Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔

✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢t + 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

Asma'u Muhammad Auwal (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
ASMEETAH
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZa

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ ᵏᵒ ʷᵃˢᵘ ˡⁱᵗᵃᵗᵗᵃᶠᵃⁱ, ⁱʸᵃ ˡⁱᵗᵗᵃᶠⁱⁿ ᵐʸ ᵉⁿᵉᵐʸ ᵏᵃʷᵃⁱ ᶻᵃ'ᵃⁿᵃ ᵗᵘʳᵃʷᵃ...
𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗻⃪𝗲⃪ (1)



꧁꧂

*(C.D.S)*
Chief of Defence staff
Chief Suraj Mahendra Marka shugaban sojoji na ƙasar U.S wanda a baya ya zauna anan ƙasar Nigeria dake garin Babban Birnin F.C.T Abuja, yana da mata ɗaya wato Agent Madam Parveen jami'ar C.I.D da ƴaƴansu uku!
Babban Ɗansa shine Marshal. Mohandas Suraj Mahendra,
Sai kuma Ɗansa na biyu shine Commander. Rakesh Suraj Mahendra,
Sai kuma Autarsa Amreesha Suraj Mahendra,
C.D.S Suraj ya rasa Ɗiyarsa Amreesha tin tana ƴar shekara biyu a duniya ta hanyar hatsarin mota da sukayi ita da mahaifiyarta Madam Parveen a hanyarsu ta dawowa daga garin Kaduna zuwa Abuja, wacce Madam Parveen ita take driving ɗinsu
Anan suka samu babban hatsari anyi nasarar ceton rayuwar Madam Parveen amma saidai ita Amreesha yarinya ƴar shekara biyu ba'a sameta a cikin motar ba, an dudduba ko ina a wajen da sukayi hatsarin amma an gaza samun koda ƙyallenta ne balle gawarta, iyayenta sun shiga damuwa mai tsanani na rashin ɗiyarsu Amreesha, yanzu shekara goma sha takwas da faruwar wannan Al'amarin, shin Amreesha tana raye ne ko dai ta mutu? ALLAHU a'alamu....

Sai dai wannan family christal ne, gaba ɗayansu jami'ai ne hakan yasa suke da wani tambari na zanen catoon ɗin bindiga a gadon bayansu daga iyayen har ƴaƴan, kuma itama wacce aka rasa wato Amreesha tanada wannan tambarin, babban burin C.D.S Suraj shine idan Amreesha ta girma zata zamo jami'a ta musamman acikin sojoji amma kash lokaci guda ya rasata...

Amreesha wasu masu farauta ne suka tsince ta acikin jeji a yashe, saida tayi wajen shekara guda a hannunsu tukun suka yanke shawarar kaita gidan marayu ko za'a samu iyayenta tinda su har yanzu sun kasa samun iyayenta, a wannan lokacin kuwa iyayen Amreesha har sun bar Nigeria sun koma ƙasar U.S gaba ɗayansu domin sun saddaƙar da cewa ɗiyarsu Amreesha ta mutu....

꧁꧂

Chief of Army's staff
Chief Muhammadu Zaiduddeen Bature. yana zaune a nan ƙasar Nigeria dake garin Abuja G.R.A. su uku iyayensu suka haifa daga shi sai ɗan uwansa Sarki Abubakar Zaiduddeen Bature, mai martaba sarkin ƙasar Jidda, sai ta ukun su Aunty Yolash tana aiki a ministry of education dake garin Bauchi..
Chief Muhammad Bature
Matarsa ta farko itace Hajia Fateema wacce ALLAH yayi mata rasuwa tin shekarun baya sakamakon haihuwar ƴan biyunta wato the twins,
MAJOR GENERAL RAZHDEEN (M.G.R) da kuma SURGEON DOCTOR ROSHAN (S.D.R).. daga baya Chief Muhammad Bature ya Auri Matarsa ta biyu Hajia Kilishi wacce yanzu take zaune dashi da yaranta Biyar duk Mata, ta farko itace Meenat sai ta biyu kuma Pinky sai Ruky da Ummy sai Autar ɗakinsu wato Tiny itace ƙaramar cikin su, Hajia Kilishi taso ta samu ɗa namiji amma ALLAH bai bata ba, tin akan ƴarta Tiny aka cire mata mahaifa sakamakon matsala da mahaifanta ya samu, tayi kukan rashin samun yaro namiji sannan tana baƙin cikin yanda Chief Muhammad yake nuna so da ƙauna wa ƴan biyunsa duk da ba'a waje ɗaya suke ba,
M.G Razhdeen yana zaune a ƙasar U.S anan yake da aiki, gidajensa kuwa sun kai goma sha a ƙasar U.S babban amininsa kuwa shine Marshal Mohandas ɗan gidan C.D.S Suraj.
shi kuma S.D Roshan yana zaune a ƙasar Egypt anan Babban hospital ɗinsa yake....

