Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallo suke bin ko'ina na gidan,tabbas! Naira tayi kuka wurin gina wannan katafaren gidan mai kyau da tsari kamar a asar waje,har masaukin bai ya kaisu,kasancewar Sa'eeda taje da buWe ofar shiyasa da suka buWe sai ofar ta buWe,lokacin Sadam da Sa'eeda suna zaune a two seater suna manne da juna(wanga toyayya haka),runtse idonsa Sauban yayi da arfi ganinsu a haka amma su ko a jikinsu,haka Maryam ma saida gabanta ya faWi ganin Sadam,domin kuwa ya mata bala'in kwarjini da kyau,har zuciyarta ta fara harsaso mata wani abu a game dashi.(kingani-kingani kwalelanki Haj. Mairoro===)

Zama sukayi bisa three seater,a gabansu kuma tray din kayan marmari ne da ruwa,da fara'arta Sa'eeda ta ce


"Sannunku da zuwa manyan baina,fatan kunzo lafiya"

Cikin sanyin murya suka amsa mata da cewa


"Yawwa"

Sannan suka gaishesu,Sa'eeda ce ta ce

"Bismillah ga ruwa da dan kayan marmari wallahi bansan da zuwanku ba da na shirya muku girki,I'm sorry for that"

"Haba wannan ma ya isa,muna godiya sosai" cewar Maryam

Dain shiru yayi na Wan wani lokaci kowa na karanta wasikar zaki a zuciyarsa, sai can Sauban yayi gyaran murya tare da fara magana


"Munzo neman yafiya a wurinki Sa'eeda,kanmu a asa muna neman gafarki akan abubuwan da muka miki a baya,don Allah tare da son da kikewa fiyayyan halitta wato annabinmu kuma manzonmu Muhammad (S.A.W) ki taimaka ki yafe mana,tabbas! Allah yayi ikonsa akanmu tun kan aje ko'ina,munga isharori kala-kala kuma mabanbanta duk akan cin amanar da muka miki"

Shiru Wakin ya sake yi,can Maryam ta Wora daga inda Sauban ya tsaya

"Don girman Allah Sa'eeda ki yafe mana ko zamu samu sassauci a cikin zuciyoyinmu,wallahi munyi nadamar abubuwan da muka miki a baya"

Idanun Sa'eeda na kallon asa,hawaye na gangarowa bisa kunchinta tuno da abubuwan da suka faru baya tayi,sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tayi sannan ta ce


"Na yafe muku Allah ya yafe mana baki Waya"

"Alhamdulillah mun gode sosai Sa'eeda Allah ya kara muku so da aunar juna tare da dawwarma da farin ciki a rayuwarku, ya kara daukakaku,mun gode sosai" cewar Sauban

"Mun gode sosai Sa'eeda" cewar Maryam

Murmushi Sa'eeda tayi sannan ta ce


"Babu damuwa,ana tare"

Sadam ne yayi gyara murya wanda tun sanda suka fara magana bai ce ko *kanzil* ba sai yanzu yake da niyyar saka baki


"To Alhamdulillah tunda an yafe ma juna,Allah ya yafe mana baki Waya,tunda yanzu kamfanin da kake aiki a matsayin manager na mallaka ma My darling Star Sa'eeda so wani tunani ne yazomin yanzu,babu dadi ace kana aiki a arashin Ex girl friend dinka,it sounds somehow koni bazan iya aiki a arashin budurwata ba misali balle Ex girlfriend Wina,idan kana so zan iya baka wani aikin a sabon Kamfanin da zanyi lauching Winsa next month a nan garin Kaduna,amma fa idan kana da ra'ayi,kaje kayi shawara idan ka amince zaka iya sanar ma P.A Wina saimu mu baka muaminka na Manager a kamfanin"


"Sosai ma kuwa ai yallabai babu wata shawarar da zanyi hakan yayi Wari bisa Wari,ina godiya sosai Allah ya ara Waukaka tare da nisan kwana"

"No karka damu"


Haka suka cigaba da hirarsu sannan sukayi sallama,Maryam ta amsa numban Sa'eeda saboda su dinga gaisawa.Har gate Sadam da Sa'eeda suka rakasu tare da musu abin arzii,suna godiya haka suka taga motarsu.Dawowa Sadam da Sa'eeda sukayi cikin falon tare da cigaba da wasansu.


