Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko Mimi ta tashi ta kawo mata abinci amma taga bacci take. Har tagama komai Mimi na bacci, ta fitowa da mimin kayan da zata saka dan a tsarinta tana tashi take wanka kana ta yi break fast. Doguwar rigar atamfa mai laushi ta dakko mata, bataga Dan kwalin rigar ba so saita dakko mata kashka medium irin wanda ake dorawa saman doguwar rigar ta hada mata da atamfar ta ajiye a kusa da Mimi gefen gado. Kana ta fita gurin kitchen gurin moses inda suke haduwa gaba daya da ragowar ma'aikatan suna ganin yadda yake girki suna hira.



Dake hausawa sunce baya bata da kadan, Mimi cikin baccinta taji ya Bature na tashinta, ta farka a firgice ta kalleshi tace "harka dawo?" yace mata "eh" kawai ya zarce dayi mata wasannin soyayya. Ta xare jikinta don batason wannan harkar sam a halin yanxu tace masa bari nai wanka, ta dingisa ta wuce bathroom. Tana wanka tana tunanin meya dawo da ya Bature gida yanxu shi da yace mata yau meeting garesu? Da wannan tunani ta fito wankan, abun mamakin sai ta samu dakin wayam babu kowa, da sauke ajiyar xuciya a fili tace "dama nasan bazai dawo yanxu ba, May be mafarki nayi"





Ta shafa mai tana saka riga ta hangeshi kwance ta cikin madubi tsirara akan gado, gabanta yayi wata irin faduwa. Ta juyo taga gurin wayam, ta kuma kallon madubin ta hangoshi kwance. Hankalinta yayi wani irin tashi tayi yunqurin ihu amma ta kasa don bakinta ya sarqe.






Tana cikin wannan haline taga ya dunfarota, ta runtse ido tana so tayi ihu ko addua amma bakin ya rufe gam, dalilin ihunta kuwa ganin wannan mutumin mai nufota tsirara da nufin sex da ita al'aurarsa har qasa take wato takai gwiwarsa kuma wai sex xeyi da ita. A fuskarsa dai kamannin mijinta sak, amma tasan mijinta bashi da wannan mummunar Al aurar. Allah ya temaketa ta yunqura ta miqe tare da xarar mayafinta tai waje da gudu. Tafiya take tana waige amma ga mamakinta binta yake tsirara yana dariya.




Ta nufi gate dake brain din irinta yarace wai saita nufi office din su Bature a nufinta taje taga shine wanda ke binta koba shi bane. Me gadi ya bude mata gate yana cewa 'sannu madam jiki yayi kyau, gidan alh ishaq xaki leqa kenan?" ta fita ba tare data tankashiba sabida hankalinta yayi gaba.




Ta tari napep a layin ta fada masa yakaita Company din NNPC. Ya fara tafiya da sauri don yaga alamar sauri take don suna tafiya tana waige. Ita kuma anata bangaren ya Bature take gani har yanxu yana binta kuma tsirara yana dariya ga mamakinta kuma sauri yake har yana wuce ababen hawan dake gudu kan titin.




Yana ajiyeta ta shige cikin ma aikatar da gudu, yana cewa hajia kudin bata saurareshi ba ita kawai burinta ta gujewa wannan dake binta kuma taje office din ya Bature taga shine koba shiba.





Sai dai abunda yayi mata cikas bata San office din nasa ba tunda bata taba xuwa ba, dan haka ta nufi babbbab hall din da suke meeeting inda ta hango jamian tsaro jibge gurin suna gadi.




Ta nemi shiga suka hanata tare da tambayar wacece ita, ta dunga nuna musu mutumin dake binta tare da ce musu gurin mijinta xata. Sukace ta tafi tabasu guri su basuga kowa ba, daya daga ciki yace "su kyaleta da alamar mahaukaciya ce"




Suna ta dauki ba dadi tsakaninsu da ita, su sun hanata shiga, ita kuma ta kafe saita shiga sabida wanine ke binta.





Daga cikin dakin meeting din suka farajin hayaniya tayi yawa, mr Alex ya tura Hanifa taje taga meke faruwa. Ta miqe dan cika umarninsa





Duk da tanada masaniyar abunda ke going amma sai datayi mamakin ganin Mimi anan tana fada da sojojin. Direct tace "ku barta ta wuce matar Eng SULAIMAN A AZEEZ ce, tana da tabin hankali" ta bawa Mimi hanya ta wuce tana wani shu'umin murmushi na cikar buri.





