Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a banxa ya haukace asan Mimi.




Hanifa ke xaman jiran Bature ya furta yana sonta amma taji shiru, gwaggoriya ce tai mata famfo cewa taje tai masa tuni tunda uwargida tace da aikinsu a jikinsa. Ta yarda da wannan shawarar kawai tana jiran sulaiman din ya fita daga damuwarsane.





Ana cikin haka Anty mami taxo 9ja, wacce mutuwar uban mijinta ya kawosu ita da mijin. Acan katsina suka sauka wato family house din su mijin. Lubna ke fada mata Mimi babu lfy amma bata fada mata ainihin abunda ke faruwa ba.




A gidan mumy ta sauka data iso kano, ita da mumy sukaxo gidan mama. Anty mami tayi matuqar kaduwa da ganin Mimi da kuma jin asalin ciwo.





Hausawa sunce "ranar naka sai naka, dadin xama kuma sai bare." a takenan Anty mami ta manta duk wata qiyayyar Mimi, kuma dama can ita tanason Mimi aurenta da Bature ne bata soba. Ta dunga kallon Mimi tana kuka tace "Mimi me kikeso in sai miki? Fadamun kinji Mimi duk abunda kikeso kinga ni yar uwarkice bayan haka kuma Dan uwana kike aure." tai shiru kamar yadda ta saba tanabin Anty mami da kallo. Ta kwanto Mimi jikinta tanacewa "Mimi ko kinaso intafi dake can Canada insaki makarantar rainon ciki kiyi xamanki kedasu Raudah?" wannan karonma shiru Mimi tayi. Babu yadda Anty mami batai ba taji muryar Mimi amma abun ya gagara. Ta dunga kuka duk kuwa da taurin xuciya irintata, tayi nadamar abunda tayiwa Mimi last xuwanta kano, yanxu gashi tana nema Mimi tace wani abun amma babu baki.




Da Anty mami ta matsa sai Mimi ta fadi abunda takeso taga Mimi ta kasa magana sai tasa kuka, itama mimin tasa kuka. Ta rungume Mimi jikinta tana lallashinta. Mumy taji dadin wannan daidaito da aka samu tsakaninsu. Da xata tafi kudi ta bayar masu yawa wai a siya mata duk abunda takeso.



Daga kano Abuja ta nufa, ta furgita lokacin dataga Bature ya dawo office wajen taran dare. Ta kalleshi tasa kuka, gaba daya ya canja. Suka samu xama a daren ta dunga kwantar masa da hankali cewar maryam ta samu lfy maganace kawai batayi. Ta godewa Allah da batai sillar rabuwarsu da matarsa ba, yanxu kawai rabasu akai nadan lokaci ya xama haka inaga an rabasu gaba daya, anan ta saduda kuma tayi niyyar fita a rayuwar aurensu.




Washegari ta rakashi aski aka cire masa sumar kansa akai masa gyaran fuska, sai ramarsa ta kuma fitowa. Suka dawo gida ta yanke masa farce tasashi yayi wanka ta bashi abinci a baki. Ta gyara bedroom din da ya cika da kayan wanki.



A ranar ta tara ma'aikatan gidan, ta dunga yimusu bala'i da hausa in hausar ta kakare ta koma turanci, inta fiskanci basa gane turancin da koma hausa. Ita zarginsu take sunada hannu a abunda ya samu Mimi, a cewarta inbata hanyarsu babu yadda xa ai Mimi ta samu wannan matsala, kuma xatai bincike indai ta tabbatar da hannun wani a ciki tofa hukuncinsa life in prison. Sun tsorata da ita don ita din gwanar masifa ce. Baqo a xuciyarsa yace "wannan mata da masifa take kamar ba jinin mumy da Dady ba"




Ta dakko masu aiki aka saka matakan tsaro a gidan dake aikine na kudi, wasu shegun qofofine wanda sai sun tantance mutum kafin ya shiga ga cameras kota ita kamar xaka shiga fadar gwamnati.




