Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dijat tayi, tare kuma da bud’e bakinta da niyar yin magana.

Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir saurin d’aga mata hannu alamun dakatarwa.

Kallonsa Aunty Dijat din tayi, lokaci guda kuma itama ta sauke kanta k’asa.

Hakanne kuma yasa gaba ki d’aya d’akin ya dauki shiru, babu abunda ke tashi sai sautin fitan numfashi, da kuma ajiyar zuciya da suke ta saukewa dukansu akai akai.

Almost 10mn kafun Abba Kabir din ya sake d’ago Kai ya kalli Jannart, cikin tausayawa da kuma danne abundake cikin zuciyarsa yace.

“Jannart kinji abunda nace, Ina fatan bazaki bijirewa umarnina ba kamar yadda kika al'ƙ’warta min.”

Kai Jannart din ta d’ago Ahankali ta kalli Abban nata.
Domin sai takejin maganganun nasa tamkar wani abu na daban, wanda bata tab’aji ko sanin akwai shiba.
Ita dai tasan kalmar Aure, amma batasan haka kalmar kan zuwarwa mace cikin zuciyarta ba, batasan ya rayuwar cikinsa yake ba.
Saidai koma meye ta sani bazata tab’a bijerewa umarnin Abban nata ba.

Idanunta tasake mayarwa k’asa, kana kuma Cikin sanyi ta jinjina masa Kai, alaman “Eh.”

Ajiyar zuciya mai k’arfi Abba Kabir din ya sauk’e, cikin kuma son sake tabbatarwa kansa amincewarta yace.

“Jannart duk da cewar bani nahaifeki ba, amma matsayin uba nake awajenki, haka kuma Kallon y’ata ta cikina nake miki, wannan yasa bazan tab’a yi miki dole ba, shin kin amince da hukuncin dana yanke akanki?”

Kanta ta sake jinjina masa, tare da bud’e Labb’an bakinta da takejin sun danyi mata nauyi a hankali tace.

“Eh Na amince Abba, duk hukuncin daka yanke akaina dai-dai ne.”

Numfashi Abba Kabir din ya fesar, tare da sake gyara zamansa.

Kana yace.
“Alhamdulillah naji dadi kwarai, Insha Allahu kuma yanzu akwai shirye shiryen da zamu fara, Domin banason lokaci ya ja da yawa.”

Kanta ta d’an langwabar gefe, kana cikin yanayin sanyi tace.

“To Abba, amma akwai abunda nake shiryawa, saboda ranan alhamis dinnan, zanyi wani program, Dan Allah Abba kabani dama, nasamu nayi shirin nan, Idan yaso daga baya komai ma sai ayi.”

D’an murmushi Abba Kabir din yayi, tare da cewa.

“Karki damu Jannart, shirin da nakeyi akannaki ma zaikai har bayan alhamis din, saboda haka kina da ishashshen dama na y’an wasu kwanaki.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e, tare da d’an sakin murmushi, saboda yanzu ta danji sanyi acikin ranta, Yayinda ta kuma k’ara samun hope akan cewar Lallai lailai bazata rasa aikinta ba.

Aunty Dijat kuwa Kallon Jannart din tayi, Yayinda takejin tasananin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarta.

Lallai Tabbas tasan cewa, Jannart din bata san komai ba, aharkar auratayya sai abunda ta karanta a musulunce, wanda hakan yasa dole tana buk’atar mai taimaka mata.
Sanin wasu abun a zahiriyar rayuwar duniya more Especially aure.
Tasan Jannart cikekkiyar janitalauce, sabida kan haka aka reneta aka bata tarbiya, bin umarnin na gaba da ita, ya zama komai na rayuwarta bata da zabin kanta ko ra'ayinta sai abinda manyan ta suka faɗa, shiyasa suke sarrafa ƙwaƙwalwarta sun hanata yancinta sun dakufeta bata da wani abu sai amsar umarni daga garesu.
Shiyasa ta kasance mai sauƙin kai da rauni kana ga tarin haƙuri.
Wanda suke tasirin hanata tsayuwa kan ra'ayinta.


