Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har yanajin tamkar ya rufe guards din da duka.

Sukuwa k’attin banzan, sun matukar ji haushin zagin da Alhajin yayi musu, aso da niyarsu kuma shine su tanka masa, amma kuma saidai tuna cewar zai iyasa a dauresu ne, yasa basu tanka masa ba, sad’ab-sad’ab haka suka kwashe komatsansu suka fice daga cikin gidan.

Junaid kuwa zaman dirshan yayi, yana Mejin wani irin tafasar zuciya, saboda alluran nasa ta motsa, sosai matukan da Barrister Kabir ya sharara masa suka tsaya masa arai.
Lallai Barrister Kabir din yayi sa’a, kasancewar shi kanin mahaifinsa, domin yau da ace wanine daban Yayi masa hakan ba Barrister din ba, yayi rantsuwa bindiga zaisa ya harbe mutum.

Acan b’angaren Barrister Kabir din kuwa, yana fita daga cikin gidan, motarsa da yayi parking awaje ya shiga, bayan yayiwa motar key ne kuma, ya saki wani irin Murmushi, mai kama da dariya.

Hakika irin wannan firgicin ya jima yanaso ya gani, akan fuskar Yayan nasa akan Jannart dama shima Junaid, wannan tsoron shiyake matukar so yaga yayi tasiri acikin zuciyarsu

“Tu kunnma Alhaji Idi Sale Dakata, wannan kadan daga cikin bangon littafin tashin hankalin da zaka fad’ane anan gaba.”

Barrister Kabir din ya fad’a abayyane, kana zuciyarsa cike da nishadi ya nufi gidan Dr Sajo domin dama duk abunda yakeyi dazun, pretending ne kawai ba komai ba.

Koda ya isa gidan Dr. Sajon kuwa, ya samu Doctorn na nan kasancewar yau din weekend babu aiki.

Har cikin falon Dr Sajon kuwa ya shiga, bisa jagorancin wani Dan matashin saurayi wanda zai iya kai sa'an Rayyern.
wanda kuma yake dan Dr Sajon ne.

Yana shiga cikin falon ya durk’usa guiwowinsa ak’asa, tare da kai goshinsa k’asa, yayiwa Allah Sujjada, wani irin farinciki yakeji acikin zuciyarsa, bayan ya d’ago daga sujjadan ne kuma ya kalli Dr. Sajo dake kallonsa yana murmushi, cikin matukar farinciki yace.

“Alhamdulillah Allah abun godiya, doctor shawararmu tayi, komai da muka tsara ya tafi yanda ya kamata, Insha Allahu yanzu kwata-kwata ma hankalinsu bazai tab’a zuwa kaina ba.”

Murmushi Dr Sajon ya faɗada lokaci daya kuma farinciki ya bayyana akan fuskarsa.

Barrister Kabir kuwa ci gaba yayi da cewa.

“Junaid ya daure kansa da kansa, da zaluncin da yakeyi wa Jannart tsawon shekaru.
yanzu shikansa Yaya Idi bai isa yayi wani tunani akan abunda ya shafeni ba, Alhamdulillah Allah.”

Still murmushi mai kama da dariya Dr Sajon yayi, cikin kuma jin dadin labarin da Barrister Kabir din yazo masa dashi yace.

“Masha Allah Barrister Kabir, wannan abu yayi dadi, haka mukeso yanzu kaga mun dauke hankalinsu daga kan komai, zasu tsaya wa abu daya ne kawai, inda kaikuma zaka ci gaba da bincike, da kuma kara Adana hujjojinka, sannan Jannart kuma tana killace a gidan mijinta, Alhamdulillah Wannan shine matakin nasara na farko da muka fara hawa.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace.

“Insha Allah, da sannu duk wani kulli zai warware, gaskiya kuma zatayi halinta, yanzu sunacan hankalinsu duk atashe, musamman shi Yaya.”

Dariya Dr Sajo yayi, tare da gyara zamansa, cikin ya bawa shirin nasu yace.

“Aikinmu yayi kyau gaskiya, Allah kuma ya dafa mana.”

“Ameen summa Ameen.”

Barrister Kabir din ya amsa, zuciyarsa wasai babu wani alaman damuwa.

