai baqin cikinka ma ya isa ya xubar da cikin. Kuma wlh indai nadama ce baka fara ba, ka cuceni ina qaunar yarinyar nan ka rabani da ita" ta qara fashewa da kuka. Abba ma ya kalleshi yace "baka cuci maryam ba, ba kuma ka cuceni ba kanka ka cuta. Na yarda da kai kasa ina jin haushin yar mutane ashe kaine babban dan iska, sabida haka kajira sakamako wlh sai Allah ya saka mata"



Badamasi ya matsa kusa da qafar Umma ya riqo hannunta yace "Umma share wahayenki, baki rabu da maryam ba, maryam xata dawo cikin xuriar ki kuma a matsayin surukarki, domin xan auro maryam. Idon kowa a gurin ya dawo kansa. Yaci gaba da cewa tun farko ni naga maryam, ni na fara sonta, ni nafara yi mata magana. Ina shirin inje innemi soyayyarta Badaru yazowa Abba da maganar aurenta ganin haka yasa na haqura, amma wlh da nasan Badaru haka zai maltreating maryam wlh bazan haqura in bar masa ba. Saboda haka Umma ban taba neman abu a wajenku ba yanxu nazo da alfarmar neman goyon bayanku akan neman auren maryam, ba haram bane dan Allah ku kauda kai a magoar mutane ku goyamun baya."


Umma ta share wahayen farin ciki, ta shafa fuskar Badamasi tace "na baka goyon baya 100%, nasan bazaka wulaqanta maryam yanda Badaru yayiba Allah ya sa rabonka ce" ya juya gurin Abba yace "Abbana inkace in haqura xan haqura" Abba ya kalli Badamasi a nutse yace " na baka goyon baya likita, indai har kun daidaita kanku da kaina xanje gurin Alh Buhari a karo na biyu in nai mar maka aurenta" ya dunga godia yana dariya ji yake indai Mimi ta amince nan da 2 wks xa ayi komai a gama. Yau yana da daurin auren abokinsa a Danbatta amma gobe in shaa Allah zaije su gana.



Badaru da tunda Badamasi ya fara magana yake kallonshi har ya gama, ya tashi idanunsa jajur da tsabar kishi ya tari gaban Badamasi cikin sigar rigima yace "oh dama ashe san maryam kake? Shiyasa ka hure mata kunne ta ciremun ciki ta gujemun sannan ka nado sirrinmu ka kawo ko? To wlh baka isa ka auri maryam ba indai ina numfashi, kai ko kunya bakaji ka auri tsohuwar matata? Ban taba neman abu na rasa ba, na auri maryam da farko kuma yanxu ma xan kuma aurenta domin wlh saina kasa ka, ka rubuta ka ajiye, inkuma ban aureta wlh sai dai ayi biyu babu kowa ya rasa."


Badamasi yaja da baya ya kalleshi yana dariya yace "ka saba yiwa kanka kirarin duk abunda ka nema kana samu, amma inkasamu baka iya alkinta abun, kaga kodan haka Allah xai iya jarrabarka, saboda haka maryam dai yanxu rabonace in shaa Allah gara kaje ka lallaba kucakar matarka ku zauna lfy. Kuma ni bazan fada da kai ba domin yau cikin farin ciki nake dan haka kaje ka nemi irinka looser kuyi "


Badaru yakai masa duka Badamasi ya tare tare da cewa kasan in dambe xamuyi wlh karyaka xanyi ka wani tara teba sai kace me ciki. Abba ya daka musu tsawa tare da ja musu warning. Kowanne ya fita yana hararar dan uwansa. Umma tace "Alh baraka fa xata bullo idan bamu tashi tsaye ba"


Abba yayi shirin fita kasuwa ya leqa dakin Badamasi yace "Bani wayarka ka saitamun gurin maganar nan, gara insami Alh Buhari in wanke yarinyarnan a gurinsa." Badamasi ya bashi wayar tare da bude masa recording din, yana xuwa play kawai xai danna.



Baffa naganin Alh Inuwa a shagonsa ya hade fuska, don a xatonsa xuwa yayi ya qara neman alfarmar mayar da Mimi. Amma sabanin haka sai yaji yana bashi haquri tare da neman itama Mimi abata haqurin, kana ya budewa Baffa recording din ya saurara.


