Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take ba saboda duk tafi su komai,ga shegen kyau da farin jini uwa-uba samari masu kuWi,to taya zata aunaceta,tabb ai yanzu ta fara tata hassadar,babu gudu babu ja da baya,ar Gwaggo Ladi ta biyu ce wato Na'ima ta fara magana cikin sanyin murya mai nuni da nadama


"Hussaina ki yafe mana laifukan da muka miki a baya,ni da ar uwata...."


"Ke kaWai banda ni wallahi,Allah ya tsareni da neman yafiya gun wannan marar asalin" cewar babbar Wiyar Gwaggo Ladi wato ar yaya


Kowa a wurin mamaki ne ya cikasu,musamman Gwaggo Ladi wacca tayi mutuwar zaune jin babbar Wiyar ta da irin wannan magana,koda yake daman tun suna ananu ba aunar Hussaina take ba,wani lokacin ma ita take ara zuga Gwaggo Ladi, to amma yanzu fa tunds ba wani riba suke samu ba,cikin Sacin rai Gwaggo Ladi ta ce


"Yanzu ke ar yaya bazaki hankalta ba,ar uwarki tayi nadama amma banda ke,yanzu wani riba kika samu ne,amma kije kiyi mudai mun tsame hannayanmu daman Mairo tun fil-azal tana aunar Hussaina, ita bana shakku akanta,amma ke Win nan"


Nuna arta tayi sannan ta cigaba da cewa


"Kije ya rage naki"


"yale wawuya wacca batasan meke mata ciwo a kwanyar kanta ba,kowa ya ajiye makaman yainsa banda ke, kije da halinki"
Cewar Baba ransa a Sace


Tsam! Ta mie ba tare da ta kalli kowa ba ta fita abinta,kowa da ido ya bita dashi,tare da adduar Allah ya dawo da ita hanyar gaskiya. Gyaran murya Uncle Hassan yayi,daman tunda ake hirar bai ce *Ta tafasa balle sauke ba* Sai yanzu yakeson yayi bayanin maasudin abinda ya kawosu garin,magana ya fara


"To Alhamdulillah ala kulli halin,sannan muna godiya a gareka da taimakon mahaifiyarmu tare da ar uwata da kayi,bansan da wasu lafuzza zanyi amfani dasu wurin maka godiya akan taimakon da kayi mana wanda da badan Allah ya addaro ka taimakesu ba da bamusan wani hali zasu shiga ba,muna jinjina a gareka,sannan magana ta biyu shi ne sakanya Alkhairi da alkhairi zamuyi iya oarinmu akan sakanya maka da taimakon da ka mana,duk da nasan bazamu taSa iya saka mata da alkhairin da kayi mana ba,mun yanke shawarar kaika aikin hajji na wannan shekarar sannan zamu siyan maka gida a birni bayan haka za'a siya maka shaguna wa'inda zaka dinga samun kuWin shigowa duk da zamu dinga turo maka da kuWi duk wata na siyan kayan abinci,bancin haka idan ka yarda yayan mahaifiyata ya ce inda hali yanaso kazo kaida ahalinka ku Wanyi kwanaki acan saboda za'a tara an uwa domin suyi maka godiya akan taimakon da kayi mana"


"Allahu Akbar,Tsarki ya tabbata ga Ubangijin Talikai,domin nufinsa ne ba namu ba,wa'innan abubuwan alkhairai haka duk saboda taimakon da nayi muku na cancanci dumbin alkhairai haka,na rasa wasu kalamai zanyi amfani dasu wurin gode maka...."


"A'a Baba muke da godiya domin kafi haka,mu mukafi cancanta mu gode maka har arshan rayuwarmu domin samun mutum irinka a wannan duniya akwai wahala,babu abinda zamu ce maka sai godiya"


"A'a Wana kyaututtukan nan sunyi yawa,kabar maganar siyan gida a birni,wannan da muke ciki ya ishemu,kwata-kwata rayuwar kwana nawa ne zakaji ance mun tafi"


"A'a Malam ya yaro yayi niyyar siyan mana gida a birni zakace a'a,haba ai wannan *Buulu ne* wallahi ,Allah yace mu huta kaiku kana a'a Tab!" cewar Gwaggo Ladi tana gyara zamanta.


