Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna gyara dakin Mimi na xaune sun hanata komai sunce ta huta.



Suka gyara dakin tsaf safna ta ware kayan wanki ta hada wadanda suke buqatar sirri ta xuba a washing machine ta wanke ta shanya suka fesa turaruka masu qamshi. Sai yamma suka tafi.




Bai dawo gidanba sai goman dare, lokacin harta gaji da jiransa. Ya shiga wanka, ta bishi bathroom din, ta sameshi a bayan labule cikin shower ta rufe masai ta xauna akai tace "ya Bature har yanxu baka gama ba?" yace "eh Mimi luv, kinsan yau ango nake dole in cuccuda sosai" tace "hmmmm" kawai, ta gaji da jiransa tayi brush dinta ta fita taje tai shirin bacci ta kwanta.



Tajishi jikinta yana lasarta, ta watstsake ta kunna bed side lamp ta dubeshi. Ya sakar mata murmushi yace "Mimi luv ya kika tashi?" ta tureshi, ya qara shige mata yana romancing dinta tace "Stop it" yace "haba Mimi luv yaushe rabon da mu kasance haka" yacigaba da abunda yake, tace "fyade xakaimun ya Bature?"




Jim kalmar fyade data ambata ya tsaida abunda yake yana dubanta. Ta qara da cewa "lokacin da nake buqatarka ranar a kano ai qi kayi, amma yanxu dake kaine kake buqata kana qoqarin forcing dina" jikinsa sanyi qalau yace "wlh Mimi bana qi biya miki buqatarki bane wancan lokacin don toxarci ni kaina a lokacin ina da buqatar data fi taki. Amma na tuna cewar wancan lokacin kinqi na tilasa kika samu lalura shiyasa na haqura karnayi ciwonki ya tashi." ya janyota ya rungumeta yace "Mimi tun a wancan lokacin nayi alqawari baxan kuma ba, nayi na farko kinyi ciki, na biyu kinsamu lalura in shaa Allah baxan na uku ba dan bansan abunda xai faru ba" ya kashe masu fitila suka kwanta, sai taji tausansa. Tayi bacci ta barshi shikam sai da yayi da gaske ya runtsa.




Washegari bayan sunyi karatunsu na al qur'ani ya motsa jiki yaxo ya kwanta, ta dubeshi tace "yau baxaka fita aiki bane?" yace "nayi dauki hutun 1 wk" Yadukko tayi knocking tace "maryam fito kiyi wankan an sauke ruwan." tace "to" ta fita sukayi wankan harda turare ta dawo, ya dakko xumarta ya bata tasha suka koma bacci. Sai 10:00 AM suka tashi sukayi wanka da breakfast ya fita gurin cinikin gidan man. Kafin ya fita saida ta tabbatar Anty Rabi da Farida suka shigo.




