Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take da Baffa bata taba gani ya dora hannunsa akan wani da a gidan ba sai ita. Koda yake itakam a gidan tana da banbanci da kowa, domin Baffa ya mata abubuwa da yawa da bata taba gani yayiwa wani ba.


Da farko bayan qin biya mata ko sisi a cikin hidimar karatunta, yazo ya takura mata da sunan taqi aure, yayi mata auren dole sannan auren babu dadi bai taba taka gidanta da sunan yaje ganinta ba, duk kuwa da cewa dabiar sa ce xuwa gidan yayansa yaga halin da suke ciki kuma ya musu alheri. Amma ita tunda aka kaita ko waya bai taba yimata ba. Abu na qarshe shine: anyi mata sakin wulaqanci ta dawo gida ya kuma takura mata, takurar da tafi ta farko, ga kuma duka anfara jiya.



A wannan gaba taga ya dace ta karbi shawarar da xuciyarta tasha bata a kwanakin baya, dan haka ta miqe ta dauki kudi ta fita ta tsaya a soro ta aiki wani almajiri ya siyo mata abunda take buqata. Tananan tsaye yaron yaje ya kawo mata aiken, ta bar masa ragowar canjin.



Da magriba ta gama duk wani aikinta ta shige daki tunda ba azumi tayi ba, tabar mama tana shan ruwa a parlour.



Fauxa da tagaji da zaman jiran Mimi ta biyo mata zuwa sallar tarawih bata zoba ta tashi domin biyawa Mimi, dan taji har an tayar.


Ta sami mama a parlour suka gaisa Maman na shirin shiga bedroom tace "qawartaki na dakinta tun dazu kinga ma ko ruwa bata sha ba" tace to bari in dubata.



Shigar Fauxa dakin tayi dai dai da lokacin da Mimi ta daga kwalbar FIYA FIYA (abunda aka siyo mata daxu) xata kai bakinta. Fauxa ta kwala kiran "MIMI" a razane 😳 tare da doke hannun mimin. Kwallah kiran da tayi ya janyo hankalin mama daga bedroom, taiwa dakin tsinke tana tambayar lfy?. Fauxa batabi takan tambayar da mama keyi ba. Ta qarasa ta riqe kafadun Mimi tana girgixata cikin kuka tana cewa "Mimi kashe kanki xakiyi akan mutuwar aure? Shin in kashe kanki wanda ya sakeki yana da asara ne? Mesa xakiyi haka? Duk fa abunda xai faru ya riga ya faru. Ansake ki, an takura miki, anyi gulmarki, anmiki sharri. Inbaki sani ba maganganu da yawa ke yawo akan mutuwar aurenki. Akwai masu cewa cukumar mijinki kikayi kina zaginsa ya sakeki, wasu kuma suce wai sata kikai masa ya sakeki, ke harda masu cewa ya kamaki ne kina lesbian (neman mata) ya sakeki. Amma duk wandannan maganganu da nakeji bana fada miki saboda kar in daga miki hankali. Amma shine yanxu xaki kashe kanki Mimi? Why Mimi, Why. Wlh indai akan baqin cikin namiji kike haka gara ki dena, shin ni ba a sakeni ba? Ni harda Da aka sakeni mutu nayi? Ko takurar da aka yi miki ba ita akemun ba, kafin Baba ya gane gaskiya ya sakarmun mara?"



Maganganun da Fauxa keyi yabawa mama amsar tambayar da take yi, dan haka cikin kuka ta juya tabar dakin. Mimi ta gigice ganin kukan mama dan tasan ba qaramin abu kesa mama kuka ba, tai gargawar biyo bayan mama tana cewa "mama ki yafemun na tuba πŸ˜ͺ"


Fitowar mama tai dai dai da shigowar Faty parlourn, ya Ahmad na biye da ita. Dan bata gamsu da yacce tabar Mimi a jiya ba shiyasa ta kuma xuwa ta taushi Mimi. Ta iske wannan mugun lbr, fauxa ta fada mata tace "WHAT" kalmar data janyo hakalin matan gidan, nan da nan kuwa suka cika qofar dakin mama suna kallo. Ya Ahmad kuwa gurin mama yaje ya tsuguna gefenta yana nemarwa Mimi yafiyar abunda tayi.



