Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

falon tare da sallama.Sa'eeda da tunda taji parking Win motoci irjinta ya bada Ras! arin bugun irjinta shi ne sanda su Jawaad suka ce ga Uncle Sadam,wai wani irin abu ne haka,why all these,miye dalilin bugun zuciyarta idan taji sunansa huh! Katse mata tunani sallamarsu Sadam tayi,Dr. Nabila ce ta amsa musu da murmushi a fuskarta,ita ko Sa'eeda Waure fuska tayi irin bata Waukar rainin nan,tayi kitin-kitin da fuska kamar mai shirin kuka ko kuma an Sata mata rai,zama yayi a kujerar da take facing Win Sa'eeda tare da gaida Dr. Nabila cikin cold deep voice Winsa,maganarsa a tsanake yake yinta kamar wani basarake,cike kuma da izza yake gaisheta,kasancewar Dr. Nabila tasan haka Wabi'arsa take tun yana yaro haka yake magana shiyasa bata damu ba,amsa masa tayi cike da kulawa tana cewa


"Ai na zaci ka wuce kamfanin sanda na barka ashe bata tafi ba a lokacin"


Cikin cold deep voice Winsa ya amsa mata da cewa


"Eh wallahi,akwai wasu ayyuka da nake shirin kammala kafin na tafi a lokacin"

"Ayya! Sai kuma ka tsoratamin daughter ko Sadam"


Dariya ce ta taso masa amma sai kuma ya gimtse,cikin Waure fuska irin kar Sa'eeda ta kawo mishi raini yace


"Daman kinada daughters ne banda su Kauthar"

Wani tuui ne yaje malolan wuyan Sa'eeda ya tsaya,lallai ma wannan aton wato a tunaninsa da gan-gan ta tsoratani kenan,daman ashe yana magana shi ne yayi banza da ita ko,huh baisan wace ce Sa'eeda bane,katse mata tunani Dr. Nabila tayi da cewa


"Cousin Winka mana Sadam,sunanta Sa'eeda,nasan halinka da basarwa,ce nake Aunty ta sanar maka da bayyanar Hussainan Abban twins da arta"


"Eh ta sanar min suna ma India tare,amma ai ni bansan yarinyarta ba"

"Hakane kuma,ke Sa'eeda bakiga yayanki Sadam bane,duk da Wazo ka tsorata ta har taso ta tsoratani da badan tamin baya ni da nima tsorata zanyi"


Dariya take shirin taso masa amma ya dake,a zuciyarsa ta cewa 'Au ashe matsoraciya ce ma kenan' magana Dr. Nabila ta katseshi da cewa

"Au da gaske ne ka tsorata ta da gan-gan Sadam, yarinya duk tabi ta rikice...."


Bata arasa maganar ba Sadam yace


"Calm down Aunty bani na tsorata ta ba,ita dai ne taso ta tsorata kanta,batamin magana in a good manner ba,how did you expect me to give her answer,cewa tayi mutum ko aljan,to na mata kama da aljani ne ko kuma taga kofato ne a afata"


"To dai komai ya wuce Sadam,ke Sa'eeda nace ga yayanki ku gaisa amma kinyi shiru"


Sa'eeda da da lula duniyar tunani,tana ayyana abubuwa dayawa tare da neman yadda zata rama tsoratatan da yayi mata,taji Dr. Nabila na sake jefo mata tambayar bata gaisheshi ba,gaisuwa fa yooo mutumin da ya rikita ta Wazu ne zata gaisar,tabb saidai to ita bata iya rashin kunya bane,da wallahi babu abinda zaisa ta gaidasa,cikin zazzaar muryarta ta ce

"Ina wuri,fatan kazo lafiya?ya aiki? Ya gida? Ya iyali? ya rayuwa? "


