Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuje pharmacy ku siya sannan karku manta da pampers Win da nace ku siya domin shi take buata cikin rayuwarta a yanzun"

Amsa su Umma Kande sukayi tare da barin office Win zuwa pharmacy don siya abubuwan da likita ya rubuta,sai Umma Kande ta ce Iklima taje ta siyo pampers Win manya wanda za'a saka ma Nusaiba.

Satinsu biyu a asibitin tukunna aka sallamesu bayan Nusaiba ta samu saui sosai,saidai kuma ramar da tayi da bain da tayi babu inda sukaje,Abban Sa'eeda ma yayita jigilar zuwa asibitin tare da bada abinda ya sawwaa daga aljihunsa.

Haka suka tattaro zuwa gida,kullum cikin siyan pampers suke gashi da shegen tsada saboda ba ko'ina ake samu ba,taimakonsu Waya ne,shagunan da marigayi musa ya siya ne suke samun kuWi daga shagunan if not da abubuwa sun ara rincaSe musu,kullun cikin nasiha Iklima da Maman Jummalo suke ma Umma Kande akan ishara ce Allah ya nuna mata,ba sauraransu take ba hasalima cewa tayi maiyanta ne suka jefeta da aranta wai don sunga suna da rufin asiri,sunyi-sunyi Maman Jummalo akan da dawo hanyar Allah da ma'aikinsa amma inaa,ta riga da tayi nisa batajin kira.




*TUNATARWA*


*alubali ga iyaye mata masu rashin kula da tarbiyyar yaransu tare da son abin duniya,kusani kiwo ne Allah ya baku,dole ne ku kula da cinsu,shansu,lafiyarsu,tufafinsu,wurin kwanansu sai uwa-uba Tarbiyyarsu da daWi ace ai wacce yarinyarta ar kirki ce ga tarbiyya da kamewa,haka kuma babu daWi ace ai wacce yarinyarta ar isaka ce,bata da kunya,ga shegen bin maza kamar akuya,idan kika kula da tarbiyyar arki wallahi rige-rige mazan warai suyi wurin neman auranta domin kuwa kowani namiji yana buatar mahaWin rayuwarsa da gari wacca itama zata tarbiyyantar da yaransa,kinga kuwa idan baki ba arki tarbiyya mai kyau ba taya mutumin ware zai nemi auranta???*


*an uwana iyaye mata a kula da tarbiyyar yara,kunga dai yadda Umma Kande ta are da yaranta duk don rashin tarbiyyar da suka samu ne a hunnunta suka faWa halaka musamman Nusaiba, Allah ya tsaremu ya tsare aanmu da zuri'armu baki Waya*

Haka su Umma Kande sukayi ta jigilan siyan pampers Win Nusaiba har Allah yasa ta samu lafiya jikinta ya murmuro duk da ba barin siyan pampers Win zasuyi ba tunda ta dinga amfani dashi ne har arshan rayuwarta.Wannan kenan



@@@@@@@@@@@@@@


*ABUJA*


Karnuka ne bila adadin suka biyo Haj. Zulfa'u a ta Sangaren hagu,ga wasu mutane su biyu mace da namiji hannun a tsarafe dana juna suna binta,gudu take a cikin duhun daji tama rasa ina zata bi saboda hagu da dama bibiyarta ake,cigaba da gudun tayi saboda karnukan sun kusa taddota,sai can tayi tuntuSe da dutse lokaci guda ta faWi asa,haba karnukan nan kanta suka yo tare da cizonta ta a ko'ina suna haushi,ita kuma babu abinda take inda ihu da neman agaji ba,tana wannan ihun ne saiga wa'innan macan da namiji suma sunzo gunta suna nunata suna dariya,mai cikin nan ne da yara maza guda biyu tana rie dasu ta bayyana agabamta kamar walkiya,dariya ta tintsire dashi,suma an biyu maza dariya suke tayi,sai kuma da tsagaita dariya tare da fara magana cikin muryarta mai firgitarwa

"Zulfa'u arshanki ya kusa!!! Bazaki taSa guje mana ba!!! Dole yarana su Wau fansa!!! Kinga yadda arshanki zai kasance tare da karnuka !!! "

Haj.Zulfa'u da duk tayi jina-jina saboda cizon da karnukan suke mata babu akauwa kota ina a ilahirin jikinta,cikin muryarta wacca bata fitowa ta fara magana

"Karku zo!!! Kubarni da rayuwata!!! Kubarni "

Haka tayita maimaitawa su kuma mutanan sai dariya suke mata,can kuma suka Sace Dif! kamar waliya.