꧁꧂

SARKIN JIDDAH
Mai martaba sarki Abubakar Bature
Matansa biyu Babbar matarsa itace Maimuna (Mamy) bata taɓa haihuwa ba kuma an tabbatar bazata iya ɗaukar ciki ba, hakan yasa mai martaba ya Auro ƴar Sarkin ƙasar Niger kyakykyawa mai suna Maryam (Innayo) cikin ikon ALLAH bayan shekara Innayo ta samu juna biyu, a haihuwa aka yi mata Operation aka ciro mata zankaɗeɗiyar ɗiyarta mace,
Mai martaba yayi matuƙar farin ciki dajin wannan Albishir da akayi masa a yayinda ita kuma Hajia Mamy baƙin ciki kamar ya kasheta hakan yasa ta biya wa Doctor ɗin asibiti akan ya cirewa Innayo Mahaifa ba tareda kowa ya sani ba, hakan kuwa akayi sannan tasa aka sace jaririyar bayan ta rufewa jaririyar baki yanda bazata iya yin kuka ba ta hanyar tsafi data karɓo a gurin bokanta, ta biya maƙudan kuɗi akan aje a bisine jaririyar da ranta yanda baza'a ƙara jin labarin ta ba,
Washe garin ɓatan jaririya ba ƙaramin girgiza kowa yayi ba banda Hajia Mamy da kuma Doctor sai wanda ya tafi da jaririya iya su kawai suka san sirrin,
Mai martaba saida ya faɗi sumamme jin labarin ɓatarta, itama uwar ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba,
Mai martaba bayan ya farfaɗo baiyi ƙasa a gwiwa ba haka yasa aka yanka ƙaton rago ya raɗawa ɗiyarsa suna REEMAH inda ace namiji aka samu Yarima za'a sanya masa amma yanzu macece,
Shi kuwa wanda ya sace Reemah bai bi maganar Hajia Mamy ba na cewar a bisine jaririyar lokaci guda imani ya shige shi haka ya fita da Reemah daga ƙasar Jidda a sirance kai tsaye Nigeria ya kawota, bai tsaya a ko ina ba sai a gidan marayu dake garin Abuja, yana miƙata ya gudu bai tsaya bada information nashi ba, lokaci guda aka rasa shi, kafin ya bayar da Reemah daman yayi mata zanen tambarin masarautarsu dake ƙasar Jidda da ƙunar wuta yanda bazai taɓa goguwa ba har abada akan cinyarta (Lap)....

꧁꧂

Aunty Yolash
Ƙanwa agurin Chief Muhammad Bature da kuma Mai martaba sarkin JIDDAH. Abubakar Bature, Auntyn su M.G Razhdeen da S.D Roshan da sauran ƙannensu mata, ita wannan tinda take bata taɓa yin Aure ba, tasa Aikin Boko a gaba sai tarin dukiyar da take dasu, batada damuwar kowa a ranta!
Gata da farin jinin mazajen Aure amma taƙi sam tana zaune anan Bauchi a fantamemen gidan kanta amma saidai ta zuba masu tsaro a gidanta,
Aunty Yolash Smiling woman ga son temako da tausayi duk sati take fitar da zakkah sannan tasa a rabawa gidan marayu kayan Abinci da suturori da kuɗaɗe, mutane har so suke jumma'a tayi da sassafe kafin ta fito gurin aiki ƙofar gidanta yake cika da al'umma saboda ta saba raba zakkah da sadaka, kwanan nan ta rabawa gurgwaye kekuna maza da mata,
Aunty Yolash kenam babu ruwanta ita kowa nata ne, kuma Insha ALLAH muna sa ran kwanan nan zata fito zaɓen Minister a garin Bauchi....


