Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da turare suka fesa sai suka tari mai machine wanda a nan ma sai da suka daWe sannan suka samu mai machine ya Waukesu zuwa cikin auyen daga nan suka nufo tasha sai gida wanda basu suka iso gida ba sai wurin 5:00pm na yamma,a gaggauce sukayi wanka sannan suka baje don huta gajiya.


***Tunatarwa***


****Shin bakwa tunani akwai mata masu irin wannan Wabi'ar irin nasu Umma Kande da Maman Jummalo na son abin duniya da dogon buri a duniyar nan ???
Tabbas!!! Har yanzu akwai mata masu wannan Wabi'ar zuwa wurin boka da neman biyan buata wanda a arshe halaka suke faWawa sannan imaninsu ya ragu!!!
Yake ar uwata mai daraja kisani zuwa wurin boka ko malamin duba ba mafita bace agareki hasalima ara nisanta kanki kike daga rahmar Ubangiji,amfaninsa na Wan wani lokaci ne zai miki wanda a arshe illarsa tafi dutsen Uhudu a girma.
Shin mai zai hana cikin salisalin dare a lokacin da wasu suke bacci ke kuma ki tashi ki Wauro alwala kiyi sallar nafila koda raka'a 12 ne sannan kiyi wutri ki sallame,kina mai kirari ga Ubangijin Talikai akan ya biya miki buatunki na fili da na Soye kina mai an-an da kanki a garesa.Tabbas zakiga canji a rayuwarki imma kishiya ce ta tasoki a gaba kina sallar dare tare da azkar Win safe da na yamma wallahi kinfi arfinta da tsafinta da ikon mai sama.amma karki Sata lokacin a banza tare da aljihunki wurin zuwa gun boka,wai shin ba kuga Umma Kande da Maman Jummalo yadda suke wahala bane gun boka sannan koda ya biya musu buata a arshe wahala ce zata koma.
Misalin nemama yaransu mazaje da sukayi wurin boka Sankeru bayan yace musu suna son kowani irin mazaje ga yaransu masu kuWi suka aminta sun manta da kalmar kowani iri yana nuni da koda mara kyau ne ko kuma masu cutarwa amma suka yarda,zakuga yadda zasu are a arshe.Allah yasa mufi arfin zuciyoyinmu ya kuma tsafe mana imaninmu.******

@@@@@@@@@@@@@
Cikin Labari

Maman Jummalo ce bayan sun Wan huta sunci abinci ta ce ma Umma Kande wacca tayi WaiWai da afafunta a tabarma "awas ina kike ganin zamu samu jinin karnuka har kala biyu ,sannan muyi yanda boka Sankeru yace damu?

"A tunani na mai zai hana mu samu gwarawa tunda kinsan suna cin karnuka da aladu"

" Haba! "

"Allah kuwa,ke bara ma kiji har tsire da balangun karnuka sukeyi"

"To ke ina kika san suna tsire da balangun karnuka" cewar Maman Jummalo tana rie baki tsabar mamaki

"Nima Musa ne wani zuwa da yayi yake bani labari,inyamurai da gwarawa suna cin karnuka sosai,ya ara da cewa acan Calabar suna da kwa'ta nasu na kunsu,inda ake siye da siyarwan naman aladu da na karnuka,shiyasa ma bayacin namansu don baisan ko naman alade ko na kare ne suka sa a abincin ba"

"Allah Waya gari bambam,to shikenan faWuwa tazo dai dai da zama,kinga sai mu nema inda gwarawa suke a nan ko"

"Hakane kuwa,Allah ya kaimu gobe sai mu nema kwa'tan nasu,shikenan ma cika aikin boka Sankeru da wuri"

"Sosai ma kuwa,wallahi na agara yaran nan suyi aure mu huta"

"Nima kuwa awas"

Da wannan hirar su Umma Kande sukaci lokaci suna yi sannan Umma Kande ta nufo Wakinta dan kwanciya kasancewar a Wakin Maman Jummalo suke hirar.an matan nasu suna waje suna hira da samari sannan daga baya kowacce ta shigo gida wanda lokacin kusan arfe 10:00pm da wasu an mintuna,amma ko ajikin iyayen nasu.

