Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

GIDAN GANDU
Biebee Isa
Hausaebooks
Creat:- Shuraih Usman

Ku shiga shafinmu na facebook domin samun wasu kayatattun littatafan ta hanyar bibiyar wannan
adireshi na yanar gizo www.fb.com/hausaebooks

GIDAN GANDU
1⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕
Tsaki Haneefa ta qara bugawa a karo na biyu,
yanzu mu kullum haka zata dinga samu latti?
Bilqeesu tace Aifah, inda sabo ai ya ci ace mun
saba, ta cika nawa, Hanifa tace wlh baxa ta sabu
ba, bari mu dawo daga makaranta wlh mu samu
Tsoho mu gaya mishi, Islahulkhair da ke gefen
su ba ta tanka musu ba, cikin damuwa Fadila
tace Mallam Audi donAllah ka qara mata horn,
kafin Mallam Audi ya qara Horn suka hangota
tana sauri cikin yanayinta na sayih ta fada cikin
mota qirar bus, Mallam Audi Ina kwana, ya

amsa mata cikin murmushi, tace kayi haquri
wlh banga Socks dina bane, yace ba komai shigo
muyi ta tafia kar mu bata wani lokacin. Ya ja
mota ya bar haraban wakeken gidan da ke
qunshe sashe sashe..
Kusa da Islahulkhair ta zauna gefenta Fadila ce
riqe da keypoint tana karatu, Ta ce hey Sisters,
sorry i kept u waiting, Fadila ta dago ta kalleta,
cike da zolaya tace Allah ya nuna mana ranar da
zamu daina jiran Maysah, kin cika nawa, tace
wlh banga safata bane ta kalli Islah tace yadai
sisi? Murmushi ta mata tace lafya u will never
change will u? Daria ta mata ta kama kunnenta
tace sorry, ta kalli su Hanifa da bilkis a gefe
tace duk ina kwananku, a tare suka buga tsaki
tare da hararta, ba ta damu ba don idan da sabo
ta saba. Mazan da ke zaune su hudu a chan baya
tace Whatsapp bro, daya kawai ya amsata
sauran 3 hararata sukayih. Ta kalli Na'imah da
bakinta ke sake tana jalalar da miyau tace
Nimcy a rufe bakin mana, kar ki bata gaban
hijabinki, cikin tsiwa nimcy tace anqi a rufe din,
sa'idawa masu bacci da ido daya, tace Allah baki
haquri ta ciro littafinta ta shiga dubawa don yau
suke fara NECO exams...
Jikokin Alhaji Musbahu Zailani kenan masu
rubuta Jarabbawar qarshe ta makarantar
Sakwandire na TopOnwards Science College
Maiduguri, Su 10 cif zasuyi graduation bana...
***************
Assalam Alaikum tsoho me ran qarfe, Tsohon
da ke zaune kan Sofa kyakyawan gaske ne,
kadan ya rage ya cika shekaru chasa'in cif a
duniya, tsufansa me kyau ne, gyara zaman
gilashisa yayi yace Hanifa ce da Balki? Eh mune,
amma bilkisu nake ba balki ba, yayi daria yace
ja'ira, ya jarabawar? Suka ce toh Alhamdulilahi,
duk suka yi shiru, Tsoho yace me bakin shan
qwai menene? Naga magana a bakin ki, Hanifa
ta zumburo baki, tace kaga dai tsoho ka bar ce
man me bakin shan qwai, yace toh ai naga kun
kasa magana, ku fada matsalarku a magance
maku ita, Ke Me Gadon zinare menene? Bilkisu
tace daman Tsoho qara muka kawo ma,
Haneefa tayi charaf tace tsoho mu dai mun gaji,
wao kullum sai Maysah ta samu latti, gashi mun
fara jarabawa, wlh idan bamu bi a sannu ba
wata rana sai an hana mu zana harabawa saboda
latti, Mu gaskia da sakel, a san yadda zaayi
damu, ko a sama mata me kaita ta qarata chan
da lattin ta, Tsoho yayi jimm yace kuyi haquri,
kunsanta da Nawar tsiya, zan mata fada, amma

