Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dukkan alamu da Badaru yake. Can yaji yana cewa "babu batun ragonta, dan mace na da ciki bazatai ciwo ba sai ace tacika ragonta? Nidai yanxu xan kaita asibiti ya kashe wayar"



"Tashi ki shirya muje asibiti, " ya bawa maryam umarni. Sannan ya zarce da mitar cewa kasan lalurar ciki ne? Inda kai Allah ya dorawa wayasan kwakwazon da zakai? Kaiwa yar mutane ciki ka tafi kabarta da wahala. Itadai ta yunqura dakyar ta miqe tayi hanyar toilet tana godewa Allah da ya kawo me temakonta.



Cikin qarfin xuciya tai brush da wanka suka tafi. Ganin yadau hanyar yan kaba yasa tace "Aminu kano nake ganin likita ai" ya waiwayo ya dubeta yace " rana tayi shiyasa xan kaiki asibitin wani abokina da mukai karatu tare, amma shi likitan mata ne" tace ai a Aminu kano akwai yayata dake aiki acan, inka kaini ko likitan yamma ne sai nagani"



Yana kallon titi yace "sry bari na kaiki private din xaki fi samun kulawa inyaso har awo da haihuwa sai kije can. Yasan aikinsa sosai" ta sunkuyar da kai cikin kunya jin yayi maganar cikin jikinta. Ya qura mata ido cikin burgewa dan yanason mace me kunya. Aransa yana aiyana rashin imanin Badaru dan kowa yaga maryam yasan ba a dadi take ba kuma ga ciki na wahalar da ita.


Sun tadda layi kasancewar safiya ce. Badamasi yayi masa waya da kansa ya fito ya shiga dasu bayan ya nemi alfarmar na kan layi.



Yana dubata suna dan taba hirar yaushe gamo da Badamasi, ya kalleta yace maryam alamu sun nuna kina da qarancin jini a jikin ki, shiyasa kika dashe kikai haske. Badamasi yace " ba ciki bane ya kawo hasken?" Dr yace "bazan iya cewa da ciki ba ko babu, amma dai bari nayiwa sister sarah magana ta tafi da ita can nursing station tayi mata checking sosai akan hakan"


Ya kirata a waya nan da nan sai gata yace "kuje da wannan yayi mata bayani" Mimi ta bita yayin da Badamasi ya koma reception dan bawa ragowar marasa lfyar damar ganin likita.



Acan gurin nursing din sun dubata sosai taji wacce ta dubata na fadawa dayar cewa, tana buqatar aimata wankin ciki. Lamarin da yasa Mimi tsorata, domin tasha ji ana fadar wahalar wankin ciki. Dan haka ko takan mayafinta da jakar bata biba ta ranta ana kare πŸƒπŸ½β€β™€.


Badamasi na zaune yaga fitowarta daga dakin a harkitse, tana tafiya tana waiwayen bayanta taga ko nurse din ta biyo ta. Ya taho gurinta da sauri cikin rashin sani suka gabxa karo. Tai qasa xata fadi yayi saurin tarota jikinsa, jinta jikin mutum yasa ta qanqameshi tana cewa "Badaru kaji wai wankin ciki zasuyimun, kuma da xafi sannan xasu wankemun Baby dan Allah karka bari suyimun." shidai Badamasi tunda yaji maryam ajikinsa ya tafi wata duniyar, ya xaci irin mafarkan da yasa ba yine akanta dan haka ya rungumeta jikinsa tsam yana sauke ajiyar xuciya. Akayi sa a itama ta xaci mijintane ta kwanta lub.


Nurse din data biyo Mimi da jakarta da mayafi ce ta dawo dasu hayyacinsu. "oga gashi ta gudo dakaji ance xa ai mata wankin ciki" yai saurin rabata da jikinsa daya farga ba mafarki yake ba, a xuciyarsa ya dunga cewa astagfirullah Badaru kai ka jawomun da ka kula da matarka da ban kawota asibiti ba balle harna rumgumeta. Itama Mimi sai yanxu ta dawo hayyacinta, ta dunga jero neman gafarar Allah.