*TUNATARWA*

*Hattara gareku an uwana maza da mata masu cin amana tare da yuudarar masoyanku,hmmm kunga dai yadda Sauban da Maryam suka kasance saboda yaudara hadi da cin amanar Sa'eeda da sukayi.Shin wai in tambayeku meye ribar yaudara hadi da cin amanar masoyin da ya yarda dakai Wari bisa Wari,mai yasa wasu a cikin mu suke jin daWi idan suka da wasu sun shiga cikin halin damuwa saboda su,ko sun manta ne Ubangiji baya yafe hakin wani akan na wani ne,ko sun manta adduar wanda aka zalunci bata faduwa asa banza,ko sun manta Allah yana sakayya akan wanda aka zalunta tata-izan da gaggawa,wannan hawayen da yake zubarwa ko kuma take zubarwa saboda ku wallahi! Wallahi! Wallahi! Bazasu zubu a banza ba Ubangiji zaiyi ikonsa akan duk wanda ya zaluncesu ko ba daWe ko ba jima.an uwana maza da mata mu guji karye zukatan masoyan da suka yarda damu.Allah kasa mu dace*


@@@@@@@@@@@@



A Sangarensu Umma Kande lamari yai daWi domin yanzu gabanta tsutsa yake fitarwa haWi da ruwa mai yaui ga Woyin gaske,ko tafiyan kirki bata iyawa,sai an kwantar sai an tayar,har yanzu bakinta bai mutu ba,tana nan tana zuba kamar ruwan famfo,su Maman Jummalo suna oari akanta sosai.

Alhamdulillah an dace a aikin da akama Nusaiba a Abuja wanda Umman Sa'eeda tayi jagoranci komai,tun daga biyan kuWin aikin,magunguna da dai sauransu,babu laifi aiki yayi kyau sosai don yanzu ta daina yoyon kashi,har sun dawo gida ta cigaba da shan magungun nan da aka Worata a kai,har jikinta ya fara cikowa.

Su Iklima Allah ya kawo musu mazaje masu wadata ita da Jummalo,yanzu ma haka har an saka ranar auransu nan da wata huWu masu zuwa,Uncle Hassan ya bama Abban Sa'eeda jari mai tsoka sosai wanda zai dinga kasuwanci dasu,sirikinsa Sadam ya siya shakuna uku ya haWe mishi su tare da ara mishi wani jarin ya ara,kuka ne kaWai Abban Sa'eeda baiyi ba saboda farin cikin da yake ciki,yayi godiya yafi arfin cikin kwanda ga wa'innan bayin Allah,kasuwancin saida atamfofi,shaddoji,laisussuka,da dai sauransu ya fara,babu laifi kasuwancin nasa na tafiyi a yadda ya kamata,ofofin alkhairai sai ara buWe masa suke ta ko'ina,har an uwansa na auye yakan tura musu kuWi wanda zasu tallafi rayuwasu dana aansu.


Umman Sa'eeda ne tayi wani tunani haWi da neman yardar mijinta akai,bayan sun kammala break fast suna zaune a falo suna kallon TV sai Umman Sa'eeda tayi gyaran murya tare da cewa

"Abban Sa'eeda ina so muyi wata magana mai muhimmancin gaske yanzu"


