Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bata cika dariya ba sai murmushi. Mama tagabarta masa da abinci yaci, har xuwa taran dare sannan yai sallama yatafi, mama tace da safe inyayi shirin makaranta yaxo ya karya , tai shirin bacci suka kwanta tare da yaran a kan gadonta kasancewar tai musu tarbiyyar rashin fitsarin kwance tundaga yaye suke dena fitsari, tuni sukai bacci sai ita ta rage, taji sallama tare da shigowa cikin dakin, ssukai ido 4 dame me gidan nata, yayi saurin sunkuyar da kanta ga alamu nauyinta yakeji, "kixo dakina inasan ganinki yanxu " yana gama fada ya juya ya fice. Taiwa yayanta adduar bacci ta lullubesu da blanket ta dora hijab kan kayan baccinta tanufi dakin mijin nata. Koda taje bayan kwane-kwane na borin kunyar rashin kulata da halin da taga yayanta a cikin gidan, sai maganar ta dunga hada yaran cikin motar gida ana kaisu makaranta bai amince mata qara fita bada ixininsa ba, da yake namiji dai sunansa namiji sai jin hannunsa tai a jikinsa alamu haqqinsa na aure yake nema, πŸ™ˆ tunda ya fara bata dago kanta ta kalkeshiba balle ta tayashi abunda yakeyi, har yakai ga kwantar da ita akan gadonsa alokacin tayi yinqurin hanashi abunda yake wanda shi kuma alokacin yakai matuqa wajen San cimma burinsa hakan yasa ya samata qarfi ya fiya buqatarsa. Tayi kuka a wannan dare kuma ta tabbatar da tarasa Al amin har abada, tun kafin asuba tabar dakin nasa takoma nata tai wanka ta kwanta. Tsahon daren intace ta runtsa tayi qarya.

Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahma Muhammad {hajia}


Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }


Page 6⃣


BAYAN WANI DAN LOKACI.


Xuwa wannan lokacin tuni fadima wato (mama) ta zama yar gida agidan Baffa domin ta ware ta fuskaci qalubalen rayuwar dake tunkaro ta. Yayanta Kullum suna jikinta, babu abunda ke fitar dasu gidan sai xuwa makaranta, har Ahmad da yake qaunar yayanta shima ta jima da maidashi dan gida, tana qaunar yaron kamar ita ta haifeshi kuma tana tausaya masa kwarai da gaske, safe har xuwa dare yana da kwano a wajenta ma ana tana bashi abinci ta dauke hidimar karatunsa tsaf kamarsu bashi kudin makaranta dinka masa uniform da kuma tilasa masa xuwa makarantar. Da yake dan halak ne yaron, yana mutuqar girmamata da yi mata biyayya kamar ita ta kawoshi duniya. Duk da baqar maganar da takesha a cikin gidan nacewa ta samu dan daba nata ba tayi ruwa tayi tsaki a harkarsa . Bata taba kulasuba saboda dan Allah takeyi kuma aranta takance Da da dukiya ai ba ai musu mugunta, kuma da basai wanda ka haifa ne lallai yake jin qankaba .

