Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har saida suka shirya, yace "da kina nema ki bata mana wannan kyakykyawan yanayin da wani shirmen tunaninki ki fara fushi dani bakisan fushin me ciki bata sauka da wuri ba?"




Ma masallacin asuba bayan idar da sallah ya fadawa limamin asakashi a addua matarsa nada ciki yana barar adunga sata a addua Allah ya rabasu lfy. Ya kawo kudi ya bayar.




A office ma yau sai walwala yakeyi yana faran faran da kowa aciki kuwa harda Hanifa da suke yar tsama kwana biyu baya amma yau sabida yana cikin farinciki sun shirya. Biyar nayi ya nufi gida.




Mimi kuwa tashi tayi ta tarar ya fita don yanxu ita da bacci sun daura abota, tana shirin dora abunda takeson ci Farida ta shigo taxo musu da taliyar hausa dafaffiya da manja da yaji suka zauna suka dunga ci sai da suka tashi da ita tas kana masu aiki suka gyara gurin su kuma suna gefe suna hira.




Sai da aka kira laasar Farida ta tafi xataje tasa hannu a girkin dare, Mimi kuwa tana sallah wanka tayi tasa wani blue din wandon Jeans da yellow din shirt. Fes yaxo ya sameta, yana xuwa ya buqaci baqo ya tattaro masa duk wani maaikaci na gidan.




Suka hadu a falo suna mamakin wannan kira, ya dubesu bayan sun amsa gaisuwarsa. Yace "inason kowa ya maida hankali akan aikinsa sosai duk da kuna qoqari amma a qara musamman wadan da ke kula da part din madam. Banaso ko tsinke inga tana daukewa sabida tana da lalura irinta ciki a halin yanxu". Mimi take gefensa kunya ta kamata ta sunkuyar da kai sabida harda yan tsaffin dake aiki a gidan a gurin da matar me gadi. Suka rude da yimasa murna dafatan Allah ya inganta. Ya amsa ya dubi moses wato kukun gidan yace "daga yau na hanata shiga cikin aikinka ka kiyaye duk abunda takeso xata fada maka ka dafa ko kuma ta koya maka yadda akeyi" ya amsa yes sir"




Yakai dubansa ga grace da kuma dayar wato Ester yace?"kune masu tsaftace shashinta sabida haka a kula da kyau kar abar guri da danshi ta zame in hakan ta faru Allah ya kiyaye daureku xanyi" suka amsa da girmamawa sannan ya juya ga Aisha sabuwar me aikin da suka taho da ita daga wacce mumy ta samo musu yace "Aisha daga yau kece me kula da cikin dakin Mimi da tsaftace toilet dinta da duk wani motsinta wanda ya danganci nan kema ki kiyaye" ta amsa da "to" ya dubi Mimi yace "madam hakan yayi miki?" ta gyada kai kana tace "amma ni banji ka fadan aikina ba kuma kasan xama haka baxai yiwu ba motsin yanada amfani" ya dubeta yace "ki dunga gyara gado kina shiryamun drawer ta sai Aisha tayi ragowar" tayi dariya tace "ina neman alfarma abarmun gyaran dakinmu da toilet, innaji baxan iyaba na nemi taimako" ya kasheta da murmushi yace "anmiki"




Ya dubi matan wato maaikata mata yace "Don Allah kar a ringa barinta ita kadai, indai anganta ita kadai ko kuma in mutum ya gama aikinsa yaxo ya debe mata kewa don batason kadaici qofa a bude take ga kowacce mace a cikinku." ya dubi yan tsaffin guda biyu yace "Don Allah Baba duk abunda takeso ko yake da hadari ga masu lalura irin tata sai a fada mata" suka amsa suma kana ya sallamesu. Yakai dubansa ga Bako yace "Bako sai a kula sosai a tabbatar kowa yana aikin dana dorashi akai, ita kuma maryam duk abunda takeso in sun fada maka koda bana kusa ayi qoqarin samar mata" ya amsa cikin girmamawa sannan yayiwa Mimi fatan sauka lfy.