Hira suka d’an tab’a kad’n da Dr Sajon, kafun daga bisani Barrister Kabir din ya tashi ya tafi.

Acan gidansu Rayyern kuwa, kusan atare suka jero wajen shigowa cikin gidan.
Wanda kuma dawowarsu kenan daga sallan asuba.

Abba, da kuma Dr. Rayyern ne agaba, sai Ramadan da Riyyam-nsra dake take musu baya.

Ahaka suka k’araso cikin babban falon dake k’asa, tare da neman waje kowannensu ya zauna.

Mamy kuwa sanin zaman shan coffee al’adar mazan gidanne, yasa tun kafun su dawo daga masallacin ta gama had’a musu coffee wanda yaji kayan k’amshi.

Ganin shigowarsu Cikin falonne kuma yasa, Mamy daukan coffee din tare da tahowa cikin falon.
Zama tayi a tsakiyarsu

Kana ta fara tsiyayawa kowannensu a mug ta mik’a musu.
Riyyam-nsra ne ya Karb’i Mug din coffee din da Mamyn ke mik’o masa, tare da tank’washe k’afafunsa, cikin yanayin jin dadi yace.
“Mamy ngd. Da wannan al'farmar, da na samu.
Wanda yake sawa nake ga kamar ina gaban Mammy na dan itama haka takeyi min
da zaran nadawo amasallaci sai ta bamu abun tab’awa.
wannan yana d’aya daga cikin abunda yasa naji zaman gidannan yafi min na hotel.”
Dariya Mamy da Ramadan sukayi, domin hatta Abba ma saida ya dan murmusa.

Shikuwa Rayyern gaba daya ma ya dauke wuta, Yayinda ya Kawar da kansa gefe, ahankali yake sipping coffee din, ko gefen dasu Riyyam din suke kuwa bai kalla ba.

Mamy kuwa bayan ta kammala had’a musu komai ne, ta mike tare da komawa kitchine, mug din coffee din da ta had’ashi musamman dan Jannart ta d’auka, Koda ta fito daga cikin kitchine din, batare da ta tankawa su Ramadan da Riyyam dake hira ba.
kaitsaye ta wuce dakin Jannart.

Ahankali ta murd’a handle din kofar falon ta shiga, kamar kuma yanda ta tsammata hakanne ya kasance, saboda babu kowa acikin falon.

Kaitsaye kofar bedroom din ta nufa, Koda taje tsayawa tayi abakin kofar tare, da d’an k’wank’wasawa kana cikin kulawa takira sunanta.

“Jannart.”

A can cikin Bedroom kuwa.
Jannart dake zaune akan sallayan jin muryar Mamyn na kiran sunanta ne yasa ta, amsawa aladabce.

Mamy kuwa dake tsaye, jin Jannart din ta amsa ne, yasa ta tura kofar dakin ahankali ta shiga, bakinta dauke da sallama.”

Ganin Jannart din da tayi akan sallayane kuma, yasa kata sakin Murmushi, cikin kulawa tace.

“Masha Allah Jannart kin tashi ashe.”

Kai Jannart din ta jinjina alaman Eh, lokaci daya kuma tayi kasa da kanta, cikin sassanyar muryarta dake bayyana zallan ladabinta tace.

“Mamy inakwana.”
Yalwataccen murmushi Mamyn tayi, tare da cewa.
“Lafiya lau Jannart, fatan kema kintashi lafiya ya jikinki?”
Cikin jin daɗi tace.
“Da sauki sosai.”
Jannart din ta bata amsa tana medan wasa da yatsun hannunta.

“Masha Allah, haka akeso Allah ya kara sauki”.
“Amin Mamy ngd”.
Jannart ta kuma faɗa.
Ita kuwa Mamy murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“Ga coffee nan mai zafi maza ki shanye shi.
zakiji d’umi cikinki zai ware.”

Mamyn ta fad’a tana me ajiye mata mug din Coffee din.

“Toh Mamy Nagode.”

Still Jannart din ta fada tana mekokarin gyara zamanta.

Mamy kuwa murmushi tayi tare da cewa.

