Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

allurar da akai mata oho? Ta dakko shaving cream (veet) ta shafa a jikinta ta qalqale gashin. Ta salla wankanta da mayukan wanka da subulai, ta dauki sabon pant a drawer ta manna pad ta saka. Ta gyare jikinta da mayuka da perfumes masu sanyin qamshi, ta dauki doguwar rigar atamfa a kayan Faty ta saka. Tai mata cif sakamakon ramar da tayi, ta danyi simple make up ta fito tas da ita.


Ta iske Faty da Ahmad da yaran zaune a parlour suna kallon drama (madhubala) a mbcbollywood. Tace "ya Faty har lokaci yaja haka baki tasheni ba? Tace "sry Mimi shigata biyu da nufin in tasheki saina tarar baccin ya muki dadi shiyasa na gyaleki. Ta samu guri kusa da Faty ta zauna, suka gaisa da Ahmad, ya jajanta mata jikin sannan ya zarce da yi mata nasiha. Dan har ga Allah yanason Mimi ganinta yake kamar uwa daya uba daya suke, tunda shi bashi da yan uwa.


Taje fridge ta dakko robar ice cream ta dawo ta xauna tanasha suna hira. Ji take kamar karta tafi dan xaman yayi mata dadi. Ahmad ya kalli Faty yace, tashi ki kaita gida kada muyi rashin hankali. Faty ta yunqura tare da miqawa Mimi wata leda tace kinga a siyayyar da mukai kin manta baki dauki masuka da turare ba shine na koma na siyo miki" Mimi ta leqa ledar taga muyakan da take amfani dasu ne cocoa butter (palmers) Set dinsa har sabulunsa sai turaren da take amfani dashi da sure na feshi da sauran spray. Ta dunga godia.


Sai da Ahmad ya bata 10k, sannan ya jaddada mata duk sanda take buqatar taimako ta fada, kada ta qara zama ciwo yaci jikinta haka. Saida Ahmad ya temaka suka saka kayan a mota saboda kayan da yawa. Har sun fara tafiya Faty ta tuna da fankar da tasa chaji, ta dawo ta dauka. Suna tafiya suna hira cikin nishadi ta dauki jakar Mimi ta saka mata ledar magungunan da suka siya tare da kudi sannan ta qara da cewa gashinan ki kula, ki rabu da namiji ki dainasa baqin cikinsa a ranki, lfy tafi komai kuma shi kansa inbaki da lfy bazai zauna dake ba, so dat ki lallaba lfyarki.


Suka tsaya yahuxa suya dake kabuga ta sai mata kaza da furar habib. Kafin suje gida anyi sallar magruba saboda sun tarar da hold up.


Suna gama shiga da kayan Faty ta juya gida. Mimi da bata sallah xataiba da kimtsa kayan takai kowanne muhallin daya dace. Tana zaune tana lazimi aka kira sallar isha ta tashi tasa kayan bacci dan jikinta fes yake bata buqatar wanka. Bata damu da dawowar Badaru ba domin ya kunna inji, ta kunna fankarta wacce tai chaji full. Iskar fankar na kada ta tana danna waya (chating) a zuciyarta cewa take "Allah ya sakawa yaya Faty da alkhairi badan taimakonta ba da tuni ina zaune cikin zafi.


Takwas nayi ta balli maganinta tasha dama tana timing. Ta janyo kazarta ta bude ta fara ci da bisimillah. Qarar injin da taji ya tabbatar mata da dawowar Badaru, ya shigo dakin yayi tozali da Mimi. Idonsa fes akanta saboda hasken wutar lantarki, tayi masa kyau ainun kamar sake masa ita akai.


Yayi saurin qarasawa gabanta tare da cewa "maryam sauki ne ya samu haka da wuri? Sannu" ta danyi murmushi tare da gaisheshi. Ya amsa idonsa na kan ledar gabanta wanda qamshin kazar ya cika dakin, yace " harda hidima haka? " ta amsa da cewa "eh yaya Faty ce tasaimun da wannan fankar (ta nuna masa fankar) yace " to madallah haj Faty kenan bataso kudi su zauna lfy" (kuji banxa🀣)


Ba kunya ya tayata suka cinye kazar sukasha furar, lamarin da yayiwa Mimi dadi. Domin yaune rana ta farko da suka taba cin abinci kwano daya da Badaru.


