Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda a danginsu ba'ayin kishiya???*........



*Da alamu dai su Umman Sa'eeda sun haWu da ahalinsu,shin zasu samu farin ciki ko ko akasin haka???*.......




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions<9<9=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku new updates zafafa* <9<9=C=C=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ==%=%=%=%=%



*Ina aunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* <<<<=ؖ=ؖ<9<9=C=C=ؘ=ؘ





Daga alalamin

=؍=Narrnarhh Bukar ==؍






Comments and share =O=O=OFisabilillah.


[5/9, 8:00 PM] Narnarhh Bukar:

< *NACINA YA JAWO MIN* <





*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen*
')





*TASKIRA WRITER'S FORUM*
*T.W.F*



*WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends



*AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?id=6615ba31404e6e2687888ab9



*TELEGRAM*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk



*WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y



*BOOK 2*



4 3 ----4 4



Yauma zaune suke a ofar Wakinsu Sa'eeda kasancewar tunda Sa'eeda tayi musu sallama ofar Wakinsu ya koma wurin shan iskarsu,Umma Kande ce ta kasa hauri ganin yadda awarta ta koma gwanin ban tausayi,cikin sanyin murya Umma Kande ta fara magana

"awas anya ba komawa wurin boka Sankeru zamuyi ba,ko za'a samu wata mafitar game da cikin nan? "

Maman Jummalo ce ta mata wani mugun kallo tare da cewa

"Haba kawas yanzu abinda ya faru dani bai ishemu ishara ba,nidai na daina zuwa wurin boka in shaa Allah, zan nema gafarar Ubangijina akan laifukan da nayi masa a baya,domin cikin nan nawa ishara ce Allah ya nunamin,a farko Allah ya sanya ishararsa akan aanmu amma bamu gani ba kuma bamu dandara ba muka sake zuwa wurin boka,shiyasa yanzu ya sake saukar da ishara babba a kaina,domin sai yanzu nasan zuwa wurin boka babban asara ne,amfaninsa na Wan wani lokaci ne gajere,kinga awas mu tuba ga Allah sannan mu naimi yafiyarsa,ko ma rabauta ranar gobe iyama,wacca don ita kike zuwa wurin bokan tabar mana gidan ai"

TaSe baki Umma Kande tayi tare da turo Wan kwalinta gaba sannan ta fara magana

"A'aa hahhh! Hasfy ai saiki cemin kin koma malama ustaziya bagadadiyyah,wannan wa'azi haka Allah yace Annabi yace saikace matar Sudais na Makkah,hmmm to bari kiji Hafsy, ni Saratu jikar Sarkin ruwa yanzu na fara zuwa wurin boka,babu gudu babu ja da baya,zuwa wurin boka sai inda mai ya aremin,domin zuwa wurin boka yamin rana babu abinda zance sai godiya,kika sani idan mukaje wurinsa mu samu mafita game da wannan cikin? "

"Allah ya tsareni ni Hafsy na ara zuwa wurin boka don neman biyan buatuna,bokan daya Wirkamin ciki shi ne zai nemamin mafita,inaaa babu ni a cikin wannan saSon,ishara ce Allah ya nunamin kuma nagani na Wauka masu hali irin nawa ina roa musu shiriyar Allah"

Tafi Raf! Raf! Raf! Umma Kande tayi harda buga cinya tare da sheawa da wata ar bazawarar dariya irin na an bariki tana cewa

"Ahayyeee Chasssss!!! Hasfy yaushe kika tuban da zaki roama wasu shiriyar,kin tabbatar da tuban naki ta amsu,wai wai wai ni jikanyar sarkin ruwa,kodai na dauko miki lasifikan masallanci layi ne ki fara wa'azin Hafsy"

