Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alama baki da hankali,da wannan shigar zaki je gun abokaina,wai yaushe zakiyi hankali ne Maryam,nidai na shiga uku an kawomin rainon yarinya,ke kullum sai ance miki kiyi kaza,kibar kaza haba mtsw!!! "



Fita yayi ita kuma ta saka hijab ta fito suka gaisa da abokan nasa,cewa yayi suje dining suci abinci,babu musu suka mie musamman Captain Fu'ad wanda ya Webo yunwarsa,yazo yaja girkin amarya.(hmmm Captain Fu'ad a shirya cin girkin Maryam kuku====C)




Zama sukayi a dining room Win sai Sauban yayi serving Winsu,kasancewar ya umurci Maryam ta wuce Waki,serving Winsu yake amma zuciyarsa na dukan tara-tara bama uku-uku ba,ganin yadda colour Win abinci yayi so scary babu kyan gani,gashi baya fidda wani aroma mai daWi sai uban auri,haka dai ya gama serving Winsu shima yayi serving kansa sannan ya samu guri ya zauna.



Captain Fu'ad ne farkon fara kai spoon Win abinci a bakinsa wanda a lokaci guda amai ya tasa sama jin wani uban arni,ga yajin data zambaWa a ciki,kai kai kai,amai Captain Fu'ad yake kwarawa babu akautawa lokaci guda ya Wau gorar ruwa ya kwankwaWe,baiji yajin ya daina masa zafi a baki ba,ya ara Waukar wata sabuwar goran ruwan ya shanye,su kuma Sauban ganin yadda Captain Fu'ad ya rikice lokaci guda suka kasa cin abinci tare da miewa suka nufo inda yake suna masa sannu.Bai amsa musu ba ya mie ya dauki key Win motarsa ya fita,har waje Sauban ya bisa yana basa hauri haka ya yalesu suka tafi,a fusace ya shigo falon har bedroom,lokacin Maryam na kwance abinta,batayi aune ba taji saukan zafafan maruka har guda huWu lokaci guda,habawa a haukace a mie tare da sakin wani razanannan ihu,bai yaleta ba saida ya mata dukan tsiya tare da ce mata ta tafi gidansu gobe,sannan ta tabbata ta goyi girki tare da gyaro munana halayanta kafin ta dawo gidan.Fita yayi baibi takan kukan da take ba ya wuce wani Wakin ya kulle tare da kwanciyarsa.



Washe gari Maryam ta tattara kayanta ta nufi gidansu,wanda Sauban yasha tsinuwa a hannun iyayenta kasancewar arya da gaskiya ta faWa musu,su kuma babu bincika ba sukaita zaginsa.Wannan kenan





@ @@@@@@@@@




angarensu Umma Kande da Maman Jummalo da alama basuyi nadamar abubuwan da suka faru da yaransu ba,domin har yanzu iyayyar Umman Sa'eeda da ita Sa'eedar na nan daram! A zukatansu.



Suna zaune su duka da yaransu wato Iklima da Jummalo,sai Umma Kande ta ce



"Kodai mu ara komawa gun Boka Sankeru ne muji a ina aka samu matsalar"



"Tabb wallahi ko kusa Mama karku fara,yanzu duk abinda ya samemu bai zamo muku isharaba,harda rasa Wiya kikayi amma bakiyi ladama ba Mama"



Cewar Iklima wacca ta harzuar sosai saboda halin uwarta ta domin haushinta take ji sosai,Maman Jummalo ce ta ce



"Haba Iklima daWi da hutu muke nema muku ai,wannan ma matsala aka sam....."