Ranar ma cikin mutane ta yini dan safna ma ta kuma shigowa, sukayi ta riritata, ya Taheer ma ya shigo daya taso aiki. Safna har tausa tai mata, Mimi tana cewa "haba Anty safna ki bari mana Aisha taimun" tace "barni nayi miki matar yaya dan da bakyanan munga banu horonce mana yayi gara mu lallaba masa ke" yauma sai magrib ya dawo, tayi kwalliya tayi kyau. Sukaci dinner ya dunga lallabata duk sai taji ya bata tausayi, a take gurin taiwa kanta fada. Shin meke damunta har ta hana mijinta haqqinsa jiya? Bai cancanci haka ba a gurinta, mutumin dake sonta tare da tattalin farin cikinta, ta manta lokacin da Badaru yake kwanciyar wulaqanci da ita kuma daga baya yacimata mutunci. Tayi kuskure, ina laifin me sonka? Jiya ta kwana cikin tsinuwar mala'iku sabida gujewa shinfidar mijinta. Ta dunga neman gafarar ubangiji, ta juya ta dubeshi yana xaune kusa da ita yana matsa mata qafafunta dake kan cinyarsa. Ta gyara xamanta, ta dakko qafarsa ta dora bisa cinyarta itama tana matsa masa. Ya janye yace "barshi Mimi, keda baki da lfy?" ta kuma dawo da qafar kan cinyarta ta qurawa tafin qafarsa ido, jajur yake kamar qafar jariri yayin da qafar take fara sol kamar jikinsa gata doguwa mai dauke da yatsu dogaye, takai lips dinta tsakiyar tafin qafar ta sumbata. Ya lumshe ido, ya budesu ya kalleta tace "ya Bature ina sonka, kayi haquri abunda nai maka jiya ka yafemun na mata mummunar fahimta" ya jawota kan cinyarsa ya xaunar, yace "na yafe miki maryam tun a jiyan. Kuma wannan dalilin yasa nake kuma macewa akan sanki, sabida duk sanda kikayi kuskure kina saurin ganewa Kuma ki nemi afuwa" ta kwanta kan jikinsa tace "inka shirya nima na shirya amsa kiranka" ya miqe ya sabeta sukai bedroom.



Ba tare sun canja kaya ba suka fada gado, tunaninsa ya qare akanta, mace mai ciki sai bakai da gaske ba saita zautar dakai, an gurji juna ranar. Ya haqura badan ya gaji ba sai dan karya wahalar da Mimi luv, suka koma hira mai cike da soyayya kamar ba dare ba. Ya dakko wasu takaddu a drawer ya dawo ya kwanta yana fuskantarta. Ya miqa mata ta farko, ta karba taga takardar gidace a kano wanda yake unguwar Kuntau. Sai ta biyun ita kuma takardar gidan gonace itama dai a kano kuma duk malakarsa ce dan sunansa ne jiki. Ta dubeshi dason qarin bayani, yace "xabi daya acikinsu, inason mallaka miki" ta kafeshi da ido, kamar yadda ya saba yayi qasa da kansa, indai ta ware masa wadannan dangerous eyes nata sai yayi qasa da kansa dan baya iya jurewa kallonsu fitina suke haddasa masa. Tace "ni kuma ya Bature? Sabida me?" yace "sabida nayi niyya tun da dadewa, ginin gidanne ba a gama ba sai yanxu" tace "to, ka xabarmun wanda yafi dacewa dani ka bani, kasan bani da wani xabi sai naka" ya matsota yana murmushi yace "nasani Mimi luv, nima bani da mashawarcin daya wuceki. Ni a ganina ki xabi gidan, na gama komai anxuba kayayyki, part 6 a ciki kowanne sama da qasa, yan haya kawai xaki xuba kuma kayan sakawa kawai xasuje dashi, sabida kar a samu matsala ma bank na bawa gidan akan 500k kowanne part a shekara, su kuma xasu dora nasu su xuba yan hayar. Kinga kawai babu ruwanki da matsalar yan haya lokaci nayi xakiji alert. Inaga gidan xaifi kawo miki kudi akan gidan gonar. Ta shige qirjinsa tana hawaye tace "ya Bature nagode Allah ya qara budi ya rabaka da iyaye da duniya lfy ya baka xuria mai albarka. Allah ya sa kayi kyakykyawan qarshe." yayi mata wata irin runguma kamar xai ballata, yaji dadin adduarta sosai. Ya nuna mata vedio din gidan, ta dunga santin kyan gidan da tsarinsa lallai dole ace haya 500k wannan gida kamar hotel, tace "ya Bature gidan yayi kyau dama mu koma. Yaja hancinta yace "sai dai inkinaso in munje kano mu sauka ciki mu kwan biyu kafin asa yan haya." Ya dago fuskarta daga jikinsa yace "amin Mimi luv, amma ki nunamun godiar a aikece mana" ta gane nufinsa. Ta baje kwanyarta ta ajiye kunya guri daya ta fara masa wata salon soyayya, ya xauce mata tunkan aje ko ina ya fara surutai. Sai data tabbatar ta cire masa duk wani kwadayi akanta sannan ta kyaleshi.