Waiwayowa yayi tare da cewa


"To,ina jinki sahibata"

an murmushi tayi sannan ta ce


"Wata shawara ce nazo da ita kuma ina fatan zata karSu a wurinka,ganin Umma Kande a irin wannan hali,gashi su Iklima sun kusa aure,ita ma Nusaiba muna mata fata samun miji a nan kusa tayi auran ita ma,shi ne nace mai zai hana ka auri Maman Jummalo domin idan yaran sukayi aure gidan watsewa zaiyi,ya zama babu kowa don kasan Maman Jummalo da wuya ta cigaba da zama gidan,kaga idan ka aureta zata cigaba da kula da Umma Kande sannan yaranka zasu samu madogara tunda ni ba'a gidan nake ba yanzu,kuma yaran sun Wauki Maman Jummalo a matsayin mamansu,kaga a na





























































































































 n dadi zasuji idan ka auri Maman Jummalo"


Shiru yayi yana kallonta ko ifta idanunsa baya yi,sai can ya sauke goron ajiyar zuciya sannan ya ce


"Kenan...............




*Mu haWu a pages na gaba kuma pages Win kusa da arshe don cigaba da karanta wannan kayataccan littafi mai ilmantarwa*
'
'
'=%=%=%=%


*Shin Abban Sa'eeda zai yarda ya auri Maman Jummalo kamar yadda Umman Sa'eeda ta bijiro masa,don ara inganta rayuwar yaransa tunda Umman Sa'eeda bata gidan ko kuma zaiyi fatali da shawarar da ta kawo masa???*..............



*Da alama LOVE BIRDS=J=J an dawo hanyar Allah===,shin kozasu cigaba da dramar da suka saba na rashin zaman lafiya ko kuwa zasu daina???*............

*Umma Kande dai ana nan baki yai mutuwa a nan ana kiran SANKERU==C,shin zata samu lafiya ko kuma akasin haka???*..........

*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions<9<9=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku new updates zafafa* <9<9=C=C=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ==%=%=%=%=%




*Ina aunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* <<<<=ؖ=ؖ<9<9=C=C=ؘ=ؘ



*Daga alalamin*

=؍= *Narrnarhh Bukar* ==؍




*Comments and share =O=O=OFisabilillah*.


[6/6, 8:36 PM] Narnarhh Bukar:

< *NACINA YA JAWO MIN* <




*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen*
')


*TASKIRA WRITER'S FORUM*
*T.W.F*


*WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends



*AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9


*TELEGRAM*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk



*WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y



*BOOK 2*

*Second to the last pages=C=C=C*



6 7 ----6 8


an murmushi tayi sannan ta ce


"Wata shawara ce nazo da ita kuma ina fatan zata karSu a gareka,ganin Umma Kande a irin wannan hali,gashi su Iklima sun kusa aure,ita ma Nusaiba muna mata fata samun miji a nan kusa tayi auran ita ma,shi ne nace mai zai hana ka auri Maman Jummalo domin idan yaran sukayi aure gidan watsewa zaiyi,ya zama babu kowa don kasan Maman Jummalo da wuya ta cigaba da zama a gidan,kaga idan ka aureta zata cigaba da kula da Umma Kande sannan yaranka zasu samu madogara tunda ni ba'a gidan nake ba yanzu,kuma yaran sun Wauki Maman Jummalo a matsayin mamansu,a tunanina hakan zaifi dacewa"


Shiru yayi yana kallonta ko ifta idanunsa baya yi,sai can ya sauke goron ajiyar zuciya sannan ya ce

"Kenan bakya kishina Hussaina"

"Haba ina kishinka sosai ma kuwa,saidai duk abinda mutum zaiyi a rayuwa dole idan zaiyi *sara ya dinga duban gatari* ,taimako ne zamuyi Sulaiman na farko mun ara inganta rayuwar Maman Jummalo saboda aure shi ne cikar martabar Wiya mace sannan bazata koma kauye ba,kaga tana buatar aure tunda ba tsufa tayi ba sannan zata kular matlka da matarka sosai saboda aminiyarta ce,kaima karan kanka zakaji daWin ganin ana kula maka da matarka haWi da yaranka idan hidimar hakan ta taso tunda ni ba gidan nake ba,da ace a gidan nake da wallahi bazan kawo shawarar ka aure Maman Jummalo ba saboda ina matuar kishinka amma yanzu babu maganar kishi tunda ba gida daya muke ba"