Baffa yayi matuqar tsorata da lamarin Badaru, ya kalli Alh inuwa yace " kace dan iska ka kawomun cikin manyan kaya ni kuma banyi bincike ba na dauki salihar mace na bashi" Alh inuwa yace "wlh Alh bansan abunda Badaru ya aikata ba kenan, shiyasa na kawo maka abunda yayi kaji. Amma dan Allah kayi haquri kuma ka bawa maryama haquri babu hannuna a abunda aka aikata mata kuma wlh da nasan haka zaiyi da ban nema mishi auranta ba" Baffa yace " shikenan nagode da sanar dani da kayi shi kuma ya je dan kansa ya cuci marainiyar Allah"


Baffa yayi sakato yana tunani, lallai ya tafka kuskure a baya. Ya dauki ya yabawa dan iska yana zaginta da goranta mata, amma kuma duk abunda Badaru yayi bashi da laifi, shine babban mai lefi da bai riqe su da daraja ba kuma ya nuna maryam din ba wata bace.


Tausayin Mimi da soyayyarta ta dirar masa nan take, dole Mimi tace bazata koma gidan Badaru ba saboda ya zalunceta sannan ya biyota da sharri shi kuma ba bincike yahau ya xauna. Jin soyayyar Mimi yake har cikin bargonsa kuma yaji yana kunyar hada ido da ita da uwarta.



Badaru na zuwa gida ya samu Nafee a parlour tana kallo, ya kalli parlour komai kaca kaca ya kalleta da yake a kusa yake neman masifa yake sai yace "ke haka ya dace kibar guri ki xauna kina kallo dake ke jaka ce?"


Ta kalleshi sheqeqe tayi dariya tace " jakai dai, ni da kai in ban gyara ba kai baka da hannun gyarawa?" kafin ta ida fada ya kifa mata mari.



Batai wata wata ba ta dakko plate din da ta gama cin indomie yanxu ta jefa masa tana huci, sannan ta dora da cewa "ga dukkan alamu ka saba ganin tsohonka na jibgar gyatumarka shine kazo xaga gwada a kaina, to wlh duk randa ka qara dukana wlh saina sake maka kaciya 😳"



Ya tsorata da mutuqa da maganar Nafee, bece uffan ba ya shige bedroom dinsa, ya rasa abunda yake masa dadi. Shi yanxu yasan duk wanda ya fadawa abunda Nafee ke masa dariya zaiyi saboda yacce ya daukaki Nafee. Ya dunga juyi akan gado ya kasa bacci, har akai sallar laasar bai fito ba ga yunwa na addabarsa kuma yasan Nafee yau bazata bashi abinci ba. Ya tashi yayi wanka yayi sallah, ya zabo kayansa na qure adaka yasa. Gurin maryam xaije ya bata haquri ya nemi yafiyarta, yasanta da sauqin kai xata haqura su koma aurensu.


Ya samu Nafee zaune ta cokala dauri ture kaga tsiya tana sanaar (kallo), ya tsaya domin yayi mata magana, ta dauki remote ta qure volume alama batason jin abunda xaice, dan haka ya fice.



Ya dade a qofar gidan Baffa babu dan aike kuma bashi da no Mimi. Mimi ta fito domin zuwa gurin fauxa, tana sawo kai waje idonta cikin na Badaru gabanta ya yanke ya fadi ta diririce, ta juya da nufin komawa gida yayi wuf ya damqe hannunta yajata cikin sit room din dake soron farko.



Cikani, baka da hankaline xaka riqe mani hannu? "ta fada cikin fita hayyaci. Ya sassauta riqon da yayi mata, amma still yana riqe da ita karta gudu ya fara magana murya a kwance " maryam dan Allah kiyi haquri nasan na bata miki naci zarafinki na hadaki da iyayenki na tauye haqqinki na kuma toxarta ki. Amma wlh nagane kuskurena abaya na aureki ne dan shaawa amma xaman da mukai da ke nagane kyawawan halayenki da son addininki hakan ya jawo miki soyayya a gurina." Mimi tayi sakato tana kallonsa wai dama Badaru ya iya magana a hankali? Kuma dama yasan duk abunda yake ba dai dai yake ba? Tambayar da takewa kanta kenan.


A bangare guda kuma Baffa dake azumi (azumin kaffarar rantsuwar da yayi ta Mimi saita koma gidan Badaru, ya fara yau) ya dawo gida da wuri domin ya kawo salad din da yakeso a kwada masa yayi buda baki dashi. Yana xuwa soro aci burki dan jin maganganun dake fitowa daga sitroom. Da farko bai gane mai maganar ba, amma jin an ambaci sunan maryam ya gane me maganar da inda maganar ta dosa. A fili yace lallai wannan yaron bashi da kunya bari inje inyi masa tsakani da yata.



