Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

5⃣9⃣



Tana sa qafarta a cikin gidan taji duk duniya tai mata zafi amma ta cije sabida taga yana cikin farin ciki bataso ta bata masa mood dinsa. Akan kujera ya xaunarta ya shige ciki ya rage kayan jikinsa ya fito kitchen, dakko wannan dakko wancan haka ya dunga hidima da ita kamar wata baquwa, ita kuma tana binsa da murmushin yaqe.




Yan aikin suka dunga shigowa suna gaisheta dayi mata hannu da jiki, yana murmushi yana amsa adduoin su har aka kira magrib ya fita.




Sai bayan isha ya dawo, yaji dadi kwarai daya sameta akan pray mat tayi sallah. Ya wuce bathroom ya hada musu ruwan wanka yazo ya kwasheta sukayi tare, suka shirya cikin kayan bacci iri daya masu sauqin nauyi. Har cikin daki ya kawo musu abinci yanaci yana bata don taqi saka hannu, suka gama ya kwashe kayan suka koma bandaki suka kurkure baki da lestirine suka dan zauna har xuwa 9:30pm suna kallo a TV din dake bedroom din.



Mimi dai ba kallon take ba, hankalinta a mugun tashe yake don inuwar dodon photo kawai take gani cikin TV din, bayan haka kuma sai gilmawar mutane take gani ta saitin window din dakin.



Anasa bangaren shima yanajin bacci, amma ya dan dakata ne abincin da sukaci ya narke kafin su kwanta.



Dataga abun bana qare bane saita ce masa "ya Bature nikam xan kwanta" ya dubeta yana naxartar da take ciki yace "to Mimi luv" ya tashi don rakata bandaki amma ita ta kasa miqewa, ya lura yace "ya dai Mimi?" ta cije baki tace "qafatace ta dan riqe na kasa miqewa" ya dagata ya kaita, tayi fitsari yace tayi alwala, ta danso tirjewa amma ya tilasa mata tayi. Kana yazo ya kwantar da ita.



Ya kwashe kayan kallon, ya kimtsa komai shima ya dauro alwalar kana yaxo ya kwanta gefenta yana karanto azkar din kwanciya bacci ya tofesu shi da ita ya jata jikinsa yana mata wasanni.




Tayi luf kamar mai bacci, amma bashi take ba runtse ido tayi sabida gane ganen da take. Ta fara samun saqonsa na soyayya, tun tana daurewa har ta kasa ta fara yunqurin kwatar jikinta. Tace "ya Bature ka ajiye wannan rayuwar a gefe don Allah, nidin banason gidannan yanxu daurewa nake kuma ni kadai nasan abunda nake gani, kuma nakeji a jikina, kaga inkace xaka tsiro da wannan abun xafin xaimun yawa xaka xalunceni."



Jikinsa yayi sanyi da kalamanta amma shima yanayin da yake ciki ya qazanta da zai iya haqurin da yayi sabida haka yace "maryam ni kuma haqqina xaki shiga wlh, da ace xan iya haqura dana haqura amma na miki alqawari baxan dadeba ina samun nutsuwa xan kyaleki."




Badan ranta yaso ba abun yacigaba, yanayi tana tureshi kamar yau ya fara kusantarta, haka dai badan yaje inda yakeson xuwa ba koya samu nutsuwar ya haqura dan taqi barinsa yayi yadda yakeso dondaima jarabace irin ta namiji da haqurin yafi.




Ya tashi yaje yayi wanka don baya kwana da janaba, tana kallonsa yaxo ya dauketa itama ya mata. A halin yanxu abunda take gani ya qazanta har mace take gani tana yafitota da hannu. Ta runtse idonta daga kallon matar, ga qafarta ta isheta da xugi kuma abun takaici ta kasa furta kalmar tsari ko guda daya.



Ya jawota qirjinsa yana shafa bayanta har yayi bacci, itakam tafi 2 hours bata samu bacci ba sai daga baya wani bacci cike da qaxaman mafarkai ya kwasheta.





Yau ya rigata tashi sabanin da da ita ke tadashi, ya janyeta jikinsa ya kwantar da ita akan filo yayi toilet don dauro alwala. Gabansa yayi wata irin muguwar faduwa lokacin daya hangi jini face face a gaban rigarsa ta bacci. Ya koma dakin da gudu ya murgino Mimi daga kwanciyar da take ya fara cajeta yana neman daga inda jinin ya fito jikinta don yasan shidai ba ajikinsa ya fito ba itace kwance akan qirjinsa.




