Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanayin yanda yakejin kansa a matuk’ar gajiye ne kuma, yasa bai wani bata lokaci wajen yin wankan nasa ba, bayan ya kammala wankanne kuma ya dauro alwala, kasancewar haka ya sabarwa kansa, baya tab’a kwanciya babu alwala.

Ahankali ya murda handle din bathroom din ya fito, hannunsa rik’e da wani towel, Yayinda gargasan jikinsa kuwa ke jik’e da ruwa, sunyi wani irin kwanciya lub, wanda kuma hakan shiya sake bayyana hasken fatarsa.

Cikin yanayin nutsuwar daya zamar masa sabo, ya tsane duk jikinsa, tare da karasawa gaban dressing mirror ya shafa mai ajikinsa, bayan ya kammala shafa maid’inne kuma, yabi jikinsa da wani men body spray mai kamshin gaske.
Yana kammala duk wani abu da zaiyi kuwa, ya k’arasa gaban wardrobe dinsa, tare da ciro wani sabon towel ya daura akan waist d’insa, yayi hakanne kuma saboda sometimes yafi jin dadin bacci, idan babu wani kaya mai nauyi ajikinsa, kamar dai towel yanajin dadin bacci da towel sosai.

Numfashi ya fesar adai-dai lokacin da yayi amfani da wani remote, wajen yin off na hasken wutan dake cikin dakin.

Anutse ya haura saman tattausan gadonsa, tare dakai hannunsa ya kunna two bedside lamp din dake gefen gadon.

Ai kuwa yana ajiye kansa akan pillow, yaji sautin kiran waya na tashi daga gefensa, hannunsa yasa yadan dafe kansa akasalance, saboda Allah Yasani kwata kwata at this time bayason damuwa. Idan ya gaji bacci kawai yake so yayi, domin da hakanne kawai zaiji he’s okay.

Kallonsa ya mayar ga inda Ramadan ya ajiye masa wayoyin nasa uku, wato samsung da kuma iphone d’insa wacce, mental problem dinnan ta dazu ta kwankwatsa masa da tsinin takalmin ta, wanda dududu yasan kudin takalmin nata bai wuce 10 to 12k ba, amma gashi tazo tayi masa asaran dubu daruruwa sai kuma yar karamar woyar.

Jawo wayoyinnasa yayi ahankali tare da ture iPhone d’in gefe, ya dauk’i Samsung S21 ultra din da take ta ringing, ganin sunan Sulaiman na yawo akan screen d’in wayarne kuma, yasa shi picking call d’in.

Koda ya amsa sallamar da Sulaiman din keyi masa kuwa shiru yayi, sai shi Sulaeman d’inne, daga can
b’angaren yace.

“Ya akayi nak’ikk’ira d’ayan layinka akashe, sai yanzu na samu wannan? Ykk fatan dai kana lapia, sarkin rainin hankali shine harda wani cemin ba yau zaka dawo ba, kai dai kam Rayyern naga randa zaka daina miskilanci.”

Idanunsa ya d’an lumshe, tare da sauke ajiyar zuciya, kana agajarce yace.
“What’s up ai gani nadawo ko?.”

Kai Sulaiman ya girgiza domin kuwa idan da sabo ya saba da halin Rayyern Mai-nasara.

“Nothing nakiraka na sanar dakai kada ka manta, gobe ne fa taron likitoti da za’ayi hope zaka je ai?.”
Sulaiman ya fad’a da kulawa.

“Insha Allah.” Still ya fada yana me gyara kwanciyarsa.

“Okay to saida safe kurman dole, mitsss mutun baya gajiya ma da shirun.”
Sulaiman ya fad’a yana me katse kiran.

Rayyern kuwa ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da fesar da wani irin numfashi.
"Ashyhhhhh". wanda kuma yayi hakanne saboda zogi da yakejin yatsar k’afarsa nayi masa, duk da kuwa yasha magani, amma dai har yanzu yakanji k’afar nad’anyi masa zogi.
Labb’an bakinsa ya cije da d’an k’arfi tare da rumtse idanunsa, lokaci daya ya soma tuna yanda yarinyar tayi masa babban b’arna, kuma wai dan saboda tsabar raini, ko hakuri ta kasa basa dan girman kai, sai wuki-wuki da ta soma yi masa da mayun idanunta.