"Matsala! Matsala! Kika ce fa Mama, wallahi bazamu sake biye muku ku kaimu ga wahala ba,da alama kema kamar yadda Iklima ce bakiyi nadama ba,to bara kuji tun a asibiti ni da Iklima muka shirya komawa Islamiya,don ara sanin Allah da addinin mu,wanda kuka kasa bamu"



"Tabbas kuwa Jummalo zan tambayi Sa'eeda yadda karatun islamiyarsu take"



Umma kande ce ta hayayyao Iklima da masifa tana cewa



"iyar maiyiyata zaki nema shawara wurinta Iklima"


"Maiyiyarki ko ko ce maiyiyarta,wani irin asiri ne baku musu ba,amma gashi sai cigaba suke, ku kuma kuna nan jiya iyau"cewa Iklima



"Rufemin baki dan Ubanki,da hassadar Umman Sa'eeda aka haifeni sannan yanzu ma na fara nuna mata iyayya wallahi, koya kika ce awas"



"kkkwaraiii da gaske yanzu muka fara nuna mata iyayya"


Suna cin hakane akan kira numban Umma Kande wanda tsabar masifa bata duba mai kiranta ba ta amsa kiran


"Hello"


A can ne ake mata magana,wanda lokaci guda ta rikice tana cewa


"Mai wayar!!! "


A can aka ara tabbatar mata,habawa sakin wayar tayi a asa haWi da zaman an bori,tana ihu da kururuwan ta bani ta lalace shikenan ta mutu.Kanta su Maman Jummalo sukayi suna tambayar lafiya mai ya rafu,cikin kuka haWi da majina take cewa


"Na shiga Uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa!!!na mutu na lalace wayyo ni Saratu!!!! Yanzu..................










Mu haWu a pages na gaba My Esteem Fans=C=C=C<9<9<9








****Wata sabuwa inji an caca,wani bala'in ya kuma saukar ma Umma Kande ne???.....






****Anya Zaman Sauban da Maryam zai cigaba da wanzuwa ganin yadda tun kan aje ko'ina an fara kai duka tare da tafiya gida???.....









****Shin Fadila zata haura da Sadam kamar yadda ya haura da ita koko yaya???......






*****Shin wasu abubuwa ne suka faru shekaru aru aru a baya wanda Momin Sadam da ahalinta suka kasa mancewa???........







Ku cigaba da zubo ruwan comments>>>=C=C=C=؝=؝=؝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaWantar,ilmantar tare da faWakar daku>>=C=C=؝=؝<9<9<<<<<<









Ina matuar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar aunar>>=C=C=؝=؝<9<9<<<<<<=ؖ=ؖ=ؗ=ؗ=ؓ=ؓ









Daga alalamin
=؍=Narrnarhh Bukar ==؍





Comments and share =O=O=OFisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar:

< NACINA YA JAWO MIN<









Narrnarhh Bukar
'





<9Perfect Essential Writer's
Association<9
(' P. E. W. A('





Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002






Masu telegram zaku iya following Wina ta wannan link Win>,=C<=G=G=G
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk









<9<9<9I'm not born to be a writer but born to be a great professional writer
'
'
'=C=C=C<9<9<9






<<<<<






3 7 ----3 8







Suna cin hakane aka kira wayar Umma Kande wacca tsabar masifa bata duba mai kiranta ba ta amsa kiran

"Hello"

A can ne ake mata magana,wanda lokaci guda ta rikice tana cewa

"Mai wayar!!! "

A can aka ara tabbatar mata,habawa sakin wayar tayi a asa haWi da zaman an bori,tana ihu da kururuwan ta bani ta lalace shikenan ta mutu.Kanta su Maman Jummalo sukayi suna tambayar lafiya mai ya rafu,cikin kuka haWi da majina take cewa

"Na shiga Uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa!!! Na mutu na lalace wayyo ni Saratu!!!! Yanzu mai yayi saura gareni,yiiiiii!!! Yiiiiii!!! "

"awas wai meya faru ne,kinsamu a duhu,ga kuma kuka kina yi"

"Maman Jummalo gobara ta tashi da Musa!!! Shikenan Wana a duniyi,yanzu ya tafi ya barni,ina ganin bala'i da masifa ni Saratu!!! Wayyo Musana!!! Shikenan ko gawan Wana bazan gani baaaaa!!!! Yiiiiiii!!! Yiiiiiii!!!

