Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace wlh babu chajine. Sannan suka kebe daga can qarshen tabarmar dake gurin. Yan gurin sunata zolayarsa da ango meya fito da kai yanxu, ba mun baka hutu ba.


Mekudi abokin Badaru ne, duk da cewa halinsu ba daya ba, domin mekudi irin mazannan mayun mata bashi da aikinyi sai yawan yaudarar yayan mutane duk da cewa yana da mata har yaya biyu, gashi Dan duniya na qarshe.


Bayan Badaru ya gama fada masa abunda ke faruwa na kasa kauda budurcin Mimi (kuji rashin sanin ciwon kai πŸ˜’). Mekudi yace " to kodai tayi cushe cushe nan nasu na mata a wajen? Kasan hakan nasa irin hakan"


Badaru yace "banajin hakan, domin yarinyar bata da rawar kai irinta yan matan yanxu, bayan haka kuma bata sona banaji zatai wannan abun da nufin burgeni, nafi dauka dai halittartace hakan. Yarinya fa yar baiwa ce ya fada yana dariya, sannan ya dora da cewa ta hadu dan kawai banasonta ne"


Yace to shikenan yanxu inada wani ragowar magani yana Mota ka hadiya tunda naga amatse kake, kafin in samo maka wani. Yawwa mutumina cewar Badaru wlh na matsu inji ya lamarin yake πŸ™ˆ.



Suna tsaye kofar gidan su Nafee, hira suke, awanni 3 kenan da shan maganin da Mekudi ya bashi, amma ga dukkan alamu maganin ya fara aiki a jikinsa, dan ji yake kamar cafko Nafee.


Yace mata "ni bara in tafi Nafee" ta marairaice tace kace baka santa amma tunda ka aureta inkazo Allah Allah kake ka koma gunta, me hakan ke nufi?


Yace "yi haquri yau kam banajin dadi ne, amma gobe innazo xan dade kinji" yana kaiwa nan ya fice ko takanta be kuma bi ba.

Yana xuwa ya ganta a duhu ga zafi saboda qanqantar gidan, wayarta babu chaji dan haka take zaune a duhu.


Yaje ya tada inji, kunna fankar parlon . Ta saki ajiyar xuciya dan zafi ya dameta kuma zafi kan iya tayar da ciwonta. Yaje yayi wanka ya xuba abinci yaci.


"Zo" yace da ita yana kashingide a jikin kujera, yanajin wani irin feelings.

Ta marairaice cikin zubar da kwallah tace "Badaru kayi haquri wlh kaina ciwo yake tun renda aka kawoni gidannan"

Yayi dariyar mugunta yace to aini ba kanki xan taba jikinki kawai nakeso, saboda haka kixo kafin na tashi nayi miki abunda xakiyi nadama.

Tai saurin qarasawa inda yake da rarrafe Jin abunda yace, "cire rigarki" ta zaro ido 😳. Haka dai saida yasata tai tik ta hanyar tsoratar da ita.


Sannan ya buqaci ta tashi tayi tafiya a gabansa a hakan, lamarin da ita kuma taqi yarda duk kuwa da yadda yakai da naci dole ya haqura, ganin tana bata masa lokaci kuma ga magani na aiki a jikinsa yasa ya huqara ya haye kanta anan kan centre carpet din parlon da kuma fitila akunne (Dan tsabar rashin sanin ciwon kai da rashin kunya).


Ashe kuwa gaskiyar Badaru da yake cewa ta tanadi ambulance, domin kuwa bata tabajin labarin daren farko me wahala irin nata ba.


Tun tana yunqurin kwatar kanta harta gaza ta xuba ikon Allah ido, ta gurxu iya gurxuwa cikin mugunta da wutar ciki ya kauda budurcinta.


Ya dunga kuka wiwi yana sambatun kiran sunanta ( dan rainin wayo ashe kasan sunantaπŸ€”) tare da alqawarin riqeta iya rayuwarsa.


Wannan dare ma bata runtsaba saboda ji take kamar an tsagata da reza an mata tsarki da attaruhu. Yayin da Badaru yake bacci harda munshari alamar cikar buri, kuma munsharinsa ya temaka kwarai wajen hanata bacci.


Sai gab da asuba ta samu baccin shedan ya kwasheta (na shedan mana tunda zai hanaka sallar akan lokaci).


