Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp.

Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal,
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻...

Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa.
*Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya*

Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala*

Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy*

🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻.


Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂.


*Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo*









By
*GARKUWAR FULANI*







*TUBALI*

PAGE 3

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*FREE PAGE*
*ƊANƊANO*
*NMETTARI enji men nfulɓe*


"Jibi". Ya bata amsa a taƙaice yana mai kallon Kyakkyawar fuskarta.

Ita kuwa gyara zamanta tayi tare dasa hannu ta amshi cup ɗin ruwan sanyin, da Hajia Rabi'ah ke miƙa mata-ta ajiye shi bisa Stoll din baƙin glass dake gabanta.
"Nagode". Ta faɗi cikin nitsuwa, sannan ta kalli Mahmoud dake bin fuskarta da ido.
Cikin yanayinta na nutsuwa da kuma bayyana zallan ajinta na y’a Mace tace.
“Akwai tabbacin jibi zai dawo? Sannan ta Abuja ko Lagos zasu sauƙa?".

Wayarshi ya zaro a al'jihun rigarsa yana mai lallatsata kana yace.

“In sha Allah jibi zasu dawo.
Dan last night muna tare da Deen ƙanin Usman PA'nshi.
Yayi magana da yayan nashi kan jikin mamansu ya tashi, yaushe zasu dawo.
Toh nan Usman ɗin ke cewa jibi zasu dawo.
Iya abinda na sani kenan, sauran bayani kuma sai dai in tuntuɓi Deen ɗin".
Ya ƙare maganar yana sa wayar a amsakuwa yadda duk zasuji.

“Hello Deen ya Gida".
Cewar Mahmoud.
Deen dake zaune gaban mamansu wanda yanzu ya gama magana da Usman ne yace.
"Lfy lau Alhamdulillah Mahmoud".

"Yah jikin Mama".

"Alhamdulillah jiki da sauƙi".
Ya bashi amsa yana miƙa mata maganin.

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Yah Usman ɗin yana dawowa ko?".
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Eh to, zasu dawo, amman sai jibi fa kuma nan ma wata ƙil in sun iso su kwana a Abuja wata ƙil suda nan sai ranar jumma'a".
ya ƙare mgnar da sanyi.

"Ayyah ba komai ai in dai jikin da sauƙi, jumma'a kamar yaune Allah dai ya dawo dashi lfy. Ka gaida min Mama da jiki Allah ƙara ƙarfin jiki".

“Amin Amin". yace kana sukayi sallama.

Katse kiran yayi tare da juyowa ya kalleta.
Numfashi suka sauƙe ita da Hajia Rabi'ah.
Sai kuma tace.
"Alhamdulillah, toh Mahmoud ko zaka bani number Deen".
Da sauri yace.
"A a in fa yasan me kike bincika bazai saurareki ba".
Hajia Rabi'ah ne ta amshi zancen da cewa.
"Kada ki damu Jannart in sha Allah komai zai tafi dai-dai.
Shi Mahmoud ɗin shi zai rinƙa samo mana bayani.
Tunda kuna da number’n juna zaike miki bayani, ba sai kin fito kinzo nan ba, tunda fitar naki aikine mai zaman kanshi."
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"Toh shike nan My Aunty, Ngd Matuƙa Allah ya saka da al'khairi".

“Amin Amin.” tace
Tana mai gudun kada aikin ya bar hannun yarinyar tunda kowa ya ganta dai yasan bawai tana yin aikin dan neman kuɗi ko suna bane, tana yine dan ra'ayin tane gashi du-du watanni huɗu tayi da fara aikin kuma suna jin daɗin mu'amala da ita, so dama sanyin da shirin yayi shiyasa aka canza wanda ke yinsa a baya.
Kuma da alamun tana matuƙar jin daɗin aikin.

Kiran Salman ne ya shigo wayarta.
Da sauri ta amsa tare da karawa a kunne.
"Assalamu alaikum".
Tace cikin sassayan sautin ta.

