Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kuma bayi sama ba, yana a tsakatsaki, tsawansa bai wuce tsawan hannu ba, sai rangwajejan kai kamar warya,yanada idanuwa kamar na mage, da sharSa sharSan kafakuwa kamar na babban mutum, kai in taaice muku, halittar nan batada kyawun gani hasalima mai ciki zaka iyayin Sari ganin wannan muguwar hallitta,sujjada tama wannan hallitar tare da cewa


"Yakai Sarkin Tsageru! yakai gagara badau!! , yakai buhun ara kafi arfin danna!!!, ya kai Shugaban matsafan duniya!!! Haia ka cika alawarin da ka Wauka akan bayyanar bayan shekara biyar!!! "



Wata dariya naji har asa na girgiza ashe wannan halittar ne ke busar dariyar, can ya tsagaita kamar ruwa ya Wauke ya fara magana jikake kamar asa zata tsage



"Karki yarda ayi auran!!! Karki bari ayi auran!!! Idan kuma ba haka arshenki yazo Zulfa'u,yaaazoooo arshenki Zulfa'u!!! "



Da saura ta Wago kanta tana kallonsa don a gaskiya ita batasan da wani aure ba,to wani aure yake magana akai,kasa hauri tayi ta tambayesa cikin girmamawa tare da an-an dakai



"Ya kai Sarkin matsafan duniya, yakai Boka BurumbuWu wani aure ne zan hana afkuwarsa"(daman sunan wannan halittar Boka BurumbuWu,tabbb yaci sunnansa kuwa>>>====)



Dariya ya tsintsire dashi har asa na girgiza,sai kuma ya fara kuka ko'ina na Wakin rawa yake can ya tsagaita tare da cewa



" Karki bari!!! Karki yarda!!! A hir Winki ki bari ayi auran..........







Mu haWu a pages na gaba hmmmmm wuta kan wuta=%=%=%=%




****Auransu waye ne Boka BurumbuWu yace kar Zulfa'u ta bari ayi????.......




****Shin su Umma Kande da Maman Jummalo sun tuba ko kohar yanzu basu saduda ba???........




****Yaya zamantakewar Maryam zata cika ba a gidan Sauban ganin tun a satin farko Maryam ta fara fuskantar alubalai iri-iri???.........





Ku cigaba da zubo ruwan comments>>>=C=C=C=؝=؝=؝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaWantar,ilmantar tare da faWakar daku>>=C=C=؝=؝<9<9<<<<<<






Ina matuar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar aunar>>=C=C=؝=؝<9<9<<<<<<=ؖ=ؖ=ؗ=ؗ=ؓ=ؓ






Daga alalamin
=؍=Narrnarhh Bukar ==؍

Comments and share =O=O=OFisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar:

< NACINA YA JAWO MIN<






Narrnarhh Bukar
'






<9Perfect Essential Writer's
Association<9
(' P. E. W. A('






Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002







Masu telegram zaku iya following Wina ta wannan link Win>,=C<=G=G=G
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk











<9<9<9I'm not born to be a writer but born to be a great professional writer
'
'
'=C=C=C<9<9<9









<<<<<   
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~i daku domin da bazarku nake taka rawata=C=C=C=ؖ=ؖ=ؖ<<<<<<













3 5 ----3 6







Wata dariya naji har asa na girgiza ashe wannan halittar ne ke busar dariyar, can ya tsagaita kamar ruwa ya Wauke ya fara magana ji kake kamar asa zata tsage



"Karki yarda ayi auran!!! Karki bari ayi auran!!! Idan kuma ba haka arshenki yazo Zulfa'u,yaaazoooo arshenki Zulfa'u!!! "



Da saura ta Wago kanta tana kallonsa don a gaskiya ita batasan da wani aure ba,to wani aure yake magana akai,kasa hauri tayi ta tambayesa cikin girmamawa tare da an-an dakai


"Ya kai Sarkin matsafan duniya, yakai Boka BurumbuWu wani aure ne zan hana afkuwarsa"(daman sunan wannan halittar Boka BurumbuWu,tabbb yaci sunnansa kuwa>>>====)


Dariya ya tsintsire dashi har asa na girgiza,sai kuma ya fara kuka ko'ina na Wakin rawa yake can ya tsagaita tare da cewa


" Karki bari!!! Karki yarda!!! A hir Winki ki bari ayi auran jikarki da Wa daga tsatson maiyiyarki,domin idan kika bari auran ya tabbatu,hooo hoo hoooo,asirinki na gab da tonuwa!!!


