Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan karta qara yimata haka anan gaba tace "yaya Faty ki tashi kije gidanki, nasan dake na naimi yaya Ahmad ban nemeki ba kuma da nasan ke zai turo da ban nemi ya taimakamun ba" duk tana wannan maganar ne a juye (ta bawa Faty baya).


Parlon yayi tsit na tsawon 5 minutes. Mimi da taji shirun yayi yawa ta juyo a zatonta Faty tayi fushi ta tafi. Amma me? Sai tayi arba da Faty tana tsugune tana hawaye.


Ta qura fatyn ido itama tana hawayen, ita kuwa Faty ganin yadda Mimi ta lalace ta kade yasa ta qara sautin kukanta cike da nadamar rashin xuwa taga lfyr mimin.


Cikin kuma Faty tace "#FATIMARYAM# bazasu taba rabuwa ba, bazasuyi fushi da junansu ba, matsalar Faty ta Maryam ce, matsalar maryam ta Faty ce. Mimi wannan shine alwashin mama akanmu, karki karya alqawarinnan tun yanxu πŸ˜ͺ"



Mimi najin haka ta taho da rarrafe domin babu qarfin tashi, taje ta rungume Faty. Faty ma qanqame Mimi tayi kamar xata maidata ciki.


Suka dunga a jiyar xuciya xuciya a tare, Faty ta dunga sharewa Mimi hawayenta sannan ta kwantar da Mimi a qirjinta kamar yarinya tana shafa kanta alamar lallashi.


Badaru yana tsaye, yana kallon dramar su, kamar masu shirin film. Aransa yace dama akwai irin wannan soyayyar yan uwantaka? Lallai yarannan suna san junansu.


Ya juya da nufin komawa daki, motsinsa ya sanar dasu wanxuwarsa a gurin, yayi saurin cewa da Faty "haj Faty barka da xuwa, ina wuni? " dan haka kawai yaji ta masa kwarjini duk da cewa xai girmeta da kadan ko kuma suyi sa anni.


Ta kalleshi cikin tsana, sannan ta kalli yar uwarta dake kwance kan cinyarta. Yayi tas yayi qiba yayin da Mimi ta tsummace da qare kamar me jinyar shekaru da yawa. Ta amsa gaisuwarsa sannan ta dora da cewa " ranka ya dade ya akai akabar Mimi ciwo yaci qarfinta haka? Ciwon Mimi fa ciwone me hadarin gaske kuma yana da alaqa da xuciya, duk sanda ciwonta ya tashi inbai samu kulawar gaggawa ba hakan kan iya jawowa arasa rai. Kuma babbar abunda ke motsa lalurar Mimi bacin rai"


Yayi wuqi wuqi, yana kame kame da bawa Faty haquri. Tace to gobe da sassafe xanxo in kaita asibiti dan naga abun yayi worst, xansa ayi mata booking tun yanxu.


Cikin kunya yace "to Allah ya kaimu, Allah ya bata lfy kuma za a kiyaye in shaa Allahu"


Ganin magariba ta kawo kai yasa Faty tai nufin tafiya, ta karanci matsalar Mimi harda yunwa aciki. Sannan ko zafin wannan gidan ya isa ya tashi ciwon Mimi.


Mimi kamar tabi Faty takeji, kuma ganin yar uwarta da daidaitawarsu yasa tasamu rangwamen ciwon. Faty ta lallabata da cewa tayi haquri gobe da asuba xataxo kuma, tayi wanka ta shirya kafin taxo din.



Fitar Faty befi da minti 15 ba wani yaro ya shigo da leda yace gashi inji wata mata fara a mota tace abawa maryam. Ta karba ta bude taga freshyoo me sanyi qarara guda uku.


Atake ta bude ta shanye daya, sanyin ya ratsata ta kuma bude wani tasha rabi sannan taji ta qoshi. Tayi hamdala tare da cewa "Allah sarki dan uwa rabin jiki"


Da xumudi ta kwana, saboda tana murna gobe xata fita bayan wata biyu a kulle a gida.


Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣3⃣

Dedicated to
Maryam Baita

Asubar fari Faty ta gama shirinta na tafiya, har breakfast ta hadawa Mimi. Taiwa Ahmad sallama ya kawo kudi ya bata da nufin taiwa Mimi amfani dasu a asibiti.