"In shaa Allahu karSabSiya ce domin har cikin zuciyata nayi nadama,kema awas ya kamata ki tuba,domin ita wacca kike don ita da arta basa gidan hasalima bakisan a wace duniyar suke ba,mai zaisa ki cigaba da Sata lokacinki awas,sannan ni ba wa'azi nake miki ba gaskiya tsagwaronta nake faWa miki domin wannan rayuwar ba matabbata bace,yau kaine gobe ba kai bane,mai zaisa muyita Sata lokacinmu muna Sata rawarmu da tsalle,lokaci na ara ure mana"

"To! to! Ustaziya Hafsy naji wa'azin,Allah ya karSa,sai kibari lokacin watan Ramadan idan ya kama sai a nemo miki mai ja bai ke kuma kina fassarawa,bari kiji nifa iyayyar Umman Sa'eeda da arta a jinina take,banga abinda zaisa na janye makaman yaina akansu ba,koda suka bar gidan nan ba yana nuni da na haura da bibiyar rayuwarsu bace,a'a yanzu ma wani sabon aikin nakeso ayi musu ita da arta akan karsu dawo gidan nan har abada,shiyasa nace mu ara zuwa wurin boka kinga kema saiki kai taki matsalar akan batun cikin"

"Allah ya sawae ni Hafsy da ara zuwa gun wani zindiin ato don biyan wata buatata yanzu,da Allah na dogara,kuma nasan shi zai biyamin buatuna"

Huro gajerun hancinta Umma Kande tayi tana sake taSe baki tare da cewa

"Awo Allah!!! Lallai kuwa!! Au yanzu ne kika san zuwa wurin zindiin ato bayi da amfani Hafsy, da can da kike zuwa bakisan da haka ba sai yanzu,hmmm abin da ban mamaki"

Haka Umma Kande da Maman Jummalo sukaita musayar baki akan zuwa wurin boka, ita Umma Kande tanaso ta sake dulmiyar da Maman Jummalo,ita kuma Maman Jummalo na mata wa'azi akan ta tuba ta koma ga Allah tunda wacca take zuwa wurin boka don ita tabar mata gidan.

A Sangaren yaransu Jummalo da Iklima makarantarsu suke zuwa safe da rana,ko samari ma basu kulawa balle ayi maganar aure,kai in taaice muku dukkaninsu tsoron maza suke yanzu(su Iklima anji maza====C=C=C),ji suke idan sukayi wani auran komawa gidan jiya zasuyi.Kasancewar ajin matan aure Jummalo da Iklima suke,basa shiga sabgar an ajin saboda duk sun girmesu sosai wasu ma zasu iya haihuwarsu.

Iklima da Jummalo suna zaune a aji suna jiran malami ya shigo,kunnan Iklima ya yajiyo mata abinda ya kusa birkita mata lissafi wato Maman Jummalo nada ciki cikin ma na boka,wata ce a bayansu take sanar ma matan suna dariya harda shewa.Da sauri Iklima ta taSo Jummalo haWi da ce mata ta saurara abinda ake faWa a baya,babu musu Jummalo ta kasa kunnanta don taji me ake cewa,ai wani irin Damm!!! Darammm!! Damm irjinta yayi,jin wata a cikin matan na cewa Mamanta nada cikin boka shiyasa yanzu take saka niaf.Da sauri Jummalo ta mie tana kallansu,jikinta na rawa zatai magana Iklima tayi saurin rufe mata baki dan tasan idan batayi haka ba,matan auran zagesu tsaf! zasuyi ciki da waje tare dayi musu gori saboda halin iyayensu,gwara tun kar ayi karma a fara,jan hannunta tayi zuwa waje tare da Waukar jakan makarantarsu,wucewa gida sukayi,Jummalo babu abinda take inba kuka ba,tana mamakin wai yau mamanta ce da cikin boka a jikinta sannan ita kuma zata samu anwa daga tsatson boka,wayyo wayyo ni Jummalo,wannan wace irin addara ce ta samesu haka rana tsaka,a haka suka iso gidan Iklima na faman bama Jummalo hauri akan tayi shiru mutane na kallansu amma ina bata mutane take ba,ita ta wannan addarar da ta samesu ne hankalinta yake.