Lokaci guda ta masa tambayin duk don kar ta sake mishi magana,shi kuwa gogan tun sanda ta fara magana irjinsa ya bada Ras! Why hakan ke faruwa dashi ne game da wannan yarinyar,meyasa muryarta take mishi daWi ne,har so yake tayi magana duk don yaji muryarta why! Why! Why! All this is happening to him,katse mishi tunani Dr. Nabila tayi da cewa


"Sadam ya tana gaidaka amma shiru kai bata amsa,ai irin haka da kayi ne Wazu ta tsorata"

"Sorry,kowa da komai na lafiya Alhamdulillah"


Shima amsar ya bata a dunule don yaga sai wani ciccijewa take tana kitin-kitin da fuska,Dr. Nabila ta ce

"To can kamfanin fatan komai yana tafiya daidai babu wata matsala"

"Eh Aunty Alhamdulillah,komai yana tafiya a yadda na tsara,sannan wannan handama da babakeran da manager tare da wasu daga cikin ma'aikatan da sukeyi duk na daile hanyoyinsu baki Waya"


*Waiwaye*


A lokacin da Sa'eeda ta ruga sama da gudu,shima dariya ya tintsire dashi harda bubbuga afa cigaba da aikinsa a laptop sai kuma can ya kashe laptop Win tare da miewa ya fito waje,P.A Winsa ne mai suna Mukhtar ya iso inda yake da sauri yana cewa


"Barkha da fitowa yallaSai"

Bai amsa masa ba sai suka nufi inda motocinsu suke ,da sauri wani bodygaurd Winsa ya buWe masa mota ya shiga,sai shi kuma Mukhtar ya zauna a front seat,drivan ne ya tambayi Sadam cike da girmamawa akan ina zasu,ce masa yayi *Rice company* wato kamfanin sarrarfa shinkafa ,babu musu yaja motar tare da sanar ma sauran drivers na motocin biyu,a tsakiya motar da Sadam yake ta ciki take, gaba da bayan duk bodygaurd Winsa ne masu baakyan suit,haka suka isa kamfani babu Sata lokaci kasancewar akwai jiniya a motar bodygaurds Win shiyasa suka iso da wuri.

A Sangaren manager wato Sauban da ma'aikatan kamfanin duk sunyi cirko-cirko a cikin kamfanin suna jira zuwan *CEO* Winsu wato *Sadam Dauda Gali Mai Nasara* mazansu da matansu kowa murna yake tare da osawan zuwan mai gidansu banda manager wato Sauban da tsirarun wasu ma'aikatan masu handama da babakere a kamfanin,dan P.A Winsa Mukhtar ya daWe da sanar da suna hanya,shiyasa dukkanin ma'aikatan harda masu shara,gida,securities duk sun hallara.Ma'aikatan mata sai gyara fuskarsu suke,wasu ma harda ara powder da jan baki ko Allah zaisa ya taya,duk da sunji raWe-raWin baya kula mace duk kyawunta.

Jiniya suka da alama mai gidan ne ya iso,ai da sauri mai gida ya wangame gate ,sai motocin suka danno cikin kamfanin da gudu,direct suka isa inda ma'aikatan suke a tsaye,motoci ne suka tsaya,da sauri bodygaurd suka firfita har da P.A sai kuma wani bodygaurd ya buWe kofar inda Sadam yake ciki,afarsa na dama ya fara fiddowa sai da yakai kusan mintuna uku kafin ya fito complete,Wooow! Wasu daga cikin ma'aikatan mata suka faWa,nima mai Wauko muku rahoto juyawa nayi don ganin meya sakasu irin wannan shaui haka, ai babu shiri nima na furta Wooow! Ba tare da nasan sanda kalmar ta fito ba,domin dole duk macan da tayi arba da Sadam ta ruWe,saboda Wan gaye ne na ajin farko,kyakkyawa ne sosai,ga sajensa yayi luf! Gwanin ban sha'awa,sumar kansa da gemunsa duk sun sha gyara,kai daga gani kasan ana kashe musu dollars,yanada tsawo amma ba can ba,gashi da faffaWan irji,kai in taiaice muku Sadam za'a iya kiransa da *Ingarman namiji* wato mai cikakkyan halitta,ga tsadaddun kayan da ya saka duk da farin yadi ne amma mai shegen tsada,ga hularsa mai ube ta asalin Maiduguri,agogansa ma abin kallo ne,ga zoben azurfa da yake maale a hannunsa na da shegen kyau,kai! Kai! Kai ! Abun dayawa,kar na cikaku da suturu lokaci ya ure,da sauri Sauban ya iso gunsa haWi da russunawa yana gaisheshi,suma ma'aikatan haka sukayi,shi kuma gogan ko uhmm! Bai ce musu ba,saidai Mukhtar ke amsa musu gaisuwar.


