Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a can Sadam ya tsantsara gidansa na keca raini,furnitures Win da Uncle Hassan ya mata a gidan aka saka,a kwana na hudu su Sa'eeda suka dawo Kaduna saboda clearance Win da ake na masu bautar asa akwai wanda tayi missing batayi ba,daman ko lokacin da Sadam ya kammala karatunsa baije camp ba,maudan kuWi ya biya sai kawai yake zuwa clearance wanda ba koda yaushe ba.


@@@@@@@@@@@@



*KADUNA*


Sai wurin 5:13pm na yamma suka iso Kaduna,direct suka wuce unguwansu wato Miloniyan City,akwai mai gadi a gidan tare da mai bama flowers Win gidan ruwa,tun a corner da zata sadasu da layin mai gadi ya wangame gate saboda aran jiniyar da yaji,tsayawa yayi shi da mai bama flowers ruwa suna jiran uban gidan nasu,danno motocin sukayi cikin gidan,da sauri su mai gida suka nufi inda motocin suke,fitowa sukayi daga motar tare da gaisawa da mai gadi da mai bama flowers ruwa,nufa ofar gidan sukayi kasancewar akwai key Win gidan a hannunsu,bayan sun buWe suka shiga ciki,akwai ura a falo dama gidan baki Waya,haka Sa'eeda ko hutawa batayi ba ta fara gyaran gidan,ko'ina da ko'ina sannan da Wora musu girki da yake akwai kayan abinci a gidan sai dai nama da vegetables nd babu wanda driver yaje ya siyo,Sa'eeda ba ita ta kammala gyaran gidan da girki sai wurin bayan Isha'i,duk ta gaji gashi kwanan nan wata iriyar kasala haWi da yawan bacci ke damunta,da wuri take bacci tunda suka iso Nigeria.

Jollof Win taliya da abarba juice tayi musu haWi da fruit salad,bayan Isha'a Sadam ya dawo daga masallaci wanda yake a cikin gidan nasa ya zauna suka ci abinci,ba'ayi minti goma da kammala cin abincinsu ba Sa'eeda ta Singire nan da bacci,mamaki ya cika Sadam kwata-kwata arfe nawa ne yanzu da zata yi bacci,shifa yaga tunda suka dawo Nigeria take yawan bacci babu gaira dalili.

TattaSata yayi yana kiran sunanta

"Sa'eeda Sa'eeda"

Cikin muryar bacci Sa'eeda ta amsashi da cewa

"Ummm Ya Sadammm"

"Baki da lafiya ne my darling star"

"A'a bacci nake ji Ya Sadam"

aukarta yayi zuwa sama ganin baccin na idonta,tare da kwantar da ita.Sati biyu da dawowansu suka je gidan Umman Sa'eeda da Dr. Nabila acan suka wuni sai dare sannan suka dawo gida.

Washe gari suka shirya zuwa Kamfani shida Sa'eeda domin gabatar da Sa'eeda a matsanin *CEO* Win Kamfanin, daman Mukhatar ya sanar da zuwansu.Motoci Uku suka jeru zuwa Kamfani,Sadam da Sa'eeda suna a mota Waya tare da Mukhtar a gaban mota,gabansu motan bodyguards ne haka bayansu motan bodyguards ne,haka suka nufi kamfani da jiniya.

A can Kamfani kowa na tsaye a harabar Kamfanin suna jiran isowar *CEO* Winsu,kowa da kowa ya hallara,mazansu da matansu,ga manager Sauban da sauran ma'aikata duk sun hallara,matan wurin sai zumuWi da zuba ido suke saboda ganin wacca mai gidansu ya aure,wace ce wannan wacca ta cire tuta haka.Kai tsaya suka danno cikin Kamfanin da gudu wanda har wurin inda ma'aikatan suke suka faka,da sauri aka buWewa Sadam ofar,wani bodygaurd ne zai buWewa Sa'eeda murfin ofa Sadam yayi saurin dakatar dashi,da kansa yaje ya buWe mata kowa a wurin na kallon ikon Allah,fitowa tayi daga motar tana sakar mishi sassanyan murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushin,bag Winta ta Wauka sannan ya rufe motar