Suka koma office din Dr, nurse din tayi masa bayanin matsalar Mimi da kuma qin yadda ai mata wankin cikin. Ala dole ya rubuta mata maganin ciwon mara dana qarin jini. Badamasi ya tambayeshi akan cikin. Yace "yanxu kam bazan iya cewa da ciki ba ko babu tunda akwai lalura da yawa a tare da ita, sai dai ko in kun kuma dawowa ayi scanning. Ga maganin ta dage da cin abinci da shansu kuma basu da qarfi koda da cikin baxasu illatashi ba" sukai sallama suka tafi.



A hanya suna tafiya tace masa "dan Allah karka maidani gidannan na kwana ni kadai jiya nasha wahala, bansan abunda hali xaiyi ba yau." ya dubeta yace "to Maryam ai bani da ikon kaiki wani gurin bada ixinin mijinki ba, amma bari in masa magana saboda akwai hatsari abari ki kwana ke kadai" ya dakko waya ya kirashi tanaji yana masa bayani, can ya miqo mata wayar yana cewa gata. Tai sallama be amsa ba bare ya saurari gaisuwar da take masa ya hau masifa " kince bazaki kwana gidanki ba ko? Uwar langwai to kitafi duk inda xaki tunda kinsa anmun titsiye inna dawo kya dawo." yana kaiwa nan ya kashe wayar, itama ta kashe ta miqa masa tare da cewa kaini yahya gusau gidan yaya Faty.



Koda suka isa gidan sun samu ya Ahmad na nan, dan haka koda yaya Faty ta fito domin temakamata su shiga ciki yaga bata lokaci ne dan haka ya dauketa cak yakaita har cikin parlourn. Badamasi ya dunga kallonsu cikin birgewa, domin sai ka xata Ahmad ne dan uwan Mimi ba Faty ba.


Badamasi ya dade a gidan suna hira, saboda family din sun burgeshi. Faty ta dunga jerawa Mimi sannu ta duba magungunan da aka bata. Tare sukayi dinner sannan tasha maganin kana Badamasi ya tafi.


Yau dadi takeji xata kwana gidan yaya Faty, har dare sunata hirarsu cikin nishadi sannan suka nemi makwanci, yaya Faty ta dunga mitar ramar da Mimi tayi amma koda mimin ta fada mata ciki ke wahalar da ita sai mitar ta koma murna. Suka raba dare suna hirarsu sannan sukai bacci.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣7⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Kwanaki uku da tayi gidan Faty yazo mata da wani irin canji, har mamakin nishadin da take ciki takeyi. Sai take ganin rayuwarsu kamar lokacin da suke gida kafin suyi aure. Suci abinci tare, bacci tare, sannan gashi ya Ahmad duk sanda xai shigo saiya shigo mata da abun kwadayi, yakance me ciki ba a rabata da kwadayi, sai kace shi xa a haifawa dan. Amma aduk sanda ta tuna xata koma gidan Badaru sai jikinta yayi mugun sanyi sannan gabanta yayi ta faduwa.


Rana ta biyar a gidan Faty wanda ya kama da satin Badaru daya a Lagos, da yammaci suna zaune ana hirar da aka saba anata dariya. Mimi zaune a gefen Faty akan kujera 3 sitter tanacin guava, yayin da ya Ahmad ke gefensu akan kujera 1 sitter yana basu lbr sai dariya suke.



Badamasi yayi sallama ya shigo, Mimi na ganinsa gabanta ya yanke ya fadi. Nan take nishadin da take ya qare kuma duk wanda ke parlourn ya lura da wannan canjin na Mimi. Ko Badamasi bai fada ba tasan Badaru ya dawo kuma xuwa yayi ya maida ita kamar yadda ya alqawaranta.


Suna gama gaisawa ya fada musu labarin dawowar Badaru tun safe, kuma yace yaxone ya maidata gidan. Ya Ahmad ya katseshi da cewa "shi maiyasa bazaizo ya dauki matarsa ba? Sati daya baka gari? Inka dawo ai iyalinka ya dace ka nema kaji lfyarsu, ko akuya ka bari da ciki sati daya inka dawo ai ka binciki lfyarta. Wannan abunda yakeyi sam babu tsari a cikinsa, na kuma gaji dab nake da indau mataki akai " ya qare maganar cikin bacin rai πŸ˜”. Badamasi ya bude baki da nufin kareshi ya Ahmad ya tsai dashi "karkace komai, nasan halinsa kuma shirun da akai masa baya yana nufin Mimi bata da gata bane, kawai muna kau da kaine saboda iyayenmu" Faty na gefe na share hawaye .