Sauban yayi musu jagora ko'ina na kamfanin haWi dayi ma Sadam bayani dalla-dalla cike da girmamawa akan yanayin yadda abubuwa suke gudana a kamfanin,sai daga baya kowa ya nufi office Winsa da murna domin kuWi ne aka bi kowannansu dashi mai yawa.Office Win manager Sadam nufa tare da Sauban da Mukhtar, a nan Sauban ya baje masa komswi dake tafiya a cikin kamfanin bisa tsarin Sadam, umarni Sadam ya bada a kira masa accountant shima yazo yayi masa bayani,ba'a Wau lokaci ba saiga accountant yazo,shima kamar yadda Sauban yayi bayanihaka yayi shima,yadda kuWi ke fita da shiga da duk abinda ya jiSanci harkar kuWi saida yama Sadam bayaninsa,tare dayi masa albishir Win asusun kamfanin ya aru sosai ba kamar da ba,daWi sosai Sadam yaji jin komai na Kamfanin na tafiya a yadda ya tsara.


Saboda wannan albishir da accountant ya bama Sadam, shima albishir ya bama su Sauban akan ya arama kowani ma'aikaci dubu #5000 ga salarinsa ma'ana daga yanzu an ara dubu #5000 ga salarin kowa.Wannan abu yama kowa a kamfanin daWi harda ananun ma'aikata alkhairin ya shafa ,godiya tare da addu'ar gamawa da duniya suka shiga jera masa musamman masu shara,securities da masu gadi,bai ara awa Waya ba ya baro kamfanin zuwa gidan Aunty Nabila saboda ya gaji,yanada buatar hutawa.



*Cikin Labari*



"Maa shaa Allah Sadam, Allah ya tayaka rio tare da kawo maka mata ta gari,don gaskiya na agara naga kayi aure Sadam"



Shiru yayi babu amsa,to mai zece mata shi da ko budurwa baida ita,ina shi ina aure yanzu,shi fa har yanzu baiga macen da yake ra'ayin aura ba,katse mishi tunani Dr. Nabila tayi cewa


"Hmmm daman nasan ba amsani zakayi ba,kaiWin Sadam Allah yasama kanada budurwar"


"Aunt bazaki gane ba,wallahi har yanzu banga wacca ra'ayinta yazo Waya da nawa bane"


"Toooo daman sai ra'ayi yazo Waya ake aure kenan,hmmm mubar zancen don nasan baso kake ba,yanzu dai tunda kaine bao a gidan, me kake so a girka"

shiru ya Wanyi tana tunani sai can yace


" Alkubus da miyar ganye da pepper soup Win naman rago"


TaSe baki Sa'eeda tayi a zuciyarta tana cewa 'yayaya da yayan ganye,mtws! Sai shegen iyayin tsiya,katse ta Dr. Nabila tayi da cewa


"Sa'eeda tashi ki girka mana alkubus da miyar ganye sai Jamila ta taya aiki tunda yayanki yana so"



"Wannan ce zatayi girkin"

Nuna Sa'eeda yayi,Wagowa tayi Sa'eeda tana masa kallon irin yama rainata,Dr. Nabila tace


"Sosai ma kuwa,she knows how to cook sosai,don't worry kaida kanta zaka jinjina mata"


TaSe baki yayi tare da cewa


"Hmmm Allah yasa"

Miewa Sa'eeda tayi ko kallon inda yake batayi b ta nufi kitchen Win tare da kiran Jamila don ta tayata aikin,nan da nan girki ya kammalu wanda sai wurin bayan magrib suka kammala,basu sukaci abinci ba sai bayan isha'i wanda daman haka al'adan gidan take.