“Mchewww.” Yayi tsuka abayyane tare da cewa.
“Da wani dan bakinta kaman na tsuntsu, dama irin wayannan ƴan yaran. Sam ba kai daya garesu ba.”

Yakai karshen maganan yana sake gyara kwanciyarsa, tare da sakin kowanni irin tunani ya kama ambaton sunan Allah Acikin ransa, da haka bacci ya d’auke sa, yau ko samun daman duba system d’inshi baiyi ba.

Taheer Quest Palace.

Riyyam-Nsra ne kwance akan makeken bed din dake cikin d’akin hotel d’in daya kama.
12:30 am kenan amma har yanzu wayarsa kirar iphone 11pro ne ke rik’e ahannunsa, Yayinda yayi kwanciyar nan irinta rub da ciki, gaba d’aya hankali, tunani da kuma nutsuwarsa ya badasu ne ga wayar tasa, Inda yake ta receiving DM da kuma comments na mutane, akan videos d’in daya sake d’azu na shigowarsa Nigeria, inda mutane da yawa kanyi masa message akan cewar, suna matuk’ar son su had’u dashi, ciki kuwa harda y’an mata masu tambayarsa awanni masauk’i yake, domin acewarsu zasu kawo masa ziyara, burin mutane da yawa shine su had’u dashi suyi videos, wasu kuwa zallan kyawunsa ne yake rud’arsu, wanda hakan yasa suke bayyana maitarsu afili, ko kunyar kai da addininsu basaji, amatsayinsu na musulmai, kuma yaya mata, wanda kowa yasani Mace nada matuk’ar daraja, amma Ina wasu matan kam haka suke watsar da kansu kamar shara a bola.

Shikuwa Riyyam nsra ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewar, mutanen Nigeria nada matuk’ar mutumci da kuma iya karrama bak’o, sannan da yawansu suna nuna masa k’auna k’warai.

Bayan ya gama amsa DM na mutane ne kuma yayi posting videos d’insa, wanda yayi musu shida Rayyern, Yayinda a k’asan videos d’in yayi godiya da irin karamcin da Rayyern d’in yayi masa, wayyo Allah ai kuwa kaman jira mutane suke, suna gama watching na videon ya fara samun new comments and DM, wanda shi kansu bazai iya amsasu duka ba, Yayinda mafi yawancin mata kuma suka sake haukacewa, nanfa kowacce ta fito ta fara maganganu kala-kala, harda masu tambayarsa wai dan Allah ko zai had’asu da kyakkyawan yayanshi.
Shidai ya gani amma baiyi reply ba.

Bakin shi ya dan zumbura gaba tare da cewa.
“Wayyo wannan Hamma Rayyern ɗin ya kashemin kasuwa fa, ji duk an shareni sai mgnarsa ake,”.
Ya kare mgnar da murmushi
Ana Cikin hakanne kuma saiga k’iran Nasir Ahmad ya shigo cikin wayar tasa.

Koda ya d’aga hira suka sha inda Nasir Ahmad ya dinga yi masa fadan cewa bai Kirasa ba, da kuma mai yasa zai sauka a hotel, saboda da ace yakirasa da bazai taba bari ya sauka a hotel ba.
Hakuri Riyyam din ya basa, daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu, ananne Nasir din ke tambayan a Riyyam hotel din daya sauk’a, bayan ya fad’a masa cewa a Taheer ya sauk’a ne kuma sukayi sallama, inda Nasir din ya shaida masa cewar, Gobe Insha Allah zaizo nan Taheer Guest Palace din, ya d’aukesa su tafi gidansu...!


Uhummmmm, akwaifa abu a wanga littafin, fatana dai Allah ya bamu aron rai da lfy, mu gama lfy, amman kam ku shirya karatu da murmushi a fuskokinku🤝🏻🥰




By
*GARKUWAR FULANI*







📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 7
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*FREE PAGE ne*

*TUBALI littafine na kuɗi, ki biya sannan in saki a Group inda zanke posting, biya 500 in saki a ƙaramin group, ko kuma ki biya 1k Hajia in saki a special Group kisha karatu cike da shaukin da salama hajiata, turo kuɗin ta asusuna na GTBank 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in kuma babu damar turawa ta banki zaki iya sayan katin mtn ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp na 09097853276*


Ahmad na kashe wayartasa kuwa shima ya kashe data d’insa, saboda zuwa yanzu bacci sosai yakeji.
Duk da cewar yana iya kaiwa har 2:00 am a online, amma dai yau kam yayi tafiya ya gaji sosai, dole yana buk’atar bacci.
Cikin abunda bai wuce 10mn ba kuwa bacci mai nauyi da gajiya ya d’aukesa.

