Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

driver yazo ya Wauki Abban twins a Airport zuwa asibitin.Bayan sun isa asibitin,sai ya fito tare da nufar female ward na asibitin, direct numban Wakin da Dr. Nabila ta sanar masa can ya nufa.


Shiga Wakin yayi da sallama,cak! ya tsaya yana kallon Sa'eeda wacca take facing ™ofar Wakin,kallon ™urilla yake ma Sa'eeda babu ko ™yafta ido,itama kallonsa take cike da mamaki ganin mai kama sak da Ummanta,haske ne kawai bambamcinsu,suna a wannan yanayin ne sukaji tari mai ™arfi,da sauri kowa yakai duban wurin gadon,Umman Sa'eeda ce ta farka haWi da tari saboda ™irjinta zafi yake mata tare da azababban ciwon kai,da sauri kowa ya nufa gadon haWi dayi mata sannu,Abban twins ne yakai dubansa ga Umman Sa'eeda, lokaci guda ™irjinsa ya bada Darrammmm!!! Ganin kamarsu ta Saci,tabbas wannan ce Hussainarshi,tabbas ita ce Hussainarshi,cikin murya mai sanyi haWi da tsoro Abban Twins ya kira Umman Sa'eeda

"Hussaina"

Umman Sa'eeda dake cikin tsananin ciwo ta waiwaya da™yar inda aka kira sunanta,zaro idanu tayi waje ganin mai kama da ita sak! Hannu na rawa Umman Sa'eeda take nuna Abban Twins tana cewa


"Hhassann Hassannn kaine ba'a mafarki ba,kaine! Kaine,ku cemin ba mafarki nake ba,Hassan Wina ne ya dawo gareni,mama kullun cikin cewa take zamu haWu,zamu haWuuuu.......?

Fashewa Umman Sa'eeda tayi da matsananci kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai sauraronta,da Sauri Abban Twins ya iso gunta tare da ri™o hannunta wanda ba'asa canular ba,shima kukan ya fara ganin ´ar uwar wacca yake mutuwar so da ™auna,babu ranar da zatazo mishi ta wuce ba tare da yayi tunanin ´ar uwarsa da mamansa ba,kullum tunani yake a wani hali suke? Wani irin rayuwa sukeyi?  A ina suke? Me suke ci? Me suke sha? Wani irin muhalli suke a ciki,me,me tambayoyi bila adadin yake ma kansa a kullum. Saboda zuciyar ta kasa yarda sun mutu,kullum zuciyarsa ce masa take suna nan lokacin huWuwarsu ne baiyi ba.Cikin kuka Abban Twins ya fara magana wanda ba kowa ke jin abinda yake faWa ba

" Mmmama fa,tana ina itaaa"

Wani sabon kuka Umman Sa'eeda ta fashe dashi tuno da Mamanta tare da wahalhalun da suka sha a baya,girgiza kai Umman Sa'eeda take tana kuka,ga raWaWin ciwo da duk ilahirin jikin yake gashi yanzu an tuno mata da rayuwarsu ta baya.Babu wanda a cikin Wakin bai zubda hawaye ba saboda yadda suke kuka zai tabbatar maka sunyi kewar juna domin jini ba wata bane,tun daga kan Dr. Nabila,Iman tare da uwar gayya Sa'eeda kuka suke sosai saboda tausayin da ya shigesu,baka jin  maganar kowa a cikinsu saidai shasshe™a haWi da jan majina.

Suna a wannan yanayin ne saiga Likita ya shigo Wakin tare da nurse,turus yayi a tsakiyar Wakin ganin yadda kowa yake zubda ™walla shi a tunaninshi ko patient Winsa ne ta rasu,amma daya ™ara kallon gadon mara lafiyar sai ya ga itama kukan take sosai,fuskar likitan ne ta sauya,cikin Sacin rai ya fara magana

"Haba don Allah, wani irin abu ne haka,ku da zaku kwantar mata hankali amma ku kuke ™ara saka kuka da  damuwa,please kuje waje ku zauna tana bu™atar hutu yanzu sannan inaso na ™ara dubata"