Daga b’angarensa kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Wa alaikissalam, Jannart kinbi diddigin Rayyern d’in? Kuma wane lbri kika samo mana a kanshi? "

Cikin yarda da kai tace.
"Duk motsinshi na cikin tafin hannuna!".
Dariya mai sauti Salman yayi.
Hakama Hajia Rabi'ah da Mahmoud.
"Karsashi’nki da ƙarfin guiwarki akan aiki yana burgeni Jannart”.
Cewar Salman.
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Toh ba doleba Salman, tunda naji ana shirin korata, ai sai inda ƙarfina da hikimata suka ƙare".

Cikin wasa yace.
"Ke har wani ƙarfi a garreki da dai kin tsaya a hikimar na yarda".

Murmushin daya sanya beauty point ɗin ta lotsawa tayi.
Haka dai suka ɗan tattauna batun bayan ta mishi bayanin abinda ta ji kan dawowarshi.

Saida tayi sallan azahar ne kuma ta fito suka nufi gida.

A kan hanyarsu ta komawa ne, Baba Ado driver'nta ya ɗan juyo ya kalleta cikin kulawa yace.
"Jannart yanzu dai ciwonki da sauƙi ko?".
Numfashin ta ɗan fidda kana a hankali tace.
"Alhamdulillah da sauƙi dai zance, amman yana yawan motsa min a kwanan nan kamar yana son tashi."
Cikin tausayawa yace.
"Toh amman har yanzu babu wani maganin da ake baki sai allurar da akeyi duk watan ne?".
Kai ta gyaɗa mishi tare da cewa.
"Eh".
Numfashi ya ɗan fesar kana yace.
"Allah ya sauƙaƙa yasa zakkan jikine al'farmar Annabi da al'ƙur'ani".
Cikin jin daɗi tace.

“Amin Baba Ado nagode!".

A can Ethiopia birnin Addis Ababa, kuwa.
Riyyam-nsra ne tsaye gaban wayarsa daya tsaida.
Rawa yakeyi da murmushi a fuskarsa.
Sai kuma ya kalli gefensa.
Wata kyakkyawar budurwa wacce a ƙalla suyi sa'anni.
Murmushi yakeyi cikin harshen Hausa yake cewa.
"Jibi iwar haka ina hanyar Nigeria, su Zayton kuma sai dai ayi ta aikin zumbura baki.
Fan's ku gani, wai kishi takeyi dani".
Da sauri ta kai mushi bugu tare da matso ƙwallar idanunta, tana faɗin
"Mammy! Mammy!!".
Wata kyakkyawar matace mai Kekkyawar sura da jiki da shiga ta kamala, wacce kyan surarta ya iya boye ainihin shekarunta, ta fito daga cikin wata ƙofar da fuskantar inda ya kafa wayar tashi.
Ɗan gudu-gudu da tsalle-tsalle yake yana zagaya parlon Zayton na biye dashi a baya.
Da sauri yayi tsalle tare da ɗan sakin ƙara yace.
"Ohh Mommy".
Jin ta ɗan sa hannu ta bugi ƙeyarshi.
Tura baki yayi tare dasa hannunshi ya shafa ƙeyar yana mai zazzarewa Zayton ido.
Abin gwanin ban dariya da ka gani kasan akwai Kekkyawar shaƙuwa, ƙauna, tausayi, da son juna.
Ɗauke wayar tashi yayi ya sake video a shafinsa na TIKTOK.
Kun san matsalar su kenan ƴan TIKTOK duk abinda zasuyi ko sukeyi sai sun nunawa duniya, More Especially irin Riyyam-nsra da yayi shuhura yayi zarra da dubban dubatan masoya mabiya, musamman a cikin kwanakin nan da yai mgn da Hausa ya janye mana hankalin matasan Nigeria, domin kuwa ayanzu followers d’insa harsun d’arawa two million.
Gane abin da yayi dinne kuma yasa. Mammy matsoshi da kyau ta kama kunnenshi ta ɗan matse.
Ƙara ya kuma ɗan saki, wanda yasa Zayton tuntsirewa da dariyar jin daɗi tana ɗaga mishi gira.
Ita kuma Mammy cikin ɗan faɗa tace.