Washegari.

Ajere suka dawo daga sallan asuba, Abba da Baba Mauɗo suna gaba kana su kuma suna biye dasu da Ari da Hadi.
Su a farfajiyar gidan suka tsaya wurin aiyu kansu.

Inda su kuma kaitsaye suka nufi babban falon gidan, koda suka k’arasa azaune suka samu Mamy hannunta rike da carbi tana ja, ganinsu da tayi dinne kuma yasa ta sakin murmushi, Yayinda Rayyern da kuma Ramadan suka gaisheta cikin girmamawa.

Itakuwa Mamyn fuska asake ta amsa musu, tare da tashi ta had’a musu coffee mai zafi.
Domin hakan d’abiarsu ce dukansu, idan suka dawo daga masjid sai sunsha coffee.

Bayan sun gama shan coffee dinne kuma kowannensu ya haura side d’insa.

Rayyern dai yana shiga bedroom d’insa, kwanciya yayi tare dajan blanket ya rufe jikinsa, bayan ya rufe idanunsa ne kuma, yasoma gabatar da azkhar d’insa na safiya, domin neman kariya daga wajen Allah Mahalicci mai kowa mai komai.
Yana cikin yin azkhar dinnasa ne kuma bacci ya daukesa.

7:00 am dai-dai kuma ya farka sakamakon alarm din gefen bed d’insa dake ta kara.

Kaitsaye toilet ya wuce tare da Sakarwa kansa ruwa, bayan ya kammala wankane kuma ya fito, inda ya kimtsa kansa cikin wasu had’add’u kuma tsadaddun riga da wando na leather suit navy blue colour, Yayinda long sleeve d’insa ta kasance sky blue, irin mai taushin nan.
Tabbas bak’aramin kyau kayan yayi masa ba, Musamman da ya bayyana asalin kwarjini, haiba da kuma cikar zatinsa.
Uwa uba kuma ga wani daddad’an kamshin turaren dake tashi ajikinsa.

Wasu had’add’un navy blue toms kirar companyn Italy, daya saka ak’afafunsa ne kuma suka sake kawata kyawun Shigar tasa, Yayinda tsadadden agogon dake daure akan tsintsiyar hannunsa keta shining.

Ahankali ya gama d’aura navy blue necktie awuyansa, tare da juyawa ya d’an kalli kansa amadubi, Tabbas shi kansa ya gamsu sosai da sosai, da shigar,
Dan shigar tasa ta d’aukar hankali ne, musamman ma k’awataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda take bak’a sidik mai yawan sheki.

Dan kawar da kansa daga Kallon madubi’n yayi, bayan yasa hannu ya d’auki briefcase d’insa, wanda ya saka duk wani abu mai mahimmanci nasa aciki.
Kaitsaye cikin takunsa dake bayyana nitsuwarsa ya nufi hanyar fita daga cikin dakin, direct kuma falon k’asa ya nufo.
Koda ya fito falon acan kitchine ya hango Mamy tsaye tana aiki.
Yayinda Ramadan kuwa ke gefenta yana taya ta y’an wasu aikace aikace-aikacen masu sauk’i da maza zasu iya.

Ido ya lumshe tare da d’an takowa zai shiga kitchine din, saidai kuma maganan da yaji Ramadan na fad’a ne yasashi d’an daka tawa.

Acikin kitchine din kuwa Ramadan ne tsaye yana ɓarewa Mamy Maggi yana mai cewa.

“Please Mamy tunda dai shi Hamma Rayyern yace muku, a fara yi min aure shi ko mgnar kansa ba yi yakeyi ba.
To nikam dan Allah da Manzonsa abani dama nayi dan Allah, Mamy kiyiwa Abba magana, nidai gaskiya aure nakeson yi.”
Ya kare maganar fuskarsa d’auke da zallar shagwab’a.

Mamy dake tsaye kuwa murmushi tayi tare da d’an girgiza kanta, kana tace.