Xaman gidan Baffa xamane na kowa kansa ya sani, saboda ko su matan ajunansu ba jituwa sukeba kullum fada suke kamar masu ganin hanjin juna gasu da ido akan yayansu, baki isa koda kauda buta kisa dan wataba sai dai kisa naki. Amma auro musu fadima da akai sai yasa suka hada kai saboda su yaqeta. A Kullum cikin goranta mata suke me yawon aure aure ta auri qani ya mutu ta auri yayansa, gashi abun takaicin Sun koyawa yayansu wannan dabi a tayi mata rashin kunya da yi mata habaici, yayansu maza ne dai babu ruwansu domin bazatace ga ranar da wani aciknsu yayi mata wani abu na batanci ba. Duk sanda xatai girki a gidan babu mai tayata da koda dauke cokali ne haka xatai girkin ta gama a wahale kasancewar bata saba girkin gidan yawa ba. Yayanta kuwa ganin idonta baisa anfasa dukansu ko xaginsu da aibatasuba, amma abun burgewar shine bata taba nunawa tasan anai musu hakan ba balle tayi magana, wannan ya qara baqanta ransu domin anayine domin tayi magana ko ranta ya baci, kawai dai abunda tasani shine bata yarda tabar yayanta da qazanta ba ko yunwa ko jahilci ta tsaye musu tsayin daka akan wadannan abubuwan. Agabanta xa a dakesu kuma asakasu aikin da ko ita data haifesu bata sasuba saboda aikin yafi qarfinsu amma saita kau da kai. A irin hakan wata rana Adda Halima yayar fadiman taxo ta tarar Anty jamila na dukan Mimi kamar xata kasheta wai kawai dan ta aiki mimin siyan omo kanti ita kuma mimin tace Mata mama tace babu kyau mata suje kanti sai dai maza, shine ta kamata tana duka Lamar ita takawota duniya babu wanda yayi yunqurin ceton mimin har uwarta dake can falonta tana dinki a kan keke tayi burus kamar ba yarta ake duka ba, sai Faty daketa kuka tana ihu tare da kiran azo atemaketa Anty xata kashe mata yar uwa. Ana cikin hakan Adda halima ta shigo gidan Kai xaye taje ta angaje jamila ta kwace Mimi tare da dauke Jamilan da Mari, sannan ta dora da cewa me wannan yar ficiciyar yarinyar tai miki kike mata irin wannan dukan? Shiru Anty jamila tai saboda Marin da akai mata ya shigeta, sai Faty ce ta mayarwa da Adda halima yadda akai . Tace yayi dai dai akan taqi xuwa aikenki kike mata wannan dukan? In gaskiya ne abun naki meyasa baki aiki naki yayanba? Ta juya ta kalli ragowar mutanen gidan da suka fito kallo sannan tace wlh tlh ku kiyayi taba yaran nan, marayun Allah kun hanasu sakat, me suka yimuku? Magana ta farko kuma ta qarshe wlh duk Randa wani acikin ku da yayanku ya qara sa hannu akan yayan fadima wlh kotuce xata rabamu. Tana kaiwa nan ta kama hannun Mimi da Faty tayi waje dasu ta xubasu a motar da aka kawota driver yaja suka tafi, kotakan fadima batabi ba saboda da ranta ya baci kuma tasan fadiman najin abunda akeyi tayi shiru.

Bangaren fadima kuwa sukuku tayini Baffa na dawowa da magriba taje ta sameshi da kukanta akan yakaita gidan Adda halima, ganin tana kuka yasa bai tambayi baasiba saboda ya dauka addan ce ba lfy yasata a mota suka tafi. Koda sukaje addan kin kulata tai ta hangi su Mimi da Faty a dining Sunayin dinner tare da yaran Adda da kuma dady mijinta tuni Sun sake cikin yara da yake yawanci akwai sa anninsu acikin yaran addan. Fadima taje ta riqe hannun adda tare da saka kuka, tace yi shiru fadima aini bakimun komai ba face amanar yaya da Allah ya baki kika kasa kula dasu kuma na kwashesu inke bakiso ni inaso, sai alokacin Baffa yaji abunda ke faruwa, wasa wasa dai adda ta hana fadima Yaya tun ana ganin wasa takeyi har dady da Baffa sukasa baki amma ta qeqashe qasa tahana, da yake ance da uwa sai Allah koda Mimi tagamacin abinci ta kyalla ido taga mamanta ai saitai gurinta da gudu ta kwanta jikinta, da haka Baffa yace tabar yaron ta taso su tafi ta miqe ta yafa gyalenta Mimi ta riqe hannun uwarta xata bita adda ta bita ta dauketa ta saka ihu, ta ajiyeta Tare da cewa maxa bita dan gidanku uwar taki da batasan ciwonki ba tana xaune xa a kasheki tai shiru, Faty take gefe taga suna shirun fita tace da Adda mummy nima xanbi mama, ta riqe baki tace au kema? πŸ€” to ai kun kunyatani xo kibita in ankasheku ta huta. Da haka ta bawa fadima yayanta tare da ja mata kunne sosai.

To tundaga wannan lokaci akasamu sauqin abun domin suna shayin Adda halima sosai domin itadin bata barin ta kwana kuma tsaf Sun san xata aikata abinda ta fadadun koma fiye da haka. Tundaganan babu wanda ya qara yunqurin dukan yayan fadima sai dai kyara da hantara da xagi. Ni kuwa nace zagi ai zagawa yake kuyi tayi πŸ™„.


Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ

Writing & story by rahama Muhammad {hajia }

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }

Page7⃣

ASALINSU

Mahaifin Maryam su 2 ne a gurin iyayensu wanda suke fulanin gombe usul awani da ake kira kaltungo, Baffa Buhari shine babba sai AL AMIN wanda yake shine mahaifin su maryam din tun suna yara qanana iyayensi suka rasu, sun taso agurin dangi har xuwa girmansu Buhari secondary skul kawai ya gama ya tsunduma kasuwanci da yake anbar musu gadon dukiya sosai, dakadan dakadan kasuwancinsa ya bunqasa har ya kasance maxaunin Kano State saboda itane cibiyar kasuwancin arewancin qasarnan. Yana kasuwancinsa a kasuwar singa na sai da kayan abinci da kayan masarufi, da quruciyarsa sosai yayi aure saboda kudi da yake dashi, ya auri matarsa Hajara (umma) kamar yadda yayanta ke kiranta.

AL amin kuma yafi maida hankali a karatu, duk da yayan nasa yaso kwarai ya tsundumashi harkar kasuwanci ya dunga gocewa har daga baya ya fahimci bayaso ya qyaleshi .

Yayi karatunsa na Law anan ABU zaria ya kammala yaje Law skul dake Lagos ya dawo. AL amin matashin saurayi fari tas kyakykyawan gaske kamar yayan nasa Buhari. Ya dawo xaman gida a inda umma hajara ta dunga yimasa cushen qanwarta husna wadda take gidan a lokacin tana yiwa Umma xaman dabaro a dalilin haihuwar da tayi, tun be ganeba har ya fuskanta hakan yasa ya dena shigowa cikin gidan sosai indai ba kamawa tayi doleba duk abunda xaiyi yana yi ne iyakar shagonsa dake qofar gidan. Saboda sam husna batai masa badan bata da kyau ba sai dan bata cikin jinsin matan dake burgeshi .

Ta bangaren mahaifiya kuma asalin mahaifiyar su MARYAM bafulatanar ce domin iyayenta fulanin garko ne ta jihar Kano, su 9 mahaifiyarsu mai suna MARYAM (hajia) ta haifa da babansu mal SULAIMAN guda 7 maza kuma sune manya sai Adda halima sannan Fadima wato mahaifiyar su MARYAM itace kuma auta mazaunan unguwar tudun maliki.

Fadima ta gamu da iftila'in rayuwa tun tana yar shekara 7 wani Mara imanin wanda ba asan ko wanene ba Yayi Maya fyade (rape) yayi mata kaca kaca wanda hakan ya jawo mata baqin jini a lokacin yan matancinta dan kaf saida akaiwa sa anninta aure amma ita babu labari har ta shekara 14 (kasancewar ba makarantar boko sukeba, dan mal sulaiman yayansa maza kawai ya yadda suyi ilimin boko ) a zamanin budurwa mai shekaru 14 babbar budurwace sosai kuma da kunya a ganka da yarka a wancan lkcin mai wannan shekaru babu aure, duk wanda ya fito neman aurenta sai yan unguwa su tareshi su fada masa abunda ya faru kanta, daga haka har aka dena xuwa gaba daya. Ba tare da shawarar kowa ba Mal Suleiman ya dauki auran fadima ya bawa wani abokinsa direban babbar motar haya (Wanda yake sana arsu daya shima matuqin mota ne) mazaunin qauyen maberaya ta jihar sokoto a wancan lokacin a yanxu kuma zamfara. Saboda xaman fadima haka ya dameshi kwarai, yayiwa Mal Ali bayanin abunda ya faru a kan fadima shi kuma yace yaji ya gani ba komai aishi Me rufa masa asirine.

Lokacin da yaxo da maganar aurar da fadima ga Mal Ali hajia ta shiga mugun tashin hankali ita da yan uwan fadiman karma Adda halima taji lbr domin tana mugun San fadima, amma dole sukai haquri saboda sanin halin ubansu mafadacin gaskene.