A gigice ta farka tana cewa

"Boka BurumbuWu ka taimakeni!!! Zasu dawo!!! Zasu kasheni!!! Wayyo!!! Wayyo ni Zulfa'u!!! "

Mai aikinta ce ta shigo Wakin da gudu kasancewar da yamma ne bayan Asr,tayi baccin tare da yin wannan mummun nan mafarkin mai tsoratarwa tare da firgitarwa,cikin tashin hankali mai aikin ta ce

"Hajiya lafiya? Ko a kira miki likita ne ko kuma Haj. Amina tazo"

"A'a karki kira kowa!!! Tafi!! Tafi!! Kawai!!"

Mai aikin zata sake magana Haj. Zulfa'u ta daka mata tsawa da cewa

"Ki tafi nacee!!! Bana buatar kowa yanzu!!! "

Jiki na rawa haka mai aikin tabar Wakin saboda tsawan da Haj. Zulfa'u tayi mata,abinda tunda take da ita bata taSa mata kenan tsawa,zancen zuci ta fara 'Anya Hajiya alau take kuwa kwanan nan,kullum cikin firgici take da tsoro,ko abincin kirki ta daina ci,fita ma yanzu ta daina,gashi ta hana bai zuwa gidan,ko miye dalili oho! ' haka tayi ta zancen zucinta har ta sauka daga matattakan benan zuwa kitchen daman girkin dare take sai taji ihun uwar Wakinta shiyasa tazo da gudu don jin ko lafiya.

Haj.Zulfa'u duk hankalinta ya tashi matua ainun,gashi bokanta ba yanzu zai bayyana gareta ba sai nan da wani Wan lokaci,tunani take wai shin meke shirin faruwa da ita ne a kwanan nan,mai yasa take yawan mugayan mafarkai da miiyiyarya ne,wayyo boka kayi sauri kazo ina neman agajinka da gaggawa,haka tayita tunaninta har akayi sallar magrib daman ita ba sallar take ba,ta riga ta sallamawa boka BurumbuWu komai nata.(Ya Salam>>>, Allah ka tsare mana imaninmu)

Tun daga ranar kuma sai bata sake mugayan mafarkai ba,ita a tunaninta bokanta yaji da wannan Samgaren wato tsareta da ahalinta na daga abin cutarwa da ya mata alawari a baya saboda sharudWan da take bi nasu.Wannan Kenan


@@@@@@@@@@@@@


*KEBBI*

Cin nasara su Sa'eeda suka kammala exams tare da tahowa wansu da warwatarsu zuwa Birnin Kebbi don halartar warya-waryar walimar da za'a gudanar a family house Winsu wanda har an uwa na nesa sun fara zuwa,tun daga wasu maota jahohin har an asar waje,irin su Sadiya second born Win Momin Sadam dama wasu an uwansu da suke da matansu a asar waje duk sun hallara a family house wato asalin gidan *Alhaji Kabir Dikko* .

Su Umman Sa'eeda da Momin Sadam sun dawo daga Umra tun a satin daya gabata,Umman Sa'eeda tayi ar iba,ga fatarta ta murje tayi haske sosai kasancewar daman wahala ce ta saka yin duhu,sanda suka dawo direct daga airport aka wuce da ita zuwa family house,murna iya murna domin Umman Sa'eeda taga an uwanta,kowa sai murnar bayyanarta suke,musammam tsoho mai ran arfe wato Baba Garba,ji yake kamar anwarshi Maimuna ce ta dawo garesa,har da kuka yayi saboda farin ciki,masauki mai kyau part guda aka ware ma Umman Sa'eeda daman ita Momin Sadam daga airport ta wuce gida kasancewar Daddyn Sadam shima gobe zai dawo daga tafiyar da yayi.