"Yanzu Ladi a wannan shekarun naki kike magana hutu,keda kike fuskantar abari amma kina maganar zuwa birni"



"A'a Malam bana fuskantar abari,mutuwa ba yanzu ba da yardar Allah kuwa"


Dariya maganar Gwaggo Ladi tabama kowa,wato tsoran mutuwa take haka,shima kansa Baba saida ya dara irin wannan tsoro haka,ita kuwa sai faman anance idanunta take tana Sata fuska irin an Sata mata rai,a cikin zuciyarta tana cewa 'Al Qur'an sai munje birni ko kai ko kaso,kawai muga samu muga rashi,idan kai kai zuwa toni tafiyata zanyi wallah,muje can muyi *ara'i* kuwa.Umman Sa'eeda ne ta ce



"Wata shawarar ta faWomin,tunda Baba zaije Hajji kaga saisu tafi tare da Gwaggo Ladi, hakan zaifi dacewa"


"iyar nan da gaske wayyo daWi,ashe zanga Wakin Allah da dabinon annabi harda zam-zam da safa da marwa,wayyo daWi,ke ar nan Allah yayi miki albarkha da ahalinki,ya jian Maimunatu mutuniyar kirki,ayyyiririiiiiiiii!!! "


GuWa Gwaggo Ladi ta cillara wanda ya karaWe gidan baki Waya kasan mutan da an iya guWa,tare da mie tana juya tana cewa


"iyar albarkha Hussainatu!!! iyar alkhairi Hussainatu!!! Mai imani sai Hussainatu!!! Um-um-um-um um-um-um!!! Mace mai kyauta sai Hussainatu!!! Kai aaaayyyyiiiririiiiiiiii Hussainata!!! "


Babu wanda bai dara ba musamman Sa'eeda cikinta kamar zaiyi ciwo saboda dariya koni mai Wauko muku rahoton saida na dara domin yadda take tiar rawa babu ji babu gani dole kayi dariya,harta Uncle Hassan ya dara tare da mamakin wannan tsohuwar da alama tayi rawar kai a sanda take yarinya.Baba tsoho ne ta katse musu dariya da cewa


"Haba Ladi wannan ba girmanki bane rawa,kin tsufa amma bakisan kin tsufa ba,haba don Allah,kinga amfani taimako a rayuwa ko Ladi,kinga a sanadin taimako Allah ya nufemu da tafiya aikin hajji a wannan shekarar,shiyasa nake ce miki a kullum ka taimaki wanda yake buatar taimako domin bakasan wataran ya rayuwa zata kasance ba,ban taSa kawowa zanje aikin hajji a rayuwata ba,amma a *sanadin taimako* Allah ya nufeni da ziyartar Wakin Allah"


"Hakane malam sai yanzu na tabbatar alkhairi danone,sannan hassada ciwo ce babba maganinta sai Lillahi,gashi wacca nake ganin ba kowa bace ta biyamin aikin hajji,Allah kenan don Allah Hussaina ki ara yafemun"


"Haba Gwaggo ai na daWe da yafe miki,Allah ya yafe mana baki Waya"


Ameen kowa ya furta a bisa labSansu,sai wurin yayi shiru kamar mutuwa ta gitta,sai can Baba yace a Waura ma bai abinci,Uncle Hassan ne yace yazo musu da kayan abinci a booth bara a kwaso cikin gidan,fita yayi sannan yasa bodyguards kwaso kayan abinci zuwa cikin gidan kama daga buhun shinkafa ar gwamnati,katon Win taliya,maccaroni,kwalin indomie,galoon Win mangyaWa,manja,krate-krate din kwai,madara da dai sauransu,haka akayita shigo dasu ciki gidan,mai Gwaggo Ladi zatayi inba callara uban guWa ba tana rawa harda juyi tana cewa