Hannunta Aunty Dijat din ta rik’o, kana cikin tausasawa tace.

“Naji dadi da kika amincewa maganan auren nan Jannart, Domin kuwa aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, acikin aure akwai abubuwa da yawa, farinciki da kuma akasin haka, amma ni naji ajikina cewar auren da zakiyi shine zai zame miki Tubalin farin cikin ki, Rayuwa zata sauya miki Jannart, zaki zamanto Mace mai y’anci, k’uncinki zai gushe, Yayinda haske zai bayyana acikin rayuwarki Insha Allah, sannan kuma ako da yaushe kiyi riko da addu’a, Domin abubuwa sukanyiwa bawa tsanani ne Idan yana wasa da addu’a, Addu’a makamin mumini ne Jannart, musamman gake, da ace bakya sakaci da addu’o’i da ko Junaid da yake yawan musgana miki, bazai tab’a samun daman fuskantar ki ba, saboda Allah zaina baki kariyarsa akoda yaushe.”

Kai Jannart din ta jinjina, cike da gamsuwa da maganganun Aunty Dijat din kuma tace.

“Insha Allah zanna rik’o da addu’o’i, Nagode sosai Aunty Dijat.”

Murmushi Aunty Dijat din tayi, tare kuma da cewa.

“Ba komai Jannart, Allah Ubangiji ya kawo mana saukin damuwarmu.”

Da Ameen suka amsa dukansu, Yayinda Jannart din kuwa ta d’an kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, ganin lokaci yaja sosai ne kuma yasata, d’an mikewa tsaye.

Tare da Kallon Abban nata tace.

“Abba zan tafi wajen aiki kada nayi latti.”

Kai Abba Kabir din ya jinjina, had’e kuma da mik’ewa tsaye yace.

“Allah ya kiyaye hanya Jannart ya kuma Kareki aduk inda kike.”

Da Ameen ta amsa, tare kuma da daukar jakarta, ta juya ta fice daga cikin dakin.

Sam bata damu da maganan auren da Abban yace zaiyi mata ba, saboda batasan menene zata tsinta acikinsa ba, wannan yasa ko tambayan wanda sa’a aura mata din da kuma sunansa batayi ba, Ita dai ahar kullum tamkar rak’umi da akala take, duk inda aka jata zuwa zatayi.
Saidai kuma tana da tabbaci cewa Abban nata bazai yi abunda zai cutar da ita ba.

Koda ta fito compound din gidan, kaitsaye wajen motarta ta nufa.

Tana shiga cikin motar kuwa Drivern yaja suka tafi, Yayinda kattin guard dinta suka rufa musu baya.

Kaitsaye hanyar tashar tasu ta Arewa24 suka nufa.

Jin yanda suka mik’i titi ne kuma yasa ta, jingina bayanta da jikin kujerar motar, tare da lumshe Idanunta.

Ahankali ta sauk’e wani irin ajiyar zuciya, Yayinda kalaman Aunty Dijat kuwa suka shiga dawowa cikin kanta filla filla.

“Aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, Aure shi zai zame miki tubalin ginuwar farincikin ki.”

Abunda kwakwalwarta ke maimaita mata kenan, wanda kuma har yanzu ta kasa warware kalaman.

Meyasa Aunty Dijat din tace aure zai zame mata tubalin farin ciki? Menene acikinsa? Wacce kalan rayuwa ce zatayi, har kuma ta samu farinciki bayan zata zaune akarkashin wani ne wanda bata saniba bai santaba.
Ya yake irin Yah Junaid da Daddy ne ne ko irin Yah Azeez da Abba? Wai shin menene ma manufar auren nata da Abba bai gaya mataba?

Tayiwa kanta duka way’annan tambayoyin da ko kusa bata da amsarsu, ba kuma ta da mai amsa mata su yanzu.

Batasan komai akan hakan ba, ba ta kuma tab’a tunanin hakan acikin kwakwalwarta ba, shiyasa takejin duk wata kalma da ta shafi aure, amatsayin bak’on abu.