Family house Win babba ne in fact layi guda ne,kuma duk cike yake da an uwa,ginin zamani ne,akwai masallaci da makarantar islamiya a ciki,ga tangameman gate mai shegen kyau,part-part ne gidan kuma painting su iri Waya ne babu bambamci,ga inter-lock a ko'ina na gidan,harda wurin wasan yara,da kuma babban hall wanda a ciki ne ake duk family meeting tare da shagulgulan sallah,hall Win babba ne gashi yasha decoration gwanin ban sha'awa.Haka Family house Win ya cika mai da an uwa na kusa dana nesa,yaransu da manya,order abinci aka ba wani hotel don yin walimar.

Tun safe kowa ya fara shiri,Sa'eeda na a part Win da aka ware ma Ummanta,acan ta shirya cikin tsadaddun lace wanda Momin Sadam ne tasa a Winki mata tare da Ummanta,sunsha kyau sosai,sai walwali suke,ga wani haWadWan takalmi half cover da jakarsa ta saka ita da Ummanta iri Waya saidai colour Win ne ya bambamta,wooow kawai zan iya furtawa saboda kyauwun da sukayi,haka suka fito ita Ummanta zuwa Wakin taron kowa ya hallara har da goganku Sadam shida amininsa Kamal,a saman hall Win akwai kujera two seater acan aka umurce su da su zauna,babu musu suka je wurin suka zauna.

"Wooooow!!! What a precious angel from paradise!!! " cewa Kamal

Sadam da hankalinsa ke akan waya ya Wago don ganin abin abokinsa yake dabo haka,dummmmm!!! Haka zuciyarsa ta bada,ganin Sa'eeda cikin wannan shiga ta alfarma,a gaskiya duk tafiye-tafiyan da yake tare da hulWa da mutane maza da mata bai taSa ganin mace mai kyau irin Sa'eeda ba,gashi kayan da ta saka ya mata mugun kyau sai kace amarya duk da ba wata kwalliya tayi ba,tunina ya lula yana ayyana abubuwa da yawa na game da ita,shifa tunda yabar Kaduna yake tunanin Sa'eeda tare da girkinta,muryarta yake ara tariyowa a sanda tace mishi shi mutum ne ko aljan,harda shirman da tayita yi lokacin da ta shigo Wakin ba tare da tasan akwai mutum ba,katse mishi tunani Kamal yayi da cewa

"A gaskiya yarinya Allah ya mata baiwar kyau da sura"

Ai tuni wani malolon abu ya tasoma Sadam tare da tsaya mishi a wuya,wani irin haushi Kamal ya bashi,tsaki yayi tare da cewa

"Kaifa daWina da kai shegen son mata,wannan yarinyar kake yabo haka,mtws! "

"Yarinya fa kace,tabb da sauranka wallahi,yoy never know what is called hot babe Man!"

"Kaga malam ba abinda ya kawoni nan bane,kacika surutun jaraba,haba kabari idan kaje gidan radio sai kayi mana! "

Dariya Kamal yayi wato shidai mai hali baya barin halinsa kenan,Sadam da miskilanci.Uncle hassan ne ya buWe taron da adduar dayake jiya shima ya iso asar,addu'a sosai akayi sai daga baya kowa ya fara gabatar da kansa gasu Umman Sa'eeda, bayan kowa ya gabatar da kansa sai aka miama tsoho mai ran arfe wato Baba Garba micro phone don ya bada tarihi,cikin muryarsa wacca bata fita sosai saboda tsufan da ya fara bama su Umman Sa'eeda tarihi kasancewar bata taso a cikin suba,ya fara da cewa



*TARIHI* ( *tare da wasu Sangare na abubuwan da suka faru shekaru aru-aru* )