Babu musu kowa ya fita har Abban Twins wanda ji yake idan ya fita wani abu zai iya samun ´ar uwarsa,a kujerun dake a receptionist suka zauna,cikin Wumbin farin ciki Dr. Nabila ta fara kiran ´an uwansu da abokan arzi™i kama daga wa'inda suke a Kebbi,Kano,Abuja,har wa'inda suke a ™asashan waje duk ta kira ta sanar musu da ganin su Umman Sa'eeda da tayi.koda aka sanar ma Momin Sadam akan bayyanarsu Umman Sa'eeda ai a rikice tare da Wumbin farin ciki  tace gata nan zuwa yau Win nan ba sai gobe ba.

Kiran daddyn Sadam tayi a waya tana sanar mishi da anga su Hussaina amma tana asibiti dasu Hassan da matarsa,shima farin ciki yayi sosai,kasancewar baya ™asar da dashi za'a je amma yana dawowa zuwa jibi zai shigo Kadunan,kamar yadda Dr. Nabila taiyi ta sanar ma ´an uwansu bayyanarsu Umman Sa'eeda haka itama Momin Sadam tayi harda abokan arzi™i,hatta yaranta duk suma ta sanar musu.Koda Dr. Nabila ta sanar ma mahaifinta kuka ya fashe dashi,yana cewa akaishi kun ´ar uwarsa,shidai akaishi gun ´ar uwarsa,ha™uri akaita bashi akan ita ´ar uwar tashi ta rasu,Wiyarta ce Hussaina da ´arta aka gansu,duk da haka hankalinsa ya™i kwanciya wai shi ko yaranta ne sai an kaishi ya gansu,kunsan tsofaffi da kafiya,da ™yar aka shawo kansa da dubara akan gobe za'a kawoshi wurinsu,da wannan bayanin tsoho mai ran ™arfi hankalinsa ya kwanta.

Kasancewar da safe lamarin ya afku,Momin Sa'eeda sai wurin 5:18pm na yamma ta iso Kaduna tare da motoci har Uku masu kare lafiyarta,direct asibitin suka nufa da jiniya,koda suka iso asibitin, Momin Sadam bata jira an buWe mata ™ofa ba,ta fito da kanta tana sauri haWi ta sassarfa ta wuce female ward har Wakin da aka kwantar dasu Umman Sa'eeda tare da bodygaurd har uku,a ™ofar Wakin bodygaurd Win suka tsaya ita kuma ta shiga ciki da sallama,amsa mata sallamar ´an Wakin sukayi,cike da murna Dr. Nabila ta rungume favourite Auntynta,itama Momin Sadam ™ara rugumeta tayi sosai,sai a sannan ne Momin Sadam da hangi Sa'eeda wacca take a ra™ube kusa da Ummanta a kan gado,sakin Dr. Nabila tayi tana nuna Sa'eeda tare da cewa

"Amma daga gani ko ba'a faWa ba wannan ce ´ar Hussaina ko"

Murmushi Dr.Nabila tayi tana cewa

"Tabbas kuwa,sunanta Sa'eeda "

"Maa shaa Allah, tabarakallah,zo nan my gorgeous daughter "

Sauka Sa'eeda tayi daga kan gadon ta tako har inda Momin Sadam take tana Wan murmushi,russunawa tayi zata gaisheta,Momin Sadam tayi saurin ri™ota haWi da rungumeta tsamm! A jikinta,Wagota tayi tana cewa

"Maa shaa Allah, wannan kama haka,ai sai nace Wiyar Hassan ce"

Dariya Dr. Nabila tayi sannan tace

"Bake kaWai ba Aunty wallahi farkon ganin da nama Sa'eeda saida gabana yayi mugun faWuwa,saboda tsantsar kamar da suke da Abban Twins, kasa ha™uri nayi na tambayi sunanta da garin da mahaifinta yake,da ta cemin ita ´ar Kaduna ce,sai kawai na basar,kinsan kusan kullum saina ma Abban Twins maganar Sa'eeda, dayake Allah bai ™addara a lokacin zance ta kaini wurin mahaifiyarta ba,sai yanzu da Allah ya nufa da haWuwa mu ta hanyar accident"

"Ikon Allah kenan,ita Hussaina bacci take kenan"

"Eh wallahi, Abban Twins ma bai daWe da fita ba saig....."