Tana shiga gurin ta fara cewa "ya Bature! Ya Bature!! Kana ina? Kaxo xai kasheni, ko kaine ka turoshi ya tsoratani?" Bature kansa sunkuye yana rubutu ya tsinci muryar Mimi tana fadar haka.






Ya tashi da sauri ya nufeta, tuni ta fita hayyacinta sai maganganu take wanda rudi yasa baya gane abunda take fada. Duk gurin yayi shiru ita kawai ake sauraro, Hanifa na tsaye jikin qofa tana murnar Mimi fa lokaci yayi domin da alama hauka ya kankama.



Yaje ya riqeta yana girgixata da cewa "Mimi ki dawo cikin hankalinki plz, waye xai kaaheki? Meya kawoki nan?" ta dubeshi ta kuma dubi me kama dashi wanda har yanxu take ganinsa yana mata dariya tare da kiranta da "taho Mimi luv nine ya Baturenki" ta dunga kallonsu a tare, ta rasa waye na gaskiyar, take anan kwakwalwarta ta juye ta kwallah qara ta xube qasa sumammiya.





Wadanda ke gurin suka taso xasu tayashi daukarta, ya tsaidasu da cewa xai iya. Ya ciccibeta cikin rashin sa a mayafin dake rufe kanta ya xame ya fadi qasa, tsautsayi yasa ya takashi bai saniba aikuwa satsin tiles dana mayafin ya kwasheshi yayi qasa ya fadi Mimi dake hannunsa kuma ta fadi gefe wanwar kan cikinta.





Qarar faduwarta da kiran sunanta da yayi a tare suka fito, beyi ta nasa faduwanba ya nufeta a gigice yana girgixata da fadin "maryam ki tashi, maryam ki taimakeni ki bude ido" duk wanda ke gurin sai da ya tausaya masa ciki kuwa harda Hanifa da itace silar faruwar komai.





Akayo kansu gaba daya ana masa sannnu cikin sauri ya dakko wayarsa ya kira ya Taheer da ishaq a taqaice ya fada musu abunda ke faruwa.





Suna tsaye cirko cirko yayin da Bature ke tsugune gaban Mimi da bata motsi yana kuka haiqan ya Taheer ya iso. Ya dudduba Mimi shima take ya fara hawaye don gani yake Mimi ta mutu. Isowar ishaq yasa suka tsagaita da kukan, ya tsuguna ya dinga chaje Mimi, ya dago yace musu tana da rai tabbas. Ya Taheer cikin hanxari yace "to sulaiman inaga a sada yarinyar nan da iyayenta tunda har abun yakai haka ta fara fitowa." ishaq yace hakane yafi dacewa.





Bature badan yaso ba ya yadda, Taheer yace bari yaje ya samo tiket. Ishaq kuma ya fara bata taimakon gaggawa don numfashinta ya dawo.





Mr Alex ya matso cikin tausayawa yace "ya bada jet dinsa akaita" Bature yaji dadi sosai sukai godia, nan take ya kira pilot din yazo da jet din, Aka dora Mimi kan gadon marasa lfy ishaq ya juna mata drip da oxygen Taheer da Bature suka shiga jet din ya daga xuwa kano.





Meeting din daba a qarasa ba kenan, akaita jimamin halin da matar Eng sulaiman ke ciki.




Ishaq be koma asibiti ba gida ya nufa.



Hanifa kuma gwaggoriya ta kira ta fada mata abunda ya faru cikin farinciki amma bataji dadin tafiya da Mimi kano da akaiba. Gwaggoriya ta kwantar mata da hankali cewa ai a kano sai tafi nesa da sulaiman don tasan yana kaita zai juyo ya dawo Abuja sabida aikinsa ita kuma acan xata sulale ta gudu ta shiga dawa. Hankalin Hanifa ya kwanta da jawabin gwaggoriya ta bar damuwa data fita har sadaka tayi murnar aikinta yaci, kuji kwaba yan uwa wai layya da kare.





Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 6⃣0⃣




Ishaq yana isa gida ya samu Farida har bed room tana shirin wanka daure da towel. Babu sallama ya balbaleta da masifar cewa tana ina har Mimi ta fita taje office din sulaiman sabida tsabar shashanci da sakaci irin nata?



