Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mgn da ƙarfi.
Cikin nitsuwa yace.
“Bana buƙatar had’a hannu daku a cikin kasuwanci na!!!".
Ya fad’i hakan in don’t care manner, domin iya gaskiyarsa ya fadi kamar yadda suka nemi ji.

Idanu suka zazzaro gaba dayansu.
Yayinda Dr. Lukman dake gabansa ta gefensa bisa hagu yace.

“Haba Dr.Rayyern ya zaka fad’i haka, agaban mutanen da yawancinsu sun haifeka, at least dai ai ya kamata ka daraja su ko dan sun fika gogewa a harkar tunda tun kan a haifeka suke juya kobo ta zama dubu...”

Wani irin kallo da Rayyern din ya watsawa Dr.Lukman d’inne yasashi saurin rufe bakinsa gum, saboda hatta hantar cikinsa saida yaji ta kad’a.

“Bazan had’a hannu dasu ba, na fad’a na kuma sake maimaitawa Ni DR. RAYYERN BASHEER MUHAMMAD MAI-NASARA bazan had’a hannu dasu ba!!!”
Ya fad’i maganar da muryar dake bayyana iya gaskiya, da kuma zallan rashin tsoro ko shakkar kowa dake wajen.

Gaba dayansu shiru sukayi sai Alhaji Ma’aji wanda yake da company'n Ma’aji and Sons ne ya d’an muskuta, tare da fad’in.

“Meyasa bazaka had’a hannu damu ba?”
Wayarshi ya ɗan zaro cikin aljihunsa kana ya ɗan danna kaɗan sannan ya medata cikin aljunsa tare da cewa.
"Awa ɗaya dana baku cikin ɗaƙiƙun rayuwata da Allah ya aramin, kunci 21mn saura muku 39mn, in kuma kun gamane zan tafi."
Cikin hatsala Alhaji Yawale yace.
"Toh meyasa kace bazaka haɗa hannu da mutane ba".
Juyowa yayi ya ɗan kalleshi kana yace.
“Sabida tafiyata da taku ba iri ɗaya bane.
Muddin muka ce zamu haɗa hannu, dole gefe ɗaya zai rinjayi ɗaya,
ta yiwu ku rinjayeni.
Ku ɓata min kekkyawan TUBALIn da aka ginamin.
Ko kuma Ni in rinjayeni in ruguza muku mummunan TUBALIn da kuka gina tun da daɗewa, in ɗauraku bisa tsarina wanda kuma nasan bazaku lamunci hakaba.
Dan haka muyi tafiyar a rabe shi yafi.
Domin ni dai a atafiyata talaka nake dubawa.
Ku kuma aljihunku kuke dubawa, ni kuma ba haka bace a tawa tafiyar, domin ahar kullum talaka nake dubawa, da rayuwarsu, manoman da suke noma abinci, su yake zuwa ya gagara yafi karfinsu, Yayinda ku kuma kunanan kuna juya abincin da suka noma da wahalarsu, yana zame muku manyan kud’ad’e, Sam baku damu da talakan daya noma abincin ko yaci ya koshi ba, ko bai cika wannan duk ba damuwar ku bace, saboda haka.
Bazan had’a hannu daku aci gaba da cutan talakawa ba, domin sudinma mutanene kamar kowa!!!”.

Wani irin murmushi mai cike da tarin ma'anoni Barrister Kabir Saleh Dakata yakeyi, yana mai kallon Rayyern ido cikin ido cike da alamun so, da kuma tsoro can ƙasan zuciyarsa.
Su kuwa sauran gaba ɗaya a hatsale suke

Cikin yanayi hasala Alhaji Idi Sale Dakata yace.

“Okay wannan dalilin shi yasa ka zagaya gaba d’aya, kan manyan manoman da ƙanana da suke sayar mana da abinci ka hanasu sayar mana, har sai sun gama sun ware wanda zasu ci kafun su kawo mana mu mu saya?.”

“K’warai kuwa hakane, saboda hakkinsu ne kuma guminsu ne, ya zama lallai tilas cutarwar da kukeyi musu ya isa haka, Manoma bawai bayinku bane, domin da ace babusu yau da dukkanku baku kai wannan matakin ba, har yaushe zaku daina ci gaba da cutan mutanen da suke taimakon ku?.”
Ya kai k’arshen maganan nasa, cikin wata irin Muryar dake bayyana, cewa a shirye yake da yayi fito na fito da kowanne daga cikinsu, Sam babu alaman tsoron acikin zuciyarsa.