“Ba komai Jannart, ki saki jikinki, Idan kinsha coffee din kuma zaki iya komawa bacci, ki dai samu ki huta kinji ko.”

Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamyn kuwa cike da kauna, hadi da yaba hankalin yarinyar ta juya ta fita.

Ganin fitar Mamyn ne kuma yasa, Jannart daukan coffee din ahankali ta soma sha, saboda dadin da coffee din yayi ne kuma yasa harta shanye feye da rabinshi, batare da ta farga ba cin cikinta yayi dumine kuma yasa aje sauran.
Alhamdulillah kuma ta danji karfi ajikinta.

Mamy kuwa tana fita daga dakin Jannart din, direct kitchine ta sake wucewa.
Dan soma shirin aikin breakfast.

Yayinda kuma har yanzu Ramadan da Riyyam ke zaune acikin falon suna tad’i.

Kasancewar tuntuni Rayyern ya tashi ya haura sama, Koda yaje dakin nasa ma kuma kwanciyaya yayi, saboda gaba daya Daren jiya baiwani samu isashshen bacci ba.

Cikin sa’a kuwa Yana kwanciya bacci ya d’aukesa.

7:30 pm dai-dai.
Mamyn ta kammala had’a duk wani abu da takeyi.

Ita da Riyyam ne kuma suka jere duk abincin akan dining table, Yayinda Abba da kuma Ramadan ke zaune acikin falon.

“Bismillah komai ya zama ready, Ina Rayyern bai sauk’o ba ko.”

Mamy ta fad’a adai-dai lokacin da take ajiye plate plates na cin abincin.

Jin abunda ta fad’ane kuma yasa Abba dake zaune yana karatun Alqur'ani juyowa ya kalleta, cikin tausasa harshe yace.

“Masha Allah, amma nikam daga yau na daina cin abinci acikin ku.
ana shiryamin nawa Acan dining table dina”

Murmushi Mamy tayi, cikin gamsuwa da kuma fahimta mijin nata tace.

“To shikenan Ranka ya dad’e Insha Allah, naka shirin ma na musamman zanna maka.”

Yar dariya sukayi, Yayinda Riyyam-nsra kuwa Kallon Abban yayi, cikin nishadi Yace.

“Abba Kai bazakayi irin na turawa bane.”

Murmushi Abban yayi, tare da girgiza kansa yace.

“To ni ai ba bature bane Riyyam.”

Kai Riyyam ya jinjina aransa yana mejin dadi, saboda akaron farko kenan da yaga Abban yayi masa murmushi, tabbas yaji dadin abun.

Mamy kuwa cewa tayi, Ramadan da Riyyam duk su taso suzo suci abinci.

Aikuwa dama kaman jira suke, zama sukayi akan dining table din, Yayinda Mamy da kanta tayi saving dinsu, kana Itama tayi saving din kanta.

Abba kuwa har yanzu yana nan zaune acikin falon.

Suna cikin cin abincinne kuma Mamy ta d’an d’ago Kai ta kalli Abban.

Cikin tausasa muryarta irin na mata masu ladabi ga mazajensu tace.

“Yauwa Alhaji, yarinyar nan Jannart kaga irin yanayin yanda tazo gidannan, komai anyisa ne asace a boye.
Hakan yasa batazo da suturun sawa ba, sai nake ganin maizai hana, Indai babu matsala a fita aje asamomata suturun sawa.”

Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwar abunda Mamyn ta fad’a yace.

“Tabbas ya kamata kam asamomata kayan sawa, tun dai ayanzu kam duk wani hakkinta ci da shanta da sutura jinya yana wuyan Mijinta ne, saboda haka ku tambayesa ya bada kudi, Idan yaso sai kije kiyi mata duk wata sayayya da ta dace.”

Kai Mamy ta jinjina, cikin kuma yin kasa da murya da alaman ladabi tace.

“Mijinta kuwa?”

“K’warai kuwa shid’in dai, ai yanzu duk wani nauyinta ya rataya ne akan wuyansa ne.
Hakkinsa ne dole kuma shi zai sauke dan haka ya fara da wurima.”

Kai Mamyn ta jinjina, kana a gamsashe tace.