maganar raba tafiya duk bata taso ba, tun
lokacin yayyunku da sukayi aure tare ake kaisu
makaranta kunga lokaci guda ba za a bar
wannan qaidar ba, Hmm ai daman munsan baka
san laifinta ka fi sonta cikin jikoki, da sauri yace
haba yan jikoki na, wlh duk daya na dauke ku,
ku bari zanyi shawara da iyayenku, ku saurareni
kunji? Sukayi godia suka mai Sallama.
*******
Ta kalleshi tace Tsoho tunda nagama karanta
ma Jaridar bari naje nayi karatu dukda bamu da
paper Gobe sai Jibi, yace RUMAISA'U Meyasa
kike sa 'yan uwanki latti? Kullum ke kadai suke
jira, ko so kuke a hanaku shiga makarantar! Duk
cikin lallabi yake mata magana, ta yi raurau da
fuska tace, kayi haquri InshaAllah zan daina,
yauma don safata ta shige wani gurin ne ai da
bansamu latti ba, yacr donAllah ki daina kinji?
Tace InshaAllah, yace yauwa idan kin shiga cikin
gida ki kiramin Hajia Babba, tace toh Tsoho ta
miqe ta fita, a ranta tace InshaAllah sai na riga
kowa shirin makaranta jibi, ba za a qara jirana
ba sai dai na jira...Tayi Sassan Matan tsoho
domin kiran Hajia Babba, da Sallama ta shiga
dakin Hajia babba ce da Abida (Maman Hanifa)
a dakin, suna ganinta sun ka bata fuska, ta gaida
su ba wanda ya amsata, tace Hajia Babba tsoho
na kiranki, ba ta jira ta ce komai ba, ta fice don
bata son jin zagin da za a jefi kakar ta dashi ba.
Anty Abida ta buga tsaki tace jikar Mayu kawai.
Hajia Babba taja tsaki tace wanda suka gaji tsiya
game da miqewa don ansa kiran mijinta Tsoho.
*******
Gidan Alhaji Musbahu Zailani, wanda yan
unguwa da sauran mutane ke ma laqabi da
GIDAN YAWA, gida ne katon gaske gari guda ne,
me qunshe da sashe sashe, su biyu kachal
mahaifan su suka haifa, shida Qaninshi me suna
Rabi'u iyayensu asalin yan qasar Chadi ne yan
Shuwa Arab, Shekara 2 kachal ya ba qanenshi.
İyayensa sunyi hijira zuwa qasar Nigeria garin
Maiduguri inda suke sana'ar sirfani da
dinki,Bayan Rasuwan Mahaifansu Musbahu ya
rungunmi qaninsa suka cigaba da wannan
sanaar dinki, har Allah ya buda musu, sun samu
İlimi me inganci na arabi da boko. Kafin suka
fara habaka Sanoin su ta wani sigar.. Har suka
zama matasan Attajirai.
A kasuwan da suke Sanaarsu, Akwai Wata
yarinya Karime da ke kawo musu tallan fura
fura, yau da gobe ya sa suka saba da Musbahu
har suka fara Soyayyah, ba ayi wata wata ba ya