"Alkhairi ya samesu!!! Alkhairi ya samesu!!! Yiririii nanaye!!! Yiriri nanaye!!! Zamuci daWi kai kai!!! Zami ci daWi kai kai!!! Casssss!!!! "


A nan ba su Sa'eeda saida suka dara sosai,ashe haka wannan tsohuwar take da darun tsiya,saima taje birni a gaskiya akwai cin dariya wallah,cewar Sa'eeda a cikin ranta tana dariya. Haka aka gama shigo da kayan sannan Uncle Hassan da Baba suka tafi masallaci tare da wasu bodyguards,a gida kuma Mairo da yayarta Na suka Wora sanwar rana saboda bai,bayan Mairo tasa an yanka zabbi har biyar daga gidan saboda bain,su Umman Sa'eeda da Momin Sadam da Sa'eeda wani babban Waki aka ware musu ba kamar Wakin da aka bama su Umman Sa'eeda a shekarun baya da sukazo ba,wannan Wakin babba ne ga kuma babbar kafita da wata arama,ciki suka shiga tare da Waukar butoci domin alwala tare da sallah.su Mairo da yayarta sai gyaran kaji suke harda Gwaggo Ladi uwar daru,babbar yayarta tasu wacca Gwaggo Ladi take kiranta da ar yaya har yanzu bata dawo ba,tana can bain ciki ya ara lulluSe zuciyarta ganin Umman Sa'eeda cikin kwanci      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  yar hankali da wadata ba kamar a da ba duk da ada Win ma tafisu.A can gidan ar yaya sai kai da kawo take tana neman yadda zata illata rayuwar Umman Sa'eeda ,sai can tayi wani munafikin murmushi,tare da fita daga gidanta.


Gidansu Gwaggo Ladi ar yaya ta koma tare da arta lokacin har sun kammala cin abinci suna hira,Uncle Hassan da Baba suna zaure suna hira abinsu,su kuma bodyguards da drivers an kai musu nasu abincin kasancewar sai gobe zasu koma Kaduna.Da sallama ar yaya ta shiga gidan,amsa mata sukayi sai tazo wurin Umman Sa'eeda tare da durusawa tana neman yafiyarta akan laifukan da ta aikata mata,da murmushi a fuskar Umman Sa'eeda tace ta yafe mata,zama ar yaya ta samu tayi tare da shiga hirar anayi da ita,Gwaggo Ladi sai kallon ar yaya take saboda tasan halinta akwai manufa a wannan neman yafiyarta ta,tasanta tun tana yarinya bata bada hauri balle neman yafiya,uwa-uba harda durusawa,lallai akwai *Lauje cikin naWi* tana da manufa kenan,sannan bazata taSa bari ta cutar da Umman Sa'eeda ba saboda itama tayi taga babu riba balle ita,dole ta saka ido a duk motsinta, cewar Gwaggo Ladi wacca ta lula cikin kogon tunaninta akan babbar arta ar yaya.


Haka suka cigaba da hirarsu wanda sallah ce ke tasar dasu,su Mairo da Naima sai wurin arfe 8:45pm na dare suka tafi gidan,ita ar yaya bata wani daWe ba tace zata wuce gida sai gobe zata dawo, da Allah ya kiyaye hanyar gida suka bita dashi sannan suka cigaba da hirarsu.



