Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata.




Tarayyarsa da Hanifa tananan a yadda take, har yanxu bata saduda ta daina bautawa na tsugune ba Kullum kudinta suna can. (ni kuwa nace dama kin tashi kin shaidawa mai duka gwanin hukunci da wannan yawon da kike ke a kode xaninki a kode ga asarar dukiya)




Basu jima da dawowa ba hutun sallah suka sami baquncin Anty mami taxo 9ja Abuja yin wani aiki kuma a gidan su Mimi ta sauka, Mimi na ganinta gabanta ya yanke ya fadi amma duk da haka ta danne taje ta taro ta ta karbar mata akwatin hannunta tana cewa "sannu da xuwa Anty mami" tana wani yatsina da basarwa ta banbare Mimi daga rungumar da tai mata, ta samu guri a falon ta harde. Mimi da hadiman gidan suka dunga xarya dan samar mata abun buqata, sai da suka cika centre table din gabanta da nau ikan abinci da kayan motsa baki sannan Mimi taje ta gyara mata daya daga cikin bedroom din dake part din duk da a gyara yake tasa sabon bedsheet da maganin sauro na feshi ta turaren wuta kana ta kai mata jakarta da akwati dakin ta dawo falo gurinta don su gaisa.





Ta durqusa har qasa daga gefenta tana gaidata. Ta juyo tana hararta tace "amma dai kya bari in ci abinci in huta kafin ki isheni da gaisuwarki ta fi'ili" duk da Mimi taji haushin maganar saita danne a fuskarta bata nuna komai ba tace "to" ta tashi ta xuba mata abincin ta shiyaya mata ruwa da lemo ta tura mata gabanta sannan ta koma gefe ta rakuye.





Dake isowar yamma tayi tana cikin cin abincin ya Bature ya dawo, ya nuna farin cikin ganinta sosai ya matsa kusa da ita kamar xai shige jikinta suka gaisa tana fada masa aiki taxo na company dinsu kuma xatai 2 wks ne. Mimi ganin ta amsa gaisuwar Bature duk da tana cin abincin itama ta matsa ta kuma gaisheta. Bature ya kalleta yace "Mimi sai yanxu xaki gaisheta?" kafin tai magana Anty mami ta rigata da cewa "eh ai wai ita isashshiya yanxun ma ganinka yasa ta gaisheni inaka da bakaxo ba baxan samu arxiqin gaisuwar ba, nafi awa daya a gidannan amma ko kallon inda nake batai ba sai yan aiki take ba order a kawon abinci ga mayunwaciya" ya juya yanawa Mimi kallon tuhumar abunda tayi. "ta danne duk wani mamakinta na qaryar Anty mami ita cikin qasqantar da kai tace "yi haquri Anty gani nayi kinacin abinci shiyasa na bari ki gama ki nutsu saimu gaisa, bakyayo doguwar tafiya tun daga wata qasa in tareki da gaisuwa ba" cikin gamsuwa Bature ya jijjiga kai yana duban mami yace "Allah sarki Mimi badai hankali ba, Anty Kinji nata uxurin shiyasa baku gaisa ba" ta bata rai jin baiga lefin matarsa ba. Mimi kuma ta matso ta gaida ita, ganin idon Bature yasa ta amsa da dan sakin fuska. Mimi aranta mamaki take ada duk dangi sun shaida bayan yan uwan Anty mami babu wanda takeso kamar Mimi ko xuwa tai tsarabar Mimi ta dabance amma yanxu gashi duk wannan soyayyar da take mata ta koma tsana a dalilin ta auri qaninta. To me xa a kira wannan abun? Son Baturen take har abun ya xama kishi ko kuma Mimi ce bataso ta auri dan uwanta? Bata da amsar wannan tambayar shiyasa ta miqe ta shiga ciki ta barsu suna hira da yar uwarsa.




Da dare gurin cin dinner ma harta zauna cikinsu don cin abinci Bature yanata jan Anty mami da hira, ita kuma tana bashi amsa da e ko um. Can dai tagaji ta dubi inda Mimi take tace mata "wai ke bazaki barmu muyi hirar xumunci bane komai sai kinji?" Mimi ta dubi shahin da Bature yake, fuskarsa bata nuna komai ba sai cin abincinsa yake ganin haka ta miqe da plate din abincinta ta nufi gefen falon inda Coffee table yake ta xauna tanaci. Abincin ya fita daga ranta amma intaqici kamar tayi fushine bataso kuma Anty mami ta gane taji haushin abunda take mata.