kai gaisuwa gun iyayenta, yace ba su da kowa a
Qasar nan sai qaninshi. Mahaifin karime yace
bakomi an bashi karime, ana haka ne diyar
kishiyar Maman karime ta shigo daga tallan
Goro, ta gaidasu, Baban yace sannu Hajjo kin
sha rana shiga kan kabad ki dauko samira na
nan da abinci kici tace to, Rabiu ya bi bayanta da
kallo chan yace Baba wannan fa? Yace hajara
kenan, qanwar Karime ce, amma ba uwarsu
daya ba, uwarta ta rasu, sukace Allah ya ji
qanta, Baban ya miqe yace ina zuwa, ya shige
ciki, Musbahu ya lura Akwai magana bakin
qanenshi, yace yaya dai Rabiu? Yace Yaya
wannan yarinyan ta man, bansan ko babanta ze
ban ita ba, Musbahu yace bari yazo a kwatanta
daman gwara kayi auten kaima, ko da baban ya
dawo Musbahu ya sanar dashi buqatar qaninsa,
Mallam yayi shiru yace baqi taku ba, amma
Hajjo bata da kowa sai Allaj sai ni, Hajjo tasha
wahalar kishiyar uwa, ta na kan sha, Zan baka
hajjo amma sai kayi man Alqawarin cewa zaka
riqe man ita da amana, da sauri Rabiu yace
wallahi na amince baba, zan riqe maka ita da
amana. Yace toh shikenan na baka ita bayan Sati
2 kuzo a daura aure. Sunyi murna gaba ki dayan
su...
*******
Da daddare Mallam ke gayama maman karime
yadda sukayi da meson Karime, murna fal
ranta, Allahu Akabar, ashe zan ga Auren Karime
nah, kai madalla madallah, yace ai ba auren
karime kadai zaki gani ba, harda na hajjo, take
Annurin fuskarta ya dauje dif, tace bangane ba,
yace Qanin Musbahu ke son Hajjo kuma har na
bashi ita, maman karime ta daka tsalle ta re da
riqe qugu tace Kam babban balaeen chan....
2⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Sai kuma ta
fashe da kuka, yanzu mallam ni zaka tona wa
asiri? Eyi? Yace bangane tona miki asiri ba, dan
ka ga ba ni na haifi hajjo ba shine zaka aurar da
ita ko neman shawara bakayi? Ynx idan tayi
aure wazai na kai mun talla? Ko ni kakeso na
fita tallan da kaina? Takaici ya hana mallam
magana sai kawai ya fice ya bar dakin...
*****
Tadihn su sukeyi irin ta masoyan da, Hajjo ta
shigo da Sallama a fuskarta, Musbahu ya amsa
da murmushi, yace Amaryarmu, nan da nan
karime ta hada gabas da yamma, tace wato
Rabiu ba xai janye ba koh? Me zaayi da wanda
ba a san asalinsu ba? Hajjo ta shige cikin gidan
da sauri tana matsar qwallah, Musbahu ya bata

rai yace haba karime me yasa kike haka neh?
Sai kace ba Mahaifinku daya ba? Charrr uban,
Allah ya sawwaqe, daman wayace ma baban mu
daya? To tsaya kajih yanda abun yake, da ita
kishiyar maman mu ta shigo gidan nan, Agola
ce, kuma da ta rasu, shine babana ya riqeta, ni
kadai ral mahaifana suka haifa, Musbahu yace
najih dai, be kamata kina nuna qyamarki gareta
a fili ba, ko kina kishi ne don ta fiko kyau, wani
mugun ashar ta lalayo ta dinga zage zage da
qyar ya lallabata tayi shiru. Ya shaida mata gobe
zasu je Chadi don sanar da kawunninsu auren
su, ta mai Allah ya kiyaye
******
Ko da Su Musbahu suka isa qasar Chadi suka
tarar da Kanin Mahaifinsu Ya rasu me dakinshi
batafi wata 2 ba itama ta rasu, Musbahu ya kalli
Rabiu yace kaga Rabiu inaga mu tafi da su
Mudassir da labaran Nigeria, yara ne ba su fi
shekaru 10 ba su da kowa yanzu sai mu, yace
Yaya duk yanda kace hakan zaayi...
Haka kuwa akayi Washegari suka kama hanyar
Nigeria. bayan kwana 2 aka daura auren
Musbahu da Karime, da kuma Rabiu da Hajjo.
Dan madaidaicin Gida ya kama musu, suka
zauna tare da yanuwansu Labaran da Mudassiru,
Musbahu yace Karime ta riqe su, fir taqi ita
bazatayi bautan yara ba tun kafin ta fara samun
nata, haka Rabiu ya kwashe su ya kaima Hajjo
su, ta amshe su hannu bibiyu.
*****
Bayan Shekara daya.
A daddafe ta szuwa ta kai kanta bangaren
Karime, kuka takeyi tana kiran Yaya ki
taimakeni, bayana zai balle, Karime da ke zaune
tana tamnar cingam ko kallo bata isheta ba, nan
Hajjo ta xube tana murqususu, amma karime
bata ce mata ci kanki ba, Tunda Hajjo ta samu
ciki Karime ta ji wani tsanarta ya shigeta, jin
haushinta daya ya zaayi hajjo ta samu ciki? Ita
bata samu ba? Ta sha kai ma cikin hari tun yana
qarami amma bata samu nasara ba, Kishinta
takeyi Sai kace kishiyoyi, ta dinga juyi a qasa
amma ko kallo bata samu ba daga karime,
maqociyarsu ce Umm Afeef ta shigo gidan da
Sallama, ganin hajjo a qasa yasa ta qarasa gunta
tana sallami, me ya sameki haka? Ko naqudar
ce? Sannu, ta kalli karime tace kedai bakiji
dadin rayuwarki ba, wai shin mini daya kuke
aure da zaki nuna mata wannan halin ko in
kula? Karime tace Maman Afeef wlh ki fita
idona zamu kwashi yan kallo dake. Cikin