Washe gari bayan kowa ya karya kasancewar da sassafe mairo ta kawo musu da abin karyawa,koda ar yaya tazo da nata abin karin ta samu har sun shirya harda su Baba da Gwaggo Ladi za'ayi tafiyan domin har kebbi State zasu bayan sunje anyi musu passport tare da visar tafiya asa mai tsarki,ciza yatsa ar yaya tayi saboda *plan A* Winta ya rushe,saura *plan B* wanda shi ne arshe,suna shirin tafiya sai ar yaya ta dubi Umman Sa'eeda tare da cewa



"Hussaina ni bana manta ba,ata ta tafi miki da gyalenki gidana ba,yoo ni ina na sani ashe gyalen yana a hannunta,saida muka isa gida sannan na lura"


Lokaci guda take maganar tare da ciro gyalen,murmushi Umman Sa'eeda tayi tare da cewa


"Karki damu ar yaya Wauka kawai nabar miki,kinga ga wasu kayan ma ki haWa dasu na baki kyauta"


Rasss!!! Rass!!! Rarasss!!! Rass!!! Rass!!! Haka irjin ar yaya ya daba domin idan Umman Sa'eeda bata yafa gyalen ba babbar matsala ce ba arama ba,saboda abinda tayi ma Umman Sa'eeda kanta zai koma idan Umman Sa'eeda bata amsa ba.



*Waiwaye*



A lokacin da ar yaya tabar gidan zuwa gidanta,tafiya take amma zuciyarta na *saa da warwara* akan yadda zataga arshan Umman Sa'eeda, daman ita tun tali-tali ba aunarta take ba,koda ta shiga Wakinta wanda ciki Waya kuma arami ga uban tarkace kala-kala saboda azama ce sosai ,ar yaya batayo gadon tsafta wurin Gwaggo Ladi ba,Mairo da ar uwarta sunfita tsafta da Waki mai kyau,su uku ne a wajen mijinsu kuma kowacce ita take cida kanta da aranta saboda mijin bai ciyar dasu gashi lusari ne na arshe,saidai idan ma sunyi su Wan sammishi yaci,malalaci ne na ajin arshe.


Kasa zama ar yaya tayi tana tufka da warwarar yadda zata Sullowa Umman Sa'eeda da sauri kafin su koma birni don ta lashi takobin kodai ta halaka Umman Sa'eeda ko kuma ta illata rayuwarta ta har abada,tafiya take a Wakin idan takai *Gauro sai takai mari* can ta saki wani munafikin murmushi tuno da malam Tanko Kwandi,babban malamin zaure ne a garin nasu,kuma malamin duba,yanada almajirai sosai a gidan nasa,nan da nan tafita daga gidan zuwa gidansu Gwaggo Ladi domin Waukar wani kaya na Umman Sa'eeda saboda shi malam Tanko Kwandi da kaya mutum yake amfani wurin yin sihirinsa,tare da wata arta taje gidan,daman tun a hanya ta tsara yadda zata nemi yafiyar Umman Sa'eeda tare da durusa mata wurin neman yafiya domin *Durusama wada ba gajiyawa bane* sannan dole ta koyi *ladabin kunama* ta yadda haarta zatafi saurin cimma ruwa,haka kuwa akayi domin duk plans Winta sun tafi a daidai har tayi sa'ar Waukar gyalen Umman Sa'eeda tare da ma arta lokacin hankalin kowa baya wurin,yarinyar ce ta fara fita sannan sai ar yaya daman tun a hanya ta sanar ma arta yadda zasuyi aikin,itama ra fita.(Ya Rahman tun yarinya na arama har ankoya mata makirci>>>)


Komawa gida tayi tare da siyar da wtea tunkiyarta ga maociyarsu sannan ta nufa gidan Malam Tanko Kwandi,tana isa babu Sata lokaci ta sanar masa abinda ke tafe da ita,bayan ta kammala bayananta ya fara zane-zane a asar dake gabansa,can ya Wago ya dubeta bayan ya kammala, saida ya fara sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ya fara magana


"A gaskiya bazamu iya kasheta ba,saidai mu illata ta idan kinaso,saboda ruhinta mai arfi ne bata wasa da addu'ah"


Shiru ar yaya tayi tana kallonsa,can ta ce


"Tunda shegiyar tanada ruhi mai arfi,jefa mata susar jiki,kaga shikenan kullum batada sukuni saina susar jiki"