“To shikenan Insha Allah zanyi masa magana.”

Daga haka kuwa babu wanda ya sake cewa komai, suka ci gaba da cin abincinsu.

Bayan sun kammala ne cin abincinnasu ne kuma suka dawo cikin falon.

Mamy kuwa Ganin lokaci ya danja sosai ne, yasa ta kalli Ramadan, kana cikin kulawa tace.

“Ramadan jeka kiramin Hammanku, gashi har kusan goma ko breakfast bai sauk’o yayi ba.”

“To.” Ramadan yace tare kuma da mik’ewa ya haura sama, Koda ya k’arasa d’akin Rayyern d’in, samunsa yayi acikin blanket yana ta bacci.

Batare daya tashesa ba kuma ya juyo, tare da dawowa falon.
Tun kafun ya zauna kuma ya kalli Mamyn tare da cewa.

“Mamy Hamma Rayyern fa bacci yakeyi, ni kuma gaskiya tsoron tashinsa nake kada na tashesa kuma ya hauni da fad’a.”

D’an Jim Mamyn tayi, tare da mik’ewa tsaye tace.

“Shikenan badamuwa bari na fad’awa Abban ku.”

Kaitsaye falon Abban ta wuce.

Koda taje zaune tasa meshi, zama tayi ad’an gefensa kana cikin tausasa Murya tace.

“Natura Ramadan ya kira Rayyern, amma yace bacci yake har yanzu bai tashi ba, ka kumasan Rayyern kwata kwata baya so atashesa Idan yana bacci kasan matsalar ciwon kansa.”

Kai Abban ya girgiza bayan ya tankwashe kafafunsa ne kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamyn, cikin bada umarni kuma yace.

“Yau dai kam atashesa daga baccin da yakeyi, saboda yana da kyau yasan cewar yanzu bawai lokacin kansa kawai yake dashi ba.
Yana da lokaci wata, maza ki tura Ramadan ya taso sa.”

Kai Mamyn ta jinjina, cikin Dan ladabtar da murya tace.

“Ramadan yace yana jin tsoron tashin sa, kada Yayi masa fad’a”

“To ke kije ki tasosa.”
Abban ya fad’a kaitsaye.

Jin hakanne kuma yasa Mamy yin shiru, saboda tasani Sam Rayyern bayaso Idan yana bacci azo atashesa any how, musamman kuma kasancewar yana da matsalan ciwon Kai, shiyasa Mamyn ma take gudun yin duk wani abu dazai takurasa, domin tun yana karaminsa, Idan yana bacci bata cika son tashinsa, saidai idan ya gaji ya tashi dan kansa.

Fahimtar hakanne kuma yasa Abba mik’ewa tsaye, tare da cewa.

“To ni bari naje na tasosa da kaina.”

Hakan kuwa akayi inda kaitsaye ya nufi sama, nan sashin Rayyern din.


Yana zuwa kuwa ya tura kofar dakin ya shiga.

Still Rayyern din bacci yake.
Yayinda ya lullub’e duka jikinsa da blanket.

Karasa shigowa dakin Abba yayi,
Idanu ya ɗan zuwa fuskar Rayyern ɗin yana mai tuno wata kamanceceniya.
Numfashi ya ɗan fesar tare kuma da matsowa ya daura hannunsa dai-dai kan wuyan Rayyern din, Jin da yayi jikin Rayyern d’in babu alaman zafi ne, yasa shi soma kiran sunansa a nitse.

“Rayyern! Rayyern!! Rayyern!!!.”

Abban ya kira sunansa sau uku cikin kuma yanayin Dan daga murya.

Take kuma sauti da Amon muryar Abban ya ratsa kunnuwansa, wanda hakan ya sashi soma bud’e lumsasssun idanunsa ahankali, lokaci daya kuma jijiyoyin kansa suka amsa.

Saidai Ganin Abban nasa da yayi atsaye ne yasashi karasa bude idanunsa.

Abba kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa.

“Katashi daga wannan baccin da kakeyi kaje kaci abinci, sam baka karya ba, sannan kuma ka kawo kudi za’aje a iyawa matarka sayayya.”

Jin an ambaci mata ne kuma yasa shi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin zallar yanayin shagwab’a yace.