Sanyin ruwan daya shafa matane yasa ta farka, "sannu maryam, kin hadu ni nasan bada banxa na gigice akanki ba, gaskiya xan huta, fatana ki koyi dauriya dan naga kedin raguwa ce" kalaman Badaru kenan. Kuma yana gama fadar hakan yasa kai ya fice, ba tare da la akarin yayi mata tagargazar da xata buqaci temako ba.


Yauma kamar ranar itace ta gyara kanta tayi sallah, ta nade xanin gadon da ya baci da wani abu chakal .kamar jirwaye da kuma ruwan ciwo. Amma babu jini sam. Ta shinfida wani.


Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣1⃣

Dedicated to
Maryam Baita


A hankali rayuwa taci gaba da tafiya, lokuta na gudu tunda gashi Mimi ta samu kimanin wata daya da rabi a gidan miji.

Ixuwa yanxu yan gidansu kaf babu wacce bataxo mata ba inka dauke Faty, domin ta kasa xuwa gidan Mimi, ko meye dalili oho.

Kuma duk wanda yaxo tanajin dadi sosai, kusan ma ince duk takun saqar da suke da wasu daga cikin yan gidansu xuwansu gidanta ya goge mata komai aranta, duk da cewa in anxo sai anyi habaici da kushe gidanta da kuma jajanta mata irin mijin data samu.

Fauxa kam xuwanta daya gidan duk kuwa da nacin da Mimi ke damunta dashi a waya na rashin xuwanta. Takance "Mimi ni bamai aure ba aga ina yawan xuwa gidanki sai ace naqi zaman aure inaso inkashe miki naki "

Dake ita din ba gwanar qawaye bace, sannan kuma mafi yawan qawayen basusan tayi aure ba, sai ya xamana babu wata qawa inka dauke fauxa da taxo gidanta. Lamarin da yayiwa Badaru dadi, domin shi a tunaninsa qawaye na iyasa Mimi tayi masa bore kan axabar da yake mata.


A fannin kwanciyar aure dai Mimi ta kasa sabawa da salon Badaru, domin ita dai ixuwa wannan lokaci Kullum abun sabo yake gareta. Mekudi ya riga ya bata Badaru da shan maganin qarfin maza, kawai dan aganawa yar mutane azaba.


Saboda da haka Kullum Badaru cikin buqata yake, baya duba cewa ita din abun Sam be qarbeta ba duba da yanda take jigata aduk sanda ya kusanceta, wataran ma har rasa numfashi take na wucin gadi (ciwonta).


Yau laraba, kuma tun 7:30 Badaru ya fita a cewarsa akwai wadanda zasuzo siyan kaya shagonsa a kasuwa zaije ya sallamesu.


Bai dawo gidan ba sai yanxu, 11:45 am, ya datta Mimi duke a qofar kitchen tana shirya kayan wanke2 da tayi. Tana cemasa sannu da xuwa bebi takanta ba, kawai hannunta ya kama kiiiii yayi daki da ita.


Yana xuwa ya axata kan gado ya cire wandonsa, yana me cewa "kinga abunda ya dawo dani, wata nagani yanxu a kasuwa shedan ya qawatamun ita shine na dawo insamu nutsuwa"


Yana fadar haka ya farmata ya fara yunqurin shigarta, babu batun romance a salon kwanciyar Badaru sam, yanayin kwanciyarsa dai tafi kama da kwanciyar da manxon Allah (s w a) ya siffata masu yinta da dabbobi, wadan da suke farwa mace batare da tayar mata da tata sha'awar ba.


Sai da ya biyawa kansa buqata, sannan ya lura da pink din janbakin data fente bakinta dashi, ya bashi sha'awa kwarai, dan haka ya nufi bakinta da nufin kissing dinta, tai saurin kauda kanta.


Ya tsaya, yana qare mata kallo da Jin haushin ta hanashi tsotsarta yace " wai ke kina nufin bazan sha bakinki ba? Inafa lura dake duk sanda nazo shan bakinki sai ki kauda kanki, sai kiyi tayi kinwa kanki, tunda nasamu abunda yafi baki ajikinki kuma ina yanda naso dashi ai shikenan"


Bayan yayi shirin fita ya sameta akan gadon har yanxu bata gama wartsakewa ba da dirxar da yayi mata, yace " ni xan fita inason inbiya gidane in duba Abba yau be fita kasuwa ba wai kansa ke ciwo" tace to Allah ya sawaqe, kai mai sannu.