5:30 AM agidan Mimi tai mata, ta samu Mimi tayi wanka amma tana zaune bakin gado bata shirya ba saboda jikin ya motsa mata. Suka gaisa da Badaru ta shiga cikin daki.


Haka ta dunga bincika drawern Mimi da nufin dubo mata kayan da zata saka, domin duk kayan sun yamutse (anyi wanki babu guga). Gashi kayan sai qarnin sabulun wanki suke. Dakyar ta samowa Mimi zani da dankwalin atamfar dutch wax (holland) da shirt (domin rigar atamfar tayi mata yawa saboda ramar da tayi) ta saka. Ta dakko humra ta zazzga ta murxa a jikinta (domin humrar kadai take dashi, turarurrukanta tuni sun qare, dan bata saka turare daya tafi gane ta hada kaloli da yawa. Kuma da Badaru suka hadu suka qarar tunda shikam baya siyan turare ya saka sai da yaga Mimi dashi ya tayata suka qarar anga banxa 🀣) ta dan gyara fuskarta, ta hade kitson kanta tasa ribbon. Ta yafa mayafi kumar suka fito.

Suka tadda Badaru a parlour ya dakko 500 ya bawa Mimi tare da cewa "ga wannan ku riqe ko za'a buqaci wani abun" Faty tai saurin cewa "no bashshi babu abunda xai gagara da ixinin Allah" .


Bakwai a AKTH (Aminu kano teaching hospital) tai musu inda Faty ke aiki. koda likita yaxo ita ya fara gani saboda sanayya da kuma booking din da sukai.


Suka gaisa da Faty likitan mai barkwanci, yana duban Mimi ya duba file dinta dake gabansa yace " fatima kina da wannan African queen din shine baki bani na aura ba? " Faty tai murmushi tace "Dr babu rabone shiyasa baku taba haduwa ba, amma Mimi ai tana xuwa nan"


Ya duba record din ciwon Mimi, yace "maryam meyasa kike sa damuwa a ranki? Bakisan ciwonki bayason damuwa ba? ". Mimi dai shiru tai masa kanta na qasa.


Ya rubuta allura yace Faty taje ta karbo yanxu a pharmacy ta kawo masa xai mata. Allurar 9k ce saboda haka ya rubuta note, dan acikin albashinsa xa a cire. Faty ta dunga yi masa godiyar karamcin da yayi mata, yace bakomi ai zaman tare ne ya kawo.


Bayan fitarta, nasiha ya dunga yiwa Mimi cikin hikima. Duk cewa baisan matsalarta ba. Suna haka Faty ta dawo, ya fasa allurar ya nemi jijiyar hannu yayi mata, sannan ya buqaci ta zauna ta huta xuwa 10 minute saboda allurar nada qarfi.



Cikin qanqanin lokaci, Mimi taji nauyin da qirjinta yayi ya sauka, numfashinta ya koma fita normal. Ta dago ta dubi likitan tace "nagode Allah ya biyaka da gidan aljannah naji dadi". Yayi murmushi yawwa maryam nagode da addu a Allah ya qara sauqi, suka dauki takardar magunguna suka fita.


Suka tsaya cikin asibitin suka sai magunguna. Sannan Faty ta tsaya ATM ta ciri kudi suka tafi. Ta miqawa Mimi travelling mug cike da tea murtuk dashi (hadin kauri inji Mal kabiru dadin kowa πŸ˜‚) tace shanye. Mimi ba musu ta shanye domin tana ganin shayin yawunta ya tsinke domin rabonta da shayi da madara tun madarar amarci. Bayan ta gama sha ta miqa mata food warmer cike da soyayyar doya da kwai da miyar qoda a gefe. Tace "kici ki qoshi dan ba gida xan
kaiki ba". Taci doyar ta qoshi nak, atake wata nutsuwa ta saukar mata. Lallai ta yarda matsalarta harda yunwa a ciki.


Direct zoo road ta tsaya inda Mimi keyin saloon, ta ajeta tace a gyara gashinta a wanke mata qafa, sannan ta tafi tace xataje ta dawo.


Suka taya Mimi ta tsefe kan, aka shamfe shi, sannan aka dora da steaming. Akai mata gyaran fuska (cire gashin fuska) ba abunda bai buqatar gyara, nan da nan saiga Mimi tayi tar fuskar ta washe.