“Abba kudi kuma, ni fa banida kudi.”

Tsareshi da ido Abban yayi, kana cikin tsare gida yace.

“Ka kawo kudi za’ayiwa matarka sayayya nace, ko kamanta cewar yanzu duk wani ci da sha da tufatarwar ta yana wuyanka ne?”

Bakinsa ya d’an tura gaba, kana cikin lumshe ido, ya mirgina gefe tare da saka hannunsa akan bedside drawer, ya d’auko Atm card d’insa, mikawa Abban atm card din yayi, still yana ta tura baki tamkar wani karamin yaro.

Abba kuwa karb’an atm card din yayi, batare daya sake cewa Rayyern din komai ba ya juya ya fice sabida yasan Ramadan yasan pin number sa.

Yana fita kuwa Rayyern ya sake langwab’ar da kansa, cikin wani irin takaicin yarinyar da aka tashesa daga baccin da yakeyi ta sanadiyarta, kwana daya kawai tak da tayi agidannasu, yau gashi har an fara takura rayuwarsa da shiga sabgar sa a kanta.


Abba kuwa Koda ya sauko kasa, atm card din ya bawa Mamy tare da cewa.

“Kisaya mata duk wani abu da kikasan zata buk’ata, maganan suturun sawa kuma ki saya mata isassu, komai da komai ahada a saya mata.”

“To Insha Allah, zan saya mata duk wani abu daya dace.”

Ramadan dake gefe ne kuma yace.

“Mamy nida Riyyam zamuyi miki rakiya, ko Riyyam.”
Ya ƙare mgnar yana kallon Riyyam-nsra.
Kai Riyyam ya jinjina cikin sauri, hade da cewa.

“Eh Mamy zamu rakaki, Ado Bayero Mall zamuje ko Jifatu, ko kuma Mudassir and Brothers?”

Murmushi Mamy tayi, tare da cewa.

“Shoprite dindai zamu fara zuwa, saboda nasan akwai komai da komai, Idan akazo b’angaren dogin riguna kuma, sai muje Jifatu, yanzu dai bari naje na shirya saina zo mutafi.”

“To.”
Suka amsa mata.
Ramadan kuma juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
“Wai ni kam yaushe kasan Kano haka!?.”
Kai ya shafa tare da cewa.
“Nida jihata ƙasata!”.
Kiran wayarshi da akayi ne yasa baibi ta kan furucin Riyyam-nsra ba.

Yayinda ita kuwa Mamy kaitsaye bedroom dinta ta wuce, bayan tayi wankane kuma ta shirya kanta acikin, wani tsadadden leshi, tare da yafa mayafinta cikin kamala ta fito.

Kaitsaye kuma d’akin Jannart din ta nufa.

Koda ta shiga falon, yanzun ma bata iske Jannart dinba shiyasa kaitsaye ta wuce cikin d’akin.

A dai-dai lokacin kuwa Jannart din, zaune take abakin gado, hannunta rike da wani dan littafi na turanci tana karantawa, wanda kuma yana daya daga cikin, yan abubuwan da ta taho dashi.

Ganin Mamy da tayi ne kuma, yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa, Mamy kuwa murmushi tayi, kana cikin kulawa tace.

“Jannart nida Ramadan da Riyyam zamuje kasuwa, sannan Abbanku ma zasu fita yanzu saboda naji dazu suna magana da Baba Maud’o akan cewar zasuje wani waje.”
Cikin girmama tace.
“Toh Mamy sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya”.
Amin Mamy kana ta daura da cewa.
“Yanzu ki fad’amin me dame kikeso asayo miki Idan munje.”

Kai Jannart din ta dan sunkuyar k’asa, cikin sanyin murya, had’i da tsantsar ladabinta ga Mamyn tace.

“Mamy duk abunda kika sayamin yayi.”

Kai Mamyn ta jinjina cike da gamsuwa kuma tace.

“Masha Allah! To bari muje saimun dawo ko. Idan zaman dakin ya isheki, zaki iya fitowa falonki kisha iska, ko kallo kiyi nasan zai d’ebe miki kewa kafin mu dawo”.