Tsuru-tsuru Haj. Zulfa'u tayi da idanu tana sauraransa,a zuciyarta tana cewa. 'Na shiga uku ni Zulfa'u daga wancan sai wancan,da wanne zanji,da farko ance karna bari muhadu da tsatsonta,yanzu auran da ma bansan da wanzuwansa ba ake cemin karna sake ayi auran,yau naga ta kaina'. Kamar Boka BurumbuWu yasan mai take ayyanawa aranta ya ce


"Zulfa'u duk abinda muka sanar miki tabbatacce ne in har baki bi umarninmu ba! Kisani munyi iya yinmu domin mu halaka sauran ahalinta ammaa.....!!!


Wani irin gigitaccan kuka ya fashe dashi wanda duk ilahirin Wakin na girgiza gashi shi kanshi arar kukan babu daWin ji,kai in taaice muku kamar saukan ruwan sama mai arfin gaske haka kukan nasa yake.Yakai tsawan mintuna 10 yana wannan kukan,ita kuma Haj. Zulfa'u abin duniya ya mata katutu a yuwa,kanta a due tana sauraran kukan nasa,sai kuma can ya tsagaita tare da cewa cikin amon muryarsa mai firgitarwa


" Basa wasa da sallolinsu biyar a duk rana,suna azkar Win safe da na yamma,suna nafilfilun dare,sun tsare yaransu da addu'o'i masu arfi,mun kasa Zulfa'u!!! Mun kasa!!! "


Jinjina kai Haj.Zulfa'u tayi saboda abinda Boka BurumbuWu zaice ya kasa to ba aramin abu bane,tabbas ya zaman mata dole tayi taka tsantsan kar asirinta na shekaru aru aru su bayyana dako kashinta ya bushe,dole ta hana faruwan wannan auran duk da batama san dashi,wannan dole ne ta hana,haka tayi ta ayyana abubuwa a ranta kafin daga bisani Boka BurumbuWu ya ara da cewa


"Zamu barki yanzu! Sai bayan shekara biyu wanda a lokacin zamu linka miki kariyar da muke baki sosai,domin lokacin abubawa zasu fara rincaSewa,dole mu kareki Zulfa'u! Dole mu kareki domin kina mana biyayya tare da bin umarninmu haWi da sharudWanmu! Zamu tafi! Zamu tafi Zulfa'u! Sai bayan shekara biyu! Muna ara jajjada miki ki kula! Ki kula Zulfa'u kar iya auran jikarki da Wa daga tsatson maiyiyarki Zulfa'u! Karki bariii!!! Karki bariii!!! Mun tafiii!!! Sai watarannn!!! "


if kamar waliya ya Sace a lokaci guda hasken ya Sace sai duhu ya mamaye Wakin bayi Waga,a cikin duhun ne Haj. Zulfa'u ta lallaSa ta kunna bulb Win Wakin sannan ta harharWa kayan tsafinta ta sakasu a cikin ayataccan akwati arami mai kyawun gaske saita saka akwatin a wani akwati babba shima mai kyau saita maida a arashin gadonta.Sannan ta hau tanameman gadonta na alfarma ta kwanta,ta kai tsawan awa Waya amma Sarawo bacci yai ziyartatta sai kusan sallar subhi bacci ya Wauke ta,ba ita ta farka ba sai wuraran 11:23am na safe kasancewar babu sallah a tsarin rayuwarta hasalima tun tana da shekara 35 a duniya tayi sallama da bautar Allah hatta zuwa Hajji tun a wannan lokacin ta daina saidai bautawa aljan tare da zubar da jinin baayan karnuka 50 a duk shekara.