Shiru tayi yana kallonta sai can ya ce


"Hussaina kinzo min da magana mai girma wacca wawalwata ta kasa Wauka,zanyi shawara tukunna idan da hali ila na amince,idan kuma zuciyata tai yarda wallahi komai zakiyi bazan amince ba,to wai da kike cewa na auri Maman Jummalo, idan kuma tai amincewa fa"

"In Shaa Allah zakama amince itama haka zata amince angon Hafsy"

Tana maganar tana dariya

"Au! zolayata ma kike Hussaina,ya miki kyau"

"Ni na isa na zolayi gwarzon namiji kamarka,wace ni Hussaina"

Dariya shima yayi ba tare da ya bata amsa ba suka cigaba da kallonsu.Bayan kwana biyu yayi shawara sai ya amince itama Maman Jummalo ta amince,nan da nan maganar aure yayi arfi har auyensu Maman Jummalo Abban Sa'eeda yaje,ba tare da Sata lokaci ba aka daura musu aure a can tunda har sadaki ya biya,su Nusaiba da Iklima sunyi murna sosai da wannan auran.

A Wakin Umma Kande ta tare bayan an cire komai na Wakin tare da ara gyarashi haWi da sabon fenti,kayanta ta dawo dasu Wakin Umma Kande, saida suka sha amarci har na tsawan kwana uku sannan suka raba kwana bayan yakai Maman Jummalo gidan Umman Sa'eeda wanda yanzu har da mota garesa wanda sirikinsa Sadam ya siya masa,Sa'eeda ma tayi murna sosai duk da kishiya aka ma Ummanta amma dai koba komai Maman Jummalo zata kula da tarbiyyar su Nusaiba kamar wacca ta haifesu sannan zata kula da Umma Kande idan yaran sunyi aure kasancewsar auransu baifi wata uku ba.

Bayan sati uku da bikinsu Maman Jummalo da Abban Sa'eeda jikin Umma Kande ya tashi gadan-gadan,hauka tubaran ga surutai barkatai babu daWin ji balle sauraro,gashi gabanta yanzu yama tashi aiki saboda tsutsotsi ke fita mararan ga wari,yaranta sunyi kuka sosai da wannan halin da Mamansu ke ciki.Yau kowa yazo Wakinta harda Umman Sa'eeda da Sa'eeda saboda ciwon nata yafi na kullum tashi,sai faman ihu take tana cewa

"Sankeruuuu!!! Sankerunaaa kazo!!! Kazooo"

Haka take ta faWa tana girgiza kanta,idanunta duk sun fiffito waje,sai faman kokawa take da lumfashinta still bakinta bai bar kiran Sankeru ba,kowa na ambata maka kalmar shahada amma ina Allah ya rufe mata bakin ambaton sunansa saidai Sankeru=.Haka har rai yayi halinsa kalmarta da karshe ita ce Sankeru.(Allah ka tsaremu da yin mummunan arshe===)

Kuka yaran nata suka fashe dashi babu ji babu gani suna kiran sunan mamansu,amma ina rai ya dade da yin halinsa,haka aka kira wata malama tayi mata wanka sannan aka saka mata likkafani haWi dayi mata sallah sannan aka kaita gidanta na gaskiya.Haka su Maman Jummalo,yaranta,Umman Sa'eeda da an uwanta na Maiduguri suka cigaba da karbar ta'aziyyarta har na tsawan kwana bakwai sannan gidan ya watse kowa ya kama gabansa,aka bar Maman Jummalo da yaran Umma Kande suka cigaba da zaman makoki.Bikinsu Iklima da Jummalo baifi saura wata biyu ba.

