Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tafe take cike da gajiya saboda tafiyar da tayi daga Law skul (makarantar koyar da aikin lauya) xuwa gida sakamon samun hutu 1 wk da sukayi tazo gida domin yin hutun, sanye dake cikin suit baqaqe riga da skirt kamar yanda yake ga dokar makarantarsu, sai dan Baby hijab dake maqale a wuyanta kayan sun mata cif sun fito da surarta, qafarta sanye cikin rufaffen takalmi (cover shoe) baqi sai jakar goyo irinta dalibai itama baqa, ataqaice dai hijab dintane kawai fari a jikinta, jakar na goye a bayanta wacce ke dauke da yan kayan da xata iya buqata kamarsu brush, charger da kuma system din ta ( wato laptop) sai wayar dake riqe a hannunta. Duk da gajiyar da tayi hakan bai hana kyanta fitowa ba, babu kwalliya ko digo a fuskarta sai gashin gaban goshinta wanda baya iya rufuwa koda ta kwatanta rufeshi fatarta tayi tas ta kuma yin kyau saboda zama guri daya data samu. Mimin mama da Yaya Faty kenan .

Harta qaraso cikin rilar wacce xata sadata da sorayen gidansu bata kula da wanxuwar su Badaru a cikin gurin ba, wanda su kuma tunda ta tunkaro gidan suke kallonta harta shigo cikin rilar shigowarta yasa suka sauke ajiyar xuciya atare suka kuma shagala da kallonta ganin tana shirin shigewa cikin gidan yasa Badamasi tashi da hanxari ya qarasa inda take tare da cewa "Assalamu alaikum" . Yayin da Badaru ya kashingida ya cigaba da kallonta bako qiftawa. Bayan sun dan gaisa da Badamasi sama sama saboda ta qagu ta qarasa gida, ya kalleta a karo na barkatai sannan yace kamar daga makaranta kike ko? Taqanyi yaqe tace eh, ok wace skul kike? Ina Law skul ne dake nan jihar kano, ta bashi amsa a gajarce. Kai 😳 kice da Barrister nake tare, yasunan malamar? Maryam ta bashi amsa tana murmushi 😊. Barrister maryam gaskiya kin burgeni inason inga mace tayi karatu me xurfi haka. Well naga a gajiye kike ni sunana Badamasi wancan na kwance yayanane sunansa Badaru munxo gurin Babanki ne, kuma ina fata daga yanxu xumunci ya shiga tsakaninmu. Tace to nagode bari na qarasa, Ok to Mimi sai nazo karki manta sunan Badamasi da haka suka rabu ta shige gida.