Dariya sosai Malam Tanko Kwandi yayi can ya ce


"A gaskiya kinsan kan mugunta wallahi, zamuyi yadda kikashe amma fa akwai sharaWi mai girma atattare da wannan sihirin"


"FaWamin ko mene ne,zan cikashi indai har waccan shegiyar zatayi susar jiki a shirye nake"


Gyaran murya Malam Tanko Kwandi yayi kafin ya fara da cewa


"SharaWin shi ne,yanzu zanyi aiki akan abinda kika kawo sannan dole ki bata kayan tayi amfani dasu,idan kuma tai amsar kayan to kisani susar jikin kanki zata dawo sannan naki sai yafi nata sau miliyan"


Shiru ar yaya tayi tana nazari,ta yarda ko kuwa,wata zuciyar tana cemata *a'a* karta yarda wata zuciya tana cemata *Eh* ta yarda tunda tasan yadda zatayi ta amsa gyalen, gyaWa mishi kai tayi tare da cewa


"Na yarda"


"To shikenan idan aka samu matsala ba daga ni bane,ki kuka da kanki"


aukar gyalen yayi tare da yin wasu *Surkullensa* sannan ya yamutsa gyalen tare da tottofe gyalen da wasu surutai wanda ni kaina gwanar Wauko muku rahoto na kasan ganewa,yakai kusan mintuna sha-biyar yana wannan surutan sannan ya miata,tare da cewa


"Ki tabbatar da kin mia mata hannu da hannu kuma ta yafa sannan "


Tsayawa yayi da maganar tare da Wauko wani ullin magani a wata ar jakar fata irin na wanzamai haWi da mia mata,sai ya cigaba da cewa


"Ga wannan ki saka a cikin abincinta,ki tabbatar da taci abincin sannan ki mia mata gyalen,idan ta amsa ta yafa a jikinta,hmmmm lokaci guda zata fara susar jiki tare da iface-iface,sannan duk maganin duniyar da za'ayi mata bazata taSa warkewa ba,don haka ina miki kashedi akan ki kula!!! Ki kula sosai!!! Ki tabbatar da taci abincin sannan ta yafa gyalen!!! "


Amsar gyalen tayi jiki na rawa tana ce masa zata kula sosai,kuWin aikin ya umurta ta bashi babu musu ta irgo kuWin ta mia masa har da Wori a sama wai ya ara(ar yaya hmmmmm muje zuwa,My Esteem fans ince wani ko kuma inyi=7=7=7 )


Haka ta nufo gidanta cike da murnar nasara,shirye-shiryen karin kumallon da zata girka musu ta fara yi tun cikin daren,wanda da safen da ya dace taje da wuri sai akayi rashin sa'a iccan da aka siyo mata duk jiaku ne ba masu ci bane,sai wurin 9:21am na safe takai girkin kuma koda takai su har sun karya suna ma shirin tafiya harda su Baba da Gwaggo Ladi.



*Cikin Labari*



ar yaya da taga alamun idan tayi wasa Umman Sa'eeda tai yafa gyalen to faWin hausawa da suke cewa *aiayi koma kan masheiya* to lallai zai tabbata akanta,nan takai ta fara roonta Allah da annabi ta amsa gyalen ta ita bataso ta yafe tana cewa


"Don Allah kibar kyautan nan wallahi,amshi kayanki ina ni ina saka gyale mai tsada haka"


"A'a wallahi na baki duniya da lahira, Wauka ai kinfi arfin gyale a wurina ar yaya"cewar Umman Sa'eeda


"Na roeki da Sarkin Sammai da assai ki amshi gyalen nan,wallahi ban iya yafashi don yafi arfina" cewar ar yaya har idanunta sun ciko da walla


Sheee kowa a wurin ya bita da kallo har Gwaggo Ladi wacca tasha sabbin kayanta,Gwaggo Ladi ce lamarin ar yaya ya fara bata haushi saboda ta osa su hau mota mai A.C suje birni tana magana cike da Sacin rai tana cewa


