Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farko, ATM dinta da yayi expire wanda dole sai taje ta gyara kafin ta samu hurumin fidda kudi. Na biyu kuma shine takunkumin da Badaru ya qaqaba mata, domin tun sati 2 da xuwanta gidansa ta tambayi xuwa kitso yace mata baya cikin tsarinsa fitar matarsa daga gidan aure inbada lalura ba, kuma koda xata fita ma yanaga sai ta shekara a gidansa. Wannan shine dalilin da yasa ko daxu da yace zashi gida duba Abbansa batace xata bishi ba, saboda yace wannan shine tsarinsa.


Da yake ance me dΓ‘ wawa, saboda jan yayansu da take ajiki yasa be kitson take xuwa har gida tai mata kitson da baya wuce kwana 5 ya tuje saboda Kullum cikin xubawa kai ruwa take da kuma yanayin halittar gashinta, domin kanta shampoo din da tayi da biki ya dade da fita, kuma bata da wani man shammpoo din da take amfani dashi (mega growth) domin kaf cosmetics din lefenta ba irin wanda take amfani dasu bane, kuma yawanci anrabar dasu ga dangi (kamar yadda akeyi a al adance).


Kudin hannunta sune kayan miya, siyan salak in buqatar cin salak din ta taso, sune biyan kudin kitso da kuma siyan sabulun wanki. Domin akan idonta Badaru kan hada wankinsa ya bayar a wanko a gogo masa, amma bai taba hadawa da nata ba. Gashi ita kuma bata iya wanki ba zata iya cewa tunda take bata taba wanke kayanta na sawa ba, iyakacin wankinta undis suma a washing machine take watsasu ta wanke.


Duk da cewa Badaru yasan bai taba kawo kayan miya gidansa ba, hakan baya hana in yaga anyi abinci da miya koma har da nama ya zauna ya take tumbinsa, kusan ma bayacin abincin gidan sai yaga Cima da canja maana anyi me dadi, Ko kunya bayaji ko kuma ya tambayi ina akasamu kayan girkin saboda tsabar San banxa (san banxa mesa gidan yari cika πŸ™„πŸ˜„).


Yau da gobe tafi qarfin wasa kuma xara bata barin dami dan haka kudin hannunta bai gaxa 800 ba, dan haka ta tambayeshi ya bada kudin wake (abunda bata taba yiba, wato tambayar Badaru abu koda kuwa haqqinsa ne yayi). Acikin wannan 800 din data rage mata tanason siyan pad dan lokacinta ya kusa, ga siyan sabulun wanki ga, ga kudin wankin, sannan ga kanta ya dameta ya cika ya sarsarqe alamun yana buqatar shampoo, amma da yake hakan bata samuwa dole ta biya kudi a kitse matashi. Gashi tanason siyan wake ta hada a dahuwar shinkafa dan tagaji dacin fara da mai.


Atake a gurin ta samowa kanta solution, domin kudin bazasu isheta ba, saboda haka ta yanke shawarar siyan always (pad) tunda ita dole ce, kasancewarta mace me xubar da jini a lokacin al ada yasa sinqi daya bata isarta sai daya da rabi ko biyu. Yanxu da rayuwa taxo mata a haka ta yanke shawarar hadawa da tsumma, ragowar kudin xata sai sabulun wanki tai wankin da kanta tunda ba kudin kai wankau, sannnan ta bada kudin kitso ai mata kitso ragowar kudin ta sai wake ta dafa a shinkafa.


Rayuwa kenan abar tsoro wai yau maryam ce da wanki. Ahankali ta furta "rayuwa ce wataran sai lbr, dama aure a 2 ne ko kaci gaba ko kaci baya."

Tana kaiwa nan a tunaninta ta miqe ta fara aiwatar da abunda ta shirya.


Badaru bayan ya isa gidansu ya duba jikin Abbansa, yana zaune suna dan taba hira da Abban ummansu take gefe sai kallonsa take asace, saboda kunya irin ta dan fari.

Can dai ta kalleshi tace ina wajen su maryam din? Yace ko lfy, ai canake da ita xakuxo duba alh?

Yayi saurin cewa tananan qalau tace ma a gaisheshi da jiki, ni banason gantaline a tsarina banason matata ta fita.