Bayan isha ya dawo masallaci ya shiga wanka, ita kuma tana dakin tanata xarya daure da towel so take ta shiga bathroom din suyi wanka tare kamar yadda ya dade yana buri amma ta kasa. Can ta runtse ido ta shiga, ya bita da kallon mamaki yana xaune cikin qaton bahon wanka wanda ya cika ruwan dumi da sabulan ruwa sai kumfa ke tashi da qamshi. Mamakinsa ya qaru lokacin da yaga ta cire towel din ta nufeshi, ya qurawa jikinta ido komai ya qara girma daga bobs dinta har hips wanda ada bai kula ba sai yanxu jikin ya kuma haske tas. Ta shiga cikin bahon, ya janyota tsakiyar qafafunsa yasa soso yana wanketa ya fara yi mata magana a kunne "Mimi luv amma dai inkin haihu jikinki baxaiyi wannan abun ba ko?" tace "wanne kenan?" yace "wannan murmurdrewar ciki ya yakutse stregcht mark (nankarwa) ko kuma kiyi tumbi wannan plat tummy din naki ya baci" cikin dariya tace "inyayi hakan dena sona xakai?" da sauri yace "Allah ya sawaqe just banaso ne amma ni koya kika xama ina son abata a haka" tace "to ai duk akwai maganinsu inba nayi, amma dai ba lallai bane jiki jiki ne wasu basai sun haihu ba in sukai qiba sukeyi, wasu kuma koda qibar da haihuwar basayi is defense da irin kyan jikin mutum. Amma dai manya na cewa ba a gane kyan mace saita haihu sabida lokacin in jikinta bashi da kyau duk sai tai ragaf jikinta ya baci in kuma me kyauce wato jikinta xakaga kamar bata haihu ba saima tsam da jikinta xaiyi tayi kyau sabida sabon jini yaxo mata." yace "to in shaa Allah kina cikin masu kyan jikin"




Yaci gaba da juyata son ransa wai yana mata wanka, yace "Mimi amma dai yanxu na tashi daga rago ko tunda na miki ciki?" ta hade rai tace "gaskiya ni ya Bature banason irin wannan zancen sai kace wasu yan iska😞" yana dariyar zolaya yace "ai kuwa kowa ya ganki yaga yar iska tunda ga shedar iskancin nan a jikin ki. Haka kika dunga bina kinamun wayo kika amshemun samartaka har saida kika maidani Dan iskan nima 🤣" ta fara kukan shagwaba tana bugunsa, ya sassauta dariya yace "sry na janye Mimi luv nine dan iskan tunda na hanaki sukuni saida nai miki ciki" haka suka dunga wasa acikin ruwa har kusan taran dare, kana suka shirya suka fito yin dinner.





Ta xage tayi white rice da stew din da akai sosai, yana kallonta asace alama cikin nata mai sauki ne don duk abunda ta samu ci take tayi nak sai dai in kwadayin ya motsa.





Washegari ma kafin ta tashi bacci ya fita, ta dunga takaicin halin da wannan ciki ya sakata taita baccin asara har mijinta ya fita tana kwance. Ta lalubi wayarta ta kira baqo tace masa in akwai inda xa a sami wainar gero da quli a nemo mata ita takeson ci.





Ya fita nema babu dadewa ya dawo ya samota awani gidan abinci anqawatata da kabeji, ta karba tanaci Farida ta shigo suka faraci tare amma Sam wainar babu dadi wadda ake a Local area tafi dadi. Farida tace mata taxo su fita xata supervising gidan abincinta daga nan su biya shagonsu suga yadda ake tafi da cinikin.




Ta kirashi a waya ta fada masa inda xasu, yace adawo lfy amma su kula sosai sabida abunda yake tare dasu.



Farida ke tuqin suka isa gurin. Mashaallah komai tas da tsafta anata shige da fice, masu kula da gurin kamar suyi musu sujjada Mimi tace akwai tradicional food? Cikin girmamawa sukace wanne xa a kawo musu a ciki? Tace " tuwon dawa da miyar kuka" suka kawo ta wanke hannu taci Farida sai yamutsa fuska take ita bai mata ba. Daganan can boutique dinsu sukaje, Mimi a xuciyarta tace kudi shegu ganin yadda ake wani basu girma duk da sun girmi duk yaran shagon. Suka duba komai har sabuwar order din da akayo da kuma record na ciniki komai babu matsala kana suka tafi.