“Wato kai Riyyam baza ka taɓa canzawa bako, duk motsinmu sai ka bazamu a duniya? Kai kam inaga kana gab da nuna duniya yadda kake kashi ma ko".
Hannunshi yake ɗan yayyarfawa tare da cewa.
"Afwan Yaah Mammy na tuba, wayyo Hamma Mammy zata tsinke min kunne".
Dariya Zayton tayi tare da cewa.
"Zai aikata fiye da hakama Mammy ja kunnen da kyau".
Hannunshi ya kai ya bugi hannunta tare da cewa.
"Yarinyar nan ki shiga hankalinki fa".
Fuska ta haɗe tare da cewa.
"Waye yarinyar yaro in ka manta in tuna maka nice babba 15 minute nake baka, kaga kuwa dole ace da mijin iya baba, dan 15 minute ba 15 second bane".
Sosai Mammy ta saki murmushi suna matuƙar sata nishaɗi da ɗebe mata kewa, da danne mata duk wani ƙuncin rayuwa, Especially in suna faɗa kan girma.
Zayton son girma kamar gyambo, 15 minute da take bashin nan ji takeyi kamar shekaru goma sha biyar take bashi.
Gefe ta zauna kana suka zo suka sata a tsakiya.
Cikin sakin fuska ta shafa kan Riyyam-nsra tare da cewa.
"Zoh nan autana".
Gwalo yayiwa Zayton tare da ɗaura kanshi bisa cinyarta tuni kuma ya sake haɗa video.
Murmushi yakeyi yana yiwa Zaiton signal tare da cewa.
"Mammy asamin al'barka".
Da sauri itama ta sako kanta tare da cewa.
"Mammy ai nice mace, dan haka ya riƙe girman ya matsa ni in kwanta".
Cikin yin ƙasa da murya Mammy tace.
"Ya isa haka ku bari, Dida na bacci kada ku tada min ita".
Toh sukace dan yadda tayi mgnar ba wasa.
Bayan ya saki wannan video ɗin ne kuma.
Ya gyara zamanshi ya fuskanci Mammy da kyau jin tana cewa.

“Riyyam sam hankali na. baya kwanciya da wannan rawan kan naka! Ina jin tsoron kayi nesa dani, gaba ɗaya ka juye ka zama ɗan nanaye, ka zama tamkar mazari duk inda kake sai rawa, sai waƙa, sai haɗa comedy duk inda kake waya na hannu, kai kaɗai a ganka kana dariya ko kana kuka ko kana haɗa fuska ko layi, kai gasu nan dai barkatai, ka zama ɗan Film a fili ka rubuta lbri ka tsara ka bawa kanka umarni kayi shirin.
Ga ɗan karen yawo yau kace zaka tafi waccar ƙasar, gobe kace zakaje waccar gashi ka zama babu sirri duk inda kake an sani, shiyasa nake jin tsoron zuwanka Nigeria duk inda kaga mata sai ka bisu da ido".

Da sauri ya gyara zamanshi cikin nitsuwa kamar ba shiba yace.
"Mammy babu komai sai al'khairi, ki yarda dani bana wani mugun abu, in ke bakya gani na ai Ubangijin talikai daya busan numfashin yana ganina".

Uhum tsakanin uwa da ɗa kenan ya gane cewa tana zargin shi ne ko tana tsoron taɓarɓarewar tarbiyarshi.
Cikin sauƙe nannauyan numfashin tace.
"Wlh badon dole ba, bazaka jeba, amman ba komai Allah ya kaika lfy ya dawo da kai lfy.
Sai dai dole ka nitsu ka dena wannan rawan kan".

Hannunshi yasa ya kame kanshi kana yace.
"Toh Mammy na dena".
Murmushi tayi hakama zaitun.

Washe gari ranar Laraba, Kano Nigeria.

Cikin bacci taji numfashin ta, na fita a cushe, kana tana shaƙan zazzafan ƙamshin turaren sa mai masifar ƙarfi da tafiya da numfashin ta.
Idonta ta buɗe cikin wahalar numfashi.
Da sauri ta ida buɗe su duka tare da fisgo numfashin ta a wahalce.
Sabida ganin Yah Junaid da tayi sunkuye a kanta hannunshi na kan ƙirjinta.
Wani irin tsuma da karkarwa jikinta ya farayi, da azaban ƙarfi.
Cikin tsananin tsoro da razanin ta yunƙuro zata tashi, tare da furta "innalillahi wa innalillahi raji'un."
Wani irin azabebben tsoro firgita kaɗuwa da gigitane suka dirar mata lokacin ɗaya jin yadda yasa hannunshi ya matse ta tare da murtuƙe fuskarshi.
Cikin tsananin rawan jiki take zaro ido murya da baki na rawa tace.
"Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Y... Ya... Yah... Juna..Junaid, me haka!!”