D’an numfasawa tayi, tare da watsar da duk wani tunani dake cikin ranta, dai-dai lokacin kuwa suka iso babban parking space dake cikin tv station din.

Bayan Baba Ado ya gama dai-dai-ta parking din motar ne kuma ta fito, kaitsaye ta nufi cikin gidan tv’ nasu.

Ahankali take taka k’afafunta, Yayinda kowanni taku da zatayi yake dauke da jan hankalin mai Kallon ta.

Azahirin gaskiya kuma awajenta tafiya takeyi normal, Yayinda duk wani mai Kallon ta kuwa, ke ganin tafiyar tata tamkar tafiyar hawainiya, saboda komai nata na dabanne, tana da wani irin tsarin halitta mai matukar burgewa, wanda kuma ko ita kanta batasan cewar tana dashi ba.

Tura kofar babban office dinnasu tayi ta shiga bakinta dauke da sallama.

Jin Sauti da amon zazzakar muryar nata ne kuma yasa, duk mutanen dake cikin office din juyowa suka kalleta.

Wani dogon tsaki Asiya taja tare da kauda kanta daga kallonta.

Ita kuwa Jannart Sam hankalinta ba a kanta yake ba, duk da irin Kallon da taga tanayi mata kuwa Amma bata damu ba.

Fuskarta d’auke da murmushi ta k’arasa wajen, Aysha Lawal da kuma Salman wanda suke zaune awaje daya suna duba wasu takardu.

Murmushi Aisha Lawal din ta sakar mata, tare da cewa.

“Jannart Idi Saleh Dakata yau kinyi lattin zuwa wajen aiki, saboda haka sai munciki tara.”

Murmushi mai kama da dariya Jannart din tayi, har saida fararen hak’waranta suka bayyana, hakan kuwa shiyasa dimples dinta duk suka lotsa.

Kafad’an Aysha’n ta d’an buga, kana cikin muryata da babu hayaniya sosai tace.

“Kai Aysha kwata-kwata fa mintuna 10, na kara akan yanda nake zuwa kullum.”

“Eh duk da haka dai.”

Ayshan ta fad’a tana murmushi.

Jannart kuwa zama ta d’anyi agefe dasu, tare da dawo da Kallon ta ga Salman Wanda ya saki idanu da baki yana Kallon ta.

Had’a idanu da sukayi ne kuma yasa shi saurin janye idanunsa daga kanta.

Itakuwa Jannart batare da ta fahimci komai na daga Kallon da Salman din keyi mata ba tace.

“Good morning colleague.”

Gashin kansa ya d’an Sosa kana awayance yace.

“Morning Colleague, fatan kin tashi lafiya ya jikin naki.”

“Da sauki sosai, Domin nama warke yanzu babu wani abu dake damuna.”

Jannart din ta fad’a tana me ajiye Jakarta,
Adai-dai lokacinne kuma Hajia Rabi'ah da Aunty Fauziya D Sulaiman suka shigo, cikin sashin su Jannart din.

Ganin Jannart din da sukayi acikin office dinne kuma yasa, Aunty Fauziya D Sulaiman sakin murmushi, kana cikin jin dadi da kamala da mutuntaka tace.

“Masha Allah gaskiya Jannart ansamu lafiya, tunda har an fara fitowa office.”

Murmushi Jannart din tayi, cikin kuma jin dadin kulawan da yan office din nasu ke bata tace.

“Alhamdulillah my Aunty Fauziya naji sauki, kuma Ina saka rai da fatan cewa Insha Allah Gobe ma zan gudanar da program dina.”

Kai Aunty Fauziyan ta jinjina, tare kuma da matsowa kusa da Jannart din sosai.

Cikin yin k’asa da murya irin ta maganan sirri tace.

“Masha Allah, amma Jannart kinaga kuwa Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din zaizo.”

Kanta tad’an langwabar tare kuma da juyawa, ta kalli Salman wanda shidinma kuma Kallon ta yake.