wahalaliyar muryan hajjo tace umm afeef
marata, bayana, ta fita da gudu tana fadin ina
zuwa Bata tsaya ko ina ba sai gidan Unguwan
zoman garin Ummu Anisa, ta ce ki temaka
haihuwa tazo ma hajjo, ai ko da gudu suka fito
suka nufa gidan, har ynx hajjo na qasa ta na
mutsu mutsu, maman Anisa tace kamata
mukaita ciki, Karime tace Waaa? Ai wlh ba zaa
shiha da najasa dakina ba, ummu Afeef ta buga
tsaki tace in fitsari banza ne, kaza ma tayi,
Ummu anisa tace rabu da marar tausayin nan
kamata mu kaita bangarenta, nan suka bar
karime na ta zazaga masifa. Suna ko shiga daki
Hajjo tayi wani yunkuri ta santalo danta, Kai
Masha.. Maman afeef ba ta rufe baki ba sai ga
wani dan ya fito, cikin murna tace Yan biyu-- sai
ga wani dan ya kuma fitowa, Guda maman afeef
ta sake da qarfih, ummu aneesa sai sannu take
ma hajjo, kafin aka gyara hajjo. Da yaranta
maza kyawawa kamar babansu. Ummu Afeef ta
fita waje da sauri taga karime na labe tana
leqe, ummu afeef tayi shewa tace samun Yan
uku sai 'yar baiwa, Karime ta dafe qirji tace na
shiga uku, Yan uku? Maman afeef na fita ta
samu almajiri kayi maza kaje kasuwa kace ma
malam Rabiu hajjo ta haihu ta samu yan uku.
Da gudu almajiri ya ruga.
Karime kuwa kamar tayi hauka, sai sambatu
take tayi, Hajjo ta haihu? Ta samu yan uku?
Kuma maza? Jar ubanchan, wlh bazata sabu ba.
Da balaee nima sai na haihu cikin watan nan
hka ta dinga haukanta...
Da gudu Rabiu da Musbahu suka shigo gidan,
kallo daya zaka musu zaka san suna dauke da
tsantsar farin ciki, Hajjo har tayi wanka tayi
kyau abunta, Rabiu ya kwaso yayan ya rungume,
ya miqa ma yayanshi, Musbahu ya amshesu
tare da musu addua, Allah shi rayaku.. Nan
ummu aneesa tace a bar hajjo ta samu bacci,
Yan gidan kuwa Labaran da mudassiru sai
murna suke tayi Nene Hajjo ta haihu.
Musbahu ya shiga cikin Gidanshi jiki na rawa
yake ta qwalawa Karime kira yana Karime
karime, Hajjo ta haihu har daki ya bita yana
gaya mata, Yan uku ta samu, kuma duka maza,
Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, shi be
ma lura da yanayinta ba, yace wai baki san hajjo
ta haihu bane ba? Cikin tsawa da masifa tace
Tou Sai Me? Ya dan kallota, karime lafiya? Ta
miqe tace ita ta kawo hakan, ta sabi zaninta ta
bar gidan, shiko Musbahu tunani yake me yayi
zafi haka?