Ta shiga gidan ishaq don taji yana ina Bature ya xama haka? Amma ganin da tayiwa ishaq da Farida ya hanata masifar da tayi niyya domin suma duk sun qare Farida sai uban ciki a gaba wanda yakai 7 months.



Jiki sanyaye ta xauna kan kujera tace "ishaq baku da lfy ne naga duk kunyi wani iri?" yayi qasa da murya yace "Anty mami rashin lfyar Mimi da kuma halin da sulaiman ke ciki ya maidamu haka. Mimi ta tafi da farin cikin mutane da yawa" ita da ta shigayin masifa sai ta bige da nasiha.




Kwananta uku a Abuja ta koma kano, ranar anyiwa Mimi sauka a take ta bada kudin rago tace a siyo a yanka a sadakar.



Ta samu mama da mumy a killace ta xana musu halin da sulaiman ke ciki ta roqesu da indai baso suke ai biyu babu ba tofa su bashi matarsa. Uwa da Da sai Allah, mumy jikinta yayi sanyi tana kuka tace 'Duk wanda yayiwa maryam mugun abunnan wlh baxan yafe masa ba don ya watsa mana rayuwar yaya" suna cika sati daya ta juya Canada ita da mijinta, bayan ta kuma bawa Mimi maqudan kudi, ta tafi da burin son jin muryar Mimi amma har tatafi Allah baisa Mimi tayi magana ba.




Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 6⃣2⃣



Assalamu alaikum. Masoyan Mimi ina neman afuwa, anatamun maganan cewa "Hajia ya dace ace Mimi ta huta da wahalar rayuwa haka" wasu ma har waya sukemun ana roqon Anty Rahmatullah ta saurarawa Mimi 😊. To naji kuma duk nagode soyayya ce ta kawo har akemun haka kuma nagode sosai. Amma ina qara baku haquri, abunda nakeson fans dina su sani shine; 50% na labarin AL'AMARIN MARYAM true life story ne (wato ya faru a gaske) ragowar kuma na qarane sabida nishadantarwa. Sabida haka sai anyi haquri komai ya kusa xuwa qarshe. Tanxz nd luv u all 😊❀


Hanifa ta shiga cikin office dinsa lokacin break, kamar yadda tayi tsammani aiki yake a maimakon break din. Sai data zauna ya lura da xuwanta, takai hannu ta dau frame din dake kan table din wanda ke dauke da pic din Mimi da Bature ranar daurin aurensu, sanye da fararen kaya sun qurawa juna ido. Ta ajiye frame din da cewa "Allah sarki maryam ya jikinta kuwa?"




Ta sosa masa inda ke masa qai qai yadan bata attention yace "da sauki nagode da kulawa" ta qara gyara xama cikin siyasa tace "Sir, dama inason muyi wata magana, so inata jiran inga kasamu nutsuwa daga halin da kake ciki" ya runtse idonsa yace "baki da damuwa da halin da nake ciki kiyi maganarki, i m all ears"




"Dama naga maryam babu lfy kuma ko baka fada ba kowa yasan kana neman kulawar mace a yanxu shine nace maixai hana ayi maganar auren mu yanxu? Nayi alqawarin kula maka da maryam"




Kallonta yake cikin tsabar mamaki da son xuciya irin nata, saida ta ida yace "bansan ke akuya bace sai yanxu, kin dauka kowa daqiqi ne irinki? Matar tawa babu lfy kikemun maganar in aureki? Wato ga mahaukaci irinki ko? To bari kiji ko ada bani da raayin aurenki balle yanxu, bana buqatar kulawarki akan maryam kuma ko tana da lfy ko bata da ita inason abata a haka. Na haramtawa kaina kowace mace, sulaiman mijin maryam ne ita kadai"




Ta katseshi cikin bacin rai "dakata sulaiman, so fa ba hauka bane, akan inasonka saika kirani akuya? Akan mahaukaciya kake cimun mutunci to w.... " marin dataji bisa kuncinta biyu shiya hanata ida maganarta. Ta bude ido razane tana kallonsa, ya xago ya damqo hannunta ya jata kiiiiii ya fita da ita daga office din.