Wani irin bak’inciki da kuma k’unci ne suka cika zuciyar Alhaji Idi Sale Dakata, wanda hakan yasa shi hasala, ak’ufule yace.

“Indai wannan k’udurin naka ne basai kana da rai da lafiya zaka cika saba, Lallai Tabbas ayi mugani idan zai yiwu!”
Cikin tsoro Barrister Kabir Saleh Dakata ya juyo ya kalli yayan nashi Alhaji Idi Sale Dakatan har ya buɗe baki zaiyi mgn kuma, sai yayi shiru ya juyo yana kallon Dr Rayyern Mai-nasara da yayi.
Murmushin dake bayyana izzarsa da fito da kwarjininsa, kana ya d’ago ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata.
Cikin bayyana rashin tsoronsa yace.
“Kwarai saida rai da lafiya ake komai, amma kuma abun jin dadin shine babu wani mai rayawa ko kashewa sai Allah, babu kuma wani wanda ya isa yin abunda Allah bai nufa ba, koda wayeshi kuwa.”

Sosai Alhaji Ahmed Tambari ya jinjina kanshi, hakama Barrister Kabir Saleh Dakata, fuskarshi suka zubawa idanu.
Suna tuno irin kamarsa da ya ƙalubalancu shekarun baya.

Dr Lukman kuwa rumtse idanunsa yayi sabida murya Rayyern na tuna mishi wata muryar data gabata.
Da ƙarfi ya kuma rumtse idanunshi sabida hatta ɗan maƙolloton wuyan RAYYERN irin na wancan mutumin ne.
Da sauri ya buɗe idanunsa jin Alhaji Abdu Tababa na cewa.
“Tabbas babu mai rayawa ko kashewa sai Allah amma.
Yaro ka san cewa komai akwai sanadi.
Toh Lallai watarana za’ayi sanadin da zuciyarka zata tsaya da bugawa ka kiyayi kanka.”

Alhaji Abdu wanda yake aboki ga Alhaji Idi Sale Dakata ya fad’i hakan cikin hasala.

Shikuwa Rayyern awannan karon dariya yayi harsaida fararen hakoransa suka bayyana, saboda shi gaba d’aya dattijawan ma gani yake kamar basu San mesukeyi ba, domin harya fara tunanin cewa girma ne kawai ya Kamasu.

Mik’ewa tsaye yayi ahankali tare da daukar glasss dinsa dake aje bisa table d’in, taku daya biyu yayi ya tsaya tare da juyowa ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata.

Fuskarsa dauke da wani murmushi mai rugurguza zuciyar magauta yace.

“Idan akwai Allah to babu wani wanda ya isa da juyya RAYYERN Mai-nasara dole ya dakatar da Dakata in dai kan sayan k’udiri ne.”

Cikin fushi Alhaji Idi Sale Dakata ya buga table din dake gabansa, tare da fadin.

“Karya kake yaro, wallahi kai karamin al'haƙine, domin kuwa mun munji da wayanda suka fika tauri da tsaurin ido ma, saboda haka kai ba komai bane.”

Still wani irin murmushi yayi Cikin kuma nuna halin ko inkula yace.

“Wai tsoro kuke bani ne?".

A hatsale Abdu Tababa yace.
"Isa muke nuna maka".

Ronƙofawa yayi kanshi kaɗan kana yace.
"Hmmmm nifa RAYYERN Ina da taurin kai, ni nan Rayyern babu wanda ya isa sakani abunda banyi niyya ba, haka kuma babu wanda ya isa sakani yin abunda zai sab’awa addinina, idan kuma kuna ganin wasa ne to Lallai magwaji ya gwada ya gani!!!.”
Ya ƙarashe mgnar da ɗan sauti.

Kana ya D’an rank’wafo bisa kan Alhaji Idi Sale Dakata, cikin hade fuska da kuma zafin zuciya yace.

“Ina raga muku ne kawai saboda waɗannan fararen gemun dake kan fuskokinku, amma akasin haka hmmm nima zan iya take kowa kuma ya taku!!!”

Yana gama fad’in hakan ya juya afusace ya fice daga cikin dakin taron.