Farida ta tambayeshi cikin rudewa da neman maimaita mata abunda yace Mimi tayi. Cikin masifa kamar xai daketa ya fada mata duk yadda akai.



Ya dakata da fadan da yake dai dai lokacin da yaga Farida tayi xaman yan bori tana ihun kukan kiran sunan Mimi dan Allah a temaketa a dawo da mata da Mimi.



Ai tuni ya dena fadan ya dawo lallashin Farida da fada mata Mimi yanxu an wuce da ita kano kuma xata samu sauqi in shaa Allah. Shima dai a ranar aiki ya sameshi don farida taqici taqi sha sai kuka da kiran sunan Mimi da kuma cewa lallai saiya kaita kano itama dan gani take Mimi mutuwa tai suke boyewa. Haka ya yini lallashinta har bayan sallar asr.




Ya yiwa Baqo waya yace ya tattaro masa duk masu aikin gidan su sameshi anasa gidan.



Cikin qanqanin lokaci sukaxo suka sameshi, ya dunga binsu da kallo yana kada qafa, mugun haushinsu yakeji kamar ya tashi ya rufesu da duka.




Ya fara magana cikin qunar rai "abun takaici ne ace duk yawanku a cikin gida har maryam ta sulale ta fice baku sani ba, bayan kudin kunsan tana da lalura ba a rufe muku ba" suka rude da jimami da kalaman kare kansu na basusan fitar madam ba.




Ya daka musu tsawa da cewa suyi masa shiru, sukai tsit suna sauraransa yace "sakamakon abunda sakacinsu ya haifar antafi da maryam kano, dalilin haka ni kuma na koreku aiki gaba dayanku." falon ya cika da koke kokensu, farida tana zaune tana jinsu batasa baki ba idonta yayi jajur sabida kukan data yini yi.




Ya daka musu tsawar cewa su bace mai da gani, suka tashi jiki a sanyaye suka dunga fita Aisha ce kadai ta rage. Ishaq ya kalleta yace "ke xaman me kike?" ta matso kusa da qafafunsa cikin kuka tace "Dan Allah Alh kayi haquri, wlh lokacin dana bar madam bacci takeyi, sai yanxu da kaxo da lbrin abunda ya faru. Nidai kasani motar kano yanxu in bita can in tayasu jinyarta badon a bani kudi ba, sai don rama dinbin alkhairin da tayi yimun" ishaq yayi dan jim, Farida ta dafashi "ya ishaq ka kyaleta ita, amanace sosai tsakaninsu da Mimi" yace "to shikenan kije xuwa da safe sai inkaiki tasha ki tafi kano dan yanxu dare yayi."





KANO

Isarsu direct Aminu kano teaching hospital (AKTH) suka sauka. Dake abun na manya ne da gaggawa aka amshesu aka wuce da ita A&E. Likitocin emergency suka rufu kanta a qoqarin neman numfashinta.




Ya Taheer shi yayi waya ya sanar da gidajensu halin da ake ciki dan Bature bashi da nutsuwar haka, duk nacin likitocin da ya fita ya basu gurin suyi aikinsu amma dole suka kyaleshi domin yaqi fita qememe.





Faty wacce ta zama metro a halin yanxu ta riga kowa isowa don tana cikin asibiti wayar mama ta sameta tana kuka ta fada mata ankawo Mimi yanxu bata da lfy.




Ta tsaya akan Mimi tana taya likitocin aikinsu, suma sun qara bawa Mimi kulawa da suka gane sis din metro Faty ce. Aka bawa Bature takaddar biyan kudin gado da sauran charges din yaje ya biya. Amma qememe yaqi fita sai ya Taheer ne yaje ya biya aka bata gado.




Likitocin suka fito dan ansamu komai ya dawo normal amma tana bacci. Lokacin mumy, mama Dady da Baffa sun iso hankalinsu tashe. Faty ke musu bayanin Mimi ta samu bacci yanxu.




Suka dunguma dakin hankalinsu tashe yake har yanxu, mumy keta tambayar Taheer wane ciwone wannan farat daya Mimi tai wannan uwar rama kuma har aka kawota gida?




Sun sami Bature a dakin yana zaune gefen gadon hannunsa riqe hannun Mimi. Sai da suka xauna suka nutsu kana ya Taheer ya bude musu komai tun farkon ciwon har kawo yau.