"Wai dole ne sai ta saka gyalen ar yaya,ce nike ta ce kiWau gyalen tare da sauran kayan nata kyauta,amma kina maida mana agogon hunnu baya,da yanzu har mun isa birni "


Cikin murya mai cike da damuwa haWi da tashin hankali ta ce


"Nawa ne da zan saka gyalen, ai ba nawa bane,ta amshi gyalenta banaso wallahi"


"To bazata yafa gyalen ba idan ma wani ulla-ulla kikayi a cikin gyalen saidai ki saka,mara imani" cewar Momin Sadam wacca tun jiya take ankare da duk motsin ar yaya ita haka nan taji bata kwanta mata a rai ba kamar sauran.


Ce musu akayi su ake jira nan da nan suka mie,zumbur ar yaya ta mie tana cewa


"Wallahi baki isa ba!!! Sai kin yafa gyalen nan!!! Dole ne ki yafa gyalen!!!"


Da sauri tayo kan Umman Sa'eeda da gyalen, kafin da iso wurinta Sa'eeda ta saka mata afa nan take ar yaya ta faWi asa ji kake timmmm!!! Lokaci guda ta fara susar jiki tana ihu,ai cak!!! Su Umman Sa'eeda suka tsaya hadi da juyowa saboda ihun da sukaji,ihu take sosai tana susar jiki tana cewa


"Wayyo!!! Wayyo!!! Wayyo!!! Ku sosamin jikina!!! Ku kawomin wua ko laujeeee !!! Kai kai kai a sosamin!!! Kai kai kai a sosamin!!! Nace ku sosamin"


Kallonta kowa yake yana mamaki,wasu harda dariya musamman Sa'eeda saboda yadda take susar jikin nata sai kace motsattsa,can kuma ta mie tare da bin bangon Wakin gidan tana susar jikinta kasancewar gidan babu flastan bango,sai faman goga bayanta take a bangon gidan ta ihu haWi da cewa


"A sosamin!!! Ayimin susar jiki!!! Wayyo yaiyayi!!! Na cuci kaina na biyewa ruWin zuciyataaa,akaini gun Malam Tanko Kwandi!!! Kwandiiiii!!!!"


Ai wani irin daka tsalle tayi tana cire rigar jikinta saiga nonuwanta masu kama da slippers sun bayyana suna rangaji,susar jikinta tare babu ki babu gani,su kuma sun kasa cemata komai ko kuma kawo mata Wauki domin yawancinsu mutuwar tsaye sukayi suna kallonta musamman Umman Sa'eeda wacca ta lula kogon tunani a zuciyarta tana cewa 'Lallai Allah da girma yake,kenan cutar susar jiki ar yaya taso sakamin,wato shiyasa ta dage saina yafa gyalen, Wan Adam hmmm Allah kasa mufi arfin zucoyoyinmu' haka tayita zancen zuci,suna a haka suka ji sallamar Baba da Uncle Hassan kasancewar Sa'eeda ta ruga waje ta sanar musu abinda ke faruwa,ai da sauri suka iso gidan,Cak! Uncle Hassan da Baba sukayi ganin ikon Allah,ar yaya susar jikinta take haian babu ji babu gani tana ihu tana kiran sunan Malam Tanko Kwandi yazo ya taimaketa,shiru kowa yayi yana kallon ikon Allah musamman Gwaggo Ladi tana kallon yadda babbar Wiyarta ta koma saboda mugun nufi lallai hassada batayi ba,suna a haka sai can Uncle Hassan ya ce


"Waye Malam Tanko Kwandi din da take cewa a kaita wurinshi"


Baba ne ya ce


"Wani Hatsabibin malamin duba ne a wannan garin,wurinshi taje ila,wai meye ya faru ne kuni mana bayani"