Dai-dai lokacin kuwa mota k’irar Black Benz ta faka a farfajiyar wajen, ahankali Jannart ta zuro da kwawayan legs dinta waje, wanda suka sha dogon takalmi na al'farma, sannu ahankali kuma itama ta fito daga cikin motar gaba daya.

Wata irin fitinanniyar gown ce mai masifar kyau ajikinta. Yayinda ta yane kanta da mayafin rigar, wanda hakan ya fallasa asirin kyawunta mai daukar hankali, daga gefen damanta kuwa Abdull ne ya fito, inda hannayensa ke dauke da wasu manyan basket guda biyu.
Domin zuwa sukayi musamman dan kawowa su Daddyn nasu da kuma Barrister Kabir abinci, saboda sun shaida musu cewar suna da taron da zasuyi, shiasa Momy tayi girki na musamman aka kawo musu.

Dai-dai isowar Jannart steps din da zata haura zuwa cikin hall din, shi kuma Dr. Rayyern ya fito daga cikin hall din ransa a matuk’ar b’ace ga wani irin masifeffen ciwon kai wanda ihun dattawan nan suka sakar mishi, ga yatsarsa dake zogi dan baima sha mgnin da safe ba.

Karab idanunsu suka sark’afe acikin na juna, saidai kuma ganinsa da Jannart d’in tayi ne yasa ta saurin janye jikinta baya.

A cikin hall ɗin kuwa gaba ɗaya sun hargitse kowa da abinda ke faɗi.
Haka yasa Barrister Kabir Saleh Dakata miƙewa da sauri ya nufo woje yana mai bin bayan Dr Rayyern Mai-nasara.


Shikuwa Rayyern kasancewar afusace yake shiyasa ko sake kallonta baiyi ba, direct ya nufi wajen motarsa wanda hakan yasa Jannart ta bisa da kallo.
Har saida ya b’acewa ganinta.
Yayinda Barrister Kabir Saleh Dakata ma da yanzu ya fito sai binshi da idon yayi.

Abdull dake tsaye ne ya kalli Jannart tare da cewa.

“Ya dai kinsan sane?”

Dan kauda kanta gefe tayi, batare kuma da taja zancen ba tace.

“Eh muje kawai.”
Jin hakan ne kuma yasa Abdull Sakai.
Da sauri suka tsaya ganin ƙanin mahaifin nasu, sai dai hankalinsa baya kansu.
Motar Rayyern Mai-nasara ya zubawa ido.
Yana mai motsa lips ɗinshi a hakali.


Jin muryar Abdul ne ya sashi ɗan juyowa, ya amsa gaisuwar yayi tare da kayan kana yace.
Su tafi gida.
Daga nan suma suka juya gida.

Rayyern kuwa daga Cikin company din direct cewa yayi driver ya dawo dashi gida.

Hakan kuwa akayi suka nufo gida kai tsaye.

A nan Nassarawa G.R.A kusa.
Riyyam-nsra ne ke tsaye ajikin wani tamfatsetsen gate na alfarma.
Wanda garin yawon zafaye anguwar da sukeyi ne da tattaki shida Nasir ɗin shi suka gilma ta gidan.
nan kuwa Nasir yace.
"Riyyam-nsra ya tsaya suyi video a gate ɗin gidan.

A hankali yake shafa tarin sumar dake kwance akansa.
Ahmad dake tsaye agabansa yana rike da, wayar Riyyam dinne yayi dariya tare da cewa.

“Nifa wallahi yanzu kam nagaji da rik’e wayannan, tun d’azun kake cewa zakayi video da waƙar hausa amma ka kasa, sai kace wani bak’o a harkar.”

Dariya shima Riyyam din yayi tare da cewa.
"Kafa san hausar tawa kar inje bin waƙar bai hauba."
Murmushi Nasir yayi tare da cewa.
"No kada ka damu zaiyi."
Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da shafa sumar kanshi kana, ya ɗan ware sawunsa.
lokaci d’aya kuma ya nutsu, tare dasa Ahmad yayi start din videon, cikin abubuwansa irin na tiktodians daya saba, ya soma rawa tare da bin wata waka dake tashi acikin wayar, inda yake cewa.

“Niba gida ba niba mota ba,".
Yayi mgnar yana nuna gidan bayan nashi
Kana yaci gaba da cewa.
"Bamai tarin dukiya masu yawa ba, Babana shiga gwamna ba, ba shugaban k’asa ba ba kuma member ba".