Sukai jugum jugum suna sauraransa, mumy ta kalli ya Taheer tace "amma Taheer kaci amanarmu a matsayinka na babba a tsakaninsu, don sulaiman bashi da hankalu kaima baka dashi kenan? Marainiyar Allah bata da lfy kusan 3wks ku hada baki ku rufe mana? Nagode kwarai Taheer wlh in maryam ta mutu saina daureku kaida sulaiman"




Taheer ya gigice yana bawa mumy haquri, bai zaci xata dau abun da zafi haka ba.




Ta dunga watsawa Bature harara cike da tsanarsa tace "nagode sulaiman kamar nasan abunda xai faru naji hankalina bai kwanta ka tafi da ita ba" ta daka masa tsawa "tashi ka bacemun a gurin" Bature dai bayajin abunda suke cewa balle yaji tsawar mumy, yacigaba da riqon hannun matarsa.




Mumy a ganinta rainin hankaline yana jinta, ta tunkareshi Faty tai saurin tsaida ita tana kuka tace "mumy yanxu duk ba wannan ne abunyi ba lfyar Mimi itace agaba, abunda xai faru ya riga ya faru" dole mumy ta tsaya.




Mama dai babu baki sai ido takebinsu dashi tana share hawaye. Dady kuma yanata kiran consultants daya sani a asibitin ta cikin wayarsa, yayin da Baffa ke kallon Mimi cikin jimamin jin wai maryam din yanxu ko tafiya batayi.






Xaman jigum jigum ya biyo baya har xuwa yamma, Mimi bata farko ba gadai oxgyen an saka mata da wasu manyan ingina. Sabida alfarmar Dady da Faty manyan likitoci keta zarya akan Mimi, tuni suka nemi asibitin Abuja aka turo musu duk record din ciwon on-line.




An turata xuwa dakin xray akai mata brain CT scan (photon kwakwalwa) photon da yakanyi 1wk kafin ya fito ita sabida gata a cikin 1 hour ya fito consultant a bangaren ya duba yace brain dinta normal take babu komai akanta.



Adai cikin wunin aka kaita physiotheraphy (bangaren likitan qashi) suma xray din sukai aka tabbatar babu matsala kamar yadda result din ya nuna a Abuja.



Duk wannan abun da ake Mimi bata sani ba don bata farko ba, a qarshe aka maidata Female medical ward, aka bata aminity (wato daki ita kadai) aka qara mata wasu inginan akanta da hanci sai qafar da suka daddaura wasu manyan qarafuna sukayi hanging din qafar da qarfen saman gadon.



Dukkansu sun rame a wuni guda kawai, anyi anyi Bature yaje gida yaci abinci yayi wanka tunda ance Mimi bacci take amma yaqi. Dady ne ke faman dashi mumy kam babu abunda tace masa tsakaninsu harara in sun hada ido dan mugun haushinsa takeji.




Magrib tanayi bayan idar da sallah Audu yazo, shidin ma dawowarsa aiki kenan lbr ya sameshi a gurguje ya kimtsa yaci abinci ya taho. Ya samu Baffa da Dady sun tafi gida, mumy da mamane kawai a gurin sai Faty daketa zirga zirga.



Suna gaisawa ya Bature ya dawo daga sallah, yayi fici fici dashi. Ya tashi yaje gurinsa suka gaisa yana masa yame jiki bejiba ya koma mazauninsa wato kan gadon Mimi ya riqe hannunta.





Mama ke masa bayanin tun safe yake haka riqe da ita, anyi anyi dashi yaje gida ya yi wanka yaqi. Yace "mama ke da mumy kuxo muje gida ku kintsa sai ku dawo tunda gani ga ya Bature ga Faty, in yaso inkun dawo saimu koma ku kuma ku kwana da ita. Suka yarda da shawararsa dan suma din tun safe suke tsaye yakamata suyi wanka suci abinci.



Ya debesu ya fara kai mama sannan ya kawo mumy gida ya wuce gidansa, yasmin na tambayarsa jikin Mimi yace da sauki kawai. Ya debi kayansa qanana Set 2 ya fice. Sai daje eatry yayi siyayyar snack dasu ice cream kana ya sayi fura. Ya koma store ya sayi soso dasu brush da kayan tea kana ya koma asibitin.




Yasamu ya Bature yadda ya bashshi Faty kuma ta fita. Ya rufe dakin yaje toilet ya hada masa ruwan wanka yakai masa komai sannan ya fito yace "ya Bature dan shiga ka watsa ruwa" baiyi gardama ba Don shima yana buqatar hakan.