"Ya Rahman!!! " cewar wata a cikinsu

Hannunsu suka sarafe dana juna suna takowa wurin da suke,sanye take da baar abaya wacca tasha adon stone masu yalli da kashe ido,a gaskiya Sa'eeda bata da makusa,gashi tafiyarta asar waje ta aro kyau da haske,fatarta sai glowing take irin skin Win mutanan China.(hmmmm mudai mun baza kunnuwa,ayya babu alamar tambaya a wannan ibar da hasken da Sa'eeda tayi kuwa===>>>)

Duk takun da Sadam da Sa'eeda suke yi daidai yake da tafiyar mugawan zuciyar Sauban,ya murza idanunsa yafi sau a irga saboda ya tabbatar ba mafarki yake ba,sannan ba gizau Sa'eeda take mishi ba,lokaci guda ya rikice,ga irjinsa sai faman dukan tara-tara yake bama uku ba, he can't just believe what his eyes are seeing,Budurwarsa ta komar matar mai gidansa,how will that on earth happen.(Hmmm saima kaji maasudin abinda ya kawosu====C=C=C)


Suna isowa wurin kamar ance Sa'eeda ta kalli gefan Sauban,karaf! Kamar magnet haka idanunsu ya sarafe,lokaci guda gaban Sa'eeda ya bada Dummmmm! Cikin rawar murya Sa'eeda tace...............




*Mu haWu a pages na gaba my Esteem fans don cigaba da karanta wannan chakwakiyar=C=C=C
'
'
'<<<*



*Ali yaga Ali,ga Sa'eeda ga Sauban hmmmm,akwai ura koya zata kaya???*............



*Shin su Iklima zasu samu mazajen aure kuwa,sannan Nusaiba zata warke daga yoyon kashi kuwa???*............


*Wai ina ar yaya mai susa,sannan su Gwaggo ladi zasu dawo birni kuwa???*...........



*Shin Umma Kande zata Samu lafiya ko kuwa a haukar zata mutu???*........




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=C=C=C,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions<9<9=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuWo muku new updates zafafa* <9<9=C=C=ؖ=ؖ<<<<=ؘ=ؘ==%=%=%=%=%



*Ina aunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* <<<<=ؖ=ؖ<9<9=C=C=ؘ=ؘ





*Daga alalamin*

=؍= *Narrnarhh Bukar* ==؍



*Comments and share =O=O=OFisabilillah*.


[6/3, 1:40 PM] Narnarhh Bukar:

< *NACINA YA JAWO MIN* <




*Narrnarhh Bukar*
( *The Amazing Pen*
')




*TASKIRA WRITER'S FORUM*
*T.W.F*



*WATTPAD*
https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends




*AREWABOOK*
https://arewabooks.com/book?=6615ba31404e6e2687888ab9



*TELEGRAM*
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk



*WHATSAPP CHANNEL*
https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y




*BOOK 2*


6 5 ----6 6



Suna isowa wurin kamar ance Sa'eeda ta kalli gefan Sauban,karaf! Kamar magnet haka idanunsu ya sarafe,lokaci guda gaban Sa'eeda ya bada Dummmmm! Cikin rawar murya Sa'eeda tace


"Mai idona yake ganemin kamar Sauban"

Mijinta adai yaji mai ta ce saboda bada arfi tayi maganar ba,da sauri Sadam ya kalleta alamun tambaya kashe masa ido tayi da cewa

"Zaka ji komai da zarar mun koma gidan da yardar Allah"

"Ok"

Duk wannan tattaunawar da sukeyi babu wanda a cikin ma'aikanta yaji mai suka cewa illa nuna Sauban da Sa'eeda tayi wanda koshi kansa Sauban Win bai san mai ta ce ba,Sauban kuwa tuni ya jie da gumi tsabar ruWu saboda abin yazo masa a bazata,taya hakan ta faru? How? When? Sauban da sauran ma'aikatan suka gaishe dasu cike da girmamawa shi Sauban Mai gidansa kadai ya gaisar tare dayi masa Allah ya sanya alkhairi,ganin Sauban bai gaida Sa'eeda ba yasa Sadam ya ce masa cikin cool deep voice Winsa