Wani irin masifeffen kallo ya watsa mata, tare da kai hannunshi duka biyu kan breast ɗinta, yayi musu wani irin masifeffen kamu wanda yasa ta saki wani irin gigitaccen ƙara, lokaci ɗaya kuma numfashin ta ya fara off and Dawn, ciwonta na gab da tashi.
Shi kuwa Junaid wani irin sanyi yakeji a ransa tare da rumtse tafin hannunsa.
Mom kuwa dake ɗakinta, ita da Abdul cikin razanin jin sautin muryar Jannart ta miƙe tsaye jiki na rawa, ta fito falo.
Dai-dai lokacin kuma Jannart ɗin ta fara wani irin fiffizgewa sabida numfashin ta dake shirin barin gangan jikinta.
Wata iriyar fitinenneyar zufa mai cike da zafi, ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.

“Hahhhh! Uhhhhhhhh!! Fuhhhhhhhheeeeyyyy!!! M...Mom!"
Ta fuzgo maganar da ƙarfi lokaci daya kuma numfashin ta ya dena shiga sai fifita.
Jiki na rawa Mom ta kutsa kanta cikin ɗakin nata.
Shi kuwa Junaid wani irin fitinenne abu yakeji yana tsirgar masa.
Hannunshi ya kirjinta. Tare da yiwa breast ɗin ta wani azabebben riƙon da saida yaji.
Gamsuwa shaiɗan cinsa.
Kana ya juya ya nufi ƙofar fita.
A bakin ƙofar sukayi kiciɓis da Mom.

Wani irin mugun kallo ya watsa mata.
Ita kuwa Mom wani irin kallon tuhuma take binshi dashi.
"Mchewww".
Taja wani dogon tsaki ganin bazai bata hanya bane yasa ta matsa gefe.
Wucewa yayi tare da cewa.
"Sai kiyi ai".
Ita dai bata bi ta kanshi ba, ta wuce cikin ɗakin.

A gigice ta nufi kan gadon tana kiran ta.
"Jannart! Jannart!! Jannart!!!".
Ta Ƙarisa kiran sunanta a gigice tare da hawa kan gadon ta jawota jikinta tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Abdul! Abdul kazo".
Da gudu Abdul ya nufi ɗakin sabida dama yana falo Juinad ne ya hanashi shiga.
Cikin ruɗani tace.
"Abdul kira min Daddynku. Ka gaya mishi jikin Jannart ya tashi".
Da sauri yace.
"Toh Mom amman bari in fara kiran Dr Lukman".
Ya ƙare mgnar yana kara wayarshi a kunne.
Ita kuwa Mom sai jijjiga Jannart daketa kokuma da numfashin ta takeyi.
Cikin rauni Abdul yace.
"Assalamu alaikum. Daddy".
"Na'am Abdul ya akayi ne?".
Alhaji idi sele Dakata dake zaune a Office nashi Barrister Kabir Saleh Dakata na zaune a gabanshi.
Ya amsawa Abdul da kulawa.

“Daddy jikin Jannart ne ya tashi, na kira Dr Lukman kuma baya ɗagawa".
Da sauri yace.

“Innalillahi Bari in kirashi yanzu-yanzu".
Ya ƙare mgnar da katse kiran.
Cikin kula Barrister Kabir Dakata yace.
"Yaya lfy kuwa? Jikin Jannart ko?".
Cikin damuwa yace.
"Eh".
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
Bari inje mu tafi asibiti".

Tuni kafin yayi wata magana ma ƙanin nashi ya fita.
Abdul ya kuma kira tare da cewa.

“Ga Abbanku na zuwa da likita".
Toh yace kana ya katse kiran.
Shiru yayi yana nazartar irin son da Ƙanin nashi keyiwa yaranshi, Especially ma Jannart yana mata wani irin so na musamman.
So na da ban a cikin yaranshi.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da meda kai ya jingina da kujera.
A hankali yake jujjuyawa, yana mai ƙoƙarin kauda tunanin da zuciyarsa ke kawo mishi.