Kai Salman din ya jinjina mata, cike dason bata karfin guiwa yace.

“Karku damu Insha Allah Zaizo.”

Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, tare da daura hannayenta akan kafad’an Jannart din.
Murya atausashe tace.

“Karki damu Jannart, ko da ma ace bai samu zuwa goben ba, ai kina da sauran chance harna tsawon one week, Insha Allah kuma muna saka ran dacewa.”

Kai kawai Jannart din tad’an jinjina, tare da komawa ma zauninta ta zauna, lokaci daya kuma duk jikinta yayi sanyi, domin tasan gobenne kawai last hope dinta, kasancewar bata da tabbacin cewa, wani satin zata kasance available, musamman ayanzu da Abba Kabir yake kokarin fara shirye shiryen b’oyeta.

“Yah Allah Kabani sa’a.”

Tafad’a k’asa-k’asa, tare da maida idanunta ta lumshe, saboda gaba daya yanzun ta karaya da komai.

Salman kuwa daya karanci tarin damuwa akan fuskar Jannart din, ji yayi komai na Office din baya yi mishi dadi, duk yanda yaso ya daure zuciyarsa akanta kuwa baya tab’a iyawa.

Haka yake d’agowa time to time yana satan Kallon ta.

Itakuwa Jannart samma batasan yanayi ba.

Aysha Lawal ce kawai take lure dashi, fahimtar abunda ke ran Salman din agame da Jannart dinne kuma ya sakata sakin murmushi.
Batare kuma da tace komai ba taci gaba da ayyukanta.

Haka dai Jannart ta kare gaba d’aya wuninta a office din, duk yanda kuma taso kawar da fargaban dake ranta ta kasa.

K’arfe 5 dai-dai tayiwa su Salman da Aysha Sallama,kaitsaye ta wuce gida.

Koda suka iso gidan nasu, haka ta fito daga cikin mota gaba daya duk jikinta asanyaye.
Direct falonsu ta nufa, inda tana shiga cikin falon kuma wayarta dake rik’e a hannunta ta soma kara.

Kallon ta ta mayar kan screen din wayar.
Lokaci daya kuma murmushi ya bayyana akan fuskarta, saboda sunan Yah Azeez da ta gani.

Picking call din tayi, tare da kara wayar akan kunnenta.

Sallaman da tayi dinne kuma yasa Daga can b’angaren Yah Azeez ya amsa mata, tare da cewa.

“My y’ar k’anwa Jannatuwa, bari na fara bada hakuri kafun ki shigo da korafin rashin kiranki da wuri da banyi ba.”

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan shagwab’e fuska, tamkar Yah Azeez din yana ganinta. Tace.

“ai saura kad’an nayi maka fushi Yah Azeez, kuma da baka kirani yau ba ko hmmm, ko kakira bazanji rarrashi ba.”

Murmushi Yah Azeez din yayi, cikin tsananin so da Kaunar yar uwartasa yace.

“I’m sorry Jannart wallahi aikine yayimin yawa kuma na kira sau biyu Mom ke ɗagawa tace kina bacci, yanzu ya jikin naki, Ina fata kinji sauki sosai.”

Kanta ta jinjina had’e da cewa.

“Naji sauki sosai Yah Aziz, Domin yau har wajen aiki naje, yanzu shigowa ta ma gida.”

“Masha Allah Lallai jiki yayi kyau, To Allah ya kara afuwa, sannan kuma ki kara hakuri kinji Jannart, Insha Allah watarana sai labari, komai da Junaid keyi miki zaizo ya wuce, kuma Allah zai saka miki akan duk wani cutarwa da Junaid keyi miki, shima kuma zai ga sakamakon abunda ya aikata.”

Idanunta ta d’an lumshe, saboda har acikin zuciyara taji sanyi da dadin kalaman Yayan nata, inama da ace shine akusa da ita ba Junaid ba, Lallai da taji dadin duniya, Domin ko ayanzu da baya kasar, yana iyaka kokarinsa wajen bata kulawa, da nuna tausayawansa agareta.

Numfashi ta d’an fesar kana Asanyaye tace.

“Nagode Sosai Yah Azeez, kuma Insha Allah zan kara hakuri akan wanda nakeyi.”

Murmushin Jin dadi Yaya Azeez din yayi, Domin dama yasan tuncan k’anwartasu mai biyayyace, akan duk wani abu daka umurceta.

Still cikin nuna kulawa yace.
“Yauwa y’ar k’anwata, yanzu fad’Amin akwai wani abun da kike buk’ata ne, ko kud’i sai na tura miki ta account, ki saya duk wani abu da kikeso.”

Murmushi tayi, hadi da cewa.
“A’a Yah Azeez bana buk’atar komai.
Domin last week Abba Kabir yayimin shopping, sannan kasan akwai kudi da yawa a account dina, ko salary na Idan anturomin bana sayan komai dasu.”

Ajiyar zuciya Yah Azeez din dake kan wayan ya sauk’e.
Nandai suka d’an tab’a hira kafun daga bisani sukayi sallama.

Bayan ta kashe wayar nata ne kuma ta lek’a kitchine ko zata ga Momy, saboda tunda ta shigo babu motsin kowa agidan.

Ganin kitchine din bakowane kuma yasa kaitsaye ta wuce bedroom dinta, saboda tanason yin wanka Tsarkin data samu.
Akwai kuma wasu bayanai da zata had’a acikin system dinta.

Acan B’angaren Dr. Rayyern Muhammad Mai-nasara kuwa zaune yake akan wata had’add’iyar royal chair, Yayinda yake sanye da wani had’add’en suit mai kalan ruwan k’wai ajikinsa.

Daga gefe guda kuwa drinks da kuma Chocolate d’insa ne, sai kuma sabuwar wayarsa Iphone daya k’ara saya, dake rik’e ahannunsa.

Inda kaitsaye ya shiga cikin contact d’insa, yana neman wani numbern tsohon abokinsa, Salisu, saboda yanason yiwa Salisu din ta’aziyya kasancewar yaji labarin rasuwar Baban shi.

Yana cikin tsaka da duba contact dinne kuma, idanunsa suka sauk’a akan numbern Salman.

Numbern da Idan bazai manta ba, sune wanda suke son ganinsa, ya kuma yi musu alk’awari zuwa.

Saurin sanya hannunsa yayi ya dafe kansa, saboda sai ayanzu ne ma abun ya fad’o masa, gaba daya kwata kwata ya manta ma dasu.

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da dan cije Labb’an bakinsa.

Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

“Allah Nagode ma daka tunatar dani, Allah kada ka bani ikon daukan al'k’awarin da bazan iya cika shi ba.”

Jawo wayarsa yayi ya duba date da kuma rana.

“Today is Wednesday, gobe ne al'k’awarin dana d’auka kenan zai cika, Insha Allah zanyi kokari naje, kodan yaronnan ya tsira da aikinsa, ya kuma samu abunda zai ciyar da iyalansa.
Tabbas zanyi cancelling duk wani schedule dina na Gobe, har sai na samu naje tv station dinnan, bazan tab’a zama mai karya alk’awari ba Insha Allah bazan zama sanadin rasa aikinsa ba.”

Ya fad’i hakan, yana me mik’ewa tsaye, tare kuma da d’aukan laptop d’insa.

Kaitsaye ya koma wajen zamansa da yake na musamman, acikin katafaren office din da yake new company’n’ sa.


Tahir Quest Palace.

Riyyam nsra ne kwance akan makeken gadon dake dakin hotel din, wanda kuma yanzun gama wayarsa da Mammy da kuma Zaiton.

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da juyowa ya kalli, matashiyar budurwar dake kwance agefensa.

Almost 1hour kenan yanzu da zuwan ta wajensa, wanda kuma itama sun had’u ne da ita anan Tiktok, Yayinda itama take cikakkiyar celebrity ce a Tiktok din, sannan kuma yar asalin Nigeria ce cikin Kano tayi shuhura a iya tiƙa rawa da bin waƙa, ga iya sa fitinennun suturu masu bayyana tsiraici hakan yasa kasuwarta ke ci.