Jin abinda Umma Kande ta ce gidan ya kaure da kuka haWi da iface-iface musamman Iklima wacca suka fi shiri da Musa,tayi kuka haWi da birgima a asa kamar sabuwar kamu.Maman Jummalo itama tayi kuka sosai tare da ba Umma Kande hauri,amma ina Umma Kande kamar wata zautatta haka tayi,gashi tayi zaman an bori haWi da cire Wan kwalin kanta tana ihu da kururuwa

" Musa! Musa! Musa! Ka dawo karka tafi ka karbi,kaine rayuwata,ka dawo,ka dawo Musana na roekaaaaaa!!! "

Waiwaye

******Abinda su Umma Kande basu sani ba game da rasuwar Musa shi ne,kasancewar Musa Wan daudu ne kuma mai harka da manya-manyan mata a Calabar,manyan matan suna zuwa Waukarshi har gidajensu domin suyi sharholiyarsu sannan su biyashi maudan kuWi saboda yasan sirrin mata sosai.

Hausawa suka ce tsautsayi baya wuce ranarsa,ranar data kasance ranar da Allah ya Wauki ran Musa shi ne,wata customersa ce tazo har gidan karuwai ta Waukeshi suka tafi gidanta,zama yayi a falonta sai tace bara ta girka musu abinci sai suji daWin harkar dakyau,bayan matar da Waura girki a gas cooker mai mazaunai hudu sai ta fito falon,tana zuwa sai Musa yayita janta da kissarsa ta riakun an daudu,habawa tuni mata ta manta da abinda ta Waura kan gas cooker suka fara masha'arsu,wanda har girkin ya one,tukunyar tayi bai amma hankalinsu baya a jikinsu balle suji auri,nan da nan wuta ta tashi a kitchen kan kace me ta gauraye ko'ina,su Musa kafin suyi wani aune,wuta ta shigo falon,haka su biyu suka one urmus sai ashi,wannan ne asalin sanadin mutuwar Musa******




*Cikin Labari*



Suna a wannan yanayin ne saiga Baban Nusaiba ya shigo gidan kamar an jefosa,tun daga zaure yake jin ihu da kururuwansu Umma Kande wanda hakan ne ya sashi saurin shiga gidan,samun Umma Kande yayi a zaune a asa,ta wage afafunta haWi da saka hannuwa a kai tana ihu.cikin sanyin murya ya tambayi lafiya,Iklima ta sanar mishi Musa ne ya rasu,bai sake ce da ita komai ba ya fita daga gidan,fuskarsa babu yabo babu fallasa,shidai gashi nan,mutuwar ma ba damuwa yayi da ita ba,to baya cikin hankalinsa.

Tun safe Sa'eeda da Ummanta basa nan,ita Sa'eeda taje IT, ita kuma Ummanta daga shara ta wuce aikin biki a bayan layinsu,basu san da abinda ke faruwa ba.

Da sallama Sa'eeda ta shigo gidan,cak ta tsaya ganin ikon Allah,yau su Umma Kande ne ke kuka haka duk da lokacin rasuwar Zaliha tayi kuka amma wannan karon kamar hauka take,wai meke faruwa ne? Mai ya samesu haka?,tambayar kanta tayi,wanda babu amsa,taso ta buWe Wakinsu ta shiga ba tare da ta tambayi mai ya samesu ba,amma ina bazata iya ba,ita mai raunin zuciya ce ga mutane,haka tayi kasadar tambayar Iklima mai ya faru.Cikin kuka Iklima ta sanar ma Sa'eeda Musa ne ya rasu yanzu.

"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,Allahumma gafir lahu,warhamhu,wa'afi anhu,Allah ya gafara masa,yasa ya huta,yasa kuma aljanna ce makoma a garesa,Allah ya baku hauri tare da juriyar rashinsa"

Iklima da Jummalo ne suka iya bata amsa,amma Maman Jummalo tare da mai gayya mai aiki wato Umma Kande basu san mai take cewa ba tsabar tashin hankali da ruWun daya samesu.aki Sa'eeda ta wuce wanda bata jima ba saiga Ummanta ta dawo,itama tambayarsu tayi mai ya faru,Iklima ce ta bata amsa,salati tayi tare da yi mishi addu'ar Allah ya gafarta masa ta wuce Waki.

Haka su Umma Kande suka ci-gaba da zaman makokin Musa wanda har an uwanta da Maiduguri saida sukazo ta'aziyya,yanzu kullum da hijabi zakaga Umma Kande haWe da carbi saikace tasan me ake cewa===,bayan anyi arba'in Win Musa wanda ba'a kawo gawarsa ba kasancewar urmus ya one,Umma Kande ta yaki ce saka hijabi haWi da rie carbi,wannan karon Nusaiba batazo ba saidai kira a waya tai musu ta'aziyya saboda yanzu bata samun lokaci sosai,tauraronta ara haskawa yake a harkar luwaWi da kuma lesbianism,wanda bata wannan asa bata waccan.

Bayan rasuwar Musa da wata biyu su Iklima da Jummalo suka shiga islamiyar da Sa'eeda tayi sauka,ajin matan aure suka shiga saboda babu wani abun kirki da suka sani dangane da addinsu su.Wannan kenan


@@@ @@@@@@@@


*Bayan Wata Shida da Sati Biyu*



A Sangaren karatun Sa'eeda kuwa,sun kammala IT yanzu kuma sun shiga shekarar arshe a karatunsu wato 400 level,yawanci lecturers Win da suke Waukarsu sababbi ne,masu zafi babu wasa a tattare dasu.Farkon shigarsu ajin wata sabuwa lecterer ar gayu ta fara Waukarsu wani course,shigowanta ajin tayi tozali da Sa'eeda, cak ta tsaya tana kallonta babu ko yafta ido,kowa a ajin kallansu suka komayi ganin wannan ikon Allah, mata daga zuwa aji ta kafe Sa'eeda da kallo babu ko yartawa,kusan seconds 20 sai kuma lecterer ta arasa cikin ajin still idanunta akan Sa'eeda, kasa hauri matar tayi ta tambayeta da harshen turanci

"Young Lady what's your name please? "

Sa'eeda da tunda ta haWa ido da wannan sabuwar lecterer irjinta ya fara duka,gashi taga matar sai kallonta take babu ko iftawa,miewa tayi cikin ladabi ta amsa mata cikin hatshen turanci

"My name is Sa'eeda Sulaiman"

"From which State"

"From Kaduna"

"Alrght seat down"

Ba haka ran matar yaso ba domin akwai abinda takeso ta tabbatar akan garinsu,saboda wani abu take ji a zuciyarta game da wannan yarinya,amma ya zata tabbatar tunda ta ce ita ar Kaduna ce,sha re zancen tayi,tazo gaban Allon haWi da gabatar da kanta cikin harshen turanci wanda take magana cike da warewa

"Good morning class,My name is Dr.Nabila Abubakar Kabir Dikko,nice to meet you all"

Duka ajin suka amsa mata cike da murna saboda matar ta gama tafiya da imaninsu,ga turancin da takeyi daga ji kasan ba'a Nigeria tayi karatu ba,saboda yadda take amfani da phonex wurin lanwasa harshenta.Cike da warewa Dr. Nabila take musu karatu,gashi ta iya bayani mai gamsarwa,lokaci-lokaci idanun Dr.Nabila na kanta Sa'eeda wanda har yanzu ta kasa gasgata abinda zuciyarta take ayyanawa game da yarinyar,haka ta kammala musu lecterers ta fita,kamar jira an aji suke tana fita kowa ya fara yaba Dr. Nabila saboda warewa da gayunta.

Haka suka ci-gaba da karatunsu a 400 level first semester cikin nasara,a semester Win ne aka rarraba Walibai ga project supervisors nasu,luckily Sa'eeda aka bama Dr.Nabila, haia Dr Nabila taji daWin bata Sa'eeda da akayi a matsayin project student Winta,koba komai zata samu damar tambayanta abubuwa da dama wanda suke cikin ranta tun a ranar da tayi tozali da ita.

Sa'eeda ma haka abin yake a wurinta domin har labarin Dr Nabila take ba ma Ummanta,saboda tanada kirki sosai gashi tunda Dr.Nabila ta zama supervisor Winta take taimakonta da kuWi ko wasu abubuwa,duk da Sa'eedar bata son amsa amma babu yadda ta iya saboda jan idon da Dr. Nabila take ma Sa'eeda idan tai amsa,an aji sunyi gulmar har sun gaji musammam squad Winsu Maryam wai Sa'eeda na shisshigema Dr.Nabila saboda taga tanada kuWi sosai,ga sabuwar Land Cruiser baa wanda take hawa,haka dai suka gaji da gulmar suka sa musu ido.

A Sangaren awancen Sa'eeda da Iman baza muce komai ba saidai muce maa shaa Allah,domin awancen da sukeyi na tsakani da Allah ne babu hassada balle yashi,ba aramin daWi Iman taji ba ganin yadda Dr.Nabila take son Sa'eeda, hakan na mata daWi a rai koba komai ganin awarta cikin farin ciki na daWaWa ranta.Wannan Kenan


@@@@@@@@ @@@@


A Sangaren LOVE BIRD=J=J=J wato Sauban da Maryam,tunda ya ce ma Maryam taje gidansu gyaro hali tare da koyan girki har yanzu bata dawo ba kusan wata biyar kenan,gashi har sun koma makaranta amma tai dawowa hasalima acan take tafiyarta makaranta abunta,tunda iyayenta sun Waure mata gindi akan sai Sauban yazo da kansa ya bada hauri kafin ta koma gidansa,shi kuma ya rantse koza ta shekara a gidansu ba zaije bikonta ba,domin laifinta ne ba nasa ba.Maryam nasan komawa gidan mijinta amma bata samu fuska gun iyayenta ba saboda sun kafe akan lalle-lalle-ilalla sai yazo ya bada hauri da kansa.

Shi kuma Sauban yanzu ya fita a harkarta musamman shawarar da Mom Winsa tazo mishi dashi wanda ya aminta sosai akan shawarar da ta yanke.

Yau ne ya shirya zuwa gidansu Captain Fu'ad domin yanason ya bashi shawara tare da ara bashi haurin abinda ya faru a gidansa kasancewar Captain Fu'ad auransa ya matso saura sati Waya,kuma ya samu hutu a wurin aikinsa Port harcourt.Bayan mai gadi ya buWe ma Sauban gate ya shigo da motarsa yayi parking tare da nufar part Win Captain Fu'ad, da sallama ya shiga falon kasancewar ofar a buWe take, amsa masa Captain Fu'ad yayi tare da miewa yana sakin wani shegen murmushi babu gaira babu dalili,tunda Sauban yaga yana mishi wannan munafikin murmushin yasan mugunta ya gani,cikin Waure fuska Sauban ya ce

"Malam ya da shigowa na ka mike tare da sakin murmushi"

Dariya Captain Fu'ad yayi tare da cewa

"Haba Angon Mairo kuku,kyau naga ka ara shiyasa ni sakin murmushi ganin aminina kuma Wan uwana na samun kwanciyar hankali"

Eh tabbas! Yau naga ta kaina da Fu'ad, nasan kashina ya bushe,badai yazo gidana yaga yadda muke rayuwa ba shikenan ai na kaWe ni Sauban, katse mishi tunani yayi da cewa

"Ka zauna mana Angon Mairo kuku,kana hutawa fa"

"Oooo God!!! Haba Fu'ad wani irin iya shege ne haka,ko ruwa baka bani nasha ba amma ka wani cikani a surutu marasa ma'ana"

Dariya Captain Fu'ad ya tintsire dashi harda rie ciki yana nuna Sauban yana sake tintsire dariya,Sacin rai iya Sacin rai Sauban yake ololuwa.Cike fusata yace da Captain Fu'ad

"Wallahi zanbar maka Waki naje na gaida Mom tunda naga alama wawalwarka ta taSu"

"Sorry friend wallahi yadda ka koma ne yasani dariya"

"Ok nagane wato ga mahaukaci yazo ko? "

"A'a fa Sauban,why are misunderstanding my words,ummmm wallahi ba haka bane"

"No hakane mana,ga angon Mairo kuku ba wacca kaja girkinta harda amai da shan gorukan ruwa har biyu,ai dole kamin dariya Fu'ad"

Dariya Captain Fu'ad yayi tare da yima Sauban waa harda rawa yana cewa

"Da so samu ehh!!! Ace ta iya girki,ar fara first lady mai kyau sannan ace tanada kirki ehh,inba kasamu ehh! Inba kasamu ehh!! Inba kasamu ehh ehh ehh habawaaa!!! "

Dafe kansa Sauban yayi yana cewa

"Kai kai kai yau naga ta kaina,shikenan ai tunda kasan sirrin gidana na kaWe,don Allah mubar wannan shirma,muyi abinda ya dace Fu'ad"

"Tohhh Angon Mairo kuku,ina sauraranka"

Baza yayi da abinda ya ce don idan ya biye halin Captain Fu'ad sai su shekara a haka,cikin muryar damuwa Sauban ya fara magana

"Fu'ad wallahi ina cikin matsala babba"

With serious voice Captain Fu'ad ya ce

"Subhanallah,meke faruwa Sauban"

" Ai komai ma ya faru Captain, Mom ce tazo min ta wata shawara a lokacin Maryam nace taje gidansu gyaran hali akan na ara aure,duk da nima inada wannan burin amma ba'a nan kusa ba,kwata-kwata yaushe akayi bikinmu ace har na ara aure, gashi Maryam duk yadda naso ta natsu tasan hakin mijinta amma ya gagara,idan na lanwasota ta nan saita Salle ta can,tana da matsaloli masu yawa wallahi,rashin iya girki,baar magana,rashin girmama na gaba da ita,ga uban azanta,gayu kawai ta iya amma duk abinda matar aure ya dace ta sani babu abinda Maryam ta sani,could you imagine pads Win da tayi amfani dashi after her mensturation a toilet ta barshi saidai ni dana shigo toilet Win na Wauke tare da jefarwa,how did you think i can tolerate her stupid atitude Fu'ad, common gyaran Waki Maryam bata iya ba,balle akai kan uwa uba girki,inaa inaa dole na samo ma kaina mafita wallahi,don bazan iya jurar halayanta ba,gashi tunda nace taje gidansu gyaran hali har yau tai dawowa,kuma na rantse babu inda zani bikonta"

Shiru Captain Fu'ad yayi yana kallon aminin nasa cike da tausayi duk da shi yajama kanta tun farko,sauke ajirar zuciya Captain Fu'ad yayi kafin ya ce

"Kaga illar dana hango maka tun a baya kai ganewa,irin wannan matsalar na hango maka Sauban amma ina sai kayi burus da shawarata,ka irinta nan Sauban kwata-kwata yaushe kayi auran amma har ka fara fuskantar matsalolin da ko wa'inda suka shekara goma basu fuskanta ba,i told you from initial not just by mere looking zaka san wacca ta dace ka aura ba,shi aure da kake ganinsa akwai features da mutum yake bi kafin yasan wacca tafi cancanta ya aure,amma kai ina kyau da gayu haWi da social life ya ruWeka,kai kafi son mace very social,beautifuland classy bayan the most impotant features Win aure ka barsu,like addinin mace,kamewarta,natsuwarta,tsaftarta,Wabi'unta da dai sauransu,duk da wannan baka duba ba sai kyau da wayewarta kawai,taya zakuji daWin auran bayan turbar da kuka Wauka kaida ita ba mai Sulle muku bane,alhakin Sa'eeda ne tun kan aje ko'ina Allah ya fara saka mata,mace mai hankali, natsuwa,ilimi,ga uwa uba tarbiyya duk Sa'eeda ta tattarasu amma saboda wani dalili wanda baikai ya kawo ba,ka wofantar da damarka Sauban"

Shiru Sauban yayi yana sauraron abokinsa,wanda sai yanzu yake gane kuskuransa,tabbas yayi wasa da damarsa,sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya ce

"Duk abinda ka faWa Fu'ad gaskiya ne,na riga na Sata rawata da tsalle,sai yanzu na gane illar da kake nunin abaya amma nayi burus da shawararka,yanzu dai nothing we can do tunda is already a past"

"Hakane,yanzu wacece Mom ta baka shawarar da aura "

"Cousin sister Wina ce wacca take a Malaysia tana karatu,yanzu haka baifi watanni huWu ya rage ta dawo ba"

*Waiwaye*



****Wata Waya da tafiyar Maryam,Mom Win Sauban ta kirasa har bedroom Winta,bayan ya shiga da sallama ya samu wuri ya zauna,cikin girmamawa ya gaisheta,ita kuma ta amsa masa cike da kulawa tana murmushi,shiru Wakin yayi na tsawan wasu seconds duk a lokacin idanun Momin Sauban yana kan Sauban ganin ya rame sosai,gashi ba annuri a tattare dashi,gyaran murya tayi sannan ta kira sunansa cikin sassayyan murya

"Sauban"

Gaban shi ne ya faWi jin irin wannan kiran sunan da ta masa,domin idan Mominsa tanason ta faWa mishi wata muhimmiyar magana,sunansa take fara kira cikin sanyin murya.Dagowa yayi yana kallonta tare da cewa

"Na'am Mom"

Cikin muryar damuwa ta fara magana

"Yanzu haka Sauban ka koma? Duk ka rame kayi bai,ko baka da lafiya ne?"

Girgiza mata kai yayi alamun a'a sannan ta cigaba da cewa

"Sauban wata shawara na kawo maka kuma na tabbata mai Sullewa ce da yardar Allah"

"To Mom ina sauraranki"

Ci-gaba da maganarta tayi tana cewa

"Aure nake so ka ara Sauban,tunda ita waccan batasan mai yake me yake mata ciwo ba"

Daramm! Gabansa ya faWi jin wani sabon tashin hankali,ba wai bayason ara aure bane,a'a da wuri haka ko shekara Waya ba suyi ba,cikin girmamawa ya ce

"Momina da wuri haka,nifa ko budurwa banda ita yanzu"

"Da wuri kuwa Sauban tunda ba samun kulawa kake wurin Maryam ba,hasalima ban ga amfanin auran ba tunda ana yinsa ne don samun natsuwa,amma kai sai akasin haka,yanzu dai akwai Khairat ar wajan Auntynku Habiba wacca take karatu a malaysia,tana da hankali da natsuwa ga ilimin addini dana boko,ita naso ka aura tun farko amma ka nuna kai Sa'eeda kakeso wanda ni sai yanzu nagane ashe makirci Haj.Labara ta ulla don ka auri ar wantarta,gashi dai yanzu aure baiyi riba ba hasalima faWuwa aka samu,zan baka numbanta ku daidaita kafin ta dawo tunda ta kusa kammala karatun nata"

"To Mom ba damuwa,Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi"

DaWi ya kama Momin Sauban jin Wanta ya karSi shawarata,murmusawa tayi sannan tace

"Allah ya maka albarkha,yasa aanka sumaka biyayya irin yadda kamin kuma kake faranta mun rai,Allah yasa ta zamo sanyin idaniyarka tare da farin cikinka"

"Aaaameen ya Hayyu ya Qayyum"

Tashi yayi haWi da mata sallama ,yasan khairat farin sani,tabbas ba arya tanada tarbiyya sosai da natsuwa, haba sai yanzu yaji hankalinsa ya fara dawowa jikinsa.

Tunda ya amshi numban khairat soyayya ta ullu a tsakaninsu,babu laifi akwai natsuwa a tattare da ita.*****



*Cikin labari*


Bayan Sauban ya gama faWawa Captain Fu'ad yadda sukayi da Mominsa harda soyayyarsa yanzu ta ullu a tsakaninshi da Khairat, ya wuce gida.

Kwana uku da zuwansa gidan Captain Fu'ad sai ga Maryam ta shigo gidan kamar an jefota,a lokacin yana falo ya baje abincin da yayo takeaway Winsa yana ci.Sallama tayi ta shigo tare da akwatinta,babu yabo babu fallasa ya amsa sallamarta ya cigaba da cin abincinsa hankalinsa kwance.Kasa hauri Maryam tayi ganin yadda bai nuna yayi maraba da zuwanta ba ta ce

"Haba Sauban ko sannu da zuwa babu"

"Oooh sorry,sannu da zuwa"

ara maida hankalinsa yayi ga abincinsa,sai can ya ce

"Hope kin gyara halin naki da nace ki gyara"

Kallonsa tayi da mamaki wai halinta,to ita wani hali take dashi da zata gyara mtsw! Sai kuma can ta ce

"Na gyara shikenan"

"Better"

"Wai Sauban wani irin wulaanci ne haka,jiba yadda kake amsamin magana babu kulawa haba"


Cak ya tsaya daga cin abinsa,sai ya Wago yana kallonta asa da sama a zuciyarshi yana cewa 'Wai me wannan take dashi da na dage sai na aureta,gashi babu abinda na mora sai wahala,damn it! ' katse mishi tunani tayi da cewa


"Ko zuwa gidanmu bikona bakayi ba,gashi ba kira a waya balle nasan ka damu dani,yanzu kuma na dawo ko maraba ba kayi da zuwana ba,wai miye haka,nima fa shegiyar kaina ce wallahi,bar ganin kana duka na ina yaleka,kaci darajar son da nake maka ne wallahi"


Wannan karon miewa yayi yana mata wani shegen kallo irin na in kin isa,sai kuma ya saki yayataccan murmushi yana kallonta kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya ce


"Darajar so huhhh!!! Kina sona ne kike zagin Mom Wina? Kina sosa ne kike in abinda nake so? Kina sona ne kike faWamin baar magana,haka ake so a garinku? To bari kice gwara na sanar miki tun yanzu karki ce na munafin ce ki AURE ZAN ARA"


Darammm!!! Dammm!!! Darammmm!!! Tashin hankali wanda ba'asa mai rana,zuciyar Maryam ce ta tsinke lokaci guda,wawalwarta ta tafi hutun wucin gadi na wasu sakanni,kirjinta dukan tara-tara ya fara bama uku-uku ba,dafe irjinta tayi da hannu bibbiyu tare da waro idanunta waje tana cewa

"Kishiya Sauban zakamin!!! "

"warai kuwa Maryam"

Ai wani irin daka tsalle Maryam tayi,haWe da cira gyalanta da Wan kwalinta lokaci guda tana cewa cikin masifa da bala'i har idanunta sunyi ja


"Kan bura Uban can!!! Wallahi tallahi baka isa ba!!! Yau akwai bala'i a gidan nan!!! Yau akwai yain duniya na uku a gidan nan!!!...............





Mu haWu a pages na gaba don jin wannan Chakwakiyar chakwalkwalin da yake faruwa a gidan LOVE BIRDS wato=J=J=J Sauban da Maryam====
'
'
'



*****shin su Umma Kande da Maman Jummalo sunyi nadama ko ko har yanzu akwai sauran rina a kaba???......






*****Shin mai yasa Dr Nabila take kyautatawa Sa'eeda sannan wasu abubuwa takeso ta tabbatar game da Sa'eeda???......



****shin Maryam zata yarda Sauban ya ara aure kuwa,ganin yadda ta haukace lokaci guda???......



Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku

Please Login or Register in order to submit comment