Sunan mahaifinmu Alhaji Kabir Dikko matarsa Waya wato mahaifiyarmu mai Suna Hajiya Suwaiba,mahaifinmu asalin dan Zamfara ne a aramar Hukumar Gora dake a jahar Zamfara,kasuwanci ne ya kawo mahaifinmu Kebbi State har Allah ya Waukakashi tare sama kasuwancinsa albarkha,annan mahaifinmu biyar ne duk maza wanda suma sun dawo Kebbi wurin mahaifinmu da zama kasancewar shi ne babba a Wakinsu kuma iyayansu sun daWe da rasuwa,haka har Allah ya bama mahaifinmu ikon siyan layin nan complete saboda a zamaninsu yana Waya daga cikin sharararrun an kasuwa masu kuWin gaske.

Mu uku ne wurin Mahaifinmu babbar yayarmu sunanta Mariya ta haifi yara uku amma Ruayya,Salima sai Mubarsk amma biyu sun rasu saura Rukayya(Momin Sadam),sai kuma ni mai suna Abubakar,ina da yara hudu,Kabir mai sunan Mahaifinmu, Suwaiba mai sunan Mahaifiyarmu,Maryam sai Nabila (Dr.Nabila),sai Mahaifiyarki mai suna Maimuna,ita ce autarmu ta haifi an biyu maza amma suna da shekara uku a duniya dukkaninsu lokaci guda suka rasu,sai ku kuma,iyayenmu sun bamu ilimin boko dana zamani,shiyasa a duk ahalinmu babu wanda baiyi karatu ba.


Hussaina haia addara ta faWama mahaifiyarku a lokacin tana tsohon ciki,kasancewar abokina ne ta aura wato *Alhaji Sani Mai Gado* shahararran Wan kasuwa ne kuma Wan boko,matarsa Waya Zulfa'u,ya auri Maimunatu ne saboda bayajin daWin zama da matarsa saboda munanan halayanta,sai kuma Allah yayi nufinsa da auran Maimuna wacca ta haifa mishi yara har huWu amma biyu sun rasu (Twins)sai tsohon cikin dake jikinta.


Ban mantawa ana gab da Satan Maimuna abokina Alhaji Sani ya kirani akan yanaso ya kai addarorinsa kotu sai bayan yaransa sun girma idan ya mutu sai a raba musu gado,dalili na tambayeshi akan hakan,bai Soyemin abinda ya gani da idonsa ba da daddare ya tashi sallar dare yaga matarsa Zulfa'u tana surkulle tana faWin sunan Maimuna da yaranta harda shi kansa,dalilin hakan ne da safe ya kirani,ni kuma babu Sata lokaci nazo har Abuja inda suke mukaje kotu akai cike komai tare da addamar da adaddorinsa har ma na asar waje, bayan dawowana Kebbi ne Alhaji ya kwanta ciwo sai kuma a lokacin muka nemi Maimuna da yaranta muka rasa,babu inda ba'ayi cigiya ba amma shiru,sai kuma bayan wata Waya naje Kaduna wurin wani abokani na kaSe Hassan da motana a rashin sani wanda shi ne asalin ganin Hassan da mukayi,a kullum ina zargin Zulfa'u da Satan Maimuna saboda abinda Alhaji Sani ya faWamin game da ita,ban Wau mataki a wannan lokacin ba saboda Satan Maimuna amma yanzu komai zaizo arshe da izinin Allah,sai munga arshan Zulfa'u in sha Allah.