“Nidai ba ruwana kayiwa Hamman naka magana, ya gayawa Abbanku cewar ya barka kayi aure, domin Abbanku zaifi saurin aminta da maganarsa.”

Sake shagwab’e fuska Ramadan yayi, tare da karyar da wuyansa gefe, kamar zaice wani abu kuma sai yayi shiru.

Rayyern dake bayansu kuwa ɗan guntun murmushi yayi, tare da d’an d’aga sautin muryarshi, Cikin kulawa yace.

“Don’t worrie Ramadan, Isha Allah zan gayawa Abba cewar kanason aure ya barka kayi aurenka, ku haifa mana babies dozin-dozin ko zamu samu gidan nan zai daina zama shiru.”

Juyowa dukansu sukayi suna kallonshi, Mamy kam mamakine ya isheta, sakamakon jin abunda Rayyern din ya fada, wato shi bazaiyi auren ba, saidai yasa ayiwa wani, har yau itakam tana mamakin hali irin na Rayyern, Sam kwata kwata mata basa gabansa, babu wata Mace daya tab’a gani arayuwarsa yace yana so, shidai hakanan yake tana fata Allah ya nuna mata sanjawarsa.

Shikuwa Rayyern juyawa yayi kaitsaye ya nufi bedroom d’in Abba.

Koda ya isa kofar bedroom din yana knocking, Abba ya bashi daman shigowa, bayan kuma sun sake gaisawa ne, ya bud’e briefcase din dake rike ahannunsa, wasu files ya ciro daga cikin jakar, wanda yayi aiki a kansu tun jiya da yake cikin jirgi, mik’awa Abban files d’in yayi tare da cewa.

“Abba ga way’annan files d’in already nasaka hannu a kansu, sannan daga ciki akwai takardun engines din da muka saya a US.”

Kai Abba ya jinjina tare da karb’an takardun, cikin kulawa yace.

“Masha Allah, yaushe ne zakaje meeting d’in da zakuyi, naji ance harda govenor da ma wasu manya manyan Doctor’s, sannan tare da Ramadan zakaje ne?”

Sake gyara zamansa yayi kana aladabce yace.

“A’a Abba bada Ramadan zamu jeba, saboda yau suna da aikin da zasuyi anan cikin hospital shida Sulaiman, maganan shiga meeting din kuma 11:00 am daidai ne.”

Again kai Abba yasake jinjinawa cike da gamsuwa yace.

“Masha Allah To Allah Yabada sa’a.”

Da Ameen ya amsa sannan ya mik’e tsaye, atare kuma suka fito shida Abban nasa.

Inda suka iske Mamy da Ramadan sun gama jere komai akan dining table.
Batare da wani b’ata lokaci ba kuma, suka zauna atare su duka suka soma cin abincin, kasancewar chips and sauce na egg da kuma fruit salad and ketchup Mamyn ta had’a musu, amma shidai yafi k’arfi wajen shan tea.

Acan b’angaren Riyyam-Nsra kuwa yau tun tashinsa yakejin zuciyarsa wasai, ga kuma wani irin nishad’i da yakejin kansa aciki, sosai yakejin shaukin Nigeria na shiga jikinsa.
Bayan yayi wanka ne kuma ya shirya kansa cikin, riga da wando masu kyau da tsada.

Waya da kuma earpiece d’insa ya dauka, kana anutse ya fice daga cikin dakin nasa, direct wajen hotel din ya fito, saboda hakanan yaji yanason zaga unguwar da yake, duk da kuma akwai restaurant acikin hotel din, amma yaji sha’awar zagawa ko zai samu wani difference restaurant dancin abinci.

Haka dai yadinga dan tattaki acikin unguwar, har dai ya samu wani had’add’en restaurant ya tsaya anan yaci abinci, bayan ya gama ne kuma ya sake dawowa hotel d’in daya sauk’a, To anan nefa ya samu Nasir Ahmad yazo, cikin farinciki shida Nasir suka rungume juna, tare da zama suka fara hirarsu na yaushe gamo..

Gaba d’ayansu zaune suke akan dining table suna breakfast.
Yayinda kowannesu ke gudanar da harkar dake gabansa, amma Banda Junaid daya kafawa Jannart ido, wacce take zaune akan kujerar dake facing nasa.