Sha tara ta arxiqi suka hada mata, kamar wacce xatai tafiyar shekara. Har Badamasi ya dunga jinjina soyayyarsu ga Mimi. Faty bata fito rako Mimi ba saboda kuka da take bataso tasa mimin kuka itama, sai ya Ahmad ne ya tsaya aka loda kayan a bayan motar sannan ya kawo kudi ya bawa Mimi, har anrufe motar ta fito da gundu ta fada jikin ya Ahmad tasa kuka ya kamo fuskarta ya share mata hawaye yace "maryam kici gaba da haquri Allah ya na tare dake, baxaki taba tabewa ba a rayuwarki" ya bude motar ya sakata suka tafi.




***** ***** ******

Bata canja xani ba rayuwar da suke a baya itace dai, gashinan abun babu tsari kamar a jahiliyya period.



Kimanin kwana 11 da dawowarsa daga Lagos kenan daren ranar suna kwance, ya hauro kanta yasa qarfi ya danneta. Kimanin sau uku kenan yana yin hakan, inya gama buqatarsa yaji bai gamsuba yayita zaginta yana ci mata mutunci.



Yanxun ma hakace ta kasance, ya shigeta da dukkan qarfin da Allah ya bashi. Taji xafi kwarai harta kwallah qara, yaja dogon tsaki yace "qarar me kikemun? Wai nufinki xafi kikaji? Abunda duk kin bude kin tale, innaxo shigarki kawai ji nake na rufta babu wata madatsa πŸ˜³πŸ™ˆ shine har xakice kinji xafi?"


Tai qasa da murya"wlh Badaru tun lokacin da ciwon sanyin nan ya samemu inkanayi ji nake kamar kana xubamun yaji daurewa kawai nakeyi, da kabari naje asibiti da tuni mun warke." cikin hargowa da daga murya yace "ya sameki dai, dan ni tuni na warke, ai nakawo miki magani kikaqi amfani dashi ke lallai sai na asibiti ko Baturiyya? To wlh baki isa ba dan mugunta kin hanani inji dadi dake? Wlh wlh whl yau ko xanyi sau dari sai naji dadi xan kyakeki ya rage naki"



Yana kaiwa nan ya farmata kota ina juyata yake yayi, tun tana jin xafi harta denaji. Numfashinta ya fara gazawa. Batasan iya lokacin da ya shafe yana durxarta ba, ita dai tasan yayi mugun dadewa yana abu daya. Sannan ya sauka ya koma gefe ga dukkan alamu gajiya yayi bawai biyan buqatar ya samu ba.



Kukansa ya dawo da ita hayyacinta, inda cikin kukan takaici yake cewa "maryam kin cuceni, kin xalunceni, ni zakiyiwa haka ko? Ni zaki hana jin dadi dake ko? Kimanin wata daya kenan Kullum cikin buqata nake kin kasa biyamun ita. Kije Allah ya isa ban yafe miki ba, in Allah ya yadda bazaki gama da duniya lfy ba. KE MARYAM ALLAH YA TSINE MIKI." 😳😳😳😳



Jin furucin Badaru na qarshe yasa tai xunbur ta miqe, tare da cewa "Badaru me yayi zafi haka??? 😳" ya bata amsa da cewa "ubanki ne yayi zafi" yana fadar haka ya fita daga bedroom din.



Wani irin yanayi ta shiga ita ba matacciya ba ita ba rayayya ba. Kukan ma ta kasa, tsinuwa daga mijin aurenta? Akan abunda bata da iko akai? Tab akwai matsala. Saboda da gajiyar dirxar da Badaru yayi mata batasan sanda bacci ya kwasheta ba. Sai ana kiran sallatu ta farka, qasanta wani irin xugi yake mata kamar ansa reza an ketata taje tai wanka tai sallah ta roqi Allah sauki da gaggawa kan halin da take ciki.


Sukuku ta yini saboda tsinuwar da Badaru yayi mata ta taba xuciyarta sosai, ta qudure a ranta inya kunna inji da dare ta samu chajin waya xataiwa ya Faty maganar infection din ta kawo mata Magani, domin wulaqancin ya isheta haka gara ta naimi magani ya dunga samun biyan buqata axauna lfy domin ita batasan tashin hankali (Allah sarki rayuwar ya mace, Kullum cikin sadaukarwa namiji take.) babu abunda ta iyaci ranar illa ruwan lipton da lemon tsami.



