Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su Ya Nazifa tazo jidda ma tazo ya Akila ma haka ya Fatima tazo gidan Baba Sa"idu ma ya cika su Jaleela yan lagos sun sauka jamila ce bata zo ba uwar mijinta ba Lafiya sai Jawahir itama ta iso.
Ana jibi Daurin aure Hidaya matar ya Nazir ta iso Daga Lagos ashashen Hajiya uwa take Sauka Daman in tazo,Ya Nazir sai jibi zai iso tace.
Amaran kuma Kaf dinsu suna Gidan su Ya Jafar chan Hajiya ta roki Baba Mallam ya bari suka tafi Danginta yan Maiduguru sun zo suna chan suna gyaran Amaran sannan Bakin bazanga ma mata sun zo mazan sai Ranar Daurin aure.
Kowa yazo yaga Balarabiya sai yace Daga ina sai ace Amaryan D'anmallan ne Abunda ke bama kowa mamaki yadda Sakina tajata ajiki Ko'ina suna Tare kamar kawaye,Sarood bata da Zabin kanta sai abunda Sakina tace kamar itace jagoranta.
Da su ake ta Hidima gidansu suke kwana ammh kullum suna nan anguwan Danmallam shi kanshi yayi mamakin yadda Sakima ta Saki Lokaci Daya sai da yafi kowa Murna da hakan ganin yadda ta karbi Sarod Hannu Bibbiyu Hajiya bata ce komai ba Domim ita a kan Hurumim D'anmallam Mallam yafi ta karfi ta wannan bangaran.
Amina Bakinciki take in za"ayi taro Saboda yadda kowa ke mai dasu jakai yayi ta sakasu aiki.
Kusan ita da Hamida da Hanne gidansu suke kwana Saboda su ya Zeenatu suma chan suka tare da Amaran yau aka kawo musu Sabbin kayansu da Hijabai Dukansu iri Daya na Amaran ne kadai ya bambamta sai na iyayensu mata.
Yau kwata kwata basu zauna ba sai saasu aiki akeyi,aikin ma na Wahalan Cirema yara pampers ko Ronensu su kuma suna ta aikin yi Cake da Donut da meatpie,suna ta sakawa cikin Takeway wanda za"a raba gobe wajen Walima ga Drinks nan da Ruwa cikin Falon Aba na Hidima da Rabo banda wanda ke chan Gidan Baba Mallam rabawa akayi nan ana Snaks gidan Baba Mallan suna gyaran kayan Miya na abincin da zasu yi su ya Jaleela kuma ana fama da suyan kaji da Nama.
Sakina dai bamai ganinta tana Shashen Anty Amarya ita da Sarood ko aiki batayi ba kuma wanda ya Damu duk da itama chan gidansu akwai Biki Tunda yayanta da suke Uba Daya Sadiyan zata aura.








*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki har inda kike*

_Ya Allah ina rokon ka da ka Saukar da Farinciki,salama da kwanciyar hankali Da Aminci, zaman lafiya Da kaunar juna,sadaukarwa da yarda da,kima da mutumtawa, martabawa agidan auranki *AISHA ALTO* (Sisina) Allah yasa,kin shiga a sa"a Allah yasa gidan zamanki ne na har Abadan Da"iman Ameen_


*🅿️11*

Amina ta gaji da sakasu Reno ya"yan da ake yi ko kuma dawainiyar Cire pampers duk wanda Yarta ko D'anta yayi kuka su ake kwalama Kira su zo suyi Dawaniya Hamida da Hanne basu nuna gajiyawarsu ba sai Amina Domin ta tsani in ana sha"ani a Rika nuna su yara ne basu isa komai.
Dalilin haka yasa taja su hanne suka koma Chan koridon gidan wajen Dakunan da su ya Jafar sukayi zama Tun suna matasa sai ya zamana nan Aba ke sauke yan"uwansa maza in sun zo Daga gusai ko wasu baki dai Dakunan duka akwai Cafet da katifu aciki Wannan karon ma nan yan gusai suka sauka matan mazan sai Ranar Daurin aure zasu taho.