Bayan ta farka daga baccin ta nufa hadWan toilet Winta mai shegen kyau tayi wanka haWi da brush sannan ta fito ta shirya cikin lafiyayyan atamfanta super holland wanda tasha duwatsu a duk ilahirin dokuwar rigan,ga gwalagwalen da ta saka a wuyanta da kunnenta harda awarwarayansu guda shida,flat shoe ne ta saka sannan ta fito daga Wakinta,kai kai kai ta haWu iya haWuwa wallahi idan ka ganta zakayi tunani ar shekara 50 ba 78 a duniya ba,domin jikinta kwata-kwata bai nuna alamun tsufa ba ko kuma furfara a gashinta wanda zai nuna tsohuwa ce,tafiya take mai cike da taama da izza,zakayi tunanin ar sarki ce har ta isa dining room wanda tasan already mai aikinta ta gama shirya mata kayan kalaci a food warmers,zama tayi a ayattaciyan kujerarta wanda babu irinta a wurin,serving kanta tayi duk da kaWan ta saka abincin kasancewar yau tana cikin damuwa sosai saboda ganawar da tayi da Boka BurumbuWu, shiyasa yau ta tashi da kalasa a cikinta.Haka taci abincin kaWan sannan ta koma falo ta zauna haWi da kunna television, kallon tv kawai take amma babu abinda take fahimta na daga abinda suke cewa,lulawa tayi cikin tunaninta tare da nema ma kanta mafitar yadda auran jikarta da Wa daga tsatson maiyiyarki bazai faru ba.Haka tayita zama a falon ita kaWai kasancewar daga ita sai mai aikinta ne a gidan sai kuma in yaranta da jikokinta sunzo mata ziyara.


Wurin arfe 3:09pm na rana Haj. Zulfa'u na zaune a falon taji alarm Win ofa na ara alamun ana son shigowa,mai aikinta ne da sauri da fito daga Wakinta zuwa ofar tare da buWewa,baki ta sake tana kallon bain sai kuma ta ce


"Laaa!!! an asar waje a gidan,oyoyo sannunku da zuwa"


Tayi maganar tare da basu wuri suka shigo Wakin,Fadila ce da Amminta suka musu zuwan bazata,da gudu Fadila ta shiga falon tare da daka tsalle ta rungume kakarta don tsabar farin ciki.Haj Zulfa'u dake zaune ta lula wani sabon tunanin jin ar aikinta ta ce ga bain asar waje,wato autarta Hannatu da Fadila kenan, 'wayyo na shiga uku ni Zulfa'u, ya tabbata Boka BurumbuWu, kenan maganar auran ya kawosu,dole na hana auran nan,dole ne'. Tana cikin zancen zuciya taji an wani rungumeta,tasan wannan aikin bana kowa bane illa na Fadila,ilai kuwa ita ce.Fadila ce ta ce cikin murna


"Oyoyo Granny wallahi nayi missing Winki sosai,ke kuma naga alama bakiyi missing Wina ba"


Tana maganar cike da shagwaSa irin na ajebos rainon asar waje,murmushi Haj.Zulfa'u tayi duk da ba a cikin yanayi mai kyau take ba amma dole ta kula da jikarta wacca tafi soyuwa a gareta a duk jikokinta,cewa tayi


"Ni awa nai missing Win jikata wacca tafi soyuwa a gareni,ai kullum da kewarki nake kwana kuma da ita nake tashi Fadilatuwa tahh! "


Suna cikin hirar ne saiga Ammin Fadila ta iso gunsu da fara'arta,samun kujera one seater tayi ta zauna tana ganin dramar Mamanta da arta,hakan na sata nishaWi sosai,katse musu hirar tayi ta cewa


"Hajiyarmu mun sameku lafiya? "