@@@@@@@@@@@@@

Kamar yanda suka shawarta akan neman inda kwatan gwarawa yake aiko sunyi sa'a don sun samu kwa'tan gwarawa a cikin Farin gida wanda yake hanyar Mando.Sun samu ana gab da fara yankan karnuka da aladu dayake da sassafe suka fita,nan suka fara ai watar da aikin boka Sankeru sannan suka nufo gida dan kammala aikin.

Haka suka yi exactly yanda boka Sankeru ya ce dasu don kar asamu kuskure.Yaransu suka taru wuri Waya kamar yanda boka Sankeru ya ce dasu.

Da Iklima aka fara,matsowa kusa da bottle Win ruwan tayi sannan sai Umma Kande tace ta wanke fuskarta sau uku,haka tayi yanda tace ba tare da musu ba,sai Jummalo itama tayi yanda Iklima tayi, sannan Zaliha.

Duk wannan abun da suke Nusaiba na gefe ta chatting abinta.Maman Jummalo tace da Nusaiba tazo itama tayi,dan taga alama batada niyyar yi kamar yanda an uwanta sukayi.

BuWar bakin Nusaiba tace"Nifa gaskiya bazanyi wannan abun ba,kawai kuyi hauri dan komai zakumin bazanyi ba"

"Laaaaa!ehhh lallai Nusaiba wuyanki ya isa yanka" cewar Umma Kande

Kowa a Wakin duban Nusaiba yake da mamaki itako ko ajikinta don ta rantse bazata wanke fuskarta ba kamar yanda taji jiya Mamanta suna hira da Maman Jummalo.

Waiwaye

Alokacin da su Umma Kande suke tsaka da hirar yanda zasu samo jinin karkuna susa a maganin da boka Sankeru ya basu,ita kuma Nusaiba ta dawo kenan zata shigo Wakin Maman Jummalo dan nuna mata wani sabon film a waryata dayake Maman Jummalo akwai son kallon fina finai.

Isarta ofar Wakin keda wuya ta jiyo hirarsu akan aurar dasu zasuyi aikuwa tsayawa tayi wurin ofar Wakin taji komai sannan ta wuce Wakinsu a zuciyarta tana faWin 'Wallahi ba auran da zanyi,kurum ina cikin cin duniya ta da tsinke zaku wani tado da batun aure to wallahi bazata saSu ba wai bindiga a ruwa,bazan taSa yin yadda kuka ce ba,bayan auran babu komai cikinsa sai wahala da bauta,gashi sugar Wina Alhaji Sagir yamin alawarin dani zaije Dubai muyi sati Waya kuma nasan zan ara wayewa ,da sake wallahi inaaaa tabb!!

aukar buta tayi ta nufa bayi dan karma mamanta tasan da dawowarta gidan.

Cikin Labari

Maman Jummalo ce ta katse shirun da mamakin da ya cika an Wakin dashi "Haba Nusaiba gata fa muke muku,kowace mace ba tada buri inta girma tayi aure ta hayayyafa,kinga ba daWinmu bane ace muganku haka ga samari Allah ya baku amma ba kuyi aure ba,kuma ku kanku kunsan da zunWen an layi da muke sha mu da ku"

"Nasan da wannan Maman Jummalo amma gaskiya kumin uzuri bazan wanke fuskana ba da wannan ruwan, shi aure ai nufi na Allah ne ,kuma yanada lokaci,idan lokacin aure na Allah ya nufa nayi ai zanyi basai kun Sata kuWinku".(Hakane kam Malama Nusaiba ikon Allah===C).

"Yanzu Nusaiba watsa mana atsa a ido zakiyi kenan ,kinsan wahalar da mukasha duk don faranta muku rai amma da abinda zaki saka mana dashi kenan" cewa Umma Kande

"Nifa sai dai ayi hauri amma bazan wanke fuskana ba wallahi" cewar Nusaiba tare da mikewa ta fita daga Wakin,kowa ya bita da kallo haWe da mamaki musamman su Umma Kande da Maman Jummalo don su kaWai suka san wahalar da suka sha kafin samin wannan maganin.

Babu yanda suka iya tunda tace bataso ,ai ba tilas farin cikinsu ma shi ne su sauran yaran sunyi musu biyayya kuma suna sa ran haarsu zata cimma ruwa koda Nusaiba kaWai ce batayi aure ba sun rage jin surutun mutane akan yaransu.