Ya dubeta cikin burgewa yace "kai! mimi luv kin hadu fa qarshe, shiyasa akemun yanga ko?" taja karan hancinsa tace "hmm, ni mamakinka nake. To lokacin da bananan ya kakeyi" yace "Mimi ai sai da kwanciyar hankali sha'awar ke xuwa. Wlh lokacin ko kadan bana tuna wani abu wai sex, ke nifa lokacin inaga mace na xama" ta sheqe masa da dariya, ya dauketa suka tafi wanka suna fitowa suka fara nafilfili dan shima yanxu baya baccin dare inbai sallar ba bayajin dadin bacci Mimi ta tarbiyanceshi akan hakan.



Washegari yana gida, ita kuma Farida ta shigo suka hauka hau hira. Farida ta fara fada mata kasuwancinsu, bayan kwanciyarta ciwo kaya sun qare a shago ansamu riba sosai amma ancire albashin yaran dake jiran shagon ragowar kuma ishaq ya hada a uwar kudin aka kuma sayo Kaya. Mimi tace "to hakan yayi Allah ya saka da alkhairi" Farida ta kuma dakko jakar leda ta dunga fidda kudi kowanne tasa sunan wanda ya kawo da kuma adadin daya kawo ajiki. Tace "gashi kudin kayanki ne aka dunga kawowa, wasu anbawa Bature ragowar kuma gasu. Duk kayan sun qare kuma ana nema, tunda kin samu lfy sai a saro kayan kar business ya raunana" Mimi ta karbi kudin ta ajiye a gefe tace "to nagode Allah ya barmu tare" Farida ta dubeta tace "naga kin ajiye baki qirga ba" Mimi tayi murmushi tace "dan kin bani abu harsaina qirga Farida? Ban yadda dakeba kenan? Allah ya sawaqe abun duniya ya hadamu" Farida tace "hakane besty, Allah ya qara hada kanmu" Mimi ta dakko mata takaddun gidan da akai mata kyauta jiya ta nuna mata.



Farida ta dunga godia da murna kamar ita aka bawa ta riqe hannun Mimi tace "maryam kinji dadinki, Allah ya daukaki sakamakon haquri da juriya da kuma miqa lamura gareshi. Haqiqa rayuwarki darasi ne ga wanda suka sanki kuma suka san tarihin rayuwarki. Muma gashi da muka rabeki muka kuma koyi wasu halayenki munacin albarkacinki Allah ya saka da alkhairi ya barku tare da sulaiman." tace "amin Farida"




Rayuwa me dadi cike da soyayya suke kamar yadda yayi mata alqawari ga wata kulawa ta mussaman. Yadukko tsaye take kam akan maganin Mimi, kuma Bature yayi musu baxata dan be hana aiwa Mimi komai ba wani sa'inma shike dafa maganin wanka kuma yayi mata. Basa xuwa awo daga ita har farida gida ishaq ke turo wata nurse tai musu har makarantar rainan ciki ishaq ya sakasu wadda suke xuwa weekend kuma kowacce dole saida mijinta take xuwa yana ganin yadda suke exercise din masu ciki kuma har yadda ake kwanciya da mace me ciki ake nunawa maxan. Abunda yake musu dadi be wuce ganin yadda cikin Mimi ya tashi ba yayi girma kamar jira yake a dawo gidan babansa cikin qanqanin lokaci da dawowarta. Duk sanda akayi maganar cikin ya girma indai ba a gaban wadanda yake tsananin kunya bane yakance "ai allura nake masa safe da dare shiyasa yake girma" Mimi inya fadi haka kunya tana kamata. Amma fa da gaskiyarsa domin ta sakar masa jikinta suna gurxar amarcinsu jaraba yake sosai ita kuma bata iya hanashi sabida son da take masa.