"Lafiya lau auta,ya kuke da mijin naki"


" Duk muna lafiya ya ce ma a gaidaku,shima yana nan kan hanya idan ya gama abinda yake, zaizo har nan ku gaisa in shaa Allah "


"Maa shaa Allah, toh Allah ya kawoshi lafiya"


"Ameen ya Allah"


Kallon Fadila Haj. Zulfa'u tayi tana murmushi sannan ta ce


"Kwana biyu da banganki ba sai naga kin aramin girma da kyau"


Murmushi Fadila tayi don Fadila na mugun son a yabi kyaunta,sai ta ce


"Awwwn Granny,shiyasa nake ara sonki Muah! Muah! Muah! "


Hannunta ta sumbata har sau uku alamun kiss tare da hura ma Grannyn nata,haba mai Hannatu da Haj.Zulfa'u zasuyi inba dariya ba,don idan da Fadila a wuri ka dinga shan dariya saboda shirmanta yayi yawa.Haj .Zulfa'u ce tace


"Ku tashi ku watsa ruwa nasan kafin kugama angama abinci sai kuci ku huta,da daddare mayi hirar da hujja,babu musu suka tashi don watsa ruwa suji daWin jikinsu,bayan sun fito sukaci abinci kana kowa ya baje don huta gajiyar jirgi da suka sha.


Da daddare su Fadila da Amminta sukaje Wakin Haj. Zulfa'u don yin hirar yaushe gamo,sun sameta tana zaune akan sofa a tare da ita kuma coffee ne tana kurSa,zama suma sukayi a sofar dake kusa da ita,a lokaci guda suna gaisheta amsawa tayi cike da kulawa tare da cigaba da kurSar coffee Winta,a sannan ne Hannatu ta gyara zama don su tattauna akan maasudin zuwansu Nigeria.


" Hajiyarmu kin kusa aurar da jikarki fa"


Murmushi a fuskar Hannatu take sannarwa Hajiyarta,ita kuma a lokacin da kurSi coffee Winta kenan taji ance ta kusa aurar da jikarta wato Fadila dai ta bokanta yamata kashedin karta bari ayi auran,habawa da sauri da zubar da coffee dake a bakinta, irjinta na dukan uku-uku tare da cewa


"Da gaske!!!"


A tunanin Hannatu duk murna ce ta sakata zubar da coffee na bakinta,sai ta ara da cewa


"Da gaske Hajiyarmu,a can asar yaron yake karatu,babu laifi yanada tarbiyya don Daddyn Fadila har Nigeria ya aiko aka tambayi halayyarsa tare da asalinsa,Wan Kebbi ne yaron,gasu da dukiya gida da waje"


Da sauri Haj. Zulfa'u ta dakatar da Hannatu da cewa


"Yaron waye a Kebbin? "


Caraf Fadila ta cafke wacca tunda aka fara maganar bata tsoma bakinta ba sai yanzu ta ce


"Granny Mum Winsa jikar Alhaji Kabir Dikko ne sannan Daddynsa sunansa Alhaji Dauda Gali mai Nass.........."


"Dakata Fadila!!! "


Jikin Haj. Zulfa'u na rawa jin tabbass yaron daga ahalin maiyiyarta ce batasan sanda ta daka ma Fadila tsawa ba,hankalinta a tashe ta fara magana


"Inaa!!! Inaa!!! Bazaiyu ba auran nan,kunsan halinsu kuwa Auta da zaku kai Fadila gidan,duk da binciken da kukayi ba komai kuka sani akan wannan mugayan ahalin ba sai ni Haj.Zulfa'u"


Tare da nuna kanta,arya ce ta sumbuWo musu akan ahalin basu da kirki bayan ita ce ma ta rushe musu farin cikinsu,yanzu kuma tana niyyar goga musu bain fenti duk don a fasa auran,domin tama kanta alawarin bazata taSa bari ayi auran ba inhar tana araye.Dole ta Wau mataki don auran ya rushe ko ta halin aa.Fadila da tunda Haj Zulfa'u ta daka mata tsare tayi gummm da bakinta bata sake magana ba sai yanzu da taji kakarta na niyyar tasa a fasa auranta da masoyinta,wani malolan bain ciki ne ya tsaya ma Fadila a wuya batasan sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tana cewa