Sosai Nasir yake murmushi yana jinjina mishi sabida yayi masifar kyau da bin waƙar hausa.
Cikin karsashin ganin Nasir na jinjina mishi yaci gaba da cewa.
"Banje makaranta maitsada ba, banje Dubai ba kuma banje London ba.
Gidanmu ba a G.R.A ne ba, ban d’auki selfie nasa Instagram ba.
Ko zana zamma saniyar ware wallahi ni baza na zam makaryaci ba!!!”
Sosai yake wani irin rawa mai ƙayatarwa yayi masifar kyau.

Dai dai lokacin kuwa Motar Dr Rayyern Mai-nasara ta kunno kai dai dai wajen gate din, Yayinda motar Ramadan ma ta kunno kai ta b’angaren hagu, saboda shima yanzun nan shigowarsa cikin layin nasu.

Atare suka ci wani irin birki tare da zaro idanu saboda G.....




Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻



By
*GARKUWAR FULANI*








📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 8
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE ne*

*Littafin TUBALI na kuɗine hamzarta ki biya kafin a gama free PAGE in saki a Group, ƙaramin group 500 special Group 1k ne, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin mtn ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp 09097853276*

Ganin Riyyam Nsra da sukayi, domin daga Rayyern har Ramadan kusan atare idanunsu ya sauk’a akan matashin yaron dake tsaye ajikin gate din gidansu.
Wanda shima kuma Rayyern din d’ago kansa kenan da zaiyi, ya sauk’e idanunsa akan na Rayyern dake zaune agaban motarsa, inda yake zaune akan kujerar mai zaman banza, ya zauna agaba dinne kuma saboda lokacin daya fito daga hall din taro, na Dakatas company ransa a matuk’ar b’ace yake, wannan yasa bai tsaya wani tantance inda zai zauna dinba, kawai sai ya bud’e gaban motar ya shiga ya zauna.

Sam kwata-kwata babu alaman murmushi akan fuskarsa, saima tsananin b’acin ran da yasa fatar fuskartasa tayi jajur, haka ma idanunsa, ga kuma wata yar jijiya da ta bayyana akan goshinsa, sosai yakejin kansa na d’anyi masa ciwo, wanda kuma hakan ya faru ne saboda d’an yawaita magana da yayi yau din, da kuma ihun da way’ancan dattawan suka dingayi masa tsakar aka.

“Laaah Hamma Rayyern!!”
Riyyam-nsra dake tsaye fuskarsa d’auke da tsananin farinciki da kuma mamakin ganin Rayyern d’in ya fad’a, yana mai d’an matsawa daga jikin gate d’in, kaitsaye ya nufo wajen da motar Rayyer’n d’in ke tsaye.

Still fuskarsa dauke da murmushi yace.
“Thank God dama zan sake ganinka anan kusa, jiya kun b’acemin a airport nasha wahala sosai awajen neman ku.”

Idanu Dr Rayyern Mai-nasara ya lumshe duk da cewar, baya iya jiyo abunda Riyyam d’in ke fad’a, amma ya daiga bakin yaron na motsi kuma ya karanto abinda yake faɗin.

Dai-dai lokacin kuwa daga cikin gidan, Baba Mauɗo ya wangale musu makeken gate d’in, wanda hakan yasa direct driver’n Rayyern din ya tura hancin motar ciki.

Wulgawan da motar tazo yine kuma yasa Naseer dake tsaye ya sauke idanunsa akan, wani handsome guy dake zaune acikin motar, wanda yake matuk’ar kama da abokinsa Riyyam-nsra.

Bakinsa ya wangale cike kuma da tarin mamaki yace.
“La Riyyam kalli wani maikama da kai.”

Murmushi Riyyam yayi tare da nade hannayensa akirjinsa, yana mai bin motar Rayyern da ta shige cikin gida da kallo.

Ramadan dake cikin motarsa kuwa, tun d’azu mutuwar zaune kawai yayi, tare da bud’e ido da baki yana kallon matashin saurayin, da yake ganinsa tamkar hoto copy din Yayansa Rayyern.
Lallai Tabbas wannan kamar da yake gani akan fuskar yaron, da kuma ta Hammansa Rayyern ta b’aci.