A wurin cin abinci kamar yadda Dr. Nabila ta ce sai Sadam yayi santin abincin haka kuwa akayi,don ajiye miskilamcimlnsa yayi s gefe ya fara kwasar girkin Sa'eeda yana santi,Kauthar uwar surutu sai da ta ce

"Uncle Sadam girkin da daWi ko?

Murmushi ya mata don babu bakin magana,itako Sa'eeda ko takan zantuttun da suke batayi ba tacigaba da cin abincinta hankal 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~i kwance.

Haka Sadam ya kwana gidan kasancewar akwai enough room a gidan su kuma P.A da bodygaurd Winsa a boys quarter suka kwana ,sai washe gari ya wuce Kebbi da maarrabansa,ita kuma Sa'eeda ta cigaba da shirye-shiryan exams Winsu da first semester 400 level wanda baifi saura kwana biyar ba.


A Sangaren Umman Sa'eeda jiki saidai mu ce Alhamdulillah domin lafiya ta samu,yanzu ma suna shirin tafiya Umrah tare da Momin Sadam sai daga baya su wuto Kebbi inda suma su Sa'eeda suna kammala exams zasu taho Kebbi domin yin warya-waryar walimar murnar dawowar Umman Sa'eeda da arta cikin ahalinsu.Wannan kenan



@ @@@@@@@@@@



A Sangaren *LOVE BIRDS* =J=J wato Sauban da Maryam abubuwa sai a hankali duk da yayan Momin Sauban yazo tun daga Zaria don yayi sulhu akan Maryam ta koma gidan mijinta tayi hauri,amma ina in hauri iyayen Maryam sukayi wai sai Sauban ya janye auran da yace zai ara don su a danginsu ba'a yin kishiya.

" Wannan ne baku isa ba"

Cewar Momin Sauban, harara da dalla ma Haj. Labara wacca ta ce sai Sauban ya janye auran daya ce zaiyi,arawa tayi da cewa

"Aure wannan kamar anyi angama ne,kuma idan ma nan gaba yanada ra'ayin ara aure zai ara koda biyu ne kinga sai su cike hudun,zama da kishiya dole ne agareta,sannan ni *walki ce dede ugun kowa* duk wacca ta shirya nima na shirya,mu zuba mu gani"


Cikin Sacin rai Haj.Labara ta bata amsa da cewa


"Ahhhayye chasssss! Ashe ko tsautsayi yana niyyar kaiki ramin kura,domin ba'a taSa dangin mu a zauna lafiya,idan ke yanzu kika zo to mu a nan muka kwana,mu nan da kike ganinmu"

Nuna kansu tayi wato ita da Momin Maryam tare da wata anwarsu Momin Maryam sannan ta cigaba da magana


"Mu Tsuliyar dodo ne wallahi! Wallahi! Wallahi duk wacca ta taSamu to ta taSoma kan bala'i da masifa,ke a hirWin wallahi karan-batta damu babu daWi fa,da munsa haka kuke da ko mutuwa Maryam zatayi wallahi baza mu bari ta auri Wan iskan Wanku ba"


Cikin masifa Momin Sauban ta ce


"Da nasani tabb! Ai ni nayi da nasanin haWa zuri'ah daku,dangin marasa tarbiyya,baku koyawa arku komai ba sai rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da ita shi ne kuke iya cewa kunyi da nasani,da nasaninku na banza da yofi"