@@@@@@@@@@@@@@

Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta sunata shirye shiryan fara karatun Sa'eeda a KASU.Babu laifi Sa'eeda ta Winka an kalolin kayanta kala shida da hijabai uku da veils guda uku, sai takalma uku da jakar makaranta ar madaidaiciya sai kuma side bag Waya baa.Umman Sa'eeda ta siyoma Sa'eeda waya Vivo ar arama second hand wacca batasha jiki ba saboda tasan zata buaci babbar waya tunda yanzu tana a university ne.

Haia Sa'eeda tayi farin ciki sosai da wannan wayar duk da arama ce amma ji take kamar iphone 14 pro max aka bata,tana tama Ummanta godiya yafi cikin kwando.

Kasancewar yau asabar,Umman Sa'eeda da ita suna Waki suna hira akan batun shirin fara karatun Sa'eeda ranar Monday

Umman Sa'eeda tace "Sa'eeda Monday zaku fara karatu,ina mai miki nasiha da kiji tsoran Allah a duk inda kike,ki guji awayan banza wa'inda suke kai mutum ga halaka,ki maida hankalinki sosai akan karatunki,banda samarin banza duk da inada yaini akan tarbiyar da na Woraki akai,amma kiji tsoran Allah ba mutum ba,ki kasance mai hauri da juriya tare da yafiya wa wa'inda suka zalinceki,amma karki yarda a wulaantaki ko kuma a takaki ,ki kasance jaruma mai fuskantar duk wani alubalan da zaizo miki a rayuwa hakan zaisa ki cimma babban rabo a rayuwarki,banda kwaWayi da hangen nesa,kinga dai yanda Allah ya yayi damu don Allah ki gode masa banda kallon na sama dake a kullum ina baki shawaran ki dinga duban na asa dake hakan zaisa miki natsuwa da kuma godewa Allah akan ni'imar da yayi miki bisa wasu"

Ta Wau lokaci tana ma arta nasiha game da rayuwa tare da hankaltar da ita abubuwa da yawa dangane da rayuwa,kasancewa University zata fara zuwa,akwai kala kalan mutane a can,wanda kamar bariki ne kazo nazo kowa yana yin yanda yaso ne babu takura ba kamar secondary ba shiyasa tayi mata nasiha duk da ta yarda Wari bisa Wari akan tarbiyar arta.

Sa'eeda dai shiru tayi tanajin nasihar Ummanta wanda ke ratsa ashinta ya shiga cikin jijiyoyinta har ya kewaye ko'ina na jikinta,haia jikinta yayi sanyi sosai kuma tasa aranta duk wuya duk rintsi bazata wofantar da nasihar Ummanta ba,kamar painti ne a dutse wanda baya taSa goguwa ,haka kamar kwaWone wanda aka kulleshi ta key sannan aka jefa key Win a tsakiyar taiku wanda babu ranar Waukowa to haka ta Wau nasihar Ummanta.

Bayan ta kammala mata nasihar ne ta ara da cewa"Niko Sa'eeda na manta ban faWa miki ba na samu aikin gwamnati za'a dinga biyana dubu #20,000 duk wata,kinga zan dinga saving Win #5000 a banki saboda registration Win karatunki na duk shekara,sai kuma #15,000 na dinga baki kuWin mota sannan kuma sauran muci abinci dasu"

Murna Sa'eeda ta somayi don jin wannan abin alkhairi daya samesu,haia Allah abin godiya ne,cikin murnar Sa'eeda tace "Ummina wani kalan aikin gwamnati kika samu kuma waya miki hanyar aikin?..................