Haka akai biki aka kai fadima gidan Mal Ali dake maberaya, gidan gandu bayan matansa 2 da yaya 17 harya aurar da wasu ma, ga kuma tagowar yan uwansa dake cikin gidan. Haka dai suka baro fadima uwa ta mutu saboda tunda akai maganar aurenta da Mal Ali ta koma wata iri kamar mai tabin hankali, suka rabu suna kuka ita kuma tana binsu da ido kamar zararriya.

Saida ta kwana 2 bataga angon nata ba, anabata abinci agidan irin cimar mutanen qauye wanda ganin bataci suka dena kai mata dan yanda aka kai haka aka dakkoshi, dan abun motsa baki da kayan fulawa na kayan garar da aka kawota dashine takeci, bata fitowa sai xata bandaki wanda take mugun kyama domin ko wanka takasayi a ciki. Arana ta ukun ne ta fito ta wanke bayin cike da tashin xuciya saboda jikinta ya dameta da ciwo tana buqatar wanka tayi wankan tafito tarar da mutan gidan sun cika tsakar gida da daurin qirji suna ganinta aka hau dariya da habaici ko kallo basu ishetaba ta shige dakinta.

A daren ne kuma mijin ya shigo dakinta tare da kazarsa ta amarci, alkcin yake fada mata wai tafiya yayi kudu dakko kaya shiyasa taji shiru amma gashi ya dawo suci amarci πŸ˜‚. Duk yadda yakai da sweet mouth (dadin baki) fadima taqi amince masa, ya haqura ya kyaleta har kwanakin girkinta suka qare ya bar dakin, girki ya kuma dawowa kanta ya dawo dakin da sam cimma burinsa saboda ya kwaditu kwarai da fadima kyakykyawar mace jajur da ita ga quruciya, koda taqi yarda dashi yaso kwada mata qarfi ta saka masa ihu dole ya haqura ya kyaleta saboda gidan yawa suke ga yayansa da jikoki cikin gida da kunya aji tanai masa Ihu.

Saida aka shafe wata biyu cur a haka xaman gidan sam ya gundureta kwarai, duk sanda ta fito tsakar gidan da nufin yin wani abu zata tadda cincurundun matan gidan a gidin bishiya suna ganinta xa a ce " ritayar birni sai qauye ga gwallin ga shafe shafen amma anrasa miji a birni sai a qauye " sai a tafa a kwashe da dariyar cike da shaqiyanci irin na shegun qauye (shegu qauyawa πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚) . Duk da tana dakewa ta nuna bata gane da ita sukeba amma abun yana damunta. A bangaren mijin ma dangantaka tsakaninsu tayi tsami, saboda taqi yarda dashi ya dena bata dan kudin kashewa da yake bata da kuma lallabawar da yake mata shima tsakaninsu sai hantara aganinsa hakan zaisa da yadda dashi. Tayi baqi ta rame ta fita hayyacinta duk ta koma kalar yan can.

Ana cikin hakan girki yaxo kanta kuma a daren ya nuna zulamarsa akanta wanda hakan yasa ta dunga kurma ihu har mutan gidan suka tashi suka firfito tsakar gida, kunya ta hanashi fita baqin ciki yasa ya jawo wayar radio ya dunga tsula mata yana kwallo da ita har sai da yaji ya huce ya kyaleta. Anatada sallar asuba a masallaci ya fita itama ta tashi tasa hijabinta tasa takalma ta fita, lokacin data isa tasha gari ya fara shaaa, tashiga motar Kano bata da ko sisi tayiwa direban motar bayani bata da kudi amma insinje Kano zata bashi ya kaita har gida yayi shiru yana kallonta can yace ke yar Mal manu ce? Naga Kama, tai saurin cewa eh ni yarsa ce fadima yace to lfy naganki haka kuma anan? Tai shiru sannan yace bakomi mun taba aikin mota tare dashi ashe yata ce muje ba komi har gida xan kaiki. Kafin motar ta cika ya sai mata shayi da bread Shayin kawai ta iya sha tana Allah Allah motar ta cika sutafi dan gani take kamr Mal Ali xai biyo bayanta. Da haka motar ta cika suka daga.