Tana gamawa taje tai shirin bacci bata jirashi ba, don taga abun nasu nayi ne.



Acan kuma bayan sun gama cin abinci shi da Anty mami hirar tasu daki ta koma wato inda aka sauketa. Tana zaune kan gadon dakin shi kuma ya dora kansa akan cinyarta suna hira. Anty mami tanason Bature fiye da kowa cikin qannenta, shima kuma biyayya yake mata kamar ita ta haifeshi. Batason yafison matarsa kanta Kardai Mimi wacce take ganin bata dace da Dan uwan nata ba.




Tana shafa sumar kansa ta sako masa xancen dake cin ranta "sulaimanu ya dace fa ka ganemi wata macen ka qara aure, zamanka da wannan ita kadai baxai yiwu ba tana illolin da ba a iya xama da ita kawai ba a matsayin matar aure. Kaga na farko ita din bazawara ka aureta, sannan kuma nasan ba santa kake ba akwai dai dalilin da yasa ka aureta wanda har yanxu na kasa gano menene, dalili na uku kuma bafi girma shine ba haihuwa xatai ba don duk da nema dakai a rufemun case dinta da tsohon mijinta sai da naji xancen, kaga kuwa ina kai ina xama da macen da bata haihuwa?"



Ya qurawa Anty mami ido yana tsananin mamakin inda taji xancen matsalar Mimi da Badaru ya haddasa mata, a iya saninsa sai da mumy ta hadasu duka ta kwabesu akan kar a fada mata to waye kenan ya bujurewa maganar mumy ya fada?




Tunaninsa ya koma kan batun da tayi na qarin aure, ya hada maganarta da nacin Hanifa na ya aureta, to kenan inma qarin auren ne Hanifa zai aura? Dake lokacin giyar asirin Hanifa ya dan sakeshi sai yayi saurin kauda wannan tunanin a xuciyarsa. Hanifa ba irin matar da yakeson aure bace tundaga kan halittarta har xuwa halayyarta in case of xai qara auren kenan.



Hujjarsa kuwa itace yar soyayyar da suka fara da Hanifa ya gane wacece ita, don sosai take kwada masa suyi soyayyar banxa wato ta tabe tabe, dataga yaqi ganewa sai ta fito fili ta fada masa wai shidin bai iya soyayya ba don in namiji nason mace Allah Allah yake yakai hannu jikinta. Ya nuna mata shi sam wannan baya gabansa Last xuwansa gidansu wanda bai qara marmarin komawa ba fada sukai sosai akan ta xauna akan cinyarsa cikin bacin rai ya nuna mata bayason hakan suka rabu baram baram.




Tun daganan bai qara xuwa gidansu ba, kuma itadin kanta ta fice mai arai. A raayinsa bayason macen da xata nuna tanason ya tabata ko tanason kyansa har gara wacce xata nuna kudinsa takeso anasa raayin.



Ya dubi mami cikin kulawa yace "Anty mami Dan Allah waya fada miki maganar Mimi da ex dinta? A iya sanina mumy tace kar a fada miki amma acikin yayan gidanmu har xa a samu wanda mumy xata hana abu amma yayi?" cikin kulawa itama ta dubeshi tace "ba wannan na tambayeka ba kawai ka amsamun maganar auren don shine burin danasa gaba a yanxu" cikin rashin bawa waccen maganar mahimmanci yace "tabbas nasan little ce ta fadi maki kuma sai nawa mumy waya na fada mata"




Anty mami tace "karka janyowa little fadan mumy dan wlh ba ita ta fadan ba, maijidda ce ta fadamun" yayi shiru yana tunani lallai xaiyi takakkiya har kano yaje yaci uban Maijidda in bata fita daga harkarsa ba, ina ruwanta da matsalar Mimi dahar xata dunga yaya tawa a dangi. (in baku manta ba Maijidda yar wan su mumy ce wacce taqi aure sabida tana jiran ai masu hadin gida da Bature) yace da mami "lallai xanci uban yarinyar nan, don ubanta taqi aure tana yawan karatun boko shine ni xataxo ta tasamun mata a gaba?" Anty mami ta yatsine fuska tace "can itaku ni dai bani amsar tambayata" ita kanta Anty mami Maijidda batai mata ba kuma ta dade da sanin Maijidda nason Bature don har da ita ta kama qafa taga babu hanya ta haqura. Don Maijidda wankin idonta da wayewarta tayi yawa intana abu kamar karuwa ko shigarta irinta jaruman Hollywood take.