Shigo gidan su Jummalo sukayi afu jajan hankali tashe,Umma Kande suka taras tana zaune ita kuma Maman Jummalo ta kewaya bayi,Jummalo ce cikin kuka ta ce

"Umma Kande da gaske ne mamana nada cikin boka a jikinta"

"Waya ce miki Jummalo" cewar Maman Jummalo wacca fitowarta kenan daga bayi

"A Islamiya ne muka ji matan aji suna zancen cikin boka harda dariya da shewa a lokacin malami bai shigo aji ba" cewar Iklima


Shiru Maman Jummalo tayi tana kallon arta,ita tama rasa wasu haruffa haWi da kalmomi ne ya dace ta tattaro wurin gina jimlolin da ta tabbata zasu bada ma'ana tare da fahimtar da arta addarar da ta samesu,babu yadda suka iya,Umma Kande ce ta katse shirun da sukayi,tana cewa


"To mene ne abin kuka Jummalo, ai matsalar daga mamanki ce,tuntuni nace mata mu ara zuwa wurin boka ko za'a dace cikin ya fita amma tai,ita ga mai tsoran Allah wai ta tuba da zuwa wurin boka,kinga kuwa ai dole a dinga gulmarku tare da zunWanku akan wannan cikin"

Cikin fushi Maman Jummalo ta ce

"Haba awas ya kuma ina neman yadda hankalinta zai kwanta ba tare da tasan abinda ke faruwa ba,ke kuma kina neman canjamin alalami,haba awas a gaskiya banji daWin abinda kikayi ba,addara ce kuma tana iya faWawa kan kowa,kinga Jummalo abinda matan ajinku suka faWa a kaina gaskiya ne,ishara ce Allah ya nunamin game da zuwa wurin boka,na tuba na koma ga Ubangijina,ita ma awas naso ta gane ishara ce Allah ya nuna mana amma tai,ya zanyi da ita"

Gyara Waurin girji Umma Kande tayi,sannan ta kakkaSe tabarmata haWi da cewa


"To Malama Ustaziya Hafsy jikar Sudais idan kin gama wa'azin, Allah ya bada lada,ni nayi Waka"

Binta sukayi da kallo,sai can Jummalo ta ce

"Naji daWi da kika gane abinda tun tuni muke fatan ku gane akan illar zuwa wurin boka,daga yau kome an aji zasu ce game daku,bazamu sake tankawa ba"

"Hakane kuwa Jummalo, kar mu biye musu, kawai maida hankalinmu akan karatunmu"cewar Iklima

Haka dai su Jummalo da Iklima suka cigaba zuwa Islamiyarsu,sannan tun daga ranar suka dena biyewa an aji,ko kuma an layi.Wannan Kenan


@@@@@@@@@@@@



*ABUJA*


Wani irin asurgumin daji ne Haj. Zulfa'u ke faman gudu a cikinsa,ko'ina na dajin duhu ne babu haske,ga wani irin baayan tsuntsaye masu yawan gaske a kan bishiyun dajin suna wani irin kuka babu daWin ji balle sauraro,ciyayin da suke a dajin masu ayoyi ne,duk takun da Haj. Zulfa'u zatayi sai ara ta soketa,amma ba jin zafin sukar da ayan taimaka take ba a'a mutanan da suke tunkarota ne take jin tsoronsu tare da fargabar kar su cimmata,amma ina gudu Haj. Zulfa'u take kamar ba gudu takeyi ba,kamar wuri Waya ne take babu canji ga wa'inan mutanan ara kusantota suke ,dukkaninsu da fararan kaya,ga wani irin haske na baibaye dasu,a sama suke tafiya ba tare da afarsu ta taka wa'inan ayoyin ba,tana wannan gudun ne sai gasu sun cimmata har gabanta.Dariya suka fara yi babu akautawa,sunayi suna nunata,ita kuwa sai uban haki take tana rufe idanunta saboda haskensu dayake kashe mata idanu.Mace ce mai tsohon ciki ta rie hannun wasu an biyu maza,sai kuma wasu an biyun Mace da Namiji amma manya ne sosai don zasu wuce shekara talatin da takwas a duniya,su kuma suna gefe Waya.Matar nan mai ciki ta fara magana cikin amon muryarta mai firgitarwa