Yadaukko ta fuskanci Mimi sosai, sai yanxu ta gane sirrin soyayyar da mumy ke mata. Wato Mimi wata irin yarinya ce me dattako da kirki kuma da wuya ka xauna da ita bata shiga ranka ba domin irin mutananne masu tsananin kirki, da kirki na yawa da saitace yayiwa Mimi yawa. Da wuya tai maka abunda xai sosa maka rai, inkuma tayi bisa ajixanci irin na dan Adam takan gaugauta baka haquri da neman yafiya. Xaman da take dasu Kullum cikin tambaya take "yadukko me kikeso? Me xa ai miki? Me xan miki? Ko inmiki tausa?" yadukko kanji kunya duk sanda Mimi take mata haka, takance "maryam keda aka turoni kula dake saiki bige da bautamun?" ta fuskanci abunta bai rufe mata ido ba, hannunta sake yake komai yadukko waja waja ake mata, kai maryam bata tsaya nan ba ko ma'aikatan gidanta mai kirkice da sakewa dasu kuma ba yadda zasu rainata ba. Yadukko dai tace taga gurin xama, xata xamanta anan yaranta duk wanda ke buqatar gaaninta yaxo ya ganta. Inda ake ganin mutuncinka ake kulawa da kai a nanne gurin xama. Kuma akai dace yadukko tana jan girmanta sosai, bata shiga sabgarsu inka ganta falo Mimi taxo bawa magani ko dubata ko sun hadu ana hirar weekend, tafi gane taje can baya gurin tsaffin gidan masu aiki susha hira irin tasu ko tana daki tana kallo.




Me gadin gidansu wanda Kullum xaka ganshi da qur'ani yana karatu kuma yana aikinsa na gadi yana tofa abunda yake karantawa a ruwa Kullum ya aikowa da Mimi shi, ita kuma babu kyamata takesha.




Kwanansu goma sha biyar da tafiya, mumy tana can hankalinta duk yakasa kwanciya duk da Kullum cikin waya suke da vedio Call. Daren alhamis taiwa mama waya da umartarta ta shirya gobe in sun dawo aiki an sakko juma a xasu tafi Abuja da ita da mumy din ganin jikin Mimi, mama tace "Adda indai kinje ai shikenan," mumy tace "aiko sai kinje kin gano diyarki itama ta ganki taji dadi, bayan haka ma ai baki taba zuwa gidanta ba yanxu kam kyaje dubiya da ganin daki. Kuma ban yarda ki fadawa Bature ko Mimi xamuje ba, so nake muyi musu baxata muga yanayin xaman nasu." tace "to Adda Allah ya kaimu, bari inje in fadawa Baffa"





Tana fadawa Baffa ya amince, harda cewa "gobe da safe ki dunamun insa akawo kwan zabi a gidan gona, ni kuma inna fita xan aiko da danyar goba ai mata tsaraba. Ai gara kuje nima jikin nata yana raina da akusa ne da duk kwana biyu saina leqa" mama taji dadi tace "to shikenan Baffa angode"





A ranar andata mama zaune tsaye, ta dunga aike kasuwa ana siyowa Mimi duk abunda takeso, ta daka mata yaji barkono da daddawa, tai mata alawar madara, kantu, ta siyo mata manja a sabon gari me kya, kana hada mata garin dan wake. Tana aikinta cikin nishadi tana ayyana gobe inyanxu xataga miminta, kai! Allah ya sakawa Dan uwa da alkhairi wato Adda halima kamar ta shiga xuciyarta taga da tunanin Mimi take kwana take tashi kawai dauriya take. Taiwa Faty waya ta fada mata gobe xasu Abuja ta turo a dau Dady sabida makaranta. Faty ma tace xata aiko driver da kaya akaiwa Mimi sai atafi da Dady.