Tana ihu tana turjewa tare da cewa "sulaiman ka tsaya, ina xaka kaini don Allah kayi haquri" bai kulata ba, yacigaba da janta mutane na kallonsu ana yan surutai, wasu ma binsu suke suga inda xai kaita. Kuma dama shidin tseguminsa ake da cewa duk wannan haduwar tasa matarsa mahaukaciya ce. Bai direto ko inaba sai office din mr Alex, ya wurgata ciki.



Mr Alex ya miqe tsaye yana kallonsu, sulaiman na huci. Hanifa na kuka, kafin ya tamvayi abunda akai Bature yace "karabani da wannan masifar, ka rabani da wannan anobar, nagaji da xama da ita. Hanifa tayi silar bacin ran maryam da dama kafin yau ta kirata da mahaukaciya."



Mr Alex ya jinjina lamarin, Hanifa tayi wauta yadda sulaiman ke qaunar matarsa ai kisama zai iya a kanta ba rabuwa da mutum ba. Hanifa ta rarrafa ta riqe qafarsa tace "na tuba sulaiman na janye kalamaina akan maryam, ka yafemun Allah ma muna masa laifi ya yafe bare yan Adam. Sulaiman har kauce hanya nayi sabida soyayyarka" ya cillata gefe guda, yace "ai kinsaba kauce hanya, da nabiye taki da tuni kin maidani hamshaqin maxinaci" a xaton Bature abunda take nufi kenan. Ya kalli mr Alex yace "a canjamun sect, kuma namiji nakeso ba mace ba. Wlh indai ba a janxa wannan anobarba xan aje aiki"





Dajin haka Hanifa tayi dif ta qura masa ido, lallai kwabarta tayi ruwa. Ta kuma tunkararsa yayi saurin kaucewa yace "karki tabani, ko a hanya kika nuna kin sanni saina saka an sassaba miki kammani" yakai dubansa gurin mr Alex yace "a tura wani ya kwaso mata karikicanta a office dina wlh inta kuma saka qafa ciki ni nabar aiki" ya juya ya fita.




Xuciyarta ta bushe ta kasa kukan, tabi bayansa da kallo Allah ya dora mata masifar son sulaiman akansa ta kauce hanya, yaci ace ta haqura dashi sabida wulanqancin da yayi mata tun akan auren maryam, amma xuciyarta taqi sarara mata soyayyarsa, taso ace ya biye mata sun watse wataqil inta maida kwadayinta a kansa ta samu sauqin soyayyarsa amma sai akai rashin dace duk wayewarsa baya cikin maxinata. Yanxu gashi ya rabu da ita gaba daya, meyasa asirinta baya kamashine? Me gari ya waya yanxu? Ta bata lokacinta, ta bata kudinta, ta sabi ubangijinta, ta shiga haqqin baiwar Allah wadda batai mata laifin komai ba, a qarshe agaban dubban mutane ya cimata mutunci kuma ya rabu da ita. Nan take nadama ta saukar mata taji ta tsani kanta, wai itace yau tai silar haukacewar mutum? Meya jawo mata? (son zuciya da xugar gwaggoriya) lallai manxon Allah yayi gaskiya da yace "mafi qin abun bautawa a akan qasa son xuciya" ita yanxu gashi ya kaita ya barota. Tayi asarar lokacu, dukiya, mutunci kuma duk babu riba. Inta mutu yanxu mezatace da Allah? A fili tace "maryam ki yafemun na xalunceki ba tare da kinyimun laifin komaiba. Allah kaimun hukuncin daya dace da tsinanniya muguwa irina" ta fashe da kuka meban tausayi.