"Zulfa'u!!! A tunaninki zaki iya guje mana ne!!! A tunaninki dubararki zatasa kar mu cimmiki ne!!! A tunaninki hangen nesanki zaisa bazamu iya taddoki bane!!! Inaaa Zulfa'u kinyi kuskure!!! Kuskure babba!!! Domin kuwa kin yanke bishiya amma kin manta baki haWa da tushanta ba!!! A lokacin da wawalwarki ta raya miki bishiyar ta bushe ta zama itce babu genyan,sai kuma a lokacin Allah ya tayar da tushan nan ta baki cire ba,sannan tushan ya zama reshe biyu mabanbanta,wanda gefe daya da ganye wani gefan babu ganye,sai kuma Allah ya ara nufinsa da mayar da reshan mara ganye ya zamu mai ganye hadi da kusanto da rassan guda biyu wuri Waya!!! Dubararki ta are Zulfa'u!!! Alalamin rubutunki ya are domin zasu dawo Waukar fansa Zulfa'u!!! Zasu dawo nan kusa Zulfa'u!!! arshanki ya kusa zuwa Zulfa'u!!! Kinga Tushan da kike manta baki cire ba can!!! "

Nuna wa'inan an biyun mace da namijin tayi,duk a lokacin Haj.Zulfa'u hannunta na kan fuskarta ta kare idanunta saboda hasken mutanan, mai cikin ne ta cigaba da cewa

"Ki jira arshanki Zulfa'u!!! Rassan nan suna nan dawowa!!! "

Dariya suka cigaba dayi suna nunata harda an biyun nan maza dake rie a hannun mai cikin suma dariyar suke, sai kuma Difff !!! Mutanan suka Sace,ihu mai arfi Haj. Zulfa'u ta fara tana cewa

"Karku dawo!!! Karku zo wurina!!!"

A gigice Haj. Zulfa'u ta farka daga mummunan mafarkin da tayi babu salati balle sallallami sai ba kiran Boka BurumbuWu don ya kawo mata agaji(Wa'iyazubillah>>>)

Mafarkin akwai firgitarwa da bada tsoro sosai,dube-dube ta fara yi don tabbatarwa ko ba'a cikin wannan asurgumin dajin take ba,ga duk ilahirin jikinta ya jie da gumi kamar wacca ta fito daga wanka,tashi tayi tare da kunna wutar Wakin,agogon Wakin ta duba haWi dazaro idanu waje ganin arfe 2:35am na dare,wannan mummunan mafarkin ya sameta.Haka ta zauna irjinta da dukan tara-tara tana tunanin me zatayi ganin kar tsatson maiyiyarta su cimmata, don idan suka cimmata ta tashi aiki kenan,domin arshanta ne zaizo,tunani ne kala-kala fal a ranta,ta rasa waya Waya da zata Wauka,kowace hanya idan ta Wauka saita karkace ta kasa bullewa,ta kasa kawo mafita akan wannan matsalar da take ci mata tuwo a warya,ta hanata rawar gaban hantsi,kar dai ace reshe ne ke shirin juyewa da mujiya,wayyo!!! Da shikenan tata ta are babu sauran wata rina a kaba.Haka tayita tunani har daga arshe Sarawo bacci ya sureta batasan da zuwansa ba.

Washe gari haka ta tashi da kasala tare da Sacin rai,jinta take kowama ta tsane shi illa ahalinta,ji kake kamar da hallaka duniya ta zauna ita kaWai da ahalinta,haka ta shirya zuwa downstair domin karin kumallo.Kasancewar bikin Fadila ya arato yanzu baifi saura sati biyu ayi bikin ba,har an biki na nesa sun fara zuwa wato an uwanta na Niger dayake mahaifin Haj. Zulfa'u Wan asalin Niger ne,ci-rani ne ya kawoshi Nigeria har Allah ya addara zaman a Nigeria.