"Idanunka basu ga Madam bane,kowa ya gaisheta amma kai baka gaisheta ba"

Ras! irjin Sauban ya bada a zuciyarsa yana cewa 'What! in gaishe da Sa'eeda wacca nayi soyayya da ita a baya,a gaskiya girmana ya faWi idan na gaidat....' Katse mishi tunani Sadam yayi da cewa

"Manager naji kayi shiru what's going on in your brain"

Firgigit kamar wanda aka tsikara Sauban ya dawo cikin hayyacinsa tare da gaisheta duk da zuciyarsa ta yamaci yin hakan amma ya zaiyi tunda matar mai gidansa ce,cikin girmamawan dole ya ce

"Sannu da zuwa Madam,fatan kunzo lafiya"

Wani irin Wauke kai Sa'eeda tayi kamar bata ji gaisuwan da Sauban yayi mata ba,kuma sarai taji sa amsar ne bayi niyyar basa ba,Mukhtar ne yace ma Sauban

"Manager, Madam bata ji mai kace ba"

Wani tuuin bain ciki ne ya tasoma Sauban tare da zuwa masa daidai wurin *tantani-mawallatonsa* ya tsaya cak! Wallahi ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba Sa'eeda taji mai ya ce,kawai dai wulaanci take so tayi masa shiyasa tai amsa gaisuwarsa,cike da takaici haWi da Sacin rai Sauban ya sake gaidata da cewa

"Sannu da zuwa Madam, fatan kun zo lafiya"

"Lafiya"

Ciki-ciki tayi maganar wanda alilan ne a cikin ma'aikatan suka ji mai ta ce,Mukhtar ne ya ce ma Sauban su kaisu ko'ina na kamfanin saboda Madam Sa'eeda ta gani,babu musu ya musu jagora sauran ma'aikatan suka biyo bayan su Sadam suna take musu baya.Haka Sauban yaje dasu ko'ina na kamfanin tare dayi musu bayanin Sangarorin kamfanin, bayan ya kammala bayani ne sai suka Wunguma zuwa babban hall na kamfanin wanda ake meeting a cikinsa,daman tuni an gyara ko'ina,har kayan ciye-ciye an kawo saboda wata warya-waryar walima za'ayi duk da basu san maasudin taron ba,har Mukhtar bai san me Uban gidan nasa zai faWa a meeting Win ba,bayan kowa ya samu wuri ya zauna,Sadam da Sa'eeda suna a high table,Manager Sauban da sauran manyan ma'aikatan kamfanin suna a side tables,sauran ma'aikata da wasu securities haWi da cleaners suna a kujeru.Mukhtar ne ya mie tare da cewa

"Assalamu Alaikum an Uwa na wannan Kamfanin mai akbarkha"

Amsa masa sallamar sukayi sai ya cigaba da cewa

"Ina muku fatan alkhairi sannan Mai gidanmu,Sadaukin Uba,mai sharai kukanmu,CEO Alhaji Sadam Dauda Ghali Mai Nasara zai yi magana yanzu,don haka kowa ya kasa kunnansa dakyau wurin sauraron wani alkhairi yazo mana dashi"

Mic Win ya mia ma Sadam cike da ladabi haWi da anan da kai,amsa yayi sannan ya mie zuwa inda aka tanardar doyin magana,cike da izza ya taka zuwa wurin,cikin cool deep voice Winsa ya fara magana da cewa

"Assalamu Alaikum"

Amsa masa sukayi sannan ya cigaba da cewa

"Bazan Wau lokaci ina magana ba,saidai zan je kai tsaye akan maasudin taruwanmu a nan,haia inajin daWin yadda kuke tafiyar da Kamfanin nan mai albarkha,so yau nake ara muku wani albishir da Sabuwar *CEO* Winku wacca zata cigaba da jan ragamar wannan Kamfanin mai albarkha,My Darling Star Sa'eeda Sulaiman,na tabbata zaku ji daWin kasancewarta a matsayin *CEO* na wannan Kamfani,sannan kar kuga ita mace ce kuma tanada rauni ku kawo mata raini,idan na samu Waya a cikinku yana handama da babakere a wannan Kamfanin to ya tabbata lokacin barinsa wannan Kamfanin yayi,domin duk tsare-tsaran da nayi a baya dasu za'a cigaba da bi sannan zan dinga bibiyar komai na wannan Kamfanin,Fatan zakuyi maraba da Princess Wina Sa'eeda,My Darling Star zo ki gabatar da kanki"