A rana ta goma da rasuwar Umma Kande Abban Sa'eeda ya shigo gidan a fusace yana wallama su Iklima da Jummalo kira,su kuma lokacin suna Wakin Maman Jummalo suna hira har Nusaiba da Mamam Jummalo,sai suka tsinkayi kiran Abban Sa'eeda,da sauri su Iklima da Jummalo suka fito tare da amsa masa kiran,su Maman Jummalo da Nusaiba daga baya suma suka fito saboda jin yadda Abban Sa'eeda yayima su Iklima kiran kamar yana cikin Sacin rai,tabarma ya umurci Jummalo ta Wauko haWi da kujera domin maganar mai muhimmamci ce,a tsaya bazasu iya tattaunata ba,da sauri da Wauko tabarma da kujerar daya umurceta tare da shimfiWa tabarma shi kuma ta mika mishi kujerar kasancewar ya mata nuni da ta mia mishi kujerar, zama yayi a bisa kujerar sannan ya umurci su Iklima da Jummalo su zauna bisa tabarma,babu musu suka samu wuri suka rakuSe kamar marasa gaskiya,su Mamam Jummalo da Nusaiba wani Sangare na tabarmar suka zauna tare da maida hankulansu kacokam! ga Abban Sa'eedan.Gyaran murya yayi sannan ya fara magana cikin Sacin rai

"Iklima da Jummalo kai harma da Hasfy kun kyauta kenan da baku sanarmin da mazajensu Iklima basu *Sakesu ba* kunyimin adalci na rashin faWamin saidai naji majalisar layi ta Wauka akan inaso na aurar da yarana akan wani auran,hakan ya dace da kuka i sanarmin"

Dummmmm!!! Haka irjinsu Iklima da Jummalo ya bada jin an anbato musu bala'in da Allah ya kuSutar dasu a baya,tuni Iklima uwar hawaye har ta fara zubda walla,itama Jummalon zubda wallar take,ara tambayarsu yayi amma shiru babu amsa domin basu san taamaiman mai zasu ce dashi ba,Maman Jummalo ce ta ce


"Baban Nusaiba kuskure dai an riga da an tafka,ayi hauri na rashin sanar makan da bamuyi ba,wallahi ba yaran kaWai ba koni tsoron mazajen yaran nake, domin ni da mariyanya Umma Kamde da yar muka sha a hannunsu balle yaran da sukayi rayuwa dasu a gida Waya"

TaSe baki yayi sannan ya ce

"Wannan kuta shafa bani ba,ni nace kuje wurin boka nemama yaranku mazaje? Ko kuma sanda kukayi shawararku keda ita kun saka dani ne,ce nike ku kuka yi *KiWinku kuma kuka yi rawarku* to sai yanzu zaki ce tsoro kike ji,kina nufin su Iklima da Jummalo a Waura musu aura akan wani auran kenan"

Da sauri ta girgiza masa kai tana cewa

"A'a Baban Nusaiba ba haka nake nufin a Waura musu aure bisa wani auran saidai na faWa maka ne mazajen suna da matsaloli da dama,sannan Baban Nusaiba don Allah ka daina tado da maganar baya,kuskure ne mun aikata a baya sannan munyi nadama tafi arfin cikin kwando,bayan mun kwashi kashinmu a hannu,don Allah kabar tado da zancen baya na roeta"

"Naji, yanzu dai dole ku kiramin samarinku kuce inason ganinsu saboda zama zanyi dasu tare da fahimtar dasu akan auran da basu san dashi naku ba,idan sun ji sun amince akan zasu aureku to dole a Waga ranar auran sai bayan kunyi idda sannan za'a Waura,wannan shi ne abinda shari'ar musulunci ta gindaya akai,sannan kowaccanku ta bani address Win gidan mijinta da numban wayarsa"

Cikin rawar murya da tashin hankali Jummalo tace

"Baba address Win gidan kawai na iya riewa amma banda numbansa"

"To ai saiki rubutamin address Win a paper,ke kuma fa Iklima"

Itama kamar Jummalo bakinta na rawa ta ce

"Amm Amm nima banda numbansa saidai address Win gidan"


Dariya Abban Sa'eeda yayi sannan ya ce

"Au Allah kamar haWin baki kowa maida numban mijinsa,to idan nace komawa gidan mazajen naku......"