Ta idar da sallar laasar, tadan kwanta kan sallayar tana azkar, ta qudure aranta yau laraba intasamu dan aike xata bashi kudi yayi mata sadaka domin yau yini tayi gabanta na faduwa. Bazai wuce hudu da rabi ba 4:30 lokacin da taji dawowar Badaru, tayi mamaki kwarai dan bai cika dawowa haka ba sai inda muhimmin abu da xaiyi.



Ya wuce daki fuu sai gashi da tulin kayansa masu dauda. Ya fita tsakar gida, sai gashi ya dawo ya danqi gashin kanta ya fita da ita, ya nuna mata tulin kayan wankinsa yace "ga wanki nan kiyimun, tunda baki iya biyamun buqata ba kimun wanki, dan baxan dunga baki abinci a banxa ba" tai tsam sannan tace "to kayi haquri kaga nawa ma bayi nake amma in ya Faty ta aiko karbar nawa wankin in shaa Allah xan hada maka da naka."



Ya danqi wuyanta ya hadata da bango, sannan cikin huci da tsabar tsanar yace "ke kin isa insaki aiki kice baki ba? Wlh baki isa ba, na tsaneki wlh da inka kashe rai babu wani hukunci a kanka da kece mutum ta farko da xan fara kashewa, maryam ban taba tsanar wata halitta a duniya kamar ki ba. Saboda haka dole kimun wanki dan ubanki" ta fusge wuyanta tayi gefe ganin yana shirin kaita lahira, tana maida numfashi tace "wanki bazanyi ba kisa kuma bisimillah ka kasheni." cikin bacin rai take furta wadannan maganganun domin ranta yakai matuqar baci da xagin da Badaru kewa ubanta.



Kafin ta ankara ya tsinka mata mari ji kike kau! 😳 tayi baya cikin azama ya dora da cewa "lallai wuyanki ya isa yanka? Yauni kike maidawa magana? To dan ubanki...... "ta tari numfashinsa kafin ya qarasa. "karka kuma xagin ubana domin nasan darajarsa, kuma da yana raye wlh bazan auri wanda besan darajar iyaye kamar ka ba, maraicine ya jawomun"


Ya kuma dauketa da wani gigitaccen mari, "na xagi uban naki bayan xagima na dakeki dan haka kije ki haqoshi daga kabari yazo ya rama miki." ta dago idonta jajur " ka mareni? Wlh komai daren dadewa saina rama, wannan alqawarine na yiwa kaina."



Ya ja hannunta qiiiiii ya bude gidan ya turata waje ta fadi dabas. Sannan yace "ai basai andade ba kije yanxu ki tasoshi daga kabari kuxo ke dashi ku hadu ku dakeni, kije na sakeki kuma Allah ya isa tsakanina dake in shaa Allahu bazaki gama da duniya lfy ba."



Ya maida gidansa ya rufe, yabarta zaune babu takalmi babu mayafi. Kuma dai dai lokacin hankalin mutane ya fara dawowa kanta, aka zagayeta ana kallonta tai qasa da kanta taji duk ta muxanta. Ya qara bude gidan ya wullo mata hijabi da wayarta, jehowar da yayi tasa wayar taci screen. Ta miqe tasa hijabin qafarta babu takalmi gashi bai bari ta dakko kudi ba dan shiga Mota.




Har ta fara tafiya wata maqociyarta yar dattijuwa wacce yayanta ke shiga gidan Mimi ta biyota a baya ta tsai da ita, tace "maryam yanxu akaje aka sanar dani abunda ke faruwa, kiyi haquri indai baki cuceshi ba Allah saiya saka miki AURAN BAYA SADAKIN NA GABA." ta cire takalmin qafarta ta bawa Mimi tace saka ki tafi Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi, ta juya ta tafi tana kuka dan tana qaunar Mimi.