**Maa shaa Allah Fans wani kalar aiki kuke tunanin Umman Sa'eeda tasamu???
**Shin kuna ganin Sa'eeda zata Wauki nasihar mahaifiyarta idan ta fara karatu a University???
**Da gaske kamar yadda boka Sankeru yace auran yaransu Umma Kande da Maman Jummalo yazo shin yazo Win ko akwai matsala???
Duk ku tattaro ku hanzarto ku biyoni muje zuwa amsoshinku suna nan tafe
'
'
'

Ina matuar alfahari daku my Esteem Fans<<9<<,I love y'll=ؖ=ؓ=؝=ؗ



Daga alk'alamin

=؍=Narnarhh Bukar ==؍

Comments and share =O=O=OFisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:




[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:

< NACINA YAJAWOMIN<


Narrnarhh Bukar
'

<9Perfect Essential Writer's
Association<9
(' P. E. W. A('

Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002

1 5  -1 6

Murna Sa'eeda ta somayi jin wannan abin alkhairi daya samesu,haia Allah shi ne godiya ,cikin murnar Sa'eeda ta ce "Ummina wani kalan aikin gwamnati kika samu kuma waya miki hanyar aikin?"

"Aikin sharan titi ne gwaggo Lantana maociyarmu tamin hanya shima da yar na samu kasancewar banyi makaranta ba,dayake ina da rabo Wanta yayi min cuku cukun primary certificate sannan suka Waukeni,wani watan mai zuwa zan fara aiki in shaa Allah"

Shiru Sa'eeda tayi tana duban Ummanta 'Ya Salam yanzu Ummanta ce da sharan titi duk don ta rufama mana asiri kar mu tagayyara,Allah ka kawo mana agaji a lamuranmu baki Waya '

Duk wannan zancen a zuci takeyinsa , shiru tayi tana duban Ummanta sannan ta sauke sassanyar ajiyar zuciya sai kuma ta ce"Ummina yanzu sharan titi zaki fara yi kenan"

Tayi magana cikin sanyin muryar mai nuni da tsintsar damuwa.

Murmusawa Umman Sa'eeda tayi don tasan za'a rina shiyasa ma tun farko bata nemi shawararta ba don tasan hanata zatayi,amma wannan ce damarsu wacca zasu rufama kansu asiri tunda wankin da takeyi ba iya Waukar nauyin karatun Wiyarta zaiyi ba hasalima iya abinci kawai yake isarsu shima Win ba mai daWi ba.

"Nasan zaki ce haka,amma Sa'eeda bamu da wata hanyar bayan wannan kuma da kike cewa sharan titi ,ai zan dinga saka niaf saboda maganar mutane,kinga yanzu ba komai zan samu daga Abbanki ba,hasalima hankalinsa ba akan mu yake ba,to idan banyi wannan aikin ba ina zan samu kuWin motan da zan dinga baki kullum sannan ina zan dinga zamun kuWin biya miki registration duk shekara,ko da kuWin wanki ne zai biya mana dukkanin buatun mu? "

"Hakane Ummina,Allah ya cigaba dayi mana jagora tare da rufa mana asiri duniya da lahira"

Da"Allahumma Aameen"Umman Sa'eeda ta bita dashi.

@@@@@@@@@@@@@@@

Yau take Monday,Sa'eeda tayi shirinta tsaf,tafito Was abinta,doguwar riga six pieces na roba tasa ajikinta,tare da ar jakar makarantar ta wanda an wasu litattafai ne sai biro guda biyu a ciki.

Zama tayi bayan tasaka rigar, ta shafa Wan viseline Winta sai ta yamutsa powder kaWan ba mai yawa ba a fuskarta sai Wan kwalli a idanunta sai lipglow da tasha fa Wan aramin bakinta.Maa shaa Allah kawai zan iya furtawa,this is what we call natural beauty a turance,gaskiya Sa'eeda nada kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba amma tafi wacca tayi make up kyau da haWuwa.

Abinci taci sannan tayi nafila raka'a biyu saboda neman sa'a tare da neman tsari daga shirrin abubuwan da suke a cikin makarantar.

Daukan veil Winta tayi kalar kayan sai ta yafa sannan ta goyo jakarta a baya,sai ta dubi Ummanta tace"Toh Ummina zan tafi school"

"Ina nema miki tsari na daga abin cutarwa,tare da fatan Allah yasa ki fara a sa'a ki kuma kammala a sa'a tare da samun nasarori masu yawa,Allah ya albarkaci karatunki, ya kuma albarkaci rayuwarki baki Waya" haWe da shafa kanta tana murmushi

"Aameen ya Hayyu ya Gayyum" haka Sa'eeda ta furta tare da ara jin so da aunar Ummanta, haia tayi dacen samun uwa ta gari mai tsoran Allah haWe da hauri.