Murmushi ta sakar masa mai sanyaya zuciya,shima ya mayar mata da martanin murmushi,ma'aikata dai suna ganin ikon Allah,soyayya a bayyane babu ko sakayawa,Sauban tunda yaji Sa'eeda ce yanzu mai kamfanin ya kuma rasa natsuwarsa,irjinsa sai dukan uku-uku yake,ga wani irin gumi na tsattsago masa a duk ilahirin jikinsa,komai ganinsa yake a bibbiyu,ga kansa na wani irin sara masa,koda Sa'eeda tazo zata gabatar da kanta miewa yayi tare da barin hall Win gaba Waya saboda zuciyar bazata iya Waukar wannan tashin hankalin ba,assistant manager ne ya biyosa yana tambayar ko lafiya, girgiza masa kai kawai yake domin bakin yayi nauyin da bazai iya furta komai ba a yan,zuciyarsa na ara masa zafi kamar *garwashin wuta* ,gashi yanzu daya ga Sa'eeda sai ya sake fama mikinsa,domin wata iriyar zazzafar soyayyar Sa'eeda ta taso masa wanda ma tafi na da,assistant manager ya shiga ruWu ganinsa a haka,sai ara tambayarsa yake ko baida lafiya ne ya kaisa asibiti,a nan ba girgiza masa kai yayi da a'a,sai kawai ya masa alamar ya koma ciki,babu yadda assistant manager ya iya haka ya koma cikin hall Win.Wurin parking Win motoci ya je tare da shiga motarsa,zama yayi yana Wora kansa a sitiyarin motar,abin duniya duk ya ishesa,komai ya tsaya masa cak! wawalwarsa ta daina basa haWin kai,ya rasa ina zai je yaji daWi hankalinsa ya kwanta,idan ya je gida wani sabon tashin hankali ne domin ganin Maryam kawai zai ara saka shi wata sabowar damuwa domin ita ce silar rushewar farin cikinsa,da yanzu ya auri Sa'eeda mai hankali da natsuwa yanzu kuma tayi mishi nisa,fita yayi daga duniyarmu zuwa duniyar tunani tare da nemoma kansa mafita,yana a wannan yanayin sai can zuciyarsa ta ambata masa *Captain Fu'ad* tabbas! Wurinsa kaWai ne zai je ya samu kwanciyar hankali da natsuwa,inda tun farko yabi shawararsa da bai samu kansa cikin tashin hankali da damuwa ba,jikinsa na rawa haka ya ciro wayarsa daga aljihunsa,scrolling contacts Winsa yayi har ya samo numban Captain Fu'ad kasancewar sun kwana biyu rabon da suyi waya,dailing numban yayi tare da karata a kunnansa,ringing Waya-biyu a na ukun yayi picking tare da sallama yana cewa

"Wata sabon gani angon Maryam da Khairat"

Bai bi takan zolayarsa ba ya ce

"Kana Kaduna ne"

"Eh jiya na dawo Lafiya naji muryarka sai a hankula"

Sauban saida yaja wani dogon numfashi tare da furzarwa sannan ya ce

"Ina fa lafiya Fu'ad komai na duniyar nan juyamin yake,a bibbiyu nake kallon komai,gani ni nan zuwa yanzu"

"Subhanallahi Sauban meke faruwa ne"

"Fu'ad komai ma ya faru,komai ya faru Fu'ad na shiga uku na lalace,everything is turning upside down,yanzu zan zo"

"A'a bara nazo na Waukeka yanzu,tunda baka cikin yanayin tui"

"No karka damu zanzo yanzu in shaa Allah"