Bayan ta kwana biyu da xuwa ne kuma ta shirya xuwa gidan Rashida da Rahana (wato amaren gidan da akai biki bayan batanan) ta Ware 10k da nufin ta bawa ko wacce 5k a cikinsu. Mama sam batazo xuwan Mimi gidan Rashida ba saboda Rashida (yar Anty jamila) tafi tsananta qiyayyar Mimi akan kowane mahaluqi dake gidan Baffa, qiyayyar Rashida ga Mimi a bayyane take kowa yasan Rashida ta tsani Mimi tsana ta qarshe, domin anshayin taro acikin gidan ko a wajen gidan Rashida tayiwa Mimi gorin aure (tun kafin ita Rashida tayi auren kenan) ko kuma ta duxgata agaban mutane ko qawatenta. Dan akwai lokacin da yaya Zainab yar ita Rashidan wato yar dakin Anty ta haihu ranar suna duk antaru anata aikin dambun shinkafa a gate din gidan Anty Zainab din anata hira kowa na tofa albarkacin bakinsa, hirar dai akan karatune da kuma wahalar samun aiki, Mimi tasa baki acikin hirar da cewa " ai aiki kam na wahala akasar nan indai baka da wanda kasani saika gama karatunma ka xama jobless Allah dai ya kyara qasarnan, sai kuwa tsulum Rashida tasa baki tare da cewa "ai koba aiki inkanada mashinshini sai kai auranka ka huta, damuwa akan aiki ai Sai irinki wadanda kukai kwantai kuka kai matakin bandaro (🀣🀣🀣🀣) ,ta fada tare da kwashewa da dariya. Kowa agurin yayi qim maganar ta bashi mamaki domin bata taba fitowa fili ta fadawa mimin magana ga da ga hakaba, maganar ta daki Mimi kuma tai mata ciwo saboda ganin yadda gurin yake acike da mutane daga na gida har qawayen Anty Zainab da dangin mijinta, ta rasa abunda ta tsarewa Rashida take mata wannan muguwar qiyayyar, duk da tasan cewa a yayan Baffa wadanda suke santa basu wuce 4 ba xuwa 5 amma ba wanda yake mata qiyayya kwatan kwacin wadda Rashida ke mata tasha goranta mata abunda ba ita ta dorawa kanta ba (jinkirin aure) hawaye ya wanke mata fuska ta kasa dago kanta ta kalli kowa a gurin saboda jitayi duk ta muzanta, qarar marin ta tajine ya dawo da ita daga tunanin da take, tai saurin dagowa taga wanda aka mara tai toxali da Rashida riqe da kunci gefe kuma ga yaya Faty tana huci da alama itace ta mari Rashida. Dai dai lokacin kuma Rashida ta yunquro cike da fitsara ta fara nuna Faty tana cewa akan wannan πŸ‘ˆπŸΌ ta nuna Mimi kika mareni? Dan ance tayi kwantai? Qarya nai batai kwantan bane? Shekararta nawa batai aure ba? Age mate dinta hardame yaya 4 amma ita ta gaza samun even tsayayyen saurayi saboda rashin kamun kai, duk wanda yaxo sai tabashi ya dana, ya za ai kuwa ya aureta? Kema Faty (yau ko yaya fatyn babu πŸ˜„) duk randa kika kuma taba fuskata da sunan duka wlh sai.. Adaidai lokacin Anty Adawiyya wacce akaje cikin gida aka fada mata abunda ke faruwa ta sharawa Rashida mari ta kuma kifa mata wani, sannan ta dora da xagin Rashida da yimata gargadi cikin kakkausan lafaxi kasancewarta Principal din makaranta kusan tasan takan iya shege (kusan principals ba wasa 😜 akwai displine) . Ko takansu Faty bata kuma bi ba taja hannun Mimi ta bude motarta dake cikin gate din tasaka mimin aciki sannan ta koma cikin gidan ta debo duk wani abu nata da taxo dashi da na mimin ta xuba a Mota Anty Adawiyya na kiranta ko juyawa bataiba bare ta nuna taji, duk kuwa da tsanin girmamawar da sukewa Anty Adawiyya sabida itace babbar yar Baffa (mai haquri bai iya fushi ba) amota suna tafe Faty kuka take kamar Mimi koma fiye da ita, fuskar tayi jajur kan Hancinta har Pink yake saboda kuka. Wannan shine dalilin da Mimi ta daina xuwa taro domin intaje sai anmata abunda akasan ranta zai baci koda cikin hirane, kuma shine dalinlin da yasa bata xauna bikin su Rashida ba kar atara mutane aci mata mutunci. Duk da Anty tasan da duk abunda Rashida kewa Mimi amma ko afuska bata tava nunawa Rashida tayi lefi ba.

Mimi nikam da xaki haqura da xuwa gidan Rashida duk abunda ki kai niyyar bata ki aika mata dashi sabida gudun fitina. Mimi tayi murmushi tare da dafa cinyar mama tace mama duk lalacewar Rashida duk qiyayyarta gareni yar uwata ce jininmu daya kuma innaje gidan Rahana banje gidan Rashida ba bakya ganin hakan xai xama abun magana? Mama tadan nisa kana tace eh hakane kam kuma ai duk tsiyarta tunda gidanta kikaje ai batayi miki ba, yawwa mama kingane kenan. Mimi ta fada. Mama ta kalli yar tata, sanye take da riga da skirt na atamafar nouvo dark blue me adon Yellow ta saka veil (mayafi) Yellow tasha daurinta me steps ta bude tsakiyar daurin inda gashinta da tai dunnot dashi ya fito, Mimi ta taba mama tace mama kodai infasa xuwa naga hankalinki bai kwantaba, Maman tai saurin cewa a a wlh uwata kyau kikayi shiyasa nake ta kallonki, Allah ya kiyaye hanya Allah ya sa asamon suruki. Mimin tayi murmushi ta sunkui da kai cike da kunya sannan ta fita.

Duk da ba wani good time suke da Rahana ba, amma ta karbeta da girmamawa ba kamar a gida ba da suka rainata dan batai aureba, hakan kuwa yayiwa mimin dadi sosai Rahana ta zagaya da ita taga gidan ya tsaru komai tsaf mijin nata nada yan canji (kudi) πŸ˜„ har ta kirashi ya sunkuya har qasa ya gaida ta, itama kuma taja girmanta ko 30mnt bataiba a gidan ta bata 5k taita godia.

A gidan Rashida kam to abun babu dadi domin Mimi na shigowa falon tahauyin wayar qarya tana cewa "kedai bari ai duk macen da batai aure da wuriba ta cuci kanta domin kinsan in mace ta wuce 25 yrs ance ita damai haihuwa goma duk daya namiji yake jinsu, nikam na dace inkinga yanda my Adams ya dunga tarairayata ba har pant wankemun yake yanxu hakama yaban kyautar Mota, abun Allah tana cikin wannan maganar ne wayarta tai qara alamar kira ya shigo, wanda hakan shiya fallasa wayar qaryar da take dan taciwa baiwar Allah mutunci, nan danan kuwa ta dibibice ta wayance da cewa wata wayar ta shigo. Suka gaisa tana wani daga kai ita adole madam saboda ta auri me kudi da gidan alfarma, batacewa mimin tashiga taga gidaba itama batai gigin leqa ko ina a gidan ba, tadai kira kukunsu tace ya kawo mimin pure wata (ruwan leda) ita kuma tace ya dakko mata gorar ruwan Faro, yaje ya kawo kamar yadda tace Mimi ta dauki ruwan tasha ita abunma dariya ya bata dan ita ba baquwar ruwan roba bace, ta bata kudin da ta kawo mata tare da cewa ta gaida me gidan inya dawo ta karbi kudin a yatsine ta watsasu kan centre table din dake dakin cike da ixxa tare da cewa xan fada masa kina gaidashi inban manta ba 😏 ko tashi bataiba balle ta raka mimin tana daganan tace ki gaida gida.

Ta tafi tana qissima kyan gidan Rashida a ranta, Allah me yadda yaso dama Rashida macece mesan qawa da fantamawa da kuma rayuwar kece raini gashi kuma Allah ya bata. Koda taje gida babu wanda ta fadawa abunda Rashidan tai mata sabida fadar bata da amfani, da haka ta qarasa kwanakin da xatai a gidan dagan tai gidan yaya Faty ta qarasa kwanakinta sukasha hirarsu ta xumunci, daga can ta koma skul cike da kewar yan uwanta danma ta kusa gamawa.


Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ




πŸ“FANTASTIC STARS WRITE
{F S W }

WRITING & STORY BY
rahma Muhammad {hajia}

Editing by
Maman khairat 😍


Page 1⃣3⃣

Alh Inuwa da Haj Kaltume wato mahaifan su Badaru yan asalin misaune da jahar bauchi harkar kasuwanci ta kawoshi garin kano, kuma harkar kasuwancin ce ta hadashi da Baffa (alh Buhari) yayan biyar biyu maxa Badaru sannan Badamasi sai mata guda 3 kuma sune qanana yanxu haka kowacce tai aure tana gidanta kasancewar ba ba karatu suke me xurfi ba iya secondry suke tsaya saboda alh inuwa bashi da wayewa irinta Baffa, haka ma kuma a fagen kasuwanci Baffa yayi masa fintunkau, duk da cewa shima dai baza a kirashi talaka ba yana sahun masu rufin asiri. Badaru sam baiyi wani karatun boko mai zurfiba domin yana gama secondry skul yayi nufin ajiye karatu sai dai kuma abbansu yanason yayansa maxa suyi karatu me xurfi, ala dole Badaru yayi applying a AMINU kano college of islamic (legal) tunda result dinsa baiyi kyan da xai shiga jamia ba kuma dama yafi qarfi a bangaren arabic saboda ko secondry dinsa ma arabic skul yayi. Ko da ya shiga legal din ba wani maida hankali yayi ba domin hankalinsa yafi karkata kan kasuwancin mahaifinsa da yake a kasuwar singa yana saida kayan masarufi. Da kyar da sudin goshi ya kammala diploma a legal saboda shi dama can karatun boko be dameshi ba ko kadan kuma yana daukan duk wanda ya zaqe da neman ilimin boko a matsayin Bayahude be bautawa turawa, awani bangaren ma yana yimasa kallo kafiri kafiri (waiyazubillah). A bangaren halitta farine tsamurmuri bashi da tsaho ko kadan sai yar qiba daya fara bayan kammala karatunsa, hakan yasa yayi tumbi kamar dan yaye πŸ˜„, ga dukkan alamu inyasamu Jin dadi anan kusa zaiyi qiba wacce xata qarawa xubin halittarsa muni sosai. Irin mutanenne masu zafin aqida da taurin kai da kuma kafewa akan abunda suke ganin dai dai ne koda kuwa sauran jamaa suna kallon abun a matsayin kuskure, a fuska bashi da muni duk da kuwa karan hancinsa da yaso ya shafe wanxuwar idanunsa πŸ‘€ a fuskar ma 'ana idanunsa qananane sosai ya tara qasumba har xuwa dan madaidaicin gemunsa. Saboda burkitaccen ra'ayin Badaru yasa bai cika abokai ba, saboda kallon kowa yake a matsayin bayahude daya shagala da bautar masu jajayen kunnuwa (turawa), sai dayake bahaushe yace ba a rasa nono a ruga hakan yasa Badaru bai rasa dai daikun abokai ba masu irin ra'ayinsa. A fagen soyayya kuwa ya dade da fadawa tarkon wata yarinya Nafeesa yarinyace batafi 16-17 years ba, dominshi a ra'ayinsa babu auran babba aciki yafison yara wacce zaiyi tarbiyyarta ya juyata san ransa, amma fa a ganinsa (ni kuwa nace banda irin yaran yanxu, domin sunfi manyan iya shege) 😊 yanason Nafee wajen shekararsu 2 tare da ita. Nafeesa kyakykyawar gaskece fara wanda hanken fatar tata yasamu tagomashi da bleaching (dama ance yanxu farare ne ke bleaching) yar siririya sosai ko ince shapeless, duk da cewa Badaru yafison yaga mace dirarriya wato 8 figure, amma a kan Nafeesa wannan raayi nasa ya kasa tasiri saboda san dayake mata. Itama a bangarenta babu kamar Badaru duk duniya 😳 ( wai ina ruwan kucaka πŸ˜‚) saboda hidimar da yake mata, biyayya take masa sau da qafa kamar mijin auranta ko ince kamar ubanta wanda hakan ya qara janyo mata soyayyar gurinsa. Qiriri Nafee ta tsaida karatu tun tana JS 3 saboda Badaru bayaso tai ilimin boko dan kartafi qarfinsa , iyayenta kuma suka xuba mata ido saboda kar suce lallai sai tayi Badaru ya daina yimata hidima ta koma xaman kashe pant ( xaman banxa da yawon bin gidajen maqota) kasancewar iyayen nata masu qaramin qarfi kwarai, tun shekarar data gabata Badaru ya kai kudin aure kuma akai musu engage ana jira ya gama ginin gidansa asaka rana kuma gaf yake da gama ginin.


A bangaren halayen Badamasi qanin Badaru kuwa xan iya kiran lamarin da bil akasi, domin duk da kasancewarsu uwa daya uba daya halayensu kishiyoyin junane, Badamasi yayi karatunsa har xuwa jamia inda ya jika burin mahaifinsu na xama cikakken likitan qashi kuma yasamu aiki a babban asibitin Dutse ta jahar jigawa, duk da suna kama da Badaru a fuska hakan be hana Badamasi cikar kamala da cikar halitta fiye da Badaruba shikam yana da tsaho fiye dana dan uwansa ga saje da ya tsayar kuma yake gyarashi, dan bokone sosai kallo daya inkai masa xaka iya gano hakan daga yanayin shigarsa, atsarinsa ya fison mace matashiya ba yarinya ba ba kuma over age ba (tsaka tsaki) kuma mai ilimin addini dana boko sannan wayayyiya wacce xata iya kula dashi, baiyi katarin samun macen data hada wannan abubuwa ba sai kuma yanxu daya ga Mimi, tundaga lokacin da suka hadu xuwa yau kimanin 5 wks kenan Kullum tana maqale a ransa da wata irin faduwar gaba da yake a duk lokacin daya tunata, ya rasa dalilin dayasa har yanxu ya kasa komawa gidan ko no wayarta ya karba dik da cewa kuwa takanas yake baro dutse duk sati da nufin xuwa gidansu amma yana zuwa saΓ­ xancen ya shiririce ko wani abun ya sha gabansa. Da yayi tunanin fara yiwa abba maganarta dan anemar masa auranta in da hali ma so yake a hada bikin dana Badaru, amma sai yaga gara ya fara neman soyayyarta yanda xasu gina gidansu cikin soyayya da fahimtar juna.


Yau asabar xaune suke a falo su 4 abba, Umma, Badaru da Badamasi. Sun gama breakfast kamar yadda suka saba, Badaru ya sunkuyar da kansa ya fuskanci iyayen nasa dake saman kujera sannan yace " Abba xuwan da mukai na qarshe gidan abokinka Alh Buhari naga wata yarinya a gidan ta kwantamun araina sosai, tunda na ganta nake addua kimanin wata 2 kenan nayi istikhara naji lamarinta ya kwantamun kwarai shine nace bara nai maka magana a neman izinin zuwa neman auranta kamar yadda addini ya tanada " iyayen sukai quri suna kallonsa, Badamasi dake gefe can akan kujera gabansa yayi wata irin muguwar faduwa wayar dake hannunsa ta subuce ta fado, abunda ya janyo hankalinsu kansa yai saurin daukar wayar tare da saita kansa kana ya kasa kunne yaji amsar da abba zai bashi, amma sai Umma ta riga Abban magana da cewa " Badaru 😳 kana da hankali kuwa? Ita kuma Nafeesan da ka kaiwa kudin aure take xaman jiranka kayi yaya da ita kenan? Ko fasa aurenta kayi??. Yayi qasa da kansa cikin sigar ladabin da yake yaudarar mutane dashi sannan yace " a a Umma ban fasa aurenta ba itama xan aureta inna kammala ginina tunda da sunanta nake ginin kuma itace ta tsara yadda takeso,,,,,.. Uwarka Badaru naci Uwarka nace ta fada tare da yimasa daquwa sannan ta dora da cewa an fada maka kowa mahaukacine irinka? A gidan uwarka xaka iya hada mata 2? . Abba dake zaune yana nazarin Badaru ya dakatar da ita da cewa ya isa haka Kaltume βœ‹πŸ½ shin ba namiji bane mata 4 aka halasta masa aure meye dan ya hada biyu lokaci daya ya aura?. Ya juya ga Badaru kai kana sonta ko? Yai saurin gyada kai, to abu yayi kyau dama nadade ina burin hada xuria da Alh Buhari ashe Allah ya rubuta hakan, ya fada yana murmushi. Sannan ya juya kan matar tasa tare da cewa ke kuma abunda nakeso dake kisawa abun albarka ai bazai kasa ruqe mace biyuba ke ko hudu zai iya riqewa in shaa Allah, sannan ya ciro waya daga aljihunsa yana cewa bara muji wacece acikin yayan na Buhari kakeso don alkhairi akewa hanzari.

Bangaren Badamasi kuwa yanaji abba ya goyi bayan mahangurbar da Badaru yayi masa ya saddaqar maryam ba matarsa bace yasan cewa xurfin ciki ya kaishi ya baro, abari ya huce shike kawo rabon wani, kuma yasan Badaru yafishi fada a gurin abba nesa ba kusa ba yasan koda shiya fara farta yanasob maryam sannan Badaru ya fada daga baya wlh abba Badaru zai nemawa auren, dan haka ya sulale yabar falon a lokacin ya hada komai nasa yayi ya kama hanyar Dutse da nufin xuwa yayi jinyar xuciyarsa ba tare da yayiwa kowa sallama ba dan bayason asan halin da yake ciki, ya bar abun a xuciyarsa dagashi sai ubangijin daya halicceshi.

Bayan gaishe gaishe da tambayar iyali tsakanin Baffa da abba ta cikin waya sannnan abba ya tambayeshi da cewa " ai dankane yaga yarinyar gurinka yakeso, to kasan ni bana gane yaran naka sabida suna da yawa, Baffa yadan nisa kadan sannan yace " eh to yanxu dai ai ba yan mata a gidan duk na aurarsu yaran da suka rage yanxu qananane basufi shekaru 9-10 ba. Abba yace a wannan dai inaga babba ce dan har yana cewa bayaso auran ya dau lokaci, toh? Cewar Baffa kuma a gidana ya ganta? Eh tabbas yace nan yaga ta shiga da alama ma wai aikin jarida take dan ya ganta da baqaqen kaya. Baffa ya chafe maganar da cewa auhoooo πŸ€” MARYAM ce ai yar gurin Aminu qaninace da ya rasu, tana can makarantar Horas da lauyoyi amma befi sati 6 ya rage ta kammala ba. Wanne acikin yaran yake sonta? Abba ya amsa da cewa Badaru ne, to mashaallah abun yayimun dadi wlh, aikai mai aurar da MARYAM ne saboda haka kawai inkun shirya kukawo dukiyar aure. Lar lah lah Alh haka da sauri inji abba yana murmushin Jin dadi, Baffa ya amsa masa da tome xa a jira tunda ansan asali aishine dama abun nema a aure. To shikenan nagode da wannan karamci kuma in shaa Allah xaka jini kafin muxo. Da haka sukai sallama suka kashe wayar.