Yana ta kallon Mimi wai ta burgeshi qarshe, ya kalli qafarta yar dundubus da ita har tafi jikinta haske yatsunta kansu abun kallone be taba lura Mimi takai haka ba sai yau (dama ya xa ai kasani? Wahalar gidanka tasa tayi kaushi) ya ruqo hannunta yana murxawa cikin shauqi "maryam tashi muyi shirin kwanciya" ya fada yana mai qura mata ido. Azuciyarta tai masa dariyar mugunta, saboda tasan bata da tsarki.


Ba musu ta miqe taje tai brush, shima ganin tayi yaje yayi amma ba batun wanka duk kuwa da tsamin ranar da yake. Ta feshe jikinta da turare ta kwanta hankalita kwance yau ba kawo farmaki 😜.


Tayi mamaki kwarai da taji ya kashe inji, ya shigo dakin yana me cewa tunda ga fanka ai sai man injin ya huta. Yana hawa gadon ya kamata ya rungume yana shafar gashin kanta yana cewa "maryam kinada shiga rai, komai naki me kyau ne" tadan motsa bakinta cikin sigar murmushi har dimple dinta ya lotsa. Lamarin da Badaru yaji ba abunda yake muradi illah ya hada bakinsa da nata. Amma yasan bazata yadda ba shiyasa beyi yunqurun hakan ba, domin yau hakanan yaji bayason batawa maryam rai.


Ganin abun nasa yana nisa yasa tace masa bata da tsarki, atake ya saki wani mugun tsaki tare da tureta daga Jikinsa, ya koma gefe ya kwanta. Dama hakan take jira dan haka ta gyara kwanciyarta ta maida fankar dai dai saitinta tai adduar kwanciya bacci.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣4⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)


Tasamu canjin rayuwa saboda taimakon Faty, ta rabu da matsalar zafi saboda fankar da Faty ta sai mata. Koda babu wuta takan bada fankar da 50 naira akai mata wani company dake bayan gidanta kadan mai gadin gurin ya karbi hamsin din yasamata caji, saboda company ne basa rabo da wuta.


Sai dai da yake rayuwa indai kai imani baka rasa jarrabawar ubangiji, sai wata sabuwar matsalar da bullo mata. Matsalar kuwa itace; kawo abokai da Badaru ya tsiriyi cikin gidan saboda yaga cimar gidansa ta canja (ansamu mai dadi).


Ba kawo abokan nasa ne problem dinba ko kuma abunda zasuci, cin mutunci da toxarcin da Badaru keyi mata agaban abokan nasa shine babbar matsalar.


Sau tari zai cika gidan da abokansa duk kuwa da qanqantar gidan, wanda hakan ke hanata sakewa sai dai ta takure kanta adaki. In fita parlour ta kamata ko duba girki sai dai ta saka hijabi, har mamakin inda ilimin addininsa yake take domin babu addini sam acikin abunda yake, kodan ya takura mata yake hakan? Sannan bayan tayi hidima dasu da jikinta da aljihunta (domin babu ko sisinsa aciki) sai kuma ya dunga zaburarta yana daka mata tsawa agabansu, a qoqarinsa na nunawa abokansa cewa ita din bata isa komai ba.


Yauma hakace ta kasance, domin tare suka shigo da wani abokinsa sani around 5;30 pm. Suka taddata zaune parlour ta tasa fanka agaba tana shan iska, a xuciyarta bata gajiya da yiwa wacce ta sai mata fankar adduar alkhairi (ya Faty)


Tai saurin miqewa ta shige daki da nufin suturta jikinta, domin shimice kawai a jikin nata. "kinaji ana sallama dan rainin hankali baxaki amsaba" cewar Badaru. Sani abokinsa yayi saurin tareshi da cewa "bakaga hijabi zata dakko ba, laifinane dana shigo kai tsaye ban tunanin halin da xan taddata ba" ta fito sanye da jihab me hannu tana cewa "sannunku da xuwa" ta gaishe da Sani, sannan ta nufi kitchen ta qara sanwar abinci dan ganin baqo, ta debo musu ruwa da kwalin exotic ta dora akan tray ta glass cups ta kawo ta koma daki ta zauna.