Driver yaxo, Faty ta bada tsakin masara akaiwa Mimi, da busashshiyar rama, bushashen kifi, kafikaxa cikin bokiti sai nama soyayye cikin samira wanda ta lura Mimi tanaso kamar me ta xuba mata kakidi akai. Mama ta dunga yiwa Faty godia a waya tana roqon Allah ya qara hada kansu. Ta debowa Mimi kayan data dinka mata, maternity gown wanda take shiga kasuwa da kanta ta siyo cotton materials masu kyau da laushi wadanda basu da damu ajikin me ciki sabida zafi taxo ta xauna ta tsantsara masu dinkin dogwar riga me kyan gaske wacce xata sake aciki kuma zatai kyan kwalliya, wanda duk gayun mutum inga rigar xaiyi shaawarta. In Faty nada ciki take siyowa tai mata, tun Mimi bata da lfy ta siyo bata dinka ba har suka tafi babu shiri. Yanxu ma ba duka ta dinka ba, guda 7 kawai ta samu dinkawa da tasan da tafiyar da tayi qoqari ta dinka mata duka. Ta gogesu tsaf ta hada a kayanta.



Ranar juma a ana sakkowa masallaci mumy ta iso da ita da drivern da xai kaisu. Itama kayane niqi niqi, dambun nama tasa akai da uban kilishi an nadeshi a qatuwar takadda kamar sutura da gireba bokiti guda. A cewarta kwana daya zasuyi, in sunga lfyarsu gobe xasu juyo gida.



Umma ta kalli uban himilin kayan da ake futa dasu da sunan xa a kaiwa Mimi kawai, a xuciyarta tace "wannan yarinya da gata take, ita halima ko irin kishinnan da surukai batayi.



Suka dau hanya, drivern mumy babu wasa ya dunga sharara gudu dasu. Basu isa ba sai dab da magrib rana na gab da faduwa.




Basu tadda su Mimi gida ba, aka dunga shiga da kayan da suka xo dasu cikin babban falo. Baqo ya rasa ina xai saka mumy, ya dunga zarya tsakanin kitchen da falo sai da yaga ancika musu gabansu da kayan taryar baqi. Yaxo kusa da mumy kamar xai mata sujjada yace "mumy sannunku da xuwa, yanxu kuke tafe ya hanya?" ta amsa masa suka gaisa da mama. Yace "oga sun fita da madam babu jimawa, amma nasan duk inda suke suna hanya tunda ankusa kira. Bari in kirashi a waya" ta tsaidashi tace "kyalesu muna son musu surprise ne" yan aikin gidan suka dunka xuwa gaida mama da mumy suna cewa "ga babar madam da oga."



Mama kallon aljannar duniyar da Mimi ke ciki take, tana godia ga Allah ya xuciyarta. Ashe duk yadda ake fadamata kyan gidan Mimi ya wuce faduwa a baki. Ta dunga kallon hotunan su Mimi da Bature dake falon, ta kuma kallon pics dinsu ita da Faty da Mimi ranar yinin auren Mimi wanda sukasa kaya iri daya.



Yadukko ta shigo suka kuma kacamewa da murna ana gaggaisawa, mumy kallon yadda yadukko ta canja take acikin kwanaki 15, tace a xuciyarta wannan yarinya Allah ya saka mata da alkhairi, kalli yadda yadukko ta janxa a cikin qanqanin lokaci.



Suna kiran sallar magrib suna shigowa, basu lura da mutanen dake falon ba. Sun shigo suna yar rige rige ita dashi, ya rigata tace ita bata yarda ba suka kuma komawa baya, dai dai qofar shigowa falon. Ya kuma rigata tasa kukan shagwaba wai ita wlh wayo yake mata. Su mumy na kallonsu cikin mamaki. Little tace "ya Mimi, kece baki ganeba dan yafiki tsaho ne sosai shiyasa ya fiki sauri, duk takunsa daya a matsayin naki uku yake" ta dago ta qurawa little ido kamar a mafarki take ganin su mumy yau a gidanta. Bature kuwa baiyi mamakin xuwansu ba don yasan dole mumy xata biyo sahun Mimi.