Cike da tu’ajjudi ya k’araso da motarsa zuwa bakin gate din gidan, tare dayin k’asa da glass din motar yana me sake Kallon yaron da har yanzu murmushi ke bayyane akan fuskarsa.

Ganin kuma yaron ya dan juya masa baya, ya kuma tare masa hanya ne, yasashi danna horn.

K’aran horn dinne kuwa yasa Riyyam-nsra da kuma Naseer juyowa, suka sauk’e idanunsu akan Ramadan dake kokarin tura hancin motarsa cikin gidan.

Idanunsu gaba d’aya suka zubawa fuskarsa, Yayinda lokaci daya Riyyam-nsra yaji wani irin abu ya daki kirjinsa, saboda Kallon fuskar Ramadan da yayi, ganin kuma kamar idanunsa na d’anyi masa gizo ne, yasashi sanya tafukan hannayensa yadan mutstsuke su.
Saidai kuma yin hakan da yayi ya sake tabbatar masa da cewar, bawai gizo idanunsa keyi masa ba, Lallai Tabbas fuskar wanda ke zaune acikin motar, tana shige da fuskar Mammy ce da kuma ta Zaytoon dinsa.

Wani irin mamaki ne ya lullub’esa, Yayinda Naseer kansa shima daya ga kamannin fuskar Mammyn Riyyam dana Zaytoon, akan ta Ramadan dake zaune acikin motar yace.

“Allahu Akhbar Allah Mai girma Riyyam kalli wani maikama da Zayton da Mammy’n ka, gacan kuma wani mai kama da kai, kodai y’an uwanku ne sud’in?”

Naseer ya kare maganar yana mai kallon, Riyyam wanda tuntuni ya nufi cikin gidan.
Ganin hakanne kuma yasa cikin sauri Naseer din rufa masa baya.

Riyyam-nsra kuwa yana k’arasa shigowa cikin gidan, Dr.Rayyern Mai-Nasara na fitowa daga cikin motarsa,
Haka ma Ramadan.

Cikin dan hanzari Riyyam din ya karasa, batare kuma da tunanin komai ba, ya ware duka hannayensa tare da fad’awa jikin Rayyern d’in, ya d’an rungumesa da k’arfi.

“Naji dadin ganinka sosai Hamma Rayyern, nanne gidanku?, waye wannan Hamma Rayyern?”

Riyyam-nsra yayiwa Dr. Rayyern duka tambayoyin, tare kuma da d’aga hannu ya nuna Ramadan dake tsaye, shima bakinsa d’auke da tarin tambayoyi.

Tsumammun idanunsa ya lumshe ahankali, tare kuma da sauk’e wata irin ajiyar zuciya, Tabbas kafun iyanzu yanajin zuciyarsa na matuk’ar tafasa, saidai kuma gashi yanzu lokaci daya yaji zuciyar tasa nayin sanyi.

Hannayensa yasanya ya d’an janye Riyyam daga jikinsa, kana ahankali yace.
“Eh. kanina ne, Ramadan.”

Murmushin matuk’ar mamaki da kuma Jin dadi Riyyam yayi, cikin halinsa na faram-faram da sakewa, ya rungume Ramadan din, kana da d’abi’arsa ta wayewa yace.

“Sunana Riyyam-nsra kuma naji dadin had’uwa dakai Hamma Ramadan.”

Murmushi mai dauke da wani irin Jin dadi, tare da zallan k’aunar yaron da yaji yana shigarsa alokaci guda Ramadan yayi, cikin kuma nuna zallan farincikinsa yace.

“Me too, amma wai a ina kasan Hamma Rayyern dina, da har kuke matuk’ar kama haka?”

Murmushi Riyyam-nsra yayi, kana cike da tsananin mamakin sautin muryar Ramadan irin tasa yace.
“Acikin jirgi muka hadu dashi jiya, nima nayi mamakin kamannin da mukeyi dashi sosai, amma kuma Allah babu yanda baya ikonsa, saboda haka ne ma ya zama Hamma na!!”.

Riyyam ya kare maganar yana me bin Dr.Rayyern da kallo, wanda tuni ya soma tafiya harya kusa isa kofar da zata sada shi da babban falon gidan.