Baqo ne ya siyo tandar wainaganin Mimi yanxu bata da abun so kamar wainar gero da yar tsala kuma wacce ake siyowa bata mata yadda takeso, yace matarsa ta dunga yi mata duk sanda takeso. Matar me gadi tace akawo ita tadau nauyin wannan, hakan yasa Kullum da safe Mimi ke samun abun breakfast irin wanda takeso. Bature yaji dadin wannan abu da sukayi sun tayashi son abunda yakeso.





Cikin yan kwanaki kadan tai wani irin kyau ta dashe tayi tas ta xama fara sol sabida ciki, kulawa kuwa har kunya takeji wani sa in duk wata halitta ta gidan hankalinta nakan Mimi. Bature ya dauke mata komai na hidimarsa, sau tari kafin ta tashi ya fita aikinta a gidan kawai ta gyara gadon dakinsu ita dashi ta wanke toilet ta kuma gyara kayansu na sawa sai wankin undis a washing machine. In kuma yana gida yana gefenta ko ruwa xatasha saiya dauko mata robar in xama xatai saiya kyara mata gurin xama.




In kuma baya gida sukan cika falon kowa yana qoqarin sata farin ciki, wani lokacin sai tasa a kawo mata yayan Bako taita hira suna mata shirmensu tana dariya ko kuma su fice da mazajensu da daddare suna yawan xuwa shan ice cream.



Sosai Aisha ke mata biyayya ta kwadata sosai taga bata da matsala kamar yadda mumy tace, xata iya cewa bata tabajin dadin xaman aure irin wannan lokacin ba. Ishaq yaso taje can asibiti ayi mata scanning aga kan cikin amma taqi tace lokacin beyi ba suka haqura tunda sunsan cikin befi wata daya ba da yan kwanaki.




Ana cikin haka Faty ta haihu, ranar ta kira Mimi ta sanar mata amma namiji ta haifa a maimakon macen da take qulafaci. Mimi murna kamar me, tun a ranar ta soma shirin tafiya amma har akai kwana 5 da haihuwa bai barta ta tafi ba don cewa yayi baxai bari taje da wuri taita aiki ba ta jawo masa asarar abunda ya sha wahala kan ya samu.




Tayi fushinta har ta sakko don kanta ta koma lallashi, ana gobe suna da safe tana ta hada jaka xata tafi. Sai lodar Kaya take nata da wanda ta saiwa Faty da baby. Ya dubeta yace "kiyi sauri mu ajiyeki a airport din karkiyi late" tace "to, ai kaqi fadamun kwana nawa xanyi" yana gaban madubi ya bata amsa "karki damu kiyi tafiyarki in lokacin dawowar ki yayi xan kiraki ki taho" cikin munna tace "to yayana, ai nasan tunda baka barni tafiya da wuri ba xaka bari in dade, Allah ya sa ka barni in wata daya inxaga dangi sosai har garko xanje da gombe" yana dariya yace "karki damu shekara ma xakiyi, fatana Allah yasa karsu gane abunda ke qunshe a mararki don kunya nakeji kowa yasan abunda mukai kan hakan ta samu" cikin damuwa tace "wlh kamar ka shiga xuciyata nima banaso a sani amma dai xan daure baxan nuna inason komai ba. Inkuma sunce nayi fari da yawa ince mai na canja" ya yaba da dabarar data kawo yace "yawwa gud idea" suka sauketa a airport ya juya office.





A gidan Faty ta sauka, ta tarar sunata aikin suya shinkafar da za a yi amfani da ita gurin fried rice gobe ba tare data suta ba tasa hannu suka dinga aiki sai da suka gama cikin dare kana suka nutse daki da ya Faty suka gaisa ta dauki jariri, ta bata kayan data lafto duk yan waje suna zaune ya Ahmad ya dawo. Ya zauna cikinsu aka fara hira har kusan dayan dare kana ya basu guri suka kwanta.



Washegari suna yaro yaci sunan baban ya Ahmad, suka fara aiki tun asuba har wajen 11 gida ya fara cika komai ya kammala sai kayan cikin rago da suke wuta basu qarasa soyuwa ba. Taje tai wanka tasa Kaya ba tare da tayi kwalliya ba, yan gidansu duk sunxo batasan mumy taxo ba sai data fito falo ta tarar da ita a xaune.