Hasken bed side lamp yayi masa kadan, ya kunna wutar dakin haske tanyar abunda ya tashi Mimi kenan. Yana duba duk jikinta ita kuma tana kallonsa a firgice don ta rasa dalilin hakan. Can ta hangi jini malele a gaban rigarsa takai hannu ta taba, da danshi a gurin lamarin dake nuna jinin bai dade da xuba ba. Ta gigice sosai tace "ya Bature jinin meye wannan jikinka, ciwo kaji?" yace "maryam ba daga jikina jinin yake ba a jikinki ne tayani dubawa" sunata duba jikinta ya hango bushashshan jini gefen kunnanta. Ya kamata ya riqe yana tambayarta kunenta na ciwo ne? Tace "babu abunda kemin ciwo sai qafata" da kyar ya tafi masallaci ya barta ita da Aisha. Ana idar da sallah ko adduar da akeyi bai tsaya ba yayo gida, a gaggauce ya shiryata suka tafi asibiti.





Dake ishaq ya kwana akan aiki basu sha wahala ba aka hadasu da sashin kunne, sukai iya dube dubensu babu komai suka bata magani kana sukaje bangaren yan qashi sabida qafar dakyar take takata tana dingishi, suma nan xray akai take aka cire photon consultant yazo wajen qarfe tara ya rubuta report babu komai a qashin qafar sunfi xaton ciwon qafar masu cikine ta fara tun yanxu, suka rubuta mata man ciwon qashi me zafi "volini" aka sallamesu sukayo gida.




Sai wajen goman safe ya tafi aiki bayan ya kai Mimi gurin Farida kuma ishaq yana gida ko wani abun zai taso.




Safna daga gurin aiki gidan Farida ta wuto dan sai yau tasamu labarin Mimi babu lfy ta bakin mijinta abokin Baturen. Suka hadu suna hira tare da sako Mimi aciki amma batasa baki sai dai tai murmushi. Safna ta karbi maganin ciwon qafar ta mulkawa Mimi shi tun daga cinya xuwa tafin qafar. Anty Rabi ma nan ta taho suka hadu har bayan laasar suna tare lokacin kuma Bature ya shigo gidan, yaji dadin yadda ya samesu sun sata tsakiya sunata lallabata. Suka gaisa sannan safna ta buqaci ganinsa suka kebe.




Tace "ya Bature anya wannan ciwo na Mimi baxa a sanar dasu mumy ba? Yadda na ganta da kuma kukan ciwon qafar da bayanin Anty Rabi abun ya tsoratani kuma fa bata magana anya ba ciwon iska bane" ya watsawa safna daquwa hade da harara yace "to bakinki qanin qafarki, innaji xancen nan yaje kano sai nayi mugun saba miki, matsalace qarama kuma munje asibiti akanta anbata magani an tabbatar babu komai sannan kuma ai mun isa kulawa da ita basai anje kano ba kinsan mumy tanaji xatace a dawo da ita gida kuma ni gaskiya ina buqatar matata kusa dani, kuma karki kuma cewa ciwon aljanu ni matata mata da iska. Kedai kawai abunda nakeso dake ki dunga shigowa inkin dawo aiki kina ganin jikinta aimun isa kula da ita, gaki ga ya Taheer gasu ishaq" safna ta jinjina kai dan taga idon ya Bature ya rufe da tsananin son maryam, shi kawai burinsa xamanta kusa dashi kar a rabasu amma inba haka ba kowa yaga maryam yasan ciwonta na iskane. Tace "to shikenan xan dunga shigowa in shaa Allah amma dai ya Bature a hada da addua kuma xansa ayi mata sauka" yace "yawwa safna karki bari mumy taji ko Faty" tace "to"




Yasaka Mimi agaba suka koma gidansu. Kamar jira ake ta shiga qafar ta rikice da wani irin azabar ciwo, ta xube a dai dai kofar shiga falo don tsaiwa ma ta gagara. Ta dubeshi tace "ya Bature xan mutu qafata" ya sunkuya ya shafa qafar kana ya ciccibeta yana cewa "sry Mimi luv xata dena tunda ansaka magani.




A kan gado direta ya shiga wanka, ta runtse ido ta rasa abunda yake mata dadi tayi mugun tsanar gidan ga wata faduwar gaba dake addabarta. Ta dunga jiyo wata murya tana kwallah mata kira a gigice, tun tana sharewa har kiran ya fara yawa ta miqe dakyar tana dingishi ga gumi tanayi sabida azabar ciwon qafa ta nufi kofa don ganin me kiranta, Allah ya saka dai dai lokacin ya fito wankan.









Ya isa gurinta da sauri yana cewa "maryam ina xaki haka?" ta cije lebenta na qasa cikin azabar ciwo tace"kirana ake tun daxu bakaji ba?" ta fada tana nuna masa saitin qofa. Ya kalli gurin data nuna yace "ni banji komai ba Mimi, kunnenki ne kawaia" tasa kuka tana cewa "wlh kirana ake kuma mamace ke kirana don muryarta naji" a tsorace ya dubeta yace "mama kuma? Mexai kawo mama nan da yammanan?" dakyar da sudin goshi yajata suka koma suka xauna. Ya dorata cinyarsa yana qara shafa mata maganin hadi da lallashinta yace "maryam kiyi haquri nasan ni na haddasa miki ciwonnnan, sai da kikace bakyaso na kusanceki amma nabi son xuciyata. Nasan dana haqura da kinanan qalau dake, ya marairaice ya riqe hannunta yana furta i m sry Mimi luv, plz forgive me na biyu kenan in shaa Allah baxanyi na uku ba "binsa take da ido bata fuskantar maganarsa ita kawai burinta ya saketa taje kiran da ake mata don har yanxu kiranta ake kuma da muryar mama.





Da yaga bata hayyacinta sai yaqi fita masallaci a gida yayi sallar sukai jam i tare, sukaci abinci ya bata magungunanta tasha xuwa taran dare suka kwanta. Yauma dai kamar jiya gane gane ta dungayi kafin bacci ya dauketa mara dadi da munanan mafarkai, kuma ya tashi da jini fiye dana jiya a jikinsa wanda yau yaga inda jinin ke diga ta kunnen Mimi data kwanta donyin bacci. Wajen 2"30 AM ya tashi yaga tana birgima a qasa tana hawaye, a razane ya taho gurinta yana tambayarta lfy? Ta nuna masa qafarta yakai hannu zai taba tasaki wata gigitacciyar qara da sauri ya janye hannunsa. Ya taba jikinta xafi rau.



Ya dauki towel da ruwan sanyi ya dunga goge mata jikin ya shafa mata maganin ciwon qafa kana ya bata paracetamol tasha ta kwanta, yayi sa azazzabin ya sauka kuma ta samu bacci. Amma shi kam idonsa kyam a kanta tana sharar bacci akan cinyarsa.




Ya xubawa jinin dake diga daga kunnenta ido, diga yake babu tsayawa yayin da Mimi ke bacci. Wani irin tausayin yarinyar yarufeshi yana hawaye yana tunani wannan wane irin ciwone? Ai sai jininta ya qare wace irin lalurace ta samu Mimi haka ga ciki a jikinta? Kodai laulayin ciki ne yaxo mata da haka? Yana kallonta gami da kuka da tunani har garin Allah ya waye tangararau bai sallah ba. Danma yau saturday babu office saida Mimi ta tashi daga baccin kana ya shima ya tashi donyin sallah. Xuwa wannan lokacin jinin daya xuba jikinta bashi da iyaka, dan wandon jikinsa ya jiqe sosai har bed sheet ya baci.




Ya dunga tambayarta ya jikinta ina ke mata ciwo kanta na ciwo? Ta bashi tabbacin babu inda ke mata ciwo sai qafarta wadda yanxu bata iya yakawa sai dai ya dauketa duk inda xataje.

******* ******* ********


Yan kwanakin da suka biyo baya AL' AMARIN MARYAM ya qazanta sosai, kamar jira ake ta dawo gidan matsaloli sukai chaaaa. Xubar jini daga kunne har sun saba da hakan tunda yanxu hartakai inxasu kwanta sai ansaka zani sabida zubar jinin. Abunda suka fuskanta duk sanda Mimi ta kwanta danyin bacci xubar jinin xatace salamu alaikum domin baya dena xuba saita tashi, duk da cewa baccin ba me dadi take ba.



Qafarta ta kunbura tayi suntum har kyalli take kamar a tabata ta fashe, Mimi dai yanxu bata tafiya sai dai a turata a well chair.




Ciwo yayi tsanani bata um bata um um sai dai komai ayi mata. Kuma duk abunda akace tayi yi take babu musu, babban tashin hankalinsa batacin abinci saiya takura mata ko kuma asaka mata drip.