Tananan zaune tana yan danne dannen waya taji xuwan wasu abokan nasa har su 3 domin taji ya ambaci sunayensu. A xuciyarta tace yau kuma anan xa ai mana zaman majalisar kenan.


Ta tashi domin ta duba abincin data dora, ta gaishesu ta wuce kitchen. Ta gama komai ta maida miyar kan gas domin ta qara dumamata ta jiyo Badaru na kwala mata kira, ta fito parlour ta dan durqusa gefensa "gani" ya dubeta yana wani daga hanci yace " ke wace irin mahaukaciyar mace ce mara tsari? Bakiga nayi baqi bane? Ko sai nace ki qaro wasu kofunan da lemon? Banason dabbanci." Ba tare da tace komai ba ta miqe taje ta kawo wani kwalin lemon da kofuna ta ajiye, tana shirin juyawa yace " abincin ma sai nace ki kawo ko? To karki kawo" tai saurin xuba abincin a warmers har tana qonewa saboda kar wani cin mutuncin ya biyo baya. Domin tana jiwo shewar abokan nasa, suna yaba masa yadda yake tafi da ita. Har wani a cikinsu wanda bazata iya gane kowaye ba yana cewa "da kyau mutumina haka akeson mutum ya xama jan wuya a gidansa"



Ta hada musu komai na abincin a gabansu, sai da ta tabbatar ta hada komai sannan ta nufi daki. Badaru yayi saurin katseta da cewa "waye bawan gidanku anan dazai zuba musu? " ta duqa a takure take saboda kallon da wasu acikinsu suke mata, xata fara xubawa Sani yayi saurin katseta da cewa "a a jeki maryam mungode kowa zai xuba nasa" dan ya lura a kunyace takeyin komai.


Badaru yace "a a ta xubawa kowa umarnina ne, ni naga damar haka. Tana gama xubawa ta miqe ta shige daki. Sani ya dubeshi ransa adan bace " ka daina haka Badaru, wannan yarinyar kyautace Allah ya baka ka riqeta da amana ku zauna lfy. Yawanci yaran yanxu basu cika bin miji haka ba, bare ita da take da xurfin ilimi" Badaru ya daga murya, domin yanaso Mimi ta jiyo abunda zaice "yo ni ina ruwana da ilimin mutum, ko parpesa ce ita bai dameni ba domin miji ta rasa na taimaka mata na aureta, inba dan nidinba da tuni tanacan a jabe gidan ubanta"




Yayi sa a kuwa domin duk maganar da suke akan kunnen mimin sukayi saboda tana da ji sosai, kuma dakin bashi da xurfi. Hawaye ya wanke mata fuska, lallai yau wulaqancin na Badaru yafi na koyaushe. Muryar daya daga cikinsu ta katse mata tunani inda yake cewa "au wai kana nufin tana da ilimi? " Badaru ya bashi amsa da cewa "degree ne da ita akan fannin sharia" wanda yayi tambayar yace "Tab ai wlh gwanda daka riqe mata wuta daka sake mata rainaka zatayi musamman intasan tafika ilimi mata yan boko mugayen yan rainin wayo ne. Kai kuma sani da kake wani xance ai mata xuma ne da wuta ake cinsu" Sani ya balla masa harara yace "inkasan ba shawarar arziqi zaka bayar ba ka daina xuga xugagge yana ciwa yar mutane mutunci"



Badaru yayi saurin tareshi cikin hargowa "kaga sani ya isa, ni ba wani wanda yake zugani haka nayi niyyar tafi da gidana kuma haka nakeyi. Intaga xata iya xama dani a haka ta zauna, in kuma bazata iya ba sai in mata saki daya taje gidan nasu ta dandana xama taji. Ai tasan rufa mata asiri nayi, kaf gidansu ita kadaice budurwar data rage. Sannan tace xata kawomun wani fi ili? Bokon banxa bokon wofi meyasa bokon nata be bata mijin aure ba. Wlh ko shugabar qasa ce ita dole ta bini yadda nakeso intaqi ga hanya nan. Nasan kina jina MARYAM in bazaki iyaba kixo ki tafi gidan ubanki."