Yayan Momin Sauban yayi saurin dakatar dasu da cewa


"Haba wani irin hauka ne haka,kuna manya daku amma kuke yin abu kamar yara,sasanci ya kawoni ba jin shirmanku ba,ni yanzu nazo kuyi hauri Maryam ta koma Wakin mijinta kawai "


Momin Maryam ce ta ce

"Idan kaga Maryam ta koma gidan nan to sai Sauban ya janye magana auran da zai ara wallahi"


Momin Sauban ita ma a hasale ta ce


"Aure ko babu gudu babu ja da baya sai anyishi,idan kun gadama ku ara tarbiyantar da arta tare da nuna mata sanin girman na gaba da ita ko kuma ku rie ta karta dawo gidan wannan ya rage ruwanku,amma ku sani babu Sauban babu sakin Maryam har abada ko bayan raina ban yarda ya saki Maryam ba domin saina tabbata muku da alfaharin da kuke akan danginku ba'a muku kishiya ni na kaudashi,domin dole Maryam ta zauna da kishiya"


Tashi tayi ba tare da tabi takan zantuttun da Haj. Laraba dasu Momin Maryam suke kamar zasu cinyeta da masifa ta wuce abinta,shima yayanta biyo bayanta yayi yana mata faWa akan biye musun da dayi,murmushi tayi,sai da suka shiga mota tace

"Bari kajiYaya,ai rashin sani ne yaya na bari Sauban ya aura ar danginsu,duk da awata ce Haj. Labara ta ut da ut amma bamu taSa maganar kishiya da ita ba,shiyasa bansan yadda danginsu yake ba kuma koda tazo min da cewa, yarinya da Sauban yakeso ya aura bata da asali sai nace ya fasa auran yarinya kawai tunda bata da asali,sai ta sake cemin ko zai aura Maryam yarinya ar uwarta saboda tanada hankali da natsuwa,ban musa ba nace ya aure ta,ashe ashe shegiyar mata makirci ne suka ullama yarinyar da asali Sauban yakeso mu kuma bamu sani ba,saboda arsu Maryam na mutuwar son Sauban shiyasa sukayi ulla-ulla haWi da makirci duk don ya auri Maryam Win,dama ace tanada tarbiyyar wannan mai saui ne,shegiya ce yarinya ta bugawa a jarida,bata iya kula da miji ba,rashin tsafta,rashin iya girki,ga uwa-uba rashin kunya duk ta haWa"


Rie baki Yayan Momin Sauban yayi yana mamaki wato saboda rashin ta ido suke cewa wai baza a mata kishiya, ehhh lallai ai da sauransu dan ko nan gaba Sauban yace zai ara aure to saiya ara.Haka sukayi ta faWa a mota har suka isa gidan Momin Sauban, shi kuma Yayanta ya wuce Zaria.Sai Momin Sauban ta cigaba da shirye-shiryan bikin Wanta Sauban da Khairat.Wannan kenan.



@@@@@@@@@@@@


A Sangarensu Umma Kande da Maman Jummalo komai normal yake duk da ba wani kuWi yake zuwa musu sosai ba kasancewar yanzu basa samun kuWi ta hannun Nusaiba,summa kwana biyu basuji Nusaiba a waya ba,duk da ko'ina take a asar waje saita kira Umma Kande tare da ce mata tana asa kaza da kaza.Abban Sa'eeda kuma sai dai na abincin yau da kullum yake basu domin babu laifi yana matuar okari da iyalinsa wurin ci da shansu.


Maman Jummalo dai an koma ga Allah,kullum idan su Jummalo da Iklima suka dawo daga Islamiya sai sun koya mata abinda aka koya musu, babu laifi abubuwa da dama na rayuwarsu Maman Jummalo, Iklima da Jummalo sun canja musamman yin sallah akan lokacinta,basa wasa da sallah,duk abinda suke da sun ji an kira sallah zasu mie suyo alwala haWi da sallah,harda wa'azuzzukan malamai da dama a wayoyinsu,kullum cikin saurare suke musamman Maman Jummalo domin tayi yainin gyara bayanta don lahirarta tayi kyau.Ita kuwa sha kundum uwar gayya Umma Kande ko ajinkinta hasalima da sun fara jin wa'azi zata tashi daga wurin ko kuma da wuce Wakinta.Ta riga da ta gama imani da aikin boka(Wa'iyazubillah>>>)

A kullum gani take shirme suke yi,shiyasa yanzu bata shiga harkarsu harda arta Iklima saboda wa'azin da take mata a kullum akan ta tuba kamar yadda Maman Jummalo ta tuba amma ina ta riga da tayi nisa bata jin kira.


Kasancewar yau Juma'ah babu Islamiya,su Iklima na tsakar gida tare da iyayansu suna hirar cikin farin ciki da annashuwa ga cikin Maman Jummalo sai girma yake,suna cikin hirar sukaji sallama tare da shigowa,maza ne su biyu sun saka nose mask suns rie da wata mata wacca na kasa gane wace ce har cikin gidan inda su Iklima suke da iyayansu suka kai matan tare da ajiyeta,da sauri su Iklima da su Umma Kande suka mie tare da toshe hancinsu saboda uban warin da matan take sai kace kashi,cikin tashin hankali Umma Kande tace



"Wazan gani ni Saratu!!! Nusaiba kece................




*Mu haWu a pages na gaba my Esteem fans=C=C=C
'
'
'*



*wata sabuwa inji an caca,tofa mai ya samu Nusaiba haka harda kowa ya toshe hancinsa???ya akayi ta rame tayi bai???? Meke faruwa da ita haka???*........



*Da alama akwai drama babba tsakanin Sadam da Sa'eeda ganin yadda basa jituwa amma kuma zuciyoyinsu suma ayyan abu Waya??? To mene ne wannan abun haka???*......




*Love birds anata yain duniya na uku ani karewa,ko yaushe zasu are oho,shin Maryam zata haura da komawa gidan Sauban ko kuwa har yamzu sonsa na nan a zuciyarta???Wani irin shiri iyayen Maryam sukaye game da arin auran Sauban ganin yadda ba'a ma danginsu kishiya???*....




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions<9<9=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku new updates zafafa* <9<9=C=C=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ==%=%=%=%=%





*Ina aunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* <<<<=ؖ=ؖ<9<9=C=C=ؘ=ؘ




Daga alalamin
=؍=Narrnarhh Bukar ==؍


Comments and share =O=O=OFisabilillah.

[5/12, 9:08 PM] Narnarhh Bukar:

< *NACINA YA JAWO MIN* <




*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen*
')




*TASKIRA WRITER'S FORUM*
*T.W.F*




*WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends


*AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?id=6615ba31404e6e2687888ab9


*TELEGRAM*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk


*WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y



*BOOK 2*



4 7 ----4 8





Kasancewar yau Juma'ah babu Islamiya,su Iklima na tsakar gida tare da iyayensu suna hira cikin farin ciki da annashuwa ga cikin Maman Jummalo sai girma yake,suna cikin hirar sukaji sallama tare da shigowa,maza ne su biyu sun saka nose mask suna rie da wata mata wacca na kasa gane wace ce har cikin gidan inda su Iklima suke da iyayansu suka kai matan tare da ajiyeta,da sauri su Iklima da su Umma Kande suka mie tare da toshe hancinsu saboda uban warin da matan take sai kace kashi,cikin tashin hankali Umma Kande tace

"Wazan gani ni Saratu!!! Nusaiba kece haka!!! Meya sameki!!! Wayyo!!! Wayyo ni Sarere na bani na lalace!!! Yiiiiiiii!!! "

Kowa a wurin hancinsa a toshe yake saboda warin kashin da jikin Nusaiba yake,duk ta rame ta koWe tayi bai sosai,idanun nan nata duk sun shige ciki saboda muguwar ramar da tayi,ita bama jin mai suke cewa take ba,domin tana a cikin mawuyacin hali ne.Kowa a wurin saida ya tausayawa halin da Nusaiba ke ciki,Umma Kande ai kuka take sosai tana ara duba arta,ita bama ta warin da yake fita daga jikin arta take ba a'a yadda arta ta koma ne hankalinta ya tashi akai.Mutanan da suka kawota ne wani daga cikinsu ya ce

"Ni ba Hausa ooo,daga Lagos muke ooo,so na help we help say make we bring gam to her family make you kuku take her hospital me she no die ooo"

Idanu suka tsira ma bayaraban,domin a cikinsu babu wanda yake jin turanci,yooo Islamiya ma ba zuwanta suke ba ina ga boko akwai ura,gwara shi akan Wayan,haka mutumin ya ara tambayarsu still da turanci

"Bucket with water make we wash the pupu she do for our car"

Bucket kawai suka iya ganewa a duk cikin maganarsa,Jummalo ce ta Wauko mishi bokiti haWi da ruwa a ciki ta mia mishi,fita sukayi babu jimawa suka dawo da bukitin tare da yimasu sallama.

Tashin hankali wanda ba'a samai rama,hauka ne kawai Umma Kande batayi ba,gashi mikin mutuwar Musa saida ta fama,ji kake tana ihu da kururuwa kamar wata motsattsa,tana cewa

"Shikenan na mutu na lalace!!! Waye gatana a duniya yanzuuuu ni Sarere jikan sarkin ruwa!!! Wayyo na shiga uku na lalace!!! Shikenan masu tallafamin sun are!!! "

Maman Jummalo ne ta harzia saboda ihu da kururuwan da take,domin wa'azin da sukeji wani malami yayi bayani akan babu kyau idan wata musiba ko mutuwar wani naka ya sameka kayi ta kururuwa ko kuma iface-iface,anfiso ka yawaita salati tare Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,ko kuma Allahumma ajurni fi musibati haka wa aklifni khairan minha.Hakuri tayita bata tana cewa

"Haba Umma Kande wannan kururuwan da iface-ifacen da kike ba ita bace mafitarmu a yanzu,Waukarta ya dace muyi mu kaita asibiti don neman lafiyarta,don Allah kibar kukan nan ki kwantar da hankalinki,da izinin Allah zata samu saui"

Ita sai yanzu ta tuna da wata aba wai asibiti,ai kamar an tsikareta haka ta mie tana cewa

"Iklima maza-maza ki tare mana keke napep yanzu mu kaita asibiti,yi sauri,yanzu-yanzun nan"

Da sauri Iklima ta fita tare da nema musu keke napep,ita kuma Umma Kande da Maman Jummalo tare da Jummalo suka cicciSe Nusaiba zuwa bayi,tare da yi mata wanka a gurguje,kayan Iklima suka saka mata,suna cikin shiryata saiga Iklima ta shigo tana ce musu an samu keke napep Win,sauri-sauri sukayi suka saka mata kayan tare fesa mata turare saboda warin da jikinta yake,kashi ne yake fita daga duburarta babu full stop,ga kashin da shegen wari,haka suka cicciSeta har cikin keke napep Win,Maman Jummalo da Umma Kande ne suka shiga ciki,sai ita Iklima ta taran musu wani tare da amsar ATM card Win Umma Kande saboda ciro kuWin da za suyi amfani dashi a asibiti.



*Waiwaye*


Abinda su Umma Kande basu sani ba shi ne,hanyar da Nusaiba ta Waukoma rayuwarta ba mai Sulle mata bane,domin kuwa babu abinda Nusaiba batayi kama daga sex,lesbian,luwaWi,shaye-shaye da dai sauransu harda biyan buata da kare,duk ta haka tanayi,har ungiya ta kafa na tatattun an duniya a Lagos area na Hausawa,domin tun sanda Alhaji Sagir ya fita da ita asar waje abubuwa suka ara dulmiyar da ita,ya haWata da gogaggun an bariki maza da matansu,masu harkoki kala-kala tun kama daga lesbian,luwaWi,shaye-shaye dama masu biyan buata da karnuka(Wa'iyazubillah,ke duniya ina zaki damu>>>)

Haka ita ma ta goge a cikinsu harda tattoo take dake a wuyanta da mazaunanta, ta zama shugaban kanta,babu irin abinda batayi, gasar cin duri ne,gasar amfani da kare ne duk babu wanda batayi,shiyasa kuWaWe suke shigo mata kamar hauka,tana kashesu kamar iska,tare da turo ma Umma Kande maudan kuWade ita kuma Umma Kande tana sa mata albarka tarw da murna,arin daWi rashin faWan Umma Kande ga Nusaiba ne yasata ara shiga halaka,gasarta da arshe wanda daga shi ne Allah ya jarabceta da yoyon karshi,anyi gasar yin amfani da kare ne,wanda ashe karan yanada cuta wanda ba'a sani ba,sai bayan an gama gasar ne har Nusaiba ta dawo Lagos sai ta fara yoyon kashi,abu kamar wasa sai ya tsananta,komai nata ya are har takai ta kawo bata iya fita daga Wakinta,wa'inan bayin Allah ne suka tausaya mata ganin kowa ya guje ta,tayi musu kwatancan gidansu a Kaduna sai suka kawota.



*Cikin Labari*

Mai keke napep Win sai masifar yake saboda warin da keke napep Win yake har suka isa asibitin,bayan ya sauke sune sai Maman Jummalo ta biya kuWin keke napep Win,suka cicciSeta zuwa cikin asibitin,shi kuma mai keke napep saida ya nemi inda ake Wiban ruwa ya wanke keke napep Winsa saboda warin kashin da cike ilahirin keke napep Win. Duk inda su Umma Kande suka wuce da Nusaiba sai an toshe hanci,haka har suka isa cikin asibitin inda nurses suka sakata a gadon marasa lafiya zuwa cikin emergency room,likitoci ne har biyo suka duufa a kanta,wanda basu suka fito ba bayan awa biyu lafiyayyu,cikin Sacin rai da takaici wani likita ya umurci su Umma Kande su biyoshi Office,haka suka bishi kamar raumi da akala har Office Winsa,ko zama baiyi ba ya fara zazzaga musu ruwan masifi,ta inda yake shiga ba nan yake fita ba,tsuru-tsuru su Umma Kande sukayi,yoo basuda abin faWa,sai can kuma likita ya zauna tare da ce musu su zauna,cikin sanyin jikin haka suka lafe a kujerun kamar kajin da wai ya fashe musu a ciki.Cikin natsuwa likitan ya fara musu bayani game da ciwon Nusaiba yana cewa

"Saidai kuyo hauri da yanayinta a yanzun,domin ciwonta ya zama chronic babu yadda muka iya,zamu bata gado,amma fa zaku sha aikin siyan *pampers* Win manya saboda yanzu dashi zata dinga zama koda kuwa jikinta ya samu saui,dalili saboda duburarta ta tashi aiki,abinda yake controlling fita da tsayuwan kashi ya lalace ta hanyar abubuwan da takeyi ko kuma mu'amalar da akayi da ita a bayanta,so blame yourselves na rahin kula da tarbiyyarta,don ta dinga amfani da *pampers* kenan har arshan rayuwarta,zan rubuta muku magani tare da allurorin da zaku siya"

Shiru kowaccansu tayi tana tunani kala-kala aranta,musamman Umma Kande wacca take tunanin ayya ba Sammu aka mata ba ita da aanta,taya komai nata zai dinga taSarSarewa,katse musu tunani likitan yayi da miama Umma Kande wata ar paper tare da cewa

"Gashi

Please Login or Register in order to submit comment