Faty kallon Mimi take da wata irin fuska 😑 wacce babu wanda ya taba ganinta da ita. Mimi tana rabe jikin bango, cikin kuka take furta "am sry, am so sry sister" Faty batabi takan haqurin da Mimi ke bata ba, ta kifawa Mimi mari, ta kuma kifa mata wani, ta qara mata. Ataqaice dai sai da tayiwa Mimi mari guda 6 xafafa. Mimi idanunta a runtse, bata dauke kanta ba, ba kuma ta fasa furta "am sorry sister"


Wadanda ke bakin kofa suna kallo abun yayi matuqar girgizasu, domin ba qaramin abu zaisa Faty ta daki Mimi, bama su taba gani ko fada Faty taiwa Mimi ba bare duka. Dan haka kansu ya qulle suka rasa lefin da Mimi ta aikata Faty ke mata wannan hukunci. Kuma ta wani barin abun ya burgesu domin daga Anty har Umma babu wacce daya daga cikin yayanta na sama ya isa yayiwa na qasa hukunci haka, ba ai gagarumin yaqi ba. Kuma daya abun burgewar har wanda akaiwa hukuncin yana bada haquri.



Faty na gama marin Mimi itama ta fashe da kuka, ta janyo mimin ta rungumeta tsam suka xube qasa tana shafa kan Mimi tare da cewa "is Ok sister" Fauxa ma ta matso kusa tana lallashin Mimi cike da yabawa hukuncin da ya Faty tayi mata. A xuciyarta tana aiyana duk renda Allah ya bata yaya mata xatayi iya yinta ta hada kansu kamar yadda mama ta hada kan Faty da Mimi.



Yan kallo kuwa dole suka watse ganin film ya qare. Ya Ahmad ya tafi ya bar Faty ta kwana, saboda halin da mama ke ciki.



Can tsakiyar dare suna kwance kan doguwar kujera, mama dauke da Dady kan cinyarta, sai Faty dake zaune tana bacci Mimi kuma ta tada kai da tata cinyar. Tun faruwar abun Mimi ke bawa mama haquri amma mama tayi kunnan uwar shegu kamar batajin abunda Mimi ke fada, yanxu ma sai kuka take tana qara neman gafarar mama. Mama ta shafa fuskarta tace "na haqura Mimi, amma ko wane irin hali xaki shiga karki qara yunqurin halaka kanki, kinga ku kadai nake daku in kintafi kinbar yar uwarki ni da ita ya xamuyi? Bakisan rayuwarki nada matuqar mahimmacin a gurin mu ba? Danme xaki kashe kanki akan wadanda mutuwarki sukafi so akan rayuwarki? Mimi kiyimun alqawari daga yau zaki cire duk wata damuwa a ranki ki fuskanci abunda ke gabanki. Da ace mutane suna riqe abunda ya riga ya wuce wlh da baqin cikin ya kashe rabin mutanen duniya. Saboda haka past is gone forever, ki gyara present dinki, future kuma ki barwa Allah shi yasan abunda future xata xo miki dashi."



Mimi ta gyada kai cike da gamsuwa da kalaman mama, sannnan ta qudure yin aiki da abunda maman tace mata.


Ta yunqura ta miqe xataje toilet domin canja pad din jikinta da ta jiqe, mama tai saurin cewa ina xaki? Tace " xan canja pad ne" wani farin ciki ya xiyarci mama, jin Mimi taga jini wanda hakan ke nuna babu ciki kenan. Ta dunga godia ga Allah domin batason Mimi ta haihu da Badaru. Tace da mimin muje in rakaki, Mimi ta zaro ido 😳 tace "mama toilet din xaki rakani?" mama na tafiya tace "eh nasani ko ki kuma yunqurin halaka kanki" Mimi ta marairaice tace " mama zargina kike wlh bazan kuma ba na baya ma da nayi kuskure ne."