Ya jima a toilet din, yayi komai har brush, ya fito ya shafa mai da perfumes ya saka kayan da Audu ya kawo masa. Yaji dadin jikinsa sosai, sai alokacin yaji gajiya bacci da yunwa sun rufeshi. Audu ne ya bashi tarkacen kayan da ya siyo, yana hillatarsa da hira yaci sosai ya kuma shanye furar tas. Faty ta shigo tana musu sannu, itama sai a lokacin ta samu xama taci abunda Audu ya siyo. Ta karbi Babynta a hannun me raino wanda yayi kuka har ya gaji ta bashi nono. Sunata hira ko ince jimami har 10:17 lokacin mumy da mama suka dawo, mumy dauke da tea flask mama kuma food warmer.





Suka qara jimantawa juna, mumy tace Faty ta tafi ita da Audu da Bature su kuma su kwana da Mimi. Bature qiri qiri yace "nifa babu inda xanje wlh" mumy ta haushi da xagi tana cewa "Dan ubanka kasan kana santa ka bari ciwo ya ragargajeta haka?" mama ta shiga tsakaninsu don ita Bature tausayi yake bata.




Likita da Faty suka kuma shigowa ya qara duba Mimi yace "bacci take kuma xata iya farkowa koda yaushe, sannan sunyi magana da wani likitan qashi a Dala zaizo gobe ya dubata shi da wani likitan kwakwalwa inma da yiwuwar a canja mata asibiti xuwa na Dala xa a canja" sukai godia ya fita. Audu ya dau Faty suka tafi ya kaita gida shima ya wuce nasa gidan.




Bature kuma ya miqe kan doguwar kujerar dakin ya fara bacci, yayin da mama da mumy sai lokacin suka zauna kan centre carpet din da sukaxo dashi suna cin abinci tare da jimanta ciwon Mimi. Mama kecewa "nikam Adda da anhaqura da surkudawa Mimi allurai mun koma gida anyi na musulunci don yadda Taheer yayi bayanin ciwonta kamar dasa hannu aciki" mumy tace "nayi wannan tunani fadima amma a bari xuwa goben muga farkowarta" Bature dake kwance yana sauraransu gabansa yayi wata irin faduwa, wannan shine abunda yake gudu ace xa aiwa Mimi maganin gida su riqe mai mata da sunan magani. Wlh kuwa baxai yadda ba ko sama da qasa xata hade, qafarsa qafar Mimi. Dan haka ya fara motsa kwanjinsa tun yanxu da cewa "mama maryam fa laulayin ciki ne ke damunta kawai, kuma tun a can munyi magani ta warke yaune abun ya dawo, munyi magana da wani abokinmu likita acan Germany ishaq na nema mana Visa ana samu xan wuce da ita can ayi duk abunda ya dace inta haihu ma dawo ki..... " mumy ta katseshi da cewa "Dan ubanka munsa da kai cikin maganarmu? Inka kuma saka mana baki saina zabga maka mari, karka nayi shiru akan abunda kayi kaxaci na haqura ka cuci banxa wlh saina maka hukunci, maryam kuma mu da kai naga wanda yafi iko da ita. Taqamarka daya dai matarkace ko? To ni kuma nina haifa na aura maka kuma innaga dama ina iya tsinka igiyar auren in aura mata wani tunda bakai kadai na haifa ba" jin haka yayi tsit, mama kuma haquri take bata.





Sun kwanta suna baccin suna farkawa sabida ko Mimi xata tashi. Qarfe uku dare nayi mama ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala da duqufa kan abun sallah tana nemarwa diyarta sauqi gurin Allah. Har akai kiran sallar farko shima Bature ya miqe yayo tasa alwalar ya fara nafilfili. A lokacin ne kuma Mimi ta tashi, tanata jijjiga gadon abunda ya farkar da mumy ta isa gurinta tana kiranta. Bature yayi gaggawar sallame sallar a xuciyarsa yace tabbas abunda mutum ya sabayi ko mutuwa xaiyi yana mutuwa akansa, tashin qarfe hudun dare yabi jikin Mimi ko a halin ciwo saita tashi.