Sa'eeda ce ta fara koro musu bayani tiryan-tiryan harda dramar da akayi akayi akan gyalen sannan ta taWiyetan da tayi saboda nufo Ummanta da tayi da gyalen da susar jikinta da tayi duk babu abinda ta tsame komai ta sanar musu, shiru su Uncle Hassan da Baba sukayi suna kallon ar yaya wacca ta fita daga hayyacinta tana faman susar jiki tana iface-iface tare da kiran Malam Tanko Kwandi ya kawo mata agaji.Duk da muguntar da taso yima ar uwarsa amma haka yace su shigo da ita mota akaita wurin malamin da take faman kira,ai nan Baba yace babu inda zasuje,ita da taso illata Hussaina shi ne zai kaita,murmushi Uncle Hassan sannan ya ce


"Baba komai ahalinka zasu mana bazan damu ba saboda a baya ka taimake mu,sannan ita wacca tayi muguntar ai gashi ya faWa kanta,shi daman sharri Wan aike ne yanzu ba gashi ya dawo mata ba,ta gina ramin mugunta babba gashi yanzu ta fada cikinsa,kawai yanzu mukaita wurin malamin, tafiyar mu sai mubari gobe in shaa Allah"


"Tabbas ka cika Wan halak kaida ar uwarka da Mahaifiyarka,shikenan tunda kace haka a kaita Win,ashe daman ladabin kunama tayi jiya tanada munafa a cikin ranta"


"Ni daman tun tuni ban yarda da ar yaya ba,saboda tun tasowarta bata bada hakuri balle neman yafiya koda ta laifi tayi,nima nayi kokwanto a jiyan wallah ashe tanada manufa ai gashi nan abinda nake miki tsoro gashi ya sameki saboda hassada,nace miki nima nayi babu riba balle ke" cewar Gwaggo Ladi wacca sai yanzu ta tsoma baki a tattaunawar da ake.


Haka su Mairo da yayarta mai suna Na'ima suka taimaka ta shiga motar,su Umman Sa'eeda, Momin Sadam,Sa'eeda tare da Gwaggo Ladi suka shiga mota ta biyu,lokacin shiga motar saida akayi daru da Gwaggo Ladi,su Mairo aka bari gida.kasancewar Baba yasan gidan Malam shi ne a gaba da Uncle Hassan yana mishi kwatance ,a bayan mota ar yaya cw ra bodyguards har biyu,a haka har suka iso gidan Malam Tanko Kwandi,gida ne babban mai kyau saboda Malam Tanko Kwandi shahararran Malamin duba ne,wanda har an siyasa ne,an kasuwa ne,manyan mata ne karuwai ne da dai sauransu suna zuwa wurinsa saboda aikinsa yanayi sosai.


Suna isa lokacin yana zaune tare da manyan almajiransa,sai bodyguards dinsu Momin Sadam suka fito da ar yayaya tanata faman ihu da susar jiki,Malam Tanko Kwandi yana ganinta ya tintsire da wata muguwar dariya harda bubbuga afa,miewa yayi tare da ce masu Uncle Hassan da sauran mutanan bisimillah,su shigo ciki da ita,babu musu kowa ya shigo cikin Wakin da yake duban nasa a ciki,dayake Wakin babba ne shiyasa ya Waukesu baki Waya,bayan kowa ya samu wuri ya zauna tare dayin shiru saidai ihun ar yaya da susar jikin da take yi babu ji babu gani, gyaran murya Malam Tanko Kwandi yayi sannan ya fara magana


"Sannunku da zuwa baina,meke tafe daku"


"Magani mukazo ka mata" cewar Uncle Hassan yana cilla masa harara


Dariya ya tintsire dashi ji kake Kya! Kya! Kya! Babu akautawa,saida yayi dariya ma'isarsa sannan ya ce


"Magani! Magani! Hmmmm! Da alama bata sanar muku da sharadin dana gindaya mata ba"


"Wani sharaWi kenan,sannan ko zaka iya sanar mana abubuwan da ta ce maka"cewar Baba


" Eh zan iya sanarmu sosai ma kuwa, farko da tazo ta sanar min tanaso a kashe wata mata mai suna Hussaina wacca tazo gidan iyayanta"