Ta matsa jikinta tana gaisheta, mumy tana shafar kan Mimi dake qasa tace "lfy lau Mimi ya mijin naki?" ta amsa mata kana ta gaida matar qanin Dady dake kusa da mumy. Lubna take xaune kan kujerar dining danta na kuka tace "Dan Allah Anty Mimi goyashi tunda fita xaki inna goyashi baxai bari in xauna ba. Mimi tace to ta karbeshi ta sabashi abaya tai waje. Aranta tanajin dadin girmamawar da su lubna ke mata a matsayin matar wansu duk da sun girmeme mata amma tundaga kan audu har xuwa auta little babu mai fadar sunanta kai tsaye sai dai suce Anty Mimi ko matar yaya.




Tana ta aikin juya kayan cikin ragon suna daya kusa soyuwa har yaran yayi bacci, ta koma ciki ta saukeshi a bedroom ta fito falo. Habib dan wata cousin dinsu na kuka ta karbeshi shima ta goyashi ta fita da sauri sabida kallon da mumy take binta dashi duk inda tayi.



Mumy ta juya kallonta xuwa gurin Haj Hawwa faccalarta tace "Hawwa sai nake ganin yarinyar nan cikine da ita ko?" da rashin fahimta a fuskarta tace "wacce kenan Anty halima?" tai qasa da murya tace "maryam mana matar Bature" tace "bari ta shigo ingani aini ban kula ba amma mu ciki sati daya ma muna iya ganeshi jikin mace"



Mimi ta shigo ta kwance Habib da yayi bacci ta miqawa uwarsa shi tace "karbeshi baccinsa beyi nisa ba sabida hayaqi na dawo dashi ciki" ta karbeshi tace "yawwa na huta rigimarsa"




Haj hawwa ta tsirawa Mimi ido harta fita ta dawo da kallonta ga mumy tace "tabbas ciki gareta, bakiga duk ta dashe ba tayi fari fau haba Anty halima ai ko ya kamata ki gane maryam qaramin ciki gareta" mumy bakinta yaqi rufuwa, nan take ta dakko waya ta turawa mama wacce bataxo ba text na abun farincikin daya samesu. Mama na ganin text din ta kira mumy tana wani irin farinciki.




Tana gama suyar hancin ta xubo a plate ta wuce dakin ya Faty ta badeshi da yajin daddawa, yawunta sai tsinkewa yake sam ta manta da wani zancen kar agane cikine da ita. Taxo falo cikin su Lubna ta faraci, wannan abun da tayi shiya tabbatarwa dasu mumy abunda suke zargi.





Tana gamawa ta miqe zata fita, anty Zainab din gidansu tace "Mimi dan goyamun mamana tunda fita xaki bacci takeji" Mimi ta miqa hannu xata karbeta Haj Hawwa tace "kai jama a, itama dai kwa kyaleta nata Dan yayi kwari a mararta kun jibge guri daya ita da bata da son jiki sai aiki take tana muku rainon yaya" Mimi najin haka ta fasa karbar yarinyar tayi bedroom da sauri.




Lubna ta kalli su mumy tace "Dan Allah Umma Mimi cikine da ita?" Haj Hawwa tace "wlh da gaske gashi nan sai kwadayi take" yasmin tace "haba gaskiya mana naga tayi wani mugun haske" falon ya dauki sowar murna cikin Mimi kamar itace mace ta farko da xata haihu a zuriar gidan.




Ana cikin haka saiga almajirin ya Faty ya dawo da aiken da Mimi tai masa na siyan goba (guava) Anty yasmin ta karba tai cikin daki inda ragowar suke da Mimi. Tana xuwa tace "me ciki ga saqonki yaran da kika aika ya dawo" Mimi ta qunshe kai a tsakiyar cinyoyinta cikin kunyar duk yadda takai ga kaf kaf dinta saida suka gano cikin jikinta.




Duk wadan da ke dakin suka xuba mata ido aciki kuwa harda me jego Faty, yasmin ta tabbatar musu da gaskiyar xancen ta hanyar fada musu abunda ya faru a falo yanxu. Suka dunga murna suma Anty Adawiyya harda guda. Faty kuwa tsurawa Mimi ido tayi tanason gano cikin da akace Mimi nadashi.