Ya isa gurin Mimi wacce take kiran sunansa bakinta tar tana cewa "ya Bature xai kamani ka ceceni" abun dariya mumy ta hanashi qarasa kusa da Mimi ta shiga tsakaninsu tana cewa "kinga maryam bude idonki ki ganni mumyn ki ce a gida kike cikin kulawarmu babu wanda xai kamaki" itadai Mimi tunda ta hangi ya Bature ta bayan mumy take miqa masa hannu yaxo gurinta. Mama dake watching komai ta taso ta kamashi takaishi kusa da Mimi kana mimin tayi shiru tana qara damqe hannunsa kamar bata lura da wanxuwar su mumy a gurinba ko bata ganesu ba.




Yana shafa kanta dayi mata magana a hankali aka samu ta koma bacci.




Qarfe bakwai da rabi na safe ta kuma farkawa, lokacin dakin ya cika da yan dubiya kuma hayaniyarsu ce ta tasheta. Ta kwallah qarar kiran ya Bature, hankalinsu ya dawo kanta. Baffa da Dady suka matsa suna mata sannu, bata amsa ba ta fara sambatun a cire mata qafarta ta isheta da ciwo. Ta fincike qarafan da suka saka mata a qafar tana ihu, Faty tai saurin matsawa tana riqeta tare zare mata drip din karta jiwa kanta ciwo. Shigowar Bature tare da Dr yasa tai shiru.




Ya qaraso ya riqeta ya tadata zaune tanata sambatun ciwo, likitan ya fara aune aunensa tana dukansa da cewa ita ya kyaleta ya Bature ya cire mata qafar tunda yace ko babu qafa zai zauna da ita. Dr. Yace yana ganin afara kiran likitan kwakwalwa don matsalar brain dinta tafi tsamari yanxu don wannan abun da take shine matakin hauka na farko.





Kukan mama ya katse musu maganar da suke, inda take kuka tana cewa "wanene haka yayimun wannan aiki? Wanene ya jefemun yar da ciki a jikinta? Me maryam ta aikatawa wanda yayi mata wannan abu so ake ta shiga duniya da ciki kome?" Baffa ya taso ya riqeta yana bata haquri, Mimi sai lokacin ta lura da mama.




Tace "mama ki yafemun mutuwa xanyi, qafata da kaina ciwo sukemun. In na haihu a hayyacina koba a hayyacina ba na bar miki abunda na haifa duniya da lahira nasan xaki soshi ki masa tarbiyya yadda kikaimun" mumy da Faty suka saka kuka a tare. Likitan yace da Dady a ragu a dakin xaiwa Mimi allurar bacci. Amma Mimi tace "kar wanda ya fita akyaleta tai sallama da yan uwanta ta nemi yafiyarsu." lamarin daya saka kowa kuka a dakin.




Ta kama hannun Bature da Faty ta riqe gam tana hawaye, Faty ma kukan take, shi kuma Bature idonsa jajur. Mama ta matso tanawa Mimi adduoi tana tofa mata. Nan take Mimi ta rikice tana ihu ita batason wannan tofin tana qoqarin dukan mama. Bature ya tashi ya kama mama yakaita bakin kofa yana cewa "Dan Allah ku kyaleta tunda bataso, ya yarinya bata da lfy xa a xo a kama yimata tofi aka?" su mumy kallonsa suke sororo da alamu ya manta matsayin mama a gurinsa. Mumy cikin lallashi tace "Bature wannan ya nuna cewa ciwon Mimi iskace tunda batason a tofa mata ayar qur ani" ta kalli Dady tace "inaga Dady mu nemi sallama aje ayi na gida kawai" Baffa yace "haka ne dai dai Halima" take anan Bature ya hausu da fada cikin fita hayyaci yace shi babu inda xa akai masa maryam dan visarsu ta kusa fitowa zasuje Germany.




Dady daya lura dansa baya cikin hayyacinsa sai ya fara lallabashi da cewar ba rabashi xa a yi da Mimi ba just xa a riqetane na wani lokaci tanajin sauki xa a dawo masa da ita.




Ya fincike hannunsa daga riqon Dady yace "baxan baku itaba, meyasa kuke hakane? Kai rabaka da kai da taka matar? Sama da shekaru arba in kuna tare, sai ni dan mugunta xaku rabamu" ganin abun nasa ya wuce hankali mumy taxo ta zabga masa mari, Mimi ta saki wata ajiyar xuciya me kamada shaquwa. Mumy ta qara kifa masa

Please Login or Register in order to submit comment