Mumy tai qasa da murya tace da mama "fadima kinga yayan xamani, yarinya munacan muna tattalinta dan ganin ta dawo hayyacinta abu ya gagara amma dubi cikin yan kwanaki mijinta ya gyarata" mama tace "hm Adda nima tunanin da nake kenan, yaran yanxu sai su baka kunya, yadda Mimi ta nuna tanason biyoshi ai ko bamu yarda ba sai ta saci hanya ta gudu"


Ta tafi da gudu, mumy tana cewa "hankali, yi a hankali maryama" bata kula ba, taxo ta hadasu duk ta rungume tana cewa "mumy na, mamana, my little u'r highly welcome" suma suka rungumeta. Shidai alwala yayi ya tafi masallaci. Suma Mimi ta jasu dakin kusa da nasu ta kai musu kayansu sai dataga sun tada sallah kana ta fito, a gurguje tai wanka tayi sallah ta fito kitchen. Taji dadi da taga Baqo yasa an qara abinci sannan an kuma wasu abubuwan sabida xuwan baqi. Suka dunga xarya saida ta suka cika qatuwar ledar cin abincin data shimfida a falo sannan ta koma daki tai sallar isha.



Yana shigowa tasashi wanka tana axalxalarsa yayi suka shiga dakin su mumy suka dattasu gaba daya akan gado suna hira. Suka rankaya falo. Akai gaishe gaishe, Mama kalan diyarta take yadda tayi shar kamaninta nada sun dawo kamar ba mimin datasha jinya ba. Mumy ma ta yaba da yadda ta samu su Mimi, sai yanxu hankalinta ya kwanta. Cikin da suke qorafin baya girma ya tashi yayi kurcici ya turo gaba sosai. Mimi ta xuba musu abinci suka faraci, wani irin farin ciki take yau gata ga mama a gidanta, ga kuma mumy uwarta kuma surukarta.




Bature ya kalli mumy yace "mumy kinxo supervising kenan?" ta watsa masa harara tace "eh shi naxo mara kunya, Bature ka kiyaye ni, na fuskanci tunda na wanke Mimi na baka raini ya shiga tsakaninmu" yana dariya yace "nidin banxa mumy? Tuba nake"




Mama ta kalli yadukko tace "yadukko dama kiyi xamanki anan cikinsu" Bature yace "ai dama taxo kenan mama, nan xata xauna ta samu miji in aurar da ita" suka sheqe da dariya. Yadukko tace "qaniyarka, bakaine mijin ba, ko inada wani bayan kai"





Sunsha hira, suka fito da tsaraba, Mimi ranar tayi ciye ciye, in ta fara cin wannan aka fito da wancan saita koma kai. Suka koma daki akai shirin bacci. Suka dawo aka kuma xama dakin su mumy aka kafa wata hirar, yadukko tana fada musu irin xaman da suke da kulawarsa ga Mimi. Mama tace "aiko baki fada ba yadukko, ga yarinya nan tayi shar daga dawowa"





Har wajen sha daya basu tashi ba, mumy tace "ku tashi ku tafi dakinku, muma mungaji kwanciya xamuyi" Mimi tace "mumy babu inda xanje wlh, kuxo intafi in barku? Ta miqe ta dakko manyan barguna ta shimfida musu ita da little a qasa yayin da su mumy ke kan gado. Shima Bature ya saka filo akan sofa yace "nima baza a wareni ba, gara ayi dafaduka." babu yadda mumy batayi ba su fita sukaqi dole ta kyalesu. Ya ciro wayarsa ya kira Anty mami vedio Call. Suka hadu gaba daya ana hira da ita. Ta dunga murnar ganin jikin Mimi yayi kyau tace "kai nayi farin cikin ganinku haka inama ina kusa. Tace da Mimi. "Mimi cikin na motsi?" kunya ta hana Mimi bata amsa, sai Bature ne ya bata da cewa "eh sosai ma kuwa" tace "kuje a duba Baby girl ne ko boy, inason yo siyayya gaba daya dan nagama siyan unisex." yace "to anty mami" bakinsa yaqi rufuwa sabida kulawar da yaga Anty mami na bawa Mimi