Ai da wani irin sauri su Iklima da Jummalo kamar haWin baki suka ce

"A'a Baba,kayi hauri"

Kuka riris suke yi suna roonsa akan kar a maida auran,hausawa suka ce *Mai Waki shi yasan inda yake masa yoyo* wannan haka yake domin su kaWai suka san walaha,bala'i haWi da azabar da suka sha a baya.Tausayi suka ba Abban Sa'eeda sai ya ce

"Wasa nake muku ai, ku share hawayanku,yanzu ina waje ku rubutomin address Win gidajen nasu ku kawomin saboda yau nake so na kira Hassan akan batunsu don bazan iya tun kararsu ni kaWai ba saida babba sannan tsayayye, karku manta da kiran samarin naku akan ina nemansu anjima da daddare"

"To Baba"

Fita yayi daga gidan,Iklima ta shiga Waki tare da Wauko musu jakar islamiyarsu,address Win gidan mazajen nasu na baya suka kwafe a takarda domin kamar *zane ne a bisa kan dutse* wanda baya iya goguwa a zukatansu.Jummalo ce ta kaima Abban Sa'eeda papar a waje, a lokacin da ta kawo masa paper yana waya ne da Uncle Hassan tare da yi masa bayani akan matsalar data bullo na auran yaransa bayan akwai wani auran akansu,sosai Uncle Hassan ya ce zaiyi jagora zuwa gidan mazajen nasu,amma sai ya fara jin ta bakin yaran tukunna don ya tabbatar ba arya suke ba sannan sai ya Wau mummunan mataki akan mazajen nasu saboda *Cin zarafinsu* mazajen sukayi,a haka ya kammala wayan tare da amsar paper ta koma cikin gidan.

Washe gari da safe saiga Uncle Hassan yazo gidan tare da kiran Abban Sa'eeda kasancewar yau Saturday shi yasa ya samu damar zuwa,shigar dashi gidan yayi bayan ya umurci su Iklima da su fito da tabarma waje.Da sallama ya shigo gidan tare da zama shi da Abban Sa'eeda a tabarma, su Iklima da sauran an gidan suka fiddo da wata tabarmar suka zauna,Abban Sa'eeda ne yayi gyaran murya tare da cewa

"To Alhamdulillah,yanzu ga Hassan yazo don kuyi masa bayanin komai akan zamanku a gidan mazajenku kar ku Soye komai sannan karku ara komai,iya gaskiya muke buatar, ko ba haka Hassan"

aga masa kai yayi alamun *EH* sai ya cigaba da cewa

"To yanzu muna sauraranku"

Shiru wurin yayi, Jummalo ce ta fara kwararo labarin rayuwar da tayi a gidan mijinta tun a daren farkonta har zuwa ranar da Ubangiji ya bata ikon guduwa daga gidan,bata Soye komai ba sannan bata ara komai ba.Itama Iklima sanar musu komai tayi a game da zaman auranta a gidan mijinta tun daga daran farkonta,da amfanin da yake da ita ta bayanta tare da abokanansa har video Win abubuwan da suke mata ta sanar ma Uncle Hassan, Tabbas! Ko ba'a faWa ba Uncle Hassan da Abban Sa'eeda sun girgiza da jin labarin Iklima musamman Uncle Hassan labarin yayi matuar tayar masa da hankali,jin labarin yayi kamar wasan kwaikwayo,gyarar murya Uncle Hassan yayi sannan ya ce

"Naji bayananku,sannan in shaa Allah zamu kwato muku hakinku musamman ma ke"