KuWin mota ta mia ma Sa'eeda sannan sukayi sallama,Sa'eeda ta fito daga Waki.

A tsakar gida kuwa Maman Jummalo ce tafito yin alwala kasancewar bata tashi sallar asuba ba,hasalima gwara ita akan sauran an gidan don Umma Kande sai wurin 9:00am take sallah su kuma sauran yaran sai sanda suka tashi daga bacci,kai kai kai abun dai babu tsari.

Da wani mayan kallo Maman Jummalo take bin Sa'eeda dashi tana ayyanawa a zuciyarta 'Gaskiya kyawun yarinyar nan ara fitowa yake kullum kamar ba cikin angin rayuwa suke ba'

Katse mata tunani Sa'eeda tayi da gaisuwa "Ina kwana Maman Jummalo"

"Lafiya lau,sai ina haka" tayi maganar ne dan ta bigi cikinta

"Makaranta zani" kasancewar Sa'eeda tasan kanta yasa tai sanar mata University zata tafi,hasalima ba susan yanayin karatunta ba.

TaSe baki tayi irin ko ajikinta Win nan,saboda yaransu sun wuce da ajinta. (Ni kuma nace sun wuce ajinta a jahilci ba===).

Ko irin a dawo lafiya Maman Jummalo bata iya ce mata ba haka tana kallonts wuce zuwa makaranta,dayake tsakanin gidansu da Kasu tafiyar mintuna arba'in ne shiyasa dole ta dinga hawan keke napep zuwa school.

Bayan ta fito gida ta tari mai keke napep a layin nasu kasancewar keke napep suna yawan wucewa saboda hanyar mai kyau ne babu tudu da kwararo sosai.

@@@@@@@@@@@@@@@

Lokacin da mai keke napep ya sauke Sa'eeda,Walibai maza da mata suna shiga cikin makaranta, mutane ne ba bambamta addini,al'adu da yaruka,itama sawunsu tabi zuwa cikin makarantar, dayake sanda suka zo screening har department Winsu sunje ita da Maryam yasa bata wani Sata lokacin neman faculty Winsu ba,direct ta wuce department Winsu,sannan ta nemi ajin an 100L ta shiga.

Tana shiga ta samu front sit ta zauna kasancewar ita ma'abociyar zaman gaba ne tun tana primary,bata daWe da zuwa ba sai ga Maryam ta shigo,tasha tsadaddun kaya kamar zata biki ga make up da tasha,ta Wauro jakar an gayu ,ga takalmi high heel da tasaka,tana wani cat walking ita ala dole ar jami'a.

Nufo inda Sa'eeda take da zama tayi tana murmushi suka gaisa sannan tace ita bazata iya zaman gaba ba daman itama tun primary a middle seat take zama,ai kuwa taci sa'a mace Waya ce a seat Win,tako je ta zauna.

A haka Walibai sukaita shigowa har Head of Department Winsu ya shigo yayi welcoming Winsu tare da yi musu nasiha da jan hankali akan karatunsu,sannan daga baya lecturers suka fara shigowa haWe da introducing kansu ga Waliban da course Win da zasu dinga offering Winsu dashi.

@@@@@@@@@@@@@

A nan ne kowa ya bada number wayarshi saboda za'a buWe class group,haka kowa ya bada number shi,kasancewar Sa'eeda sabon layi ne akan wayarta bata haddace ba ya sakata ciro wayarta dan ta duba number nata,ji tayi a bayanta ance

"Ikon Allah ashe daman har yanxu akwai vivo,ai duk na zaci an primary suke amfani da vivo dan yin games ba an University ba" cewar wata matashiyar budurwa

Ta kusa da itace ta amsa da cewa"Wallahi kuwa kamar ma second hand ne a hannunta"

"Second hand ne kuwa,tabb wallah ko anina wanda yake secondary infinix daddy ya siya mai"

Suko an aji kowa kallonta yakeyi ,wasu na zunWenta,wasu kuma na gulmarta,duk tana jinsu amma babu wanda ta kula,hasalima haddace numbanta tayi sannan ta maida wayarta jaka ta bada number ko a jikinta.

Kasancewar yau ne aka fara karatu,ajin nasu bai ciki ba kuma ma lecturers ba kowa ya shigo ba sai next week karatu zai fara zafi,shiyasa suka tafi gida da wuri.