"Wallahi yana da kirki ga addini,ina sonsa,karku rabani a masoyina"


A hasale Haj .Zulfa'u ta ce


"Masoyin Ubanki! Nace masoyin Ubanki! Wawuya don ana taimakon rayuwarki karta faWa ga halaka amma ke baki gani,kaunar da nake miki ne yasa nake faWa miki illar auran wannan ahalin amma ke gamai masoyi kin fara kuka,waya sani ma ke kika fara cewa kina sonsa"


Kuka Fadila take sosai domin a gaskiya tana aunar Sadam sosai,gashi yanzu taga Amminta ta yarda da maganar kakarta har tana cewa gobe zata kira Daddynta ta sanar masa kawai ya fasa zuwa Nigerian daman saboda maganar auran Fadila ne yasa yakeso yazo wurin danginsa su tattauna amma yanzu kawai ya fasa zuwan Allah ya kawo mata miji na gari.


Haka akaita drama a wannan family a kan batun auran Fadila da Sadam wanda Haj. Zulfa'u ta nace akan Fadila bazata auri Sadam ba saboda ahalinsa ba mutanan arzii bane,kowa a family ya yarda da zancen Haj. Zulfa'u har Daddyn Fadila domin shi dama yanada wanda yakeso Fadila ta aura amma tai ita sai Sadam, ita ko Fadila yanzu ne wutar so da aunar Sadam ke ara ruruwa a cikin zuciyarta.Anyita bata hauri akan ta haura da Sadam amma ina.wannan kenan



Bari mu lea Birnin Kebbi=C=C=C




@@@ @@@@@@@




KEBBI



Motoci ne har biyu na alfarma sukaje Airport Win AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT wanda yake a Sokoto state domin Waukar Sadam Dauda Gali Mai Nasara,sun isa a international Airport Win a daidai lokacin jirginsu Sadam ya sauka,saida akayi tsawan mintuna 30 kafin mutanan cikin jirgin suka fara sauka,VIP section na jirgin ne suka fara sauka,wanda Sadam yake a ciki,mutum daya-biyu- uku na hudun ne wani yakkyawan gaye ya fito daga jirgin yana taku cike da izza da jarumta irin na masata masu jini a jika,taku yake har ya sauko daga jirgin yana rie da briefcase baa a hannunsa,shi kuma ya saka black suit mai shegen tsada,ga gemunsa da gashin kansa duk sunsha gyara,daga gani kasan ana kashe musu maudan kuWi,duk inda ya gilma sai an kallesa saboda kyau da kwarjini da Allah ya masa,a can naji wasu yara an biyu lokaci guda suka ce


"Uncle! Uncle! Uncle! "


Inda yaji ana cewa Uncle ya waiwaya habawa kafin ya gama tantan ce yaran tuni sunyo kansa da gudu suna masa oyoyo oyoyo Uncle,rungumesa sukayi tsabar murna saboda a lokacin da yake gida yana Waukar yaron yawan shaatawa,shiyasa suke sonsa kuma koda ya tafi karatu,kusan kullun sai sun dami Mom Winsu akan yaushe Uncle Winsu zaizo ya kaisu shopping.Shima rungumesu yayi sosai tare da shafa kansu,a sannan ne Aunty Sakina da Kamal abokinsa suka zo inda suke da murmushi a fuskarsu sannan kuma a bayansu akwai body gaurd kasancewar yanzu Daddyn Sadam ya ara shahara sosai,fuk inda zaije saida bodygaurd masu kare lafiyar,shiyasa a sanda zasuzo daukar Sadam aka tafi da mota biyu haWe da body gaurds.