Dummmmmmmmmm!!!!!!!!!!!!! Haka irjin Umman Sa'eeda ya bada kamar bomb ya tashi a ahon zuciyarta haka taji,lokaci guda ta dafe irji tare da waro manya-manyan idanunta waje tana cewa


"Kasheni!!! ar yaya kikeso ayi,Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,yanzu har iyayyar da kikemin takai ki bada kuWi ayi min asirin mutuwa, ya Rahman"


Kuka Umman Sa'eeda ta fashe dashi mai ratsa zuciyar duk mai sauraronta,kowa a Wakin mamaki da al'ajab ta cikasu,harda Baba da Gwaggo Ladi suma maganar da rikita musu wawalwa,Malam Tanko Kwandi baibi takan kukan Umman Sa'eeda ya cigaba da cewa


"Bayan ta sanarmin ta udurinta akan ita Hussainar, sai na duba mata,faWa mata nayi sihiri bazai taSa iya kasheta ba saboda addu'o'in da take a kullum saidai ta faWi wani abun da take so ayi mata,sanarmin tayi tana so a saka mata susar jiki har ashan rayuwarta,ni kuma nace mata akwai sharaWi akan idan ita Hussainar tai yafa gyalen to ta tabbas susar jikin sai koma mata sannan nata zaifi na wacca takeso a saka mata yawa,kuma na ce mata babu maganin susar jiki a duk inda za'a je,koni kaina banda maganinta balle makarinta"


Shiru Wakin yayi kowa yana nata karanta wasiar jaki,sai can Baba yace


"A dauketa mu tafi,daman *duk wanda ya Wibo da zafi ya kai bakinsa* shi daman sharri Wan aiki ne duk idan yaje sai ya dawowa mai shi,gashi nan ya koma miki,wallahi *Albasa batayo halin ruwa ba* idan kuwa da tayi da baki aikata abinda zaije ya dawo miki ba"


Miewa yayi,suma sauran suka mie,Gwaggo Ladi ta ce


"Na nutsar dake akan illar Hassada da bain ciki amma kini ji,nidai babu ruwana kuma gobe-goben nan zamu tafi birni musha A.C ,ke kika jiyowa kanki"


Wucewa tayi abinta zuwa mota,har a lokacin Umman Sa'eeda na kuka jin wannan mugunta haka,amma Alhamdulillah tunda Allah ya tsareta daga sharrinta,ita kuwa ar yaya haka aka Wauketa tana susar jiki haWi da iface-iface tana kiran Malam Tanko Kwandi ya kawo mata agaji, shi kuws babu abinda yake inba dariya ba,suma almajiran nasa sai dariya suke mata suna nunata,ko nima na Wan dara saboda yadda take susar jikin nata dole ka Wan dara=.


Haka bodyguards suka shiga da ita cikin motar,da farko gidan mijinta Baba ya ce akaita sai mijim yace inaa ba'a gidansa ba taje can ya saketa saki Waya daman ya taSa sakinta saki biyu a baya shikenan ta cike uku reras! Haka suka dawo da ita gidan,gashi su Baba da Gwaggo Ladi sunce tafiya birni babi fashi tunda ita ta siyowa kanta da kanta,yarinyar wacca bata wuce shekara 14 yanzu zata dinga zama da ita kafin su Baba su dawo garin domin yarinyar bazats iya kula da ita ba.



Washe gari da wuri suka karya kumallonsu tare da shirin cikin sauri saboda Uncle Hassan yanada ayyuka a gabansa,haka sukayi ma su Mairo da Na'ima sallama sannan suka fito wanda lokacin arfe 9:12am na safe,suna cikin niyyar shiga mota saiga wani mai machine da mutum a bayansa ya faka a wurin motocin nasu,sauka yayi tare da biyan mai machine kuWinsa,juyawan da zaiyi Karaf! idanunsa ya sarafe dana Umman Sa'eeda,nan take zuciyoyinsu suka bada Daramm!!! Damm!!! Dadammm!!!

Please Login or Register in order to submit comment