Shi kuwa Barrister Kabir yana fita kai tsaye.
Asibitin Hamda
Ya wuce. Yana mai kiran babban Dr.
Yana tafe cikin gudu kamar maiyin doguwar tafiya.

Yana isa kai tsaye Office ɗin Dr Sajo ya wuce.
Yana ganinshi ya miƙe tsaye tare da cewa.
"A a Ƙanina! Ka iso, ko ina mara lafiyar?".
Cikin girmamawa da alamun tsohuwar amintaka yace.
"Barka dai Yaya Sajo, dan Allah kayi haƙuri mara lafiyar tana gida.
Ni kuma daga Campany’n Yays Dakata nake, so kafin in koma gida in ɗaukota komai zai iya faruwa, kasan matsalar cutar athsman shiyasa nace bari in biya mu tafi tare. Dan Allah kayi haƙuri".

Murmushi Dr. Sajo yayi tare da fara tattara abin buƙatarsa yana mai tuno amintaka da mutuntakar da ke tsakaninsa dasu a baya.
Cikin kuma kula da amintaka yace.
"Ba komai ƙanina muje, dama na gama yau bani da aiki".
Cikin jin daɗi ya juya ya fita, shi kuwa yana biye dashi a baya.

Motarshi suka shiga, shiyasa yake taka motar da kyau.
Tsoro yakeji yasan yadda ciwon ke wahalar da ita.

A can gida kuwa, gaba ɗaya Mom da Abdul sun rikice.
Ita kuwa Jannart tuni ta gama gigicewa ta fita haiyacinta, fuskarta nan tayi jazir.
Sai fuzgo numfashin takeyi da ƙarfi.

Wayar Abdul ne tai ringing yana ɗagawa yace.
"Abba jikin fa ya tsananta".
"Subahanallahi Abdul gani nan zuwa yanzu".
Toh yace kana ya katse kiran.

Suna isa kai tsaye cikin gidan sukayi.

Abban na gaba Dr Sajo na biye dashi a baya.
Suna shiga Dr. Sajo ya fara aikinsa, allura yayi mata dan samun dai-dai-ta numfashin ta.
Allah cikin ikonsa kuma a take ta fara sauƙe ajiyan zuciya, lokaci ɗaya jikinta ya fara sakewa.
Sai ga wani irin bacci mai nauyi ya kwasheta...

Kusan a tare suka sauƙe ajiyar zuciya baki ɗayansu.
Cikin kuma sauƙe numfashi Abba yace.
"Alhamdulillah".
Hakama Mom.
Abdul kuwa shiru yayi yana mai jin tausayin yar uwar tasa.

Dr. Sajo kuwa, harhaɗa kayan aikinshi yayi, kana ya kalli Barrister Kabir, gyaran murya yayi tare da cewa.

“Ciwonta yayi zurfi a jikinta, kuma bata bin doka da ƙaidar maganin yadda ya kamata".
Da sauri Mom tace.
"Ai ba'a bata magani Allura kawai akeyi mata duk wata".
Cikin mamaki yace.
"Allura kuma? Toh wacce iriyar Allura ce duk wata kuma!?."
Cikin sanyi Abdul yace.
"Gaskiya bamu san wacce iriyar Allura bace".
Da sauri Dr Sajo ya kalli Barrister tare da cewa.
"Wanne Dr ne yake duba ta?".
Numfashi mai nauyi Barrister ya sauƙe kana a hankali yace.
"Dr. Lukman ne".

Wani irin shiru Dr Sajo yayi tare da alamun nisan nazari.
Kana yace.
"Ok muje ko Barrister".
Toh yace kana suka nufi hanyar fita.
Sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Mom dake gyarawa Jannart din kwanciyarta, cikin nitsuwa yace.

“Kada ki damu, zata samu lfy in sha Allah, sannan zamu canza mata Dr da zai na kulawa da ita da kyau".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Mun gode".

A hankali Dr. Sajo ya juyo ya kalli Barrister Kabir dake jan mota, dan medashi asibitin sa.

“Ƙanina akwai buk’atar a canzawa Jannart likitan da zaina dubata.”