Duk yanda taso danne xuciyarta abun ya gagara kuka take wurjanjan, batasan yadda akaiba sai ganinta tayi a parlourn adai dai lokacin da yake cewa "ai kinsan yadda kika sha wuya kika zaunu kafin Allah ya kawo miki ni na aureki, ki qoqari ki kashe auran kina budurwa ma kin rasa miji bare kina BAZAWARA."




Sai a lokacin ya ankara da wanxuwarta a parlourn, ya kalli idonta da fuskarta gabansa yayi mugun faduwa domin bai taba ganinta cikin wannan yanayin ba duk abunda yake mata.



Sani yayi saurin shan gabanta ganin ta nufi qofar fita, a qoqarinsa na dai daitawa, yace MARYAM Dan Allah dan darajar iyayenki kiyi haquri kar fita. Ta tsaya cak! Badaru dake gefe ya saukewa boyayyar ajiyar xuciya ganin ta tsaya.



Sani yace Badaru, beye lefin yarinyar nan? Saboda ni kayi haka? Daga gaya maka gaskiya xaka ci mata mutunci haka? Lefin me tayi maka?


Mimi ta matso kusa dashi ta kalleshi, yai saurin yin qasa da kansa. Tace cikin nutsuwa da qarfin zuciya " kayi haquri qaddarace ta hadamu, amma karka manta kai ka ganni kace kanaso ba talla aka kawo maka niba. Kuma tabbas miji na rasa shiyasa na aureka, inba dan haka ba ai babu wacce xataso xama da namiji irinka. Kuma da Allah ya hanani miji daga baya ai yabani kai? To haka nake sakaran duk renda Allah ya sa ka rabu da ni Allah xai bani wani mijin. Gari da yawa ai maye bayacin kansa Badaru. In shaa Allahu yadda Allah ya doramun jarrabawar xama da kai xai bani ikon cin jarrabawar, wlh nima ba Jin dadin xama dakai nake ba. Allah ya na madakata yana jiranmu kuma zai mana sharia"



Simi simi daya bayan daya abokan nasa suka fice, kodan kada aure ya mutu ace ta sillarsu ne. Ya rage sai Sani kawai, ya kalleshi yace "yanxu wannan abun da kayi me gari ya waya? Burgewa kayi? Ka tauna asirin gidanka a idon duniya. Allah ne kadai yasan inda wannan zancen zai tsaya, kuma tunda da wata niyya kake kawo abokai gida daga yau babu abokin da xai kuma xuwa gidanka. Ya juya ga Mimi yace MARYAM kiyi haquri, anbata miki Allah ya baki haquri ya huci xuciyarki." ya juya ya fita.




Tunda ta shiga daki bata qara fitowa ba sai da akai kiran magriba ta fito alwala, ta taddashi zaune a yayi tagumi. Daganan bata qara fitowa ba har wajen 9:03 taji ya tada inji tayi shirin kwanciya ko wanka bataiba bare cin abinci dan ranta har yanxu a bace yake.


Tanajin lokacin da yaxo ya kwanta kusa da ita, tai saurin rintse ido. Dan jitayi wata irin tsanarsa ta taso mata. Bata tabbatar da Badaru bashi da kunya ba sai da taji hannunsa a jikinta yana lalubarta. A tunaninta yau zai haqura tunda sunyi sabani, amma ina mayen ya kasa haquri duk kuwa da ya gwada yin haqurin ya kasa. Tai masa banza taqi bashi fuska, take banxa ne sai ya fara qoqarin gwada mata qarfi zai shigeta, a salonsa na kwanciyar awakai. Ta qanqame jikinta ta hanashi yin hakan, dole qanwar naqi yayi amfani da lallashi ta hanyar cewa "maryam dan daure ki barni nayi, na kasa bacci kinsan na riga na saba" sama sama ya samu nutsuwa ba kamar yadda ya saba ba.




Ya koma gefe ya kwanta yana tunanin da maryam din ta tafi dazu da ya zaiyi? Dole ya sake taku, kodan lalurarsa ya xama dole ya zauna da maryam dan bayajin xai iya haqura da buqatarsa koda ta kwana daya ne. Dan yana sahun mabuqata ga kuma qarin magunguna da yake sha, bayan haka kuma bai gama more kudinsa ajikin maryam dinba.