Yasmin ta matsa jikin Mimi ta miqa mata ledar gobar sannan tace "congrat maryam, indai macece a cikin ki inawa Adil riqo tun yanxu don dake da ya Bature in colour dinku suka tashi haihuwa fure suke haifa wanda kan xama abunso ga kowa." Faty ta katseta da cewa "gaskiya Anty yasmin Dady ya rigaki, shima tunkan cikin ya samu yake riqo" aka kwashe da dariya gabadaya dakin Anty Adawiyya tace "ke kunji mata ko wacce tanawa danta na fari campaing babu ko kunya, to ai nice uwar yar don haka sai wanda naga dama xan bawa kudai kawai ku fara toshi tundaga yanxu" aka kuma saka dariya Anty Zainab data shigo yanxu tace "wai da alama wannan Baby xatai farinjini daga fadar akwai cikinta har ta samu samari biyu?" haka dai sukasa Mimi tsakiya suna zolaya tun tana kunya harta ware.





Tacinye gobar tas ta miqe a gado tai kwanciyarta ta fara sanaar datafi karbarta wato bacci. Lokaci xuwa lokaci Mumy kan leqo dakin taga lafiyar Mimi, abun ya bawa mutane da yawa mamaki. Haj hawwa tace "wannan suruka taki Anty halima yar gatace, bantaba ganin inda ake son suruka haka ba." bata tashi ba sai qarfe uku, tai sallah da wanka tayi kwalliya da kayan datai musu iri daya ita da Faty. Gida ya cika sai hidima ake mumy ta hana Mimi yawan zirga zirgar da take ta datseta saidata tabbatar Mimi taci abinci sannan tace ta zauna duk abunda takeso su Lubna su miqo mata.



Sai magrib mumy suka tafi, kafin ta tafi ta tabbatarwa da Faty ta kula da Mimi sosai karta bari taita wannan zaryar sabida qaramin ciki bai juri wahala ba. Daga qarshe ma sai mumy tace "gobe Mimi ta taho gidanta in sun gama aikin nama don tasan inta zauna anan dole xataita aiki" Faty tana dariya tace to mumy in shaa Allah xan turota da wuri.





Sai da dare yayi sosai qafa ta dauke Faty ta tambayi Mimi akan cikin "Mimi dashen akai miki ko kuma Allah ne ya kawo?" Mimi ta kwanta a kafadar Faty tace "ya Faty babu wani dashe, Allah maji roqon bawa shiya dubi rauninmu ya bamu" Faty tace "Alhamdulillah, inaji ke xaki haifi macen dana dade ina qulafaci Allah ya inganta ya rabaku lfy ssurukar Dady 😄" ta miqe tai dakin Ahmad don fada masa labarin cikin Mimi. Mimi tasa jaririn agaba tana kallo tana ayyana lokacin daya rage ta samu nata dan. Da haka bacci ya kwasheta.





A wannan dare wadanda suka san labarin cikin Mimi Allah yayi yawa dasu aciki harda Dady wanda mumy ta fada masa, mama ta fadawa Baffa, Faty kuma ya Ahmad sai yasmin data fadawa Audu. Abun dai kamar hadin baki duk wacce ta koma gida daga gidan suna saita fadawa mijinta labarin cikin Mimi. Sai dai abunda mumy bata sani ba shine shin Bature yasan da labarin cikin ko bai sani ba? Tasanshi sarai da shiririta tanaso ta fada masa ya kula da Mimi sosai amma kunyar yimasa maganar cikin take.




Da wuri suka fara aikin naman don haka suka gama akan kari suka gyara gidan tas, Mimi tai wanka ta shirya Faty ta dibar mata nama sunan da yawa ta sa mata wani a kakidi ta bata yaji shima kamar itace ta haihu ita kuma tayi hakan ne don taga cikin Mimi alama yanason naman suna. Ta bawa mumy nata naman, sukai sallama ta hada kayanta kaf tai gidan mumy wacce tun daxu take wayar cewa Mimi ta taho.




Kusan qarfe uku ta isa gidan mumy tana xuwa dakin mumy taje tai kwanciyarta bayan sun gaisa da mumy din. Bata tashi ba sai kusan biyar, tai sallah ta fita falo suka kuma gaisawa da mumy sannan tão kitchen tasa hannu a girkin dare duk da hanata da mumy takeyi taqi hanuwa, saida ta xuba shinkafar tuwo a ruwan kan gas sannan ta koma daki tai wanka tasa doguwar rigar atamfa sakakkiya taci kwalliyarta ta fito ta dora miyar agushi.