Shi da ishaq Kullum suna yawan asibiti ana aunata amma antabbatar lfyarta lau daga qafar har kunne babu problem. Sai dai Kullum ana bata maganin qarin jini sabida xubar jinin da kuma maganin bacci.



Kwana take kukan ciwon qafa da kuma ita ya barta taje kiran mama, wai ita a lallai mama ke kiranta. Ta fige ta lalace sosai.



Yasha fadawa ishaq cewa indai cikine yasa Mimi wannan abun to shikam a cire cikin domin xai iya xama da Mimi ko bata haihuwa ba. Ishaq na yawan kwantar masa da hankali cewa, babu ruwan ciki lalura ce kawai Allah ya saukar mata, amma cikinta lfy qalau yake. Abun dai gwanin tausayi dan sun daina ta cikin balle a aunashi ko bashi kulawa, kawai ta lfyar Mimi suke.




Xuwa yanxu yan aikin gidan sun gama fuskantar matsalar madam din tasu, suna xuwa dubata kuma kowa yana mata adduar data dace da addininsa. Baqo ya sami Bature da xancen ciwon Mimi bana asibiti bane yana ganin aljanu ke shafarta. Bature ya balbale Baqo da fada kamar ya dakeshi yana cewa "karya qara kirawa matarsa aljanu, shi matarsa bata da aljanu laulayin ciki take in kuma ya kuma cewa tana da iska to a bakin aikinsa." ya sunkuyar da kai yana bashi haquri, a xuciyarsa kuma yayi masa uxuri domin shi kansa Baturen ya xama kamar wani zararre.



Baba me gadinsu yaxo har daki duba Mimi wani yamma daya jiwo ihunta akan ciwon qafar, ya dunga kallonta cikin tausayawa. Ya kwantar da halshe da hikima irinta manya yace da Bature "Alhaji inaga yarinyar nan kamar akwai sammu acikin lamarinta, dan da ace ciwon asibitine xuwa wannan lokaci da ko bata samu lfy gaba daya ba yaci ace ta samu saukin wani abun." Bature ya dubeshi yayi shiru, Baba mai gadi ya dora da cewa "duk wanda yayiwa wannan yarinyar mugun abu yacika marar imani, wannan yarinya meta sani in banda kyauta tawa wadanda suke tare? Lallai duniya taxo qarshe indai har xa a Jefe irinsu haj maryam" Bature ya tsaidashi cikin gaxa sauraran maganganunsa, darajar furfurarsa ya gyaleshi donshi ya tsani ace ciwon Mimi bana asibiti bane. Yace "Baba addua kawai xakai mata Allah ya yaye mata" Baba yace "xan temaka alh dan shine hanyar da xan nunawa madam alherin da tayi mana kenan, xan dunga bada tofi ana kawo mata Kullum tasha a shafa mata a qafar" Bature yace "to angode Baba" ya fita daga falon, shi kuma ya sauke ajiyar xuciya dan dama ya matsu yabar gurin dan ya shafawa Mimi maganinta na ciwon qafar. Ya matsa kusa da Wll chair din ya taba kafadarta, ta dago idonta da suka kuma fitowa sabida ramar da tayi tana kallonsa. Yace "sannu maryam, Allah ya yaye miki ya mayar kaffara ya tashi kafadarki" tace "ya Bature na gurgunce ko?" ya sumbaci bakinta yace "maryam ko da qafa ko babu qafa ina sonki a haka, ki daina maganar gurguncewa kinji" tace "to, amma yaushe mama xataxo? Banaso in mutu ban nemi yafiyarta ba" yace "maryam baxaki mutu yanxu ba in shaa Allah, sai kin haife wannan cikin na jikinki kin shayarmun da Dana nononki yayi koyi da kyawawan halayenki" tai shiru tana kallonsa kawai, yaci gaba da yimata hira me dadi tana murmushi.