Duk da bata taba turje masa a gurin kwanciya ba sai yau, amma yana mamakin duk sanda ya batawa maryam rai to ranar baya samun yadda yakeso ajikinta. Duk da kuwa ba hanashi takeyi ba, amma duk qoqarinsa baya gamsuwa. A fili yace dole in gyara lamura na da maryam kodan shimfidata.


Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣5⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Su 3 ne kawai zaune a majalisar, Badaru, Mekudi sai wani abokinsu da suke kira KB. Hira suke yayin da KB ke daga gefensu kadan yana karatun news paper. Badaru ya kalli Mekudi yace "ya babu lbr ne? Na jika kwana biyu shiru? " Mekudi yayi wani shu'umin murmushi sannan yace "yo ni ana raba ni da lbr ne? Kamar ka shiga xuciyata ansamo wani be zafi, amma fa a tube yake ita zaka matsa ka cusawa kafin ka shiga, sauran bayani kuma xaka bani lbr da kanka. Ya fada yana daga gira"


Badaru ya washe baki tare da cewa "Allah mutumina πŸ˜„? Yana ina? Bani " mekudi yadan muskuta tare da cewa " sai dai fa yana da illah, yakan bata mahaifa ko hana haihuwa gaba daya, saboda haka ka kula, amma dadi kam xakaji dadi kamar ka mutu 😜" Badaru ya miqa masa hannu suka tafa yace " yo ni ina ruwana, ai dama bandamu in haihu da ita ba, amfanin ta kashe qishirwata da ita".


KB da tunda suka fara maganar hankalinsa na kansu ya magantu "Badaru me kake shirin aikatawa? Sirin shimfidarku kake budewa anan? Har kake shirin batawa yarinya mahaifa? to wlh karka soma. Kai kuma mekudi kaji tsoron Allah ka tuna kana da yaya mata in akaiwa yarka haka xakaji dadi? " sukai tsit suka sunkuyar da kai, saboda suna respecting KB dan ya girme musu.


Suna idar da sallar magriba Mekudi ya tashi tafiya Badaru ya miqe shima tare da cewa " Bari in koma gida nasan tana zaune a duhu ba wuta."



Yayi saurin tadda mekudi a motar sa yana shirin tashin motar ya bude ya shiga, ya miqa masa hannu "Bani maganin" mekudi ya sheqe da dariya yace "shege baka haqura ba" shima yayi dariyar tare da cewa "aimu bama wasa da kayan aiki". Ya miqa masa maganin a kwalinsa tare da cewa "ka kula". Badaru ya fito ya shiga tasa motar, yayi gida yau ko gurin Nafee baya son xuwa tunda ya samu.........



Mimi tayi mamakin barin jikin da Badaru keyi a kanta yau, duk da ba sabon abu bane a gurinta sambatunsa a shimfidarsu. Tana jin lokacin da ya cusa mata wani abu a gabanta. Tai saurin yunqurawa xata tashi, yasa hannu ya danneta. Tace "meka sakamun a jikina?" cikin rashin nuna kulawa ya bata amsa "xan cuceki ne? To vaseline na saka saboda kin matse da yawa na kasa shigarki" daren ranar ta gurxu a hannun Badaru, ga wani irin ihu da sambatu da yake tana tsammanin maqota na kusa zasu iya jiyoshi.



A dan wannan tsakanin Badaru ya xama wani irin qasurgumin jarababbe, kullum cikin yin abu daya yake. Ba dare ba rana, domin da ranar Allah xai baro kasuwa yazo gida ya shafe awanni yana dirxarta. Kuma in dare yayi ma babu hutu, sai yayi aqallah sau 3. Ita har mamaki take sam baya gajiya, zata iya cewa tunda aka kawota gidan Badaru yau kimanin wata hudu kenan (4 month) bai taba fashin kwanciya da ita ba, sai dai in period take.


Lokaci guda ta qare ta lalace, a xuciyarta take cewa ashe da ba wahala nakesha ba, yanxu ne nake ainihin wahala. Gashi dai bata nemi komai ta rasa ba (Faty ta tsaya mata) amma jarabar Badaru tasa ta xama kamar tsumma. A gefe guda kuma ga rashin mutuncinsa domin babu abunda ya fasa, sai ma qaruwa da yayi.


