Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yana hawa gadon ya amshe wayarta da take chating ya ajiyeta gefen gado, ya fara balle mata botiran gaban shirt din jikinta. Shauqin son Mimi din ne yau yake damunsa kuma dama anjima ba a hadu ba, ya fara binta da hot romance dinsa kamar yadda ya saba, sosai yakeson wankewa Mimi zuciya saboda bacin ran da tayi dazu.




Taga abun nasa na neman zarcewa ta riqo fuskarsa ta qura masa ido ya fara futa hayyacinsa, taji tausayinsa tace "ya Bature bani da tsarki fa" bai kulata ba sai maida fuskarsa da yayi yana lasar wuyanta kana yace "haba Mimi ni xaki yiwa wayo?" ganin da gaske be yadda ba taci laya "ya Bature wlh da gaske nake" ya dago ya bar abunda yake jin ta rantse yace "yaushe hakan ta faru bansani ba?" tace "yau da asuba na tashi dashi, nima nayi mamaki don banji ciwo ba ko kadan sai ganinsa nayi" ya danne abunda yake taso masa yace "to Allah yasa ciwon ya rabu dake kenan" ta amsa adduar da yayi. Ya matseta tsam a qirjinsa tana shafa kansa har ya samu relief.





Allah Allah yake ya isa office ya samu Hanifa yaji dalilin abunda tayi masa a jikin rigarsa jiya, yace da driver ya qara sauri don yaso makara tunda sai da suka kai Anty mami.




Hanifa ta shigo gaisheshi kamar yadda ta saba, bai amsa ba sai tambaya yayi mata cikin daure fuska "mesa kikasa min lips dinki jikin rigata jiya?" tayi tsit kanta a qasa, ya kuma maimaita tambayar yana waro mata idanu. Cikin firgita da yanayinsa tace "Sir, ba ba ba nice ba" ta fada tana qiqina. Ya buga table din gabansa cikin tsawa yace "to uban waye inbake ba? Nine kenan? Tunda daga ni sai ke a office din" tai tsuru tsuru a tsorace take dashi sosai don fada yake kamar ya daketa. Ya qarashe fadansa da cewa "to inma kinyi donki haddasa fitina tsakanina da Mimi ne to kinyiwa kanki don bakison darajar aure bane shiyasa kikai haka, kuma fitinar da kikai niyya ba ayiba don muna da fahimtar juna da matata. Wlh Hanifa kika kuma yin abunda kikai sai kin bar office din don canjaki xansa ayi, da bacin ran Mimi gara in rabu dake har abada" ya qara watsa mata kallo "get out of my sight"




Ta fita wajen office din tana hawayen baqin cikin cewar da yayi da bacin ran Mimi gara rabuwa da ita. Ta ciro waya ta kira gwaggoriya ta fada abunda tasa tayi tayi amma ba a dace ba don hakan ya janyo mata cin mutunci. Gwaggoriya ta bata haquri da cewa karta kuma hakan tunda zai dau matakin korarta a office dinsa, ta kwantar mata da hankali da cewa indai da malamai a duniya bazasu watsar da makamansu ba sai ta auri sulaiman.



******* ******** ********


Tun daga ranar Anty mami ta tsiri indai taje office ta dawo da daddare sai ta bawa Mimi aikin lecture din da sukai ta shigar mata a system, Mimi kan shafe tsahon dare har xuwa 2 na dare tana typing kuma ko xata kwana a xaune Anty mami baxata tausaya mata tace taje ta kwanta ba har sai ta gama, wanda a lokacin mami takai wajen kai 10 na baccinta. Kuma tayi hakanne don ta hana Bature da Mimi damar kebewa suyi soyayyarsu tunda Baturen ya fara bijirewa hirarta ta dare yana mata qaryar ciwo.





Ranar data farasa Mimi wannan aiki Mimi sauri ta dungayi don ta gama ta tafi gurin mijinta wanda tasan baya bacci sai a jikinta. Tana gamawa tai wa Anty mami dake gyangyadi sallama, anty mami ta wartsake jin Mimi har ta gama shigarda uban aikin data bata a syatem. Tace cikin mamaki "kai amma kinyi sauri kina da saurin typing, bari inbaki ragowar ki shigarmun" Mimi cikin kunya tace "Anty mami bari inje in kashewa ya Bature fitila in dawo, nasan yayi bacci da fitila a kunne" Anty mami ta daure fuska tamau tace "Dallah zauna kimun aiki, jarababbiyar banxa inda shi ya damu dake yadda kika damu dashi ai da tuni ya biyo sahunki" ta xauna jiki sanyaye ta fara aikin data bata.