*Cikin Labari*


Haka Baba Garba kammala bada tarihi babu wanda a cikin Wakin taron bai zubda walla ba tuno da abinda ya faru a baya,Umman Sa'eeda kuka take harda shasshea ashe kishiya ce sanadin tarwatse ahalinsu,kishiya ce ta hallaka Mamanta da an uwanta,kishiya ce ta saka musu unci da damuwa a zukatansu wayyo duniya ina zaki damu,itama Sa'eeda saida tayi hawaye jin tarihin asalinta da kuma abinda ya faru shekaru da dama,amma kuwa anyi azzalumar mata,sheWaniya,in sha Allahu arshanta yazo,miama Umman Sa'eeda microphone Win akayi,itama ta bada tarihin rayuwarsu tun daga rayuwarsu a auyen Damari har auran da tayi, irin alukalen tare da wahahalun da tasha duk saida ta bada labarinsu,babu sauyin da kake ji a Wakin taron saidai sautin kuka da fa ce majina,saboda akwai tausayi a labarin rayuwar Umman Sa'eeda,Uncle Hassan yayi kuka iya kuka jin yadda ar uwarsa ta rayu cikin wahala,dole ne ya faranta mata,lokacin jin daWin ta yazo ita da arta,walimar cin abinci aka fara,ma'aikatan hotel Win suke bin kowani table da abinci kala-kala tare da abubuwan sha iri-iri suma.


Fitsari ne ya matse Sa'eeda kasa hauri tayi ta mie don ta zaga,har taje tayi fitsarin wurin dawowa bata sani ba tana kalle-kalle kanta ya bige a irjin mutum,ji kaki us! Ai ba shiri ta Wago kanta don kallon wanda ta bige,Ras! irjinta ya bada ganin wanda ta bige,shima kallonta yake babu ko yaftawa,suna a haka sai can ta taSe baki tare da fuskar kuka tana cewa


"Kawai kawai ka bige mutum amma ka kasa bashi hauri"


Mamaki maganarta ta bashi,au shima ya bigeta ce yake wurin kalle-kalle yana waya bata sani ba bige shima zai bata hauri,tabb! Ai kuwa tana ruwa,uffan bai ce mata ba sai ma kira daya shigo wayarsa zai Wauka ya ce ta ce

"Mugu kawai,mai tsorata mutum"


"Nine mugu? "


Kusa da ita ya araso yana tambaya tare da kashe kira,ai ba shiri Sa'eeda tace *afa mai naci ban baki ba* ita a tunaninta dukan ta zaiyi,saida tayi nisa da wurin da yake ta juya ta ce


"Eh Win,Eh din,Nace mugu,mugu mugu Sadam"


MurguWa masa baki tayi tare da arasawa cikin Wakin taron da gudu,tsayawa yayi yana kallon gun da tabi,komai nata birgeshi yake,wanka ma kansa mari yayi tare da cewa


"Wake up Man,what's wrong with you"


Haka aka kammala walimar kowa ya wuce gidansa,na nesa kuma suka wuce Wakin bai,Su Umman Sa'eeda da Dr Nabila gidan Momin Sadam suka nufa saboda tace tanaso Umman Sa'eeda ta kwana biyu wurinta,haka suka Wunguma zuwa gidansu Momin Sadam har da su Aunty Sadiya da Aunty Sakina wato yayyin Sadam.


Sun isa gidan wurin 5:45pm na yamma,wani sabon girkin aka Wora na dare saboda karuwan family da aka samu,sai bayan Isha'i aka zauna cikin abinci harda Kamal kasancewar ya zama Wan gida,sai faman satan kallon Sa'eeda yake yana cin abinci,Sadam dai yana ankare da abinda Kamal yake,shi ya rasa mai yasa ya damu da Sa'eeda haka da baya ko so wani Wa namiji ya kalle ta,haka dai suka kammala cin abin,dai suka dugunzuma zuwa falo tare da fara hirar yaushe gamo,harda Daddyn Sadam yana wurin ana hirar dashi,sai can Kamal ya kasa hakuri ya ce


"Ammm Dad nifa nayi kamu a gidan nan,Ina son Sa'eeda da aure,Dad a taimaka a bani ita"


Darammm!!! Dammm!!! Dammmm!!! Haka irjin Sadam ya bada, baisan sanda ya Waga muryarsa cikin fushi kowa yana jinsa yace


"Ayi mata miji!!!................... "





*Mu haWu a pages na gama my Esteem fans=C=C=C=C
'
'
'<9<9<<<<=ؖ=ؖ*



*To waye ne mijin da Sadam yace anyiwa Sa'eeda??? Mai yasa yake jin abu a game da Sa'eeda???*......