Yan kwanakin da suka biyo baya ta dan samu sauki, amma fa ba sauqin aikin gida ba saukin damuwar dake xuciyarta a bisa amfani da shawarar mama. Ta kuma yardarwa kanta xatai karbi rayuwa a duk inda taxo mata.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 3⃣1⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Ranar da Mimi tayi wankan tsarki ranar Faty tazo gidan, ta tasa Mimi a gaba harda yan kayanta set 2. Mimi tace "ya Faty Baffa inyaxo ya tadda banyi aiki ba xaimun fada." Faty ta fallara mata harara "xan dura miki xagi Mimi, ana xancen lfyarki kina xancen fadan Baffa? Ko kin manta abunda Dr yace in kinga jini insamiki wani magani?" Mimi ta marairaice tace "ya Faty ai na warke ko sati banyi ina amfani da maganin ba na daina qaiqaiyin, wlh kamar ban taba yiba." Faty ta kuma watsa mata harara tace " ke wlh sai kin bini in yaso in kin dawo Baffa ya kasheki bashi kikejin tsoro ba?" tace tuba nake sis muje 😊



Bayan sunsha ruwa sun huta, Faty ta dakko maganin tasa safar hannu tace da mimin kwanta. Mimi ta waro ido tace "ya Faty😳 yanxu wai saina bude jikina?" Faty tace "a a karki bude insa miki magani, amma ai kin budewa Badaru ko? Mimi najin haka ta kwanta ta bude jiki, Faty ta gama yi mata gwaje gwaje tasa mata magani. Tanata tsaki tare da cewa " wannan mutumin ya cuceki Mimi dole sai anmuki stitches (dinki)" Mimi ta zaro ido cikin kidima 😳😳😳 tace "ya Faty na samu qari ne? Naga masu haihuwa akewa dinki" tayi tsaki tace "ba gara wacce ta haihu dake ba, ita tasan haihuwa tayi. Kuma ba sai lallai masu haihuwa akewa dinki ba. Ba qari kika samuba amma ya miki barna a jikin ki ya nuna mugunta wajen kusantarki, gara ma da Allah yasa nagani amma wannan in kikayi aure ai sai kiji kunya, wata 5 a gidan miji amma wani mijin ya sameki sakwakwa haka ai sai yace qarya ake cutarsa akai."


Washegari kuwa tana dawowa daga aiki tace da Mimi ki shirya in ansha ruwa xamuyi aikin, na siyo kayan aikin masu kyau wanda in anyi basai an ware ba zaibi jikin ki.


Kafin asha ruwa Mimi ta tsure, mugun tsoron dinkin takeji kamar tace a fasa. Haka dai ta haqura aka fara dinkin, tunda aka fara ta runtse idonta tare da cije lebenta saboda azaba. Har akayi stitches din aka gama ko tari bataiba, Faty ta dunga yabawa dauriyar da Mimi tayi. Mimi ta kalleta tace "ya Faty xai kai kwana nawa kafin ya warke?" Faty tace "kayan aikin da nayi miki amfani dasu masu kyau ne, amma duk da haka ya danganta da irin jikin ki da kuma irin kulawar da kikayi dashi." ta bata magani ta hadiya saboda ya kashe xafin gurin, ta qara da cewa indai jikinki me kyaune gurin zai koma fresh kamar baayi dinki ba.



Kwananta biyar a gidan Faty, ta samu nutsuwa da kuma sakewa ga kulawa da shiga ruwan dumi saboda stitches din. Nan da nan kuwa ya kame kamar bame dinki ba tafiyarta ta koma normal. Kuma a ranar ne Baffa ya lura ko kuma aka kai masa gulmar Mimi bata gidan. Shima daya lura sai yaga baya ganin kai kawonta a tsakar gida, kuma tsaftar gidanma ta ragu saboda masu aikin sun karbi aikinsu, lokacin da Mimi na aiki gidan yafi tsafta.



Dan haka ya bugawa Mimi waya yace ta taho kafin ranta yayi mugun baci, a cewarsa tunda batai zaman nata gidanba bazataje ta kashewa wata nata auren ba.


Sai wajen goman dare ya Ahmad ya maidota gida. Ta dunga lallaba jikinta saboda kar stitches din ya samu matsala, duk abunda xatai tana kula sannan ko mama batasan da xancen dinkin ba.



Azumi ya tasamma qarewa anata shirin sallah, a wannan lokaci ita kanta tasan ta samu sauki. Domin tana jin jikinta a matse kamar lokacin da tana 15 years, ita kanta tasan ta samu canji a jikinta. Gashi ta dan murmure saboda kwanciyar hankali data samu.