Ana wanke mata qafa Faty ta dawo, ana gamawa ta biya kudin suka tafi. Direct shoprite suka nufa, suka fara da gurin electronics Faty ta sayi reachargable fan (fankan da akewa chaji). Sannan suka shiga gurin provision tace Mimi ta dau duk abunda take buqata, dake Mimi tasan ko bata dauka ba Faty fada xatai mata shiyasa tadau duk abunda tasan tana da buqatarsu, kamarsu : mayan robobin madara da milo, omo, sugar, pads, toothpaste, cookies da sauran kayan amfanin gida. Faty ta qara mata da wasu kayan shayin irin na sachet da catoon din cake da caton din freshyo da su malt da exotic duk catons. Ta kalli Faty cikin soyayyar yan uwantaka tace "ya Faty basu yawa ba kuwa? Karba ki dorawa kanki wahala" ta kalleta tace "Mimi yanxu dan na miki abu ya xama wahala kenan? Yaushe muka fara haka dake? Ta dafa kafadarta tace, Mimi ina qaunarki mu kadai mama ta haifa, ina roqon Allah indai xai bani abunda bazan Mora miki ba kada ya bani shi ko menene" Mimi tai saurin fadawa jikin Faty suka qanqame juna. Kudi sosai ta biya na siyayyar da sukai, sannan suka dau hanya.


Lokacin da suka isa gidan Faty qarfe biyun rana, adaddafe tayi sallah sabida yunwa dake damunta. Tana idar da sallah taje kan dining table, ta cika plate da jellof din macaroni da hadin salad tayi tai qat ta dora da pepper soup. Duk abunda take Faty na ankare da ita, tabbas Badaru yana yiwa Mimi horon yunwa domin ada Mimi bata cikin jerin mata masu cin abinci, amma yanxu har mamakin cin da Mimi tayi take.


Abincin yana fada mata ta nutse akan royal bed din Faty wanda yasha shinfidu tausasa na alfarma, sanyin AC na ratsata tayi bacci me dadin gaske.

Bata farka ba sai 5:16 pm tayi salati, tare da miqa. A gaggauce ta shiga bandaki ganin lokacin sallah ya qure. Sai dai tana cire pant dinta da nufin yin wanka ta tarar period dinta yaxo, duk kuwa da cewa lokacinta yayi har ya wuce batai ba. Tai mamakin xuwan period din ba tare da ciwon mara ba, ko hakan yana nasaba da allurar da akai mata oho? Ta dakko shaving cream (veet) ta shafa a jikinta ta qalqale gashin. Ta salla wankanta da mayukan wanka da subulai, ta dauki sabon pant a drawer ta manna pad ta saka. Ta gyare jikinta da mayuka da perfumes masu sanyin qamshi, ta dauki doguwar rigar atamfa a kayan Faty ta saka. Tai mata cif sakamakon ramar da tayi, ta danyi simple make up ta fito tas da ita.


Ta iske Faty da Ahmad da yaran zaune a parlour suna kallon drama (madhubala) a mbcbollywood. Tace "ya Faty har lokaci yaja haka baki tasheni ba? Tace "sry Mimi shigata biyu da nufin in tasheki saina tarar baccin ya muki dadi shiyasa na gyaleki. Ta samu guri kusa da Faty ta zauna, suka gaisa da Ahmad, ya jajanta mata jikin sannan ya zarce da yi mata nasiha. Dan har ga Allah yanason Mimi ganinta yake kamar uwa daya uba daya suke, tunda shi bashi da yan uwa.


Taje fridge ta dakko robar ice cream ta dawo ta xauna tanasha suna hira. Ji take kamar karta tafi dan xaman yayi mata dadi. Ahmad ya kalli Faty yace, tashi ki kaita gida kada muyi rashin hankali. Faty ta yunqura tare da miqawa Mimi wata leda tace kinga a siyayyar da mukai kin manta baki dauki masuka da turare ba shine na koma na siyo miki" Mimi ta leqa ledar taga muyakan da take amfani dasu ne cocoa butter (palmers) Set dinsa har sabulunsa sai turaren da take amfani dashi da sure na feshi da sauran spray. Ta dunga godia.