Sannan tace " Dan Allah ka siyo wake so nake inyi wake da shinkafa" sai da yakai qofar fita sannan ya cillo mata 30 naira yace gashinan ki sayi waken, yasa kai ya fice.


Tai tsam tana tunani, naira talatin ai ko wake gwangwani daya baxata sai mata ba duba da yacce rayuwa tai tsada yanxu.

Tunda aka kawota gidan Badaru bai taba daukan ko naira biyar ya bata ba, da sunan kudin cefane ko kudin wani abun daban. Duk da cewa baya kawo kayan miya ko nama, tunda ya aciye abinci da maggi me star sai jarkar mai kings sai gishiri be kuma kawo komai ba.


Tunda miyar da momy ta kawo mata ta qare, bata qara sa kayan miya a idonta ba, sai da ta gaji dan kanta da cin abinci da mai da yaji (duk da cewa ada tana marmarin mai da yaji, lokacin tana cikin gata) taga cewa kanta take cuta tundashi bai cika cin abincin rana a gidan ba, na dare ma inyaga bai masa ba sai ya fita wajen mai shayi a hada masa da kwai, ko ya siyo tsire iya cikinsa yaci a gabanta babu tayi, duk da ko yayi mata tayinma baci take ba.


Da yake gidan amarya baya rabo da yara a hankali yaran unguwar suka fara shiga gidan, ita kuma tasa hannu bibbiyu ta karbesu bata nuna musu kyama ba, dan sune yan uwanta yanxu, cikin shirinta na karbar rayuwa aduk inda tazo mata.

Wadannan yara su take aika su siyo mata duk abunda take buqata acikin yan kudinta da mama ta bata, wanda little ta kawo mata. Wanda kuma tun daga su maman bata kuma aiko mata da kudiba saboda rashin dan aike.

Amma ta da wata yaxo qarshe akai salary ta saka mata kudi a acctn dinta, kamar yadda suka saba ita da yaya Faty duk wata in sukayi albashi sukan tura mata kudi ta acct dinta, hakan yasa da wuya ta rasa kudi. Amma yanxu abu 2 yayi mata togaciya daga daukan kudin da suke tura mata.

Na farko, ATM dinta da yayi expire wanda dole sai taje ta gyara kafin ta samu hurumin fidda kudi. Na biyu kuma shine takunkumin da Badaru ya qaqaba mata, domin tun sati 2 da xuwanta gidansa ta tambayi xuwa kitso yace mata baya cikin tsarinsa fitar matarsa daga gidan aure inbada lalura ba, kuma koda xata fita ma yanaga sai ta shekara a gidansa. Wannan shine dalilin da yasa ko daxu da yace zashi gida duba Abbansa batace xata bishi ba, saboda yace wannan shine tsarinsa.


Da yake ance me dΓ‘ wawa, saboda jan yayansu da take ajiki yasa be kitson take xuwa har gida tai mata kitson da baya wuce kwana 5 ya tuje saboda Kullum cikin xubawa kai ruwa take da kuma yanayin halittar gashinta, domin kanta shampoo din da tayi da biki ya dade da fita, kuma bata da wani man shammpoo din da take amfani dashi (mega growth) domin kaf cosmetics din lefenta ba irin wanda take amfani dasu bane, kuma yawanci anrabar dasu ga dangi (kamar yadda akeyi a al adance).


Kudin hannunta sune kayan miya, siyan salak in buqatar cin salak din ta taso, sune biyan kudin kitso da kuma siyan sabulun wanki. Domin akan idonta Badaru kan hada wankinsa ya bayar a wanko a gogo masa, amma bai taba hadawa da nata ba. Gashi ita kuma bata iya wanki ba zata iya cewa tunda take bata taba wanke kayanta na sawa ba, iyakacin wankinta undis suma a washing machine take watsasu ta wanke.


Duk da cewa Badaru yasan bai taba kawo kayan miya gidansa ba, hakan baya hana in yaga anyi abinci da miya koma har da nama ya zauna ya take tumbinsa, kusan ma bayacin abincin gidan sai yaga Cima da canja maana anyi me dadi, Ko kunya bayaji ko kuma ya tambayi ina akasamu kayan girkin saboda tsabar San banxa (san banxa mesa gidan yari cika πŸ™„πŸ˜„).