Acan bangaren kuma Bature yagaji da jiran Mimi ya kasa bacci sai juyi yake, ya dubi agogo 12:48 AM, ya miqe ya nufi dakin Anty mami.




Ya tarar da Anty mami na bacci Mimi na gefen gado tana mata aiki kamar tare zasu raba kudin, shigarsa yasa mami ta tashi. Abun dariya wai saita dubeshi tace "lfy?" yadanyi dariyar jin abunda yace "Mimi na biyo taxo muje mu kwanta naga daya saura" ta basar dashi ta koma xata kwanta, Mimi ganin haka tace " Anty mami in bishi?" jin furucin Mimi ta miqe tace da Bature "fita kaban guri, inta gama xata dawo ai basai ka biyota ba ko so kake ka nuna mun ban isa da ita ba" ya fita waje jin abunda tace. Ta juya gurin Mimi tace "ke kuma aikin nawa xaki bari ki tafi gurin miji ko? Ke ko tsoronsa bakyaji? Dubeshi qatoto dashi kita binsa yana daddanneki" Mimi dai sunkuyar da kai tayi tacigaba da aikin. Bata gama ba sai 1:26 ta miqe a gajiye tabar dakin donkar Anty mami ta kuma sakata wani aikin.




Ta sameshi ya jera fululluka a gabansa ya rumgumesu abun tausayi ta shige jikinsa, jinta jikinsa yasashi tashi xaune. Ya jawota yace "Mimi kiyi haquri nasan duk Anty abunda Anty mami ke miki inajin babu dadi kawai ina haquri da itane" idonta yadan kawo ruwa, tace "ya Bature ada Anty mami tana sona amma tundaga bayyanar maganar aurenmu ta tsaneni ta kuma canjamun." yana share mata hawaye yace "bakece Anty mami bataso ba, nine bataso na aurin qayatacciyar mace irinki ba. Ta fiso ta aura miki dattijo irin Dr. Mijinyawa yadda xaki xama sillar samun kudinta a koda yaushe ta buqaci hakan. Shiyasa ta ke miki hakan" ya canja salon maganarsa xuwa wasa da xolaya don ya cire mata damuwa yace "kuma abunda bata saniba shine; inda kike jarababbiyar nan data aura miki wancan tsohon ai da baxai iya miki ba, nidin dai nike iyawa jarabarki"πŸ˜† jin haka ta juyo ta dau filo tana masa dukan wasa da cewa "nice jarababbiyar ko?" shima ya dauka yana dukanta suna dariya.





Cikin sati biyun da Anty mami tayi a gidan Mimi taci gwagwa a hannunta ta hanyar sata duk wasu ayyukata na office ga kuma hantara da gyara koda agaban yan aikin gidan bata lura hakan kan iya ragewa Mimi daraja a gurinsu. Inkuwa weekend ne tana gida komai Mimi tayi bata iya ba, gashi Kullum dare bata barin Mimi sai kusan qarfe biyun dare take komawa gurin mijinta tun be saba da hakan ba har ya haqura ya saba.





Mimi sai yanxu tagane abunda ke hada Anty mami da yasmin fada, babu shakka irin wannan abun da take mata yanxu ta nemi yiwa yasmin ita kuma ta bijire.




Shikansa Bature duk ya fara gundura da xamanta duk kuwa da irin qaunar da yake mata sabida yadda ta takurawa matarsa da kuma hanashi sakewa da ita.





Ranar monday ta tafi wanda yayi daidai da kwananta 15 a gidan, harda kukanta duk yadda Mimi tagaji da wahalar Anty mami saita tsinci kanta da kewarta, lallai ranar naka sai naka dadin xama kuma sai bare.



Ranar da wuri suka kwanta ita da mijinta abunda suka dade basuyi ba, duk jikin rawa yake akanta kamar bai taba saninta ba. Ta katseshi da nuna masa batason abunda yake shirinyi. Ya marairaice mata sosai da magiya kuma dama shidin yakan dade bai buqaci mace ba, amma duk randa buqatar taxo masa baya iya haquri ko kadan. Ita kuma yau sam she is not in d mood.