"Assalamu Alaikum"

Juyawa sukayi dukkaninsu tare da amsa mashi sallama, Momin Sadam ce da murmushi take cewa

"Šan halak ka™i ambato,yanzu muke maganarka sai kuma gaka"

Murmushi Abban Twins yayi duk da ransa a Sace yake tun sanda shida Sa'eeda sukaje gidansu Sa'eeda da niyyar sanarma Abbansu Sa'eeda halin da Umman Sa'eeda take a ciki wanda saida suka kusa yin faWa da Abban Sa'eeda kasancewar ba'a hayyacinsa yake ba


*WAIWAYE*


-------lokacin da likita ya ce masu Sa'eeda su fito domin Umman Sa'eeda ta samu hutu,Abban Twins ne ya cema Sa'eeda tazo suje gidansu su Wauko kayayyankin da Umman Sa'eeda zata bu™ata sannan sai su sanar ma mahaifinta rashin lafiyar Ummanta,babu musu ta bishi suka tafi,ita ce a gaban mota tare da driver,shi kuma yana mazaunin baya,nunama driver hanya take har suka iso  ™ofar gidansu,bayan sun sauka daga motan,Abban Twins sai dube-dube yake yana ™arema gidan kallo,a zuciyarsa yana cewa 'Yanzu haka Hussaina kike rayuwa a wannan kurkukun gidan,ya Salam!!! Farin cikinki yazo Hussaina keda ´arki da izinin Allah, farin cikin da kika gaza samu tun kina yarinya,shi yanzu zaki samu,zan samar muku da farin ciki dawwamamme in shaa Allah, lokaci yayi na Waukar fansa!!! Tabbas lokacin bayyanarmu ga dangin mahaifinmu tare da ™watar hak™inmu yazo!!! ' Yana wannan tunanin ne Sa'eeda ta katse mishi tunani da cewa

"Uncle gáma Abbana can ma a majalisarsu basai an kira shi ba"

Hannunta take nuna inda Abbanta yake zauna a majalisar layin kasancewar yau baije kasuwa ba,inda hannunta yake nunawa nan Uncle Hassan yakai dubansa ga mutanan wurin,ce mata yayi tazo suje ta nuna mai Abban nata ,babu musu ta bisa har majalisar inda su Abban Sa'eeda suke zaune,sallama yayi musu haWi da yima kowannansu musabiha sannan ya ™ara da cewa

"Don Allah Abban Sa'eeda nake nema"

Abban Sa'eeda da tunda ya hango Sa'eeda annurin fuskarsa ta Wauke gabaki Waya ya fara mishi magana da faWa wanda har ´an majalisar saida sukayi mamaki wasu harda ri™e baki

"Ba Abban Sa'eeda ba saidai uban Abban Sa'eeda!!!  Ni banda wata Wiya Sa'eeda saidai daga,Musa,Nusaiba,Zaliha da Iklima amma bansan wata Sa'eeda ba"

Wani a ´an majalisar ya kasa ha™uri ya ce

"Haba Sule yanzu ´artaka Sa'eeda kake cewa baka santa ba,wai ina hankalinta yaje ne Sule,mai ya shiga ™wa™walwarka ne,haba! "

Shima wani daga cikin ´an majalisar ya ™ara da cewa

"A gaskiya wannan halin da kake nunawa ´arka tare da mahaifiyarta ba daidai bane wallahi, yanzu kalla fa kuka take "

Nuna Sa'eeda yayi wacca tun sanda Abbanta ya ce ita ba ´arshi bace ta fara kuka, cigaba da maganar yayi

"Yanzu kaji Wadi da tozarta ´arka ta cikinka da kayi a gaban kowa tare da ba™onka wanda bakasan mai yazo wurinka dashi ba Sule,yanzu kayi abinda ya dace kenan Sule"