꧁꧂ ꧁꧂


Babban gidan marayu dake garin Abuja
a ciki akwai mutane da yawa wadanda suke kai kawo manya da 'kananu kowa yanata harkar gabansa kamar gidan prison duk suna sanye da kaya iri daya ajikinsu, kuma babu halin fita ko ina babban gate a tsare yake da wasu manya manyan masu tsaro, idan kunga marainiya ta fita daga cikin gidan nan to saidai an samu wasu masu kud'i ne sukazo za6ar yarinya da zasu dauka ko a matsayin er aikinsu, su dai basa d'aukar yara sai dai yan mata wad'anda zasu iya juran aiki....

Wata zankaɗeɗiyar budurwa ce wacce bazata wuce shekara 20 ba tana zaune akan wani ɗan dakali tana wasa da wani siririn sarƙa dake lanƙaye a wuyanta mai ɗauke da catoon ɗin Jesus Christ ajiki ta ɗan ƙasin sarƙar zanen Cross ne,
Idonta akan sarƙar tanata jujjuya shi,
kwatsam kunnuwanta suka jiyo mata wani ɗan hayaniya ta gefenta, ɗagowa tayi da manya manyan idanuwanta mai ɗauke da zara-zaran eyelashe! White eyes ɗinta ne suka sauƙa akan wata mata yanda take ta dukan wata matashiyar yarinya mai buzuzun gashi irin mai murɗi-murɗin nan har gadon bayanta, yarinyar kana ganinta kasan irin yaran buzayen nan ne ƴan ƙasar Niger kyawawa,
Budurwar dake zaune ganin yanda aketa dukanta yasa ta tashi da gudu ta nufi wajen cikin sassanyar murya ta ce

"Haba ke kuwa Aunty Salma mai tayi miki ne haka kike dukanta?..."

A fusace wacce ake ƙira da Salma ta juyo tana kallonta a ƙasƙance ta ce "Ke Baiwar ALLAH ki kiyaye Ni wallahi, bana son shishshigi shin da kika taso rama mata dukan zakiyi ne?..."

Baiwar ALLAH tayi murmushi sannan ta ce "Aunty Salma meyasa bakya tausayin Ƴar Amana ne? ki dubi halin da take ciki Kurmiya ce bata iya yin magana dan ALLAH ki rinƙa mata uzuri..."

Salma ta ce "ke Baiwar Jesus domin bazan ce miki Baiwar ALLAH ba tinda baki haɗa hanya da musulunci ba Arniyar banza..."
Lumshe ido Baiwar ALLAH tayi sai ga zafafan hawaye a hankali ta buɗe su da sassanyar muryarta ta ce "Aunty Salma ina ganin mutuncinki, na roƙe ki kar ki sake ƙirana da Arniya saboda ina sallah, ina Azumi, ina karatun Alkur'ani mai girma, ina nisanta kaina daga aikata saɓon ALLAH to meyasa zaki rinƙa ce mun Arniya?..."

Kwashewa da dariya Salma tayi harda tafa hannayenta biyu sannan ta ce "a fuska musulunci a zuciya kuma kafurci, idan ke ba Arniya bace me zaisa ki rinƙa yawo da sarƙar Jesus a wuyanki? saboda kin raina wa mutane hankali koh?..."

Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi tareda faɗin "Ba haka bane Aunty Salma! tin ina ƙarama nake ganin wannan sarƙar a wuyana, duk da ban tashi a gaban iyayena ba amma nasan a lokacin dana rabu dasu nayi wayo kuma wannan sarƙar daga wajensu ya fito saboda haka zan cigaba da adana wannan sarƙar har ALLAH ya bayyano mun da iyaye na....."