To sannu me mata hakan yayi dai dai mara kunya inji Umma. Sannan ta dora da cewa " ai wannan yarinya Allah ya saka mata da alkhairi, ta gyaraka kayi tas kayi jajur da kai har wata teba ka ajiye. Wannan yarinya ta samu tarbiyyar Allah ya sakawa iyayenta da alkhairi" ta kalli abbansu Badarun sannan tace "wlh Alh tunda mukaje yarinyar nan take hidima damu ta kawo wannan ta kawo wancan, sannan ta samu hijabi ta saka a jikinta har muka taho bata cire ba, muna kan kujera tana qasa idanunta a qasa. Aini Alh banzaci acikin yaran yanxu masu xurfin karatun boko akwai irin maryam ba, haka in su Aisha (yayanta mata) sukaje mata take hidima dasu da yayansu inzasu taho, tabawa wannan mayafi wannan takalmi kai gashinan dai abun sai San barka"


Alh inuwa ya dubeta yayi murmushi sannan yace lallai kaltume wannan suruka taki tayi miki 😊 dan naga kullum in muka zauna sai kinyi bitar ahalayenta.

Tai saurin cafewa da cewa wlh kam tayimun, ai maryama ta haifu yarinyar yar halak ce, ni da Xaiji shawara ma ai daya haqura da Nafeesan yayi xamansa da wannan dan ni kam maryam tafi kwantamun.


Badaru yaji maganar kamar saukar aradu ya dago a razane 😳, yace Umma in haqura fa kikace? Shekara nawa Nafee na jirana? Innaqi auranta na yaudareta, Kuma bayan haka ma ina sonta baxan iya haqura da itaba.


Umman ta watsa masa harara tare da cewa "ai tare aka hallicceku shiyasa bazaka iya haquri ba"


Abba yayi saurin katsesu kafin maganar tayi nisa yace "ya isa kaltume, ki gyaleshi tunda yana sonta. Maryam din ma da za a aurota ai saida kika nuna turjiya, amma yanxu kinfi kowa yaban halinta. Itama wannan kikasan nata kyawun halin?"

Umma dai ta tabe baki tare da cewa Allah ya bada sa a 😏



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣2⃣

Dedicated to
Maryam Baita


Watanta biyu dai-dai a gidan, xuwa wannan lokaci ta saba da wahala, duk cewa ance ba'a sabo da wuya.


A bangare guda kuma tana cikin matsananciyar wahalar auratayya da Badaru. Irin yanda duk wata amarya da takai budurcinta gidan miji ke fuskanta a farkon aure. Ta wahala iya wahala saboda kwanciyar aure da Badaru tafi komai jigatar da Mimi.


Ga wani irin ciwon qirji da yake yawan fyadeta, saboda bacin rai da rashin cima mai dadi (mai da yaji). Tuni maganinta na numfashi ya qare, kuma tun kafin maganin ya qare intasha baya yimata aiki. Ga uwa uba zafi dakesa koda yaushe cikin daukewar numfashi take, saboda Sam yanayin ciwonta bayason zafi. Badaru kuma baya tada inji saiya dawo kuma duk inda 11 tai zai kashe yayi baccinsa inda ita kuma xata kwana fiffita da hand fan dan kiyaye lfy ta.


Babban abunda yafi damunta kuma shine; duk wannan hali da take ciki baisa Badaru ya tausaya mata yace taje asibiti ba, ko ya kaita. Hasali ma haka yake shafe tsawon lokaci yana auratayya da ita cikin shauqi da sambatu. Baya gajiya da abu daya wani lokacin sai yaga bata numfashi sannan yake saurara mata.


Bacin rai, yunwa, zafi da rashin kwanciyar hankali ya hadu ya saukar mata da wani irin matsanancin ciwon qirji. Wanda ya kwantar da ita wanwar ko sallah sai dai tayi zaune, aikin gida kuma in su abuwa (yaran maqota dake shigo mata) sunxo suke yimata, babban abin takaicin shine bata da ko naira 5 din siyan ruwan pure water. Wayarta ma kona plashing babu.


Yau monday, wanda ta kama kwananta 3 da kwanciya wanwar saboda nauyin qirji da daukewar numfashi. Ya xamana ko kwanciyar ta gagara sai dai tai ruf da ciki ta danne qirjinta saboda ji take kamar inbata danne dinba zai tarwatse. Daga waje kuwa kana iya jiyo hakin da take.