Ya fara mata dadin baki "haba Mimi ninefa in wasa kike don Allah ki dena kinsan bana iya haquri innakai haka" yayi mamakin ganin ta bijirewa duk wani sweet mouth dinshi. Ya riqe kafadunta yana kallon kwayar idonta "Mimi tunda na aureki yauce rana ta farko ta kika bijirewa shinfidata, nasan laifi nai miki shiyasa xakimin wannan hukuncin amma Dan Allah kiyi haquri bazan iya juraba kinga bani da wata matar sai ke ki bari insami nutsuwa sai ki fadamun laifina kinji Mimi na a yafemun" ta cire hannunta daga nasa ta sauka akan gadon ta koma kan sofa ta kwanta, ta lura duk yadda xatai masa bayani idonsa ya rufe baxai fahimta ba gara ta canja makwanci inyaso ya haqura dole don yau gani take ko mutuwa xaiyi baxata bashi jikinta ba don sam bata raayin abun kuma ita kanta batasan dalilin hakan ba.





Baki sake kamar sabon shashasha yake kallon Mimi da sabon salon raba musu makwanci yau. Ya tashi ya nufita halin da yake ciki yasa har tsigar jikinsa na tashi. Ya riqe dantsen hannunta yace "Mimi wani abun kika koyo na guduna a shimfida?" ta fusge hannunta a xuciye itama tace "tunda nace banaso ka rabu dani mana ko dole ne?" ya tsuguna gabanta jiki a sanyaye ganin Mimi yau ta canja masa yace "maryam kodai abunda Anty mami tai miki ne kike daukar fansa a kaina? Naga ai na baki haquri ko kuma nima ba a sona take miki hakan ba" jin abunda yace itama nata jikin ya danyi sanyi tace " ba wannan bane xan iya cemaka na manta da abunda tayimun kuma Anty mami ai yar uwata ce dole nai haquri da ita tunda inason qaninta. Kawai dai abun ne banaso Don Allah ka haqura"



Ya miqe yaje ya kwanta akan gado ruf da ciki yana runtse ido. Ita kuma ta kwanta kan sofa. Kusan awa daya da kwanciyarsa ya kasa bacci sai juye juye yake, yayin da ita tuni ta sami bacci. Yaga alama indai yanason ya runtsa a daren nan to saiya fitar da abunda ke cikinsa, ganin bashi da xabi ya tashi ya nufi Mimi.





Cikin baccinta ta jishi ya turmusheta iya qarfinsa, ta bude ido ta fara kai masa duka da hannunta a qirjinsa iya qarfinta tana kuka tana cewa "banaso, nace maka banaso inkayi mutuwa xanyi ka rabu dani" ya hada hannunta ya riqe tsam ya fara shigarta a hankali don bata bashi hadinkan yi mata romance ba. Tana jinshi jikinta tayi shiru tsit tabar kukan, matar da tace bataso sai gata tana nunfarfashi. Sun dau tsawon lokaci suna abu daya sannan ya gyaleta ya dauketa ya mayar kan gadon suka kwanta.





Sai dai a wannan daren basu rintsa ba don kwana tayi bata da lfy, xaxxabi take me zafin gaske harda rawar sanyi. Ya kashe AC ya kulle Windows ya rufeta da jibgegen blanket amma bata daina jin sanyin ba. Gashi kusan duk minti biyar saiya rakata bandaki fitsari, haka suka kwana har ya fara zargin kansa da haddasa mata ciwo, wane haukane ya kaishi yin sex da mace bataso kamar wani bagidaje? Ga abunda ya jawo nan.



Haka suka kwana da asuba ma a gida yayi sallah, ita kuma a xaune. Tana idarwa ta fara bacci, shikam ko falo bai fita ba bare wani office yananan bakin gado yana gadinta tana bacci shi kuma ya na gyangyadi. Yayiwa mr Alex waya yadau excuse ya fada masa madam ce babu lfy.