Salma harararta tayi sannan ta ce "da dukkan alamu iyayenki Arna ne shiyasa suka sanya miki sarƙa mai ɗauke da Cross ɗin Jesus Christ mttssww....".
taja dogon tsuka tare da barin wajen...

Baiwar ALLAH sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana faman zubar da hawaye, ji tayi wacce take tsaye a gefenta ta rungume ta sosai itama tana zubar da ƙwallah,
Baiwar ALLAH ɗagowa tayi tana kallon Ƴar Amana wacce ta rungumeta cikin tausayawa ta ambaci sunanta cikin sassanyar murya ta ce "Ƴar Amana kiyi haƙuri komai lokaci ne, mu cigaba da haƙuri ALLAH yana sane damu kuma Insha ALLAH zai kawo mana agaji, kowa ya tsane mu acikin gidan marayun nan Ni suna ɗaukata a mazannin Arniya alhalin ba haka bane, ke kuma saboda ALLAH ya yo ki Kurmiya shiyasa ake cin zalinki kiyi haƙuri kinji ko? ina tare dake duk tsanani duk wuya bazan rabu dake ba, ke Ƴar Amana tace..."

Itama Ƴar Amana ɗagowa tayi tana kallon Baiwar ALLAH babu bakin magana sai hawaye amma tana jin duk abunda ake faɗa...

Baiwar ALLAH hannu tasa tana gyara sumar kan Ƴar Amana wanda ya tarwatse gashin yayi buzuzu duk ya nan naɗe,
Ita kuma Baiwar ALLAH gashin ta tsantsi ne dashi har gadon baya baƙi ƙirin sai sheƙin da yake...
suna tsaye suka ji wata mata tana cewa "ku kuma pah masu fararen fuskoki me kuke yi anan? anata ƙiran sallar mangarib ku wuce ku koma ɗakunan ku..."

Baiwar ALLAH riƙe hannun Ƴar Amana tayi har sun fara tafiya matar ta ƙira sunan Baiwar ALLAH sannan ta ce "idan kunje kisa Ƴar Amana tayi sallah kar ki rinjayeta ta koma ƙabilan da ba nata ba ...."

Baiwar ALLAH ɗaga kanta kawai tayi alamar toh saboda matar itama ɗaya ce daga cikin shuwagabannin gidan,
Da hawaye a saman fuskar Baiwar ALLAH suka shige ɗakinsu, suna shiga kuma ta shige toilet tayo alwala sannan ta fito ta tura Ƴar Amana itama ta shiga domin ɗaurowa alwala,
kafin ta fito kuwa Baiwar ALLAH ta shimfiɗa musu sallaya sannan ta cire wannan sarƙar dake wuyanta ta zura ƙaton hijab tana jiran fitowar Ƴar Amana, tana tsaye itama ta fito ta saka hijab ɗinta a tare suka yi sallah kamar yanda suka saba kullum, suna idarwa Baiwar ALLAH ta ɗauki Alkur'ani mai girma ta soma karantawa itama Ƴar Amana tana zaune a kan sallayar ta zubawa Baiwar ALLAH ido ba halin yin magana amma tana ɗaukar komai a ƙwaƙwalwarta, da haka har Baiwar ALLAH ta kammala sannan ta ɗauki wannan sarƙar natan ta sanya a wuyanta gudun kar ya ɓata, saboda tana tunanin ta sanadiyar wannan sarƙar zata samu iyayenta....

Knocking aka fara musu a ɗakin da hanzari Baiwar ALLAH tazo ta buɗe miƙa mata flask ɗin abinci akayi sannan aka wuce,
Ɗakuna ne acikin gidan bana wasa ba, ko wane ɗaki mutum bibbiyu ne aciki, idan breakfast za'ayi kowa zuwa gurin babban dinning yake yi, anan ake hallaruwa kowa ya kama kujerar zamansa a jeru da doguwar table a gaban kowannen su yanda kowa zai ajiye plate ɗinsa asa masa abinci haka idan rana tayi, dadaddare ne sakamakon duhu ya fara shiga ba'a barin kowa ya fito daga cikin ɗakin shi hakan yasa ake zuwa kowa a bashi abincin darensa a ɗaki,
Kullum a cikin wannan rayuwar ake....