Yau da gobe tafi qarfin wasa kuma xara bata barin dami dan haka kudin hannunta bai gaxa 800 ba, dan haka ta tambayeshi ya bada kudin wake (abunda bata taba yiba, wato tambayar Badaru abu koda kuwa haqqinsa ne yayi). Acikin wannan 800 din data rage mata tanason siyan pad dan lokacinta ya kusa, ga siyan sabulun wanki ga, ga kudin wankin, sannan ga kanta ya dameta ya cika ya sarsarqe alamun yana buqatar shampoo, amma da yake hakan bata samuwa dole ta biya kudi a kitse matashi. Gashi tanason siyan wake ta hada a dahuwar shinkafa dan tagaji dacin fara da mai.


Atake a gurin ta samowa kanta solution, domin kudin bazasu isheta ba, saboda haka ta yanke shawarar siyan always (pad) tunda ita dole ce, kasancewarta mace me xubar da jini a lokacin al ada yasa sinqi daya bata isarta sai daya da rabi ko biyu. Yanxu da rayuwa taxo mata a haka ta yanke shawarar hadawa da tsumma, ragowar kudin xata sai sabulun wanki tai wankin da kanta tunda ba kudin kai wankau, sannnan ta bada kudin kitso ai mata kitso ragowar kudin ta sai wake ta dafa a shinkafa.


Rayuwa kenan abar tsoro wai yau maryam ce da wanki. Ahankali ta furta "rayuwa ce wataran sai lbr, dama aure a 2 ne ko kaci gaba ko kaci baya."

Tana kaiwa nan a tunaninta ta miqe ta fara aiwatar da abunda ta shirya.


Badaru bayan ya isa gidansu ya duba jikin Abbansa, yana zaune suna dan taba hira da Abban ummansu take gefe sai kallonsa take asace, saboda kunya irin ta dan fari.

Can dai ta kalleshi tace ina wajen su maryam din? Yace ko lfy, ai canake da ita xakuxo duba alh?

Yayi saurin cewa tananan qalau tace ma a gaisheshi da jiki, ni banason gantaline a tsarina banason matata ta fita.


To sannu me mata hakan yayi dai dai mara kunya inji Umma. Sannan ta dora da cewa " ai wannan yarinya Allah ya saka mata da alkhairi, ta gyaraka kayi tas kayi jajur da kai har wata teba ka ajiye. Wannan yarinya ta samu tarbiyyar Allah ya sakawa iyayenta da alkhairi" ta kalli abbansu Badarun sannan tace "wlh Alh tunda mukaje yarinyar nan take hidima damu ta kawo wannan ta kawo wancan, sannan ta samu hijabi ta saka a jikinta har muka taho bata cire ba, muna kan kujera tana qasa idanunta a qasa. Aini Alh banzaci acikin yaran yanxu masu xurfin karatun boko akwai irin maryam ba, haka in su Aisha (yayanta mata) sukaje mata take hidima dasu da yayansu inzasu taho, tabawa wannan mayafi wannan takalmi kai gashinan dai abun sai San barka"


Alh inuwa ya dubeta yayi murmushi sannan yace lallai kaltume wannan suruka taki tayi miki 😊 dan naga kullum in muka zauna sai kinyi bitar ahalayenta.

Tai saurin cafewa da cewa wlh kam tayimun, ai maryama ta haifu yarinyar yar halak ce, ni da Xaiji shawara ma ai daya haqura da Nafeesan yayi xamansa da wannan dan ni kam maryam tafi kwantamun.


Badaru yaji maganar kamar saukar aradu ya dago a razane 😳, yace Umma in haqura fa kikace? Shekara nawa Nafee na jirana? Innaqi auranta na yaudareta, Kuma bayan haka ma ina sonta baxan iya haqura da itaba.


Umman ta watsa masa harara tare da cewa "ai tare aka hallicceku shiyasa bazaka iya haquri ba"


Abba yayi saurin katsesu kafin maganar tayi nisa yace "ya isa kaltume, ki gyaleshi tunda yana sonta. Maryam din ma da za a aurota ai saida kika nuna turjiya, amma yanxu kinfi kowa yaban halinta. Itama wannan kikasan nata kyawun halin?"

Umma dai ta tabe baki tare da cewa Allah ya bada sa a 😏



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣2⃣

Dedicated to
Maryam Baita


Watanta biyu dai-dai a gidan, xuwa wannan lokaci ta saba da wahala, duk cewa ance ba'a sabo da wuya.