Tana ta aikinta tsakanin falo da kitchen suna taba hira da mumy abun shaawa kamar ba surukai ba. Little batanan tana gidan yayar Dady hutu.




Dady ya dawo suka hadu a falon gaba daya, shima kamar mumy bai dauki Mimi a matsayin suruka ba. Yana zaune bayan sun gaisa da Mimi ya fara karatun jarida, mumy kuma ta maida hankali tana kallon tashar MBC action. Mimi ta fito kitchen ta kawowa dady fura a glass cup, ya karba yasha kana ta tsiyayar masa ruwa ta miqa masa. Ya karba yana cewa "Allah yayi albarka uwata" ta tattara kayan ta mayar kitchen, shi kuma ya maida glass dinsa yana karatun jarida.




Baifi saura 20 minutes ai kiran sallar magrib ba, Mimi ta gama tuwon danyar shinkafa fara sol yayi ligif yayi laushi ta sassakashi a leda ta kawo dinning tana shiryawa kafin miyar ta qarasa. Gidan ya cika da qamshin miyar agushi wacce taji kifi.





Tana tsaye wajen dinning din kamar a mafarki ta hangi Bature a qofar falon, ta ware ido don ta tabbatar shidinne ko gixo yake mata. Kiran sunanta da yayi shiya bata tabbacin shidinne. Su mumy da basu kula dashiba sai yanxu suka xuba masa ido, shidinma yakai 5 minutes tsaye a gurin kafin Mimi ta ankara da xiwansa don tun lokacin data kawo food warmer yake gurin yana kallonta ita da yan bokon surukanta dake zaune a falon.



Dady ya katseshi da cewa "sulaimanu shigo mana" baice komai ba sai kallon Mimi yayi dake tsaye alamar ita yake so tazo taryarsa. Ganin haka Dady yacigaba da karatun jaridarsa, Mimi ta dubi mijinta dake tsaye ya marairaice yana kallonta alamar taxo. Takai kallonta kan mumy da Dady kowanne yana abunda ke gabansa kamar basusan da Bature da Mimi ba a gurin (shegu yan boko 😄)




Tana ganin haka ta nufeshi, ta karbi jakarsa dake goye bayanshi wacce take dauke da kaya set biyu, yadan rabata a jikinsa tai saurin kaucewa yakai hannu mararta yace "ya Baby na?" wannan magana daya fada karaf a kunnen mumy. Tayi hamdala a xuci ya tabbata Mimi tana ciki kuma daga Mimi har Bature sunsan da cikin, ita kam sai yanxu ta yadda danta namiji ne ada ta dauka sulaimanun aljana ta aureshi ko kuma bashi da lfy irinta maxa kuma a xatonta xaman kai da qafa suke shi da Mimi amma yanxu wannan tunanin ya kau tunda ga Mimi nan dauke da cikinsa.





Mimi tai saurin ture hannunsa ta nufi cikin falon da jakarsa, dakinsa ta nufa na da ta ajiye masa ta fito. Ta sameshi xaune akan kujerar dake tsakiyar su mumy, mumy ta kalli qafarsa tace "Baba ya kashigomun falo da takalmi har kake takamun centre carpet?" ya marairaice yana duban Mimi dake tsaye can nesa yace "mumy Mimi ce kemun wannan hidimar kuma yau ganinku ya hanata yimun" Dady ya kalli Mimi yace "maryam xoki hidimtawa mijinki mu babu ruwanmu daku"




Ta matso a kunyace ta taimaka masa ya cire jacket dinsa, ta tsuguna ta cire masa sau cikin qafarsa ta zare masa sucks tai daki. Ta fito ta kawo masa try dauke da cup din fura da ruwan roba, ya karba yasha ruwan yabar furar yace "Mimi ba a gama abinci bane yunwa nakeji nayi missing delicious dinki." tace "na kusa qarasawa kasha furar kafin na ida" yace "No barshi innasha fura yanxu kashemun jiki xatai, inkin gama naci" ana kira suka nufi masallaci shid Dady.




Basu dawoba sai bayan isha, suna xuwa dinning suka nufa. Mimi ta xubawa kowa abinci kana ta xauna, sukaci abincin sosai don girkin yayi dadi sosai.





Har kusan tara tana falo xaune yayin da tundazu yayi wanka acan daki yake jiranta,

Please Login or Register in order to submit comment