“To Mamy, amman sai yaushe zaku dawo ne?”.
Jannart din ta tambaya, cikin tausasa murya.

Murmushi Mamyn tayi, again kuma itama cikin kulawa tace.

“Jannart kinsan yanayin kasuwa, Idan ka shigesa sai abunda Allah yayi, kana lisssafin zaka dawo da wurwuri, kuma sai kaga ba haka abun yake ba.”

Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamy kuwa ta cigaba da cewa.

“Ni kaina bansan yaushe zamu dawo ba, saboda iya yanayin cikowan jama’a,n da muka samu, iya jimawan mu, amma dai Ina da yakinin bazamu wuce azahar ba.”

“Mamy har azahar.”
Jannart din ta tambaya fuska a karye.

“Eh mana Jannart, domin ya danganta da irin abubuwan da zamu saya, kuma kinga yanzu ma ana neman wajen karfe sha d’aya bamu tafiba.”

Kai Jannart din ta jinjina tare da gyara zamanta, tace.

“To Mamy saikun dawo Allah ya tsare.”

Da “Ameen.”
Mamyn ta amsa, harta juya zata fitane kuma idanunta suka Sauk’a, akan breakfast din da ta kawowa Jannart din, wanda ko tab’ashi batayi ba.

Kallonta Mamyn tayi, kana cikin kulawa tace.

“Jannart Meyasa baki ci abincin dana kawo miki ba?.”

Kai Jannart din ta dan sunkuyar kasa, kana murya asanyaye tace.

“Mamy banajin yunwa sosai ne, amma zanci zuwa anjima.”

“A’akam, banyarda da hakan ba, sam ban lamunci zama da yunwa ba sauk’o maza kici abinci kinji.”

Mamyn ta fad’a tana me kamo hannunta, ta zaunar da ita akan sofa, tare da matso mata kwanon abincin gabanta, cikin kulawa kuma tace.

“Kici abinci kinji, kada ki zauna da yunwa, domin yunwa tana illatar da lafiya, ko ke dinma irin Mijin naki ne, baku damu da abinci ba sai kayan kwalama.”

Shiru Jannart din tayi, kana Cikin matukar kunya, ta sadda kanta kasa, domin aduk sanda taji ance mijinta, wani irin abu ne takeji mai nauyi ya tsaya akan kirjinta to waye mijin? Ya yake? Me halinsa?.
Wadanan sune tambayoyin da takewa kanta tun jiya.

Mamy kuwa zuba mata abincin acikin plate tayi, tare da cewa.

“Idan kina buk’atar wani abu kafun mudawo, akwai kitchine anan cikin falon mu.
Taso ma muje na nuna miki.”

Mamyn ta fad’a tana me kamo, hannunta babu musu kuwa Jannart din ta mik’e, tare dabin bayan Mamyn suka fito, har cikin babban falon.

“Kinga wannan shine kitchine dinmu, wacccan kofan kuma anan part dina dana Abbansu Rayyern yake akwai kofar shiga da fita ta cikin falonmu wanda ba sai anbi ta nan ba.”

Mamyn ta fad’a tana meyi mata nuni da kitchine da kuma sashin su ita da Abba.

Kai Jannart din ta jinjina cike da gamsuwa.

“Can kuma dakunan k’asane irin Part ɗin dake sama ne. sai kuma sama inda anan bedroom na Rayyern, da kuma Ramadan suke, sai kuma extra part guda d’aya da yake can ta woje.
Sai nasu Baba Mauɗo, sai wanda kike ciki.
A can saman Mai gidanki yake.”

Mamyn ta k’are maganan tana meyi mata nuni da saman.

Jannart kuwa, kanta tad’an sadda k’asa, tare kuma da soma wasa da y’an yatsun hannunta, kana cikin sanyin murya tace.

“Mamy To meza’a girka yau d’in, kafun kudawo zan girka tunda dama ina zaune ne kawai babu abunda nakeyi.”

Murmushi Mamy tayi, tare da girgiza Kanta, kana cikin tsananin kulawa tace.