Haka rayuwa tacigaba, Mimi ciwo shi kuma damuwa, sau tari a office sai yayi aiki ya tura gaba sai a dawo masa dashi ace da gyara duk kuwa da kwarewa irin tasa. Sai ya xauna ya gyara ko mr Alex yasa a gyara, sarai yasan abunda ke damun sulaiman matsalar ciwon matarsa ne, yana tausayinsa kuma yana yawan kwantar masa da hankali cewa xata warke da xarar ta haihu. Kuma yaje har gida duba Mimi shi da family dinsa. Anata bangaren Hanifa tasan matsalar sulaiman sarai don sunsan Mimi babu lfy ta hanyar wacce suke bawa kudi take musu bincike akan Mimi din. Ta damu kwarai da damuwar da sulaiman ke ciki don duk ya bushe ya xama wani soko danma dan gayu ne me tsafta. Tana labewa tai kukanta ta share hawaye don tasan ciwon Mimi ne silar wannan hali da yake ciki kuma ita tana kukane don sulaiman amma badan halin da suka jefa Mimi ciki ba. Yanxu ta tabbatar sulaiman ba qaramin so yakewa Mimi ba tunda har ya shiga wannan yanayin a dalilin cutarta kawai ina ga tashiga duniya da sunan hauka? Anya shima baxai haukace ba kuwa? Bataso ciwon Mimi ya tsaya anan ba don tasan uwargida cewa tai musu hauka xatai kamar yadda magennan tayi amma kash ya akai abun ya tsaya iya ciwon qafa kawai? Lallai Mimi nada qarfin jini, amma baxatai gajen haquri ba Kullum tana kasa kunne taji yar rahotanta taxo mata da labarin haukacewar Mimi tasan a lokacin dole inyayi haukansa na wucin gadi ya haqura sannan hankalinsa ya dawo kanta, a lokacin xasu faracin duniyarsu da tsinke.

wannan shine tunanin Hanifa a Kullum.



Ya Taheer ya samu Bature da xancen kodai xa a fadawa iyayensu halin da Mimi ke ciki. Sulaiman ya futttuke ya dunga fada shifa a kyale masa matarsa ciwonta ba wani seroius bane just laulayin ciki ne, kuma suna addua suna xuwa asibiti kuma ya saka ana mata sauka Kullum a masallaci. Ya Taheer ya dunga kallon yadda sulaiman ke masa masifa kamar ada can ba girmamawa ce tsakaninsu ba, lallai ciwon maryam dab yake da saka SULAIMAN hauka. Ala dole ya haqura domin bayan ya gama fadan sai kuma ya dawo lallashi da roqon Taheer din karya bari mutan kano suji, a cewarsa in sukaji xasu karbe maryam shikuma bazai iya rabuwa da itaba a halin yanxu don in yarabu da ita yaci amanar soyayyar da sukewa juna, bayan haka kuma besan son Mimi ya masa mummunan kamu ba sai yanxu da take cikin lalura. Ya Taheer ya haqura, haqiqa suna cikin jarraba yana mugun tausayawa yan qannan nasa sulaiman da maryam.



Mai gadi ya fara kawo ruwan tofi kamar yadda yayi alqawari, amma Aisha yake bawa domin ya lura ogan nasu bayason irin wadannan abubuwan. Inya bata ita kuma takan saka pure xuma ta bawa Mimi tasha kuma ta shafe mata qafar dashi. Abun yaxo mata da sauqi don Mimi duk abunda akace tayi yi take babu musu domin brain dinta kamar ta yara ta koma, yaro dan shekara 3 na iya juyata.




Ayoyin qur anine na karya sihiri da ayyatushshifa yake mata safe da yamma, kuma Aisha kansata agaba taita karanta mata qur ani da ayoyin korar aljanu. Yarinyar nason Mimi sosai, ita ke kula da ita da duk wani shaaninta, da ita din barauniyace da tayi arxiqi a wannan tsakanin don itake gyara kayan Mimi haka xataita cin karo da kudi tana bawa Bature. Amma abunda Mimi tai mata na alkhairi baxai barta ta saka mata da sharri ba. Domin Mimi ce ta biyawa mahaifiyarta kudin aikin ido wanda ta shekara 8 tana fama dashi sabida rashin gata, sannan ta biyawa Dan uwanta kudin makaranta wanda shima rashin gata yasa ya dena duk kuwa da brain din karatun da Allah ya bashi. Kana ta kwato mata takardar saki gurin mijinta daya saketa shekaru uku amma yaqi bada takadda sai ta tashi aure yace bai saketa ba, in ta kafe ya saketa yace ina sheda?. Abun ya dade yana damunta, amma daga haduwarsu da Mimi ta fada mata duk wannan matsalar daya bayan daya ta dunga yi mata maganinsu. A qarshe ta kai mijin kotu aka rubuta sammaci aka kai masa, dake Dan iskan qaryane yana ganin sammaci ya bada takaddar dan aiken kotu ya dawo da ita. Abu na qarshe wanda Mimi tai mata kwanaki kadan kafin ta fara ciwo shine : kwato mata yaranta guda 2 mata daga hannun ubansu ta danqawa uwar aishan kana ta bata 50k tace tai jari ta kula da kanta da jikokinta.