Nuna Iklima yayi kasancewar bai san sunanta ba,ya cigaba da cewa

"Ina da aboki babba a *STATE SECURITY SERVICE* wato jami'in sirri ne kuma babba,zan tura masa bayananku domin nayi recording Win abubuwan da kuka ce saboda ita ce hujjarmu babba a yanzu,in shaa Allah zamu wato muku hakin tare da hukuntasu saboda wannan cin zarafin Wan Adam ne suka yi"

Godiya sosai suka shiga yi masa,shi kuma yana ce musu ai ba damuwa sun zama Waya.A ranar Uncle Hassan ya kira abokinsa babban jami'in sirri yayi masa bayanin komai tare da tura masa addresses Win gidajensu da kuma recording Win da yayi lokacin su Iklima suke bayanin rayuwarsu a gidajen mazajensu,sosai abokin nasa yayi alawarin yin bincike mai zurfi tare da taimaka a hukunta masu laifin.

Bayan sati Waya da wannan zancen da Uncle Hassan yayi da abokinsa,lokacin Uncle Hassan yana gida saiga kiran abokinsa ya shigo wayarsa,da sauri yayi picking daman yanaso ya kira yaji what's going on akan case Win.Sallama yayi,a can abokinsa ya amsa,abokin ne ya cigaba da cewa

"Kana gida ne? "

"Eh" cewar Uncle Hassan

"Yawwa gani nan zuwa don bayanin bana waya bane"

"Ok Allah ya kawoka lafiya fatan dai kun samu nasara"

"Sosai ma kuwa ai nasarar ma *min indillahi ne* ba daga wurinmu take ba"

"Maa shaa Allah can't wait to hear from you"

"Ok sai nazo"

Katse kiran yayi tare da kiran Dr. Nabila akan ta shirma musu girki yanada bao yanzun nan,"To" ta ce masa sannan ta wuce kitchen tare da kiran ar aikinsu Jamila, kasancewar yau lahadi dukkaninsu suna gida.Ba'a Wau awa Waya ba saiga kiran abokin Uncle Hassan kenan ya iso,ce masa yayi ya shigo cikin gidan,gyara parking Win motarsa yayi a gefen gida sannan ya shigo cikin gidan har falon gidan da yake gidan ba baonsa bane yakan zo wani lokacin harda matarsa da yaransa,su Uncle Hassan suma sukan zo gidansa,abokanai ne sosai tun suna jami'ar suke abota har zuwa yanzu suna tare saidai aikin kowa ne ya banbanta.Da sallama ya shigo falon,amsa masa Uncle Hassan yayi tare da miewa suka rungume junansu,abinci da kayan sha Dr. Nabila ta kawo tare da yi masa sannu da zuwa,twins da Kauthar zuwa sukayi gaisheta sannan suka koma sama.Bayan ya sha ruwa sai yayi gyaran murya tare da cewa

"Sarkin aguwa nasan you're eager to hear from me"

Dariya Uncle Hassan yayi sannan ya ce

"Kaima kasani ai,akwai ni da son jin labari,kace Ubangiji yayi ikonsa akai,gist me brooo"

Dariya sosai abokinsa yayi sannan ya fara magana

"Alhamdulillah Alhamdulillah,kawai zan iya cewa domin kuwa Allah yayi ikonsa akansu,Ubangiji baya yafe hakin wani a bisa na wani,so bayan ka bani informations a game dasu tare da address nasu sai na mia case din ga hukumarmu,sosai aka amincemin akan nayi jagora a case Win,nayi bincike sosai a game dasu har na tsawan kwana hudu sai a kwana na biyar muka shirya tsaf! Zuwa Waya daga cikin gidajen da kabani address Winsu,bayan mun isa gate Win gidan ko mintuna biyar ba muyi da fitowa daga motocinmu ba sai gashi an wangame gate Win gidan,wasu matasa ne biyu rie da wasu mutum kamarsu sai faman aman jini yake ta hanci ta baki gashi ya rame sosai kamar mai ciwon *HIV AIDS* sai wata tsohuwa tana biye dasu a baya tana kuka suka shiga wata mota wacca take suka da namu motocin,mudai kallonsu kawai muke,bayan sun fito sai mai gadin gidan zai rufe gate Win gidan nayi sauri masa magana babu musu ya tsaya da rufe gate Win,tambayarsa nayi akan ina neman mai gidan,cemin yayi ai wanda matasan nan suka rio shi ne mai gidan sannan wacca naga tana kuka ita ce mahaifiyarsa,ara tambarya nayi meke damunsa haka,hmmm kasan abinda mai gadin ya faWamin cututtukan da yake damunsa saida na girgiza sosai"