Cikin kulawa ya dubi gefe daya ya fara magana "Anty mami ana aure ne kan abubuwa da yawa, babba daga ciki kuma jigo shine yin aure don ibada da kuma kare kai daga zinace zinace sannan samun zuria. To ni kam duk nasamu wannan abubuwa, inkuma na qara wata matar bayan Mimi wlh Allah zai kamani da rashin adalci a tsakaninsu. Inkuma dan rashin haihuwa ne Allah ba yacce bai iyaba Kullum ina addua kuma ina kyauta xaton xai bamu"


Cikin bacin rai tace "ni duk ba wannan nake dubawa ba kuma basu nake nufi ba, just naqasu ne ace handsome kamarka kuma mai kudi kana zaune da Mimi kadai a matsayin mace." shima ya kuma gyarawa yace "Anty bara inmiki gwari gwari, indai don jin dadi ake aure ko shaawa to wlh Mimi anan bangaren ta xarce tunanina don har sawa take inrasa hankalina na wucin...... Kafin ya qarasa Anty mami ta durka masa dundu tare da runtse ido tace "ya isa basai ka qarasa ba mara kunya, ni ba wannan na tambayeka ba" Bature ya kwashe da dariya ganin yadda ta runtse ido kamar taga wani abun qi. Jin yana mata dariya ta dauki filo ta fara jifansa dashi yayi waje da gudu, anan hirar taxo qarshe ya nufi daki yayi shirin bacci ya duba agogo wajen 11 na dare. Ya samu Mimi tana baccinta ta bashi tausayi sosai don abunda Anty mami tai mata daxu baiji dadi ba just ya danne ne.




Washegari ya fita aiki, Anty mami kuma ba yau xasu fara aikin ba sai gobe don haka har ya fita bata tashi bacci ba.




Wajen 11 Farida ta shigo gidan kamar yadda ta saba a gidan Mimi take yini in ishaq ya fita don cikinta mai laulayine kuma ga kwadayi inta shigo Mimi ke dawainiyar dafa mata duk abunda takeso itace dan malele, dan wake, wainar fulawa.





Batasan da xuwan Anty mami ba, suka xube a falo suna hira kuma hirarsu ce ta tashi Anty mami. Ta jisu inda take cewa "yau kam besty Babyn ki wake da shinkafa yakeso, jiya har mafarki nayi inaci da manja da yaji" Mimi cikin dariya tace "ya kwantar da hankalinsa dama muna da jan wake yau kam sai adafa wake da shinkafa gaba daya gidan har salak da tumatur yau Baby na yayi kwadayi mai kyau don nima inason ci"




Anty mami ta fito da taqama taga wacece wannan har take fadar abunda xa a dafa a gidan. Jikinta yai sanyi ganin Farida kuma nan take ta gane ciki ne da Farida. Farida tace "au Anty mami, saukar yaushe" tana dariya tace "jiya da yamma" tace "mashaallah amarya har an harbu kenan? Ai gara haka haihuwa itace ribar aure" Farida dariya take cikin kunya don bata xaci habaici taiwa Mimi ba don ita tunaninta bai taba bata mami xataqi Mimi ba. Mimi kuwa duk da ta fahimci saqon mami sai tayi murmushi ta sunkuya tana gaidata. Ta amsa tare da cewa Mimi "kije ki gyaran daki a wanke toilet" Farida tace "masu aikin gidan basa nan ne?" cikin isa mami tace "No Just ita nakeso tayi" Farida tadan fara fahimtar abunda ke going Mimi kuma ta wuce gyara daki.




Ta gama gyara dakin tana wankin toilet safna iso, xuwanta gidan kenan na farko tun xuwan Mimi tana shigowa tace "Anty mami memakon ki sauka gidana kya sauka gidan amare?" Anty mami ta bata amsa da cewa "ga gidan Dan uwana wanda nake da iko akan komai xan taho gidanki ina rabe rabe muna hada hanya da mijinki?" sai a lokacin idon safna yakai kan Mimi dake wankin toilet. Cikin mamaki tace "Mimi kece ke wankin toilet kodai shaawa kikai?" "ni nasakata" Anty mami ta bata amsa.