A haka Badaru yazo cikin shirin fita, yana balle botiran rigarsa, ya kalleta a wulaqance tana kwance ruf da ciki a kan centre carpet din parlon yace 'bakisan wannan kwanciyar babu kyau ba a musulunce?' sannan ya dora "nifa banason langwai kin cika gida da gurnani sai kace tsohuwar kafura wai ke ciwo ko? To wlh wannan ciwon da kike rashin dogaro da Allah ya kawo miki shi" (kunji jahili πŸ˜’). Yana ida fadar haka ya sa kai ya fice dan tsabar rashin tausayi da tsaurin xuciya.


Ta share hawayenta, aranta tana ayyana ko maqiyinta bazata so Allah ya jarrabeshi da qaddarar abokin zama me taurin zuciya irin Badaru ba. Kansa kawai ya sani gashi da manmaqo da masifar rowa.


Tananan kwance har yamma, xuwa lokacin ta ida jigata. Sai dai in lokacin sallah yayi takan samu sauqi a dabi ance, saboda tasa sallar aranta.


Bayan idar da sallah ta jawo wayarta cikin qarfin hali da jan numfashi dakyar. Tana tunanin wanda xata kira, shin mama xata kira ta fada bata da lfy, ta daga mata hankali? Ko yaya Faty data watsar da ita ta nuna batayinta xata kira? (duk kuwa da cewa Faty na kiranta a waya itace bata dauka saboda ta gaji da jin uxurin Faty akan rashin xuwanta gidanta, kawai ta dauki Faty a matsayin wacce bata santa a yanxu) dole dai mama da Faty sune dolenta (ranar naka sai naka)


Yaya Ahmad mijin Faty yayi saurin fado mata ta jawo wayarta tai masa pls call me, kafin ta aje wayar ya kirata.


Ta dauka "assalamu alaikum ya Ahmad " ya amsa sallamar "mimina kina lfy? Ya naji muryarki haka? " ya fada agigice. "bani da lfy ne shine nace dan Allah ko zaka taimakamun kaiwa Badaru magana ya kaini asibiti" ta fada a wahale. "subhanallah sannu Mimi bari muga ya za ai? Sannu autarmu" da haka ya kashe wayar.


Ya tashi ya shiga bedroom gurin Faty dake zaune (yau aikin safe tayi shiyasa take gida a wannan lokacin) ya kalleta tare da cewa "fadima meyasa bakyajin maganata ne? Inashan fada miki kece babba karkiyi abunda zai bata xumuncinku da Mimi, na fada miki mama har fushi tayi dake akan rashin zuwa kiga halin da Mimi ke ciki, amma duk kinqi ji ko? To yanxu Mimi ta kirani bata da lfy kuma ga dukkan alamu tanajin jiki, babban abun takaicin shine: mijinta yaqi kaita asibiti, daya takaicin shine; ko zancenki batai ba a wayar, wanda hakan ke nuna cewa ta watsar dake kamar yadda kikai mata" yana kaiwa nan a maganarsa yasa kai ya fita.



Tunda ya furta Mimi babu lfy kuma ta kirashi a waya, Faty take a fingice. Ta tashi tabi bayan Ahmad da gudu ta fada jikinsa ta baya ta rumgumeshi tare da sakin kuka "yaya kace Mimi bata tambayeni ba? Kace Mimi bata da lfy? Yaya wlh tausayin Mimi da halin da xan ganta ciki ya hanani xuwa gurinta, bawai bijerewa umarninka dana mama ba. Yaya banason mijin Mimi tunda Mimi bata sonsa" ya dagota ya juyo da ita yana share mata hawaye, yace "my luv, bata wannan hanyar xaki nuna tausayin Mimi ba, neman kusanci da ita da maganta mata matsalarta da kwantar mata da hankali shine hanyar tausayinki da soyayyarki gareta" tace naji kuma xanyi yadda kace " duk a rude take wannan magana.


Ta shiga daki ta dakko mayafinta da key din mota ta fito, ya kalleta ina zaki? "Gidan Mimi " ta bashi amsa direct. Yace a a bari insa ta turo no mijin nata infara yi masa magana tukun. Tai rau -rau tace 'yaya Mimi babu lfy kace in tsaya injira ayiwa wannan wawan waya? Mimita cefa ba lfy? Ka bari inje xanyi duk abunda ya dace" yace "to my luv sai kin dawo kibi komai a hankali karki abunda xaki xubar da mutuncinki a gurinsa, kuma matarsa ce ya fimu iko akanta" ta gyada kai tare da ficewa.