Sau tari takanyi tunanin matan da suke cewa aure da dadi, sai ta rasa ta inda sukejin dadin auran, ta xaman takewar gida kota kwamciyar aure? Domin ita dai tunda suke da Badaru ko na second daya bata tabajin dadin kwanciya ba, hasali ma axaba takeci ba kadan ba. Da farkon aurenta tana danganta hakan da rashin sabo, amma yanxu data dan kwan biyu sai take ganin halittar tace haka. Ita dai tasan in azabar da takeji ce jin dadin aure sai take ganin ba macen da xatace aure da dadi.



A lokacin sai takejin babu abunda ta tsana a duk duniya irin sex life (kwanciyar aure). Duk da gori da qalubale data fuskanta a rayuwarta ta yan matanci sai ta kwammace gara rayuwarta ta gida da wannan rayuwar da take yanxu.



*** *** *** ***


Yau babban baqo garesu, Badamasi qanin Badaru wanda tunda akai auren bai taba xuwa gidan ba. Yauma yaxo ne bisa takurawar ummansu.



Tunda yaxo Mimi keta hidima dashi dakko wannan, kawo wannan. Duk da batasan da xuwansa ba, tai masa tarba ta musamman da girkin alfarma. Tana ta xarya tsakanin parlour da kitchen, cikin tsawa da umarnin Badaru, wanda duk fitowar da tayi sai ya nemi wani abun da zaice batai dai dai ba.


Yanxu ma tafito ne dauke da qaramin tray wanda ta doro cups da lemon happy hour na kwali ta taho, ya daka mata tsawa da cewa "wai ke komai sai anyi jiranki ne? Kinsa wani hijabi na munafurci, wazai kalleki anan? Ni da babu abunda bansani ba a jikin ki, ko Badamasi dake dan uwana uwa daya uba daya? " Badamasi ya runtse ido cikin takaicin abunda Badaru yakewa yarinya, tana qoqarin kare masa mutunci ta hanyar suturta kanta yana kwaye mata baya. A dan xaman da yayi yanxu ya fuskanci inda aurensu yasa gaba. Shiyasa yaga maryam din duk ta canja, mace qayatacciya kyakykyawar gaske me fasali amma cikin lokaci kadan ji inda Badaru ya kwararrabata. Ya gyara xaman wayarsa dake kan hannun kujera, wacce yake recording din duk abunda ke faruwa tun daxu, da nufin in yakoma gida ya sakawa iyayensu suji yadda Badaru kewa yar mutane.


Tunaninsa ya katse lokacin da yaji Mimi na ajiye lemon da ta kawo a kusa dashi. Badaru ya tsai da ita, tare da daka mata wata muguwar tsawa "ke dauke Badamasi bayashan irin wannan lemon na kanti, sai zobo kije ki kawo masa zobo" (kunji fa kamar ya siya ya ajiye) ta dauki tray din lemon tare da cewa "to bara na dafa zobon sai dai babu qanqara...... " maganar ta dauke lokacin da taga Badaru ya daga hannu da nufin kai mata mari. Tai saurin saka tray din hannunta ta kare fuskarta, hakan yasa dukan ya sauka kan farantin kayan ciki suka watse. Badamasi yayi saurin miqewa tsaye cikin razana 😳. Badaru ya dora da cewa "Dan ubanki harni xan saki aiki kice babu qanqara? Meyasa baki siya kin ajiye ba?" idon Mimi qurrr akansa tana kallonsa cikin mamaki Dan yaune karon farko da yakai hannu jikinta da sunan duka, kuma yaune karon farko da ya xagi ubanta dake qarqashin qasa.



Cinkin dinbin mamaki da razana Badamasi yace "Badaru 😳dukan mace? Kamar jahili, metai maka? Dama abunda nakiji na cewa kana tara abokai kaci mata mutunci gaskiya ne? Me tayi maka? " Badaru ya tare Badamasin cinkin hargowa kamar xai dakeshi, "baka ga abunda tai ba? Yar iska mara mutunci, duk abunda xata xubarmun da mutunci ta iya, banxa jaka"



Idanunta jajur suna digar hawaye take kallon Badaru ba komai yayi mata ciwo ba irin zagin ubanta. Cikin qarfin zuciya tace"

Please Login or Register in order to submit comment