Katse kiran yayi tare da murza key Win motar,da sauri ya finciki motar kamar ita tayi masa laifin, mai gadi da sauri ya buWe masa gate ganin yadda ya danno motar da gudu,Allah yasa mai gadin yayi saurin buWe gate da ina tunanin ta saman gate Win zaibi.(O'ohhh su Sauban hankali ya tashi===)

Gudu yake sosai a saman titi,mutane sai kallon motar suke ganin yadda mai motar yake sharar gudu kamar don shi kaWai akayi titin,nan da nan ya iso layinsu Captain Fu'ad kasancewar shima yayi aure bayan Sauban ya auri Maryam har ma matarsa ta haihu,ta haifi Wiya mace mai suna FaWima amma ana kiranta da Zahra.Tun kafin Sauban yazo gidan Fa'ud yake danna horn a jejjere,wasu masu gadin gidajen layin sai faman buWe gates suke a tunaninsu ko gidansu ne,a haka ya isa gidan Fu'ad yana danna horn,da sauri mai gadinsa ya buWe masa gate,ai kamar jira Sauban yake,da gudu ya danno motar cikin gidan har zuwa parking load ko kashe motar baiyi ba ya sauka tare da sassarfa zuwa falon gidan,koda yazo cikin falon ya tarar da Fu'ad a tsaye yana kai-kawo,zubewa yayi a saman kujerar falon kamar wani mara lafiya,da sauri Fu'ad yazo wurinsa tare da cewa

"Sauban what's going on,meke faruwa ne don Allah,na kasa natsuwa tunda ka kirani"

Bai amsa masa tambayarsa ba,saidai ya fara nuna bakinsa da hannu,yana cewa cikin muryarsa wacca bata fita sosai

"Rrruwa Fu'ad, ruwa zzzan shaaa"

Ai da sauri Fu'ad yazo Wauko masa ruwa a fridge masu sanyi har gora biyu,jikinsa na rawa ya amsa tare da buWe marfin,kwankwaWa ya fara yi ji kake wat! wat! wat! Saida ya shanye ruwan gorunan nan guda biyu tare da sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya.Fu'ad dai na kallonsa bai ce dashi komai ba yana jira natsuwarsa ta dawo masa kafin ya ara tambayarsa,Saida yakai kusan mintuna biyar a haka bai ce komai ba kansa na jingi ne a bisa kujera.Ganin hankalinsa ya dawo masa Captain Fu'ad ya ara tambayarsa da cewa

"Meke faruwa ne Sauban"

Shiru yayi bai bashi amsa ba saima sauke ajiyar zuciya da yake akai-akai sai can ya fara magana cikin kasalalliyar muryarsa da cewa

"Fu'ad komai ma ya faru,idan nace komai to komai nake nufi"

"Sauban ka fito fili kamin bayani ta yadda zan fahimceka,you are talking to me in a passive way how did you expect me to understand you and your problems Sauban"

Hannunsa yasa tare da yamutsa dumar kansa,da wani irin arfi ya buga hannunsa a saman kujerar tare da cewa

"Ya Salam,na shiga uku ni Sauban wai kasan wace ce *CEO* Winmu ya aure"

Da sauri Fu'ad ya girgiza masa kai,cigaba da magana Sauban yayi da cewa

"My Ex girlfriend ya aura *SA'EEDA* "

Da sauri Captain Fu'ad ya mike tare da cewa

"What!!!! Sa'eedan da na sani budurwarka ya aura,how comes that happen,Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Tabbas! dole ka shiga ruWu hadi da tashin hankali Sauban"

"Hmmmm Fu'ad kenan don ya aureta bashi ne tashin hankalina ba ko kuma matsalata ba,kasan mece ce babbar matsalar a yanzu? "

Girgiza masa kai Fu'ad yayi da cewa

"A'a Sauban"

Saida Sauban ya Wan nisa sannan ya ce

"A yau Win nan *CEO* Wina ya mallakama Sa'eeda Kamfanin da nake aiki a ciki *Halak malak* a gaban kowa"

" Meneeeeeee??????? You mean the whole of that your big and famous company belongs to her now!!! "