A bangare guda kuma tana cikin matsananciyar wahalar auratayya da Badaru. Irin yanda duk wata amarya da takai budurcinta gidan miji ke fuskanta a farkon aure. Ta wahala iya wahala saboda kwanciyar aure da Badaru tafi komai jigatar da Mimi.


Ga wani irin ciwon qirji da yake yawan fyadeta, saboda bacin rai da rashin cima mai dadi (mai da yaji). Tuni maganinta na numfashi ya qare, kuma tun kafin maganin ya qare intasha baya yimata aiki. Ga uwa uba zafi dakesa koda yaushe cikin daukewar numfashi take, saboda Sam yanayin ciwonta bayason zafi. Badaru kuma baya tada inji saiya dawo kuma duk inda 11 tai zai kashe yayi baccinsa inda ita kuma xata kwana fiffita da hand fan dan kiyaye lfy ta.


Babban abunda yafi damunta kuma shine; duk wannan hali da take ciki baisa Badaru ya tausaya mata yace taje asibiti ba, ko ya kaita. Hasali ma haka yake shafe tsawon lokaci yana auratayya da ita cikin shauqi da sambatu. Baya gajiya da abu daya wani lokacin sai yaga bata numfashi sannan yake saurara mata.


Bacin rai, yunwa, zafi da rashin kwanciyar hankali ya hadu ya saukar mata da wani irin matsanancin ciwon qirji. Wanda ya kwantar da ita wanwar ko sallah sai dai tayi zaune, aikin gida kuma in su abuwa (yaran maqota dake shigo mata) sunxo suke yimata, babban abin takaicin shine bata da ko naira 5 din siyan ruwan pure water. Wayarta ma kona plashing babu.


Yau monday, wanda ta kama kwananta 3 da kwanciya wanwar saboda nauyin qirji da daukewar numfashi. Ya xamana ko kwanciyar ta gagara sai dai tai ruf da ciki ta danne qirjinta saboda ji take kamar inbata danne dinba zai tarwatse. Daga waje kuwa kana iya jiyo hakin da take.


A haka Badaru yazo cikin shirin fita, yana balle botiran rigarsa, ya kalleta a wulaqance tana kwance ruf da ciki a kan centre carpet din parlon yace 'bakisan wannan kwanciyar babu kyau ba a musulunce?' sannan ya dora "nifa banason langwai kin cika gida da gurnani sai kace tsohuwar kafura wai ke ciwo ko? To wlh wannan ciwon da kike rashin dogaro da Allah ya kawo miki shi" (kunji jahili πŸ˜’). Yana ida fadar haka ya sa kai ya fice dan tsabar rashin tausayi da tsaurin xuciya.


Ta share hawayenta, aranta tana ayyana ko maqiyinta bazata so Allah ya jarrabeshi da qaddarar abokin zama me taurin zuciya irin Badaru ba. Kansa kawai ya sani gashi da manmaqo da masifar rowa.


Tananan kwance har yamma, xuwa lokacin ta ida jigata. Sai dai in lokacin sallah yayi takan samu sauqi a dabi ance, saboda tasa sallar aranta.


Bayan idar da sallah ta jawo wayarta cikin qarfin hali da jan numfashi dakyar. Tana tunanin wanda xata kira, shin mama xata kira ta fada bata da lfy, ta daga mata hankali? Ko yaya Faty data watsar da ita ta nuna batayinta xata kira? (duk kuwa da cewa Faty na kiranta a waya itace bata dauka saboda ta gaji da jin uxurin Faty akan rashin xuwanta gidanta, kawai ta dauki Faty a matsayin wacce bata santa a yanxu) dole dai mama da Faty sune dolenta (ranar naka sai naka)


Yaya Ahmad mijin Faty yayi saurin fado mata ta jawo wayarta tai masa pls call me, kafin ta aje wayar ya kirata.


Ta dauka "assalamu alaikum ya Ahmad " ya amsa sallamar "mimina kina lfy? Ya naji muryarki haka? " ya fada agigice. "bani da lfy ne shine nace dan Allah ko zaka taimakamun kaiwa Badaru magana ya kaini asibiti" ta fada a wahale. "subhanallah sannu Mimi bari muga ya za ai? Sannu autarmu" da haka ya kashe wayar.