Haka lokacin biki yayita aratowa,an uwa na nesa dana kusa duk sunzo,har da ita uwar gayyan wato Fadila da iyayenta sun iso Nigeria. Haka aka sha shagulgulan bikin Fadila tare da programmes kala-kala,duk wannan shagulgulan bikin da aka sha Haj. Zulfa'u jininta a umba yake domin tsoro takeji kar tayi arangama da tsatson maiyiyarta ta banu,haka aka kammala biki lafiya tare da kai amarya gidan mijinta wanda a satin ya wuce da amaryarsa Jordan inda yake aiki.Wannan kenan.



@@@@@@@@@@@@@


*KADUNA*


A Sangarensu Sa'eeda,tunda Ummanta da Momin Sadam suka etara zuwa India ta koma gidan Dr. Nabila da zama wanda yake a an Majalisu,gidan babba ne sosai mai hawa Waya,akwai garden da swimming pool a ciki,ga wurin parking motoci babba wanda sai iya cin motaci harda biyar,kai na taaice muku,gidan ya haWu iya haWuwa.


Wani hadadWan Waki mai bayi a ciki Dr.Nabila ta ce Sa'eeda ta zauna,kunsan ni da bin wawaf,haka nima na shiga Wakin don kashema idona kwarkwata,wooow!!! Aljannar duniya, gaskiya ko amarya sai haka,don Wakin ya haWu iya haWuwa.


A washe garin ranar Dr.Nabila takai Sa'eeda saloon tare da wurin gyaran jiki,nan da nan Sa'eedarmu ta koma kamar ar larabawa,shei kawai fatarta take,ga gyaran gashi tasha sai tace amarya,tafito yayi kyau abinta kamar ka saceta ka gudu,wunin ranar a saloon da wurin gyaran jiki Dr. Nabila da Sa'eeda suka are sai wurin 5:40pm suka wuce makarantarsu Jawaad da Jadwa wato twins wa'inda basu wuce shekara 13 ba sai aramarsu Maimuna mai sunan kakarsu Sa'eeda amma ana kiranta da Kauthar,hada suka Wunguma zuwa gidan.


Kullum sai sunyi waya da Ummanta a wayar Momin Sadam Kasancewar yanzu jikinta yayi saui sosai,a nan ne take sanar ma Sa'eeda daga India zasu wuce Saudiya don aikin Umrah kafin lokacin Hajji yayi sai ta koma,daWi kasheni haka Sa'eeda takeji aranta ashe faWin hausawa da suka ce *BAYAN WUYA SAI DAI* ba arya bane,gashi yanzu duk wahalar da suka sha a baya ta zama labari,Suna cikin farin ciki da annashuwa,ga ci mai kyau,sha mai kyau,tufafi mai kyau,gida mai kyau,babu abinda zasu ce sai Alhamdulillahi.


A Sangaren makaranta kuwa,tare suke zuwa da Dr. Nabila tana rie da jakar Dr.Nabila duk inda zata,ranar farko ar aji sunyi gulma sosai kamar bakinsu zai koma na zaSa,kasa hauri Iman tayi ta sanar musu cewa Dr.Nabila Auntyn Sa'eeda ce haka mijin Dr.Nabila kawun Sa'eeda ne,Kasancewar Dr. Nabila na gab da fita daga ajin Iman tayi magana,cak! Dr. Nabila ta tsaya,tambayar Iman tayi what's going on daya sakata faWin haka,Iman bata Soyema Dr. Nabila cin kashin da an aji sukama Sa'eeda ba harda Cin amanar da Maryam tama Sa'eeda saida Iman ta faWama Dr. Nabila duk da Maryam kwana biya ta rabu da zuwa school. acin rai iya Sacin rai Dr.Nabila ta shiga,zazzagama an aji ruwa masifa da bala'i Dr. Nabila tayi haWi da cewa da sun san suwaye ahalin Sa'eeda da kullum idan tazo aji russunawa zasu dungayi suna gaidata domin ita ar dangi ce gaba da baya sannan ahalinta gogaggun an boko ne kun cikakkun an kasuwa wa'inda sukayi fice a duniya bama Nigeria ba, tun daga ranar an aji basu sake gulmar Sa'eeda ba hasalima janta a jiki suke ita.