"Sosai ma kuwa,hmmm wai kasan a gaban kowa yake nuna mata *tsantsan soyayyar* da yake mata kuws,suna sakarma junansu murmushi kowa yana gani ba tare da jin kunyar kowa ba"

Shiru Fu'ad yayi yana tunani hadi da nazari,sai can ya kalli Sauban tare da cewa

"Kayya Sauban,kaga irin wannan ranar na gujan maka a baya,amma ka kasa fahimtana ,naso kayi hauri ka auri Sa'eeda saboda duk inda mace take to tabbas Sa'eeda takai amma sai kayi watsi hadi da fatali da shawarata,to yanzu fa! wa gari ya waya? Kai! Sauban,sakayyarta ce ta tabbata akanka gaida Maryam, ka manta rashin zaman lafiyarku tare da matsalolin da kuka samu kaida Maryam a zaman auranku har zuws yanzu,hmmm wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba *Alhakin* Sa'eeda ne ya kama ku tare dayi muku talala ta yadda bazaku taSa kwancewa ba,arin daWi sai ya ara Waukakata a samanku musamman ba kai Sauban domin babu abinda yafi tashin hankali haWi da ruWu ace *Budurwarka wacca ka yaudara a baya,ta zamo mai gidanka kuma mai faWa aji a kamfanin da kake aiki* mai yafi wannan asanci tare da tozarci,a gaskiya bazan Soye maka ba alhakin Sa'eeda ne ke Wawainiya dakai har da Maryam,domin kun cutar da Sa'eeda,kun yaudareta,kun saka cikin matsananciyar damuwa,kun ci amanarta kai da Maryam, to taya Allah zai barku Sauban!,kasani Allah baya bacci sannan baya yafe hakin wani akan na wani,har ila yau baya barin addu'ar wanda aka cutar ta tafi a banza,babu shamaki ga adduar wanda aka zalunta,Allah yayi ikonsa a kanku kaida Maryam"

Shiru Sauban da yayi yana sauraron Fu'ad, ko motsin kirki ya gagari yinsa,domin sai yanzu ya ara tabbatar da alhakin Sa'eeda ne ke bibiyarsu hadi da Wawainiya dasu shida Maryam,shiyasa tunda sukayi aure sun kasa samun zan lafiya kullum ciki rigima suke,ashe-ashe sun dade da *barin gini tun ranar zane* tabbas! Sunyi kuskure,kuskuran ma mai girman gaske gashi Allah ya saka mata akansu tun kan a Wauki shekaru masu yawa.Sauke ajiyar zuciya Sauban yayi sannan ya ce

"Fu'ad tabbas! Munyi kuskure ni da Maryam domin sai yanzu na ara tabbatar da alhakin Sa'eeda ne ke bibiyarmu tun sanda mukayi aure,har yau Win nan da Ubangiji ya ara ikonsa a kaina,tabbas! munyi kuskure,Allah mun tuba ka yafe mana"

"Sauban mafitarku a yanzu Waya ce idan kuna son rabauta sannan ku samu kwanciyar hankali"

"Mece ce mafitar Fu'ad"

"Dole kaida Maryam ku je ku roi gafarar Sa'eeda, domin idan bata yafe muku wallahi wallahi wallahi haka zaku dawwama Allah yana ikonsa akanku,amma idan kuka nemi yafiyarta to na tabbata *Allahu Gafurun Rahim ne* zai yafe muku in har ta yafe muku,sannan kuga canji a rayuwarku"

"Hmmmm hakane Fu'ad in shaa Allah hakan za muyi nida Maryam har gidanta zamu je da yardar Allah"

"Kaga yanzu sai ya zamo maka ishara,idan kaga wani zaiyi kurkure irin makamancin naka zakayi saurin nosar dashi akan illar hakan"

"Tabbas! Kuwa Fu'ad ai ni yanzu malami ne babba a wannan Sangaren"

"Allah kasa mu dace"

"Ameen ya Rahman, bara na wuce gida na Wauki Maryam zuwa gidansu yanzu"