Cikin guda Daya su Amina ke kwana Tunda Dakinsu su ya Jaleela sun zo sun koresu chan gidan baba Mallam ma ko"ina ya cika Tunda kowani Shashe cike da yake da baki Daga Duka bangaran matan kowacce Danginta sunzo Shashen Hajiya ba matsaka Tsinke cike Taf da Danginta na Maiduguri.
Nan Amina ta jasu suna Fira Yawancin Firan Labarin Littafan Hausa ne da Amina ta smu yar"uwan yi suna ta Hiran Zafira D'iya take wajen Aba tunda Babbar diyar goggonsa ce Sa"aninsu Amina ce koma nace kawarsu ce suna Dasawa da ita Saboda indai Mamata mamanta zata zo da ita take zuwa itama ta fara karance karancen Littafansa Hausa shine suka Hade da Amina suna ta Labarinsu Hanne da Hamida Tagumi kawai sukayi suna kallonsu suna mamakinsu.
Amina ce ta kalli Zafira tana Fadin"Kin karanta garin kallon Ruwa...?Labarin Faruq da khaleesat..?

Hannu Zafira ta bata suka Tafa Lokaci Daya tana Fadin"Kai kai..Na karanta wannan Littafin yayi Amina..Salon soyayyar Faruq dabam ce..!
Tare suka saka Dariya Hamida ta tabe baki tana Fadin"Ke Zafira a ina kike samun Littafan nan kina karantawa..?ammh Mamata bata sani ba ko..?
Zafira tace"Anty Aina take dasu..In ta ijiye sai na sata na karanta kuma ina aron wasu a makarantar mu..!
Amina ce tace"Hamida munafuncinki ya baci..To bata Sani ba ko zaki je ki Fadamata ne..?
Hamida tace"Ina Ruwana..?ammh aikwai ranar da Dubu zata cika..Nama fi Tsausayamiki yadda su ya Jafar zasu Bandashenki Domin sai kin Daku Abunda ko Lokacin su ya Jadwa basu yi wannan karance karancen ba Sai ke..!
Amina ta daka wani Tsaki kafin ta Tabe baki tace"In sun kamani kada su bar ni da Rai kin ji Hamida..? Ni fa bana son munafunci malama in kina son Fada musu ai ba sai kin zo kina wani Yadamin mgana ba ke bazan Fasa Karatun ba yanzu na Fara in ma baki je kin Fada ba sunanki ba Hamida .!
Tafada tana kumfar baki ganin Abun na neman zama fada Hamida na Fadin"Da ina son na Fada da Tuni an wuce wajen kema kin sani..! Kawai gaskiya nake Fada miki..!
Amina tace"Munafunci ba..Kin Saba..Hamida ki kyeleni ko?ance ba"a son gaskiyan ko Dole ne..?
Ni bana son sa"ido kowa yaji da kansa mana .!
Hamida zatayi mgana Hanne ta Tareta da Fadin"Kyaleta Hamida..!
Hamida itama ta fara harzuka cikin Daga Murya ta fara fadin"Saboda me .?Saboda ita tafi kowa sai ta rika yadda taga dama ana kyaleta..?ai ba wani abu nace ba Fadan taso kanta nayi mata ina amfanin karatun Littafan da takeyi..!alhalin bata maida hankali a duka karatunta da zai amfaneta watarana..Ammh da anyi mgana sai ace a kyaleta to bazan yi Shuru ba nima yau ina daidai da Jidalinta Wlh..!
Ta karishe Fada tana Hararan Aminar Dake kallonta kamar taga Kashi.
Kafin ta yi Dariyan gefen baki tace"ban fi kowa ba Hamida..Ammh ni Dake ba Daya bane .ke sunanki Hamida ni kuma Amina nake..Ance ba"ason gaskiyan ko ana Dole ne..?ke wai ina ma Ruwanki da Rayuwata ne. ? anki a Tsaya ayi karatun sai me..?har kina Fadin zaki iya da Jidalina na Rantse da Allah baki da wannan Juriyan da zaki iya dani in kuma zaki iya Bismillah..!