Mr Alex yana kallonta cikin tausayawa, tsammaninsa kukan rabuwa da sulaiman take donshi bai gane abunda take fada ba.



Te tashi ta fita office din da gudu tana kuka tana maganganun Mimi ki yafemun Allah kaimun hukunci a duniya" ta yanki burtali a qafa bata tsaya daukan mota ba, mutane anata kallonta kamar motsatstsiya.





Ta samu mahaifiyarta a gida wacce suke kira Hajia, yau anyi sa'a bata fita yawan gantalin ba.



Ta riqe Hanifa tana tambayarta a firgice "Hanifa accident kikai?" tayi wannan tambayar ne sabida taga idanunta sunyi luhu luhu ga fuskarta jajur sabida marukan da sulaiman yayi mata. Ta dubi yan aikin dake tsaye a kansu, alamar baxata fadi maganarba a gabansu. Hajia tace "ku bamu guri"




Suna kaucewa Hajia ta kuma tambayarta, Hanifa xuciyarta cunkushe take neman wanda xata fadawa damuwarta take. Ta kwancewa Hajia komai tundaga farkon ganinta da sulaiman har xuwa yau da kuma abunda sukai ita da gwaggoriya. Ta qarashe da cewa "Hajia ina neman kiban ixini inje infadawa sulaiman nice silar haukacewar maryam"




Hajia ta xabga mata mari tare da cewa "da ixinina kika nema lokacin da xaki haukata masa matar? Gwaggoriya ko? Itace uwarki? Dama ni can hankalina be kwanta da ita ba" ta qara rufe Hanifa da duka kota ina tana takata da qafa tana cewa "kin cuci kanki Hanifa, kin taba gani ina asiri? Wannan ba Hanifar dana shayar nona bace, gwaggoriya ta canjamun yata. Kin taba ganin nayiwa wani asiri? Tun yaushe duniya ta waye ko wadanda basu da ilimin boko sun dena asiri bare ke da kika qoshi da ilimi" Hanifa bata gujewa dukan Hajia ba sai data gaji dan kanta ta kyaleta.




Ta kwanta jikin Hajia tana kuka tace "Hajia ke kika haifeni kinfi kowa sanin ciwona, ki temakeni ki rufamun asiri ki fadamun hanyar da xanbi in gyara kuskurena kar inyi biyu babu na rasa duniya tunda na rasa sulaiman, banaso in rasa lahirata sabida hakkin maryam."



Hajia tana kallon Hanifa cikin tausayawa tace "kin kyauta da baki fadawa sulaiman ke kika haukata matarsa ba, domin da kin fada da yanxu rayuwarki na cikin hatsari." ta qurawa Hajia ido, Hajia ta kalleta tace "hanya daya ta rage mana wacce xaki gyara kuskurenki itace muje mu warware asirin da kikayiwa maryam" Hanifa ta kalleta a firgice tace "Hajia hakan xai yiwu kuwa?" ta bawa Hanifa amsa da "dole mubi duk hayyar da hakan xai yiwu. Ki tashi muyi sallah ki rakani gidan matsafiyar taku"




Sun dau hanya bayan idar da sallah, dakyar suka gane gurin don sai da suka hada da tambaya.




Uwargida ta watsa musu kallon wulaqanci bayan sun gama koro mata buqatarsu. Tace da Hanifa "aimu bama amai mu lashe, da kinsan baki shirya bata ba kika fito yawan asiri? Ku tashi ko bacemun ko kuma mu haukataku yanxu"



Hajia ta kalli uwargida, wai wannan matarce xata bude mata ido. Ta dakko wayarta ta kirawo danta soja wanda yake yayan Hanifa ta bude speaker din wayar. Ya dauka tare da cewa "Hajia ya akai akwai damuwa ne?" tace "akwai, soji nakeso a hadamun mota guda akwai wata yar matsala su xama ready in naga babu daidaito xanyo waya su taho" yace "to angama Hajia"




Ta kalli uwargida bayan gama wayar tace "xakiyi abunda nace ko sai nasa an markadeki an markade gidan?" uwargida ta miqe tsam ta fita ba tare da tace komai. Jim kadan ta dawo da kayanta na tsibbu himili guda, ta xauna ta dunga surutai tana jefasu a gabanta wuta na tashi. Ta dau tsawon lokaci tanayi, kana ta dubesu tace "xaku iya tafiya nagama" Hajia ta watsa mata kallon kyamata tace "inma karya kikai mana baki karya ba xan kuma dawowa in miki hukunci, tsibbu kuma baxan hanaki ba kije kiyi tayi wata rana qaiqayi xai koma kan masheqiya." suka tashi suka fice suna hararar juna.




A daren Hanifa taiwa munnir waya wani tsohon saurayinta kuma cousin dinta wanda ya shafe shekaru yana sonta amma taqishi har yayi aure da yayansa biyu. Yayi mamakin jin abunda Hanifa ke fada masa cewar in dai yana sonta har yanxu ya turo ayi magana. Ya gigice bakinsa na rawa ya tambayeta da gaske take mai? Ta tabbatar masa da gaske take, ya dunga godia yace xatajishi bada jimawa ba.





Kwana biyu tsakani aka kawo kudin auren Hanifa harda sa rana wata uku kacal. Munnir santa yake kamar ya cinyeta, ya dunga bata tausayi. (dama hakane dai dai, kuskurene ga wanda ke sonki kije ki mannewa wanda bai damu dake ba don salan kwantai.😜) gwaggoriya labarin engage din Hanifa ya sameta, ta dunga kiran Hanifa a waya taqi dauka. Ta nufi gidan afujajan, a xatonta sulaiman Hanifa xata aura. Tana xuwa Umma da yayyun Hanifa suka hadu sukai mata caaa, suka tsageta tas tare da fada mata anraba qawancensu da Hanifa don Hanifa yanxu aure xatai. Wanta soja yace inya kuma ganinta ko a hanyar gidansu saiya kaita barikin soji. Da wannan aka raba gwaggoriya da Hanifa. Hanifa ta rubuta takaddar barin aiki ta tura NNPC da nufin ta samu wani aikin bayan bikinta don baxata iya xama inuwa daya da sulaiman ba don har yanxu babu abunda ya ragu na soyayyarsa a xuciyarta kawai dai ta haqura ne kuma bataso ta dunga ganinsa a matsayinta na matar wani tunda tuban gaskiya tayi.



******** ******** *******


A cikin satin Mimi na uku a kano sauqi ya samu sosai, hankula sun kwanta. Faty harta koma gidanta, Aisha kuma taje ganin gida garinsu. Dakin ya rage daga Mimi, mama, Rashida sai Dady.




Duk da sauqi ya samu sosai babu abunda aka fasa na magani, sabida malamin dake mata aikin yace irin wannan lalura tana da kwan gaba kwan baya kana kuma kota warke sai anmata dafa'i sabida gaba.



Rashin maganarta dai na nan, saita kwana biyu batace da kowa komai ba amma duk abunda aka sakata xatayi. Duk da akwai burbushin lalurar a tare da ita amma damuwa itace silar wannan shirun nata. Mimi tasa damuwar mijinta a ranta sosai, abun kan bata mamaki wai ya Bature ko a wayar mama ya gaxa kira ya tambayi halin da take ciki. Ita ba a ta tata domin daga ita sai kayan jikinta aka kawota kano babu xancen waya don ko kayan sakawa maternity gown din ya Faty wacce mama ke dinka mata ta kwaso ta kawowa Mimi take sakawa, sai kuma wanda mama ta kuma dinka mata. Wannan damuwa ita ke kawo koma baya a lfyarta.




Ta rame sosai tayi duhu sabida mayunkan da ake shafa mata na magani, ciki kuma ya koma dan qarami kai kace baifi wata biyu ba, bayan ya cika wata biyar har yana shirin shiga na shida. Batacin abinci sai dole ko in sunci da Baffa, Faty na yawan fada mata in bata cire damuwa ba dan cikinta xai samu matsala tunda yanxu ma ana xargin cikin ya koma baya, ma 'ana saiya mai maita watanninsa.





Yammacin laraba suna xaune ita da mama, TV kunne suna sauraran saudi Qur'an wacce ita ake kallo koda yaushe a dakin. Ta kalli mama, a qoqarinta na kawar da tunanin Bature tace "mama bani lbrin Baba" mama ta kalleta cikin rashin fahimta, Mimi ta qara mata bayani da cewa "Baba yana sona?" mama ta shafa kanta tace "sosai kuwa Al amin yake sonki maryam. Kullum kina sabe a kafadarsa yana yawo dake ganin likita sabida Allah ya halicceki mai lalura." Baffa daya shigo tun daxu domin kawowa Mimi guava da ta bashi sallahu da xai fita ya kallesu uwar da yar gaba daya tausayi suke bashi. Ya matsa gabansu yace "tabbas maganar fadima gaskiya ce maryam, da ace Al amin yananan yaga kin sami lafiya da ilimin da yake buri kuyi da bansan iyakacin farin cikin da xaiyi ba. Don shidin yasha fadamun cewa yanason ki gajeshi ki xama lauya ita kuma Faty Malanje jinya, duk da baya raye Allah ya hadaku da jarumar uwa ta tsaya tsayin daka ta cika qudurin daya mutu dashi." Mimi ta kalli Baffa cikin hawaye tace "in shaa Allah saina gina masallaci da makarantar islamiyya da nufin Allah ya kaiwa Abba ladan kabarinsa. Baffa da mama suka amsa "Allah yasa."





Ranar laraba bashi da aiki a office sai dare, da sanyin asuba ya tashi ya shirya daga masallaci ya wuce ko Farida bai fadawa ba balle yayi mata sallama. Ba a xancen Bature don basa magana dashi da ishaq din a dalilin Mimi, sabida ishaq din yayi yayi Bature yaje kano ko sato Mimi ne yayi suxo su kaita abroad a duba matsalarta yaqi a dalilin haka ya dena kula Baturen gaba daya, shima ya dena kulashi tunda a halin da yake ciki yafison kadaici sai suyi kwana 3 basu hadu ba sai a masallaci shima ko sahun sallah basa hadawa. Ishaq ne kuma kano ya nufa.



A tsaya a hanya ya lodi fruit sosai hardasu coconut. Daf da shiga kano ya tsaya wata babbar store ya kuma siyan kayan masarufi dangin kayan tea da lemuka da biscuits wanda basu da illah ga lfy ko ga mace me ciki.





Sanda ya isa kano ko taran safiya batai ba, kai kace anan ya kwana. Gidansu Farida ya wuce suka gaisa yayi breakfast ya huta a sit room din gidan ya sake sosai, suka dade suna hira da iyayen Farida ya kawo tsarabar da yayo musu ya basu. Abbanta na tambayar yar lelensa, ishaq yace "wlh abba ban fada mata xanxo ba, don cewa xatai saita biyoni, kuma ga yanayin jikin nata ni kuma yanxu xan koma Mimi naxo. dubawa" abba yace "hakane kam" suka xarce da hirar ciwon Mimi Umma na fada masa cigaban da aka samu. Sai wajen 11:00 AM sukai sallama ya bar gidan





Mimi yau dai antashi da miskilancin ko jikin ne ya motsa oho. Silar kuwa shine; fauxa da taxo dubata takanas daga Lagos ta kwana biyu anan gidansu Mimin. Mimi taji dadin xuwan fauxa kowa ya shaida haka don ko maganar da batayi xuwan fauxa yasa tanayi jifa jifa. Babyn fauxa kuwa wato maryam wacce fauxan ke kira "Mimi" tunda sukaxo Mimi ta amshe yar kuma yarinyar bata da rigima takan wuni a jikinta sai xatasha nono Mimi ke bawa fauxa ita. Itama fauxan kuka take sosai da xata koma tace da Mimi in sunusi zai dawo qarshen wata xata biyoshi ta kuma ganin jikin. Tayi hidima sosai ta kudi data gaba, don tunda taxo mama ta huta wankin undis din Mimi da hada mata ruwan wanka da sata alwala da bata magani. Mama batasan Mimi nada masoya haka ba sai yanxu. Domin mutane ta ko ina barkowa suke dubiya wasu ta ganesu wasu kuma bata ganesu sai dai suce tare sukai skul da ita ko kuma dalibanta na legal. Abun shaawa har qungiyarsu ta CDS sunxo kuma harda kudi suka hada ta hanyar platoon officer dinsu suka bada aimata magani. Ta samu alheri ba kadanba, wasu kudi, wasu kayan dubiya, wasu kuma magani ko tofi kuma duk wanda ya kawo tana karba ta bawa Mimi da kyakykyawar niyya tunda shi magani dace ne.





Tun bayan tafiyar fauxa Mimi ta burkice tayi kukanta da yan rigimarta Rashida da mama suka lallabata tayi shiru, ana cikin haka ishaq yaxo.




Daga dakin Baffa bayan sun gaisa dakin mama ya shiga suka xauna a falo aka taso masa Mimi wacce ta fara bacci.




Tana ganinsa tasa kuka sabida tuna ya Bature da tayi, shima nan take ya karanci dalilin kukanta. Da kyar ya lallasheta suka gaisa, ya dunga yimata nasiha, bai mata xancen sulaiman ba itama bata tambayeshi shi dinba duk da azalzalarta da xuciyarta keyi nason jin halin da yake ciki. Ta tabbatar Anty gaskiya take fada tunda gashi har ishaq yaxo kano dubata amma babu ko saqon gaisuwa daga sulaiman din. Ta tambayeshi Farida, yace tana lfy tana gaisheta batasan xaixo ba.




Baffa ya leqo zai fita kasuwa kamar yadda ya saba yakan leqo yayiwa Mimi sallama da kuma tambayarta abunda takeso ya siyo mata. Yace "maryamu xan tafi me xan taho miki dashi?" tayi dan jum tana tunani, can kuma tace "alawar madara da kwan zabi dafaffe"yayi murmushi yace "yau baxa aci gobar ba kenan?" kafin tai magana mama ta fito daga daki tace "Mimi banda abinki ina xaiga alawar madara? Baffa ka bari xan bayar a siyo mata anan" yace "a a xansa a nemo a kasuwa, kwan kuma xanyi waya akawo daga gidan gona saiki dafa mata" tace "to a dawo lfy" Mimi ma tai masa adawo lfy.



Ishaq ya dawo da kallonsa kan Mimi, ya yaba kwarai da kulawar da ake bawa Mimi da gatan da take samu amma abun mamaki meke ramar da ita haka kamar me hadiyar allura?tunanin mijinta wata xuciyar ta bashi amsa. Tabbas Bature bai kyauta ba da yaqi waiwayo AL 'AMARIN MARYAM kuma dole inya koma ya bude masa wuta akan hakan koda xasu bata har abada.



Ya fita waje yasa yara suka dunga shigo da kayan daya lodowa Mimi aka cika falon dasu sannan ya dawo ya xauna. Mama ta fito tana masa godiyar dawainyar daya sha, ya tambayi mama "mama anya maryam nacin abinci kuwa? Dubi yadda ta qare ta lalace ya kamata a dunga kulawa kodan abunda ke cikinta" mama idonta ya cika da kwallar tausayi

Please Login or Register in order to submit comment