Su mumy da sukaxo da nufin tafiya washegari dole suka haqura da tafiya, sabida ko goman safe batai ba gida ya cika. Safna ta shigo, ishaq da Farida, ya Taheer da sauran yan uwa na kusa. Suka xauna akayi break fast tare cikin jin dadi. Farida da Mimi dai sun baje tsarabar su mumy sunaci babu ji babu gani, ishaq yanata warning dinsu da kar abunda sukeci ya bata musu ciki amma a banxa dan saida sukayi qat kana aka tashi daga falon masu aiki suka hau gyara. Haka aka yini a gidan cikin farin ciki, sai lokacin sallah maxan suke fita in sun idar su dawo. Mimi xata iya cewa tunda take a rayuwarta bata taba lokaci mai dadin wannan ba, gata ga iyayenta da yan uwanta kuma acikin gidan aurenta da mijinta. Itadai tana qaunar mutane kusa da ita, kuma akai dace mijinta ma yana da son mutane suka hadu suka gina gidansu da soyayyar yan uwantaka. Suma su mumy basu wani damu da qara kwanan ba, dan ganin farin ciki a fuskar yayansu ya kori komai.



Sai yamma liqis aka watse daga majalisar kowa ya nufi gidansa. Mama da Mimi suka samu kebewa a dakin su mimin, ta rungume mama tsam tace "mama ina sonki, kinga muhallinmu ko?" mama ta rungume diyarta tsam tace "maryam nima inasonki, naga gida, Allah yasa albarka ya qara hada kanku ya baku xaman lfy. Ki kula da ibada, karkiga Allah ya kawoki wannan matsayi ki ki wulaqanta wani kowa naki ne kuma ki riqe ibada, ki tarbiyanci danki tun aciki duk abunda kikasan bakyason danki yayi tun daga yanxu xaki gujeshi shi Dá tun a ciki ake tarbiyarsa." tana kwance kafadarta tace "To mamana duk abunda kikace xanyi. Kuma in shaa Allah baxan wulaqanta kowa ba kome na xama a duniya, ai nasha nononki na xuqi kyakykyawan dabi'a" tace "mashaallah uwata banxaci xan ganki haka ba" tana dariya tace "mama ai ya Bature dan halak ne, yana kula dani sosai, adduarku kawai ita xakucigaba dayi mana" haka sukaita hira irinta ya da uwa.



Sukai sallah har isha kana suka shirya suka fita a mota. Mama, mumy da little a baya sai Bature dake gefe Mimi na driving. Sukaje store ya dunga yimusu siyayyar tsaraba kamar hauka. Suna fitowa Mimi tace "mumy bari na kaiku boutique dinmu ku gani" tace "to Mimi" suka nufi shagon, haske tanyar kamar rana anata shige da fice. Yaran gurin na ganin Mimi suka fara sunkuyawa suna gaidata. Aka sama musu guri suka xauna, mumy sun kewaya gurin sun yaba sosai da tsarin gurin. Mimi tace sudau duk abunda sukeso, suka qi, ta daukar musu arabian gown, little kuma Mimi tace ta debi Kaya ta saki jiki ta lodi english wears sosai.



Yauma guri daya suka kwana, washegari suka kuma kaiwa har azahar kafin suyi haramar tafiya. Mimi

Please Login or Register in order to submit comment