Ramadan kuwa idanunsa yadan lumshe tare da sake rungume kyakkyawan matashin yaron ajikinsa, wanda ak’alla shekarunsa baza su wuce 21 to 22 years ba, Lallai yaji matsanancin son yaron ajikinsa, har yakai ga yanajin inama da ace yaron zai zamanto k’ani agaresa, kamar yanda shiya kasance kani ga Hamma Rayyern, Tabbas yaji gamsuwa da yaron acikin zuciyarsa, Yayinda kuma kamannin Hamma Rayyern din dake kan fuskar yaron, yasanya shi jinsa awani waje na musamman a zuciyarsa.

Hannun yaron ya kamo kana cikin kulawa yace.

“Masha Allah Riyyam-nsra mu shiga daga ciki, domin kuwa na kwad’aitu dason nunawa Abba da Mamy mu mai kama da Rayyern dinsu.”

Murmushi sukayi su dukansu, kana Riyyam ya sake rik’e hannun Ramadan k’am acikin nasa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin nishad’i, ji yake tamkar ba yaune farkon fara haduwarsu ba, yanajin kamar tuntun tuntuni ya sansu, acikin wani bari na jikinsa.

D’an juyowa Riyyam din yayi ya kalli
Naseer Ahmad dake tsaye, yana Kallon ikon Allah, tare da tu’ajjudin abunda ke faruwa.
Alama yayi masa akan ya biyosu, hakan kuwa akayi cikin dan sassarfa Naseer ya rufa musu baya.

Dr. Rayyern Mai-Nasara kuwa koda ya karasa cikin falon, direct part d’insa dake sama ya nufa, saboda ayanda yakejin kansa nadan sarawa, ba kuma yason wani abu da zaizo ya dameshi.

“Abba! Mamy! Abbana!! ku fito kuga wani abun ban mamaki!!!”

Cewar Ramadan dake shigowa cikin falon, hannunsa rike dana Riyyam-nsra.
Wanda kuma yanayin maganan nasa ne, cikin dan bayyana sautin muryarsa, ta yanda duk nisan dasu Abban suke zasu iya jiyosa, kasancewar kuma suna daya daga cikin bedroom din kasa, dake cikin falonne yasa, cikin sauri suka mik’e tsaye, tare da soma rige rigen fitowa asalin babban falon, saboda kiran da sukaji Ramadan d’in nayi musu, yadan tsinkar musu da zuciya.
Ai kuwa isowar su Ramadan din tsakiyar falon, yayi dai dai da fitowar su Abban.
Fitowar daya haifar musu da wani irin bugun zuciya, tare da matsanancin firgici hadi da zallan mamaki.

A matuk’ar mamakance had’i da tu’ajjudi, Mamy ta dafe kirjinta tare da sake, ware Idanunta akan matashin yaron da hannunsa ke sark’afe dana Ramadan, wanda idan ba k’arya Idanun nata keyi mata ba, Lallai Tabbas kamannin d’anta Rayyern ne, kwance akan fuskar yaron.

Cikin karfin halin daya kasa danne mamaki da tu’ajjudi’nta tace.
“Ramadan waye wannan? A ina kasa moshi? Kamar fuskar Rayyern nake gani akan tashi fuskar, ko kuwa dai idanuna ne keyimin gizon hakan?”

Murmushi Ramadan yayi, tare da sanya dayan hannunsa ya jawo Riyyam-nsra jikinsa, cikin kulawa kuma yace.

“Sam ko kad’an Mamy ba idanunki bane ke yi miki gizo, sunansa Riyyam-nsra, kuma tabbas yana matuk’ar kama da Hamma Rayyern dinmu, sannan Hamma Rayyern dinne ma ya samo shi, domin sun had’u ne a Ethiopia cikin jirgin da zai kawosu Nigeria.”

Shiru Mamy tayi tare da kafe yaron da ido.

Kamar dai yanda Abba ya kafesa da ido, baya ko k’yaftawa, domin tun Kallon farko da yayiwa yaron ya kasa dauke idanunsa daga kansa.
Wani irin bugawa yakejin zuciyarsa nayi, Yayinda wani abu ke tasowa tun daga cikin kasan kafarsa har zuwa tsakiyar kansa, Lallai Tabbas akwai kama aduniya, amma irin kaman Rayyern daya hango akan fuskar yaron tayi yawa.

Ramadan dake tsaye kuwa ganin irin yanda fuskokin iyayen nasu, ke cike da zallan mamaki ne yasa shi, sakin murmushi tare da jawo hannun Riyyam-nsra suka k’araso kusa da iyayen nasu.