Idanu Riyyam din ya zuba mata, Domin kuwa Wannan shine Karonsa na farko daya fara mu’amala da wata mace y’ar Nigeria.

Yarinyar dake kwance agefen nasa, kuwa ganin irin Kallon daya ke mata ne, yasa ta kashe masa Ido, tare da turo masa kirjinta gaba, wanda ko kaya babu ajikinta.

Hakan ya faru ne kuma saboda sheke ayarsu da sukayi ita da Riyyam nsra din.

Wani irin nishadi takeji acikin zuciyarta, kasancewar Riyyam din yayi mata hundred percent.

Shikuwa Riyyam da baya gajiya da tab’ewa, hannunsa yasa ya shafo kirjinta, cikin kuma yin k’asa da murya hadi da kashe mata idanunsa yace.

“Are you ready?.”

Idanu ita dinma ta kashe masa, hade da jinjina masa Kai alaman she’s ready.

Batare kuma da ta bari ya kawo kansa ba, ta hade bakinsu waje daya.

Akaro na biyu kenan yanzun da suka sake shigewa duniyar Mazinata, duniyar da muninta ya wuce misali, kyamatacciyar duniya marar kyaun gani mai cike da masifu wanda duniyar TIKTOK ya zamo kawali'unsu.


Bayan Riyyam din ya fito awankane kuma, ya shirya kansa cikin shigar daya saba yi ta kananan kaya.

Wayarsa dake aje kan table ya d’auka tare da Kallon yarinyar da take kokarin saka kayanta.

Bandir din fararen y’an one one k dake hannunsa ya cilla mata.

Tare da d’alewa saman table din ya zauna, hakanan yakejin wani irin haushi, takaici, da kuma kunci acikin zuciyarsa, Yayinda yaji ko ganin yarinyar baya mason sake yi.

Sometimes kuma baisan Meyasa yakejin hakan ba, aduk lokacin da yayi sex da mace, bayan ya samu biyan bukatarsa sai yaji duk duniyar ma batayi masa dadi.

Itakuwa Yarinyar ganin da tayi mood d’insa ya sanja ne, yasa ta tattare kudin daya watso matan ta zuba acikin Jakarta.

Bayan ta gama kimtsa kanta ne kuma tayi masa sallama ta tafi.

Kamar kuwa dama jiran tafiyan nata yake, Domin tana tafiya shima ya rufe dakin.

Bayan ya bada key din a reception ne kuma, kaitsaye ya fito daga cikin hotel din.

Taxi ya tara, tare da fad’awa mai taxi din ya kaisa can cikin Nassarawa G.R.A din.


Acan b’angaren Rayyern kuwa bai baro Companyn nasu ba, har saida ya kammala duk wani abu da yakeyi.

Koda ya fito daga cikin company din kuma, kaitsaye motarsa ya shiga.
Inda suka nufo gida.

Isowarsu bakin gate din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowar Riyyam nsra din acikin taxi.

Ganin motar Rayyern dinne kuma yasa Riyyam sakin murmushi,
Bayan ya biya mai taxi din kudinsa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin gidan.

Kasancewar tuni motar Rayyern din ta shige ciki.

“Baba Maud’o barka da gida.”

Riyyam din ya fad’a alokacin daya bud’e karamar kofar gate din ya shigo.

Baba Maud’o dake zaune kuwa, ganin Riyyam dinne yasa kashi sakin murmushi.

Cikin kulawa kuma yace.

“Yauwa barka dai Riyyam, tun safe yau baka zoba sai yanzu ka samu zuwa kenan.”

Kai Riyyam din ya jinjina tare da cewa.

“Eh, yau din nayi bacci sosai, kuma abokai na sun kawomin ziyara shiyasa Banzo da wuri ba.”

Kai kawai Baba Maud’on ya jinjina, Yayinda shikuwa Riyyam kaitsaye ya nufi inda motar Rayyern yake.