Sai 11 safe ta farka ras da ita kamar batai ciwoba jiya cikin dare ya hada mata ruwa tayi wanka, suka fita cin abinci a dining itace ma kedan kunyar abunda tai mai jiya, ya nuna mata babu komai ajixanci ne irin na Dan Adam shima ya bata haqurin hakke mata da yayi ya fada mata ba halinsa bane jiyanma ya rasa abunda yasa haqurinsa ya gaxa. Bayan sun gama ta shiga gidan Farida, shi kuma bacci ya koma.



Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 5⃣6⃣



Babu jimawa babbar sallah taxo, hutun babu yawa kwana hudu ne kawai. Ranar arfa suka isa da safe kuma a ranar suka kewaye yan uwa da daddare bayan sunsha ruwan axumin arfa da akai. Kamar yadda suka saba ko ina maraba ake dasu, mama harda bawa Mimi kayan qamshi irunsu kanumfari da citta wanda xatai aikin naman sallah. Mumy kuwa da sukaje cewa tai da Mimi karta bawa kanta wahalar aiki irin na wancan sallar ta samo mata yar tayin aiki kuma ga Aisha nan yar aikinta ta yarda da ita sosai ta bawa Mimi. A gidan hajja kam sun shafe kusan 11 dare suna hira da kakanninsu cikin nishadi, Mal manu adduoi yadunga bawa Mimi kamar yadda ya saba yana cewa ta dunga yiwa kanta da Bayahuden mijinta. Su Faty har sun rufe gida suka buga musu, ganin sune har sun kwanta Ahmad ya taso Faty wacce cikinta yayi wani irin mugun girma don har ya wuce watanninsa na haihuwa ta kumbura suntum. Ta tausaya mata sosai lallai mata suna wahala da ciki, Faty tana dan dariya tace da Mimi "karki damu an tabbatar da lfy lau muke ni da Baby kawai lokacin da Allah ya dibar masa na xuwa duniya ne beba" haka dai suka rabu cikin kewar juna tana fadawa Faty tana haihuwa ta fara fada mata ranar xata taho kano ya Ahmad yace "to unguwar xoma"





Washegari idil adhha, suna sakkowa idi yayi layya sa da rago ya yanka, kuma nan take ya rabar da naman san gaba daya ga maqota da danginsa akaita kaiwa. Kayan ciki kawai ya bari da naman rago, maaikatan da mumy ta samo mata su sukai gyara naman (kayan ciki) jikin ragon kuma aka ratayeshi. Ta tsaya ta kula da suyar akai mai kyau da tsafta. Rana ta biyu da sallah da daddare sukaje gidansu Farida gaishesu, Mimi ta dibarwa ummansu soyayyan nama. Acan suka tarar da Farida sai shagwaba take xubawa. Umma taji dadi ta bawa Mimi danbum nama ita da Farida cikin bokitai da kilishi, washegari uku ga sallah suka koma Abuja kamar yadda sukaxo su 4 sabida washegari talata xa a koma aiki hutun da federal ta bayar ya qare.



(Eid Adha Mubarakh, Taballallahu minna wa minkum)

******* ***** ******* ****


Sati biyu kenan da yin sallah, suna kwance bayan sallar asuba wata irin yunwa ta tasheta. Ta tashi zaune baya kan gadon, ta nufi dakin motsa jiki dake can qarshen falon. Acan ta taddashi kan gym yanata motsa jiki sai zuffa yake. Ta kalleshi "yaushe ka tashi bansani ba?" ya bata amsa "aini ban kwanta ba ina ganin kinyi bacci na fito tunda naga yanxu ke bakyason motsa jikin kin xama malalaciya" ta yamutsa fuska "wlh ya Bature ni kaina bansan abunda ke damuna ba these dayz in nayi haki nake nafi gane inta bacci" yace "inaga gajiyan tafiyane har yanxu bai barki ba" batace komai ba ta nufi kitchen samawa kanta abunda xataci.




Dafadunkan shinkafa ta dora, ta samu barkono ta dakashi ta afa kana ta yanka albasa ta xuba manja. Girkin dai gwanin ban haushi kamar girkin yar koyo, amma ya xatayi haka takeson ci. Ai kuwa tana tafasowa yaji ya cika kitchen din, sai tari take ahaka ta gama girkin ta xubo a plate kana ganin abincin kasan zaiyi yaji don ga yayan barkono nan burjik akai sai kuma manja kamar yayi magana. Gidan gabadaya ya kaure da qaurin girkin wanda shiya fito da Bature daga daki yaxo yaga ko wani abun aka dora aka manta. Yayi turus lokacin daya hangi Mimi da plate din shinkafa agaba da wannan farar safiyar sai loma take ga bottle water a gabanta robarsa sai diga take sabida sanyinsa.




Cikin mamaki yace "Mimi? Kece ke cin wannan abun me qauri haka da safe? Lfyar ki kuwa?" ta kalleshi na second 2 tacigaba da lomar shinkafarta karta huce, ya qaraso gabanta ya riqo hannun data dibi abinci xatakai baki yace "ke meke damunki haka?" tace "ya Bature don Allah ka kyaleni inci yunwa nakeji kuma wannan nake shaawarci" ya saketa ya koma kujerar dake fuskantarta ya xauna tana naxarinta, sai data cinye shinkafar nan tas ta kwankwade ruwa roba daya me axabar sanyi.



Tundaga ranar yake kula da duk wani takunta, gaba daya ta canja Kullum cikin cin abinci ta manja take safiyar duniya sai tayi wannan dafadukan tata me qauri taci in kuma ba itaba ta kwada garin kwaki tasa manja da yaji tai taci kwadayi dai kamar me, kuma duk abunda take shaawa sai taci ta qoshi take samun nutsuwa.



Ranar da abun ya isheshi cewa tai masa "ya Bature a ina xan samu magarya?" ya kalleta cikin rashin fahimta yace "meye magarya?" ai tanajin haka ta saka kukan shagwaba wai ya raina mata hankali ita magarya xata sha. Lokacin dawowarsa kenan daga aiki, dayaga abun nata da gaske ne sai ya ciro waya yaiwa ishaq text don bayason taji abunda xai fada. Ya kalleta yace "yi shiru ba magarya xaki sha ba? Tashi muje gurin ishaq sai ya fadamun inda xaa samo muje in siya miki" tanajin haka ta miqe ta saka hijab dinta na sallah ya tasata gaba suka shiga gidan ishaq.




Suka tararsu a falo, ishaq ya saka safar hannu ya matso kusa da Mimi take zaune yace "maryam muga hannunki" ta kalleshi kana ta maida idonta kan Bature dake gefenta tace "nifa lfy ta qalau" ishaq yace "munsani ai ba cewa akai baki da lfy ba just wani gwaji xa ai miki" jiki a sanyaye ta miqa masa hannun, ya qurawa tafin hannunta ido sannan yacigaba da jujjuya hannunta, ya gwale idonta yana dubawa sannan yace ta fito da harshenta. Bayan ya gama dube dubensa ya fara yimata yan tambayoyi, tambayar qarshe itace yace yaushe rabon da taga period. Ta fada cikin tunani don ita har ta manta da wani abu period don rabonta da yi tun Anty mami na nan, kardai ace ciki gareta? Anya kuwa hakane? In gaskiyane ya kamata ita ta fara sani, amma sabida ta riga ta sawa kanta baxata haihu ba shiyasa bata kawo ciki gareta ba.




Maganar ishaq ta katseta, inda yace da Farida taje da Mimi toilet tayi fitsari ya bata kwalba. Sukaje tai fitsarin, bayan fitowarsu ya shiga toilet din kamar 10 minutes ya fito da tsinken gwajin ciki a hannunsa yana cire safar hannunsa ya kalli Bature daya miqe tsaye yana jiran cewar ishaq din. Ya bugi kafadar Bature yace "sai yanxu na yarda kai din namiji ne ba mace ba kamar yadda nake fada maka abaya, na yadda tunda ga Mimi nan dauke da cikinka"



Bature ya tsurawa ishaq ido yana kallonsa, can jimawa idonsa ya kawo kwallah. Tabbas tunaninsa ya xama gaskiya Last period din Mimi itace wacce tayi Anty mami na nan, sannan kuma a xatonsa randa ya kasa bacci Mimi taqi yadda dashi har yayi mata dole a ranar ta dau ciki. Ashe shiyasa ya kasa haquri, rabone yasa yayi mata haka. Allah azeem.



Mimi kuwa kamar an dasata akan kujera haka tayi, da gaske itace keda ciki kodai mafarki take? Lallai Allah maji roqon bawa. Farida ta taba ta tana murmushin farin ciki tace "ba kuka xakiba besty godia xaki ga Allah da kuma adduar Allah ya saukemu lfy. Dama can ni ban yarda cewa baxaki haihuwa ba kawai dai abune na lokaci, gashi kuma Allah ya kawo mu"




Bature ya tsuguna a gaban Mimi, yace "maryam burina ya cika xan samu zuri a dake, ya fara share mata hawaye meye na kuka kuma?" tana dariya hade da kuka tace "kaima ai kukan kake" yace "aini kukan farin ciki nake" tace "nima haka" suka saka dariya a tare. Ishaq da Farida na tsaye na kallonsu. Yaja hannun Mimi sukayi musu sallama suka wuce gidansu. Har sun fita suka dawo yace da ishaq "Dan Allah broz banaso kowa yasani, nafiso inya bayyana kowa yagani" ishaq yace "baka da matsala"





Ranar taga gata gurin Bature sai wani riritata yake, kamar kwai a cokali.



Can dare ta tashi ta dunga addua da godia ga Allah daya nuna mata wannan rana, bayan ta idar gaban mudubi ta tsaya ta daga rigar baccinta tana kallon shafaffen cikinta wanda akacemata wai da Da aciki. Bataji tashin ba sai ganinsa tayi ta cikin mirrow yaxo ta bayanta ya xiro hannunsa yana shafa mararta a hankali sannan yana kallonta ta cikin madubin. Cikin kunya ya ta juya ta rungumeshi, ya dauketa cak ya mayar kan gadon.




Ya fara magana "Mimi ki fadi duk abunda kikeso inbaki ko in miki sabida kinmun abunda yasani farinciki wanda bantaba yiba" ta matso jikinsa ta kama hannunsa tace "ya Bature kome nace kaimun xaka iya?" ya riqo fuskarta yace "in shaa Allah indai inada iko dashi xanyi miki" ta xama serious tace "so nake kaimun alqawari baxakaimun kishiya ba iya rayuwarmu" yayi gaggawar sakin fuskarta dake tafin hannunsa ya kauda kai gefe yace "maryam meya kaiki irin wannan maganar?" tasa hannu ta juyo dashi tace "azatona basai na nemi wannan alqawarin ba xakaimun shi, amma sai gashi bayan na karya billena na nema har turjemun kake. Ca nake sabida bani da damar haihuwa a koda yaushe kana iyayin aure amma yau da muka tabbatar da mun sami DΓ‘ ai ya kamata in san matsayina ko?" ya juyo yana kallonta, ranta a bace yake don ta daure fuska tamau ya kwantar da kanta akan cinyarsa ya fara magana "maryam bakya gani inna dauri kaina nai miki alqawari Allah yakan iya jarrabata da qarin auren? Wanda yin hakan xaisa mutuncina ya xube a idonki ki dunga kallona a matsayin maqaryaci?" ta katseshi "dakata, nagane inda ka dosa ada naxaci sabida rashin haihuwa kana iya qara aure, amma yanxu nagane sabida baka aureni budurwa ka sami budurci a tare dani ba shiyasa xaka buqaci aure anan gaba" ya riqota don ta fara qure haqurinsa cikin bacin rai yace "karki kuma hada shirmenki da cewa bansameki budurwa ba, ai nasan da hakan na aureki kuma haka nayi raayi. Yadan sassauta murya, maryam bani da raayin xama da mace sama da guda daya amma bansan ko nan gaba ba sannan duk yan uwana da iyayena kinga wanda yake da mace sama da daya? Mu abun kamar a jininmu ne da mata daya muke rayuwa amma fa ban miki alqawari ba wannan maganar babu ita" ta fusge daga riqon da yayi mata ta juya masa baya ta kwanta batace komai ba.




Ya bita da kallo saroro, me kenan? Fushi tayi? Ya matsa kusa da ita cikin kwantar da kai yace "Mimi nayi lefi amma kiyi haquri kinji karkiyi fushi" tai kamar bacci take, yasa hannun ya dagota ya fara mata susar qadangare a bayanta. Ta fara dariya babu shiri tana tureshi ya riqeta gam

Please Login or Register in order to submit comment