Kasancewar yau Dr.Nabila bata da lecturs bata je school ba,Sa'eeda ta fita da motarta zuwa school don yanzu Sa'eeda ta iya tuin mota sosai,jiran Uncle Hassan take ya dawo ya siya mata mota dayale yace yana dawowa sai siya mata ita mota tunda ba kullum Dr. Nabila take zuwa school ba sai in tana da lectures,kasancewsr da wuri aka tashesu,haka ta nufo gida bayan taje supermarket tama su twins shopping,danno motarta tsyi cikin layin sai taga jerin motoci har uku baae a wurin gate Win gidansu,mamaki ne ya cikata,bai sukayi a gidan da alama,sai kuma idanunta suka kai kan numban motar wanda aka rubuta *SADAM 001* a matsayin numban motan,tsaki taja tana ununi ita kaWai tana cewa


"Sun wani zo sun ajiye motacinsu a gaban gidan mutane,mtwss! "


Haka taja motarta zuwa gate Win gidansu,horn tayi da arfi sai mai gadi yazo da sauri ya bude mata gate,danno motarta tayi cikin gidan har inda ake parking Win motoci,saida ta kashe motar sannan ta fito,irjinta sai bada Dummm! Dummm! Dummm! Yake ta rasa dalili,haka ta arasa cikin falon da sallama haWi da walla ma Kauthar kira da twins tana cewa

"My Twins!!! Kauthar where are you guys,I come with some chocolates for you guysss!!! "


Cikin muryarta mai shegen daWi kamar ana *Busa Sarewa* haka maganarta take fita.Sadam da tunda yaji an waWa sallama irjinsa ya bada Dummmmm! Bai taSa jin murya mai shegen daWi irin wannan muryar da tayi sallama ba,to wace ce tazo wurin Aunty Nabila mai murya zazzaa haka? Bai arasa tunaninsa ba yaji tana kiran twins da Kauthar ai cak! Ya tsaya da danna system Winsa tare da kafe idonshi a wurin da yaji sautin muryar na fitowa.Sa'eeda da taji shiru ba'a amsa sallama ba kuma sannan su Kauthar basu zo ba kenan suna upstair,arasowa cikin falon tayi tare da cire gyalenta,sai ta ajiye jakarta tana wani mia irin ta gaji Win nan,duk wannan bidirin da take Sadam idonshi kar! A kanta,ita ko batasan da mutum ba shiyasa take ta haukanta ita kaWai harda ar rawa(Oh!!! My Esteem Fans ku tayani dubawa Sa'eeda ta koma wata abu daban ====C=C=C)


Sai can taji kamar idanu na akanta,sai tayi saurin kai dubanta gun ai ba arzii ta waro manya-manyan idanunta waje tare da cewa.................




Mu haWu a pages na gaba don cigaba da karanta wannan chakwakiyar chakwalkwali haWi da rikita-rikita =C=C=C=C
'
'
'
'



*Tofa>Kaiko Sadam wani irin kallo ne haka sai kace maye,mai ya assasa bugawar irjin Sa'eeda da Sadam??? Shin mai Sa'eeda ke shirin cewa jin yadda tayi ta hauka ita kaWai harda ar rawa???*......



*wani irin mummunan mafarki ne Haj. Zulfa'u tayi haka mai firgitarwa haWi da tsoratarwa??? Suwaye ne tsatson maiyiyarta???Wace ce Haj. Zulfa'u*.......



*Da alama Maman Jummalo an tuba,shin Umma Kande taza tuba ko kuwa har yanzu wahala bata are mata ba???*.....



*wai in Nusaiba,a wace duniyar take???*.........