Baiwar ALLAH tin tana shekara uku aka kawota saida tayi shekara biyu a gidan nan kafin aka kawo Ƴar Amana ita kuma tana jaririya, dalilin da yasa Baiwar ALLAH da Ƴar Amana suka shaƙu saboda tin lokacin da ƴar Amana take jaririya ake baiwa Baiwar ALLAH rainonta, lokacin babu wasu mutane sosai a gidan, da haka suka tashi shiyasa Ƴar Amana take kallon Baiwar ALLAH a mazannin ƴar uwarta ta jini saboda ita ta tashi ta gani tana kula da ita, wanka da wanki da komai har yanzu Baiwar ALLAH ita take mata, wanka ne kawai yanzu ta daina mata, amma hatta waran kwanciyarsu ma ɗayane tin suna yara basu rabu ba.
Yanzu Baiwar ALLAH tanada shekara Ashirin 20 a duniya..
Ita kuma Ƴar Amana tana da shekara sha biyar 15 a duniya...

Kuma duk acikin su babu wacce tasan sunanta,
tin lokacin da aka kawo Baiwar ALLAH ta manta sunanta idan aka tambayeta sunanta sai dai tayi shuru hakan yasa duk wanda zai ƙirata sai dai yace Baiwar ALLAH da haka sunan ya bita kuma har yanzu bata iya tuna sunanta ba....

Ƴar Amana kuma wanda ya kawota aka tambaye shi sunanta yace musu Ƴar Amana sunanta kuma ya sanar musu cewa da haka za'ana ƙiranta har ta girma, shiyasa itama ta tashi babu suna sai dai Ƴar Amana....

Haka rayuwar ƴan mata biyun nan yake gudana acikin gidan marayu, kowa ya raina su ana musu kallon ƙasƙantattu wasu suna zargin cikin shegensu akayi aka zubar dasu, wasu kuma suna faɗin ƴaƴan ƴan gudun hijira ne,

Basu san cewa Ɗaya daga cikinsu Ɗiyar shugaban sojojin ƙasar U.S bane (C.D.S)..

Ɗaya kuma Ɗiyar Mai martaba Sarkin ƙasar JIDDAH bace kuma jikar mai martaba sarkin Niger, Ɗiyar ƙanin Chief of Army's staff na Nigeria....

BAIWAR ALLAH DA ƳAR AMANA STORY BY ASMEETAH
ku cigaba da bibiyata a cikin littafi na mai suna
*MY ENEMY...*


Comments 🙏 And Sharing book,

Ku saurari Chapter two zuwa Monday idan har na samu ƙarancin comment...
Idan kuma na samu comments yanda nake so daga Saturday zan poster kuma,

Bazaku ji Armashin chapter one ba har sai kun shugo chapter two anan labarin zai fara gobara🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢+ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

Asma'u Muhammad Auwal (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
ASMEETAH.
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ᵖˡᵉᵃˢᵉ ᵒⁿˡʸ ᶠᵉᵐᵃˡᵉˢ ᵃⁿᵈ ᵈᵒⁿ'ᵗ ᵃˡˡᵒʷ ᵗᵒ ˢᵉⁿᵈ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ⁱⁿᵗᵒ ᵐʸ ᵍʳᵒᵘᵖ🙏 ⁱᶠ ⁿᵒᵗ ⁱ ʷⁱˡˡ ʳᵉᵐᵒᵛᵉ ʸᵒᵘ, ᵃᵐ ʷᵃʳⁿⁱⁿᵍ ʸᵒᵘ ..

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (2)



꧁꧂


Ƙiran Asubar farko akan dodon kunnen Baiwar ALLAH wacce take zaune akan sallaya tana jan carbi a hankali tin ƙarfe biyu na dare bata koma bacci ba, kullum saita tashi tayi sallar dare...
tashi tayi a hankali ta

Please Login or Register in order to submit comment