Yana zuwa wajen kuwa Rayyern na fitowa daga cikin motar.

K’arasowa Riyyam din yayi, cikin sauri yace. “Oyoyo Hamma Rayyern sannu da dawowa.”

Ya k’are maganan yana me rungume Rayyern din.

Rayyern kuwa zame jikinsa ya d’anyi, tare da jinjina kansa alaman yauwa.

Kamar zaice wani abu kuma sai ya fasa, kaitsaye duk suka nufi babban falon gidan.

Yayinda afakaice kuma Rayyern ke Kallon Riyyam din, Domin hakanan yaji zuciyarsa na raya masa wani abu na daban, dangane da Riyyam din musamman kamshin turaren jikinsa da yaji wanda ya tabbatar turaren matane.

Shigowarsu cikin falonne kuma yasa.

Hankalin Mamy dana Ramadan harma da Abba ya dawo kansu.

Ganin Rayyern dinne kuma yasa Abba sakin murmushi.

Yayinda Riyyam kuwa ke biye dashi abaya.

Karasowa cikin falon sukayi suka zauna.

Inda Riyyam ya durkusa har kasa ya gaishe da Abba da Mamy, fuska asake duk suka amsa masa.

Rayyern kuwa da ya Zauna akan kujeran dake gefen na Mamy.
Kallon Abban nasu yayi tare da cewa.

“Abba Mamy barka da gida.”


“yauwa Rayyern barka dai ya company’n.”

Abba ya tambaya.

“Alhamdulillah Abba komai yana tafiya dai-dai an kusa gama haɗa komai.”
Rayyern din ya fad’a yana me d’an gyara zamansa, tare kuma da sauk’e idanunsa akan, Riyyam wanda yaje ya manne da jikin Ramadan.

“Masha Allah Allah ya taimaka.”
Abba da Mamy suka hada baki wajen fad’an hakan.

“Ameen.” Ya amsa still yana mai Kallon Riyyam.

Kwarai so yake ya fahimci yaron, saboda yarda da abunda zuciyarsa ke gaya masa, yanaji ajikinsa cewar yaron kamar yana bin mata, musamman Idan akayi duba da irin rawar kan da yake dashi, ya cika rawar Kai da yawa.

Janye kansa daga Kallon Riyyam din yayi, saboda bayason yana shiga abunda bai shafesa ba.

Ramadan kuwa dake rik’e da wayarsa d’ago kansa yayi ya kalli Rayyern din.

Cikin sigar lallashi hadi da roko kuma yace.

“Yauwa Hamma Rayyern dama kai nake jira ka dawo, please Hamma Rayyern Dan Allah ka fito da mata kasamu kayi aure, kaga Abba yace bazanyi aure ba harsai kayi, ni kuma Allah yanzu aure nakeso nayi, bana son na rasa Rayhanna please Hamma na.”

ya k’are maganan yana me d’an langwab’ar da kansa gefe.

Shikuwa Rayyern d’ago kansa yayi, da kuma fuskarsa wacce ta sanja kala zuwa yanayin bacin rai.

Wani irin kallo ya watsawa Ramadan din, cikin hade fuska yace.

“Rufe min baki Ramadan kada fa ka tunzura min zuciya Kaine zaka tsaramin yanda zan tafiyar da rayuwata? Ko ka fini sanin abunda nakeyi ne, da har zaka zo kana cewa wai nayi aure! Kai ubana ne!? ko yayana!? kama fini sanin abinda ya dace kenan?.”

Rayyern din ya k’are maganan cikin fad’a.

Wanda hakan yasa Ramadan Dan sunkuyar da kansa, cikin yanayin sanyi kuma yace.

“Ayyah Hamma Rayyern kayi hakuri Insha Allah bazan sake ba kaji kayi haƙuri.”

Kai Rayyern din ya kawar, Yayinda Abba da Mamy kuwa suka kalli junansu.

Ramadan kuma mik’ewa tsaye yayi, tare da kama hannun Riyyam-nsra suka fice daga cikin falon.

Fitansu daga cikin falonne kuma yasa Abba d’ago Kai ya kalli Rayyern din.

Yayinda su Ramadan kuwa suna fita, kaitsaye wajen Baba Maud’o dake zaune abakin gate suka nufa.

Ganin su dinne kuma yasa Baba Maud’o sakin murmushi.

Bayan sun zauna akan dogon bencin da Baba Maud’on ke kaine kuma.

Baba Maud’on Ya kalli Riyyam-nsra tare cewa.

“Riyyam ya mutanen can k’asar taku, da su Mammyn ka da Zaiton.”

Murmushi Riyyam-nsra yayi, tare da gyara zamansa ya kalli Baba Maud’on cikin kuma jin dadi yace.

“Munyi waya dasu dazu kowa da kowa yana nan lafiya, sunma ce na gaishe da kai, saboda na tura musu hotonka, har Zaiton tana cewa wai itama zata zo ka nad’a mata irin abunda kake sawa afuskarka, wai zatana boye fuskarta saboda Samarin dake damunta.”

Yar dariya Baba Maud’o yayi, tare da jinjina kansa.

Cikin jin dadi yace.

“To shikenan Idan tazo zan koya mata yanda ake na dawa, ai rawani ne ba komai ba, nadashi kuma ba wahala.”

“To Baba Maud’o nima dai ai watarana zaka koya min ko, sai naje na koya mata.”

Kai Baba Maud’on ya jinjina alaman.

“Eh.” Daga haka kuma suka ci gaba da hiransu.


Ethiopian.
Adai-dai lokacin ne kuma Mammy dake zaune akan sallaya ta kurawa, hoton dake kan screen din wayar nata idanu, wanda kuma hoton Baba Maud’o ne da Riyyam ya turo mata.

Azahirin gaskia ba kuma tana Kallon hoton da wata manufa ko tunani bane.

Kawai dai tana mamamkin irin shigar da taga mutumin yayi ne, saboda su anan basu tab’a Ganin irin shigar ba.

Ajiye wayar nata tayi tare kuma da watsar da duk wani tunani dake ranta, kaitsaye ta mike daga kan sallayan ta shige kitchine.

Acan falo kuwa Abba dake Kallon Rayyern d’an gyara zamansa yayi.

Tare da fuskantar shi kana cikin yanayi masifa faɗa da kuma umarni yace.

“Uhmmm RAYYERN kenan.
Saboda kawai yace maka kayi aure shine kake daka masa irin wannan tsawan? Da ɗaga jijiyoyin wuya.
To shi meyene laifinsa, saboda kawai yace ka cika martabarka, ka kuma raya sunnar Annabi Muhammad SAW shine, yayi laifi?”.
Ya ƙare mgnar tare da tsareshi da idanun
Da dole yasa RAYYERN yayi ƙasa da kansa.
Shi kuwa Abba kwaffa yayi tare daci gaba da cewa.
“Yoh wai kai azatonka da tunaninka haka zaka ta zama babu aure ne, saboda kawai kaga na zuba maka ido tsawon shekaru, kayi tunani da hankalin ka fa Rayyern, ayanzu Kai ba yaro bane, Domin kuwa kabawa shekaru 30 baya, shin kana tunanin banason yin aurenka ne? Ko atunaninka bana da buk’atar Ganin aurenka ne? To kasani duk da cewar nasan tabbas na sakar maka ragaamar komai, na tara maka ayyukan da sukafi karfinka, bawai Ina nufin ka zauna haka babu aure bane ba wurin aiki kawai nake son ganin kamalarka ba harda aure, Tabbas banajin dadi aduk sanda ka nuna cewar babu maganar aure kwata-kwata agabanka, kaine babba

3 Comments On TUBALI
avatar
khadija-dauda

1 year ago

Reply

Pls inason littafin tubali

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to khadija-dauda

ki karanta anan

avatar
fatima-muhammad-8-7

12 months ago

Reply

Pls ina Sauran chapters din tubali naga wanna chapter 30 ya tsaya kuma bai kai kar she ba

Please Login or Register in order to submit comment