³an majalisar ne sukai mishi caaaa!!! Akan abinda ya faWa ba daidai bane,shi kuma Uncle Hassan ido ya zubama Abban Sa'eeda ko magana ya kasa jin wannan irin tozarci haWi da Satanci daya jefi ´arsa dashi,hakan ya nuna Hussaina ba jin daWin zaman auran take ba ita da ´arta,shi kuma Abban Sa'eeda ko a jikinshi,duk maganar da zasuyi saidai ya taSe baki irin Oho dai ku kuka sani.Cikin murya mai nuna Sacin rai da damuwa Uncle Hassan ya fara magana wanda kowa a wurin saida yayi mamaki banda Abban Sa'eeda kasancewar baya cikin hayyacinsa,cewa yayi

"Naji abinda ka ce,sannan daga yau Hussaina da Sa'eeda sumbar gidanka da zama,bancin ™addarar da  tasame mu,wallah da baka isa ka tsaya  Waya daga cikin jerin da Hussaina ya cancanta ta aura ba,domin tun daga kallon kurkukun gidanka na tabbata ba mutumin arzi™i bane,kuma ilai sai gashi ko faWa maka abinda yake tafe dani baka tsaya kaji ba,ka fara nuna min halin Wan akuya! Well daman nazo sanar maka da Hussaina tayi accident wanda kuma shi ne mafarin haduwanta da asalin ahalinta wato ´an uwanta da ni Win nan "

Nuna kansa yayi sannan ya ™ara da cewa

"Ni ne Hassan Winta,yanzu banda ta cewa saboda Hussainata tana asibiti, amma kasani duk randa ta ce ta gaji da zaman aure dakai to ka tabbata rabuwarku tazo kenan,yanzu ma kaci darajar Hussainata ne da kuma ´arka wacca ka tozarta if not da nasa a Waureka a gidan kaso Waurin rai da rai,amma ka kula nan gaba domin ba'a shiga gobar Hassan Sani Mai Gado a zauna lafiya koma uban waye"

TaSe baki Abban Sa'eeda yayi tare da cewa

"Oho dai,can ta matse muku a matse-matsin hammata,ku tafi can ku ™arata,shikenan na jefar da ™wallon mangwaro na huta da ™uda,Mtwss! Aikin bazan! "

Uncle Hassan bai sake bi takan zantuttukan Abban Sa'eeda ba yaja hannun Sa'eeda suka tafi wacca har a lokacin  kuka takeyi sosai gwanin ban tausayi,cikin Sacin rai ya ce ta shiga ciki ta Wauko duka credentials Winta dana Ummanta banda kayansu ta fito yana jiranta,haka Sa'eeda ta shiga gidan da sallama amma shiru alamun ba kowa duk da koda akwai mutane ba amsa mata sallamar za'ayi ba koda yake yanzu idan Jummalo ko Iklima suna waje sukan amsa musa sallama ita da Ummanta, kasancewar akwai extra key a hannunta dashi ta buWe Wakin haWi ta fito da duk abinsu mai amfani banda kaya,Wan akwati ™arami ta fito dashi waje,tana niyyar kulle Wakin saigasu Umma Kande da Maman Jummalo amma ita Maman Jummalo akwai ni™af a fuskarta kasancewar yanzu da ni™af take yawo,tsayawa sukayi baki buWe suna kallon Sa'eeda, murmushi ta musu tare da cewa

"To Umma Kande da Maman Jummalo a yayyafe,domin yau zamu bar muku gidanku nida Ummanta, wanda kuka gani a waje shi ne Uncle Hassan wato abokin haihuwar Ummina nazo tare dashi ne domin Waukan muhimman abubuwanmu,wata ™ila bazamu sake haWuwa ba sai a *DARRUS-SALAM* mu yafi juna,nasan Ummana ta daWe da yafe muku......."