Ranar 3 ga sallah gida ya cika kamar yadda suka saba zuwa, kowa cikin kwalliya ta burgewa da qoqarin nuna tattalin arziqin mijinsa. πŸ˜„



Mimi bata fita tsakar gidanba inda aketa photuna ake shewa, saboda tayi alqawarin dena shiga cikinsu duk rintsi. Tana zaune parlour tana karatun wani novel da aka turo a grp, Rashida da tawagarta suka shigo. Rashida tace ina mama? Xuwa nayi inyi kallo a dakinnan parlourn Umma yara sunyi yawa. Ta xauna akan kujerar kusa da Mimi, ragowar wadanda suka shigo tare ma duk suka nemi gurin xama. Ta kunna kayan kallon sannan tasa fefen CD na film din ZAURAWA na AISHA DANKANO, wanda takanas Rashida ta taho dashi daga gidanta dan kawai taci zarafin Mimi. Ana kallon film din su Rashida na hira tare da aibata zaurawa da tsine musu, wai a cewar Rashidan "duk wata bazawara karuwa ce, suna fakewa da xawarci suna neman maxa. Kuma da mijinki ya auro miki bazawara gara ya auro miki visites domin bazawara saita nuna miki tasan namiji. Ta kuma gyara xama tace, ai duk macen da ta fara mutuwar aure to wlh haka take qare rayuwarta a aure aure yo dama mutum dakyar ya shiga bare yanxu."


Mimi tayi banxa dasu tana danna waya, saboda ta kasa karatun novel din dan maganganun Rashida sun tabata. A zuciyarta kuwa cewa take "rashin fita cikin nasu ma ban tsira ba tunda har dakin uwata anbiyo ni ana zagina" tana wannan tunanin har film din yazo dai dai inda Aisha Dankano ke cewa "ZAURAWA" nan take kuwa Rashida ta saita babban yatsanta saitin Mimi πŸ‘πŸΌ tare da cewa "SUNE" ragowar suka saka dariya sukace Rashida baki da M.



Anty safiyya dake dakin Mimi a kwance duk abunda suke tana jinsu, kuma babu wanda yasan tana dakin. Ta fara tunanin dalilin da yasa yan gidannan suke haka sai kace ba yan boko ba, kawai dan aure ya mutu sai a takurawa yarinya. Itakam bataga laifin Mimi ba, yarinyar tanada haquri da shiga rai. Ta tashi ta fito ta riqe labulen dakin tace "tace meye haka nakeji Rashida? Waike wace irin yarinyace mai neman fitina? Ki biyota har dakin uwarta kina insulting dinta?" Rashida ta murguda baki cikin fitsara tace "babu ruwanki malama, muna abunmu iya yan gida kinxo kinsa baki, wannan aiba abunda ya shafeki bane" Anty safiyya ta nunota da yatsa tace "ke! Kikiyayeni, in kinsaba iskanci a kyaleki ni inkaimun Ali (mijinta) xansa ya casaki." Rashida najin haka tayi shiru dan tasan yaya Ali babu ruwansa ubanta zaici.



******** ******** *******

Kwana goma dayin sallah ta kuma tsintar kanta cikin jini, wanda ke maxaunin jini na biyu bayan sakinta. Kuma hakan ya nuna saura jini daya kenan ta tashi daga matar Badaru, tunda munsan cewa iddah jini 3 ce. Ba wata uku ba kamar yadda wasu ke fada, sabida ba kowace mace ke jini duk wata ba. Wata tanayin sati 3 wata kuma 25 dayz (kamar Mimi kenan).



Haka al amura sukaci gaba da tafiya, tasamu saukin rayuwa sosai saboda aikin da Baffa ya dora mata ya xamar mata jiki inbataiba batajin dadi. Sai dai surutun mutane akan mutuwar aurenta har yanxu abun be sauki ba, wannan kuma ta kance suyi su gama watan kwaram daya ne, na biyu sai gagara. Mutane kan bata mamaki, inbakai aure ba a dameka inkayi balain gidan auren ya hanaka xama nanma asaka agaba.


Duk magribar duniya fauxa kan shigo susha hira sai goman dare take tafiya. Wanda hakan kan yiwa Mimi dadi, kuma yakan debe mata kewa. Dan ita Baffa ya hanata fita ko kofar gida. A cewarsa kunya yakeji aganta ace yarsace kuma bazawara ce. Dan haka suka qara shaquwa sosai da fauxa. Duk wani abu da take buqata fauxa take bawa ta siyo mata.



Sati hudu dayin qaramar sallah katin bikin Badaru yazo gidansu. Kuma a lokacinne mate din Mimi suka fara registration din tafiya service domin an bude musu portal, ta dunga kuka saboda Baffa ya hanata. Sam bikin Badaru baya gabanta bata sansa balle tai kishinsa dan haka in mata 100 zai aura wlh baxata damu ba.