Tayi kyau sosai cikin shigar maroon abayan dake jikinta, wanda ta sake bayyana haske da kyaun fatarta, kasancewar bata saka bra bane kuma, yasa ta jawo mayafin abayan nata ya sauk’a harkan kirjinta.

Saidai kuma gaba daya kwata-kwata bata da wata nutsuwa awajen, saboda irin Kallon da taga Ya Junaid nayi mata, kwata-kwata ya hanata sakat, ta kasa koda cin abincin.

Daddy ne ya kalleta kana cikin tsananin kulawa da so yace.
“Jannart kici abinci mana, kodai jikin naki ne?.”

Kanta ta d’an girgiza ahankali, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace.
“A’a naji sauki Daddy.”

Kai Daddyn ya jinjina.

Shikuwa Junaid tsuka yayi azahiri tare da cewa.

“Bawani rashin lafiya dake damunta, iskanci ne da kuma zallan rashin gaskiya kawai, munafuka mai fuska da zuciya biyu”
Ya k’are maganar yana mai saka k’afarsa ta k’asan dining table d’in ya take ta.

Idanunta ta rumtse da k’arfi saboda zafin da taji na abunda ya mata.

Duk da cewar Daddyn nasu yaga hakan kuwa, amma baice kala ba saima ci gaba da cin abincinsa da yayi.

Abdul ma da tausayin yar uwartasa ya cika masa zuciya kasa cewa komai yayi, domin yasani koda wasa yayi magana, yanzu sai Ya Junaid din yayi kasa-kasa dashi.

Momy kuwa zuru tayi kawai tana kallonsu, domin har acikin zuciyarta ta kasa gane wani irin ahali ne take zaune acikinsu tsawon shekara da shekaru, har yau ta gaza gano manufar wasu daga cikin ahalin, abunda zata iya akullum kawai shine saka ido, da kuma jiran ranar da komai zai fito fili Jannart ta samu enci kamar ko wacce ɗiya a gidan ubanta, lokacin ɗaya taji idanunta na cicciko da hawaye sabida tausayin mairaini Jannart.

Asashin su Rayyern kuwa anutse duk suka kammala breakfast dinsu, bayan yayiwa su Abba da Mamy Sallama ne
kuma, suka fito atare shida Ramadan zuwa compound din gidan, inda ya samu Hadi driver d’insa na jiransa.

Ganin ya shiga mota ne kuma yasa Ramadan shima shiga cikin tasa motar.
Kaitsaye maigadi ya wangale musu Gatie suka fice daga cikin gidan.

Suna hawa titi kuwa kowannensu ya kama hanyar inda zashi, Yayinda Ramadan ya wuce Mai-nasara hospital kaitsaye, shikuwa Rayyern government Hause ya nufa, domin acanne babban hall din da zasuyi taron yake.

Gaba d’aya compound d’in had’add’en wajen aciki yake da tarin manyan Mercedes benz, G waggon, da kuma range rover iri da kala, motoci ne duka da suka amsa sunansu ta manyan masu kud’i, Yayinda kuma kowa dake zuwa wajen ya kasance babban Doctor ne maiji da kansa, wanda kuma ya k’ware da sanin makamar aikinsa.

Gaba d’aya kowannensu sanye yake da suit ajikinsa, Yayinda kuma suke tafe cikin nutsuwa.
Sai-dai kuma ga mamakina duk inda Rayyern ya wuce sai naga wasu daga cikin doctors din na bashi girma, like suna respecting nasa, duk da kuwa cewar wasu da yawa sun fisa shekaru, amma sanin makamar aiki da k’warewarsa yasa suke jinjina masa.

11:00 am dai-dai na cika kuma Gaba d’aya suka hallara acikin babban hall d’in, da tsaruwarsa ta zarce kwatantuwa, wanda cikin mutanen dake zaune awajen kuwa harda mai girma Govenor kano.

Nanfa bayan kowa ya zauna suka shiga gabatar da taron nasu, inda d’aya bayan d’aya daga cikinsu ke tashi suyi bayani gamsasshiya, wanda kuma hakan tamkar k’arawa junansu sani ne sukeyi.

Alhamdulillah dai sun gudanar da taron nasu yanda ya kamata, inda kowannensu ya fahimci d’an uwansa, bayan anci ansha ne kuma suka rufe taron da addu’a.

Koda suka fito compound na hall d’in, kuwa tsayawa gaggaisawa da junansu sukayi.
Inda ananne kuma Dr. Lukman ya mikawa Rayyern d’in hannu sukayi musabaha.

Bayan sun gaisa d’inne kuma yakeyi masa murnar k’arin nasarar da yake ta samu, da kuma irin cigaban daya samu arayuwa.

Dakai kawai Rayyern din ya iya amsa masa, domin magana bata wani fiye damunsa ba kuma ya gaji matuƙa da doguwar jawabin da yayi a likitance.

Har ya juya zaitafi ne kuma maganar da Dr. Lukman din ke fada ya dakatar dashi.
Inda yaji yana cewa.
“Please Dr.Rayyern Mai-nasara idan babu damuwa, muna gayyatanka wani zama da zamuyi yau a Dakata’s Company Nigeria Limited.”

D’an juyowa Rayyern yayi ya kalleshi, cikin rashin gamsuwa da kuma nuna shakka ako da yaushe yace.

“Ni kuma?”.

Da sauri Dr Lukman ya cire idonsa kan idon Rayyern ɗin tare da shakkarsa yace.
“Eh”.
“Gaskiya bansan da zaman ba, impact ma banida wannan lokacin.”
Ya k’are maganar agajarce yana mai duban agogon dake daure atsintsiyar hannunsa, hakanan yake Sam bayason wasa ko kuma raini.
Tabbas yana kiyaye kansa wanda kuma hakan d’abi’a ce dake cikin jininsa, awaje d’aya ne kawai zakaga murmushi da kuma fara’arsa, shine idan yana tare da Abbansa, Mamy da kuma Ramadan sai Baba Mauɗo, akasin haka kuwa Sam baya da sakewa da sauran wasu mutane, gentle mutum ne shi kuma straighforward, duk abunda ke bakinsa ya kuma san gsky ne shi yake fad’a, in ya ma daɗi ruwanka in kaji ba daɗi ma ruwanka.
Sam arayuwarsa baya ta'ammali da fad’an k’arya ko munafurci, hakan ba d’abi’arsa bace, then ba kuma ya shiga abunda bai shafe sa ba.

Lips Dr.Lukman yad’an cije cikin kuma lallab’awa dayin k’asa da murya, yace.
“Please Dr. dan Allah karkayi rejecting gayyatarmu, domin kuwa zama ne da za’ayi da shuwagabannin companies masu ci ayanzu, ba kuma wani jimawa za’ayi ba only 1hour ma yayi, dan Allah da Manzonsa Dr. Rayyern Mai-sanara ka samu ka halarta, koda ace na tsawon 30mn ne!!!”

Shiru yayi tare da d’an lumshe idanunsa, saboda gaba daya Dr. Lukman din ya kashe masa jiki daya ambaci sunan Allah.
Tabbas akan komai idan ka ambata masa sunan Allah to yakanji zuciyarsa ta sake.
D’an numfasawa yayi tare da bud’e bakinsa ahankali yace.

“Is alright ba damuwa zanje, yaushe ne taron?”

Cikin hanzari da kuma Jin dad’i Dr. Lukman yace.

“Yau ne kuma yanzu nima can na nufa Insha Allah, ko zamu had’a hanya sainayi maka jagora.”

Kansa kawai ya jinjina, batare kuma daya sake cewa komai ba, direct ya nufi wajen motarsa, yana shiga kuwa Hadi driver yaja suka fice daga compound din wajen, ganin hakanne kuma yasa Dr.Lukman ma cikin sauri ya shiga motarsa ya rufa musu baya.

Kusan atare kuwa suka iso babban company’n, Dakata wanda yakasance kayan masarufi ake sarrafawa aciki, Tabbas company’n yana da girma kuma yana da kyau ba laifi, saboda ank’awata cikinsa da abubuwa masu kyau.

Saidai kuma ga mamakin Rayyern kwata kwata babu wasu ma’aikatan kirki aciki.

Haka dai Dr.Lukman yayi masa jagora harzuwa babban d’akin da sukeyin taro.
Koda ya shiga gaba d’aya mutanen dake wajen basu wuce su 18 ba, wanda kuma dukkaninsu suna zaune ne akan royal chairs.
Yayinda wani babban dogon table, wanda aka cika samansa da kayan drinks yayiwa gabansu k’awanya.