Ta Fada Lokaci Daya tana Chakumo Wuyan Hijabin Hamida suka Mike Atare Hamida ta Zuciya zata rikota Hanne da Zafira suka Tareta suna Fadin"Amina saketa..!
Amina na Hararanta tace"Ku gayamaya ta daina Shiga harkata..ana Dole ne nace ta kyaleni ko..?
Hanne tace"taji..Saketa..dafa mutane acikin gida in akaji fa kina ta Daga Murya.
Amina ta Saki Hamida tana Fadin"Aji mana..Sai mene..?
Daga bayansu sukaji ance"Meza"aji din..?
Gabadayansu suka juya suna kallon mai mgana Anty Shamsiya ce matar ya Jafar Tsaye daga Bakin koridon Daga alamu bayi zata shiga Domin ga Buta nan a Hannunta da Katon cikinta agaba tayi wata katuwa ba kyan gani.
Amina Tayi kamar bata ganta ba ta Juyar Dakai Hanne ce tayi saurin cewa"Bafa komai Anty Shamsiya..!
Tana kara nazarinsu tace"Fadan da kuka saba kuke yi ko..?
Da sauri Zafira tace"Wlh ba Fada bane..!
Kai Tsaye tace"To tunda ba Fada bane ku zo ga aiki..Daman tun dazu Jaleela ke nemanku zaku Daukar mata Walid ya hanata aiki Zahra ma sai Cigiyarki take ashe ku gaku anan wajen..!
Amina Sai hararanta take ta kasan ido ita ko Fadi take"oya ku zo ku wuce..Zahra ai ga su Hannatun nan fa...?ana ta nemansu..!
Ta juyatana fada daga Cikin Gida su Hamida sun tafi Amina na wajen taki Tafiya Shamsiya ta kalleta tana Fadin"Ke da kike Tsaye fa?
Amina ta Tura baki cikin kunkuni tace"Kiji da kanki dai da wani katon bakin ki..!
Tana kallonta yasa tace"Badai zagina kike yi ba ko Amina..?
Da Sauri Amina tace"ni..?cewa fa nayi gani nan zuwa..!
Kwafa tayi kafin ta juya tana Fadin"Kada ma kizo..Jaleela gafa Aminar nan taki zuwa kinsan ta batasan aiki..!
Amina ta Mele baki tana Fadin"Ai ni ba Jaka bace..!
Su hamida sun shiga cikin gida yasa ta bisu jin Ya Jaleela sai kwala mata kira take yi tana shiga taga an saka su Hanne Wanke wanke mai uban yawa Daga nan ta Tsaya afili ta Furta"Jaruba..Kamar wasu jakai..!
Bata gama Rufe baki ba aka Rankwasheta asaman kanta Dafe kan tayi tana kallon Ya Jaleela Dake Tsaye kanta Da yaronta Walid a hannunta.
Mika mata shi tayi tana Fadin"Ke da ba Jakar ba..Karbesa ki cire mai pampers ki wanke mai ina ga ya batashi ne kije Dakin mamanmu wajen kayana ki Bude karamin akwati zaki ga kaya da pampers ki Sakamai ki goyasa sai rigima yake min..!
Amina bakinta kamar zai Fado Saboda Takaichi hakanan ta mika hannu ta karbesa yadda take yi ne yasa Jaleelan kallonta tana Fadin"Kada ki kadamin da yaro..Nasan Zafinsa ko bazaki yi bane..?
Amina Dakyar tace"ni fa ban ce bazan yi ba..!
Jaleela tace"Au naga kina neman min kuka ne..?daman baki iya komai ba Mamanmu ta gama bataki..!
Ya Jawahir Dake kusa dasu tana Bare leda tace"Kamar kin sani Allah yasa ta iya ma saka pampers din..?Dama Hamida kika saka ko hannatu.Amina kiyuwarta da son jikinta bai barta ta iya komai ba..!
Jaleela ta kara Dungurinta tana Fadin"Sai kazanta..da Rashin kunya zaki wuce kiyi abunda na sakaki ko sai na mareki..!?