Mrs Muhammad 😊[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 1⃣7⃣

Dedicated to
Maryam Baita


Tun fauxa qawar Mimi, na jiran xuwan tawagar ango da sunan siyan baki har ta gaji da xaman jiran. Wajen 8:30 pm tai shirin tafiya, ta miqe ta dau mayafinta dake gefen Mimi ta yafa, tace "qawata nikam xan tafi tunda har yanxu angon be qaraso ba, kuma kinga layin naku da nisa daga titi kar dare ya qarayi inrasa abun hawa".

Mimi ta marairaice cikin zubda kwallah πŸ˜ͺ tace fauxa kema tafiya xaki kibarni kamar yadda kowa ya tafi yabarni? Fauxa qawancenmu yace haka?.

Ta xauna gefen Mimi tare da cewa qawata haquri xakiyi, kinsan nabar Aslam a gida gurin mama, kuma nasan yanxu yanacan yana kuka, indai har Baba ya dawo ya datta bananan nabarshi yana rigima fada xaimun. Wlh dana taho dashi sai najira xuwan su Badaru inyaso sa maidani gida.

Ta riqe hannun mimin sannan tace "qawata kiyi haquri komai yayi farko xaiyi qarshe, ikon Allah ne kawai bashi da farko bashi da qarshe, Allah ya sa alkhairi acikin aurenki. Kimaida AL AMARINKI gurin ubangiji, in shaa Allahu zakiyi alfahari da wannan aure, karki bari rashin son mijinki ya taba biyayyarki gareshi har irin tawa ta sameki (mutuwar aure), bana fatan haka Mimi. Ki tuna ba duk abunda kakeso kake samu ba. Kiyi biyayya, kiyi ibada, abu na qarshe da xan fada miki shine kada ki sake ki zauna da yunwa ". Na sanki Jan wuya ce ke wurin ibada, to qira akai".

Tana kaiwa nan ta juya ta tafi ita kuka Mimi kuka.

Tun bayan tafiyar fauxa take xaune a tsorace, koya taji motsi sai ta firgita duk kuwa da cewa ita din ba gwanar tsoro bace, amma yau sai tasami kanta cikin mugun jin tsoro, ji take kamar ta tashi ta xura da gudu, kasancewar ba wuta a unguwar sai chaja aka kunna.

Batasan iya lokacin data dauka a haka ba, sai ji tayi ana bude kofar gidan ta waje, alamar me gidanne. Shigowarsa parlon ya xowa Mimi da wata irin faduwar gaba matsananciya, gumi ya dunga karyo mata.

Sam bazata iya tantance ko yayi sallama ko beyi ba, domin ko yayi bataji ba balle ta amsa. Direct yayo kanta tare da cire mayafin data rufe kanta dashi yana huci kamar a fagen daga (filin yaqi) duk da a tsorace dake da abunda yayi hakan baisa ta motsa ba, ya qare mata kallo tare da hadiye wani mugun yawu duk da ramar da tayi hakan bai hana surarta bayyana ba, ya dure kallon nasa akan fuskarta ya qura mata ido yana mata kallon qurullah, abunda bai taba lura tana dashi ba kafin ya aureta yau ya ganshi wato tabon sallah take goshinta da danannen bakinta, sannan kwantancen gashin dake gaban goshinta, hakan yasa ya cire mata dan kwalin kanta, kyakykyawan gashin kanta dashi sampoo yake tashin qamshin mega growth ya bayyana, " SUBHANALLAH " ya furta afili sannan a zuciyarsa yace dama anasamun macen bahaushe da irin wannan gashin? Ya shafa

Please Login or Register in order to submit comment