Mimi ta fito bayan ta gama tana cewa "Anty safna nayi fushi fa sai yau kika leqoni? Kuma nasan yanxun ma xuwan Anty mami ne ya kawo ki ba gurina kikaxo ba" kafin safna ta bata amsa mami tace "to inba gurina tazo ba gurinki taxo? Ai tasan dake din da bata shigo ba sai yanxu da naxo don ta nuna miki wata kusan tafi wata" safna ta saurinta tace "a a ni ba haka nake nufi ba, yi haquri matar yaya guri na baku ku gama amarci don innafara xuwa saina gundureku" Mimi cikin jin dadin kalaman safna tace "Allah ya kawoki bazamu taba gundura dake ba, mutum ai baya gundura da nasa" tai waje don kawowa Anty mami breakfast.




Tana bada baya safna ta kalli Anty mami ta fara magana "gaskiya baki kyauta ba, ya daga xuwa gida xaki fara sata aiki wannan abun fa da kike sam be dace ba kuma karkiga mijinta baya damuwa wlh kawai gara yake muki amma kinkacigaba da haka wlh mutunciki zai zube a gurinsu" Anty mami cikin hargowa tace "aishi ba tanbadadde bane irin Audu kuma yana sona yanamun biyayya akan wata banxa Mimi bazai juyamun baya ba" safna ta kuma dorawa da cewa "ai kuwa inkaci gaba da nuna haka akan matarsa wlh zai taka miki burki, dama mumy tanajin ance anan kika sauka tai hasashen matsala xaki zame musu. Hasashenta kuma ya xama gaskiya daga xuwanki kin fara bautar masa da mata" cikin tsananin fushin nuna son Mimi da suke tace "to ai saiki buga ki fada mata abunda ke faruwa taxo ta koreni inkoma hotel tunda kunfison Mimi akaina" safna ta bata amsa da cewa 'ko bakice in fada mata ba nima innaga abun naki ya wuce makadi da rawa zan fada mata don banga dalilin qiyayyarki ga matan qannenki ba don xubar da girma irin haka ta janyo miki raini gurin yasmin"







Mimi ta hado abincin kari a qaton try ta kawo ta tsuguna ta hadawa Anty mami tea kana ta hadawa safna ma duk da ta qoshi amma sai data qarba don karta gwale Mimi. Ta cika musu plate da chips da platain soyayyu tasa musu wainar kwai a gefe da saka musu fork akai ta tura musu, kana ta kuma xuba musu farfeso na kayan ciki tana shirin tura musu ne Anty mami tace "wannan duk abincin ina xamu kaishi? Ko ance miki kowa cikin zani gareshi irinki?" batace komai ba ta fita ta samu Farida kwance gadonta suka fara hira kan gidan abincin Farida da aka bude na Abuja yan kwanakin da suka wuce. Suna cikin hirar ne Farida ta sanyo Anty mami ciki da tambayar abunda tagani dazu. Mimi bata boye mata komai ba ta fada mata tsakaninta da ita a da da kuma yanxu data xama matar qaninta.




Farida masifa ta dunga yiwa Mimi akan wannan sanyin da kwantar da kai baxai kaita ba gara ta horoncewa Anty mami irin yacce yasmin tayi. A fadar faridan in itace wlh saita casa Anty mami da qafarta xatabar gidan. Mimi ta bata tabbacin baxata iya ba sabida xumunci da kuma mumy, xatai haquri da Anty mami darajar wadannan abubuwa. Farida ta watsa mata harara tace "ai saiki xauna kita hadiyar baqin cikinta" Mimi tana dariyar daukan dumi irin na Farida tace "xo muje kitchen din mu dora girkin kar kuku ya rigani" suka nufi kitchen Farida ta xauna kan stool Mimi ta hadata da yankan salad ita kuma ta dora wake.




Acan daki kuma Mimi na fita safna tahau Anty mami da fada tana nuna mata kuskuren takura Mimi da taxo tanayi har gidan mijinta duk kuwa da biyayyar da Mimi ke mata. Anty mami ma tahau sai cacar baki suke kamar saanni daga qarshe dole safna ta bar mata tunda ita din ba gwanar masifa bace. Daga qarshe Anty mami ta share safna ta dakko system tana dannawa wai ita a dole tana fushi safna tai mata rashin kunya akan Mimi. Ta gaji da xaman jugum jugum ta nufi kitchen maida kayan da suka karya anan ta tarar da su, tasa hannu jin rice nd beans ake suka ida sukaje sallah sannan suka xuba a try su ukun yaji manja da yaji salak da tumatur da gurji da dafaffen kwai suka baje a falo sukaci sukai qat suka dora da coke. Ita kuwa wacce ta sawa kanta kunci tana qunshe a daki.





Sai dawowar mai gidan suka tafi, yace da Mimi yunwa yakeji bata gama abincin dare ba hakan yasa ta dakko masa guntun wake da shinkafar da yayi ragowa ta xubo masa hadin salad akai. Ya xauna yaci yana santi har yana tambayarta ta aikawa ishaq? Tace "eh Farida ta diba masa" Anty mami ta fito daga daki yana dariya yayi mata barka da gida. Bata amsa ba ta xarce da qorafin Mimi tasan tananan amma tayi wake da shinkafa, ita kuma bataso. Ya dubi Mimi dake xaune gefensa yace "Mimi luv ya akai abincin da Anty mami bataso" cikin kwantar da kai tace "yi haquri ranka ya dade, bansan bataso ba Farida ce take shaawa shine nayi a gidan gabadaya" ya juya gurin da Anty mami ke tsaye "to Kinji uxurinta Anty mami amma kiyi haquri" cikin fusata ta fara magana don ta farajin haushin tufkar da take Mimi na warwara duk yacce taso haddasa rigima tsakaninsu sunki bata hadin kai "to saiki fadamun da Farida da ni wayafi matsayi da iko a gidan?" Bature yayi saurin tareta da cewa "a a Anty duk abun bai kai haka ba, yanxu ya kikeso ayi?" cikin izzah tace "ta dafamun abunda xanyi don yunwa nakeji, don zalunci tasani yini da yunwa ni da gidan Dan uwana" ya kalli Mimi yace "Mimi luv dan daure ki samawa Anty mami abunda xataci me sauki" ta haskeshi da murmushi tace "to yaya luv" ta miqe ta nufi kitchen. Anty mami taja dogon tsaki kodai xatabi shawarar safna ta fita harkarsu? Amma kishin Mimi take sosai akan Bature.



Ta dora mata farin couscous wanda ta yanka koran tattasai ta xuba mai a dahuwar sai green beans. Gefe kuma tana duba girkinta na dare data dora (tuwon shinkafa da miyan kuka) babu jimawa ta gama ta dumama mata stew din da take da ita a fridge ta hada mata ta kai mata har daki.




Ta kalli couscous din bayan fitar Mimi, batacin couscous don haka ta dibi wake da shinkafar da aka ajiye mata tun rana taci ta barbaza kamar bata diba ba don dama tanaso don san haddasa fitini tace bataci.





Da daddare gurin dinner Mimi bata xauna cikinsu ba sabida abunda ya faru jiya. Anty mami bataiwa kanta ba wannan karon sakin jiki tayi ta kwashi tuwon shinkafa miyar kuka don ko tayi akai mata bata qin ci, tanason wannan cimar kwarai kuma sabida ita Mimi ta dafa, duk sai taji kunyar abunda tayi dazu. Ragowar tuwon tace Mimi ta ajiye mata xataci dumame. Yauma can ta barsu suna hira a falo taje baccinta.




Ranakun da suka biyo baya ta dan samu saukin takurar Anty mami sabida ta fara halartar aikin da ya kawota, sukan yini da Farida a gidanta ko ita taje gurin Faridan. Sai dare Anty mami ke dawowa, inta dawo kuma a gajiye take amma dan kishin kar Bature ya bawa Mimi lokacinsa haka xata tareshi da hira yana hamma tana hamma har sai lokaci yaja wanda takega koya koma gurin Mimi bacci kawai xaiyi.




Akwana na hudu da xuwan Anty mami gidan da yamma Bature ya dawo ya sami Anty mami gida, yau ta dawo da wuri. Mimi tamai barka da dawowa ta cire masa jacket din saman suit dinshi tada fara jiqewa saboda ruwan saman da ya sauka babu jimawa ta shige cikin daki don ajiyewa ta barsu shi da Anty mami suna hira. Shiru shiru yana jiran Mimi ta fito daki ta kawo masa abun sha kamar yadda ta saba inya dawo amma bata fito ba. Yace da Anty mami yana xuwa ya tashi yabi Mimi daki.




Ya sameta xaune kan kujerar gaban madubi riqe da rigarsa data cire masa tana hawaye, dakin da dan duhu kadan sabida hadarin daya lullube sararin sama kuma bata kunna haske sosai ba. Jin takun mutum yasa tayi saurin qudundune rigar ta boye a jikinta, sai dai ta makara don ya riga yaga abunda tayi yana xuwa yasa hannu ya ciro rigar ya qurawa rigar ido da nufin gano abunda yasata kuka ajikin rigar. Sai da yayi amfani da fitilar jikin wayarsa sannan yaga shatin lebunan mace da jan janbaki (💋)radau a jikin light ash din suit dinshi. Jikinsa yayi sanyi qalau don yasan ba Mimi bace don ita da wuya tasa jan jambaki indai ba period take ba ko kuma tasa kayan da suka dace da kalar ja, tafi saka pink ko dark purple.




Tunani take a xuciyarta tun sanda ta shigo dakin ajiye rigarsa ta dagata tana yarfe ruwan jiki da nufin ta dan shanya idonta yakai kan 💋 wannan, wato kenan Bature yawan bin mata yake shiyasa kwanaki yake yawan fitar bayan isha sai wajen 10 ya dawo? Shiyasa Kullum yake cikin yin waya babu dare ko rana kuma intana gurin baya amsawa? Lallai ita din banxa ce tun a lokacin ya kamata ta gane ba sai yanxu da abun ya girma ba har ya fara nuna mata shedar yana bibiyar mata. In kuwa ya Bature neman mata yake tabbas ya cuceta cuta ta har abada kuma wlh xata iya haqura dashi duk soyayyar da take masa don ita batason fasiqi tun farko abunda tai gudu kenan ya Faty ta kakkareshi kyakykyawan namiji kamarsa ba a rabashi da yan mata bare shi bayan kyau ga kudi. Wannan dalilin shi yasa ta riqe rigarsa tana kuka har yaxo ya sameta.




Shi kuma anasa bangaren tunanin yadda akai wannan janbakin yaxo jikinsa yake, inyaje office yakan cire jacket dinsa a rataye wasu lokutan baya sakawa sai antashi ya mai da abarsa jikinsa. Babu shakka Hanifa tayi amfani da wannan dama xata haddasa masa fitina da xargi tsakaninsa da iyalinsa tabbas sai ya dau mataki akan hakan.




Tunaninsa ya katse lokacin da yaga Mimi na shirin fita ta bar masa dakin, yayi saurin isa inda take ya riqo hannunta yana bata haquri. Bata da niyyar sauraranshi don sai kici kicin kwace hannunta take, ganin haka ya kai gwiwoyinsa qasa ya tsuguna gabanta ya riqo hannayenta. Jikinta yayi sanyi ganin mijinta a haka tace "ya Bature me haka? Ka tashi don Allah" ya katseta da cewa "MARYAM wallahil azeem ban taba aikata abunda kike zargina akai ba, kuma ni kaina bansan yadda akai jambaki yaxo rigata ba, amma na miki alqawari indai ni SULAIMAN aurene ya haifeni baxaki qara ganin haka ba" idonta cikin nasa tana xubar da kwallah tace "ya Bature basai kayi wannan rantsuwar ba, na yadda da kai da kuma abunda ka fada don Allah ka tashi" bai tashinba sai matsowa yayi kansa dai dai mararta ya kwantar da kan nasa a cikinta, ita kuma tasa hannu tana shafa masa. Yace "indai kin huce kiyimun dariya" ta washe masa fararen haqoranta kana ya miqe ya rungumeta suka fito saqale da juna.




Da daddare be zauna hira da Anty mami ba kamar yadda suka saba, yayi mata qaryar kansa na ciwo ya nufi gurin Mimi.

Please Login or Register in order to submit comment