***Rannan suna Yara sukaci suna Hassan
Hussaini da Gambo, Yaran nan abun so ne gurin
Jamaa, har yau Karime bata leqo ta gansu ba,
Rabiu wani kuka ta musamman yake ba
matarshi, Hajjo na shan wahaln yan ukun nan,
ba wanda ke tayata da rainonsu, sai Mudassiru
da Labaran, ganin hakan ne Karime ta sami
Rabiu da kuka wai ita dai a bata mudassir da
labaran, ita tana cikin kadaici, waye waye, Rabiu
be ce komi ba yace su koma gun karimen,
Musbahu ya so tambayar ba a si kawai sai ya
share. Karime ta cigaba da riqonsu don kawai
kar Hajjo ta moresu, a hankali a hankali ta
dinga chusa masu tsanar Hajjo.
*******
Abu na Allah cikin Shekaru yaran hajjo 6 har
da yanuku kasancewar duk shekara take
haihuwa wani abun Allah yaranta duka maxa,
Bayan Yan uku ta samu Ahmad da Ibrahim, sai
auta Hafiz har yau Karime ko batan wata ba ta
taba yi ba, an bi Malaman anbi yan tsibbu da
bokaye amma a banza. Musbahu na san Yaran
Yanuwansa sosai, ya sa yan uku da Amad
makaranta Islamiya..
***
A bakin kogi me kallon boader ya hango er
yarinya na kuka gashin kanta ya rufe mata
fuskarta da sauri ya qarasa yace ke me akayi
maki? Dago kanta tayi Ya Salam!! Aljana ce ko
mutun? Cikin hausarta da be fita tace wlh
mutun ce ni, ya sunanki? Sunana Aishalle daga
ina kike? Masu kamen bayih ne suka kamo mu
shine ni na gudo nayo nan, ke er wace qasa ce?
Tace kamaru, yace ina iyayenki? Ta matse
qwallah tace sun rasu da dadewa, yace ta shi na
siya miki abinci, na saki kwalekwalen da zai
kaiki har kamaru, da sauri ta girgiza mai
kai,Tace wlh ba zanje ba, banda kowa a chan,
bauta mukeyi a gidan sarki, kuma na gudu da na
koma zaa fille mun kai. Ka barni a nan kawai,
Musbahu ya tausaya mata qwarai, yace zakije
gidana? Da sauri ta daga mai kai, yace toh biyo
ni, ba gaddama ta bishi, sunyi tafiya kadan kafin
suka isa gida, tun daga soro yake qwala ma
karime kira, ta fito, kai mallam ya kake kwala
man kira kamar wani watan ramadana-- turus ta
tsaya ganin Alajana da gudu tayi daki ta na fadin
bayanka Musbahu bayanka Aljana, yayi daria
yace keee mutum ce, ta dan leqo tace daga ina?
Ya kwashe komai ya gaya mata, shine nace ta zo
ta xauna a gidan nan, Ashar ta saki, Wannan
Alajanar zata zauna dani? Wannan Mayyar? A