Bata ™arasa maganar ba taji horn Win mota alamun ana jiranta,da sauri ta Wau Wan akwatinsu tare da yi musu sallama sai wataran tana murmushi ta fita,na mujiya kowaccansu ta bita dashi tare da taSe baki irin ko ajikinsu Win nan.Umma Kande ta ce

"A tafi can a ™arata,mundai yada ™wallon mangwaro mun huta da ™uda,yanzu zamu baje mu Sararraje abinmu"

Maman Jummalo dai bata ce komai ba,ta wuce Wakinta tare da buWewa ta shiga ciki,ita kuma uwar gayyar saida ta ™ara fita waje don ganin ™wa™waf saboda tun Sullowarsu layin motar take wal™iya a tunaninsu ko ´a´an ne wata tayi sabon kamu.(Su Umma Kande badai gulma da ganin ™wa™waf,to tafaru ta ™are,sai abi wani sarkin domin Su Sa'eeda sun muku nisa=ØŞ=ØŞ=ØŞ=ØCŞ=ØCŞ=ØCŞ)

Koda Sa'eeda ta fito,samun Uncle Winta tayi a cikin mota,wannan karon a baya ta zauna,driver yaja musu motan,umarni Uncle Hassan ya bada akan su wuce supermarket zasuyi siyayya,cikin ladabi ya amsama mai gidan nasa duk da yaga alamu kamar amSata masa rai,direct suka nufi wani haWadWan supermarket na gani na faWa,cema Sa'eeda yayi tafito,babu musu ta fita tare da bin bayansa suka nufi cikin supermarket Win.Wooow!!! Kawai zan iya cewa domin babu abinda zaka gaza samu a wannan ™ayataccan supermarket wanda sai wa'inda sukaci suka tadá sannan suke zuwa shopping a cikinsa,suna shiga Uncle Hassan ya cema Sa'eeda ta zaSa musu duk abinda suke bukatar tun daga kan kayan wasa,cosmetics,da dai sauransu,haka ta fara Wiban musu kayan kaWan-kaWan,Uncle Hassan daya ga Sa'eeda shirme takeyi kawai ya fara jidar kaya kamar za'a buWe wani sabon shago,haka suka gama shopping,su kuma ma'aikanta supermarket Win suna biye dasu ni™i-ni™i da kayan har wurin biyan kuWi,direct ya ciro ATM card Win ya bada bayan an sanar masa ma™udan kuWin da kayan sukaci amma ko ajikinsa hasalima ce musu yayi suyi sauri suna Sata mishi lokaci,daskarewa Sa'eeda tayi tun sanda aka faWi ma™udan kuWin kayan,ita a tunanin zaice a rage kayan sunyi kuWi dayawa amma ko ajikinsa haka ya cire ATM card Winsa ya biya.Fitowa sukayi daga supermarket Win tare da ma'aikanta wa'inda suka fito musu da kayan zuwa boot Win motar,driver ne ya taimaka suka saka kayan complete sannan yaja musu motar,nan ma ™ara tambayar mai gidansa yayi cike da girmamawa akan ina suka dosa,ce masa yayi plazan da Dr. Nabila take kai Winkunanta zai kaisu,haka ya jasu zuwa plazan,nan ma basu Sata lokaci ba aka gwada Sa'eeda tare da bata kayan da suka siya daga supermarket domim a Winka masu , kasancewar Umman Sa'eeda baza'a iya gwadata ba,saidai estimation Sa'eeda tama telan da zai musu Winkin,nan ma Uncle Hassan tranfer Win ma™udan kuWin da za'a musu Winki ita da Ummanta yayi,sai suka wuce direct zuwa asibiti. Wannan kenan----




*Cikin labari*


Zama ya samu yayi tare dayiwa Momin Sadam sannu da zuwa,sai ya ce

"Nifa ina tunanin zansa ayi ma Hussaina Visa sai mu wuce da ita can Germany a dubata don gaskiya bana tunanin likitocin nan sun ™ware sosai "

"Wannan tunani ne mai kyau,amma mai zai hana ayi mata Visar India kaga sai mu tafi tare wurin likitan da yake dubani nida Alhaji kaga yafi sau™i tunda kai  course zai kaika Germany ba jinya ba,koya kace" cewar Momin Sadam tana murmushi