Acikin kunkuninta tace"Ni ba kazama bace.Haka kurum ko da haihuwa ni nayi ta wahala da yara..!
Suna ganin tana mgana Jaleela tace"Me kike cewa ne..!?
Wucewa tayi tana Fadin"Ni ban yi mgana ba..!
Hanne da Hamida suna Duke suna Dariya kwafa tayi ta wuce wajen Bayin waje ta dukar da yaron da bai wuce shekara Daya da rabi ba ta Zare mai ido ganin zai fara kuka tace"Kai kama bakinka..bar ganin idon uwarka Wlh kana min kuka sai na Dirkeka..!
Tafada tana Zaremai ido kamar yasani sai yayi Shuru kwafa tayi tana Fadin"Shegen yaro mai kama da Ubansa..!
Tana Ciremai pampers din tana Ta Mai masifa ubansa ya sha Zagi harda uwar ma,Amina Fadi take""Kun iya haihuwa..ammh bakusan yadda zaku reni ya"yanku ba Amina ai ba Jaka bace..!
Inda Allah ya taimaka Fitsari kadai yayi aciki a Bola ta watsashi Tana Fadin"Allah yaso ka..Da kayi kashi Wlh bazan wanke maka ba..Sai da na Sake nadeka dashi..!
Ko Tsarki batamai ba Ta Daukeshi Fuu Sai Dakin mamanmu Dayake suna ta aiki ba wanda ya Lura da ita Tana shiga ta Dungurar dashi a kasan Cafet ba kowa afalon Yasa ta Zare mai ido tana Fadin"Kai zauna anan..In ka sake ka tashi sai nayi wuji wuji Dakai..!
Gwanin Tsausayi haka ya koma ya Zauna yana so yayi kuka Lekowa tayi taga hankalin kowa baya kanta ta bar Walid chan ta sababo wajensu Hamida Daidai kunnenta tace"Ku taso mu gudu..!
Hamida ta kalleta dasu Hanne da Sauri tace"Wannan uban wanke wanke yaushe zaku gama..?ai biki suka zo su yi aikinsu ne nidai kunga tafiyata in kuna son kuyi ta aiki ku zauna..!
Tafada tana wucewa ba wanda ya Lura dasu domin yammah ta Farayi suna ta aikinsu.
Zafira ce ta fara tashi tana Sake Hijabinta Data Daure Lokaci Daya tana Fadin"Amina jirani muje..!
Daman ita ke wankewa Hanne da Hamida na Daurayewa ganin sun wuce yasa Hanne ta kalli Hamida tana Fadin'"Mu bisu Hamida in muka Tsaya Laifin duka zai shafemu..!
Ba musu suka Tsame hannunsu Daman da Hijabansu ajikinsu,Su Amina sun riga sun fita daga Tsakar gidan su Hanne Jawahir ta Hanga da Sauri ta fara kiransu"Kai ina zaku kuma..?kun gama aikin ne..?
Ai ina kafa mai naci ban baki ba su Amina Dake jiransu ganin suda gudu yasa suma suka Ruga Jaawahir ta saka Salati tana Fadin"Yaran nan basu da mutumci sunbar aikin sun gudu..!
Zahra ce ta jita tace"Amina ce zata ce su gudu..ammh Hamida da Hanne basu da kiyuya.!
Jawahir tace"Amina na Dakin Mamanmu tare da Walid..!
Bata rufe baki ba Mamanmu ta Fito da Walid a hannunta tana Fadin"Jaleela garin yaya ki bar walid a daki shi kadai sai faman yanka ihu yake..?
Zahra suka kalli juna da Jawahir kafin Tace"Daman na Fadamiki..!
Jaleela nachan suna aiki Saka Abu a Takeaway aka mika mata Walid ta karba Tana Fadin"Sai naci uban Amina Wlh..!
Zahra tace"Inda kika ganta ba..ai sai ma kin ganta sannan kici uban nata..!
Gabadaya Dariya aka saka ana Fadin Halin Amina sai Allah ya Shirya.