gidan nan? Wlh ba dai gidan nan ba, Musbahu ya
fusata yace Gidan ki ne ko nawa? Toh sai ki
hanata xama gidan nan idan kin isa.. Zuciya ta ci
karime ta daka tsalle ta damqo gashin Aishalle
Add 3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 GIDAN GANDU💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Aishalle ta sake
ihun wahala, Musbahu ya chapko karime ya
hadata da bango, ya ja hannun Aishalle yayi
waje da ita, karime na kwance kasa amma
bakinta be daina furta zagih da batanci ga
Musbahu ba, Wurin Hajjo ya kaita, tayi sauri fa
lullube jikinta da zanih, yace hajjo ga yarinya
nan danAllah aba ta abinci kuma tayi wanka a
bata kaya, Hjjo tace toh Yaya, Yace Aishalle ki
saki jikin ki, ba abunda xai sameki anan, ga
qanwata na zata kula da ke kinji? Aishalle ta
gyada fuska,usbahu ya sakai ya fice,Hajjo tace
zonan kinji qanwata? Aishalle ta matsa kusa da
hajjo tana dari Dari don ta tsorata da alamarin
karime, Jan hannunta tayi ta kaita har daki, ta
zubo mata faten doya ta bata, sosai taci abincin
nan. Sannan ta bata kaya ta sata tai wanka.
Kwanan Aishalle 5, ta sake da hajjo da yaranta,
ita ke kula da Hafiz auta, wanka da wanki, haka
kuma zata tasa su Hassan gaba tayi ta basu
tatsunniya, kullum Musbahu Sai ya shigo ya ga
ya take, Duk zaton karime Aishalle bata gidan,
don ba shiga sassan hajjo takeyi ba balle ta
ganta. Kuma ta hana su mudassir shiga balle su
kawo mata rahoton gulma.
Wasa wasa har Aishalle ta samu wata 2 a gidan
Rabiu, tayi clean ta qara wani irin kyau me
firgitarwa. Kuma tana son yaran Hajjo har
ranta, da taimakon Hajjo Aishalle ta iya abinci
da wasu gyaran da ya kamata ace mace ta iya.
Haka suke zaman su cikin aminci da yarda da
juna..
******
Yaya kana ganin karime baza ta bamu matsala
ba? Musbahu yace Rabiu ni ba raggon maza
bane, na isa da gidana, Kuma bawai zan auri
Aisha bane don na ci mutuncin karime sbd bata
haihuwa ko wani abu, aa zan auri Aishalle ne
don ina matuqar sonta kuma dan raya sunnan
manzo. Rabiu yace toh shkn Allah shi sa a dace..
Hajjo ce ta ma Aishalle bayani, tace Mamman
Hassan ba wai zan muku musu bane, amma
wallahi ina tsoron matarshi, hajjo itama cikin
damuwa tace kar ki damu kowa da halinsa zai
zauna. Allah dai ya sa mu dace..
Yau ana sallahn jumaa aka daura auren
Musbahu Zailani da Aishalle, bisa sadakin
silallan zinari 5, Hajjo ta gyara Aishalle, da

daddare Musbahu ya shigo Sashen qaninshi
yace ma Hajjo ta shigo da Aishalle sashen
karime zai hada su, sai da gaban hajjo ya fadi
kafin tace toh Yaya ga mu nan zuwa. Wuce wa
yayi sashen karime, tana xaune ta na shan rake
ko Isha'i ba tayi ba. Mallam sannu da zuwa, tace
yauwa karime rake ake sha, e wlh zaqin tsiya
kana sha? Yace aa, yo daga ina kake haka sai
uban qamshi kake zubawa, rabon da na ganka
tun safe? Kafin yace komai su hajjo suka shigo
da sallama ya amsa, karime tace wai meye? Da
daddaren ma ba za a barka ka zanta da mijinka
ba? Hajjo dai bata ce komi ba, Aishalle kuwa
gabanta ya tsanta bugu, hajjo wace ce wnnan sai
noqe noqe take kamar manahuka? Musbahu
yace Karime, tace naam mallam, zaki tuna
fuskar nan? Hajjo bude mata fuska, Hajjo ta
bude mata fuska, karime tayi zumbur ta miqe,
oh Allah Musbahu wai kai ina kake samo aljanai
masu tsigar mayu! Haka kwanaki ka kawo wata
mayyar, ai gwara wanchan akan wannan!
Wannan ai kynta ya shahara, danAllah kiyi
haquri baiwarAllah, ai kuma Allah ya hallice ku
Duk da bansan me mijin nawa ya miki ba amma
kiyi haquri, ta ba musbahu daria sai da ya dan
dara, yace Karime wannan ce na kawo miki ita
kwanaki sunanta Aishalle, kuma a yau ta zama
matana saboda na aureta, Karime ta daka tsalle
ta chakumo wuyanshi,/Ni zaka munafurta ni
zaka ci ma amana? Idan ka isa Allah ya tsinen,
babban balaeen chan, sai ta sakeshi ta wawuro
sandan rake ta maula wa hajjo a baya, hajjo ta
gantsare baya, ta yo kan Aishalle, yau sai na
daddaki kashin babba buraubaki, Cikin zafin
nama musbahu ya damqota ya jefar ya nuna ta
da yatsa, karime ki kiyayeni karime ki fita
idona, ta yo kanshi ta chakume shi, na rantse
yau sai ka sakeni idan baka sake niba ba ka
haifu ba, wlh sai ka saken, yace karime na sake
ki saki daya, ihu ta sake da qarfih tace na shiga
uku, daman basona kqke ba? Shege tsinanne
laananne, ta figi zanenta ta bar gidan da gudu
ko tsoron dare bata yi.
Ya kalli Hajjo tace Hajars kiyi haquri ni na
jamaki ko? Tace bakomai Yaya, yace nagode ki
jeki wanke fuskanki kar ki sa su hassan damuwa
tace to yaya nagode sai da safe, Aishalle Allah
ya tashe mu lafiya.
****
Bayan Wata Biyar
Zama suke cikin so da qaunar juna, abu na Allah
Aisha na dauke da cikin Wata 4, Hajjo na kula