Cikin wani irin yanayi take tafiya, tafi kama da mahaukaciya sabon kamu sam ba kuka take ba, idonta da xuciyarta sun bushe qaraf. Jinta take ita ba matacciya ba ita ba rayayya ba, abun kamar almara aurenta ya mutu cikin wata biyar da kwana shida kacal da yin auren. Batasan mutuwar aure sam koda akan maqiyinta bare a gida irin nasu wanda bata taba ganin ko yaji anyi a gidanba. Ita kuma haka QADDARARTA take, andade ba ai aure ba, anyi ba a dade ba ya mutu. Tasan qalubalene a rayuwarta qatoto, wlh duk ixayar da take ciki gara ta haqura ta xauna da Badaru da ace aurenta ya mutu. Koda kuwa takata zai dungayi yana wucewa. Kuma da tasan zai dauki matakin saki akanta wlh da gara tayi masa wankin.



Saboda tashin hankalin da take ciki yasa bataga nisan tafiyar gidan Badaru xuwa titi ba, kawai ta tsinci kanta a bakin titi. Ta tare dan sahu tace kaini yahya gusau (gidan ya Faty) dan koda wasa tasan bazata iya tunkarar gidan Baffa ba (gidansu)



Har bakin gate din gidan ya kaita kasancewar gidan a bakin titi yake. Ta sauka tace bari in kawo maka kudin.



Faty na zaune a parlour tanashan golden morn taga fadowar Mimi parlour kamar an jehota, ta miqe a razane tace "lfy Mimi, jikin naki ne ya tashi?" nabar dan sahu a waje ban bashi kudin ba" itace amsar da Mimi ta bawa Faty, tana fadar haka ta shige bedroom din ya Faty.



Bayan Faty ta sallami dan sahun, ta riski Mimi a bedroom dinta kwance kan gadonta tace "Mimi ki fadamun abunda ke faruwa na ganki a hargitse haka" dakyar ta daga ido saboda tsabar ciwon da kanta ke mata, a taqaice tace da Faty "ya sake ni" ko kalma daya bata qara akan haka ba ta koma ta kwanta kan Royal bed din Faty. Sama sama ta dunga jiyo salati da sallallamin fatyn.



Har akai sallar magriba ana gab dayin ta isha suna zaune a gurin da sukai sallah jugum jugum. Suna idda sallar isha Mimi ta kuma hayewa gado ta qudundune mugun sanyi takeji saboda zazzbin da ya rufar mata.



Duk yadda Faty tayi da Mimi taci abinci taqi ci, domin batajin ko maqogaronta abinci zai wuce, saboda wani irin malolo takeji a maqogaron shi beyi gaba ba shi beyi baya ba. Kuma itama Faty da take maganar itama bataci abincinba. Ta hado tea ta miqawa Mimi tace "karbi kisha kodan abunda ke cikin ki" ba musu ta karba tasha.



A haka Ahmad ya riskesu, dawowarsa kenan. Ya shiga har bedroom din yace "lfy Faty? Mimi jikin ne ya kuma tashi?" duk sukai masa shiru, Mimi tacigaba da shan tea din ya kalli Mimi " Mimina lfy? Ko muje asibiti?" nan ma shiru ya kuma kallon Faty yace " Faty na kiyi magana mana lfy?" a hankali Faty ta furta "sakinta Badaru yayi".



Ga mamakinsu sai sukaji Ahmad yace "ALHAMDULILLAH " nan take fuskarta ta nuna tsantsar farin ciki, dukkansu suka saki baki suna kallonsa.



Ya ajiye jakarsa ta office akan side bed, sannan ya haura kan gadon ya kwantar da kan Mimi a kafadarsa yace "maryam ki godewa Allah da ya rabaki da Badaru, domin bai dace da samun salihar mace irinki ba, MARYAM keep praying in shaa Allah sai kinsamu mijin da baki taba mafarkin samu ba haqurinki bazai tashi a baxan ba"




Ita dai bin kowa take da ido ga alama ta samu kurumta ta wucin gadi. Haka suka kwana gado daya da Faty, inta fara bacci sai ta farka a furgice sai dai Faty ta tofa mata addua ta maida ita ta kwantar. Ya Ahmad kuma kwana yayi yana nafila yana roqawa Mimi waraka gurin ubangiji, in yai sallama ya shiga dakin da suke kwance, yaga halin da suke ciki, a duk sanda ya shiga Mimi kanyi xunbur ta miqe zaune alamun a firgice take sai dai ya maida ita ya kwantar ya tofa mata addua. Da haka har suka wayi gari.




HAPPY EIDIL FITR, TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM.

Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣8⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)


A bangaren Badaru kuwa, sai bayan ya saki maryam sannan fargabar abunda zai biyo ta bangaren Abbansa ya shige shi. Amma daya tuna yanda ya tsani maryam da yacce ya suqe da xama da ita sai yaga ai yanci bana rago bane. gara kawai da ya saketa komai xai faru ma ya faru.


Ana iddar da sallar isha, ya hada tea murtuk ya soya kwai 5, kamar shi ya siya. Ya dake cikinsa sannan ya sheqa wanka ya xaba shadda, ya samu turaren Mimi ya feshe jikinsa da shi. Ko lura da cewa turaren mata ne bayi ba. Yaywa gidan su Nafee tsinke.


Tare suka fito da dan aiken da yaje kiranta kamar jira take, ko gaisawa bata bari sunyi ba ta fara qorafi "Badaru anya kuwa kana sona? Anya kuwa xaka aure ni? Nifa na fara yadda da maganar mutane da suke cewa yaudara kake"


Ya danyi dariya πŸ˜„ yace "Nafee ko gaisuwa babu za a fara da qorafi" tace da maganar na yini tana damuna.


Yace to "ki fara shirin bikin ki nan da wata biyu masu xuwa" ta waro ido tace "bayan sallah fa kenan" yace kwarai kuwa tace "wace sallah? Yace wacce sallah ke gabanmu yanxu? " tace in nayi lissafi dai dai qaramar sallah kake nufi domin yau kwana 8 ko 7 ya rage a fara axumi"


Yace yawwa yar gari, kin gane kenan. Ta daka tsalle tace "da gaske?" yace "wlh da gaske nake" ya qara murmusawa yace "kuma daya albishir din da xan miki shine : ke kadai ce dani yanxu" tai far πŸ™„ tace "kamar yaya?" yace "mun rabu da maryam daxu"



Wannan karon tanayin tsallen ta fada jikinsa (kuji rashin kamun kai) ta qanqameshi duk kuwa da cewa basu taba hakan ba. Yayi saurin cireta a jikinsa jin yana shirin loosing control. Wannan dare haka suka sha hirar soyayya cikin nishadi saboda matsalarsu ta tafi (maryam) tare da hirar yadda aurensu xai kasance.

***** ****** ****** *****


Karfe taran safe 9:00 am a gidan kakanninsu tayi musu bisa shawarar Ahmad da kuma rakiyarsa, domin ita kanta bai yadda da nutsuwar Faty ba a lokacin shi yasa ya hanata driving. Yasan tunkarar Baffa da lamarin mutuwar auren Mimi ba karamin balli zai tayar ba, shiyasa yace abi abun takan surukan Baffa ko zai zo da sauki.



Babba gidane me cike da kango a da, amma yanxu da yayansa suka xama wasu sun bigeshi sun maidashi na tsamani da tsari. A katafaren parlourn gidan sukai masauki hajja na kan kujera, yayinda mal manu kekan well chair ( saboda girma baya iya tafiya)



Tiryan tiryan Faty tai musu bayanin lamarin tun rashin lfyar maryam da kuma halin data tsinceta a gidan Badaru har xuwa jiya da auren ya qare.


Hajja tunda aka fara take share kwallah, mal manu kuwa baice komai ba sai wayarsa daya dakko ya kirawo mama yace ta sameshi gida yanxu, sannan ya kira Baffa ma ya fada masa.



Tana gurin aiki kiran ya risketa, dan haka ta kasa nutsuwa. Tasan ba qaramin abu bane zaisa Baba kiranta a wannan lokacin, sai ta barwa kanta kawai Hajja ce ba lfy. Taje office din Principal din ta naimi excuse ganin bata taba hakan ba kuma da alama a rude take yasa ya barta.



Kusan tare suka iso da Baffa, domin shigarsa kenan taxo. Ganin motarsa a kofar gida yasa ta qara rudewa. Tana saka kai parlourn gabanta ya yanke ya fadi, dan ganin Mimi ta tsummace rabonta da ita tun randa aka kaita gidan miji (halayyar uwa ta gari bata xuwa gidan yayanta sai da babban dalili) ta samu gefen centre carpet ta xauna.


Faty ta kuma yi musu bitar abunda ya faru tas (dan ma Mimi bata fada musu waye haqiqanin Badaru ba da irin azabar da yayi mata). Baffa ya miqe ya watsawa Mimi kallon kinwa kanki, dagani akwai

Please Login or Register in order to submit comment