"Haba ai duk Waya ne,bara na kira can immagration office insa ayi mata International passport ,sai ku wuce jibi amma inso samu ne gobe saisu ku wucd,don ™ila  gobe zan wuce Germany dama ™addarar haWuwa da ´ar uwata ce tasa na jin kirta tafiyar"

"Ok,bara na sanar ma Daddyn Sadam yasan da tafiya tamu kaga sai shima yázo can Win dama ya ce immediately yana dawowa zaizo nan"

"Ok toh ba matsala ai"

Shiru Wakin yayi kowa na zancen zuci,can Dr. Nabila ta katse shirun da cewa

"Kai! Shida ta kusa bara na kira larai taje ita da driver su Waukosu Afnan daga school"

"Iyayan rigima ba,tana nan dai da halinta da ™in mutane ko"

"A'a Aunty ai duk wannan rashin son mutanan duk ta daina yanzu"

"Hmmm Allah yasa dai"

Dariya sukayi sai sannan Dr. Nabila ta tambayi Sa'eeda ina Friend Winta take,sanar mata tayi ai tun sanda zasu je ita da Uncle Hassan gidansu tayi mata sallama.

Haka suka zauna har kusan 8:00pm wanda sallah ce take tashinsu suyi shi kuma Uncle Hassan sai ya tafi masallaci.Sai wurin 9:12pm na dare Dr. Nabila da Sa'eeda haWi da Uncle Hassan da yaransu suka wuce gida tare da barin Momin Sadam a asibiti bayan mai aikinsu Dr. Nabila ta aiko musu abinci tare da yaran.

A ranar Uncle Hassan ya sanar ma abokinsa wanda babba ne a offishin Immigration akan maganar International passport tare da yi musu Visa zuwa India,abunka da kuWi nan da nan Visa ta fito washe gari,haka sukayi ta shirye-shiryan tafiya zuwa India, kasancewar Sa'eeda har yanzu basuyi hutu ba yasa bada ita za'a tafi ba sai bayan exams zasu wuce Kebbi ita da Dr. Nabila domin za'a shiryama su Umman Sa'eeda ™yataccan liyafar murnar dawowansu cikin ahalinsu.

Washe gari Jirginsu Umman Sa'eeda tare da Momin Sadam ya lula sararin samaniya zuwa ™asar India,sai daga baya jirginsu Uncle Hassan wato Abban Twins ya Waga zuwa Germany.Wannan kenan.


            @@@@ @@@@@@@@@


A Sangaren  *LOVE BIRDS*  =ØJİş=ØJİş wato Sauban da Maryam kuwa abubuwa ™ara rincaSe musu yayi,domin ranar da Maryam ta dawo gidan ranar wannan lamarin ya afku,kasancewar Maryam ta suma sanda Sauban ya kaita asibiti, sanda kuma ta farfaWo shi kuma lokacin yaje Wauko musu kayan da zasu bu™ata a asibitin, da ihu haWi da kururuwa ta farka tana cewa

"Wallahi baka isa ba Sauban!!! Bazan zauna da kishiya ba Sauban!!! Ni kaWai ce matarka ta duniya da lahira Sauban!!! Babu wata macan da ta isa ta raSeka Saubannn!!! "

Da ™arfi take maganar tare da fizge canular da aka saka mata a hannu,jini na zuba amma bata bi takan jinin ba tayo hanyar waje,wata nurse tazo wucewa ta ™ofar taji wannan surutan da sauri ta kirawo wasu nurses Win don su duba kodai mahaukaciya ce aka kawo musu, da sauri suka shiga cikin Wakin,koda suka shiga ita kuma Maryam tanada niyyar fita sai suka kusa cin karo da wata nurse,jiki da rawa idanu sunyi ja sosai Maryam ta cema wata nurse wacca take suka da ita

"Šan aramin wayarki don Allah nayi kira yanzu zan baki"