Sai da Ahmad ya bata 10k, sannan ya jaddada mata duk sanda take buqatar taimako ta fada, kada ta qara zama ciwo yaci jikinta haka. Saida Ahmad ya temaka suka saka kayan a mota saboda kayan da yawa. Har sun fara tafiya Faty ta tuna da fankar da tasa chaji, ta dawo ta dauka. Suna tafiya suna hira cikin nishadi ta dauki jakar Mimi ta saka mata ledar magungunan da suka siya tare da kudi sannan ta qara da cewa gashinan ki kula, ki rabu da namiji ki dainasa baqin cikinsa a ranki, lfy tafi komai kuma shi kansa inbaki da lfy bazai zauna dake ba, so dat ki lallaba lfyarki.


Suka tsaya yahuxa suya dake kabuga ta sai mata kaza da furar habib. Kafin suje gida anyi sallar magruba saboda sun tarar da hold up.


Suna gama shiga da kayan Faty ta juya gida. Mimi da bata sallah xataiba da kimtsa kayan takai kowanne muhallin daya dace. Tana zaune tana lazimi aka kira sallar isha ta tashi tasa kayan bacci dan jikinta fes yake bata buqatar wanka. Bata damu da dawowar Badaru ba domin ya kunna inji, ta kunna fankarta wacce tai chaji full. Iskar fankar na kada ta tana danna waya (chating) a zuciyarta cewa take "Allah ya sakawa yaya Faty da alkhairi badan taimakonta ba da tuni ina zaune cikin zafi.


Takwas nayi ta balli maganinta tasha dama tana timing. Ta janyo kazarta ta bude ta fara ci da bisimillah. Qarar injin da taji ya tabbatar mata da dawowar Badaru, ya shigo dakin yayi tozali da Mimi. Idonsa fes akanta saboda hasken wutar lantarki, tayi masa kyau ainun kamar sake masa ita akai.


Yayi saurin qarasawa gabanta tare da cewa "maryam sauki ne ya samu haka da wuri? Sannu" ta danyi murmushi tare da gaisheshi. Ya amsa idonsa na kan ledar gabanta wanda qamshin kazar ya cika dakin, yace " harda hidima haka? " ta amsa da cewa "eh yaya Faty ce tasaimun da wannan fankar (ta nuna masa fankar) yace " to madallah haj Faty kenan bataso kudi su zauna lfy" (kuji banxa🀣)


Ba kunya ya tayata suka cinye kazar sukasha furar, lamarin da yayiwa Mimi dadi. Domin yaune rana ta farko da suka taba cin abinci kwano daya da Badaru.


Yana ta kallon Mimi wai ta burgeshi qarshe, ya kalli qafarta yar dundubus da ita har tafi jikinta haske yatsunta kansu abun kallone be taba lura Mimi takai haka ba sai yau (dama ya xa ai kasani? Wahalar gidanka tasa tayi kaushi) ya ruqo hannunta yana murxawa cikin shauqi "maryam tashi muyi shirin kwanciya" ya fada yana mai qura mata ido. Azuciyarta tai masa dariyar mugunta, saboda tasan bata da tsarki.


Ba musu ta miqe taje tai brush, shima ganin tayi yaje yayi amma ba batun wanka duk kuwa da tsamin ranar da yake. Ta feshe jikinta da turare ta kwanta hankalita kwance yau ba kawo farmaki 😜.


Tayi mamaki kwarai da taji ya kashe inji, ya shigo dakin yana me cewa tunda ga fanka ai sai man injin ya huta. Yana hawa gadon ya kamata ya rungume yana shafar gashin kanta yana cewa "maryam kinada shiga rai, komai naki me kyau ne" tadan motsa bakinta cikin sigar murmushi har dimple dinta ya lotsa. Lamarin da Badaru yaji ba abunda yake muradi illah ya hada bakinsa da nata. Amma yasan bazata yadda ba shiyasa beyi yunqurun hakan ba, domin yau hakanan yaji bayason batawa maryam rai.


Ganin abun nasa yana nisa yasa tace masa bata da tsarki, atake ya saki wani mugun tsaki tare da tureta daga Jikinsa, ya koma gefe ya kwanta. Dama hakan take jira dan haka ta gyara kwanciyarta ta maida fankar dai dai saitinta tai adduar kwanciya bacci.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣4⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)


Tasamu canjin rayuwa saboda taimakon Faty, ta rabu da matsalar zafi saboda fankar da Faty ta sai mata. Koda babu wuta takan bada fankar da 50 naira akai mata wani company dake bayan gidanta kadan mai gadin gurin ya karbi hamsin din yasamata caji, saboda company ne basa rabo da wuta.


Sai dai da yake rayuwa indai kai imani baka rasa jarrabawar ubangiji, sai wata sabuwar matsalar da bullo mata. Matsalar kuwa itace; kawo abokai da Badaru ya tsiriyi cikin gidan saboda yaga cimar gidansa ta canja (ansamu mai dadi).


Ba kawo abokan nasa ne problem dinba ko kuma abunda zasuci, cin mutunci da toxarcin da Badaru keyi mata agaban abokan nasa shine babbar matsalar.


Sau tari zai cika gidan da abokansa duk kuwa da qanqantar gidan, wanda hakan ke hanata sakewa sai dai ta takure kanta adaki. In fita parlour ta kamata ko duba girki sai dai ta saka hijabi, har mamakin inda ilimin addininsa yake take domin babu addini sam acikin abunda yake, kodan ya takura mata yake hakan? Sannan bayan tayi hidima dasu da jikinta da aljihunta (domin babu ko sisinsa aciki) sai kuma ya dunga zaburarta yana daka mata tsawa agabansu, a qoqarinsa na nunawa abokansa cewa ita din bata isa komai ba.


Yauma hakace ta kasance, domin tare suka shigo da wani abokinsa sani around 5;30 pm. Suka taddata zaune parlour ta tasa fanka agaba tana shan iska, a xuciyarta bata gajiya da yiwa wacce ta sai mata fankar adduar alkhairi (ya Faty)


Tai saurin miqewa ta shige daki da nufin suturta jikinta, domin shimice kawai a jikin nata. "kinaji ana sallama dan rainin hankali baxaki amsaba" cewar Badaru. Sani abokinsa yayi saurin tareshi da cewa "bakaga hijabi zata dakko ba, laifinane dana shigo kai tsaye ban tunanin halin da xan taddata ba" ta fito sanye da jihab me hannu tana cewa "sannunku da xuwa" ta gaishe da Sani, sannan ta nufi kitchen ta qara sanwar abinci dan ganin baqo, ta debo musu ruwa da kwalin exotic ta dora akan tray ta glass cups ta kawo ta koma daki ta zauna.


Tananan zaune tana yan danne dannen waya taji xuwan wasu abokan nasa har su 3 domin taji ya ambaci sunayensu. A xuciyarta tace yau kuma anan xa ai mana zaman majalisar kenan.


Ta tashi domin ta duba abincin data dora, ta gaishesu ta wuce kitchen. Ta gama komai ta maida miyar kan gas domin ta qara dumamata ta jiyo Badaru na kwala mata kira, ta fito parlour ta dan durqusa gefensa "gani" ya dubeta yana wani daga hanci yace " ke wace irin mahaukaciyar mace ce mara tsari? Bakiga nayi baqi bane? Ko sai nace ki qaro wasu kofunan da lemon? Banason dabbanci." Ba tare da tace komai ba ta miqe taje ta kawo wani kwalin lemon da kofuna ta ajiye, tana shirin juyawa yace " abincin ma sai nace ki kawo ko? To karki kawo" tai saurin xuba abincin a warmers har tana qonewa saboda kar wani cin mutuncin ya biyo baya. Domin tana jiwo shewar abokan nasa, suna yaba masa yadda yake tafi da ita. Har wani a cikinsu wanda bazata iya gane kowaye ba yana cewa "da kyau mutumina haka akeson mutum ya xama jan wuya a gidansa"



Ta hada musu komai na abincin a gabansu, sai da ta tabbatar ta hada komai sannan ta nufi daki. Badaru yayi saurin katseta da cewa "waye bawan gidanku anan dazai zuba musu? " ta duqa a takure take saboda kallon da wasu acikinsu suke mata, xata fara xubawa Sani yayi saurin katseta da cewa "a a jeki maryam mungode kowa zai xuba nasa" dan ya lura a kunyace takeyin komai.


Badaru yace "a a ta xubawa kowa umarnina ne, ni naga damar haka. Tana gama xubawa ta miqe ta shige daki. Sani ya dubeshi ransa adan bace " ka daina haka Badaru, wannan yarinyar kyautace Allah ya baka ka riqeta da amana ku zauna lfy. Yawanci yaran yanxu basu cika bin miji haka ba, bare ita da take da xurfin ilimi" Badaru ya daga murya, domin yanaso Mimi ta jiyo abunda zaice "yo ni ina ruwana da ilimin mutum, ko parpesa ce ita bai dameni ba domin miji ta rasa na taimaka mata na aureta, inba dan nidinba da tuni tanacan a jabe gidan ubanta"




Yayi sa a kuwa domin duk maganar da suke akan kunnen mimin sukayi saboda tana da ji sosai, kuma dakin bashi da xurfi. Hawaye ya wanke mata fuska, lallai yau wulaqancin na Badaru yafi na koyaushe. Muryar daya daga cikinsu ta katse mata tunani inda yake cewa "au wai kana nufin tana da ilimi? " Badaru ya bashi amsa da cewa "degree ne da ita akan fannin sharia" wanda yayi tambayar yace "Tab ai wlh gwanda daka riqe mata wuta daka sake mata rainaka zatayi musamman intasan tafika ilimi mata yan boko mugayen yan rainin wayo ne. Kai kuma sani da kake wani xance ai mata xuma ne da wuta ake cinsu" Sani ya balla masa harara yace "inkasan ba shawarar arziqi zaka bayar ba ka daina xuga xugagge yana ciwa yar mutane mutunci"



Badaru yayi saurin tareshi cikin hargowa "kaga sani ya isa, ni ba wani wanda yake zugani haka nayi niyyar tafi da gidana kuma haka nakeyi. Intaga xata iya xama dani a haka ta zauna, in kuma bazata iya ba sai in mata saki daya taje gidan nasu ta dandana xama taji. Ai tasan rufa mata asiri nayi, kaf gidansu ita kadaice budurwar data rage. Sannan tace xata kawomun wani fi ili? Bokon banxa bokon wofi meyasa bokon nata be bata mijin aure ba. Wlh ko shugabar qasa ce ita dole ta bini yadda nakeso intaqi ga hanya nan. Nasan kina jina MARYAM in bazaki iyaba kixo ki tafi gidan ubanki."


Duk yanda taso danne xuciyarta abun ya gagara kuka take wurjanjan, batasan yadda akaiba sai ganinta tayi a parlourn adai dai lokacin da yake cewa "ai kinsan yadda kika sha wuya kika zaunu kafin Allah ya kawo miki ni na aureki, ki qoqari ki kashe auran kina budurwa ma kin rasa miji bare kina BAZAWARA."




Sai a lokacin ya ankara da wanxuwarta a parlourn, ya kalli idonta da fuskarta gabansa yayi mugun faduwa domin bai taba ganinta cikin wannan yanayin ba duk abunda yake mata.



Sani yayi saurin shan gabanta ganin ta nufi qofar fita, a qoqarinsa na dai daitawa, yace MARYAM Dan Allah dan darajar iyayenki kiyi haquri kar fita. Ta tsaya cak! Badaru dake gefe ya saukewa boyayyar ajiyar xuciya ganin ta tsaya.



Sani yace Badaru, beye lefin yarinyar nan? Saboda ni kayi haka? Daga gaya maka gaskiya xaka ci mata mutunci haka? Lefin me tayi maka?


Mimi ta matso kusa dashi ta kalleshi, yai saurin yin qasa da kansa. Tace cikin nutsuwa da qarfin zuciya " kayi haquri qaddarace ta hadamu, amma karka manta kai ka ganni kace kanaso ba talla aka kawo maka niba. Kuma tabbas miji na rasa shiyasa na aureka, inba dan haka ba ai babu wacce xataso xama da namiji irinka. Kuma da Allah ya hanani miji daga baya ai yabani kai? To haka nake sakaran duk renda Allah ya sa ka rabu da ni Allah xai bani wani mijin. Gari da yawa ai maye bayacin kansa Badaru. In shaa Allahu yadda Allah ya doramun jarrabawar xama da kai xai bani ikon cin jarrabawar, wlh nima ba Jin dadin xama dakai nake ba. Allah ya na madakata yana jiranmu kuma zai mana sharia"



Simi simi daya bayan daya abokan nasa suka fice, kodan kada aure ya mutu ace ta sillarsu ne. Ya rage sai Sani kawai, ya kalleshi yace "yanxu wannan abun da kayi me gari ya waya? Burgewa kayi? Ka tauna asirin gidanka a idon duniya. Allah ne kadai yasan inda wannan zancen zai tsaya,

Please Login or Register in order to submit comment