"Ai sai kubari mu arasa gida kuyi mishi oyoyon dakyau "cewar Aunty Sakina tana murmushi


ago kansa yayi yana kallonta tare da mayar mata da martanin murmushi yana cewa


" The great Aunty! Wallahi nayi missing Winku sosai,kai duk wanda yabar gida, wallahi gida yabarshi"


Dariya Kamal yayi yana cewa


"Kaga Malam yunwa nakeji tun Wazu muke jiranku,don haka bar zancen in munje gida kwarasa,don ni ar Gusau nakaji wallah"


Dauwa Sadam yama Kamal yana murmushi tare da cewa


"To Sarki an yunwa sai mu tafi kafin ka cinyemu Wayye,nida nasha tafiya banyi orafi ba sai kai"


Dariya dukkaninsu sukayi sai Sadam ya rio hannuwan twins bayan yaba Kamal briefcase Winsa,haka suka isa Birnin Kebbi kasancewar jirginsu a Sokoto ya sauka,buWe musu katafaran gate akayi domin da jiniya suka iso gidan,bayan sun sauka ne sai suka Wunguma zuwa cikin gidan.


Mom ce da Daddyn Sadam suna zaune suna jiran isowarsu gidan saboda sunyi waya da Sakina ta ce musu suna hanya,bayan sun shiga falon da sallama a bakunansu Mom ta mie da sauri haWi da rungume autanta tana farin ciki,shima ara rungumeta yayi yana farin ciki,suna cikin hakane sai Daddyn Sadam ya ce


"Wato kaga Mom Winka ka manta dani ko"


Dariya Sadam yayi tare da nufa inda Daddyn sa yake haWi da rungumesa yana cewa


"I really miss you Dad,nayi kewarku sosai Dad"


Mom ce da murmushi fuskarta tace


"Kaje ka watsa ruwa muna jiranka a dining room"


"Ok Mom"


Tafiya yayi ya watsa ruwa ya sako sassauyar jallabiya fara tas ya fito,haka wannan familyn suke jeru suna cin abinci cikin farin ciki da annashuwa wanda ko ba'a faWa ba saboda dawowan Sadam ne daga UK,bayan cin abinci sai suka Wunguma zuwa falo,anan suka fasa hirar yaushe gamo,sai wurin Asr kowa ya mie don yin sallah,wanda Sakina ta tafi gida da yaranta,shi kuma Kamal sai dare ya wuce gida saboda bayan da sukayi sallar Asr Wakin Sadam suka wuce,sun Sata lokaci suna hira wanda sai dare Kamal ya tafi.


Bayan kwana biyu lokacin Sadam ya huta sosai Daddynsa ya kirasa part Winsa,a lokacin daya shigo falon ya tarar da Mom Winsa tana zaune itama,samun wuri yayi a asa ya zauna tare da musu barkha da dare,cike da kulawa suka amsa masa,Daddyn Sadam ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana


"Alhamdulillah ala kulli halin,yau gashi Allah ya nuna mana kammaluwan karatunka Sadam cikin nasara da aminci,muna ara gode masa da wannan ni'imar da yayi mana,sannan yau zan dana maka companies,plazas haWi da gidajan mai wa'inda mallakinka ne tun a ranar da aka haifeka,akwai companies guda uku,Waya a kaduna wanda ake sarrafa shinkafa,biyu kuma a kano,sannan akwai gidajen Mai guda huWu,biyu a hanyar Zaria,Waya a cikin garin nan sai Wayan a Zamfara,wanda dukkaninsu suna aiki tare da manya-manyan motocin mai guda shida,sai kuma Plazas guda Uku dukkaninsu suna kaduna,don haka ka jajirce ka maida hankalinka akansu,a da nasu sai kayi Masters kafin zan dana maka su amma sai wani tunani yazomin akan gwara ka fara gudanar da kasuwancinsu kafin daga bisani ka koma aro karatun"



Kasa magana Sadam yayi saboda wannan kyautar bazata da ya samu daga Mahaifinsa,tabbas dole ya maida hankalinsa kacokar a kasuwancinsa domin Daddynsa yayi alfahari dashi,cikin murna Sadam ya fara magana


"Dad bansan wasu kalmomi zan saka wurin gode maka da wannan kyauttukan bazatan da kamin ba,ina godiya sosai, Allah yasaka da alkhairi,ya ara buWi da nisan kwana,tare da lafiya mai amfani,ina godiya sosai da sosai Dad,kuma in shaa Allah zan maida hankalina sosai a kasunwancina,in shaa Allah zakuyi alfahari dani sosai,Mom ki tayani godiya ga Dad"



"Karka damu Auta,ai tuntuni na mia godiyarka ga Dad Winka"
Kallon mijin nata tayie haWi ta sakar masa murmushi mai ayatarws'a, shima murmusawa yayi sannan ya ce


"Bayan haka,magana ta gaba ita ce maganar auranka,shin akwai wacca kama alawari ?"


Duar da kansa yayi irin yaji kunyar nan,ya ce


"Eh Dad akwai wata wacca muka haWu da ita a can UK amma ita a can take da iyayenta,sunanta Fadila Marwan an galadima,sannan suna da kaka a Abuja,wacca take zuwa hutu wurinta,nasan ila Mom kinsanta,sunanta Hajiya Zulfa'u Sani Mai Gad........."



" What!! Hankalinka Sadam!! Jikar matsafa zaka kawo mana!!! "


Mom ce da wannan maganar jin an kira sunan wacca tayi silar rugujewar farin cikin ahalinsu,wacca tabar musu tabo a zukatansu,wacca har su mutu maza su manta da illar da ta musu ba,inaa Inaa.arawa tayi da cewa



"Ban yarda ka auro jikar matsafa ba gidan nan,tun daga kan Hausawa, fulani,shuwa arab,ethopia,india,saudia da dai sauran asashe kaje ka auro amma ban yarda da auro jikar matsafa ba "



Sadam da tun sanda ta daka mai tsawa,yayi shiru yana sauraron faWan da take masa,wanda ya daWe rabon Mom Winsa ta sama irin wannan faWan,in fact idan zai iya recalling to tun yana arami rabonsa da tayi masa faWa.BuWe baki Sadam yayi zaiyi magana Dad Winsa ya dakatar dashi da hannu tare da cewa




"Have patient Sadam! yi hauri da wannan yarinyar domin ni kaina ban yarda ka aureta ba,sannan kayiwa Mom Winka biyyaya ka naimi wata,Allah ya zaSarma wacca tafita zama alkhairi a gareka"



"Na haura da ita Mom,Allah ya bani wacca ta fita"



"Ameen"



Daddynsa ya amsa,ita kuwa Mom duk da taji daWin biyayyar da yayi mata,amma tuno a abubuwa da dama da suka faru shekaru aru aru,yasata zubda walla,murmushi tayi masa haWi da cewa



"Allah ya maka albarkha Auta,ya haskaka gobanka,ya kareka daga sharrin masu sharri,naji daWin yi mana biyyaya da kayi,in shaa Allah sai Allah ya baka wacca tafiya komai"


"Allah ya yarda Mom"



Daddy ne ya kallesa sannan ya ce



"Gobe sai kazo muje court domin kayi signing addarorinka in shaa Allah,sannan idan naga ka bada himma da wazo sauran addarorin zan dana mata don cigaba da kula dasu tunda yanzu tsufa ya fara tasomin"



"In shaa Allah Dad,ina godiya sosai Allah ya ara nisan kwana da lafiya mai amfani"



Da Ameen suka amsa masa kana yayi musu sallama ya wuce part Winsa wanda yake sama,duk da Fadila ce ta fara cewa tana sonsa amma yanzu kuma sonta ya fara shigarsa kaWan-kaWan




Waiwaye




*****A lokacin da Sadam yake a shekararsa ta uku a UK ya haWu da Fadila,ita kuma tana a shekarar ta biyu,a wurin taron musulman Nigeria suka haWu,kasancewar shi ne AMEER Win Walibai a makarantar,abinda yaja hankalin Fadila shi ne kyaunsa,wawalwarsa da miskilancinsa shi yake burgeta,gashi yanada saje a fuskarsa mai ara masa annuri haWi da kwarjini.



Bata Soye ba ta cuci kanta ta samesa,shi kuma a lokacin yana tare da abokinsa Sadiq suna zaune,tayi musu sallama haWe da gaishar dasu,Sadiq ne ya amsata amma Sadam ko kallon inda take baiyi ba,ya cigaba da sabgarsa,a nan ne ta bayyana soyayyar da take masa,wanda a arshe dayar Sadiq ya shawo kansa akan babu kyau wulaanta mutum,sai a sannan ne ys aminta suka fara soyyaya,har iyayen Fadila suka san da Sadam,Daddyn Fadila har Nigeria yasa akayi bincike akan Sadam,sannan ya aminta da auran nasu,wanda a yanzu komai ya taSarSare a duka Sangarorin guda biyu*****





Cikin labari




Bayan ya zauna a saman sofarsa ya kira Fadila don sanar mata suyi hauri da junansu tunda iyayensu basa so,daman duk rikita-rikitar da take faruwa a gidansu Kakarta Fadila duk ta sanar masa.



Haka dai suka haura da juna duk da a Sangaren Fadila ba haura tayi ba saida babu yadda ta iya tunda Sadam ya fita daga sabgarta,yayi deleting komai nata a wayarsa.


Sadam yanzu ya maida hankalinsa complete a harkar kasuwancinsa wanda maa shaa Allah komai yana tafiya yadda ya kamata.wannan kenan





@@@ @@@@@@





KADUNA



A Sangaren LOVE BIRDS=J wato Sauban da Maryam abubuwa ara zafafa suke.Kasancewar yanzu su Maryam suna IT kuma da wuri take dawowa gida,halayanta munana sai ara bayyana suke,gashi yanzu kwata-kwata basa shiri da surukarta kuma duk saboda halayanta ne.



Yau Saturday Sauban na gida suna hutawa a falo,ya dubi Maryam ya ce


"Dear ki shirya abinci ajima abokaina zasuzo,don Allah Maryam karki bani kunya gun friends Wina musammam Captain Fu'ad wanda tun asali ba son auranmu yake ba,please Maryam kiyi girki mai daWi wanda zasu yaba ba irin wanda kullun kikeyi muna asarar kayan abinci ba,na roeki "



Hannu bibbiyu yake roan Maryam don yasan idan aka samu matsala,shikenan Captain Fu'ad ya samu abin tsokanarsa.



Haka Maryam ta saka apron irin wararrun kuku Win nan ta shiga kitchen,tayi alawarin yau zata birge mijinta.(Har ni mai Waukan rahoto zanci hadWan girkin Maryam kuku=C=C=C)


Tayi tsawan awa huWu a kitchen tana kwaSe-kwaSe wanda ni kaina bansan mai take kwaSawa ba,duba da yadda take sharSan uban gumi,ta Sata tukane da robobi sun kai biyar ananu da manya,ga wani juice data haWa wanda bansan wani iri bane,ila sabon fitowa ne ohon mata>.Haka da sakasu a food warmers sannan ta jerasu a dining table,ta wuce Waki tayo wanka ta shirya tsaf don tarbar bain mijinta.



Da sallama suka shigo falon su uku,wato Sauban,Captain Fu'ad da kuma Waya abokinsu wanda yake aiki a Abuja sukazo.A falo suka babbaje suna hutawa sai Sauban ya mie don kiran amaryar tasa, gaban da dukan uku-uku akan Allah yasa tayi girkin hankali kar yaji kunya,samunta yayi tana chatting a wayarta tasha kwalliya abinta,kiranta yayi akan tazo su gaisa da abokansa,babu musu ta tashi zata fita,Sauban yayi Saurin ce mata


"Da

Please Login or Register in order to submit comment