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions<9<9=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku new updates zafafa* <9<9=C=C=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ==%=%=%=%=%





*Ina aunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* <<<<=ؖ=ؖ<9<9=C=C=ؘ=ؘ






Daga alalamin
=؍=Narrnarhh Bukar ==؍




Comments and share =O=O=OFisabilillah.


[5/11, 9:33 PM] Narnarhh Bukar:

< *NACINA YA JAWO MIN* <






*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen*
')




*TASKIRA WRITER'S FORUM*
*T.W.F*



*WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends



*AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?id=6615ba31404e6e2687888ab9



*TELEGRAM*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk



*WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y





*BOOK 2*



4 5 ----4 6




Sai can taji kamar idanu na kanta,sai tayi saurin kai dubanta gun ai ba arzii ta waro manya-manyan idanunta waje tana da cewa

"Wayyo Allah!!! Mutum ko aljan!!! "

Banza yayi da ita tare da cigaba da aiki a laptop Winsa,a zuciyarsa yana cewa 'Lallai yarinyar nan wato aljani ta maidani ko,da alama zan koya mata hankali kenan,batasan waye autan Mom bane' ko takanta bai arabi ba,duk kallon da take jefa mishi da manyan idanunta duk yana sane,da alama kafin yabar Kaduna saiya koyama wannan yarinyar hankali don yaga tanada rawar kai.Sa'eeda dai ta kafe Sadam da ido tana jiran ya bata amsa don ita tsakaninta da Allah tsoronsa take saboda taya zata kwaWa uban sallama amma ya kasa amsawa sannan ta shigo falon idanunta basu ga mutum ba sai yanzu kawai kamar diran mikiya tayi arba da mutum ya kakkafeta da mayun idanunsa kamar zai cinyeta,tsoro ne ya sake baibaye Sa'eeda ganin bai tankata ba saima cigaba da aikinsa da yayi,jakarta ta Wauka da sauri haWi da veil Winta tayi sama da gudu tana cewa

"A'uzubikalimatillahi tammat min shairi ma khalaa,koma aljani ne nafi arfinka da yardar Allah"

Da gudu ta haye sama kamar wacca aka biyo za'a kasheta,har bedroom Win Dr. Nabila ta shiga da gudu,shi kuma Sadam dariya abin ya basa,wai koma aljani ne,zako tasan aljani ne kuwa,cije lips Winsa yayi kaWan tare da taSe baki.Babu sallama Sa'eeda ta banko Wakin Dr. Nabila wacca a lokacin waya take da Abban twins,da sauri takai dubanta ga Sa'eeda wacca sai uban haki take sai kace tayi gudun kilometer 2,saurin sallama Dr. Nabila tayi da Abban twins duk da basu gama wayar ba tare da tambayar Sa'eeda hankali tashi

"Lafiya Sa'eeda kika shigo Waki da gudu? "

Kasa magana Sa'eeda tayi sai dai nuna ofa tana haki,ara tambayar Sa'eeda Dr. Nabila tayi,saida ta natsu hankalinta ya Wan kwanta sannan ta fara magana cike da tsoro

"Umm Ummm Aunty wallahi akwai aljani gidan"

Dafe irji Dr. Nabila tayi tana cewa

"Aljani fa kika ce Sa'eeda a gidan nan,wayyo mun shiga uku"

Dr.Nabila da shegen tsoro, itama nan da nan da rikice tana cewa

"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,yau munga takan mu ni Nabila,to ke a ina kika ganshi Sa'eeda"

Sa'eeda bata Soyema Dr. Nabila komai game da arangamar da tayi da Sadam ba a falo,dariya Dr. Nabila ta fara harda rie ciki au daman Sadam yana nan bai wuce kamfaninsa da yace zaije ba,dariya sosai Dr. Nabila tayi,ita dai Sa'eeda sheee tayi tana kallon Auntynta,to miye abun dariya a nan bayan ta sanar mata akan gamon da tayi a falo,sai can Dr. Nabila ta ce