Dariya Fu'ad yayi da cewa

"Sauban! Sauban! Sauban! Miye na gaggawa,what are you eating while na baka is falling down,ka bari zuwa gobe ku tafi la'alla yau idan kun je bazaku samesu ba tunda a Kamfani ka barsu"

"Eh kuma fa hakane,wallahi bazaka gane bane Fu'ad duk na agara naga na sauke wannan nauyin ko zan samu natsuwa a zuciyata"

"Yawwa,Allah ya Woraka akanta,yasa ta yafe muku,Allah ya shiga lamarinku baki Waya"

"Ameen Ameen ya Jabbar"

Sun Wanyi hira sannan ya Wauki motarsa ya nufi gidan domin a yadda yake bazai iya komawa wani kamfani ba,a haka ya iso gidan.Direct ya wuce Wakin Maryam domin tattaunar wannan batun,a lokacin Maryam na zaune ta saka plate agaba tana cin kallalabar da Khairat ta soya mata,don yanzu ba komai take iya ci ba,ga cikin nata mai shegen kwaWayi ne da yawan sakata amai duk tabi ta rame.Da sallama ya shigo Wakin,Wagowa tayi tare da amsa masa sallamar sannan ta cigaba da cin kallalaSarta,wuri ya samu kusa da ita ya zauna sannan ya ce


"Maryam ajiye plate Win nan a gefe,magana ce nazo da ita muhimmiya wacca tashemu baki Waya"

Jin ya ce maganar mai muhimmanci ce kuma tashafesu baki Waya ya sakata ajiye plate Win a gefe tare da maida hankalinta kacokar! Gunsa tana cewa


"Ina jinka Sauban"

Saida ya Wan nisa sannan ya fara magana


"Maryam munyi kuskure babba a rayuwarmu,kuskuran shi ne ya hanamu zaman lafiya da natsuwa a gidan nan,shi ya hanamu samun damar fahimtar junarmu har yanzu"


Shiru Maryam tayi tana nazarin wani kuskure ne haka babba da ya hana duk wa'innan abubuwan da ya lissafa,can ta ce


"Wani kurkure ne haka Sauban da ya hanamu duk wa'innan abubuwan daka lissafa"

Dafe kansa yayi domin har yanzu sara masa yake,kallonta ya Wanyi na an wasu sakwanni kafin ya ce


"Maryam munci amanar Sa'eeda! Mun mata zambo cikin aminci! Mun karya mata zuciya a lokacin da ta yarda damu! Mun wofantar da yarda da amintuwar da tayi damu! Maryam alhakinta ne yake bibiyar rayuwarmu tun bayan auranmu,ya hana mu duk abubuwan da na lissafa miki a baya,kinsan duk wa'innan abubuwan basu ne matsalarmu a yanxu ba! "

Tun lokacin da ya fara magana idanunta na kallon bakinsa ko iftawa batayi,wawalwarta na ara faWaWa mata maganarsa tare da taimaka mata wurin yin analysis Win maganar, a zuciyarta take cewa 'Ashe bani kaWai nake wannan tunanin ba harda kai,domin kafin muyi aure muna soyayyar mu mai tsafta amma daga auran mu shikenan soyayyar mu ta koma iyayya,kamar kowa na kallon hanjin Wan uwansa,bama zama wuri Waya ba tare da yin faWa ba...' Katse mata tunani yayi da cewa


"Kinyi shiru ko jikin ne"

Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana cewa


"Nima tunanin nan nake kwana nake tashi dashi,yanzu wani matsala ne haka wanda yafi wa'incan"

"Na tuna da maganar Sa'eeda da kacemin a lokacin da nazo Waukarki daga school kina amarya ta ce min "In shaa Allah sai Ubangiji ya Waukakata sama damu sannan zamu zo da kafafunmu muna roonta yafiyar abinda muka aikata mata* hmmm Maryam could imagine Mai gidana *Alhaji Sadam Dauda Ghali Mai Nasara* Sa'eeda ta aura"


"What!!! Mai gidanka Sa'eeda ta aura!!! How will that on earth happen!!! When? How? Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Ni Maryam na shiga uku!!! Sauban!!! Sauban!!! Yanzu Sa'eeda mai gidanka ta aura!!! "