A tsora ce nurse Win ta mi™a ma Maryam wayar,domin duk wanda yaga Maryam a wannan yanayin dole ya tsorata saboda zakayi tunanin mahaukaciya ce,ganin gashinta duk a birkice yake,ga idanunta duk sunyi ja,kayan jikinta a yage suke saboda damban da sukaci da Sauban.Amsar wayan tayi haWi da saka numban wayar mominta ta kira,wayar na ringing amma ba'a Wauka ba,saida ta kira kusan sau hudu kana a akayi picking,sallama acan aka mata,bata amsamata sallama bata fashe da kuka,su dai nurses Win suna kallon ikon Allah

"Mom! Mom! Mom Sauban ya cuceni! Kishiya zaimin Mom!  ´ar uwarsa zai aura Mom!,har dukana yayi daga dawowana yanzu ma ankwantar dani a asibiti Mom"

Cikin tashin hankali Momin Maryam ta tambayi wani asibiti ne aka kwantar da ita,saida  Maryam ta tambayi sunan asibitin haWi da numban Wakin sannan ta sanar mata,cike da Sacin rai Momin Maryam ta kashe wayar tare da nemo numban Hajiya Laraba wato babbar yayarsu tare da sanar mata abinda ya faru da Maryam harda dukan da Sauban yama Maryam Win,ita ma rai Sace ta ce ina ne asibitin da aka kwantar da ita,sanar mata tayi sanna ta katse kiran haWi da mi™ewa ta nufi bedroom Winta don shiryawa,tana cikin shiri saiga Daddyn Maryam ya shigo gidan da sallama, amsa masa tayi,bata bari ya zauna ba ta sanar masa da abinda ke faruwa da Maryam shima hankalinsa ya tashi matu™a ainun jin tilon  ´arsa na a asibitin saboda duka,to ma wani irin duka ne Sauban ya mata da har saida aka haWa da asibiti.Ce mata yayi ta shirya su wuce asibitin dashi don zama baigansa ba.haka suka Wunguma zuwa asibitin.

A Sangaren Hajiya Laraba kiran Mahaifiyar Sauban tayi tare da zazzaga mata masifa akan dukan da Wanta yayima Maryam, kasancewar Momin Sauban itama ba kwanwar lasa bacd,hayayya™o mata tayi itama da masifa,faWan kaci uwaka kaci ubanka Hajiya Laraba da Momin Sauban sukayi,katse kiran Momin Sauban tayi tare da saurin nemo namban Sauban,bugu Waya ana biyu ya Waga kiran,cikin  girmamawa Sauban ya fara gaisheta,bata amsa masa ba sai jefo masa tambayar bazata da tayi,tana cewa

"Me Maryam tayi ka duketa  harda zuwa asibiti Sauban"

Bai Soye mata komai akan abinda ya faru,tun daga dawowarta,da fashe-fashan da tayi da haukan da tayi masa,bai cire komai ba ya sanar mata.Shiru tayi sai can ta tambayi yanzu yana ina,ce mata yayi yana gida yazo Waukan kayan da zasu bu™ata,a nan ta ce masa karya kuskura ™afarsa ta taka zuwa asibiti domin idan yaje akwai matsala babba,cikin mamaki Sauban ya tambayi Momin akan wace irin matsala ce haka,faWa masa tayi faWan da sukayi da Hajiya Laraba wato Auntyn Maryam sannan tasan definitely iyayenta zasuzo asibitin yanzu tare da ita kanta Hajiya Larabar,don haka kawai yabar zuwa asibitin yanzu ya bari sai gobe idan ta dawo daga Zaria sai suje tare,amsa mata yayi da to sannan sukayi sallama,kwanciyarsa yayi a bedroom Winsa tare buWe shafukan tunaninsa wanda shi kansa baisan wanne ya dace ya fara Wauka ba,a gaskiya kwanan nan baya samun natsuwa tare da kwanciyar hankali,gashi komai nasa taSarSarewa yake anya Maryam bata shigo gidanshi da *farar ™afa* ba kuwa,domin har a wurin aikinsa sai a hankali yanzu,yadda yake samun kuWi ada yanzu baya samu sosai.Haka dai Sauban yayita tunaninsa daya gama wannan tunanin sai ya koma kan wancan har bacci Sarawo ya sacesa.

A Sangarensu Maryam da iyayenta kamar Momin Sauban ta sani,jiran Sauban  suke don su tugumesa akan irin wannan dukan dayama Maryam, shiru-shiru babu Sauban babu alamunsa,haka suka gaji suka wuce gida bayan ambar Hajiya Laraba da jinyar Maryam.

Washe gari saiga Momin Sauban ta dayo gidan da safe kasancewar duk hankalinta ya dawo gida domin taga abinda ke faruwa.Ko zama batayi ba suka shirya ita da Sauban suka nufi asibitin,a can suka iske iyayen Maryam Win sunzo suma duba ta *Wuta iya Wuta* domin wani sabon ya™in duniya<Ø
ß<Ø
ß<Ø
ß na huWu ya kaure a asibitin, faWa iya faWa anyi harda ™annan Sauban tare da yayyinsa saida sukazo domin Momin Sauban kiran kowannansu tayi a waya tare da sanar musu abinda ke faruwa,babu Sata lokaci dukkaninsu suka hallara a asibitin, danginsu Maryam  ma suma sunzo,asibitin kacamewa yayi da hayaniya sosai wanda a ™arshe ma'aikatan asibitin suka koresu waje tare da sallamar Maryam Win,a nan Daddyn Maryam ya ce sai Sauban ys saki Maryam don bazata zauna da kishiya ba,amma buWar bakin Momin Sauban ta ce ai shida Maryam mutu ka raba takalmin kaza ko bayan ranta babu shi babu sakin Maryam badai sunce danginsu basa zama da kishiya ba to akan Maryam zasu Wau darasin zama da kishiya ko sun™i ko sunso,kuma a shirye suke koda ™uliya manta sabo ne suka kaisu  babu gudu babu ja da baya.Haka iyayen Maryam suka wuce da Maryam gidansu.

Ita kuma Momin Sauban ta sanar ma ™anwarta akan ta faWama mijinta a saka ranar Sauban da khairat nan kusa ta fasa sai khairat Win ta dawo ™asar,domin sai ta tabbatar ma Hajiya Labara da duk ilahirin danginsu ita ba kanwar lasa bace,ita buhun ™aya ce tafi ™arfin danna,sannan duk wanda taci tuwo da ita ya tabbata miya yasha domin wasan yanzu za'a fara.

Kamar yadda Momin Sauban ta umurta a saka ranar Sauban da Khairat nan kusa haka mahaifin Khairat yayi kasancewar shi dama tuntuni yaso ayi auran a huta amma akace sai khairat Win ta dawo.Wannan kenan.


         @@@@@@@@@@@@


A Sangaren su Umma Kande da Maman Jummalo duniya ta fara musu juyin waina,musamman Maman Jummalo domin yanzu ta rame tayi ba™i sosai,kullum cikin ciwo take,ga shegen kwaWayi da takeyi yanzu,tun sanda cikinta ya fara girma ta daina yawo  babu ni™af,kullum cikin saka ni™af take kamar wata matar liman idan zata fita.


Yauma zaune suke a ™ofar Wakinsu Sa'eeda kasancewar tunda Sa'eeda tayi musu sallama ™ofar Wakinsu ya koma wurin shan iskarsu,Umma Kande ce  ta kasa ha™uri ganin yadda ™awarta ta koma gwanin ban tausayi,cikin sanyin murya Umma Kande ta fara magana


"˜awas anya ba komawa wurin boka Sankeru zamuyi ba,ko za'a samu wata mafitar gane da cikin nan? "


Maman Jummalo ce ta mata wani mugun kallo  tare da cewa.............





*Mu haWu a pages na gaba my Esteem Fans*
'ş
'ş
'ş=ØCŞ=ØCŞ=ØCŞ



*Me Maman Jummalo take shirin cema Umma Kande???  Shin zata yadda su ™ara zuwa wurin boka Sankeru kuwa???*.......



*Ganin yadda Momin Sauban ta zafafa akan Sauban bazai saki Maryam ba dole sai ta zauna da kishiya, shin wani irin mataki kuke tunanin iyayen Maryam zasu Wauka ganin

Please Login or Register in order to submit comment