Hannun Mamy Ramadan ya kamo, tare da d’an fad’ad’a murmushinsa, cikin kuma son basu cikakkiyar gamsuwa yace.

“Dan Allah Mamy ki kalli Riyyam da kyau, matuk’ar kama sukeyi da Hamma Rayyern dinki.”

Juyowa ya kumayi ahankali ya kalli Riyyam, wanda fuskarsa ke dauke da yalwatacciyar murmushi.

Shid’inma Murmushin yayi kana yace.
“Riyyam wannan itace Mamyn mu, Uwa d’aya tamkar da dubu, wannan kuma shine Abban mu, mahaifin daya kasance Garkuwa kuma jigo ga y’ayansa.”
Yak’are maganar yana meyiwa Riyyam nuni, da iyayen nasu shida Dr. Rayyern.

Yalwatacciyar fara’a ne ta bayyana akan fuskar Riyyam, Cikin matuk’ar ladabi da biyayya kuma yad’an durk’usa akan guiwowinsa, tare da bud’e bakinsa anutse yace.

“Abba da Mamy barkanku da gida, fatan zaku karb’eni kamar yanda su Hamma Rayyern da Ramadan suka amsheni, saboda daga yau Mamy kinzama mahaifiya agareni, haka ma Abba daga yau ka maye min gurbin Mahaifi.”

Kusan daina bugawa zuciyar Abba tayi, alokacin da yaji saukar muryar yaron acikin kunnensa, saboda tsananin yanda yaji muryar yaron tayi masa kama da ta Ramadan.

Yayinda daga gefe guda kuwa kwakwalwarsa ke neman juyewa, saboda wani irin tsohon tunani mai karfi dake neman dawowa cikin lissafinsa, da sauri sauri zuciyar Abban ke bugawa, musamman ayanzu daya sauke idanunsa akan yatsun kafan yaron.

Mamy kuwa da ayanzu taji zuciyarta nayin sanyi, hannayenta tasa ta d’an d’ago yaron, tare da sakar masa murmushi kana cikin tsananin kulawa tace.

“Insha Allah Riyyam mun karb’eka hannu bibbiyu kamar yanda su Hammanka suka karb’e ka.”

Murmushin tsananin jin dadi Riyyam yayi, sai alokacin ne kuma ya dago kai ya sake Kallon Abban su Ramadan d’in, da har yanzu ya kasa dauke idanunsa akansa.

Abban kuwa ganin Riyyam din na Kallon sa ne, yasashi dan sakin murmushi.

Ramadan kuwa hannun Riyyam din ya kama suka dawo cikin falon suka zauna, direct gaban fridgen dake cikin falon ya nufa, inda ya d’auko wa su Riyyam din bottle water da kuma fresh milk mai sanyi, ya basu suka sha shida Naseer da ya zama ɗan kallo.

Mamy kuwa da kanta ta k’arasa dining table, inda ta had’a musu lunch, saboda tuntuni rana tariga tayi.

Ramadan kuwa cike da soyayya yaja su Riyyam da kuma Naseer suka karasa kan dining table d’in.
Bayan kuma sun zazzauna ne Mamy tayi serving dinsu, inda ta zuba musu lafiyayyar jalop rice din da tayi, wanda yasha kayan vegetables, da pepper chicken.

Turawa kowannensu abincin tayi gabansa, tare dajan kujera itama ta zauna, anan kusa da Abba wanda shima yanzun ya karaso ya zauna.

“Rayyern fa ko bai dawo ba?”
Mamy ta tambayi Ramadan dake shirin kai loman abinci baki.

“Ya dawo amma ya haura sama, na daiga mood d’insa, kamar he’s tried, i think kuma stress din aiki ne.”

Ramadan ya fad’a yana mai hadiye abincin dake bakinsa.

Kai Mamy ta jinjina cikin gamsuwa kana kuma ta d’ago kanta ahankali ta kalli Riyyam-nsra, fuskarta dauke da murmushi tace.

“Masha

3 Comments On TUBALI
avatar
khadija-dauda

1 year ago

Reply

Pls inason littafin tubali

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to khadija-dauda

ki karanta anan

avatar
fatima-muhammad-8-7

12 months ago

Reply

Pls ina Sauran chapters din tubali naga wanna chapter 30 ya tsaya kuma bai kai kar she ba

Please Login or Register in order to submit comment