*To ta yaya su Baba Garba, Uncle Hassan da Umman Sa'eeda zasu fuskanci Haj. Zulfa'u jin ashe ita ce tayi sanadin Satan kakar Sa'eeda???*......



*Wani mataki Haj.Zulfa'u zata Wauka ,shin zata bari su haWu kuwa???*....


*Nusaiba dai an koma baby ana yawo da pampers,shin Umma Kande zata saduda ko kuwa har yanzu tana akan bakanta????*.....



*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions<9<9=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku new updates zafafa* <9<9=C=C=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ==%=%=%=%=%




*Ina aunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* <<<<=ؖ=ؖ<9<9=C=C=ؘ=ؘ



Daga alalamin
=؍=Narrnarhh Bukar ==؍


Comments and share =O=O=OFisabilillah.


[5/15, 7:59 PM] Narnarhh Bukar:

< *NACINA YA JAWO MIN* <





*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen*
')




*TASKIRA WRITER'S FORUM*
*T.W.F*



*WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends




*AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?id=6615ba31404e6e2687888ab9




*TELEGRAM*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk




*WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y




*BOOK 2*



4 9 ----5 0



"Ammm Dad nifa nayi kamu a gidan nan,Ina son Sa'eeda da aure,Dad a taimaka a bani ita"

Darammm!!! Dammm!!! Dammmm!!! Haka irjin Sadam ya bada, baisan sanda ya Waga muryarsa cikin fushi kowa yana jinsa yace

"Anyi mata miji!!! Sai kaWau na annabawa kuma!!! "

Babu wanda a cikin Wakin bai kalli Sadam ba,harta ita kanta Sa'eedar kallonsa take irjinta na bada Ras! Ras! Ras! A zuciyarta tana cewa 'Miji? Miji? A ina? Yaushe? Waye? ' tambayoyi ne take ma kanta bila adadin domin maganar tazo bata a bazata,Momin Sadam ce taji maganar tayi bambarawai,wai 'Anyi mata miji' kasa hauri tayi tare da cewa

"Sadam yaushe akama Sa'eeda miji wanda mu iyayenta bamu sani ba sai kai? "

Wuri-wuri yayi da idanunsa,shi sai yanzu ya tuno da katoSar da yayi,Wayyo! Shikenan an ganosa,asirinsa ya tonu,yama rasa wasu kalmomi zaiyi amfani dasu wurin kare kansa karsu gane sirrin zuciyarsa.Shiru yayi babu amsa cak ya mie kamar wanda wai ya fashe masa a ciki ya haura sama ba tare da ya kalli kowa a cikin falon,murmushin mugunta Kamal yayi,domin haarshi ta cimma ruwa,shi daman bawai yana sonta bane a'a kawai dai tun da yaga kallon da Sadam yake ma Sa'eeda zuciyarsa ta tabbatar da tabbas Sadam ya fada kogon soyayyar Sa'eeda sai dai shi kansa baisan da hakan ba,sannan ka mugun kishinta da yake numawa ra'ayul aini,daman ya faWi hakan a gaban kowa don ya auna kishin Sadam akan Sa'eeda tunda miskilancinsa ya hanashi bayyana mata aunar da yake mata,gashi tun kan Dad yace wani abu har mugun kishinsa akan Sa'eeda ya bayyanashi mararan a filin Allah Ta'ala,miewa Kamal Win yayi yabi bayansa,Dr.Nabila ce ta fara magana tana murmushi

" Ai ni daman tun sanda Sadam yazo gidana naga yadda yake santin girkin Sa'eeda nasan akwsi wata asa,bai dai nuna bane saboda shegen miskilancinsa"

"Yoo gashi yanzu ya nuna mararan kowa ya gani daga jin Kamal ya ce yana son a bashi ita Shikenan tun kan Dad ya ce wani abu har ya yanke hukunci, Autan Momy sai Allah da malam gari" cewar Aunty Sakina tana dariya

Suma an Wakin dariya sukayi ganin kishin Sadam a bainan nasi,har Dad ma saida ya dara,Sa'eeda ce kaWai abun bai bata dariya ba yooo wannan abun dariya ne,Mominsa Sadam ce cikin farin ciki marar misaltuwa ta ce

"Ai Shikenan sai ayi tuwona maina,dakan Waka shian Waka,wanga batu yamin daWi a rai"

Sum sum sum Sa'eeda ta mike tare da nufar kitchen duk da babu abinda zata Wauko,kunya ce duk da lulluSeta,ara tun tsirewa da dariya su Dr. Nabila sukayi wai ita ga mai kunya,Umman Sa'eeda taji daWin wannan al'amari duk da bai furta yana sonta ba amma kishinsa ya bayyanasa ba tare dashi kanta ya sani ba.

Direct Sadam ya wuce bedroom Winsa tare da faWawa kan gado,bai daWe da kwanciya ba yaji sallamar Kamal,tsaki yayi shifa haushi Kamal yake ji ya rasa dalili,jin ba'a amsa sallamar ba Kamal ya shigo Wakin har bedroom Winsa,da sallama ya shiga tare da cewa

"Assalam salam ango Sa'eedatu Baiwar Allah"

Tsaki yaja mai tsawo ba tare da ya Wago daga kwanciyar ba ya ce

"Kai kasani kuma,nidai na fada maka tun wuri ka janye makaman yakinka domin mijinta ba kanwar lasa bane,kaje ka nemi wata "

Wata bazawarar dariya Kamal ya tintsire da ita,yi yake babu akautawa harda bubbuga afa,haushi dariyar Kamal tabama Sadam wato ya maidashi mahaukaci kenan kome,a harzie ya tashi daga kwanciyar yana cewa

"Ok nagane,wato ka maidani mahaukaci shiyasa duk maganar da zanyi zata zamo abin dariya a wurinka ko,fine"

Tsagaita dariya Kamal yayi ganin abokin nasa na niyyar yin zuciya kuma yasan halinsa da bakar zuciya ba ara bi takansa zaiyi ba,bayani ya fara masa da cewa

"Man! Calm down and understand me,wallahi ba son Sa'eeda nake ba,daman plan ne nayi don na auna kishinka tare da soyayyar da kake ma Sa'eeda wanda ka kasa bayyana mata,shiyasa nace bara na gwada tambayar auranta naji ya zaka ce,sai kuwa abinda nake harsashe akai ya tabbata domin tun kan Dad ya ce wani abu har ka bada amsa a gaban kowa ba tare da kaji shakku akai ba,yanzu in nine kai ajiye miskilancina zanyi a gefe tare da mika wuyana ga Sa'eeda"

Shiru Sadam yayi yana kallonsa wato daman plan ne yayi duk don yasa asirinsa ya bayyana, 'Oh God mai ya shiga wawalwana ne Wazu da na gaza tuno da halin Kamal wurin iya shirya plans',murmushin gefan baki Sadam yayi tare da cewa

"Hmmm wato shiryamin tarko kayi Kamal, ya maka kyau tunda kasa na fallasa sirrin zuciyata a bainar nasi"

"A'a fa bainar iyayenka ne,kuma hakan yamin daWi a rai,look Sadam don Allah ka cire wannan shegen miskilancinks tare da jiyeshi a gefe don Allah ,show her your love,show her your care,show her she is the only woman in this whole planet you love and care for,mata suna son mai nuna musu so,auna tare da kulawa,kaga ni yanzu maganar da ake har iyayen sun shiga ciki,maganar aure ake yanzu, kaima idan ada baka da wacca zuciyarka take so to yanzu ai akwai,kawai ka bada kai malam bori ya hau"

"Kamal bansan yadda zan fuskanci yarinyar bane wallahi, she's so confident and bold,tana da kwarjini sosai,kullum tunanin yadda zan fuskance nake amma na gaza samun wannan arfin gwiwar"

"Karka damu da wannan yanzu tunda kowa yasan da irin son da kake mata shikenan,kai kuma sai ka dinga nuna mata soyayyar ka a fili,don nasan itama daga gani tana sonka,nifa nagane ku tun dazu a wurin taro,kowa na begen Wan uwansa amma kun kasa bayyana ma junanku abinda yake a cikin zuciyarku"

"In shaa Allah zanyi yadda kace,nagode sosai da shawarka dan uwa,plans Winka ya tafi a yadda ya dace"

Shaking hands sukayi suna dariya,Kamal bashi yabar gidansu Sadam sai wurin 9:15pm na dare tare da yima an falon sallama kasancewa suna nan suna hira har ya sauko.Tun daga wannan rana Sa'eeda ta fara wasan Suya da Sadam,batason su haWu ko wurin cin abinci ne,idan taji tsayuwar motocinsa sai ta mie tayi sama,Ummanta dai na sane da takunta,a zuciyarta tana cewa 'Zama ki bari yarinya duk randa aka kaiki Wakinsa'

Wata irin shauwa mai arfi ce ta shiga tsakanin Momin Sadam da Sa'eeda domin tun a ranar da ta fara ganin Sa'eeda tama Sadam sha'awar auranta saboda natsuwa da tarbiyyarta,sai gashi shi da kansa ya bayyana kansa.

Sati Uku aka basu Sa'eeda a school,yanzu sunci sati Waya a gidansu Momin Sadam, Umman Sa'eeda da Momin Sadam zasu z wuce can family house saboda yau za'ayi maganar tafiyarsu Abuja wurin Haj. Zulfa'u don tunkararta kawai ayi a wuce wurin tare da magana gadonsu na kotu.Suna zaune a dining area suna karyawa duka family harda Sadam wanda hankalinsa kusan akan Sa'eeda yake, kowa a wurin yana sane da abinda yake harda Dad,ita kuma Sa'eedar duk taji ta takura saboda irin kallon da yake mata daman ya daWe bai gamta ba saboda duk hanyar da zai samu don ya kanta ta yanke ta ko break fast ma batayi a dining room,yau ne Mom ta ritsata akan tare da kowa zata karya babu yadda ta iya,shiyasa yace bara ya kalleta son ransa tunda ta daile hanyoyin da zai dinga ganinta.Baida niyyar bayyana mata soyayyarsa a Kebbi,yafiso sai sun dawo Kaduna sai yaje can yayi sati Waya,tun da kamar a nan tana jinta a takure take ba kamar Kaduna ba,haka kowa ya kammala break fast Winsa tare da barin dining area Win,su Momin Sadam da Umman Sa'eeda suka fara wucewa can family house Win saboda uncle Hassan da wani abokin Baba Garba na Kusfa-Zaria sukazo tare duk saboda maganar tafiyarsu Abuja ne,malami ne na addini wanda Allah ya bashi baiwar sanin makarin sihiri kowani iri,duk da ya tsufa amma kuma saninsa na nan bai gushe ba.

Su Dr. Nabila da yayyin Sadam sai anjima zasu je can family house Win, daman haka Sadam yakeso wato Mominsa da Umman Sa'eeda subar gidan don yaga alama su Sa'eeda take jin kunya,Uwar surutu ya kira wato Kauthar,ce mata yayi taje tace Dad na kiran Sa'eeda a garden zata amshi sao ,babu musu ta ruga aguje zuwa kitchen inda Sa'eeda take da mai aikinsu tana tayata aiki,tana haki tace

"Aunty Daddyn Sadam yace kisameshi a gardan zai baki sao ki kawo ciki"

"To Cwedy gani nan zuwa"

Tsam! ta cire hannunta a aikin da take yi tare da nufo garden Win,zuciyarta na dukam uku-uku tana tunanin wani irin sao ne haka da har sai tazo

Please Login or Register in order to submit comment