Cikin zauwa Uncle Hassan ya ce

"Don Allah faWamin wasu cututtuka suke damunsa"

Gyara zama yayi tare da kurSar ruwan sannan ya cigaba da cewa

"A yadda ya sanarmin mutumin yana shan giya sannan mai neman mata ne sosai,cututtukan da yake damunsa akwai ciwon hanta wanda a sanadiyar shan giya ya samesa,sai ciwon sanyi,sannan kuma wacca tafi tadamin hankali ita ce *yana Wauke da cutar dake karya garkuwan jikin Wan Adam wato HIV AIDS* wa'innan su ne cututtukan sannan asibiti suke son kaisa saboda ciwon yaci arfinsa yanzu"

Sosai wannan labarin ya tada hankalin Uncle Hassan,ace mutum Waya yana Wauke da wa'innan manya-manya cututtuka haka,katse mishi tunani abokinsa yayi da cewa

"Ai na wannan mai saui ne akan Wayan mutumin mai luwaWi"

Da sauri Uncle Hassan ya kallesa tare da cewa

"Kace wannan mai saui ne,mutumin dake tare da wa'innan manya-manyan cututtuka ace nashi mai saui ne,how? "

Murmushi abokinsa yayi sannan ya ce

"Ai shi at least yana lumfashi sannan zai iya roon yafiyar wanda ya cuta amma wannan fa,da muka je layin tare da wanwasa ofar gidan,bayan mai gadin ya fito na tambayesa game da mutumin,shiru yayi mai gadin yana kallon nima din kallonsa nake ina jiran bayani,saida ya shafe mintuna huWu still idanunsa a kaina nima ban cire nawa idon akansa ba,sai can ya cemin,yau kwanan mai gidansa shida da rasuwa bayan yayi fama da *yoyon kashi da cutar Cancer a al'aurarsa" saboda abubuwan da yakeyi,gashi ko nan da can bai iya fita duka abokanansa sun gujesa,daman tuntuni ya rabu da an uwansa balle su taimakesa,kashi,fitsari duk a wajen yake,ga penis Winsa ya tashi aiki kwata-kwata saboda ruwa mai yauki ke fita ga shegen wari,idan mutum ya dunfaro Wakin da yake wallahi dole ya toshe hancinsa saboda warin da Wakin ke fitarwa,hmmm in taaice maka bayani shidai wannan,wucewa kawai mukayi ba tare da ce ma mai gadin gs abinda ya kawomu ba,kasan ban dandara ba na sake komawa gidan mutumin nan na farko don sake tambayar what's going on,wallahi shiga tashin hankali nayi jin a ranar da muka zo gidan a ranar Allah yayi masa cikawa,in short dai an uwan naka *TAKABA* dai ya kamasu yanzu, Allah yayi musu sakayya a ta yadda babu wanda yayi zaton haka"

Sun daWe suna hira har yaci abincin da Dr. Nabila ta girka masa sannan Uncle Hassan ya rakashi har wurin motarsa sukayi sallama. A ranar Uncle Hassan ya kira Abban Sa'eeda tare da sanarma takaba ya kama yaransa domin kuwa Allah yayi ikonsa akan mazajen namu tare da sakanya musu tun a nan duniya,Sosai Abban Sa'eeda yaji dadin wanga batu tare da yi masa godiya maras adadi,daman samarinsu

Please Login or Register in order to submit comment