"Hmmm duk wannan ba shi ne matsalar ba kuma hakan mai dameni ba"

"Sauban kana nufin wannan ba shi ne matsalar ba? To mece ce matsalar!!! Yau manga takanmu ni Maryamu"


Saida yaWan nisa sannan ya ce


"A yau Mai gidana kuma mijinta ya mallaka mata Kamfanin da nake aiki,daga yanzu Sa'eeda zata zama *CEO* din kamfaninmu"


Dafe irji Maryam tayi tare da waro idanunta waje tana cewa


"Ya mallaka mata Kamfanin da kake aiki!!! Shikenan ni Maryam maganarta ta tabbata akanmu,bakin da tayi mana a baya ya kamamu!!! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Yanzu ta Waukaka sama damu!!! Allah! Allah! Allah! Mun tuba ka yafe mana! Wayyo Allah! Tabbas! Zama bai gammu ba dole muje mu roi gafararta koma samu sassauci a zukatanmu"

"Hakan za'ayi zuwa gobe in shaa Allah, saidai bansan ina suke da zama ba"

"Ummm bara na tambayi aminiyarta Iman saita bamu address Win gidanta"

"Fine,Allah ya kaimu"

Mikewa yayi sannan yabar Wakin zuwa Wakin Khairat.

Washe gari da arfe 11:20am na safe suka nufi gidan Sa'eeda a Miloniyan City ta address Win da Iman ta turoma Maryam bayan tasha tambayoyi kafin ta bata don tabbatar da ba cutar da Sa'eedar zasuyi ba.Har gidan suka iso da taimakon address Win,fitowa sukayi tare da bin ilahirin gidan da kallo saboda tsarin gidan baiyi kama da gidajen da ake ginawa a Nigeria ba,idan kaga gidan zakayi tunanin a Dubai gidan yake saboda haWuwarsa,wanwasa ofar gate din sukayi tare da jiran a buWe musu,mai gadin ne ya buWe ofar yana kallonsu sama da asa tare da tambayar meke tafe dasu.Maryam ce tace


"Wurin Sa'eeda mukazo"

Daka mata tsawa mai gadin yayi da cewa


"Gyara kalamanki yarinya!!! *Ruwa ba sa'ar kwando bane!!!* Hajiya Sa'eeda zaki ce ba Sa'eeda ba"

Haia taji tsawar nan har cikin kwanyar kanta,shiru kawai tayi bata iya bashi amsa ba,Sauban ne ya ce


"Ayi mana afuwa wurin Hajiya Sa'eeda mukazo ka ce mata Sauban ne da Maryam matarsa"


Bai bashi amsa ba ya rufo ofar tare da tafiya zuwa ofar falon,danna alarm yayi sannan ya jira,kasancewar dukkaninsu suna falon bayan sun kammala break fast suna wasanninsu na ma'aurata sukaji arar alarm Win,tsaki Sadam yayi irin za'a katse musu jin daWinsu,miewa yayi zuwa ofar tare da buWewa,cikin Sacin rai ya ce

"Lafiya"

Cike da girmamawa mai gadin ya ce

"Ranka shi daWe wasu Saki Hajiya Sa'eeda tayi a waje,sunce ince mata Sauban ne da Maryam matarsa"


Ras! irjin Sa'eeda ya bada,mai ya kawosu gidanta kuma,hijab ta sako tare da zuwa wurin da Sadam ya tsaya tana cewa


"Kace Sauban da Maryam? "

"Eh Ranki shi daWe haka suka cemin"


Kallon Sadam tayi wanda shima itan yake kallo,duk da bayan dawowarsu daga Kamfani jiya ta sanar masa alakarsu da Sauban tare cin amanar da awarta Maryam tayi mata ta hanyar auran saurayinta Sauban duk babu abinda ta Soye masa,komai ta sanar masa,ce ma mai gadin yayi


"Kace musu su shigo,sannan idan sun shigo ka kaisu Wakin bai,zamu samesu a can"

Amsa masa yayi da

"To Ranka shi daWe"


Komawa yayi tare da buWe musu suka shigo cikin gidan,da

Please Login or Register in order to submit comment