Mrs Muhammad 😊


πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
8⃣
Azahar a cikin gidansu tai mata direban motar daya kawota ne yayiwa Mal sulaiman halin da ya ganta aciki, yayi masa godiya ya shiga da fadiman cikin gida. Ransa ya baci kwarai da yaga kwanciyar bulala ajikin ta kota ina, haka aka dunga biqinta har ta warke yayyunta maza sukace aure anyi angama. Sai dai har fadima ta share 3wks a gidan Mal Ali bai nemeta ba, hakan yasa Mal sulaiman ya nemshi cikin xafin rai yanuna masa bacin ransa kan abunda yayiwa fadima, shima Mal Ali cikin nasa xafin ran ya balbale Mal sulaiman da nasa fadan tare da cewa yar tasa ragowar wani da bata da mutunci yaje ya saketa. Jikin Mal sulaiman yayi sanyi kwarai ya tara yan uwan fadima ya fada musu kuma ya nemi yafiyarta. Dama duniya makarantace Wannan avun shiya koyawa Mal sulaimn hankali ya lura cewa bada fadima sadaka bashine mafitaba gara yayi haquri har Allah ya kawo mata wanda xai sota a yanda take. Saboda haka ya bawa yan uwanta damar da suka dade suna nema a kanta, suka sakata a makatanta library ta fara xuwa inta tashi ta shiga ajin koyar sana a dinki da saqa.

Bayan shekaru 2 fadima ta goge sosai kasancewar ansakar mata mara tana fitsari babu takura, ta goge ta cika ta xama cikakkiyar mace tuni ta kware akan dinki takan dan taba saqa amma tafi maida hankali akan dinki, ta bangaren karatu kuma ta kusa kammala primary.

A na cikin hakan suka hadu da AL amin a lokacin yana service (bautar qasa) ta dawo daga skul suka hadu ahanya ya bita har gida, Sun fara soyayya ya mace akan kyakykyawa fadimatu itama tana qaunar Guy din amma tana dari dari saboda kar yaji abunda ke tare da ita, saboda haka ta kwashe komai ta fada masa kafin asamu wani daga waje ya fada masa. Ga mamakinta saiya tausaya mata tare da bata tabbacin wannan bazai rabasu ba,

Bayan dogon dauki ba dadi da kai ruwa rana da aka samu ta bangaren AL amin. Saboda a cewar Baffa Buhari bazai auri bazawara ba sai dai ya samo wata tunda yace bayason husna qanwar hajara, shi kuma AL amin din ya kafe yace ita yakeso, duk da Baffa ba ra ayinsa bane, zugar hajara ce kawai ke aiki dashi kasancewarsa namiji mai daukar xuga, shidai kawai ya tsani fadima tun kafin ya ganta saboda yanda yaga Dan uwansa na qaunarta , wannan ra ayi nasa ya hadu da xugar hajara ya jawowa fadima tsana sosai a gurinsa, a bangaren hajara kuma ji take kamar ta kashe fadima tun kafin ta ganta, gashi alokacin anmata kishiya wato Anty jamila abun ya hadu yayi mata yawa. A karshe dai Allah yayi ikonsa domin AL amin da Fadima sun kasance ma aurata.

Ta haifi yarta fari Mace ya maida sunan matarsa, wanda hakan ya kuma janyowa fadima qiyayya a gurin Baffa da matansa, saboda hajara tayi masa famfo cewa kamata yayi AL amin din yasa sunan mahaifiyarsu amma yasa sunan shegiyar matarsa. Xuwa wannan tym din gidan Baffa ya fara cika da yaya kuma arxiqinsa ya bunqasa kwarai da gaske ya gina qaton gida me part 4( gidan da suke ciki yanxu) gida me kyan gaske ginin irin wancan xamanin da daku 2 asoro na mazan gidan da seat room daga waje da rila xagaye da gidan. Tun lokacin da aka auro fadima ta tadda yara 7 a gidan 5 na hajara 2 na jamila, daga baya suka fara competition din haihuwa, a inda nan da nan suka cika gidan da yaya maza da mata amma matan sunfi yawa.