Wannan abu yayi mutuqar farantawa Aisha rai, kunsan uwa da Da sai Allah kuma dama yayan a wuyanta suke, sannan duk wannan alheri da Mimi tayi batajin ko sulaiman mijinta ya sani ita da aishan kawai suke sirrinsu. Ita kuwa ya xataiwa wannan baiwar Allah wacce tai matá wannan dinbin alheri butulci? Wlh tasan inbata sakawa Mimi ba sai Allah ya tambayeta. Gatan kowa Allah amma Aisha tana kallon Mimi a matsayin itace gatanta kuma babban jigo a rayuwarta, tanawa Mimi duk hidima a matsayin tanawa yayarta uwa daya uba daya.



Farida da su safna, anty Rabi kusan Kullum nan suke wuni kuma suna yabawa da kulawar Aisha ga Mimi.




Dake Qur'ani warakane sai gashi a hankali Mimi ta fara samun sauqi, ta dena digar da jini ta kunne kuma qafar kumburin ya Sabe sosai kadan ya rage sai dai bata takawa. Rashin maganar nan dai shine matsalar da kuma shirmen cewar mama na kiranta.




Bature yafi kowa murnar samun wannan sauki, ya kuma dagewa da kaita asibitin a zatonsa maganin asibitine yasa hakan. Kudi kuwa baisan abunda ya kashe ba Kullum cikin sadaka yake da sakawa ayi sauka Allah ya kawo sauqi. Kuma a hankali sauqin yana samuwa shima kuma ya fara maida hankali kan aikinsa.




Ya Taheer Kullum da safe saiya shigo duba Mimi kafin ya fita aiki, kuma ya yaba da saukin da ake cewa ta samu har yaga gaskiyar Bature daya hanasu fadar bata da lfy wa yan kano, ashe da sun fada da sunyi gaggawa tunda gashi sauqi Kullum samuwa yake.




Su Farida da safna sun dan rage shigowa kowacce ta samu xama a gidan mijinta a dalilin ganin sauqi ya samu. Farida sai a lokacin ta fara awon ciki don da bata faraba tunda babu nutsuwa.




Yammacin asabar liqis tana falo tana kallo da Aisha shi kuma yana cikin dakin batasan me yake ciki ba amma dai ya dade. Ta miqe tsaye tace da Aisha bara in gwada inga xan iya tafiya?



Aisha tace "a a madam bari inxo in riqeki karki fadi" tayi dan murmushi tace 'barni dai in gwada Aisha komai saida gwaji" ta fara takawa a hankali Aisha na binta a baya karta fadi, har qofar shiga bedroom din kana Aisha ta dawo tunda tasan yana ciki.




Ta shiga ciki a hankali take takawa tana dingishi, yana cikin bathroom yaji shigowar mutum yace "waye?" tunda yasan bamai shigowa ciki sai Aisha, a iya saninsa kuma Mimi bata tafiya sai an turata a kujera. Yacigaba da kiran waye? Amma shiru.



Kamar a mafarki yaga Mimi a bakin bathroom din yana cewa "maryam kece ko mafarki nake?" ya tsame hannunsa daga cikin kumfar da yake mata wankin undis dinta (pants da bra) ya dauraye ya matso jikinta yace "maryam ke kadai kika shigo? Lallai sauqi ya samu godia ta tabbata ga Allah." ya kamota ta xauna kan kujerar daya ajiye mata suna dan hira yana wankinsa.





Ta kalleshi xuciyarta cike da tausayinsa da sonsa tace "ya Bature kai kakemun wankin undis?" ta fada tana kwallah. Yace "common meye aciki Mimi luv dan nayi miki? Ada aike kikemun ko? Yanxu Allah ya kawomu lokaci nima ina miki aiba wani abu bane" ta share hawayenta, yana aikin suna jifan juna da murmushin luv har yagama sukai alwalar magrib suka fito.




Sosai sauki ya samu, kowa ya saki jiki don abunda ya rage kawai dawowar walwalarta.



Ranar monday da wuri ya fita aiki sabida suna da meeting, kuma Mimi tayo masa rakiya har bakin mota da dingishinta sai dayaga ta koma sannan ya shiga suka tafi.




Batare data xaunaba ta shiga bedroom ta koma bacci, Aisha tanata aikinta hadi da leqawa taga

Please Login or Register in order to submit comment