“A'a ki huta kinji Januart, bana son ki shiga kitchine daga yanzu.
Idan na dawo, zan girka abincin karki damu, ai bazamu wani jima sosai ba”

Dan juya kanta, tayi, saboda zuwan su Ramadan da kuma Riyyam kallonsu ta ɗanyi kana ta juyo ta kalli Mamy, atsanake cikin yanayin dake nuna biyayyarta tace.

“Da gaske Allah Mamy zanyi girkin, kinga zaku dawo a gajiye.”

Riyyam-nsra da yake karasowa wajennasu ne yayi saurin cab’e zancen da cewa.

“Please mana Mamy kibar My Aunty tayi mana girki yau, nasan abincinta dole zaiyi dadi.”

Jin muryar Riyyam-nsra dinne kuma yasa Jannart ɗin.
Dan dago da kanta, ta kallesu dai dai lokacinne kuma Ramadan ma
Ya karaso wajen.

Fuskarsa dauke da murmushi kuma yake Kallon matar Hamman nasa.

Cikin sakin fuska da kuma walwala yace.

“Good morning my beautiful Aunty, ya kwanan bak’unta.”

Murmushi ta ɗanyi kana ta ɗan kalleshi.
Tare da cewa tace.

“Morning.”

Riyyam ne yayi saurin matsowa kusa da ita, tare da danyin kasa da muryarsa, cikin kulawa yace.

“Aha My Aunty kin tunani ko?”.
cikin ɗan sakin fuska ta gyaɗa mishi kai, alamun ta tunoshi haduwarsu a airport,
Cikin yanayin rawan kansa yace.
“Aunty Jannart ni sunana Riyyam-nsra, tiktokers nasan kinsani ko?”.
Murmushi tayi tare da gyaɗa kai, ganin yadda ya tsareta da ido.
Kuma tabbas ta tunoshi haɗuwarsu a airport.
Shima murmushi yayi tare da cewa.
“Yauwa shi kuma wannan Hamma Ramadan sunansa, kuma yaya nane, akwai kuma babban yayanmu Hamma Rayyern.”

“Please kiyi mana abinci maidadi kinji, wanda zaisa kunnuwanmu su motsa.”

Ba iya Mamy da Ramadan ba harta ita saida ta saki murmushi mai hade da dan dariya.

Mamy kuwa Ganin lokaci na k’ure musu ne yasa, tace.

“Jannart rabu da shirmen Riyyam, koma daki kije kici abincinki.
Maganan girki kuma tunda kin dage sai kinyi, ki dafa mana abu mai sauki kawai.”

Kai Jannart din ta jinjina, sannan cikin zazzakar muryarta tace.

“Mamy ku dawo lafiya.”

Da “Ameen” duk sauka amsa, inda Mamy ta had’a kan Ramadan da Riyyam sukayi waje.

Itakuwa Jannart d’akinta ta koma, duk da cewar bata wani jin yunwa amma haka ta zauna ta d’an ci abincin, bayan ta kammala ne kuma ta d’aura da, lemon strawberry da Mamyn ta had’o mata dashi.
Gyatsa mai sanyi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Kana ta yunƙura
A nitse ta mik’e tsaye tare da d’aukan plates din da taci abincin ta fita dashi.
A hankali ta buɗe ƙofar falon nata.
Kana ta sako kanta.
Cikin Babban falon.
Numfashi ta dan fesar sabida wani irin masifeffen sanyin AC'n da suke busowa duka biyu.
A hankali take takowa har ta iso tsakiyar falon.
“Masha Allah, Mamy ba dai tsabta ba”.
Ta faɗi haka tana jujjuya kai tana kallon komai doke cikin falon.
Tsab-tsab sai ƙamshi da sanyi daya wadaci falon.

A hankali ta juyo ta nufi Dinning area.
Tray'n dake hannunta ta ajiye kam table ɗin.
Kana ta juya a nitse.
Ta dawo tsakiyar falon.
Gaban tv ta nufa.
Sabida shiru da gidan yayi sai taji kamar tana tsoron gidan.
TV'n ta kunna cikin sa'a kuma kan tashar Sunnan TV yake.
Inda aka saka sautin muryar Malam Sulaiman.
Rage sautin tayi dai-dai misali.
Kana a hankali ta juya ta nufi Dinning area.
Tray'n data ajiye ta ɗauka a hankali ta nufi Kitchen kaitsaye.