AL amin yasamu aiki a tun farkon aurensu a inda yasamu aiki a jamiar da yayi karatu wato ABU kuma yana ci gaba da karatunsa, agefe kuma yana taba aiki a wata chamber kasancewarsa lawyer, suna zaune a unguwar sharada fadima ma tana cigaba da karatunta AL amin ya tsaya mata da kansa inyana gari yakan koyar da ita, ga kuma sana arta ta dinki tanayi.

Bayan shekaru 5 da haihuwar Faty ta haifi MARYAM taci sunan mahaifiyar fadima kenan suke kiranta (Mimi). AL amin ya kasance mutum mai mutuqar San iyalinsa yanasan yayansa kwarai, yakance in Allah ya yarda Faty ma aikaciyar jinya (nurse) Mimi kuma yakance shixata gada wato lawyer, in ya fadi haka fadima kance Allah ya rayaka Barrister ya kuma yara maka sister Faty da Barrister Mimi . Yakance amin amin fadimatu.

Mimi nada 4yrs ya jefata a skul sai dai ita sabanin yar uwarta miskilace kuma mai yawan lalura da fari Sun sikila ce sai da suka je asibiti sukaji sabanin haka domin bincike ya tabbar da A S ce, kawai dai Allah ya halicceta me lalura. Alokacin kuma fadima takuma samun wani cikin, cikinta na wata 6, Allah ya dauki ran AL amin a dalilin hatsari da yayi a hanyarsa ta koma Zaria gurin da yake aiki, mutuwar ta girgiza fadima da Baffa Buhari kwarai da gaske a dalilin mutuwar fadima tai haihu lokacin haihuwar beyiba ta haifi jariri dan wata 6 babu rai. Bayan 40 Baffa ya buqaci a bashi yayan AL amin, da farko fadima da danginta sunqi amma daya kafe cewa dole ta bashi domin baza a tafi da yayan dan uwansa wani gidan ba da sunan aure.babu kunya da lokacin da yan uwan fadima maza suka nemi xama sulhu yace in fadima ta matsa tanasan rayuwa da yayanta ta aureshi taje ta riqe yayanta, lamarin da taqi yarda sam saboda tasan halin matansa da yadda suka tsaneta a matsayin faccala bare kuma ta xama kishiyarsu, sannan kuma ita bazata iya cin amanar AL amin ba ta auri wansa. Shi kuma yayi amfani da wannan damar ya kwace yayanta yakai gidansa ya watsar. Kunji yadda lamarin ya kasance.


Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ

Writing&story by
Rahma Muhammad {hajia}

Editing by mmn khairat 😍

πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Pege9⃣




Maryam (Mimi) da Faty, Sun taso kai daya kasancewar Mimi mai garun jiki saita xama kamar saar Faty, baxaka taba kallonsu kace Faty tabawa Mimi tazarar shekaru biyar ba. Faty ta kasance fara sol kyakykyawar mace sosai doguwa mara jiki, kamarsu daya da uwarta sak mai yalwar sumar Kai. Yayin da Mimi ta kasance doguwa me murjajjen jiki me cikar halitta, bata da qiba Sam amma duk inda ya kamata ya xamo me cika ajikin mace kamarsu qirjinta da kuma hips to ajikin Mimi dai sai Masha Allah, dangane da skin colour kuwa Mimi wata irin colour ce ba fara bace kuma ba baqa bace ko kadan, itadai gatanan kamar ruwan xuma ( honey colour) fatarta me daukar hankalice irin colour din dake matuqar tsada a duniya, a taqaice dai xamu iya kiranta Kalar bargon kaza. Bata da wani shaharren kyau a fuska irin na yar uwarta komai nata a fuska tsaka tsaki ne inka cire manyan iduwanta farare tas, sai kuma haqoranta farare tas dogaye ,itama tana da gashi sosai koma ince duk jikinta gashi a kwance ( irin matannan masu gargasa) har fuskarta gashi ne a kwance tun daga gaban goshinta xuwa sajenta har xuwa qeyarta. Amma gashin mai qarfin gaske kamar izgar doki ga cika ga tsaho wanda yasa dole mama take mata retouching tun tana qaramarta inba hakaba baya kitsuwa yanka hannu yake. Itakam tafi kama da AL amin (mahaifinta) inka kalleta tsaf komai nata sai kaga tana kama sosai da SASHA OBAMA ( yar

Please Login or Register in order to submit comment