Sai dai muryar Badaru ta katse masa hanxari inda yaci gaba da cewa "maryam ki tunano rayuwar auratayyarmu me dadi πŸ™ˆ, ke bakya tunawa? Wlh kullum cikin kewarki nake da mafarkinki, ki dawo muje mu zauna duk abunda kikeso zan miki duk yan uwanki na gidan miji ke kadaice kika rage, kin wuce xaman gida ki dawo dakinki shine rufin asirinki"




Ta katseshi da cewa "xaman gidanmu yafiyemun zaman gidanka, kuma lokacin da sakeni ka wurgoni kofar gida baka duba cewa na wuce xaman gida ba sai yanxu? Rayuwar auratayya kuma da kake fada kaika santa har take maka dadi, abunda kawai zan iya dorarwa aciki shine: fyaden da kakemun duk daren duniya. Abubuwan kuma da kayimun a duk xamanmu na barka da mahaliccinka shi zaimun sakayya." tana kaiwa nan ta fusge hannunta ta kifawa Badaru mari, kafin ya gama mamaki ta kifa masa wani 😳.



Ta dora da cewa " yau alqawari ya cika, lokacin daka mareni a gidanka na fada maka cewa wlh saina rama gashi kuma na rama din. Zagin ubana kuma da kayi kace inje in haqoshi a kabari, bazan rama ba, domin nasan darajar iyayena sannan nasan duk daren dadewa naka uban xaije inda nawa yaje. Gida kuma basai nace karka kuma xuwa ba, saboda bata dalilina ka fara xuwa gidanba."



Baffa dake sauraransu yayi murmushi cikin jin dadin abunda Mimi tayi yace "yar halak kenan, tayi alqawari ta kuma cika maryam jinin Al amin ce domin ga halinsa nan a jikinta.

Ta fito ta koma gida memakon gidansu fauxa da tayi niyyar xuwa, shiyasa bata kula da Baffa ba dake tsaye a qofar fita. Badaru ya gama mamaki ya jawo qafafuwansa jiki babu kwari yayi hanyar waje, yaci karo da Baffa. Baffa ya nunashi da yatsa yace "karka kuma xuwarmun gida, in kuma ka kuma xuwa xan hadaka da hukuma" yana fadar haka ya shige gida.



Washe gari lahadi da yammaci aka aiko kiran Mimi, har taqi fita mama tace taje in Badaru ne taxo ta fada mata. Sai dai me tana fita taga Badamasi a tsaye. Tana ganin mutuncinsa dan haka tai masa iso sit room.


Ya xauna suka gaisa a mutunce ta tambayeshi mutan gida da gurin aikinsa. Yayi farin ciki ganin maryam din ta fara dawowa hayyacinta ba kamar lokacin da tana gidan Badaru ba, ya dunga hasketa da murmushi yana kuma jinta a xuciyarsa. Yayi mata jajan mutuwar aurenta, tace ba komai iyakacin xaman da Allah ya nufa kenan.


Ya karanto mata abunda ke cikin xuciyarsa, ta dunga kallonsa a kidime ba tace komai ba ta miqe da nufi fita. Yayi saurin shan gabanta yace "maryam wlh babu inda xaki sai kin fadamun matsayina a xuciyarki, inbaki manta ba nina fara sonki Badaru furtawa ya rigani indai ba so kike inyi hauka a kanki ba ki amshi soyayyta" itadai babu baka sai kunne, domin kanta ya daure da yawa.


Da yaga taqi magana saiya kamota ya sata a bango yayi mata rumfa da qirjinsa yasa hannu ya katangeta ta inda duk motsin da tayi saita taba jikinsa. Yakai fuskarsa dab da tata ya fara magana "Mimi ki laluba xuciyarki bazaki rasa soyayyata aciki ba, ba halinmu daya da Badaru ba soyayyar da nake miki bazata bari in cutar dake ba, xan kula dake xan baki yancinki, xakiyi duk abunda kikeso, bazan tauyeki ba irin rayuwar da kike mafarki xakiyi. Maryam fargabar me kikeyi? Bazan akiyeki kusa ba balle a dunga yi miki

Please Login or Register in order to submit comment