Ya tashi ya shiga bedroom gurin Faty dake zaune (yau aikin safe tayi shiyasa take gida a wannan lokacin) ya kalleta tare da cewa "fadima meyasa bakyajin maganata ne? Inashan fada miki kece babba karkiyi abunda zai bata xumuncinku da Mimi, na fada miki mama har fushi tayi dake akan rashin zuwa kiga halin da Mimi ke ciki, amma duk kinqi ji ko? To yanxu Mimi ta kirani bata da lfy kuma ga dukkan alamu tanajin jiki, babban abun takaicin shine: mijinta yaqi kaita asibiti, daya takaicin shine; ko zancenki batai ba a wayar, wanda hakan ke nuna cewa ta watsar dake kamar yadda kikai mata" yana kaiwa nan a maganarsa yasa kai ya fita.



Tunda ya furta Mimi babu lfy kuma ta kirashi a waya, Faty take a fingice. Ta tashi tabi bayan Ahmad da gudu ta fada jikinsa ta baya ta rumgumeshi tare da sakin kuka "yaya kace Mimi bata tambayeni ba? Kace Mimi bata da lfy? Yaya wlh tausayin Mimi da halin da xan ganta ciki ya hanani xuwa gurinta, bawai bijerewa umarninka dana mama ba. Yaya banason mijin Mimi tunda Mimi bata sonsa" ya dagota ya juyo da ita yana share mata hawaye, yace "my luv, bata wannan hanyar xaki nuna tausayin Mimi ba, neman kusanci da ita da maganta mata matsalarta da kwantar mata da hankali shine hanyar tausayinki da soyayyarki gareta" tace naji kuma xanyi yadda kace " duk a rude take wannan magana.


Ta shiga daki ta dakko mayafinta da key din mota ta fito, ya kalleta ina zaki? "Gidan Mimi " ta bashi amsa direct. Yace a a bari insa ta turo no mijin nata infara yi masa magana tukun. Tai rau -rau tace 'yaya Mimi babu lfy kace in tsaya injira ayiwa wannan wawan waya? Mimita cefa ba lfy? Ka bari inje xanyi duk abunda ya dace" yace "to my luv sai kin dawo kibi komai a hankali karki abunda xaki xubar da mutuncinki a gurinsa, kuma matarsa ce ya fimu iko akanta" ta gyada kai tare da ficewa.



Lokacin da ta isa gidan Mimi yamma tayi sosai, domin har Badaru ya dawo. Ta dunga kwada sallama Mimi na parlo a kwance tana jinta tai mata shiru, yayin da Badaru dake cikin bedroom yaji sallmar kuma yaji Mimi bata amsa ba ya fito. Lokacin Faty ta gaji da jiran a amsa mata sallama har ta shigo parlon, Mimi kuwa tanajin ta shigo ta juya baya tabar kallon qofa, ta fuskanci kujerar parlon. Badaru yana tsaye yana ganin ikon Allah, shidai yasan Faty yar uwar Mimi ce, kuma a dan iya xamansu da Mimi bai taba ganin tayiwa wani haka ba koda kuwa batasanshi ba, balle Faty yar uwarta.


Faty bata kula da wanxuwar Badaru ba dake kofar bedroom riqe da cotton (labule) ba, saboda gigitar halin ko in kula da Faty tai akanta.


Jikinta a sanyaye tasa gwiwarta kan centre carpet din dake parlon ta marairaice tace "Mimi na tuba, karkiyimun hukunci irin wannan, bazan iya jure rashinki gareni ba.



Mimi ba tare da ta juyo ba, tace "ai tunda kika iya jure 2 month baki ganni ba kuma baki damuba hakan na nuna kin yanke alaqa tsakaninmu, shiyasa nima na cireki a raina kuma ban nemi taimakonki ba. Duk mutumin daka rayu tsahon wata biyu babushi wannan sheda ce dake nuna cewa ko babushi xaka iya rayuwa"


Faty ta fashe da kuka "MARYAM karki bari shedan yayi tasiri a xuciyarki, kinfi kowa sanin cewa duk halin da kike bazan gujeki ba. Kuma duk tsahon lokacinnan wlh dake nake kwana nake tsahi, Mimi kinsan dalilin da yasa banxo gurinki ba, sai dai kiqi gasgata dalilin nawa. Mimi wallahil azim ko yayan dana haifa banai musu soyayyar da nake miki, saboda duk duniya bani da yar uwa uwa daya uba daya saike"


Mimi taji wani irin mugun tausayin Faty ya kamata amma ta danne saboda tanason hora Faty

Please Login or Register in order to submit comment