Lokacin da ta isa gidan Mimi yamma tayi sosai, domin har Badaru ya dawo. Ta dunga kwada sallama Mimi na parlo a kwance tana jinta tai mata shiru, yayin da Badaru dake cikin bedroom yaji sallmar kuma yaji Mimi bata amsa ba ya fito. Lokacin Faty ta gaji da jiran a amsa mata sallama har ta shigo parlon, Mimi kuwa tanajin ta shigo ta juya baya tabar kallon qofa, ta fuskanci kujerar parlon. Badaru yana tsaye yana ganin ikon Allah, shidai yasan Faty yar uwar Mimi ce, kuma a dan iya xamansu da Mimi bai taba ganin tayiwa wani haka ba koda kuwa batasanshi ba, balle Faty yar uwarta.


Faty bata kula da wanxuwar Badaru ba dake kofar bedroom riqe da cotton (labule) ba, saboda gigitar halin ko in kula da Faty tai akanta.


Jikinta a sanyaye tasa gwiwarta kan centre carpet din dake parlon ta marairaice tace "Mimi na tuba, karkiyimun hukunci irin wannan, bazan iya jure rashinki gareni ba.



Mimi ba tare da ta juyo ba, tace "ai tunda kika iya jure 2 month baki ganni ba kuma baki damuba hakan na nuna kin yanke alaqa tsakaninmu, shiyasa nima na cireki a raina kuma ban nemi taimakonki ba. Duk mutumin daka rayu tsahon wata biyu babushi wannan sheda ce dake nuna cewa ko babushi xaka iya rayuwa"


Faty ta fashe da kuka "MARYAM karki bari shedan yayi tasiri a xuciyarki, kinfi kowa sanin cewa duk halin da kike bazan gujeki ba. Kuma duk tsahon lokacinnan wlh dake nake kwana nake tsahi, Mimi kinsan dalilin da yasa banxo gurinki ba, sai dai kiqi gasgata dalilin nawa. Mimi wallahil azim ko yayan dana haifa banai musu soyayyar da nake miki, saboda duk duniya bani da yar uwa uwa daya uba daya saike"


Mimi taji wani irin mugun tausayin Faty ya kamata amma ta danne saboda tanason hora Faty akan karta qara yimata haka anan gaba tace "yaya Faty ki tashi kije gidanki, nasan dake na naimi yaya Ahmad ban nemeki ba kuma da nasan ke zai turo da ban nemi ya taimakamun ba" duk tana wannan maganar ne a juye (ta bawa Faty baya).


Parlon yayi tsit na tsawon 5 minutes. Mimi da taji shirun yayi yawa ta juyo a zatonta Faty tayi fushi ta tafi. Amma me? Sai tayi arba da Faty tana tsugune tana hawaye.


Ta qura fatyn ido itama tana hawayen, ita kuwa Faty ganin yadda Mimi ta lalace ta kade yasa ta qara sautin kukanta cike da nadamar rashin xuwa taga lfyr mimin.


Cikin kuma Faty tace "#FATIMARYAM# bazasu taba rabuwa ba, bazasuyi fushi da junansu ba, matsalar Faty ta Maryam ce, matsalar maryam ta Faty ce. Mimi wannan shine alwashin mama akanmu, karki karya alqawarinnan tun yanxu πŸ˜ͺ"



Mimi najin haka ta taho da rarrafe domin babu qarfin tashi, taje ta rungume Faty. Faty ma qanqame Mimi tayi kamar xata maidata ciki.


Suka dunga a jiyar xuciya xuciya a tare, Faty ta dunga sharewa Mimi hawayenta sannan ta kwantar da Mimi a qirjinta kamar yarinya tana shafa kanta alamar lallashi.


Badaru yana tsaye, yana kallon dramar su, kamar masu shirin film. Aransa yace dama akwai irin wannan soyayyar yan uwantaka? Lallai yarannan suna san junansu.


Ya juya da nufin komawa daki, motsinsa ya sanar dasu wanxuwarsa a gurin, yayi saurin cewa da Faty "haj Faty barka da xuwa, ina wuni? " dan haka kawai yaji ta masa kwarjini duk da cewa xai girmeta da kadan ko kuma suyi sa anni.