Bayan tun fito ne Maryam ta dubi Sa'eeda ta ce"Yanxu ki rasa wayan da zaki siya sai vivo kuma ma vivo arama,haba wannan ba class Winki bane wallahi,duk da bani aka yarfa a ji ba amma duk naji kunya"

Dariya Sa'eeda tayi sannan ta ce"Akwai wanda a cikinsu ya bani kuWin shiga wannan makarantar ne,ina ruwansu da wayana,inason wayana kuma ina jinta kamar iphone ,don ko a jikina don sun yarfani,hakan bai dameni ba,karatu ya kawoni ba nuna waya ba"

TaSe baki Maryam tayi sannan ta ce" Mu kuwa duka ya kawo mu"

"Toh Allah ya bada sa'ar haka"

Dayake hanyarsu Waya ne haka suka nemi mai keke napep suka nufo gida wurin arfe biyu.

Haka Sa'eeda ta cigaba da zuwa school har satin ya are,a sannan ne class time table Winsu ya fito,zama tayi tama kanta special time table na gida don tanaso tafito da flying colours kuma hakan bazai samu ba sai ta maida hankalinta Wari bisa Wari a karatunta sosai. Wannan kenan

@@@@@@@@@@@@@@@

Bangaren su Umma Kande kuwa sai dai sambarka,kamar yanda boka Sankeru ya musu alawarin yaransu za suyi aure to hakan ta kasance.

Kwana Waya da wanke fuskokinsu samari musu kuWi suka musu ca wurin neman auran yaransu.A satin ne kowaccansu ta fidda miji wanda iyaye suka shigo ciki,haka Maman Jummalo ta tafi auyansu dan sanar da auran Jummalo, itama Jummalo da saurayinta suka je auyansu gaishe da dangin mahaifinta , saurayin ya gabatar da kansa kuma yace nan bada jimawa ba zai turo da iyayensa ayi maganar aure.

Bangaren Abban Sa'eeda hakan ta kasance saida yaje garinsu duk da ya jima rabonsa da garin nasu dayake iyayensa duk sun rasu saidai yayyi da anne,duk da Umma Kande taso ta hanashi zuwa amma Maman Jummalo ta hane ta saboda gulmarta za'ayi a ce babu dangin mahaifin yara sai dai na uwa kuma hakan ba daidai bane ,da wannan yasa Umma Kande haura don batason danginsa su raSeshi gashi ba sonta suke ba sunfi son Umman Sa'eeda.

Duk wannan zancen auran da akeyi banda Nusaiba, hakan baima Umma Kande daWi ba amma babu yadda ta iya,arya Nusaiba ta shiryawa Mamanta wai awarta zatayi aure a sokoto kuma sun shau da juna sosai tanason taje bikin,babu musu Umma Kande ta amince da tafiyar.(Anyi daiiyar Uwa a nan,gaskiya su Nusaiba basuyi dacen Uwa tagari ba>>>)

Haka ko Nusaiba ta shirya an kayanta a aramin akwati a cewarta ta tafi sokoto biki,ashe Dubai zasu ita da Alhaji Sagir,fitarta gida ta kirashi yazo ya dauketa daman ya daWe da mata visa nafita asar waje,a ranar suka cillar sararin samaniya zuwa Dubai.(Nusaiba ikon Allah,ba sabamba an hau jirgi,banda auyanci dai acan===)

Bayan dawowan Abban Sa'eeda ya sanar da Umma Kande akan amincewar danginsa,sai kuma ya ara da cewa"Lokaci kaWan za'a sa ranar bikin nasy,ayi a huta gaba Waya"

Hakan yama Umma Kande daWi sosai,kamar yanda yace lokaci kaWan za'a saka bikin,haka kuwa akayi dan wata Waya aka saka bikin nasu su ukun,haka su Umma Kande suka fara shirye shiryan biki.

@@@@@@@@@@@@@@

Bangaren su Sa'eeda kuwa lectures ya soma zafi,gashi kullum sai sunje school harda ranar asabar wani lokacin.