Su basu tsaya ba sai da suka fita Daga gidan sannan suka Tsaya suna Haki Hanne tace"Ya Jawahir ta kamamu tana ta kiranmu muka gudu..!
Amina tayi Dariya tace"da kun tsaya..!
Tafada daidai Lokacin da sukaji Hayaniya suna juyawa suka ga ashe Karatun Baba Mallan ne aka tashi Maza sun fara fitowa daga masallaci.
Hamida ta zaro ido tana Fadin"Mu shige gidan Baba malman gasu ya Jafar nan sun fito masallaci kunsan in ya gammu a waje sai yayi mana mgana..!
Amina tace"mu tafi gidan su ya jafar inda su ya zulaiha suke muga abunda suke achan..!
Dukkamsu sukayi Shiru suna kallon Amina kafin tace"Dilla mu bi ta nan baya bamai ganinmu..!.
Jin haka yasa suka yarda nan da nan suka Zagaya suka bi ta baya suka fara Tafiya akuyan Daure ta samu Sake sun san gidan Dayake ba wani Nisa Sosai a kasa sukaje sai gasu abakin get din gidan Amina ta fara buga get din gam gam..gam gam.kamar zata Fasa kofar
Daga chan sukaji Muryan Abida tana Fadin"Waye haka..?ana zuwa kada ya balla get din..!
Ido suka gwalo sun san Halinta kafin suyi mgana ta Bude get din Tana kallonsu tasha kunshi ja hannu da Kafa Hararansu ta farayi Daya bayan Daya kafin tace"Daman Araina sai da naji kune..To kuma uban me kuka zo yi..?ko nan da sa"anninku ne..?
Amina tayi Saurin cewa"Mufa mun zo muga amare ne..!
Abida ta ballaa mata Harara kafin tace"ku musu mene..?kaji min yara da iyayi to bAzaku shiga ba ku juya ku koma..nasan ba wanda yasan kun fito Daga gida..!
Hanne tace"Muna ganinsu zamu tafi ko Amina..?
Da Sauri Amina tace"Eh Wlh..muma kinga basai amana irin kunshinki ba..ko Hamida..!
Gabadayan su suka amsa Domin su ba wanda yabi ta kansu ma mganar kunshi gwara Hanne da Hamida suna ma kansu Amina kuwa sai dai in Mamanmu ce ta kamata ta kunsa mata.
Abida ta Daure Fuska Kafin tace"To wlh bazaki shiga ba irin lalle na ko..?ni sa"arku ce..?kuna yara da ku sai son shiga cikin manya dillah ku wuce ku bama mutane waje..!
Amina ta tura baki kafin tace"To mu leka..!?
Abida tace"To leka..!.
Da Sauri Amina ta Zura kai ta wajen Hannun Abida Data Bake get din zata Leka taji ta Daketa abaya Dayasa ta Dawo da kanta da Sauri Abida tace"Matsa ku bani waje..Marasa kunya kawai ba sa"anku anan..!
Tana gama Fadin haka ta fara kokarin maida get din Amina ta kalleta tana sosa inda ta Daketa da karfi tace"Dadin abun ai ke ba Amaryan bace Ehe..!
Tana gama Fadin haka ta Zura da gudu su Hanne suka mara mata baya Abida ta saki baki tana kallonsu afili ta Furta"Yaran nan sun bala"in Raina ni..!
Kan bala"i zamu hadu ne duk sai kun ci ubanku..!
Tafada kafin ta maida get din ta Rufe suna Shashen ya jafar ne suna ta Hayaniya amaran Dayake Duka yan"uwan Hajiya daga Maiguduru ne sukayi musu Lalle da Kitso da kuma gyaran jiki nan suke kwana Anty Shamsiya yau chan gida zasu kwana ita da Fadila.
Daganan da suka fito sai da suka kusa gida suka Daina gudu suka Duka suna Hutawa Amina ta Dago tana Haki tace"Ya Abidar nan muguwar yar bakin ciki ce..!
Ta hanamu shiga mu gani ance ana ta mu su gyaran Amare..!