“Wow. Masha Allah”.
Ta kuma faɗa tana mai bin tsarin Kitchen da kallo komai tsab-tsab.
Kai tsabta rahmace.
Ta kuma cewa tana mai
nannad’e hannun rigarta.
Tare kuma da k’arasawa gaban sink, plates din da taci abincin ta wanke, bayan ta kammala wanke wanken ne kuma.
Ta ɗan tsaya jim a tsakiyar Kitchen din.
Cikin sanyin murya tace.
“Toh me zan dafa?”.
Tayi mgnar alamun tambayar kai da kai.
Kanta ta ɗan jinjina kana matso gaban Fridge guda biyu dake cikin Kitchen din.
A hankali ta bud’e babban deep freezer
Kai ta jinjina tare da ƙara matsowa.
Gaba daya cikinsa shak’e yake da kayan Miya, hadi da kuma naman, Rago, Saniya, da kuma naman kaji, sai kifayen da tuni sun daskare ma acikin fridgen.

Naman kaza ta d’ebo d’an da-dai.
bayan ta wanke naman ne kuma ta zubashi acikin tukunya tare da kunna gas ta d’aurashi akai, al'basa ta ɗauka wanda ta gani a jere cikin wani da karfe.
Mai yawa ta yanka kana ta watsa a cikin naman.
Kana ta ɗan kalli gefenta inda wasu robobi farare masu marafe pink color ke jere, da kayan bukatu kamarsu. k’amshi, da dandano.
garlic, kanumfari da kuma maggi Corry ta saka.
Kana ta meda marfin ta rufe.
Sai kuma taja kujera ɗaya dake gaban ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar Kitchen din ta zauna tana mai tunanin to me zata dafa musu.
Lokaci ɗaya.
Gidan ya cika da ƙamshin tafashen.
A hankali ta ɗan juyo ta kalli tukunyar daketa fidda tururi mai masifar ƙamshi.
Ganin naman na dahuwa ne kuma yasa ta mike ta sake bud’e fridge din, inda ta ibo.
Pease, green beans, carrot, green pepper, red chilies, cabbage, cucumber, onion, and liver, tsayuwa tayi na musamman inda ta yanka kowannensu, awaje na musamman, saidai Banda carrot wanda tayi greeting d’insa.

Bayan ta kammala duk wayannan dinne kuma, kazan na gama dahuwa.
Ta sauƙeshi kana ta ɗauki kaskon suya ta doro tare da zuba mai.
Kana ta fara soya shi sama sama.
Tana gama ta ajiyeshi gefe.
Kana ta ɗauko kayan miyanta duk abin buƙata
tare fara aikinta a nitse ta hada masa pepper onion chicken soup.
Gaba ɗaya kwamshin ya ƙara de ko ina.

Tana kammala had’a kazartata kuwa ta d’aura shinkafa kasancewar, fried rice and coleslaw takeson yi.
Da ɗan hanzarin taci gaba da aikinta yanayi tana ɗan jujjuyawa da waige-wauge na bakunta da kaɗaici.
Cikin abunda bai wuce awa ɗaya da rabi ba kuwa ta kammala, had’a abincin acikin babban food flask.

Bayan ta gama da abincinne kuma ta dawo b’angaren drinks.
Shaka mai dadin gaske ta had’a musu, sai kuma pineapple and orange juice.

Cikin abunda bai wuce 50mn ba ta gama haɗa abubuwan shan, gidansu Rayyern din gaba d’aya ya kacame da k’amshin daddad’an girkinta.

Ganin akwai sauran lokaci ne kuma yasa ta, had’a fan cake ta somayi.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, sai yanzu yake tashi daga kwanciyar da yayi, ahankali

3 Comments On TUBALI
avatar
khadija-dauda

1 year ago

Reply

Pls inason littafin tubali

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to khadija-dauda

ki karanta anan

avatar
fatima-muhammad-8-7

12 months ago

Reply

Pls ina Sauran chapters din tubali naga wanna chapter 30 ya tsaya kuma bai kai kar she ba

Please Login or Register in order to submit comment