Akan daya daga cikin kujerun wajen Dr. Rayyern Mai-nasara ya zauna, wacce kuma ta kasance itace take facing na Barrister Kabir Saleh Dakata.

Agefensa kuwa Alhaji idi Sale Dakata ne zaune.

A hankali ya juyo ya kalli wani dattijon daya zauna ɗaya gefen nashi, Alhaji Abdu Tababa kenan.

Numfashi ya ɗan fesar tare da ɗan kallon Barrister Kabir Sake Dakata.
Wanda tun shigowar Rayyern d’in ya kasa d’auke idanu daga kansa, domin hakanan yaji idanuwansa nayiwa Dr. Rayyern d’in Kallon sani, yanaji ajikinsa kamar a wasu shekarun baya masu tsayi ya tab’a sanin the same irin fuskar na, saidai kuma to Fuskar waye? Waya sani mai irin fuskar?
Tambayar da bashi da amsarta, bashi kuma damai amsa masa haka yasa ya gaza janye idanunsa kan fuskar Rayyern yayinda yake motsa lips ɗinshi a hakali.
Shi kuwaRayyern ido ya ɗan zuba mishi a fakaice yana nazarto abinda ke zuciyarsa .

Gaggaisawa sukayi amutumce kafun daga bisani Alhaji Idi Sale Dakata.
Ya d’an muskuta ya gyara zamansa. kana yace.

“Toh Alhamdulillah domin kusan gabaki d’ayanmu munsan abunda ya taramu da kuma musabbabin had’uwar mu anan wajen.
Idan kuma akwai wanda zance baisani ba saidai wannan yaron wanda yazo yanzu.”
Ya fad’i maganar yana nuna Rayyern da hannu, cikin isa da gadarar dake bayyana cewar akwai wani abunda keyi masa suya a zuciya.

Wanda hakanne kuma yasa Rayyern dago kai, ya soma bin kowannensu da idanu, yana mai karantar labarin dake zuciyoyinsu akan fuskokin su cikin hikima, da kuma haɗawa da ɗan lbransu da ya sani.

Shikuwa Alhaji Idi Sale Dakata ci gaba yayi da cewa.

“kamar dai yanda kuka sani munzauna ananne saboda mu tattauna akan kasuwancin mu, sannan Rayyern kaida baka sani ba kasani, munyi wannan taronne nagamayyan manya-manyan company’s, saboda akwai buk’atar had’a kawunan mu, domin mu gudu tare mu kuma tsira tare bi ma’ana, mu had’e kasuwanci’n wuri guda mu haɗa hannu ta yadda zamu tsara farashin kayan abinci da sauransu a yadda mukeso..”
Ya dire ayar mgnar yana mai kallon.
Alhaji Abdu Tababa dake jinjina kai.

Kai Rayyern ya d’an girgiza tare da maida fuskarsa ya tsuketa waje d’aya, domin lokaci guda ya dawo asalin Rayyern Mai-nasara dinshi, hazikin matashin da bayajin shakka ko tsoron duk wani magauci’nsa ya rigada ya gama saninsu in and out yasan kowa yana da cikekken bayani kan kowansu.
Gyara zamanshi yayi tare da maida bayanshi ya jingina da jikin kujera,
Kana ya ɗan juya kanshi hagu da damanshi.
Muskutawa yayi ya maida kujerar baya kaɗan kana ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya sabida zogin da yaji yatsarsa nayi mishi dan toms ɗin dake ƙafarsan ya takure yatsar da Jannart ta fasa mishi, cikin zuba musu ido ya sauƙe sassanyan numfashi, tare da cewa.
"Kuyi haƙuri".
Yayi mgnar cikin mutuntaka da girmama su.
Cikin haɗe fuska Alhaji Yawale yace.
"A kan me? Me kake nufi da muyi haƙuri? Fito fili kayi mgn yadda zamu gane?".
Numfashin mai nauyi ya fesar sabida, sarawar da kansa ya farayi sabida yadda suke

3 Comments On TUBALI
avatar
khadija-dauda

1 year ago

Reply

Pls inason littafin tubali

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to khadija-dauda

ki karanta anan

avatar
fatima-muhammad-8-7

12 months ago

Reply

Pls ina Sauran chapters din tubali naga wanna chapter 30 ya tsaya kuma bai kai kar she ba

Please Login or Register in order to submit comment