Hanne tace"Eh su yakura ne fa suma tun ranar da sukazo hajiya ta turosu nan..!
Amina tace"Ai dai zamu gansu gobe duk Tsiyanta nifa daman tunda naji muryanta nasan sai ta bamu mtsala..!
Zafira tace"bata da kirki ne..?
Amina ce"Ko kadan..Bata da mutumci ya Abida kina ganinta haka..!
Gabadayansu dariya suka saka Amina ta Cigaba da Fadin"Ke kinga gidansu Hanne..?Kaf ba mai mutumci yasin..!
Hamida tace"Kai Amina ga ya D'anmalam ai bai taba Dukanmu ba..!
Amina tayi jim kafin tace"Shi kuma wannan dama dukan yake yi da Mganarsa..!
Hanne da Hamida suka Kalli juna suna Danne Dariya Amina ta gansu ta Hararesu tana Fadin"Munafukai..!
Zafira tace"Me ya faru ki bani labari..?
Da Sauri Amina tace"Wlh kuka Fada mata sai nayi muku Rashin Mutumci..!
Dariya suka kara saka mata ta kwalo musu ido Zafira na magiyan su Fada mata Amina ta Faki idonsu tace"Wayyo bayanku maciji..!
Ai bata gama Rufe baki ba suka Zura aguje tabi bayansu tana Dariya.
Allah ya taimakesu sanda suka Dawo an shiga Sallar mangariba sai suka Lallaba suka Shige gidan Baba Malam.
Shashen Hajiya ba waje duk ya cika duk da wasu suna Kitchen din gidan suna ta soyan kaji su da su Baba Lami yan aikin gidan.
Karsahenta dai Shashen Hajiya uwa suka Shige sukayi salla adakinta ita bata ma nan tana Shashen Hajiya taje suna mgana..
Sallar kadai sukayi suka Fito su leka chan su leka chan har shashen Anty Amarya sai da Amina tace suje saboda tana son ta kara ganin gulma
Akwai suna shiga suka iske Sakina da Sarood zaune kugu Daya Jidda na Kan Cafet tana ta Hada Turaran wuta da Sabulun Salo cikin wasu kananun Robobi ita da wasu Daga cikin Dangin Anty Amarya..basu ga Sa"adatu ba bata nan tatafi kunshi an samu Sake.
Hanne ne kadai da Hamida suka gaida su Sakina banda Amina Data yi keme keme Anty Amaryan bata Falon.
Anty Sarood ta ganesu tana ta yi musu Mirmishi.
Sakina taga Amina na wani kallonsu Daya Daya yasa tace"Ke..Baki da kunya ko..?
Baki iya gaisuwa bane..?
Amina ta yamutsa Fuska kafin tace"Na gaisheku..!
Sakina tace"Karya kike..Hanne kadai da Hamida suka gaishemu da wannan yarinyar..!
Ta fada tana nuna Zafira.
Amina ta Tura baki batayi mgana ba Jidda ta dago tana kallonta Kafin tace"Wai Amina daman baki daina wannan Rashin ta idon ba ko..?ko ni ai baki gaisheni ba..?
Amina ta yi wani jim kafin tace"Ina yininku..!
Daga haka ta juya tana Jan hannun ZAafira Dake kusa da ita.
Sakina ta rike baki kafin tace"'Yarinyar nan bata da kunya..!
Amina na kunkuni tace"Eh din ai na gaisheki tunda kuma ba Duka miki zan yi ba..!
Da karfi tayi suna ji ta fice Jidda ta girgiza kai tana Fadin"Kamar ba yar gidan Baba Sa"iduba kaf ya"yan gidanan ta fita zakka..Allah ya shirya..!
Sakina batayi mgana ba baki kawai ta Tabe ta juya tana ma Sarood mgana Wacce ta maida hankalinta Sakina na jin Labaraci tun anan balle kuma Da suka koma chan Zama da Larabawan yasa yaran ya zauna mata sosai.
Kitchen suka shiga suna neman abinci sun samu Jallop din shibkafa da aka Dafa da Rana.
Amina idonta na kan manya manyan Baho cike da Naman kaza da Naman rago duk am soya Amina da nama Tuni Ranta ya biya.
Akitchen din sukaci abinci suna cikin ci Amina tayi ma Hanne Rada"Yasin sai na saci naman chan..!
Hanne tace"In aka kamamu fa..!
Amina tace"Dillah bamai ganinmu..!
Har suka gama cin abinci Amina na Tunanim mafita Su baba Lami na Kitchen da sauran mutane suna ta aiki kowa Hankalinsu baya kansu Anty Nasara ce ta shigo ta gansu yasa tace"Me kukeyi a kitchen..?
Kuje waje mana ku sha iska..!
Dole suka fice Hanne nama Amina Dariya ita kuma tayi Fuska
Shashen Hajiya suka koma suka samu chan gefe suka zauna bama wanda ya Lura dasu Amina aranta tana Takaichun yadda in ana sha"ani bamai bi ta kansu aranta tace ai suma sun girma sun wuce yara yanzu.
Suna nan har akayi sallar Isha"i suka tashi sukayi salla.
Sai alokacim Hajiya ta gansu tace"kuna nan ashe..?na zata kuna gidan Sa"idu ne..!
Hanne tace"Tun dazu muna nan..!
Tana Sauri ne ana mata mgana yasa ta wucesu Amina tace"Kowa baya bi ta kanmu..!
Hamida tace"Wlh fa kallemu kamar wasu almajirai..!
Amina tayi dariya kafin tace"Almajiran ne mana duk inda mukaje ana koranmu..!
Hanne ce ta ma Amina Rada a kunne tana Fadin"Kin fasa satan naman ne..?
Amina tace"A"a
Ku tashi muje..!
Haka suka sake ficewa Kitchen din Amina ta leka taga ba kowa sai su Baba lami su kuma suna ta Hidiman yanka Albasa suna Hira Amina ta yafito hanne tana Fadin"Ku tafi daga chan..Ni zan shiga na Debo mana zan taho..!
Hanne ta mika mata wata bakar Leda Data Dauko daga Dakin Hajiya tace"Zubo mana anan..!
Zafira ce tazo zatayi mgana Amina ta mata alaman tayi shuru Hanne ta mata rada tana fadin"Ke nama Amina zata sato mana..!
Zafira tace"Yauwa daman wlh tun dazu miyauna ya tsinke..!
Amina ta Sadada ta shiga kitchen din ta Duka ta Bude ledan ne ta rika Zuba Nama Har sai da ta Kusa Cika Hanne da Zafira suna daga bakin kitchen din suka hango Anty Amarya zuwa da Sauri Hanne tace"Amina Ga Anty Amarya nan ki taso..!
Jin haka yasa ta taso da gudu su kuma sun riga sun ruga har tana bangaje Anty Amarya,Da tayi baya tana Fadin"Ke ke..Waye anan..!
Ina Amina bata tsaya ba sai Aharaban gidan inda su Hanne ke jiransu Anty Amarya bata ga Fuskar Amina ba.
Ta shiga kitchen tana yi ma su Lami Fadan suna barin yara na Shigowa.
Haraban gidan akwai haske tunda an kunna Gen yasa Amina ta jasu suka shige wani dan lungu Dake Wajen kofar Shiga Shashen mallan da dan Duhu kadan suka ZAuna Amina ta Fito da Naman Hamida ta zaro ido tace"Amina kin Debo da yawa in aka gane fa..?
Amina ta tura wani nama bakinta Tunda naman sa ta Debo na kajin suna kusa da Baba lami yau gidan Gonar Baba malam yasha Diban kaji da Shanaye.
Sai da ta cika bakinta sannan tace"Dillah kefa kin cika tsoro..Abu da yawa wazai gane..?
Zafira ta mika hannu zata Diba Amina ta make hannunta tana Fadin"Kada ki samin hannu ko na Hanaki wlh..!
Jin haka yasa ta Dakata Amina ta Dauki Tsoka Hudu hudu ta basu Ta bama Hanne Biyar ta Dauki Sauran tana Fadin"Mai sata ke da wannan..!
Hamida tace"Kai Amina naki yafi yawa..
Amina ta balla mata Harara tana Fadin"To Sarkin korafi..Dayake ke kika je kika Debo naman..!
To wannan ma in baki so bani kayana..!
Tafada tana mika mata hannu Hanne tayi Saurin cewa"Hamida karbi abunki..Mun ji Amina tunda ke kika Debo Dauki wannan..!.
Amina ta murguda baki kafin tace"ko baku yarda bama..In mutum yaji Haushi yaje ya Debo nasa. !
Hamida tasan da ita take yi ammh bata tankata ba suna cin namansu Zafira ke fadin"Wai shanaye nawa aka yanka da kaji..!
Duk gidajen nan fa akwai Nama ko"ina ka shiga. !.
Amina tace"Waya sani Zafira..?kila sun kai dubu kajin Shanayen kuma kila goma..!
Tafada tana Tura naman bakinta Hamida tace"Haba inaga ma sun fi..Kinsan in ana Biki haka ake ta Yankosu ana shigowa dasu..!
Zafira tace'Cab...ai gidan Gonar ta kare..!
Amina tace"Ke..kina da Hankali kuwa..?Kinsan adadin Dabbobin Dake gidan gonar nan ta baba malam..?
Ke babban waje ne fa na taba gani a Wayar Ya jafar da yazo yana nuna ma su Mamanmu na rantse da wanda Raina ke hannunsa gari guda ne..!
Hanne ta karbe da cewa"To yaushe zamu je mu gani..?bamu taba zuwa ba..?
Amina tace"Kuma fa hakane..?to ammh Aba chan yake zama fa..?ya zamu yi mu je chan Hadeja Road ne fa..?
Hamida tace"Nidai ba ruwana..!
Amina tace"Sai me..?ke dai kin cika Tsoro..Hanne bari nayi shawara na Rantse koda bala'i sai mun je mun gani ko da zamu dawo a yankamu ne..!
Hanne tace"A"a fa ni wasa nakeyi..!
Amina tace"Ke fa sai an je..Inaga ma gobe saboda bama wanda ya Damu damu..!
Hanne zatayi mgana kenan sukaji mgana a kofar Falon Baba maallam gabadayansu suka Leka suna ganin Ya Uzairu ne ya fito Daga Falon mallam din Bayansa ya Shamsu ne sun saka Takalmansu sun nufi barayin da Dakumansu suke
Amina ta juyo tana Fadin"Jaruba..Daman ya Uzairu ya Dawo ne..?
Hanne tace"Eh mana tare suka zo da Ya Zulfa..!
Amina tace"Harda Ya Nazem..?
Wannan karon Hamida ce tace"A"a shi naji Ya Zahra na fadin sai gobe yace zai taho yana da Karatu gobe..!
Amina tace"Mugayen gidan.com zasu Taru Lokaci Daya bala"i..!
Hanne tana Danne Dariyanta take Fadin"Har na tuna ya Nazeem sanda ya miki Dukan Tsiya Lokacin muna aji hudu kin Tuna. ?
Amina tace"Kan bala"i ina zan mata..Ranar ai mariya na Tsungula ya kamani Shine ya fitar dani gaban aji kusan awa daya nasha ya manta dani ne na Daga Murya nace Tattasan da ka shanya ya isa Bushewa sai kazo ka kwashe..!
Gabadayansu suka saka Dariya Hamida tace"Kin ga kwashewa kuwa..Amina kin Daku fa hannu. Ya Nazeem..!
Amina ta Ciji yatsa Kafin tace"Kuma Wlh har yanzu ban yafe ba Wuta bal bal har kabarinsa..!

"kai su waye anan..?

Mganarta ta Katse ne sanda aka Dallaresu da Filita Lokaci Daya da mgana suka Tsorata gabadayansu sukayi Tsumu Tsumi.
Ya Uzairu ne zai fita shago ya Siyo katu yaji mgana daga bayan shine ya Haskasu da wayarsa.
Karisawa yayi gabansu yana kallonsu Daya bayan Daya ya ganesu mamaki ya

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment