Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Barrack Obama) kai kace sun hada dangantaka, babu a bunda ya hadata da yar uwarta Faty ta bangaren kama sai muryarsu da take iri daya sai kuma dimple (beautiful point) din da suka gada ta bangaren uwarsu, domin yawanci yaya da jikokin gidan sunada shi. Wannan kenan.

Sun taso da mutuqar soyayyar junansu, hakan baya raba nasaba da adduar mama domin duk sanda tasa goshinta a qasa tana adduar Allah ya hada matΓ‘ kan yayan nata kamar yadda ya hada nata da Adda halima, domin su kadai Allah ya bata (bata haihuba a gidan Baffa). Dayake Allah maji roqone ya amsa mata, ita kanta tana alfahari da yayanta inta kallesu tana tasbihi ga Allah, Faty kyakykywa tΓ‘ qarshe San kowa kin wanda be samu ba, da kuma Mimi wacce da wuya ka dora ido akanta kadauke batare da tasbihi game dukaba musamman inbaka da cutar hassada. Duk da yawan gorin da ake mata a gidan na cewa "duk macen da bata haifi namiji ba bata haihu ba " wannan maganace da Kullum saΓ­ Anty ( jamila) ta fada mata ita. Da yake anty kamar yadda yaran gidan ke kiranta, ta kasance mahaukaciyar mace me mutuqar kishin mama ta tsaneta da yayanta, kuma bata iya boye abunda ke xuciyarta baro baro take nuna kiyayyarta ga maman tana taqama da yayanta kwarai kuma da fifitasu akan komai da take dashi. Yayin da Umma (hajara) ta kasance makirar mace kuma karuwar cikin gida, (fir'auna a xuci Musa a kan sharshe) wacce da wuya ka gane ainihin abunda ke xuciyarta inba mugun Sani kai mata ba, bazaka taba cewa ta damu da wanxuwar mama da yayanta a cikin gidanba. Amma a gaskiyar lamari tafi Anty tsanar su, domin lokacin da aka auro fadima itace ta nemi hadin kan Anty duk da tsananin kishi da fada da suke gwabzawa a lokacin, ta shawarceta da su ajiye kishi guri guda su yaqi fadiman. Kuma ta jagoranci Anty suka bi duk wasu hanyoyi suka hana fadima haihauwa domin a cewarsu be kamata taci gadon qani sannan tazo taci gadon yayansa ba. Shiganan fita can haka sukai ta xagaye guraren na tsugune (bokaye) har sukai nasarar rufe mahaifar fadima . (nikuwa nace Allah dai be qaddara rabo tsakanin fadima da Buhari ba domin daya qaddara bokaye basu isa hana Allah ikonsa ba). A duk sanda Anty taiwa mama gorin rashin haihuwar yaya maza takance ita haihuwa ai mai albarka kawai ake nema bawai jinsi ba Allah ya yiwa wanda yabani albarka .

Arziqin Baffa ya bunqasa kwarai domin yanxu har gina gidaje yake yana siyarwa ko ya saka haya ga gidan gonaki da yake dasu wanda yake kiwon kaji, kifi , raguna da kuma shanu. Mutanen da sukecin abinci a qarqashinsa suna da yawa, xuwa wannan lokaci ya aurar da yayansa mata da dama, kuma baya aurar dasu sai ya kaisu sun sauke farali (hajji) kusan ma yarinya tana gama secondry a gidan yake kaita maka, dayake yawanci bibbiyu suke tashi yaran gidan saboda tare Umma da Anty ke haihuwa sai dai tsiran watanni. Duk da cewa baiyi karatun boko mai xurfiba ya bawa yayansa ilimi domin dukkansu sai sun haura secondry yake aurar dasu kina fara jami a level 100 xuwa 200 saiya aurarki kya qarasa agidan mijinki. Kuma bai yarda da bawa karabuti auran yayansa ba, domin yace bazai sayar da akuya ta dawo tana cimasa danga ba, sai wanda ya tara (mai kudi) komai rufin asiri sosai yake bawa auran yayansa. Kuma Allah ya dafa masa akan hakan domin wadanda yake muradin yayansa su aura shi Allah yake kawo musu (masu kudi) kasancewar yayan nasa kyawawa gasu da kwalliya da kuma ilimi domin yawanci Baffa suke yowa kuma Baffa kyakykyawan bafullacene.

Sai dai ta bangaren yayan mama ba haka lamarinsu ya kasance ba a gidan domin Faty tuni ta gama secondry har ta shiga school of Nursing (makarantar koyan aikin jinya) amma ko airport Baffa bai kaitaba bare saudia dan sauke farali. Da mama taji zafin abun amma daga baya saita barshi abisa ajizanci irin na Dan Adam, musamman data duba alkhairinsa na kaita saudia shekaru 3 abaya, sai ta goge laifin rashin kai Faty, dabeba. Baffa yana muqar San mama domin kuwa bambamci tsakanin mama da sauran matansa a bayyane yake, mama macece mai tsari kwalli tsafta iya girki Kullum cikin kwalliya take yatsunta basa rabuwa da kunshi hakan ya qarawa kyanta armashi da soyayyar miji Baffa a Kullum godewa Allah yake daya qaddara masa auran fadima ,domin shi mutum ne besan gayu da tsafta matansa kuma basu da lokacin wannan saina gasar haihuwa saboda gado.

Mama ta dade da samun shaidar karantun NCE a kwalejin horar da malamai ta tarayya (FCE), domin bayan kammala secondry school dinta a gidan galadima taci gaba da karatu bisa shawarar Adda halima wacce a lokacin take B ED (Bachelor in Education) a FCE din domin mijin Adda (Alh Abdul Aziz) dan bokone na qarshe saboda haka a hannunsa ta fara karatu tundaga yaqi da jahilci har takai matakin samun degree. Da farko Baffa yaso hana mama karatu, amma ta burkese masa dole ya yarda saboda son da yake mata da kuma tausayinta da yakeji na rashin qara samun haihuwa saboda yana sane Kullum cikin gorin haihuwa take a gidan, koda komawarta makaranta matan gidan basu wani damuba tunda ba sanin darajar ilimin sukayi ba, sai data kammala mijin Adda halima ya samo mata aiki a wata junior secondry school sannan suka nemi yiwa Baffa bore saboda baqin ciki da hassada, shi kuma yace duk wadda xatai karatu acikinsu kofa abude take kuma intagama da kansa zai sama mata aiki. Dole sukai shiru domin sunsan basu da tym din karatu.

Soyyar dake tsakanin Faty da Mimi baki bai iya fadarta, Faty yarinyace mai dattako da sanyin hali. Ta bangarenta bata hada San Mimi da komai ba, za a iya cewa tafisan Mimi da ita kanta, sai kaiwa Faty laifi ta haqura amma in kaiwa Mimi ta yini tana fushi dakai. Mafi yawan qawayenta sunan MARYAM garesu kuma tana qawance dasu ne ta dalilin alaqar sunansu da Mimi. Bata cika xama a gidan Baffa ba mafi yawan rayuwarta tana yinta ne a gidan mummy (Adda halima) dake rijiyar zaki. Mummy nada yaya 7 maza 3 mata 4. A cikin yayan mummy akwai saar Faty da kuma saar Mimi. Duk da gidan mummy gidane na yan gayu da daula hakan besa Mimi cika san xaman gidan ba duk kuwa da qaunar da mummy kewa Faty da Mimi, tasamu Faty dai amma Mimi Kullum tana jikin mama. Lokacin da mama ta tafi aikin haji 3yrs back dole tasaka Mimi xaman gidan mummy. Datai duba na tsanaki sai ta gano abunda yasaka Faty San xaman gidan, wato daddy. Mijin mummy mutum ne baisan iyalansa kuma ya sakar musu abunda sukaga dama shi sukeyi, (ba irin sakarwar da xata xama ba tarbiyya ba) Kullum yana cikinsu in dare yayi a hadu ayi karatu ya koya musu sannan a dasa hira har 10 pm sannan kowa ya nemi makwanci, hakan yajawo Faty San xaman cikinsu saboda inda ta taso tsangwama kawai suka Sani daga gurin yan uwansu wato yayan Baffa.

Abunda ke daurewa mama kai shine batasan dalilin da yasa anty da Umma suka tsani Mimi fiye da Faty ba, ita a ganinta in qiyayyace Faty ya kamata afi zafafawa ita fiye da Mimi, domin kuwa in kyau ne kaf iyalan gidan Baffa sai dai su xamo a bayan Faty domin babu wanda ya isa ya hada kafadarsa da Faty ta fannin kyau, amma memakon suyiwa Faty hassada kodan kyanta sai ya zamo Mimi akewa. Amma mamakin mama ya qarene a lokacin data fuskanci tsanar Mimi ta samo asaline fisa tsananin soyayyar da Maman da Faty kewa mimin, sai ya zamo anaiwa Mimi abune kodan mama taji haushi kota tanka musu. Hakan yasa ta gayyato dauriya ta qara akan wacce take da ita akan Mimi in anmata abu ta kau da kai, duk da ciwon da abun ke mata.


Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL 'AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}


Editing by
Mmn khairat 😍

πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }


Page 1⃣0⃣


Faty tai sallama dakin mama daga makaranta take, sanye da fararen kaya Sol (uniform) da dan hijab iyakacin gwiwar hannunta. Mama tana zaune kan sofa tana kallo Mimi na kwance itama kan sofa din ta tada kai da cinyar mama hannun mama cikin gashin mimin tana shafawa ahankali. Ta qaraso ta dafa Mimi sannan ta kalli mama, mama Mimi ba lfy? Ta tambaya arikice. Eh ciwon mara take tun safe tasha magani, amma har yanxu be saketa ba. Wayyo inji Faty ta janyo Mimi jikinta ta rungume tana mata sannu mimin ta gyada mata kai cike da galabaita. Ta maida mimin jikin mama ta dau kudi a jakarta tare da cewa ina xuwa ta fita. Can sai gata ta dawo da allura ta bude ta hada, ta kama mimin suka shiga dakinsu dake parlourn ta kwantar da ita a kan gadonsu sannan tai mata allurar. Ko minti biyar bataiba bacci ya dauketa. Taiyi sallah ta canja kaya tazo ta kwanta a bayan mimin bacci ya dauketa itama. Mama taji shirun yayi yawa ta shigo domin kawowa Faty abinci ta tarar dasu kwance kamar yadda suka saba Faty abaya Mimi agaba akan filo daya hannun Faty akan cikin Mimi yayin da mimin ta sa hannunta ta riqe hannun Faty. Wannan shine salon kwanciyar yayanta tun suna qanana wani sa in kuma su rungume juna suna baccin. Tai murmushi ta qarasa ta sumbacesu ta kashe musu fitila taja musu qofa.

Tun Faty na secondry skul masoya sukai mata ca kuma manyan masu kudi da yayan manyan mutane harda jinin sarauta, saΓ­ dai Baffa yace saita fara makaranta domin haka dokar gidan take, a bangaren Faty kuwa duk basa gabanta domin akwai tsumammiyar soyayyar quruciya aranta, duk kashe kudin da samari keyi akanta baya gabanta hasalima bata kulasu. Tanason Ahmad (yaron maqotansu wanda ke shiga gidansu gurin mama). Tun lokacin da Ahmad ya farga da manyan masu kudin dake kawowa Faty hari ya shiga tashin hankali ba kadan ba, domin ya mace akan Faty tun tana qanqanuwarta kuma da ita kadai yake tsara rayuwarsa, hakan yasa yaje ya sakawa mama kuka da roqarta ta bashi Faty indai baso ake ya kashe kansa ba. Maman ta bashi tabbaci in shaa Allah Faty bata da miji sai shi domin ta fahimci Faty ma tana qaunar Ahmad shi yasa bata kula kowa cikin manemanta.


Duk da Baffa yaso turjewa lokacin da aka gabatar masa da Ahmad a matsayin manemun Faty, domin be tabawa kamar Ahmad (talaka) auran yarsa ba, amma kafewar Faty da mama akan auran yasa dole ya sakko musamman da yaga irin dukiyar da mahaifin Ahmad din ya kawo a matsayin kudin neman aure. Domin a lokacin giyar asiri da matarsa ta dena tasiri akansa, ya kuma bawa Ahmad din gida makeke a NNDC sannan ya samar masa aiki saboda a lokacin ya gama karatunsa har yayi service. Hakan yasa Baffa yadan sakko. SaΓ­ dai sabanin yadda Baffa ya saba aurar da yayansa iyayensu matΓ‘ ko cokali basa siya shiyake komai kuma na bajinta. Amma akan Faty Set din gado kawai ya siya da Set din kujeru daya yaja bakin aljihunsa ya tsuke, abun ya bata mamaki kwarai ganin yadda yake banbanta yayansa da nata kamar ba yayan dan uwansa ba, amma sai ta danganta hakan da rashin San auran Ahmad din da yakeyi hakan yasa ta fitar da kudi maqudai da hadin gwiwar yan uwanta maza da Adda halima sukayi komai na bajinta suka yiwa Faty kayan daki domin na Baffa ma a dakin baqi aka xubasu, (dama dadin nema kenan) . Akayi aure amarya ta tare dakinta, da ike ance dan halak bai manta alkhairi Ahmad ya riqe Faty hannu bibbiyu ya zamo kamar bawa a gareta tana kammala karatu dayake maaikatan lfy basa rasa aiki, Baffa ya samo mata aiki kamar yadda yakeyiwa duk wacce ta gama karatu acikin yayansa, tana aiki a bangaren karbar haihuwa a AKTH wato aikin unguwar xoma (midwifery).



Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL 'AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}

Editing by
. Mmn khairat 😍

πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }


PAGE 1⃣1⃣




Kyakykyawar budurwace yar kimanin shekaru 25 da haihuwa, skin colour dinta kadai ya isa jawo hankalin duk wani lafiyayan namiji fadawa tarkonta bare aje ga dirinta wato structure cikakkiyar fuska gareta me dauke da πŸ‘€ darara farare kal, komai na fuskarta matsakaicine wato mastada 'a kamar yadda muka siffanta abaya, bakinta dananne kadan dauke da haqora masu kyau farare kal, wanda daka gani kasan ana ziyartar Dental clinic duk bayan wata 6 domin wankesu, koyaya ta motsa bakinta dimple dinta saiya bayyana. Duk da a ganin mutane MARYAM ba wata kyakykyawa bace compared to yar uwarta faty, ni dai anawa ganin MARYAM kyakykyawar gaskece, saboda ba lokaci daya xaka kalleta ka gano kyan nata ba, nooo sai ka nutsu sosai sannan xaka gano baiwar kyau da Allah ya azurta MARYAM dashi. Bayan haka kuma aiba fuskar mace kadai ake kalla ajikinta asan cewa kyakykyawa ce, da yake mafi yawan mutanenmu sunfi gane cewa farar fata itace kyau, wanda Sam ba haka abin yake ba. Hannayen ta dauke suke da wasu irin xara xaran yatsu wadanda aka tara musu farce (kumba) dai dai misali ma ana ba zaqo zaqo ba, gashi an qawatasu da jan lalle hannu da qafa, qafarta mai ban shawa awa yar dundubus kamar jikinta, yatsun qafarma kamar na hannaye suke zara zara. Gashin kanta wanda cikar budurci tasa ya qara haukata da tsaho da yawa ya kwanta luf saboda amfani da mayukan gyaran gashi irinsu MEGA GROWTH, kwanciyar nada nasaba da retouching da yake samu duk bayan 8 wks saboda shampo baya wuce sati 8 akan Mimi zai fita, fuskarta kawai inka kalla kasan tana gashi saboda gashin dayacika gaban goshin hadi da sajenta. MARYAM AL 'AMIN kenan (Mimi). Wacce yan watanin kadan baya ta kammala degree dinta a fannin sharia (law) a B U K.


AL 'AMARIN MARYAM ya farane tun daga kammala secondry dinta ko ince angane AL amarin ne alokacin da yakamata ace Mimi tana da manema (samari), duk wanda yaji ko yaga Mimi zaiyi mamaki kwarai ace bata da saurayi daya tilo koda na rage dare ne. Duk da cewa Mimi macece mai farin jinin mata a lokacin da take jami a, amma hakan yanada nasaba da kwakwalwa (brain) da Allah ya hore mata, hakan yasa tayi qawaye yayan manyan mutane da kuma dai dai ita yan middle class, wasu sular qawancensu saboda kamun kanta da gayu da kuma kwakwalwar da take dasu wasu kuma sunasan Mimi ne saboda haduwar jini. Sai dai a bangaren samari ba hakan take ba ga Mimi, domin xata iya cewa tunda takai xamanin yan matanci bata taba wata 1 cikakke da saurayi ba, to samarin ma duk gasunanne ma ana yarane qanana masu xaman banxa ko dalibai wanda suke qarqashin kulawar iyayensu balle abasu aure. In saurayi yazo wajen Mimi da wahalar gaske ya dawo inma ya dawo din baya wuce zuwa biyu xai dauke qafa dan kansa, kudan shekaru 6 kenan ana fama da wannan matsala, wadanda suka taso tare a yayan Baffa guda duk anmusu aure hardama yayan dangi na gurin uwa da uba, hakan ya janyo mata gori sosai ita da mama tun anayin abun cikin habaici har takai ana fitowa fili a gotanra musu, musamman inya kasance saurayi yayi musu hidima, (lokacin axumi ko toshin sallah) lamarin dake saka mimin qunci ta shige daki tayi ta kuka ba domin tana musu hassada ba saΓ­ dan ta rasa yadda zatasa kanta taji, tunda take bata tabacin ficikar namiji da sunan yana sonta ba to inama samarin suke??? Domin saita shafe shekara ko karen mota be leqo da nufin neman auranta ba. Ta rasa wani irin al amari ne wannan, ko a dangi anasamun masu goranta mata ta haryar shagube da cewa ah! Kedai Mimi kinqi aure kina jiran me kudi ko? To ai kwayi auran tare da yayanmu, abun takaicin da yawa daga masu goranta mata yan uwantane na jini kuma na jiki wanda ya kamata ace sun jajanta mata sai dai aduk lokacin da irin hakan ta kasance yaya Faty intana gurin takan kare mimin da cewa aure ai lokaci ne, ita Mimi nata lokacin baiyiba.

A bangaren mama AL AMARIN Mimi na mutuqar daure mata kai, domin Mimi macece Abida (mai yawan ibada) domin da ace ibada tana bada miji da Mimi bata rufe shekaru ashirin ba tare da aure ba, amma da yake aure AL 'AMARI ne na Allah sai gashi shiru, ta bangaren kyau, tsafta,gayu,nutsuwa da gwarjini badan ita ta haifi Mimi ba xata iya cewa ta dade bataga mace irin haka ba. Ta rasa a inda matsalar take amma ta tattara ta barwa ubangiji lamarinsa itadai kullum goshinta a qasa tana roqawa Mimi da ma masu irin matsalarta Allah ya kawo musu mafita. Duk da xuciyar mama tasha shawartar maman akan taje ta samu daya daga cikin yan uwanta maxa su hada mimin aure da yayansu kodan saboda matsin lambar da mimin ke fuskanta a gurin Baffa, amma abu daya ke taka mata burki wannan Abu kuwa shine : kada auren ya tabbata daga baya mijin ya wulaqanta Mimi saboda bashi ya nema ba, bashi ita akai, kuma dama ance matar shige bata daraja. Kuma inta xurfafa tunani sai taga da daya daga cikin yayan yan uwan nata sunso ai da sun furta San auran Mimi tunda duk SΓ‘ anin ta na bangaren jikokin mal SULAIMAN anmusu aure. Tana mutuqar tausayin Mimi, yarinyar bata da qoshin lfy amma tana da qarfin xuciya, indai Mimi na gida to mama aikinta xamane kawai ko kuma tayi dinkinta abunta sai taso xata taya Mimi da aikin girki kona shara amma duk aikin da mace ya kamata tayi a gidan miji Mimi ta daukewa mama hakan ya qara xafafa qiyayyar mimin a gurin Umma da Anty wato kishiyoyin mama matan Baffa, badan basu da yayan da xasuyi musu ba sai dai dan basu yiwa yayan tarbiyar temaka musu ba.


A bangaren Baffa kuwa shi babu ruwanshi domin aganinshi iya shegene ya hana Mimi fitar da mijin aure, saboda shi Allah bai taba jarrabashi da dadewar yaya agabansa ba babu aure da sun fara jami a kamar jira suke Allah yake kawo musu miji. Hakan yasa ya dau lamarin Mimi iya shege. " in har baki fitar da miji ba har kika kammala makaranta to tabbas xan cire hannuna daga kanki domin naga abun naki ya koma iskanci, neman xubarmun da mutunci kikeyi a unguwa gandamemiyar budurwa dake kina yawo a gari ko kunya bakiji tun kina xuwa auran sa anni kin koma xuwa na qanne." wannan shine fadan Baffa Kullum akan Mimi, wanda yau da gobe tasa mimin haddacewa kaf, kuma hakance ta faru domin bayan graduation din Mimi anyi sallah qarama ba dadewa kuma a wannan sallah Baffa ko sisi baibawa Mimi da sunan kudin kayan sallah ba lamarin da yayiwa matan gidan da yayansu dadi kwarai, kuma wannan alamarce ta nuna tabbas Baffa ya cire hannu akan Mimi kamar yadda ya alqawaranta, ko gaisheshi tai a ciki yake ammasawa shi a lallai yana fushi da ita kan abunda ba ita ta dorawa kanta ba (Allah sarki).


A yanxu haka da take shirin tafiya law school, a gidanma shirin aurar da mutum 3 biyu mata wadanda mimin ta girmesu da shekaru 3 sai namiji 1 yaya Ali, wanda ya kasance da na biyu a jerin yaya mazan gidan, domin dan Baffa namiji na farko (yaya jafar) wanda kuma ya kasance dan Umma yana kaduna yana aiki , kuma da shine yake nuna kamar yanason Mimi duk da bai furtaba amma daga baya maganar tabi ruwa tun bayan samun canjin gurin aiki daga kano xuwa kaduna. A duk lokacin da Baffa zai aurar da yaya mama ce keyi musu labulaye da xannuwan gado na alfarma a matsayin gudummmawa, wanda hakan ya zamewa Baffa jiki a tun bayan Koyan labulaye da xanin gado da mama tayi yayi bankwana da siyansu a harkar bikin yayansa, kawai in aure ya tashi xa a bata kalar kayan falon da xa ai wa amarya ita kuma zata zauna ta qure basirarta Ta tsantsara labulaye da bed sheets set uku uku ta bayar da sunan gudummawa kuma a karba bako godia kamar kudin suka bata kuma hakan bazaisa ana jimawa kadan aiwa yarta gorin aureba. Domin matan Baffa hamshaqan jahilai ne, jahilci irin wanda aka denashi saboda sauraran radio koda bakaje makaranta ba to yana existing a gidan tunbama suna fada akan yaya ba sai kaji kamar ka binne kanka, wannan yasa yayansu basu da tarbiyya ko kadan.

Gidansu Mimi gidane na kwalliya koma ince competition dinta ake da yake duk wacce ta gama karatu Baffa na samar mata aiki, hakan yasasu qarya daga yan matan gidan har wadanda ke gidan miji, yawancinsu suna da mota koma ince dukkansu wasu su suka siya wasu kuma mazajensu suka saya musu, acikinsu kuwa harda yaya Faty wacce ya Ahmad ya siya mata tun kafin ya siyawa kansa. Hakan yasa gidan ake gasar saka suttura da kwalliya da kuma shiga mota. Ta bangaren sutura Mimi kan sai hamdala tufa dai akwaita mama tayi mata, yaya Faty tayi mata, hajia kakarta ta wajen uwa wacce taci sunanta itama Kullum a hanyar yiwa takwararta sutura take , sannan mummy (Adda halima) yayar mama tayi mata sutura kam sai dai ta jira Mimi, ba Mimi ta jira ba. Hakan yasa koda Baffa bai mataba bata damuba.

Ana saura sati biyu bikin gidan ta tafi law school wanda yan gidan suka danganta haka da baqin ciki suka dunga sakin maganganu marasa dadi, domin Anty cewa tai ai dole aqirqiri tafiya law school domin da kunya a xauna to! za ayiwa yara aure ga gyatuma xaube ajabe agida.


Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL' AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ

πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }

Writing & story by
Rahma Muhammad {hajia}


Editing by
mmn khairat 😍



Page 1⃣2⃣
Yammacin ranar juma a ne rana gaf take da faduwa, a zaune akan tabar rila ta gidansu Mimi matasa ne guda biyu zaune akan tabarma suna jiran Baffa dake daga cikin sitroom din yana sallamar wasu baqi. Badaru sunan babban mai shekaru 33 sai Badamasi qaramin kenan me kimanin shekaru 30 a duniya, yayan abokin Baffa ne ya turosu gaida Baffa kamar yadda yake a al adar mahaifinsu (alh Inuwa) yakan turosu gaida abokin nasa aduk sanda ya kasance Badamasi na gari, saboda ba a garin kano yake aiki ba. Fararene tas kana ganinsu kaga fulani amma babban wato Badaru yafi Badamasi haske sai dai Badamasin yafishi jiki da kuma cikar zati irin ta maxa, sannan kuma yafishi alamar wayewa da kuma kwarjini, kodan hakan yanada nasaba da ilimin boko da Badamasin yafi Badaru oho.



Please Login or Register in order to submit comment