"Look Sa'eeda cousin Winki ne fa Sadam,Mominsa ce ta take tare da Ummanki a India,so calm down ok,yazo ne duba companies Winsa ne a nan Kaduna don yaga meke tafiya a ciki,daman ya ce duk ran da ya shigo Kaduna zai tako har wurinmu nida Uncle Win don ziyara,so kwantar da hankalinta Sa'eeda, miskili ne Sadam na ajin arshe,yana sane ya tsorataki wallahi,ni nama zaci a wuce yaje ya dawo ashe bai tafi ba"


Wata nauyayyan ajirar zuciya Sa'eeda ta sauke,yanzu hankalinta ya kwanta ba kamar Wazu ba,amma kuwa ya matuar firgitata sosai,Allah ya isa tsoran da ya bata,tana cikin wannan tunanin haWi da takaici Dr. Nabila ta katseta da cewa

"Jeki watsa ruwa yanzu,favourite food Winki yau akayi "

Murna Sa'eeda ta somayi jin favourite food Winta akayi wato jollof Win taliya da kifi wayyo daWi ,da sauri ta wuce Wakinta,wanka tayi tare da shiryawa cikin rantsattsiyan atamfarta wacca tasha adon stone sai uban walwali take,mai kawai ta shafa sannan ta fito zuwa downstairs,koda ta fito ta zaci zata haWu ta wannan Wan rainin wayon wanda ya tsorata ta Wazun,don tasa aranta wallahi saita zazzaga mishi ruwan masifa da bala'i amma haarta bata cimma ruwa ba don baya nan.(Toooo,my esteem fans ku tayani dubawa yaushe Sa'eeda ta koma masifaffa, oh ni indo!!!>>>===).

Direct ta wuce kitchen tare da zubo abinci sannan tazo falon ta zauna,kunna TV tayi sai ta fara cin abincinta cikin natsuwa,sai a sannan ne taji shigowansu Kauthar,twins da mai aikinsu Jamila,ashe basa gidan haba no wonder shiyasa taita kiransu Wazu basu amsa ba.Direct uwar rigima Kauthar tayo kan Sa'eeda da gudu tana cewa


"Oyoyo Aunty Sa'eeda ina chocolates dina"

Rungumeta tayi tare da cewa

"Yana Wakina,ai Wazu inata kiranku kuzo ga promise Win amma shiru"

"Uncle Sadam ne ya ce Aunty Jamila da driver sukaimu shopping shi yanzu baida lokaci daya yaje damu" cewar Jawaad


Ras! irjin Sa'eeda ya bada,ita ta rasa koda sunan wannan aton taji sai gabanta ya faWi why!!! Oho ila tsoron daya bata ne Wazun,zama sukayi tare da nuna mata abubuwan da suka siyo suna murna,suna cikin nuna mata ne saiga Dr. Nabila ta sauko daga upstair tana zuwa cikin falon,zama tayi kusa dasu tana cewa

"Oh ni Nabila! Ku bari ta kammala cin abinci kafin ku fara mata shirmanku mana!!! "


Murmushi Sa'eeda tayi tare da cewa

"Ba komai Aunty,suna nishaWantar dani da surutunsu,i'm happy seeing them next to me always"


"Ai gaki ga su,kwayita shirman tare ai"

Haka suka cigaba da hirarsu sai can sukaji tsayuwan motoci,ai da gudu twins da Kauthar sukayi waje suna cewa


"Oyoyo Uncle Sadam! Oyoyo Uncle Sadam"

Har wurin parking Win motoci suka je da gudu,bai gama fitowa daga motan ba suka rungumeshi suna murna,shima ara rungumesu yayi don yana da masifan son yara,shiyasa yake sake musu fuska,shifa murmushinsa ko dariyarsa a wuri biyu ne kawai kake gani,kodai yana tare da Mominsa ko kuma yana tare da yara,a nan ne zakaga dariyarsa sosai.haka ya rio hannunsu suka dugunzuma cikin

Please Login or Register in order to submit comment