da ita sosai, su Hassan na sonta Goggo Amarya
suke ce mata, Hafiz na ce mata Goggo Ama sbd
shi yana da tsamin baki, haka kuwa kowa ke ce
mata Goggo Ama, su Mudassir kullum suna
gidansu karime suna kai mata rahoton abun da
ke wakana cikin gidan, ta dau alwashin raba
Aishalle da gidan nan amma bokanta ya shaida
mata Aishalle ba zata taba barin gidan nan ba,
kuma ya hango yaranta da jikokinta cikin
wannan gidan, kuma duk wanda Musbahu zai
aura a bayan Aishalle yake don sonta a cikin
jininshi yake, Hankalin ta ya tashi ainun, babban
baqin cikinta be wuce yanda Musbahu yayi watsi
da ita, a tunanin ta zaizo yace a maida aurensu
amma shiru, gashi uwarta ta rasu, abinci ma
gagaranta yakeyi, haka ta samu babanta tana
kuka tace sai dai yaje ya ba Musbahu haquri a
maidota, yace shifa ba inda zaije, ba zata
maidashi tsohon banza ba Nan ta fashe da kuka
tana tirje tirje, don yaga uwarta ta rasu shisa be
damu da ita ba, ya fi son hajjo, duk da Hajjon
ba diyarsa bace, tsakanin da da mahaifi sai
Allah, zuciyarsa ta karaya, yace zai ma Musbahu
magana. Da kanshi yaje kasuwa gurin Musbahu,
Musbahu yace haba baba ai da ka aika an kirani
yace bkmi, nan ya gaya mai abunda ke tafe
dashi, ya danyi jimm baba yace idan baka so
dole ta haqura bawai ina maka dole bane, yace
lahh bakomi wlh ni ko ynx a shirye nake a
maida auren mu.
Haka kuwa akayi ba a jima ba aka maida auren,
bayan ya samu Aishalle ya mata bayani ta nuna
mai bakomi, amma ta shige dakih ta ci kukanta
hajjo na lallashi,. Daga bangare a ka fidda ma
Karime dakih ciki da parlo, rananr da tare su
Mudassir dadi kamar ya kashe su uwar dakinsu
ta dawo, nan ta rada musu wanih abu kunne
suka hau shewa...
******
A yau Aishalle ta suntulo danta kyakyawa me
kama da babanshi da taimakon hajjo da na
umm aneesa, ko kallo basu ishe karime ba,
amma hauka ne kadai batayi ba, takaicinta ya
akayi Ama ta riga ta haihuwa kuma namiji?
Musbahu baki har wuya yau ya gudan jininshi,
Rannan suna da yaci suna Aliyu. A rannan ne
karime ta tashi da wani kitifi wai ita ba ta san
qanshin ragon da ake soyawa, maqota basu bi
kanta ba don sun san halinta sai da suka ga tana
amai suka temaka mata, a ka kira ummu
aneesa don ta dubata, gwajin farko ta gane
karime na da juna biyu. Aifah tun lokacin

karime aka fara salon iyayi da kankamba, ba ta
san wannan ba ta san wanchan. Har Allah ya
sauketa lafiya, amma tayi baqin cikin ganin
mace ta haifa, Musbahu ya nuna farincikin shi
ranar suna diya ta ci suna Abida. To daga nan
Aishalle da karime suka fara gasan haihuwa,
duk shekara sai sun haihu, sai da Karime tayi
mata 2 Sadiya da Zainab kafin tayi namiji daya
Usman, ita kuwa Aishalle bayan Aliyu ta haifi
Umar da Abubuakar sai mace daya Maryam tun
daga maryam Ba
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment