Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauke murya tace "ko kuma Badaru ya debo ya goga miki ba."



Da xuwansu gida tayiwa Mimi alluran tasha maganin sannan Faty ta daura mata drip (qarin ruwa) domin a cewarta Mimi ta dashe da yawa jikinta na buqatar ruwa da gaggawa.



Kwana 8 da sakin Mimi aka tashi da azumin watan ramadan. Kuma suka tashi ta baquncin Baba Saude (wata yar uwa a gurin Baffa, wacce ke xuwa daga can garinsu Gombe duk azumi da kuma sallah ta karbi kayan azumi ko kuma kayan sallah da Baffa ke bawa yan uwansa nacan taje ta raba) Baba saude irin mutanenne masu fadar gaskiya, dan haka take da baqin jini gurin matan Baffa (Umma da Anty) bayan haka kuma suna baqin cikin abunda take karba a gurin Baffa ta kaiwa yan uwansa na qauye.


Mama dai babu ruwanta cikin wannan shaani, tsakaninta da Baba saude kyakykyawar muamala ce. Duk sanda tazo takan tsinci kwancen kayanta kona Mimi dana dady ta bayar akai qauye a rabar, sannan kuma takan bata yan kudi ta qara akan na Mota. Ko kunsan alheri kan saka qauna, dan haka tafi sauran matan Baffa daraja a gurin Baba saude.


Wannan xuwa da tayi ta tarar da baqin lbrin mutuwar auren Mimi, ta jimanta kwarai domin ta sauyawa halin da taga mimin aciki. Basai anfada ba kasan xaman gidan baya mata dadi, ga uwarta me haquri tasan duk cin kashin da xa aiwa Mimi mama bazatai magana ba.



Ana haka Anty ta fito tana kumfar baki cewar Mimi bata dora abincin shan ruwa da wuri ba. Baba saude ta cafe maganar da cewa "ke yanxu jamila dan yaya buhari ya dorawa maryam aiki sai ku sakar mata har abincin azumi? Ai aikin azumi yafi qarfin hannu daya "

Umma ta shiga cikin maganar da cewa " ai bamu muka sakata ba, ubanta ne ya sakata kuma dole tayi, sannan bamu mukaje taje tai rashin mutunci a saketa ba" Anty ta qara da cewa "kemadai Hajara kike bata bakinki, ai abunda uwa tayi shi yar take maimaitawa, inbaki manta ba ai haka uwar ta dunga yawan aure aure kafin Allah ya hadata da Aminu ta maqale masa sannan daga baya aka dawo kan mijinmu. Waya sanima ko garin yawan asiri akan korarmu abun ya koma kan yarta? Ai maryam gadan aure aure tayi da mugun abu a gurin uwarta, Alhmdl Allah ya mayar mata da mugun abunta kanta kuma in shaa Allahu mutuwar aure yanxu kika fara, da yardar Allah sai kin auri maza goma"


Mimi najin haka ta fashe da kuka me cin rai, mama ta fito daga daki taja hannun Mimi. Baba saude ta harxuqa ta tofa Anty yawu tare da cewa " aniyarki ta biki, kuma ki tuna kina da yaya mata, fata nagari kuma lamiri. Saboda haka wlh ki kiyayi Allah, harshenki zai jawo miki bala in da yafi qarfinki, ba a yiwa Allah ixgili" Anty tace kema taki aniyar ta biki. Baba saude tai saurin cewa "amin, ai duk wanda kikaji ance aniyarsa ta bishi yaji haushi wlh aniyar ba me kyau bace. Kuma indai ana gadon mugun abu ke hana zaman aure da naki yayan basu xauna ba."


Taci gaba da mita ita kadai a tsakar gida, haka al amuran gidannan suka dame? Lallai yaya Buhari inbewa tufkar hanci ba tabbas jamila xata watsa masa gida. Taja tsaki mtsewww. Inbanda abunsa ma meye na damuwa da mutuwar auren maryam? Sama da yaya goma suna gidan miji a xaune dan Allah ya dora masa qaddara akan daya ya kasa dauka. Bare inda mutuwar aure ta zama gama gari, aimu ko acan qauye ba a tsangwamar mace dan aurenta ya mutu.


Umma ta leqo ta taga tace da Baba saude "karki kuma cewa yarsa ce, domin shi duk nasa yayan na gidan miji a zaune basu taba zawarci ba saboda basu ga munayiba" Baba saude ta katseta da cewa "to saiki zuqe jinin maryam daga jikin Buhari domin sharia ta riga ta bashi ya" Umma tace ai shi da kansa yace ba jininsa bace, shi jininsa basa mutuwar aure. Taje can ta nemi inda tayo gadan aure aure.



Baba saude bata kuma cewa komai ba, sai daga murya tayi yanda Mimi xata jiyota tace "ke maryamu kiyi shiru kinji, Allah ya na tare dake, shi dora miki kuma in shaa Allah xai baki mafita"


Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 3⃣0⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)


A haka ta fara axumi wanda ya qarasa ramarta ta qazanta, domin sam abinci baya ciyuwa a gurinta. Ta dage da adduar neman sauki gurin ubangiji, kuma duk wani masoyinta na tayata. Kullum in ansha ruwa Mimi ke xuwa gidansu fauxa su tafi masallaci yin sallar tarawih domin gidansu fauxa yafi kusa da masallacin. Sau tari a masallacin ma bata rasa masu yin zundenta da qusqus din mutuwar aurenta.


A al adar gidan Baffa duk goma ga watan Ramadan yayansa kaf maza da mata, masu aure da marasa aure har na wani garin ana haduwa asha ruwa agida saboda sada xumunci. Kuma uku ga kowacce sallah (sallah babba da sallah qarama) suna kuma taruwa shima aci abinci a sada xumunci ayi hotuna.


To wannan karon ba ai shan ruwan goma ga azumin ba kamar yadda aka saba, saboda ya jafar bezo daga kaduna ba inda yake aiki. Sai da azumi yayi rabi (15) sannan yaxo kuma a ranar aka fara shirin shan ruwan. Yawanci duk yayan gidan mata sukanxo tun azahar a hadu ayi aikin abincin shan ruwa. To yau dinma hakance ta kasance, wadanda ke farin ciki da mutuwar auren Mimi da wuri sukazo sukaga dahir sannan suka dunga shewa suna sakin habaici. Masu hankalin ciki kuwa, abun bai musu dadi ba saboda haka Anty Adawiyya ta jagorancesu sukaje dakin mama suka jajanta mata mutuwar auren sannan suka taushi Mimi tare da bata haquri akan abunda yan uwansu ke mata. Mama taji dadin wannan karamci da sukayi mata ta dunga godia kamar sun bata wani abun.



Azahar kowa ya hallara inka cire ya Faty da bata taso daga aiki ba, duk suna baje a tsakar gidan suna aiki, masu gyara kaji nayi, masu hada zobo nayi masu gyara ayar kunun aya sunayi da masu gere dankali. Baby tai sallama ta shigo jikinta sanye da uniform da alama daga skul take. Baby itace ya ta tara a dakin Anty, shekarunta bazasu wuce 15 ba, tana aji 1 a babbar sakandire (senior secondry).


Tana shigowa wani almajiri ya biyota, "wai ana kiran wacce ta shigo yanxu" inji almajirin. Baby ta murguda baki cikin tsabar fitsara da tashen balaga tace " wlh na tsani naci, tundaga makaranta yake bina maye."


Anty tai saurin fitowa daga kitchen tace "je kace yarinya ce bata tsaiwa da samari" yaron ya fita fadar abunda aka aikeshi.


Anty ta ruqe haba cikin sigar al ajabi tace "kai wadannan yara da farin jini suke, babu dama su fita sai an biyosu. Wlh bari Baffa ya dawo mu xauna ayi magana, gara tanayin candy a aurar da ita inyaso jamiar tayi a gidan mijinta. Aini nadau darasi da barin da ya dade a gabanka, qarshe kwantai yakeyi. Wlh tana candy xan aurar da ita" (kunji fa kamar auren a hannunta yake, mudai munsan koda miji a hannu aure sai Allah yayi tunda aure lokaci ne.)


Rashida ta kalli shashin da Baby take tsaye tana murmushi saboda jin abunda uwarta tace na cewar tana da farin jini, tace "aike Baby ki godewa Allah tun yanxu anfara kawo miki hari, alamar cewa ba zaki Bandaro ba. Saboda wlh in mutum yayi kwantai ko yaje gidan mijin ba iya xama yake ba" ragowar yan jam iyar Rashida (masu qin Mimi) suka saki dariya tare da cewa "wlh kuwa 🀣🀣🀣"


Anty Adawiyya dake gefe ta cije lebe saboda duk wanda ke gurin ya fuskanci inda maganar Anty da Rashida ta nufa, Anty Halima ta kalli Adawiyya cikin takaicin abunda uwarta da yar uwarta sukai (halima yar Anty ce) tace Anty wai haka zamu zuba ido abubuwannan suci gaba a gidannan, infa akaci gaba da haka nan gaba kadan xumunci xai watse mune manya ya dace mu gyara abun. Anty Adawiyya tace " Halima mexance? Ai baka canja mutum kina ganin kwanaki da nai hukunci akan abunda Rashida kewa Mimi qarshe abun fada ya xama tsakanin Umma da Anty. Saboda haka duk wanda aka fada masa yaqiji sai a kyaleshi duniya tai masa nata karatun"



Suna zaune akan qatuwar tabarma da aka malala a tsakar gidan, kayan abinci ne jibgi a gabansu kowa na diban abunda yake so yana ci. Duk zuriar gidan sun hallara tundaga kan Baffa, matansa, yayansa da surukarsa (matar yaya Ali) da kuma jikokinsa. Anata hira ana jin abinci cikin raha, ya jafar ya kalli Baby yace "ke jeki kice Mimi ta fito, inna kuma aiko ta fito bata fito ba sai ranta ya baci." wannan shine karo na 3 da yake aikawa kiran Mimi amma taqi fitowa, kuma ba wani abu ke hanata fitowar ba sai gudun abunda ka iya faruwa inta zauna a cikinsu.


Umma tai tsaki ta dan harari jafar, tace "to kai ina ruwanka da rashin fitowarta, ai dan ta nuna muku mugun halinta ne yasa bata fito ba, tayi abu yazo ya dameta ya hanata shiga cikin mutane."



Wannan karon Mimi tare suka fito da Baby, sanye take da hijab me hannu. Faty bataso tilastawar da ya jafar yayi Mimi ta fito ba saboda tasan dole sai anyi abunda xa aci xarafin Mimi.



Ganin babu guri a inda Baby ta xauna yasa Mimi tayi nufin tsallakewa can kusa da Anty safiyya (matar ya Ali) . Ganin da Rashida tayi Mimi na shirin tsallaketa yasa ta miqe qasa tare turo qatan cikinta, Mimi ta daga qafa xata tsallaka a hankalce saboda kar ace tayi wani abun ko ta buge mai ciki Rashida tasa daya qafar ta tade Mimin. Ai kuwa ta yanke jiki ta fada kan Sumayya take zaune da jaririnta dan 4 month akan cinya, sannan ga kofin shayi sai tururi yake a gabanta. Cikin axama Sumayya ta ture Mimi daga kan jaririnta ta tura mimin kan ruwan shayin tare da cewa "bakya ganine zaki kashemun da?"

Zafin ruwan shayin bai gama ratsa Mimi ba taji saukar mari a kuncinta. Tai dafe kunci tare da dagowa taga wanda ya mareta tai arba da Baffa sai huci yake yana kallonta cike da tsana yace "dan bakisan ciwon haihuwa ba shine xaki fado mata akan jariri? Ke dan kin gaza xama a naki gidan ki haifi naki dan zakixo ki fado musu ka? Ke wace irin muguwar yarinya ce".


Umma tace ai dama tunda aka tilasa mata fitowa batai niyya ba nasan saitayi abunda xata sosa mana rai kuma shine muguntar taki xata qare akan jikana? Rashida na gefe sai murmushin jin dadi take.


Duk wanda ke gurin ya lura da abunda ya faru saboda hasken nefa tanyar a tsakar gidan. Mimi abun yayi mata yawa ga zafin qonewa ga zafin maganganun Baffa, ta fashe da kuka tace " Dan Allah kuyi haquri, inwani laifin nai muku kuka tsaneni dan Allah ku fadamun in gyara" tana kaiwa nan ta shige daki.


Ya jafar da tausayin Mimi ya hanashi daurewa ya kalli Baffa yace "Baffa wannan wane irin hukunci ne? Wlh ina kallon abunda ya faru, Rashida ce ta turota dan me xaka goyi bayansu qonata fa sukayi" Anty tai saurin kare Rashida da cewa karkai mata sharri, kawai dai ta shirya mugutar fadawa kan Rashida tasa ta naqudar dole ita kuma Allah ya bata sa a ta tureta. Baffa ya hau borin kunya da "yimun shiru jafar, kaine ka haifeni? Ko kai xakaimun hukunci a gidana"



Faty tabi bayan Mimi itama tana kuka. Jafar ya kalli shashin da mama ke zaune yaga tananan inda take ko motsawa batai ba sai dai ta kasa cin abincin sai juya tea take da spoon. Anty Adawiyya ta dakko qaramin try ta xuba duk nau in abincin dake gurin ta bawa Anty safiyya tace "kaiwa su Faty daki" Faty na zaune kan kujera tana kuka tana shafawa Mimi jelly a dantsen hannunta inda ruwan shayin ya xaba. Anty safiyya ta bata abincin tace ki tabbatar Mimi taci. Kuyi haquri Allah baya zalunci kuma ya haramtashi garemu in shaa Allah xakuga sakamako.



Faty ta dunga diban abincin da hannu tana bawa Mimi, ita kuwa ba musu ta dunga karba tanaci.



Tun jiya da abun ya faru har ixuwa yanxu da gari ya waye tunani take. Wai shin meyasa indai aure ya mutu a Society dinmu laifin kan zama na ya mace ita kadai? Wai yaushe YA MACE xata samu yanci a Society namu? Wadannan sune tambayoyin da ta rasa me amsa mata.


Kanta ke mugun ciwo, wanda tasan tunani ne ya haddasa matashi. Ga kuma yanxu mararta ta daure, alamu kamar period pain. Tananan kwance, taji ciwon marar ya fara tsananta kuma taji danshi a qasanta. A fili tace "babu ciki a jikina kenan kamar yadda Dr yace" gudun kar ciwon mara ya galabaitar da ita gashi mama ta tafi aiki yasa ta tashi taje parlour ta dakko gwangwanin maltina a fridge tazo ta balli maganin ciwon mara tasha. Lokacin ko ganin gabanta bata iyayi saboda tsananin ciwon kai.


Tana kwance tana murqususun ciwon mara da ciwon abunda Baffa Yayi mata, itadai tun take da Baffa bata taba gani ya dora hannunsa akan wani da a gidan ba sai ita. Koda yake itakam a gidan tana da banbanci da kowa, domin Baffa ya mata abubuwa da yawa da bata taba gani yayiwa wani ba.


Da farko bayan qin biya mata ko sisi a cikin hidimar karatunta, yazo ya takura mata da sunan taqi aure, yayi mata auren dole sannan auren babu dadi bai taba taka gidanta da sunan yaje ganinta ba, duk kuwa da cewa dabiar sa ce xuwa gidan yayansa yaga halin da suke ciki kuma ya musu alheri. Amma ita tunda aka kaita ko waya bai taba yimata ba. Abu na qarshe shine: anyi mata sakin wulaqanci ta dawo gida ya kuma takura mata, takurar da tafi ta farko, ga kuma duka anfara jiya.



A wannan gaba taga ya dace ta karbi shawarar da xuciyarta tasha bata a kwanakin baya, dan haka ta miqe ta dauki kudi ta fita ta tsaya a soro ta aiki wani almajiri ya siyo mata abunda take buqata. Tananan tsaye yaron yaje ya kawo mata aiken, ta bar masa ragowar canjin.



Da magriba ta gama duk wani aikinta ta shige daki tunda ba azumi tayi ba, tabar mama tana shan ruwa a parlour.



Fauxa da tagaji da zaman jiran Mimi ta biyo mata zuwa sallar tarawih bata zoba ta tashi domin biyawa Mimi, dan taji har an tayar.


Ta sami mama a parlour suka gaisa Maman na shirin shiga bedroom tace "qawartaki na dakinta tun dazu kinga ma ko ruwa bata sha ba" tace to bari in dubata.



Shigar Fauxa dakin tayi dai dai da lokacin da Mimi ta daga kwalbar FIYA FIYA (abunda aka siyo mata daxu) xata kai bakinta. Fauxa ta kwala kiran "MIMI" a razane 😳 tare da doke hannun mimin. Kwallah kiran da tayi ya janyo hankalin mama daga bedroom, taiwa dakin tsinke tana tambayar lfy?. Fauxa batabi takan tambayar da mama keyi ba. Ta qarasa ta riqe kafadun Mimi tana girgixata cikin kuka tana cewa "Mimi kashe kanki xakiyi akan mutuwar aure? Shin in kashe kanki wanda ya sakeki yana da asara ne? Mesa xakiyi haka? Duk fa abunda xai faru ya riga ya faru. Ansake ki, an takura miki, anyi gulmarki, anmiki sharri. Inbaki sani ba maganganu da yawa ke yawo akan mutuwar aurenki. Akwai masu cewa cukumar mijinki kikayi kina zaginsa ya sakeki, wasu kuma suce wai sata kikai masa ya sakeki, ke harda masu cewa ya kamaki ne kina lesbian (neman mata) ya sakeki. Amma duk wandannan maganganu da nakeji bana fada miki saboda kar in daga miki hankali. Amma shine yanxu xaki kashe kanki Mimi? Why Mimi, Why. Wlh indai akan baqin cikin namiji kike haka gara ki dena, shin ni ba a sakeni ba? Ni harda Da aka sakeni mutu nayi? Ko takurar da aka yi miki ba ita akemun ba, kafin Baba ya gane gaskiya ya sakarmun mara?"



Maganganun da Fauxa keyi yabawa mama amsar tambayar da take yi, dan haka cikin kuka ta juya tabar dakin. Mimi ta gigice ganin kukan mama dan tasan ba qaramin abu kesa mama kuka ba, tai gargawar biyo bayan mama tana cewa "mama ki yafemun na tuba πŸ˜ͺ"


Fitowar mama tai dai dai da shigowar Faty parlourn, ya Ahmad na biye da ita. Dan bata gamsu da yacce tabar Mimi a jiya ba shiyasa ta kuma xuwa ta taushi Mimi. Ta iske wannan mugun lbr, fauxa ta fada mata tace "WHAT" kalmar data janyo hakalin matan gidan, nan da nan kuwa suka cika qofar dakin mama suna kallo. Ya Ahmad kuwa gurin mama yaje ya tsuguna gefenta yana nemarwa Mimi yafiyar abunda tayi.



Faty kallon Mimi take da wata irin fuska 😑 wacce babu wanda ya taba ganinta da ita. Mimi tana rabe jikin bango, cikin kuka take furta "am sry, am so sry sister" Faty batabi takan haqurin da Mimi ke bata ba, ta kifawa Mimi mari, ta kuma kifa mata wani, ta qara mata. Ataqaice dai sai da tayiwa Mimi mari guda 6 xafafa. Mimi idanunta a runtse, bata dauke kanta ba, ba kuma ta fasa furta "am sorry sister"


Wadanda ke bakin kofa suna kallo abun yayi matuqar girgizasu, domin ba qaramin abu zaisa Faty ta daki Mimi, bama su taba gani ko fada Faty taiwa Mimi ba bare duka. Dan haka kansu ya qulle suka rasa lefin da Mimi ta aikata Faty ke mata wannan hukunci. Kuma ta wani barin abun ya burgesu domin daga Anty har Umma babu wacce daya daga cikin yayanta na sama ya isa yayiwa na qasa hukunci haka, ba ai gagarumin yaqi ba. Kuma daya abun burgewar har wanda akaiwa hukuncin yana bada haquri.



Faty na gama marin Mimi itama ta fashe da kuka, ta janyo mimin ta rungumeta tsam suka xube qasa tana shafa kan Mimi tare da cewa "is Ok sister" Fauxa ma ta matso kusa tana lallashin Mimi cike da yabawa hukuncin da ya Faty tayi mata. A xuciyarta tana aiyana duk renda Allah ya bata yaya mata xatayi iya yinta ta hada kansu kamar yadda mama ta hada kan Faty da Mimi.



Yan kallo kuwa dole suka watse ganin film ya qare. Ya Ahmad ya tafi ya bar Faty ta kwana, saboda halin da mama ke ciki.



Can tsakiyar dare suna kwance kan doguwar kujera, mama dauke da Dady kan cinyarta, sai Faty dake zaune tana bacci Mimi kuma ta tada kai da tata cinyar. Tun faruwar abun Mimi ke bawa mama haquri amma mama tayi kunnan uwar shegu kamar batajin abunda Mimi ke fada, yanxu ma sai kuka take tana qara neman gafarar mama. Mama ta shafa fuskarta tace "na haqura Mimi, amma ko wane irin hali xaki shiga karki qara yunqurin halaka kanki, kinga ku kadai nake daku in kintafi kinbar yar uwarki ni da ita ya xamuyi? Bakisan rayuwarki nada matuqar mahimmacin a gurin mu ba? Danme xaki kashe kanki akan wadanda mutuwarki sukafi so akan rayuwarki? Mimi kiyimun alqawari daga yau zaki cire duk wata damuwa a ranki ki fuskanci abunda ke gabanki. Da ace mutane suna riqe abunda ya riga ya wuce wlh da baqin cikin ya kashe rabin mutanen duniya. Saboda haka past is gone forever, ki gyara present dinki, future kuma ki barwa Allah shi yasan abunda future xata xo miki dashi."



Mimi ta gyada kai cike da gamsuwa da kalaman mama, sannnan ta qudure yin aiki da abunda maman tace mata.


Ta yunqura ta miqe xataje toilet domin canja pad din jikinta da ta jiqe, mama tai saurin cewa ina xaki? Tace " xan canja pad ne" wani farin ciki ya xiyarci mama, jin Mimi taga jini wanda hakan ke nuna babu ciki kenan. Ta dunga godia ga Allah domin batason Mimi ta haihu da Badaru. Tace da mimin muje in rakaki, Mimi ta zaro ido 😳 tace "mama toilet din xaki rakani?" mama na tafiya tace "eh nasani ko ki kuma yunqurin halaka kanki" Mimi ta marairaice tace " mama zargina kike wlh bazan kuma ba na baya ma da nayi kuskure ne."



Yan kwanakin da suka biyo baya ta dan samu sauki, amma fa ba sauqin aikin gida ba saukin damuwar dake xuciyarta a bisa amfani da shawarar mama. Ta kuma yardarwa kanta xatai karbi rayuwa a duk inda taxo mata.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 3⃣1⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Ranar da Mimi tayi wankan tsarki ranar Faty tazo gidan, ta tasa Mimi a gaba harda yan kayanta set 2. Mimi tace "ya Faty Baffa inyaxo ya tadda banyi aiki ba xaimun fada." Faty ta fallara mata harara "xan dura miki xagi Mimi, ana xancen lfyarki kina xancen fadan Baffa? Ko kin manta abunda Dr yace in kinga jini insamiki wani magani?" Mimi ta marairaice tace "ya Faty ai na warke ko sati banyi ina amfani da maganin ba na daina qaiqaiyin, wlh kamar ban taba yiba." Faty ta kuma watsa mata harara tace " ke wlh sai kin bini in yaso in kin dawo Baffa ya kasheki bashi kikejin tsoro ba?" tace tuba nake sis muje 😊



Bayan sunsha ruwa sun huta, Faty ta dakko maganin tasa safar hannu tace da mimin kwanta. Mimi ta waro ido tace "ya Faty😳 yanxu wai saina bude jikina?" Faty tace "a a karki bude insa miki magani, amma ai kin budewa Badaru ko? Mimi najin haka ta kwanta ta bude jiki, Faty ta gama yi mata gwaje gwaje tasa mata magani. Tanata tsaki tare da cewa " wannan mutumin ya cuceki Mimi dole sai anmuki stitches (dinki)" Mimi ta zaro ido cikin kidima 😳😳😳 tace "ya Faty na samu qari ne? Naga masu haihuwa akewa dinki" tayi tsaki tace "ba gara wacce ta haihu dake ba, ita tasan haihuwa tayi. Kuma ba sai lallai masu haihuwa akewa dinki ba. Ba qari kika samuba amma ya miki barna a jikin ki ya nuna mugunta wajen kusantarki, gara ma da Allah yasa nagani amma wannan in kikayi aure ai sai kiji kunya, wata 5 a gidan miji amma wani mijin ya sameki sakwakwa haka ai sai yace qarya ake cutarsa akai."


Washegari kuwa tana dawowa daga aiki tace da Mimi ki shirya in ansha ruwa xamuyi aikin, na siyo kayan aikin masu kyau wanda in anyi basai an ware ba zaibi jikin

Please Login or Register in order to submit comment