Cikin nitsuwa Barrister Kabir ya ɗan juyo ya kalleshi tare da cewa.
"Yaya Sajo meyasa!?".
Kafaɗarshi ya ɗan ɗaga tare da cewa.
"Noh ba komai, kawai dai ciwonta yanada buƙatar gamayyar likitocin zamani bawai a tsaya kan ɗaya ba, a samo wani shima ya gwada kwarewar sa".
Uhum Dr.Sajo bai tuna cewa da babban Lawyer yake mgna ba.
Cikin fahimtar wani abun Barrister Kabir yace.
"Toh ba matsala in sha Allah za'ayi haka. Amman ina zamu samu likitan?".
Da sauri yace.
"A wannan mai sauƙine, akwai wani Babban Doctor yarone matashi mai ƙuruciya da sanaiyar ilimin likitanci na juya da yau, kana harna gobe yana bincika yasan aikinsa, mun gamsu dashi, Dr Rayyern Mai-nasara."
Da sauri Barrister yace.

“Zakayi mana hanyar ganinshi kenan? Dan ance yana da wuyar gani".
Ya ƙare maganar yana yin parking.
Kai ya ɗan juyo ya fuskanceshi tare da cewa.
"Eh to Gaskiya yana da wuyar samu, saboda yawan aiyuka, kuma a wani sashin bashi da wuyar gani, in har kaje Mai-nasara Hospital ɗinsa, muddin dai yana ƙasar, toh zaka ganshi sai dai ko in baya ƙasar, in kuma bakayi sa'a ba, sai a turaka wurin wani Dr ƙaninsa da kuma amininsa ɗin ba shiba, tunda yanzu aikin Company's dinsa sun tasoshi gaba, dole ya samo wasu likitocin bayan shi.
Saɓanin da da shi kaɗai ke jan ragamar asibitin.
Amman idan nasa hannu na baku takarda zuwa gareshi kuna zuwa shi ɗin zaku gani".

Cikin gamsuwa Barrister yace.

“Alhamdulillah nagode matuƙa Yayana".
"Haba ba komai Kabir yiwa kaine. Yauwa sai kuma batun allurar da akeyi matan nan, abar yi matashi akwai buƙatar in santa, sannan ina son sanin sunan allurar".
Ya ƙare zancen yana fita daga cikin motar.
Cikin gamsuwa Barrister yace to.
Kana sukayi sallama.

Ganin lokacin sallan azahar yayine kuma yasa ya nufi masallaci.
Koda aka idar da sallah kuwa.
Gidan yayan nashi ya koma.


Ethiopia.
Dr Rayyern Mai-nasara ne. Tsaye cikin wasu tattausan Suit masu masifar kyau da taushi tare da sheƙi.
Inda Riga da wondon suit din suka kasance pink color masu dauke da zane-zanen fari, sai kuma neck tie ɗin shi daya kasance fari, yayinda long sleeve dinsa ma ta kasance white, takalmin dake kafansa kuwa pink color ne mai dauke da harafin R-M.
Sai kuma Diamond watch din dake hannunsa mai ɗan karen sheƙi da tsada.

Wayarshi kirar iphone 12pro max ne saƙale a kafaɗarshi yayinda ya mannata a kunne yana magana.
Kana kuma hannunshi ɗaya na riƙe da System ɗin shi. Daya hannunshi kuma na lallatsashi.
Bisa alamu aiki mai muhimmanci yakeyi.

Ga kuma wani irin masifeffen ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa da yake fitarwa.
Lallausan Sajenshi nan ya kwanta lib, yayiwa kyakkyawar fuskarsa kawanya sai sheƙi yakeyi.
Haka kuma Ɗan madaidaicin bakinsa mai jajayen lips na motsawa a hankali.

Yayinda siraran idanunshi suka fito ras, cikin ɗan siririn glass mai ruwan garai-garai, irin na Doctor's daya liƙashi cas bisa karan hancinsa.

A hankali ya juyo ya kalli Usman daya shigo cikin alamun shiri.
"Sir gani". Usaman ya fada anutse.

Da idanunshi yayi masa nuni da jakarsa, yana maici gaba da maganar da yakeyi a wayar.
"Uhumm". Yace tare da lumshe idonshi.

A can ɗaya sashin kuwa ba tare da damuwa ba Sulaiman yaci gaba da magana.
Sabida sanin haka Allah ya halicce Rayyern mafi akasarin lokuta maganar Uhumm, ne ko eh ko hmm koko a'a
Bai cika yawan surutu ba, da fari gani suke miskilanci ne, sai daga baya suka fahimci abin da gaskene. Dan muddin za'ayi ta surutu ko hayaniya ko magana da ƙarfi a kanshi ko kukan yaro ko babba, a take idanunshi ke kaɗawa suyi jazir, lokaci ɗaya ciwon kai ke rufeshi larurarsa.
Ido ya ɗan juyo yana kallon Usman dake tsaye gefenshi.
Yayinda kuma yake jin Sulaiman na cewa.
"Wallahi Rayyern ni kamanninku ya daina bani mamaki yanzu sai dai tsoro, Allah ko da yayi magana da hausa ko muryarshi iri ɗaya da Ramadan kuma".
A hankali yace.
"Hmmm Sulaiman social media ka biyewa ko?".
Da sauri yace.
"Dan Allah tsaya kaji, yaushe zaku dawo?".
A taƙaice yace.
"Jibi!".
Cikin fidda numfashi Sulaiman yace.

“Toh gashi kuma shi yaron yau zai taho Nigeria, ni nai zaton yau nema zaku dawo ince Allah yasa ku haɗu a jirgi kaga zahiri, abu kamar an dama kunu an raba har ɗan makolloto yake dashi irin naka fa".

Ɗan gajeren numfashi mai d’auke da gajiya Rayyern ya fesar tare da cewa.
"Uhmm, it’s Okay a gaida Baby".
Yana faɗin haka ya katse kiran.
Sai kuma ga wani kiran ya shigo.
Da sauri ya zauna bisa kujerar bayanshi kana ya amsa kiran.
Cikin tsananin girmamawa hade da ladabi da biyayya da kuma tarin mutuntaka yace.
"Assalamu alaikum".
A can ɗaya sashin kuwa, wani kyakkyawan mutum ne mai cikar haiba kamala ne, zaune.
Alhaji Bashir Muhammad Mai-nasara kenan, sai Mami mai ɗakinshi dake gefenshi.
Kana ɗan matashin ƙaramin ɗansu Dr Ramadan Mai-nasara na zaune gaban Abba'n nasu.

Cikin tarin so kula bege da kuma ƙauna,
Alhaji Bashir ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Wa alaikassalam".

Cikin jin daɗin jin muryar mahaifin nashi yace.
"Abba Barka da safiya".

"Barka dai Rayyanu".

Ido ya lumshe cike da son mahaifin nashi yace.
"Abba kuna lafiya?".

"Lafiya lau Alhamdulillah, ga Mamynku da Ramadan wai in tambaya musu yaushe zaka dawo, suna kewarka".

Murmushin gefen baki daya bayyana fararen kyawawan haƙoransa yayi, cikin kuma sauƙe numfashi yace.
"Nima ina kewarku Abba in Sha Allah yau ina hanya amman Abba kai kaɗai fa".
Murmushi yayi fahimtar cewa.
"Shi kaɗai yasan yau zai dawo kenan."
Ramadan kuwa murmushi yayi sabida jin abinda Hamman nashi ya faɗa.

Mamy kuwa Kekkyawar mace mai cikar haiba, murya ta ɗan ɗaga tare da cewa.
"Toh me zan dafa maka".

Idonshi ya lumshe fahimtar sun jishi kenan.
Cikin sanyi yace.
"Mamy'na komai ma".
Amsar wayar tayi tare da cewa.
"Cin zaƙi zai Barka kaci abinda zan dafa maka ko?".
Cikin fuskar annuri yace.
"Yesssss! Mamy".
"Toh shike nan Babana Allah ya kawo min kai lfy".
"Amin Amin Mamy".
Yace cikin lumshe

3 Comments On TUBALI
avatar
khadija-dauda

1 year ago

Reply

Pls inason littafin tubali

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to khadija-dauda

ki karanta anan

avatar
fatima-muhammad-8-7

12 months ago

Reply

Pls ina Sauran chapters din tubali naga wanna chapter 30 ya tsaya kuma bai kai kar she ba

Please Login or Register in order to submit comment