Duk karatun da aka musu a aji idan ta dawo gida sai ta tabbatar da ta iya sosai kuma ya zauna a brain Winta sannan hakalinta yake kwanciya,ta lura an ajin basa sonta saboda yanda idan akayi tambaya a aji take bada amsa har wani lokacin lecturers na mata kyautan marks hakan baya musu daWi sai suyita hararta wasu har tsokanarta suke da hajiyar Vivo,tana jinsu amma bata tanka musu hasalima ita ta saba da irin wannan halin na an aji tun tana secondary ake mata hassada kuma hakan ba damunta yake ba karatu tasa agabanta,duk da ba cika son bada amsa take ba sai idan malamin zai zagi an aji shi ne take tashi ta bada amsa.

Bangaren Umman Sa'eeda kuwa ta fara zuwa aikinta na sharan titi ta wurin makarantar su Sa'eeda kasancewar nan ne portion Win da aka Wibar mata, kullum a tare suke fita gidan ita da Sa'eeda,dayake da wuri Umman Sa'eeda take kammala sharanta ta dawo gida sannan kuma da Wora da wankin mutane.(Allah sarki Umman Sa'eeda wataran sai labari===)

Umman Sa'eeda tasan da maganar auransu Zulaiha amma tunda ba'a sata ciki ba,nata kallo ne,don wani lokacin habaici da gori suke mata wai arta batada farin jinin samari,idan taji suna wannan zancen sai tayi dariya tace kwata kwata nawa Sa'eedar take da za'a ace batada farin jinin samari.

@@@@@@@@@@@@@@@

Wasa wasa lokacin biki ya arato,baifi saura kwana biyar ba.A wannan lokacin ne akaita kawo lefan an matan guda uku,babu laifi Naira tayi kuka,saboda dukkaninsu akwati 12 aka kawo musu kamar haWin baki(Ni kuma nace maganar asiri ce fa ske malam,ai har fin haka ma zasuyi,saidai su jira sakamako =>), ga kayan ciki nagani na faWa ne bancin gwala gwalen da aka narka aciki.

Maota da an layi kowa zuwa ganin kwakwaf yake don aji daWin gulmar dakyau,su Umma Kande da Maman Jummalo sai Waga kai suke suna yada magana tare da habaici akan gorin da ake ma yaransu akan sun i aure sai tara samari yau gashi Allah yayi an bain ciki saidai su mutu.

an uwa na nesa da na kusa sun fara zuwa tun daga dangin Umma Kande na Maiduguri,da na dangin Abbansu Sa'eeda tare da dagin Maman Jummalo duk sun fara zuwa,kasancewar gidan an sake gyarashi haWe da arin Wakuna dayake gidan akwai fili sosai.haka bain suka samu wurin kwana.

A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu........................

****Tofa ya akayi daga sallamar Musa Kowa ya bishi da kallo har da sakin baki,mai hakan yake nufi>>>

***ya kuke tunanin rayuwar Sa'eeda a jami'a,shin halayanta masu kyau zasu Waure ko ko zata sauya hali.....???

***My Esteem fans ga dai su Umma Kande da Maman Jummalo ana shirin aurar da yara,shin kuna tunanin sunyi dacen mazaje ko ko akasin haka kamar yadda Boka Sankeru yace zasu samu kowani irin mazaje.........???

Duk ku biyoni zuwa next page don jin amsoshinku
'
'
'

Ina Matuar alfahari daku my Esteem Fans=ؖ=ؖ=ؖ

Daga alalamin

=؍=Narrnarhh Bukar ==؍

Comments and share =O=O=OFisabilillah.



[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:




< NACINA YAJAWOMIN<




Narrnarhh Bukar
'


<9Perfect Essential Writer's
Association<9
(' P. E. W. A('


Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002




1 7 ---1 8

A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu.

"Mai zan gani ni Hafsy,Musa haka ka koma !!!" cewar Maman Jummalo wacca fitowarta kenan daga Waki.

Wa'inda ma basu san da dawowarsa ba kowa ya bisa da kallon urilla,gaskiya dole Maman Jummalo ta ce mai zata gani ita Hafsy,haia duk wanda yasan Musa dole yayi mamakin ganinsa haka.

Mutumin da a da bai ne sosai yanzu ya koma fari sai kace bature,bancin haka ga wani askin an iska da

Please Login or Register in order to submit comment