Ta kalleshi cikin tsana, sannan ta kalli yar uwarta dake kwance kan cinyarta. Yayi tas yayi qiba yayin da Mimi ta tsummace da qare kamar me jinyar shekaru da yawa. Ta amsa gaisuwarsa sannan ta dora da cewa " ranka ya dade ya akai akabar Mimi ciwo yaci qarfinta haka? Ciwon Mimi fa ciwone me hadarin gaske kuma yana da alaqa da xuciya, duk sanda ciwonta ya tashi inbai samu kulawar gaggawa ba hakan kan iya jawowa arasa rai. Kuma babbar abunda ke motsa lalurar Mimi bacin rai"


Yayi wuqi wuqi, yana kame kame da bawa Faty haquri. Tace to gobe da sassafe xanxo in kaita asibiti dan naga abun yayi worst, xansa ayi mata booking tun yanxu.


Cikin kunya yace "to Allah ya kaimu, Allah ya bata lfy kuma za a kiyaye in shaa Allahu"


Ganin magariba ta kawo kai yasa Faty tai nufin tafiya, ta karanci matsalar Mimi harda yunwa aciki. Sannan ko zafin wannan gidan ya isa ya tashi ciwon Mimi.


Mimi kamar tabi Faty takeji, kuma ganin yar uwarta da daidaitawarsu yasa tasamu rangwamen ciwon. Faty ta lallabata da cewa tayi haquri gobe da asuba xataxo kuma, tayi wanka ta shirya kafin taxo din.



Fitar Faty befi da minti 15 ba wani yaro ya shigo da leda yace gashi inji wata mata fara a mota tace abawa maryam. Ta karba ta bude taga freshyoo me sanyi qarara guda uku.


Atake ta bude ta shanye daya, sanyin ya ratsata ta kuma bude wani tasha rabi sannan taji ta qoshi. Tayi hamdala tare da cewa "Allah sarki dan uwa rabin jiki"


Da xumudi ta kwana, saboda tana murna gobe xata fita bayan wata biyu a kulle a gida.


Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣3⃣

Dedicated to
Maryam Baita

Asubar fari Faty ta gama shirinta na tafiya, har breakfast ta hadawa Mimi. Taiwa Ahmad sallama ya kawo kudi ya bata da nufin taiwa Mimi amfani dasu a asibiti.


5:30 AM agidan Mimi tai mata, ta samu Mimi tayi wanka amma tana zaune bakin gado bata shirya ba saboda jikin ya motsa mata. Suka gaisa da Badaru ta shiga cikin daki.


Haka ta dunga bincika drawern Mimi da nufin dubo mata kayan da zata saka, domin duk kayan sun yamutse (anyi wanki babu guga). Gashi kayan sai qarnin sabulun wanki suke. Dakyar ta samowa Mimi zani da dankwalin atamfar dutch wax (holland) da shirt (domin rigar atamfar tayi mata yawa saboda ramar da tayi) ta saka. Ta dakko humra ta zazzga ta murxa a jikinta (domin humrar kadai take dashi, turarurrukanta tuni sun qare, dan bata saka turare daya tafi gane ta hada kaloli da yawa. Kuma da Badaru suka hadu suka qarar tunda shikam baya siyan turare ya saka sai da yaga Mimi dashi ya tayata suka qarar anga banxa 🀣) ta dan gyara fuskarta, ta hade kitson kanta tasa ribbon. Ta yafa mayafi kumar suka fito.

Suka tadda Badaru a parlour ya dakko 500 ya bawa Mimi tare da cewa "ga wannan ku riqe ko za'a buqaci wani abun" Faty tai saurin cewa "no bashshi babu abunda xai gagara da ixinin Allah" .


Bakwai a AKTH (Aminu kano teaching hospital) tai musu inda Faty ke aiki. koda likita yaxo ita ya fara gani saboda sanayya da kuma booking din da sukai.


Suka gaisa da Faty likitan mai barkwanci, yana duban Mimi ya duba file dinta dake gabansa yace " fatima kina da wannan African queen din shine baki bani na aura ba? " Faty tai murmushi tace "Dr babu rabone shiyasa baku taba haduwa ba, amma Mimi ai tana xuwa nan"


Ya duba record din ciwon Mimi, yace "maryam meyasa kike sa damuwa a ranki? Bakisan ciwonki bayason damuwa ba? ". Mimi dai shiru tai masa kanta na qasa.


Ya rubuta allura yace Faty taje ta karbo yanxu a pharmacy ta kawo masa xai mata. Allurar 9k ce saboda haka ya rubuta note, dan acikin albashinsa xa a cire. Faty ta dunga yi masa godiyar karamcin da yayi mata, yace bakomi ai zaman tare ne ya kawo.


Bayan fitarta, nasiha ya dunga yiwa Mimi cikin hikima. Duk cewa baisan matsalarta ba. Suna haka Faty ta dawo, ya fasa allurar ya nemi jijiyar hannu yayi mata, sannan ya buqaci ta zauna ta huta xuwa 10 minute saboda allurar nada qarfi.



Cikin qanqanin lokaci, Mimi taji nauyin da qirjinta yayi ya sauka, numfashinta ya koma fita normal. Ta dago ta dubi likitan tace "nagode Allah ya biyaka da gidan aljannah naji dadi". Yayi murmushi yawwa maryam nagode da addu a Allah ya qara sauqi, suka dauki takardar magunguna suka fita.


Suka tsaya cikin asibitin suka sai magunguna. Sannan Faty ta tsaya ATM ta ciri kudi suka tafi. Ta miqawa Mimi travelling mug cike da tea murtuk dashi (hadin kauri inji Mal kabiru dadin kowa πŸ˜‚) tace shanye. Mimi ba musu ta shanye domin tana ganin shayin yawunta ya tsinke domin rabonta da shayi da madara tun madarar amarci. Bayan ta gama sha ta miqa mata food warmer cike da soyayyar doya da kwai da miyar qoda a gefe. Tace "kici ki qoshi dan ba gida xan
kaiki ba". Taci doyar ta qoshi nak, atake wata nutsuwa ta saukar mata. Lallai ta yarda matsalarta harda yunwa a ciki.


Direct zoo road ta tsaya inda Mimi keyin saloon, ta ajeta tace a gyara gashinta a wanke mata qafa, sannan ta tafi tace xataje ta dawo.


Suka taya Mimi ta tsefe kan, aka shamfe shi, sannan aka dora da steaming. Akai mata gyaran fuska (cire gashin fuska) ba abunda bai buqatar gyara, nan da nan saiga Mimi tayi tar fuskar ta washe.


Ana wanke mata qafa Faty ta dawo, ana gamawa ta biya kudin suka tafi. Direct shoprite suka nufa, suka fara da gurin electronics Faty ta sayi reachargable fan (fankan da akewa chaji). Sannan suka shiga gurin provision tace Mimi ta dau duk abunda take buqata, dake Mimi tasan ko bata dauka ba Faty fada xatai mata shiyasa tadau duk abunda tasan tana da buqatarsu, kamarsu : mayan robobin madara da milo, omo, sugar, pads, toothpaste, cookies da sauran kayan amfanin gida. Faty ta qara mata da wasu kayan shayin irin na sachet da catoon din cake da caton din freshyo da su malt da exotic duk catons. Ta kalli Faty cikin soyayyar yan uwantaka tace "ya Faty basu yawa ba kuwa? Karba ki dorawa kanki wahala" ta kalleta tace "Mimi yanxu dan na miki abu ya xama wahala kenan? Yaushe muka fara haka dake? Ta dafa kafadarta tace, Mimi ina qaunarki mu kadai mama ta haifa, ina roqon Allah indai xai bani abunda bazan Mora miki ba kada ya bani shi ko menene" Mimi tai saurin fadawa jikin Faty suka qanqame juna. Kudi sosai ta biya na siyayyar da sukai, sannan suka dau hanya.


Lokacin da suka isa gidan Faty qarfe biyun rana, adaddafe tayi sallah sabida yunwa dake damunta. Tana idar da sallah taje kan dining table, ta cika plate da jellof din macaroni da hadin salad tayi tai qat ta dora da pepper soup. Duk abunda take Faty na ankare da ita, tabbas Badaru yana yiwa Mimi horon yunwa domin ada Mimi bata cikin jerin mata masu cin abinci, amma yanxu har mamakin cin da Mimi tayi take.


Abincin yana fada mata ta nutse akan royal bed din Faty wanda yasha shinfidu tausasa na alfarma, sanyin AC na ratsata tayi bacci me dadin gaske.

Bata farka ba sai 5:16 pm tayi salati, tare da miqa. A gaggauce ta shiga bandaki ganin lokacin sallah ya qure. Sai dai tana cire pant dinta da nufin yin wanka ta tarar period dinta yaxo, duk kuwa da cewa lokacinta yayi har ya wuce batai ba. Tai mamakin xuwan period din ba tare da ciwon mara ba, ko hakan yana nasaba da

Please Login or Register in order to submit comment