Ranar asabar data kasance ranar yinin bikin Badaru matan gidansu Anty da Umma suka shirya suka tafi duk kuwa da cewa ba wani xumunci ke tsakaninsu da Umman su Badaru ba, amma saboda a cuzgunawa Mimi suka tafi, mama kuwa dama ba a gayyaceta ba.



Ai kuwa suka dawo da lbrin irin gidan da Badaru ya qera domin sunje kai amarya, da kuma irin bushashar da yayi a bikin. Sukaita fadar magana wai ai yanxu yayi aurenso domin ya nunawa duniya yanason Nafee.



Ranar da aka kai masa Nafee a daren ya tumurmusheta, saboda yana yunwar abun. Amma ga mamakinsa a daren ya shigeta tsaf, sabanin Mimi da sai da yayi kwana biyu dan ma tagomashin maganin kuzari. Abun ya daure masa kai, gadai Nafee danya shataf (mai qarancin shekaru) amma Mimi ta fita qaramar halitta. Ashe abun ba shekaru bane. Amma duk da haka ya yaba mata kwarai tunda ya sameta cikakkiyar mace wacce ta kawo masa mutuncinta dan haka ta kuma samun gurbi sosai a zuciyar Badaru.


Itama ta bangarenta tasha wuya sosai, amma ta daure ne saboda soyayyar da takewa Badarun.



Ranar da Mimi taga jini na uku (ranar cikar iddarta) har sadaka tayi saboda farin cikin sun rabu da Badaru har abada (abunda take fata). Mama kamar ta xuba ruwa a qasa tasha, ta dunga sallar Nafila tana roqawa Mimi da duk wata ya mace samun miji nagari da ingantacciyar rayuwa.



Daf ake da babbar sallah. Cikin wata guda da aurensu suka fara samun sabani da Badaru a dalilin yawan buqatarsa, ita kuma tagaji da juriya. Abunda kuwa ya faru shine: dake ance me hali baya fasa halinsa Badaru yaci gaba da bankar magungunan qara kuzari, wanda ya qara yawan buqata akan tasa, ita kuma Nafee taga sam bazata jura ba. Duk kuwa da cewar Badaru baya ware mata qarfi kamar yadda yakewa Mimi. Sabanin haka ita yakan yi romancing dinta ya lallabata kafin yakai gaci. Kuma yanayin hakanne saboda soyayya da kuma duba qarancin shekarunta.


A bangare guda kuma bata samun yacce takeso ta wajen cima, sabida ta gama sawa a ranta inta auri Badaru zaman jin dadi xatai saboda yana da kudi, ga kuma gida daya qera mata. Shi kuma Badaru baisaba siyan komai a gidansa ba, amma duk da haka yasan xaman da yayi da Mimi babu macen da xata yadda da haka. Dan haka yake sassauta wasu al amuran. Yana siyan komai na cefanen gida dai dai gwargwado saboda har yanxu gushirin yana kan kaxa. Sada nama da kayan shayi da bai taba saiwa Mimi ba yakan saiwa Nafee da sun qare, sai dai kudi ne kwandala bata taba shiga tsakaninsu ba. Wanda Nafee taga bazata lamunta ba.



Abunda ya fara kawo musu sabani kuwa shine : tara qawayen da takeyi danta nuna musu itafa yanxu ta kere sa a ta auri mai kudi. Wanda shi Badaru sam baya qaunar yaga anshiga gidansa, kuma in sukaxo inyananan sai tace ya basu kudin mota inma bayanan saita ciwo bashi a maqota inya dawo ya biya. Kuma duk wani nama da ya siya a gidan in qawayenta sukaxo sai sun cinyeshi. A irin haka wata rana qawayenta sunxo dayar ta buqaci Nafee ta bata always ta canja, Nafee da son gwaninta ta dakko ledar always ultra gaba daya ta bata. Wacce dakyar Badaru ya siyo mata ita domin cewa yayi bai taba siya ba, kuma tai masa kudi da yawa harda cewa abar da za asa ayar har sai ansa 500 ansiya? A taqaice dai sai da aka kai ruwa rana kafin ya siyo gashi Nafee ta bada ita lokaci daya.



Yana dawowa kuwa ko sannu da xuwa batai masa ba ballantana ta bari yaci abinci tace "kaje ka siyomun always" ta fada cikin sigar rashin mutunci dan kar yace bazai siyo ba. Ya kalleta a kaikaice yace "amma kyabari inci abinci ko" ta qara tsuke fuska tace "ai babu abincin domin nayi baqi sun cinye kuma kafin na dora wani ka dawo" ya jinjina kai cikin qosawa da halinta domin ba wannan ne karo na farko da tayi mai haka ba yace "ba shekaran jiya na siyo miki ba? Harta qare kenan?" cike da isa tace "na bayar da ita daxu, domin da kunya axo a ganni a wannan makeken gidan inkasa bada ledar always ai wlh kamata yayi ka dunga saimun sunqi guda saboda qawaye na" yace "ok haka ya dace kiyi? Kinyi dai dai"



Ala tilas yaje ya siyo mata always din, domin da yaqi siyowa xama ta dunga yi ko ina tana batawa da jini daga qarshe ma da taga bai dauki abunda tayi da mahimmaci ba saita zauna akan cinyarsa ta batashi da Jinin (su Nafee yan iska🀣) dan haka ya yi saurin tashi yaje ya siyo tun kafin ta haram ta masa xama a gidan saboda qazantar jini, domin shi Allah ya yi masa kyankyamin jini.



Ranar alhamis suka tashi cikin tashin hankali, fada kacucur suke da Nafee yana fada tana mayar masa kamar ba sune masoyan da suka shafe shekaru suna soyayya ba. Dalilin fadan kuwa shine: Nafee tace ya siyo mata kaza domin ta dade bataciba a fadarta rabonta dacin kaza tun ta daren amarci, kuma wannan danqareren gidan kamata yayi ace Kullum da farfesun kaza ake breakfast 🀣. Shi kuma ya bata amsa da bazai siyo ba, domin a gidansu ma ai ba kazar take ciba, naman kasuwar ma da ta samu ta godewa Allah (abunki da wanda ya saba da fadar baqar magana) ai kuwa yana fadar haka Nafee ta taso masa kamar xata dakeshi tanayi masa warning din karya kuma sa gidansu acikin rashin mutuncinsa domin inya kuma xatayi babban rashin mutunci.



Da haka ya tarkata ya fita saboda karya zauna zuciya ta xugashi ayi batacciya. A kasuwa tunani ya yini yi na mamakin halin Nafee. Shidai a iya zamansu baisan haka halinta yake ba ashe lambu lambu tai masa, to kodai qawaye ke xugata? Wata xuciyar tace ba wasu qawaye halintane hakan ta boye makane sai daka aureta. Wannan shine ana zaton wuta a maqera ansameta a masaqa, yana zaton a gurin ruqaqqun yan mata masu ilimi irinsu MARYAM ake samun fitsara da rashin kunya wa miji ashe abun ba haka yake ba, sai gashi yar qaramar yarinya Nafee da ko secondry bata gama ba tanayi masa abunda bai taba tsammani ba. Ada ya dauka xai juya Nafee yacce yakeso ya koya mata irin aqidunsa sai yaga labari yasha banban domin tun kafin aje ko ina Nafee na neman fin qarfinsa.



Haka ya yini tunani a kasuwa, da dare ya dawo batai abinci ba. A cewarta wai ya bata mata rai saboda haka bazatai girki ba. Sai gurin me shayi yaje yaci indomie πŸ˜‚.


Dake tsohon jarababbene, a wajen kwanciya sai ya nemi haqqinsa. Ai kuwa tace "kai ka isama? Bakaban nama naci ba kazo ka mutstsukeni? Aikin banxa jarababbe kawai bakasan komai ba sai dare yayi ka danne mace" qiri qiri ta hanashi abunda yakeso kuma dole ya haqura.



A daren ya gama yanke shawarar abunda zaiyi, domin ya gaji da rashin kunyar Nafee da iskancinta. Kuma gashi ta fara hanashi haqqinsa shi kuma bashi da juriya a wannan fanni. Dama kuma cikin yunwar abun yake domin sam baya samun gamsuwa da Nafee yacce yake samu da maryam, ya saba da xagaye daya ya gamsu amma itakam Nafee sai yayi biyu xuwa uku yake samun biyan buqata lamarin da Nafeen taqi yarda dashi domin

Please Login or Register in order to submit comment